EHSAAS

Chapter 8

by @fatoumspassion

(Special girl)

Pcap yasaka da dark shades yana fitowa daga cikin jirgin saboda baya da bukatar wani ya ganeshi acikin filin jirgin kodan tsaron lafiyarsa,anitse yake tafiya harya karaso bakin kofar daze fito daga cikin airport din dedenan ya hangota abayan wata arniyar Rolls Royce,suna ficewa daga Airport din driving dinta akeyi aransa yaraya she must be from a very rich family.

wayarsa yaciro ya tura text message cikin kankanin lokaci ya iso,dawata Lamborghini dinsa yay parking gaban EHSAAS yayi mamakin gane shin dayay tafaraddaya. yafito cikeda farinciki yana fadin "uncle prince is back oyoyo" yarungumeshi, EHSAAS yamutsa fuska yay yana fadin "kasan fa banason wannan iyayin ko, let go of me," Sakinshi Aman yay yana kumshe dariyarsa don daman duk sanda ya rungumeshi se sunyi rigima waishi bayason kato yana rungumeshi, yakalleshi yana fadin "waya barka kafara tuki dakan ka? dan bude ido yay yana fadin "uncle I'm eighteen karka manta bana zanshiga jami'a," dan murmushi EHSAAS yay shi ala dole babban nan yace "that's nice" bude mishi gaban motar yay yashiga yana fadin "can't wait inga irin tukuicin da granny zata bani na kamo mata babban kifi," murmushi yay yana fadin "nine kifin ma kenan," dariya yay cikin harshen larabci yake fadin "afwan Ammi," tambayarsa ya mutanen gidan yafarayi nan yafara bashi labarin abubuwan dake faruwa a NURISTAN din tun bayan kin dowawarsa daga saudi har wayau, da yadda kawu Erfan wanda yake matsayin waziri ayanzun yadau abin da zafi yace mai martaba bayason danshi ya auri yarsa ne shiyasa suka hanashi dawowa,yace "wllh uncle yar tashi fa chuka ce tana da kyau don kyau amman babu kamun kai, ba kyan Hali, shiyasa haryanzun kaga sa'ar haihuwar kace amman batai aureba da sunan jiranka takeyi wai," " hmmmmm" kawai yace donshi kanshi yasan ko zabi aka bashi baze taba auren maisoon dinba duk da ko afuska baze ce gataba amman gulmar da Aman ke kawo mai akanta yasa yaji ita din ba kalar macen da yakeso yamayar uwar yayanshi baceba. haka kawai yatsinci kansa da tinawa da ita,yakalli Aman yana fadin "wai daman a NURISTAN akwai Christians?" Aman kallonshi yay yana fadin "laaaa uncle baka saniba da dama ma kuwa amman basu kaimu yawa ba,kwanan nan nema suke dada karfi sakamakon wani shegen pastor daya gagari al'umma waifa har da'awar arnancin yakebi kauye kauye yanayi,yanada daurin gindi daga kasashen duniya ne,mai Martaba yakulla masa kwana biyunnan," yace "Pastor kuma a NURISTAN din?" yace "kaidai bari ai NURISTAN tazama abinda tazama zamani kenan,kasan haramunne zaman pastor a NURISTAN shine yabuge dacewa waishi ba pastor bane, elder suke cemai don tsabar munafunci kaji sunansa yauwa Abraham Zion,ingaka mutumin kai kanka se kayi mamaki baida wasu shekaru amman ya iya tsara zance tiryan tiryan kamar wani dan jarida don inyayi wuta guy din yay 40 yrs sbd yanada mugun kudi,kudi kuma mazaje don gidansa ance yakusa rabin palace," yace "kudi kuma wa yake bashi?" yace "nema yake amman dai makarantar dayake running for almost ten years bazata bashi kudinnan dayake fantama wa dasuba kuma rabawa mutane yake kamar besan ciwan suba hakanne yasa yake jawo ra'ayinsu da abin duniya suketa binsa ita kanta private university din tashi mai martaba yana zargin yana yada ilimin addinin sane aciki bawai western education ba,sannan bawa yayan talakawa scholarship yake kamar banza shiyasa ZION uni din take neman karawa da federal uni ta NURISTAN" jinjina kai kawai EHSAAS yay yana fadin "Allah yakyauta." Aman so yake yacigaba da mai hira amman tunda yaji yace Allah yakyauta that means he is not interested,hakanne yasa yaja bakinsa yay kus harsuka karaso palace din ta karamin gate Aman yawuce dashi straight zuwa sashen Fulani. cikin kankanin lokaci akai musu iso ba'a gaya mata EHSAAS bane jin ance Aman yasa aka barsa yashiga don Aman mutuminta ne duk da basa shiri da kakarsa mai babban daki Aman ba ruwanshi yana daukar fulani tamkar kakarsa ta asali in kaji yana tsokanarta yana cemata fulani kasa Fulani sama,tana zaune ta kashingida saman kilishi jakadiyyar ta na dan mammatsa mata kafarta tajiwo kamshin turarenshi,turaren yazama signature dinshi duk inda ya gifta seka jishi tadauka ko hancin tane takalli jakadiyya itama data shiga dube dube daidai nan suka jiyo sallamar Aman. tsayinsa yasa Aman yakasa boyeshi abayansa kamar yajja yay intending Fulani tsabar farin ciki hannayenta tasa saman bakinta tana girgiza kanta takasa gasgata EHSAAS ne agabanta, Aman yace "yaudai se kin bani tukuici nakawo miki babban kifi har cikin dakinki" yamatsa agaban EHSAAS ya bayyana dukkanshi agabanta, zubewa jakadiyya tai cikeda murna take fadin "Allah ya temaki yarima Allah yaja daran yarima barka da dawowa,magajin mai martaba dan zaki...." daga mata hannun da EHSAAS yay yasa ta dakata da kirarin datake kokarin shiga yimai don neman samun gurin shiga, da hannu yay mata alama tafita dagudu tafice don ya kasance ita tafara kai wannan daddadan labarin.

tsugunnawa yay yana kallon mahaifiyarsa da kwallar farinciki ke fitowa a idonta cikeda soyayya da shakuwar dake tsakaninsu yariko hannayenta yasa acikin nashi yana fadin "maamaa" cikeda shagwaba wanda da yakeyi duk girmansa agaban mahaifiyarsa, rungumeshi tana fadin "babana kaine nake gani ko mafarkin dana sabane," Don taka cemishi babanta saboda sunan sirikinta mai Martaba EHSAAS nafarko dayake dashi "shshsshsshs" yafada yana shafa kanta "nine maama EHSAAS dinki yazo ya ganki" dariya kuma tashiga yi tana kankameshi take fadin "nayi kewarka abin kaunata,dana farincikina,dana sanyin idaniya,dana kaine rayuwata" saboda Fulani na matukar kaunar EHSAAS idan ita da shine takan gwada mishi kaunar da bamai yimasa ita aduniya tanada kunya da kara amman hakan baya hanata nunawa danta kulawa da soyayya shiyasa batai saken sakarma wata shi acikin gidanba kamar yajja wasu matan sarkin ke yiwa yayansu. Abainar jama'a zakaga kamar basu wani shaku da junaba amman azahiri shakuwar dake tsakaninsu yamafi karfin shakuwa sede ka kirasu da hanta da jini. Aman kallonsu yake cike da soyayya yake fadin "granny tawa, kinga danki kinmanta da dan jikallan naki koh," murmushi tai masa tana mikamai hannu alamar shima yataho ta hadasu ta rungumesu tanata sa musu albarka kafin ta sakesu tana kallon EHSAAS tasoma shafa gefen fuskarsa, "Habibi kanajin yunwa koh? kaci abinci? tashi Kai wanka zandafa maka abinci da hannuwana yanzunnan" dan kallonta yay yajja tamike tana kokarin nufar dakin ta dashi ya sanya yadan sosa keya yana fadin "maama bari naje sashena nai wankan idan nafito zandawo nan inci abincin," dan shiru tai before tace "kayi anan kawai kahuta adakina," kallonta yay yana kasa dakanshi tasan sarai kunyarta yakeji baze iya wanka a toilet dintaba yasanya tace "tohm ai shikenan in anyi abincin in aiko maka ko kuma kazo kawai" yace "zanzo habibty na ai bangaji da ganinki ba kuma bazan taba agajiya da ganinki ba mamana abar kaunata," murmushi irin na girmannan Fulani ta shigayi tana fadin "Allah yay maka albarka dana" kissing hannayenta yay duka biyun yana mikewa yana waiwayowa yana mata murmushi har suka fice zuwa sashensa da Aman mamakine ya kamani lokacin danaga fuskarsa tahadu tahade lokacin daya fito kamar be taba dariya ba duk inda yay bayi se zubewa suke suna mika gaisuwa hannu kawai yake daga musu don baida energy amsawa harya karasa babban sashen sa dakenan gari guda wanda yake daf da unguwar mai babban daki, already kafin yazo Aman yasaka amintattun bayinsa sun gyara masa ko ina fes fes dashi se kamshi ne yake tashi yashige abinsa yana rufo kofa Aman yabi kofar da kallo yana fadin "uncle yau ko falon baza abarni nashiga ba," ko sauraronshi be tsaya yiba yakarasa babban bedroom dinshi dayaji kayan alatu na asalin sarautar NURISTAN harta shikansa gadonshi abin kallone don da asalin danyar gwal akai crown din,komai na dakin abin kallo ne yashiga bathroom din ya sakarma kanshi ruwa mai sanyi.

Daga bangaren mai babban daki jin labarin yarima ya dawo beje ko bangaren mai martaba ya gaishesa ba balle akaiga ita, uwarsa kawai yasani yasa ta fusata tana ganin ai itace babba agidan kamata yay ace itace zefara zuwa ya gaisar kafin Fulani ma, hakan yasa taketa cika tana batsewa takasa hakuri kawai tamike daman yau itace da turakar mai martaba kuma tasan in yadawo daga sallar la'asar baya zama afada bangarensa yake tafiya yadan huta harse lokacin sallar magrib yake fitowa. straight can tai akamata iso tsabar gulma nacinta tamanta cewama yana barci ta banka tashige turakar sa,motsin dayaji yafarkar dashi daga barcin da dama be wani yi nisaba don tunda Allah yadaura mishi nauyin mulkin NURISTAN awiyarsa barci lafiyayye ya kauracema idon shi sedai barawo kallonta yatsaya yi yajja tashigo masan yadan sosa masa rai cikeda nutsuwa da dattaku yadan tashi zaune yana kallonta gefensa takarasa tana fadin "allah yajada ran mai martaba aimin afuwa nashigo batareda izni ba," dan lumshe idanuwansa yay cikeda nutsuwa yace "inajinki Asiya? kasa tai dakanta dan duk gigin ka mai martaba NASHWAN kwarjini ne dashi natashin hankali,tace "daman nazone in tambaye ka shin rashin mahimmanci na har yakai haka?" mai Martaba kallonta yake tasan kuma ba tanka mata zeyiba alamar ta cigaba da zancen tane hakan dayay,ta daura da "nadauka yayanka suma yayana amman yanzun ace yaronnan EHSAAS zedawo garinnan aka rasa wanda ze sanar dani,sannan tunda yadawo uwarshi ta sakaya shi a turakarta bansan mesuke kullawa ba yafito yaki zuwa ya gaisheda koda uwar soro yay shigewarsa bangarensa ance se hade rai yake kmr an aiko mai da mala'ikan mutuwa,yanzun ammin adalci kenan idan yata mimah tazo kasarnan banajin tataba zuwa straight tagaisheni gurinka take fara zuwa taje gun ita fulanin sannan taje ta gaida hasana seta dawo gurina nataba cira kai nayi magana amman shi akomai seya nuna mu bamu muka haifeshi ba,kuma....." mai martaba jin zancen nata duk kananun magana ne irin namata yasanya yadaga mata hannayensa duk biyun alamar ya isheshi haka tazuba mai ido cikeda bakinciki tai kasa dakanta yace "daman abinda yakawo ki kenan?" tajinjina kai tana kokarin share kwallar takaicin gwaleta dayay daman tasan zance kowana irine indai akan fulani da dantane baji yakeba se anyi sa'a rashin daukar maganar nabata mamaki yace "zaki iya tashi kifita kawai" yana nuna mata kofa ba damar tamusa masa hakanne yasa tamike jikinta asanyaye tai waje tana tinanin shikenan kuma EHSAAS yadawo ita tashiga uku yanzun za'aita nuna mata cewar ita ba kowa bace acikin gidannan," huci takeyi sosai akofar bangaren suka hadu da jay yakafa wani shegen bakin glass ze shiga kullum ta ganshi se taga kamar karamai kyau da haske akeyi kodan beyi aure bane har yanzun itakam jay na matukar burgeta sosai don dan gayune na ajin karshe ga ilimi ga nutsuwa ta kin karawa dan risinawa yay ganinta ya gaisheta tai murmushi tana fadin "jalal shigowarka kenan," yadan jinjina kai tace "galadima guda amman ba'a ganinku se anzo gurin mai Martaba" dan murmusawa yay yana fadin "tohm meze hadamu da sha'anin mata" "hmmmmm" kawai tafada tabishi da ido harta dena ganinsa tai kwafa kawai tana fadin "allah yakai damo ga harawa."

Kasa hakuri tai tahau motar da tazo da ita aka tukata zuwa unguwar Fulani Hajar don tanason tai mata tass akan kin aiko EHSAAS ya gaisheta tararwa tai fulani tabada sakon baza taga kowaba harse bayan magariba.

"kiri kiri shegun masu gadinnan masu kama da samudawa suka hanani shiga" tashiga bawa sarauniya hassana labari lokacin data karasa bangarenta,tace "Allah ya temakeki aikema da bikije ba bagirman ki bane keda za'a zo har daki agaidake sekece xakije kenan ma sunyi nasara akanki," mai babban daki tace "hassana kinada gaskiya gani nai cin fuskar yasoma yawa don taga ta haifi da namiji take jin kanta kamar wata star tafi kowace mace daraja agidannan tana fama dawata kodaddiyar fatarta," hassana shiru tai kawai don tasan hassada ce kecin mai babban dakin domin ko makaho yashafa fatar Fulani baze taba kiranta da kodaddiya ba.

EHSAAS bayan yafito daga wanka ko abincin bebi takanshi ba yabi lafiyar gado lafiyayyan barci yakwasa sau uku Fulani na aiko Aman dubashi yana cewa barci yake har seda akai sallar magrib ta saka atasoshi sabon wanka yafesa yadauro alwala yafito,yashafe jikinshi da hadaddun mayukanshi, yafeshe jikinsa da turarrukan designer's masu daddadan kamshi, kayansa na zaman gidan NURISTAN yasako wasu irin kayane na gargajiya da kai musu adoh nagaske kana gani kasan sunsha kudi yakafa crown dinshi da yakenan kamar turban yana zira zobunan gwala gwalanshi,sukansu kayan adon jikinsu zallar duwatsun gold ne musamman alkyabbar dake saman kayan,sosai yaji kayan sunmai nauyi ajiki amman yasan sakasun musamman a fitowarsa ta farko cikin jama'a ranar daya dawo yazama farilla ne agareshi kuma yasan hakan zesa mahaifinsa farinciki yana fitowa ya tararda Aman yanata buga video game,mikewa yay yana kashewa yabi bayanshi don yasan EHSAAS baya jira.

Aman ne yabude masa gaban motar yashiga ya zagaya yazauna amazaunin driver suka karasa babban mosque din kamsussalawat da yake farkon shigowa palace din daf da za'a tada sallar yakaraso,mutane nata zubewa suna gaisheshi awajen hakan ne yajawo hankalin mai martaba dake sahun gaba tareda babban limaminsu suka ankare da zuwan nashi,be wani jima awajen ba ya karaso aka matsa mishi hanya har zuwa inda mai martaba yake,tsugunnawa yay gaban mai martaba cikeda girmamawa yana gaisheshi kamar dai yajja yasaba dafa kanshi mai martaba yay yanajin sanyin ganin dan nashi tilo amman kai baka isa ka karanci abinda yake cikin ranshin ba don fuskarsa babu emotions kwata kwata. Amsawa kawai yay kafin yakalli waziri dake gefenshi da idanuwa yay masa magana kawai yamike yana sanarwa da malam liman yau yarima ne ze jasu sbd mai martaba na matukar jin dadi in yaga EHSAAS na limanci yana karatu cikin wannan zazzakar kira'ar tashi,lokaci nayi suka mike suka jeru asahun gaba liman yanuna mai inda yake gurinshi ada yana fadin "bismillah yarima" yana ganin haka yasan shirin mai martaba ne ba damar musawa ya karasa cikeda nutsuwa yafara iqama ako ina kake a palace din NURISTAN kana iya jiyo daddadar muryar EHSAAS ta speakers din mosque din dasuka kewaye ko ina na masarautar kuma hakanne yasanarwa da da yawan jama'ar ma da basusan da dawowarsa ba sanin yarima yashigo gari don muryarsa da karatun sa basa buya. zukatan wasu irin su Fulani fess take tana jin farinciki da alfaharin kasancewar sa danta wasu kuma gembone yay musu katutu azuciya da sukeji shikansa karatun EHSAAS din tamkar wutar dalma ake zuba musu acikin zuciya.

Bayan an idar da sallah a masallaci yazauna gefen mahaifinsa inda manyan mutane ke daukar karatu agurinshi da gun liman,shima joining dinsu yay yana koyarda wasu daga cikinsu wadan dama zasu yi jika dashi,harseda lokacin isha'ee yay shima EHSAAS dinne yajasu sallar suna idarwa bayan yagama azkhar yamike yabi bayan mai martaba ganin yafice shima dukda yunwar da yakeji amman yasan be isa yace ze koma unguwar fulani yanzun ba don dole yaje yakai gaisuwa fada don haka har fada yaywa mai martaba rakiya anan nema yasamu gaisawa da manya manyan hadiman mahaifinsa da masu sarautar garin NURISTAN irinsu wambai,waziri,galadima da dai sauransu,bayan yakai gaisuwar daman yasan ba wata hirar kirki mai Martaba keyi afada ba yamike wajen karfe tara yace masa shi ze wuce izni aka bashi yafito Aman dake mota yana jiransa dariya yafara mai yana tsokanarshi wai "irin wannan kasa dakai haka uncle prince aina dauka can zaka zauna har agama zaman fadar dakai" be tanka masa ba yasan neman tsokana yake kawai yace suwuce unguwar Fulani.

Sunsamu Fulani Hajar tashirya musu wata kwarya kwaryar walima ta abinciccikan gargajiya da EHSAAS yake matukar so,donma shi ba gwanin cin abincin bane,a qaramin falonta suka zauna kuma tasallami duk wata hadima dake kula da gun saboda daman haka takeyi in tanaso ta kasance da danta EHSAAS se wani zuba mata shagwaba yake kamar karamin yaro daga yace waccan zeci se yace karshe dai dakyar yagama ruwan idonshi akan daya, Fulani tashiga bashi da hannayenta yana kallonta yana murmushi Aman na gefe se sharhi ya keyi yana zubawa nasa cikin shima abinci seda suka kusa kammalawa kawai sukaga mutum yafado musu. Fulani dukda ranta yabaci amman seta basar cikin murmushi take fadin "maisoon kece da daddaren nan? jinjina kai maisoon take idanuwanta sunki daukewa daga kan EHSAAS,cikeda rawar kai take fadin "barka da dawowa yarima EHSAAS," kallo daya yaymata yahade rai kamar bashine yake murmushi kamar gonar auduga ba,Aman kanshi ransa yabaci don inba maisoon dinba waye ya isa yay barging cikin gurinnan ba tareda sun hukunta shiba, karasowa tai tana fadin "Allah yajada ran Fulani walima akeyi anan,irin wannan girki haka,, zana joining nima yunwa nakeji," Fulani kallon EHSAAS tai daya mike yana kallon Fulani ya karasa yana kissing forehead dinta "I'll take my leave now maama," sosai takeson takasance da danta amman kunya kara kawaici tasa bazata iya korar maisoon ba kuma tasan zuwanta ne ya koreshi don baya iyacin abinci agaban kowa nagidan inba ita, Aman se mimah ba be yarda da kowa ba komai nasa idonshi abude yake yinsa yana kaffa kaffa da lafiyarsa bayajja zatai kawai tamai murmushi tana tambayar sa "se yaushe kenan?" yace "tomorrow in sha Allah" yana nufar hanyar waje, Amman yakallon maisoon dukda tagirmeshi yawani buga mata harara yabi bayan EHSAAS,yana bakin cikin hanashi karasa cinye abincinsa datai.

Hutun da EHSAAS yasamu gaba daya baida yawa don haka ya cinyeshi a NURISTAN batareda zuwa ko inaba kullum yana tareda fulani ko mai martaba,jalila jin labarin EHSAAS yadawo cikin satin tadako tsalle tayo NURISTAN amman duk zamanta ko noticing dinta ma bayayi dake tanajin shakkarsa sosai bata shishshige masa kamar yajja maisoon ke kokarin yo hakanne yasa yafi ganin darajarta akan maisoon kodan irin rikon arzikin da iyayenta suka masa deep down yanajin indai auren hadi za'ai mishi he will prefer her akan maisoon din,uwar soro kam baki kamar gonar auduga ganin babban angonta yadawo do sosai suke dasawa da jikan nata dukda basa zama gu daya ba tareda daya ya tsokani daya ba,don idanma bata ganshi a unguwarta ba ita zata wanke kafa tatafi tasa,haka zasu hadu suyita fada harse Aman yashiga tsakani,yasamu lokaci sosai tareda iyayensa musamman in ya kasance kwanan Fulani ne mai martaba yakan kira EHSAAS suzauna suyi maganganu masu mahimmanci yana kara wayar dashi kan irin nauyin dayake kansa nan gaba,yakan daukeshi suje gidajen marayu tare,da gidan gajiyayyu sannan yakan dorashi kan matsaltsalu da kararrakin al umma yay solving,kuma yajja EHSAAS yake dealing da tackling issues cikeda ilimi da hikima yajawo mishi wani irin farinjini da kima da daraja a idanuwan jama'ar NURISTAN dan soda dama in mai martaba ya aikeshi indai matsala ta kudice zakaga acikin nasa yake cirewa yatemaki jama'a dashi wani lokacin ma har ayi agama mai martaba baya samun labari,shida mai martaba idan suna tare tamkar wasu aminai zaka gansu suna hira cikeda girmamawa da kauna mesanyi wacca idanuwansu kadai zaka kalla kagane yajja suke matukar jida juna da girmama juna,a irin wannan lokacin ne EHSAAS yay proposing bude publishing company nasa nakanshi wa mai martaba,yanason yatsaya da kafafuwansa sannan yagaya mishi duk kalar alheran da yake samu a trading din da yake mai martaba yaso yasaka mishi hannu yakara masa jari a building prince publishing amman EHSAAS ya dage kan lallai lallai yanason ya barshi yay komai da komai da kanshi da kudin sa nakan kanshi, sosai mai martaba yakejin alfahari da samun da kamar EHSAAS dukda tarin arzikinsu amman yanada zuciyar neman na kansa yanason yagina kanshi beyi relaying akan nashi ba, hakanne yasa ya shaci babbar land a one of the most expensive areas ta NURISTAN ya mallakawa EHSAAS din don yagina company dinnasa,shida mahaifinsa suka kashe suka binne ba wanda yasan me EHSAAS din yake shiryawa dake ya riga ya tanaji mazajen kudin da ze zuba aimishi ginin kwangilar kawai ya basu ya daura Aman akan aikin don lokacin komawarsa yakusa.

Akasan ranshi duk sanda yafita daga palace yana rokon Allah ya sake hadashi da yarinyar amman ko dawasa be taba yunkurin nemanta ko wani abun ba,ana haka lokacin komawar tashi yay dakyar Fulani tayarda saboda kewarsa da takejin zata da baibayeta se alokacin ne yaje unguwannin matan mahaifinsa yay musu sallama kuma ganinshi nabiyu dasu kenan tun washegarin dawowarsa dayaje ya gaidasu be sake komawa ba,mai babban daki cema me yin shishshigin zuwa ganinsa har tayo mishi girki,kuma yana nuna jin dadinsa donshi da zuciya daya yake daukar duka yan uwanshi,amman fa bayacin abincin kowa sena mahaifiyarsa da kakarshi intai ma Aman ke cinyewe, yana matukar darajasu saboda duk kiyayyar dasuke mishi idan yana gabansu yisuke yi kamar zasu cinyeshi musamman waziri Erfan,don sosai yake nuna yajja yake kaunar EHSAAS din se ake ganin kamar don Allah bebashi da namiji bane yake daukar EHSAAS matsayin nasa. JAY ne dai babu ruwanshi dashi tsakaninsu gaisuwar mutunci haka kawai jininsu be haduba,shi EHSAAS daman becika shiga sabgar mutane ba sedai kashiga tasa shikuma jay yana jida kanshi saboda yana ganin kamar rainine EHSAAS din yay masa da baya wani bashi girma don yaga kusan kansu daya,kuma sosai yakejin zafin EHSAAS dukda afili bazaka taba gane hakan ba,duk irin yajja waziri Erfan yake shiga yafita gun mai martaba yana nuna masa ko za'ai baikon EHSAAS da maisoon ne inyaso yana dawowa se ai maganar aure, straight mai martaba yace masa ya dan dakata EHSAAS karatu yake ya bari yakammala tukunna se ayi masa tayi in ya amince toh inbe amince ba baze masa dole ba jinjina kai waziri yashiga yi yana fadin "tabbas hakane ranka ya dade abinka da yayan zamani," deep down ya matukar jin haushin maganar mai martaban wato su duka da aka musu auren hadi ada ba yaya bane da yayansu da akaiwa se akan EHSAAS ne za'a ce za'a ji ra'ayin sa koh,amman yasan me zaiyi tunda maisoon tariga tagaya masa EHSAAS bama ya sauraranta ko fuskar shakuwa bebata ba saboda jalila,tsoro yake kar ace EHSAAS yar uwar Fulani ze aura domin kamar masarautar NURISTAN zata koma hannun zuriarsu Fulani ne baki daya ya dade yana ganin yarinyar agidan amman betaba kawowa don EHSAAS aka kawota ba seda maisoon din tagaya masa cikin kishi da zafin rai take sanar dashi daman tasan fulani ba kaunar ta takeyi ba shiyasa har yanzun tai shiru kan batun aurensu da EHSAAS,shiyasa yay damara wajan ganin duk mema za'a yi ayi amman dole yarsace zata auri EHSAAS kodan su samu su cimma burinsu akansa cikin sauki,alkawari ne da yadaukar wa mahaifiyarsa cewan ze dauki fansar abinda NASHWAN yay mata akan tilon danshi EHSAAS." Wannan kenan. Koda EHSAAS ya isa airport lokacin komawarsa ba irin kalle kallen da beyiba don yanason koda sau daya ne yakara ganinta amman hakan be yiwu ba har lokacin tashinsa yay jirginsu yadaga zuwa London,wannan ce final year dinsa as undergraduate hakanne yasa yazama very busy yana preparing for his final exams sannan yana internship dinsa awani publishing company a Oxford din,lokacinne yafara kammala book dinshi nafarko amman littafi ne fiction na guide na tafiye tafiye da yajja mutum yake rayuwa in diaspora littafin yakarbu sosai,kuma labarin saurayin me suna Ahmad yaja hankalin turawan da yasa companies na publishing da dama suka shiga bashi aiki tun kafin ma ya kammala karatun nashi amman baya accepting saboda he has other plans for himself yanason yakai iliminsa NURISTAN ne suma su amfana dashi,littafinnasa yana daga cikin littafin dasukai nasarar lashe gasar booker prize London na wannan shekarar

Ana hakane highschools da dama suka shiga gayyatarsa bawa yaransu talks,career guides da dai sauransu,yauma kamar kullum mails din da yasamu a mail box dinshi daya kwaso ya zube saman table dinsa yatsaya dubawa shifa ya gaji dukda yana enjoying ilimantar da yaran amman abin yamai yawa he need time too yanason yakarasa portfolio of essays dinshi da zeyi submitting next week daga takardun yashiga yi daya baya daya ko akwai muhimmiya yakaranta idon sane yasauka akan barge din makarantar GDST,besan meyasa ba haka kawai yatsinci kansa da hanzarin dauka yashiga bude envelope din,gayyatarshi sukeyi suma sunason yabawa girls dinsu lokacin panel talks da Q&A session, murmushi yay kawai yana tina kayan da yaganta dasu kusan shekara daya dasuka wuce tabbas blazer din Oxford high dinne don yajja zuciyarsa take muradin sake ganinta atake yatura musu formal acceptance din gayyartasa da sukai ta eMail domin yama kagu ranar tayi yaje ko Allah zesa yay nasarar ganinta.

Ana igobe ranar da zeje da dare seda Noah ya tsokane shi "wai yaga yanata watso da kaya yana ruwan ido yarasa wanda zesa bayan duk kayan shi designers ne masu kyau,kodai he have date ne yake boye mishi" smiling EHSAAS kawai yay yace mishi "bahaka bane yanason yafitar da kayan da zeje GDST dasune," dariya Noah yashiga mai tsiya "wai bewa manyan yanmata kwalliya ba se teenagers kodai kodai cikin teenagers din yayi kamu ne," rabuwa dashi kawai yay yacigaba da shirinsa for the first time yakejin nervousness don zeyi public speaking besan meyasa ba kodan yana expecting ganinta ne agurin ya tambayi kanshi yana dan murmusawa.

Daman shi mutum ne me aiki da lokaci,akan lokaci ya karasa cikin babban hall din Oxford High school (GDST) anyi decorating dinsa da literary posters,se kuma high table dinsa inda ze zauna,wanda table din anjere hard copies din littafinshi da journals dinshi a gurin, yanmatan duk suna zazzaune cikin tsari, uniform dinsu navy blue colour ne,shirt ce fara taciki,se skirt dinsu da bekai gwiwa ba navy blue se navy blue blazers,da white shoe da white socks din data kawo musu har gwiwa,dake yan year 13 ne seya kasance duk kusan kansu daya shekarunsu 17 zuwa 18 ne gaba daya saboda wannan shekarar zasu gama, lokacin da aka gabatar dashi suka tashi duka tsaye suna tafamai don girmama shi,seda yazauna sannan dukansu suka zazzauna suma,head of English ne na makarantar ya karbi microphone yasake welcoming EHSAAS yana dada gaya musu girman iliminsa daya samu akankanin shekaru duk da kasancewarsa undergraduate yayi nasarar lashe gasar booker prizes kuma book dinsa me suna The man yana daya daga cikin wanda suka samu most sells awannan shekarar, students din kallonsa suke with admiration suna tafa mishi musamman yajja suka ganshi dan gaye,gashi saurayi ga tsadaddun kayan dasuke jikinshi ga nutsuwa da tsari dake tattare dashi aduk inda yashiga. sosai suka shiga whispering cikin kunnan juna suna zuzuta kyawunsa da tsarinsa da kuma iliminsa,tun zamanshi gurin yaketa baza ido yanaso ya ganota cikin daliban amman me yakasa ganotan rayawa yay kodai ba a year 13 takeba dukda yagane kawayenta su favour dasuke zaune akan gaba gaba suna masa tafi da alama wata cikinsu ta ganeshi. Atakaice yashiga basu dan discussion na journey dinsa as a university student har lokacin daya fara rubuta the man da yajja yay winning booker prize din, tafi suka shiga yi suna jinjina kai don sosai yake magana da ilimi da basirar dayay drawing attention din yan matan gaba daya zuwa gareshi,thick British accent dinsa nakarawa maganganun nashi wani melody cikin zuciyar yanmatan, Cigabawa yay,yabasu labarin yajja Oxford tai shaping voice dinshi as a writer,sannan yashiga encouraging dinsu as young women dasuyi finding voices dinsu suma as early as possible suyi sharing nasu stories din, sarcastically yake gaya musu women have more stories to tell then men sbd you guys can talk very well naturally,dariya hall din tadauka don yanada very good sense of humour dayasa yan matan jin sunsake dashi lokaci daya.

Yana kammalawa yabasu damar tambayarsa ma'ana Q&A session yafara,wacca tafara daga hannu yabata damar mgn cikeda excitement take tambayar sa "meyay inspiring dinsa ya rubuta littafin the man?" Murmushi yay yace mata "his journey to Oxford shiyay inspiring dinsa, because at first he was hesitant and lost he don't even know if he can make it,so ya rubuta the man yabada labarin Ahmad don young men like him dasuke procrastinating bazasu iyaba yana nuna musu they can do it,is just a matter of taking bold steps wasu lokacin" tafi aka shiga yi tazauna tana murmushi,wata ce tasake daga hannu itama yabata damar tambaya at thesame time idonsa na searching hall din,ta tambayeshi 'ya yakeji being a student and published author alokaci guda?" Itama ansa yabata da cewa "sometimes is overwhelming amman mafarkinsa ne kuma ba dukkan mutane ke samun damar cika mafarkansu na kamar yadda yake samu ba so yana iya kokarinsa yay balancing life dinsa as a student da kuma career dinsa as a writer,he is using his chance" dariya aka shigayi tace masa "wai meye CGPA dinshi hope dai ba iya good book ya iya rubutawa ba?" murmushi yay yana kallon yarinyar yace mata cikeda wasa "aishi ko 0. Bekaiba" hall din dariya aka dauka kafin yace mata "grades basune suke defining mutum ba ko talent dinsa you can be the dump abangaren makaranta but your talent will be somewhere else kowana dan Adam da baiwa da basirar da Allah yabashi,so they should stop rating people ta hanyar grade dinsu" tafa masa akashiga yi,haka daliban suka ringa tambayarsa wata tambayar ta ilimi wata kuma ta rainin hankali harda masu kokarin flirting dashi,harda me tambayarsa "if he can write book about them,wai yasawa littafin suna The Girls of GDST and the handsome writer?" gaba daya hall din seda yahau dariya,yace musu "maybe in his next life," wata tambayarsa tai wai "Mata nawane suka taba cewa suna sonshi arayuwarsa tundaga sanda yafara rubutu har zuwa yanzun," yace "I'm not bragging but is countless" cikin raha,daya harda tambayarsa wai "would he rather never write again for instance ko kuma ya auri macen da tatsani books," yace mata "he won't choose any sbd idan matarsa tatsani career dinshi tayaya kenan zata bashi support when he is down or lost, sannan yana ganin idan ya dena rubutu kamar rayuwarsa ta tsaya chak ne," yarinyar datai mishi tambayar tana zama idonsa yasauka akanta abayan ta take idonta alumshe yake da fararen eye glasses dinta afuskarta,batasa blazers din ba farar shirt dince ajikinta, kanta ya kusa rufe rabin fuskar ta wanda ya kenan bakikkirin se kyalli yake last time daya ganta gashinta arufe yake cikin cap kodan lokacin ba school hours bane,tanada long hair sosai, tana can baya cikin wasu manyan daliban da alama sun girmeta duk sunrufeta baka ganinta,kuma da alama ma hankalinta yana kan wani gurin ba nanba. hankalinsa gaba daya yayi kanta har seda yatabbatar sungama tambayarsa question sannan yace "shima ze tambayi mutum biyi cikinsu yaji ra ayoyinsu akan abinda suka tattauna," wata yarinya agaba yafara nunawa yace "tatashi tafadi menene ta fahimta dangane da matan da suke kasa voicing out stories dinsu saboda society's dasukai helding dinsu back as girls" nan tashiga mai bayani tiryan tiryan tana kammalawa aka tafa mata straight yace "hey you?" yana nuna peace, Ganin kamarma batasan yanayi ba hankalin yan matan duka yay kanta se da wata akusa da ita tadan tabata sannan tabude idanuwanta sun danyi jaa sekace wacca tatashi daga barci,se yaga kamar kara kyau da girma sukai dasuka danyi kasa "ana tambayarki? dayar tafada mata tana nuna EHSAAS juyawa tai tana kallonshi tadan yamutsa fuska tana mikewa tashiga gyara zaman eyeglasses dinta,skirt dinta take dan janyowa kasa kamar she is not comfortable wearing it da kuma yajja EHSAAS ya kafeta da ido tanada tsayi amman yasan dukkanta batafi takasance akafadarshi ba,kuma ba siririya bace kamar yajja yay tsammani last time kayan sanyin dake jikinta yasa yay tinanin sune suka kara mata girma ashe jikintane bawai kayan sanyin ba,dukda kananun shekarunta amman hakan be hana fitoda kyakkyawan hourglass body structure dinta,dan rintse ido yay yana scolding kansa for haram look yadan saita voice dinshi before yace "are you sleeping miss?" Yafada cikeda wasa yana kallonta hall dinne gaba daya sukasa dariya tajuya tana watsa musu wani irin kallon dayasa rabinsu suka hankalta sukai dif alokaci daya tajuya tana kallon EHSAAS, straight yace mata "what is your name?" dan shiru tai tana wasa da yatsunta wannan karon idanuwanta akasa, EHSAAS mamakin miskilancinta yakeyi,sukuma yaran sanin halin peace din da shan kamshinta da jiki dakanta yasa suka fara adduar Allah yasa yai ta hadu da daidai da itane, "I said what is your name miss? yasake tambaya,dagowa tai suna hada ido takauda kanta cikeda nutsuwa da rashin hayani ta furta "PEACE," sarai yajita saboda hall din tsit yake amman saboda yanason yasake jin muryarta se yace what? Irin bejinnan ba duka hall dinne yadauka da fadin "she's Peace Abraham Lincoln" suna kyakyacewa da dariya cikeda tsokana shi kansa seda yay dariya don ya fahimci tsokanar ta sukeyi suna hadata da Abraham Lincoln, besan tada itan dayay mugun kular da ita yayba don tatsani tsayawa cikin public haka,kuma sam dariyar dasukeyi da daura Lincoln saman sunanta na peace Abraham dasukeyi be dameta ba don ita ba mace bace wacca abin mutane normal yake affecting dinta, kuma bata taba bari duk girman yarinya tai bullying dinta don tagane yaran turawannan basuda mutunci seda tabude musu ido tanuna musu batada mutunci itama suka zauna kalau. head of English na makarantar ne yakaraso gefen EHSAAS yadan tsugunna yana rada masa "he shouldn't feel disrespectful,peace din special students ce,daman bata cika paying attention ba inba ita taga damaba special case ne da ita kuma hukumar makarantar tasani don haka yayi hakuri yakyaleta," kallonta yay aransa yana maimaita special student scanning dinta yashiga yi don yanason yaga ko tana da wani disorder ne dabe ganiba amman tsaf yaganta cikakkiyar mutum, kyakkyawar teenager meji dakanta abinda yay concluding kenan,tashan balaga ne take fama dashi. jinjina kai kawai yay yace mata "tazauna" memakon tazauna din segani yay tadauki jakarta tagoya abaya blazer dinta ahannu ta nufi hanyar fitar daga hall din har kafafuwanta na harhardewa don sauri.

Be hana ta ba kuma be tambaya dan meyasa ba,amman kuma yaji ba dadi yanajin kamar taji haushi yasa yara suna mata dariya,rufe panel talk din yay aiko nan danan yanmatan suka tattaso suka zagayeshi damasu tambayarsa shi dan wana garine da masu bashi copies dinsu na the man yay musu signing yana signing din suna mai hirar da rabinta ba abinda yake ganewa don peace tatafi da nutsuwarsa gaba daya, wasu harda nuna masa poems din dasuka rubuta da kansu yana correcting din inda basuyi dede ba yana karfafa musu gwiwa,littafin favour daya karba yana duba poem din datake nuna masa wai yagani yasa yadago yana kallonta,cikeda farinciki take bashi labarin "ai tataba ganinsa a Heathrow last Christmas tarema suka hau jirgi zuwa NURISTAN ko ya ganeta?" jinjina mata kai kawai yay yana duba poem din,yana jinta tana bawa sauran kawayenta labarin cewa "ai ita tadade da ganinsa sune se yanzun suke ganinsa yanzun," cikin hikima yake kalleta yace "I'm what's that your name again? dasauri tace "favour Sir," yace "is your friend okay? naga tafita ba'a gama ba," dan jim tai kamar bata gane wacca yake nufi ba kafin dayar tarada mata "peace cefa" tace "oohhhh peace, Sir don't worry about her, she's a psychopath," sauran shekewa da dariya sukai ganin EHSAAS baya dariya yasa tai saurin nutsuwa tana fadin "sir she's okay peace is always introverted and moody,shiyasa muke yawan tsokanarta," dan jinjina kai yay before yace "naji ance special student ce tana da wani mental disorder ne? dan jim favour tai kafin tace "she's not kawai dai she don't like being around people,battason mutane kwata kwata,sannan she never let anyone in, the girl is very lonely,tana cikin damuwa sosai," cikeda mamaki yace "damuwa kuma wace iri kenan? kallon da sasha taiwa favour ne ya sanya tai saurin fadin "karka damu parent's dinta sunyi magana da school authority ne munsan she's just special amman bamusan abinda ke damunta specifically ba." Jinjina kai kawai yay yana mika mata poem dinta yace mata "is great she should keep it up" dadi taji sosai tana rungume littafin.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comments & Vote.

Guys EHSAAS is different ba irin sauran novels din dakuka saba karantawa bane I promise you wannan journey din is different you will gain alot of knowledge aciki sannan kuma zaku nishadantu because akwai twist iri iri cikin labarin.

Kudai kawai kuyita sambadamin like nikuma zanta zubo muku chapters masu dadin gaske [24/04, 19:29] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM. Wattpad:@fatoumspassion Arewabook:@fatoumspassion