EHSAAS

Chapter 9

by @fatoumspassion

(The missing bean café) Har certificate din girma da lambar yabo makarantar Oxford high ta bashi, principal din tasu ce tai insisting EHSAAS yay having cup of tea tare da ita a office tanata mai highlighting matsayi da aiki me tsoka da suka tanadar masa idan yagama karatu in yana da sha'awar aikin koyarwa, murmushi kawai yay yace mata "ya gode zeyi tinani akai," ahaka tanata mai hira har suka kammala tafito zata rakashi yace mata "yagode kawai takoma ai yazo da mota ze karasa da kanshi" cikeda farinciki tai masa bye bye har tadena ganinsa inda yay parking motarsa yanufa.

Lokacin antashi students din se fitowa sukeyi group group suna nufar hanyoyin daze kaisu gidajensu motarsa yashiga yay warming dinta yanajin dan dumi daga sanyin da yagama kwasa awajen, gefensa ya kalla dede inda ta karaso tana bude wata mota hadaddiyar gaske, pagani Zonda hp barchetta,ita kadaice ta ajje jakarta bayan sit tana karasawa drivers sit, mamaki ya kamashi waita iya tuki kenan a 17 year old duk da bema gama tabbatawar ko takai sha bakwan ba wannan karon rigar sanyice katuwa ajikinta har gwiwarta tarufe kanta da katuwar hular rigar, EHSAAS cikeda burgewa yake kallonta don komanta da takeyi a nitse takeyi,ganin tatashi motar zata tafi yasanya yay saurin baya da tashi yana blocking dinta daga fita cikin mamaki tajuyo tana kallonshi tayi kicin kicin da fuska shi dariya yarinyar take bashi alallai ita boss batason raini,gira daya yadage mata irin yadai dinnan peace datake kule dashi dauke kanta tai tana rikeda wheel din ta nuna kamar ma batasan meyay ba,gaban sit dinsa yabude yaciro wani dan karamin jotter ya yaga page daya ya dau pen,yadanyi short rubutu yay folding dinsa.

Fitowa yay daga motarsa yakarasa yana kwankwasa mata glass din kamar bazata budeba seda tadau wasu lokaci kafin tabude tana kallonshi irin what dinnan mika mata yay,kamar bazata karba ba kawai kuma seta sa yan kananun hannayenta ta karba yana gani ta jefashi dayan side din irin bama zata karanta dinnan ba,juyawa yay yaja motarsa yabata guri tafigi tata awani irin mugun speed kamar zata bige daliban dake tafiya akafa tabar harabar makarantar.

Tafiya yakeyi cikin tinani he just want to know menene damuwar yarinyar? what make her like this? Yana rokon Allah yasa ta canza ra'ayi tazo goben dukda 80% nacikin zuciyarsa ya rigada yagaya mai bazata zo ba amman zeje he will wait for her koda bazata zoba din.

Daga bangaren peace kuma seda ta karasa gaban apartment din mom dinta harta bude kofa zata fita sekuma tadawo tana dan kallon takardar data wullar ta gefen ido zuciyarta na raya mata tadauka kwakwalwarta na hanata,amman out of curiosity dasauri tadauka tana warware aranta aiko ta bude ta karanta meyasa aibaze gane ba,warware takardar tai mamaki ne yakamata ganin abinda yarubuta.

"Tomorrow The Missing Bean, 4PM. No pressure. - EHSAAS" dan shiru tai before ta zumboro baki gaba kamar yana ganinta aranta tace "waye zeje? kuma innaje ma meze cemin hunh?" jakarta tadauka tazira note din aciki tanufi cikin gidan as usual daga ita se nanny dintane suke zaune agidan,ita tamata sannu dazuwa ansawa tai ta haye sama inda dakinta yake ta karasa ta jefar da jakar anan bakin dakin tana tube kayan suma jefar dasu tai atsakiyar dakin tafada bathroom hot shower ta sakarma kanta tanajin zafin ruwan yana ratsa dark skin dinta har wani tiriri yakeyi kamshin shower gels din datake amfani dasu yacika bandakin tafito sanye da bathrobe dinta tana karasawa closet, shafe jikinta tai da maya mayan datake amfani dasu masu laushi da taushi,tafeshe jikinta da English perfumes dinta designer's masu sanyin kamshi tafito. book shelf dinta madedeci dake cikin dakin tanufa tana kallon gurin littafin sunfi dari amman tanada tabbacin duk ta karancesu sede maimaici,tana tason taje tasiyo wasu amman kuma tasan seta tambayi izinin mahaifinta wanda dokace duk inda zataje koda baya gari dole ne tasanar masa indai ba library ko makaranta ba abin na cimata tuwo akwarya hakanne yasa abubuwa dayawa ko tana bukata batta taba mai maganar zataje tasiya sedai in nanny dinta talura dakanta take gaya masa ita taje ta siyo mata. dawowa tai ta jawo wayarta tashiga Goodreads tasiyi wanda zata karanta yanzun tashiga karatu don dai dole tasata amman bata cika son karanta littafi awayaba saboda screen din yana affecting idanuwanta.

EHSAAS washegari tashi yay cikeda zulumi azuciyarsa koda yana lectures Allah Allah yakeyi agama kawai yatafi Missing bean ya jirata kar ace taje kuma be rigada ya karaso ba, se gurin hudu saura professor din yasake su aiko da sauri ya karasa dorm dinsu,ganin lokacin sallah yayi sallar ya farayi cikin nutsuwa seda ya idar tukunna ya sake kallon time dasauri yamike yafito yana kulle dakin yafito. tafiyar mintina kalilan takaishi café din corner table din dayay reserving yakarasa,waiter yazo yana tambayarsa "ko yana bukatar wani abu?" yace masa a'ah kawai inyana bukata ze kirashi juyawa yay yakoma kan aikinsa yanata kallon kofa yana addua Allah yasa yarinyar nan tazo acikin ransa shikansa besan meyasa yakeson tazo dinba kuma shikansa yarasa gane me tinaninsa da zuciyarsa suke ingizasa aikata wa kawai dai yasan akanta bashida self control,ji yakeyi yanason ya temaketa yay guiding dinta to the right path kawai yanajin inbe cirota daga kafirci ba kamar wani bangare na rayuwarsa ze samu gibi,amman tayajja zeyi hakan shi kansa be saniba. Sanyi yakeji yasa hannayensa cikin coat dinsa yana cigaba da jiranta har kusan jiran minti talatin yay amman babu ita babu dalilin ta. Daga bangaren peace kuma ana tashi daga makaranta,head of economics yatsayar da ita dalilin classwork din data kiyi a aji yace bazata tafiba harse ta kammala, ba ita kadai bace kusan susu biyar yarike sauran ganin ba sarki se Allah ba barinsu zeyi sutafi ba yasaka suka shiga rubuta classwork dinnasu, peace kuwa babu abinda takeyi anata littafin se zane don ko ze kasheta batasan ma meyay a ajin ba balle ta rubuta wata jaka take zanawa hadaddiyar gaske tanayi tana murmushi. Mr Evan yakaraso yana leka littafin ta ganin abinda takeyi yasa ya karbe littafin ya yage zanen yasake cewa tarubutu har sauran hudun suka gama bata karasa ba yabarsu suka tafi ita kuma ya tsaya jiranta ganin bata mai lokaci take har gari yafara duhu yasanya yashiga mata fada yana motivating dinta kan karatu yana gaya mata inta cigaba da abinda take zatai failing senior year exams dinta meyasa bata focusing a aji,jinsa kawai takeyi har yagama fadanshi yamaka mata littafin as she expected 0/10 taci tasaka littafin ajakarta tafito motarta tashiga tana kallon time tasan Mr Evan already yayi contacting nanny dinta yace mata shiya riketa tai aiki amakaranta so she doesn't have to be worried cewar nanny zata neme ta kallon agogonta tai tadan cize lips din kasan bakinta don tatina guy dincan yace ta sameshi 4 a café, aranta taraya kilama yagaji da jira yatafi,sekuma ranta yaraya mata if he wants to meet you dagaske aibaze tafi ba,taka motarta amugun speed tai tanufi hanyar the missing bean café in few minutes takaraso, tagama parking motarta tafito. Yana can corner seat din daya ke jiranta kawai ya hangota tashigo café din Uniform ne ajikinta wannan karan skirt dinta medan tsayi doguwar safarta tarufe ko ina dayake bude akafarta da navy blue sandals dinta,kalar hoodie din jiyace ajikinta amman wannan farace tafi tajiya tsayi da kauri hular tarufe gashinta se na gefe da gefe wanda tafito dashi glass dinta looks very steady akan dogon hancinta,tana dan waige waige da alama shi take nema wani irin dadi yaji ya da baibayeshi ganin tazo dukda lokacinsa data bata se yaji hakan ba komai bane ba,daga mata hannu yay ahankali daidai idonta na sauka cikin nasa does eyes yafada yana kiran sunan Allah acikin zuciyarsa karasawa table dinnasa tai yamike yana jamata chair dake gefenshi tazauna,rigar sanyin take kokarin cirewa sanin t shirt dince ajikinta kadai yasanya yace "don't pls!" kallon shi tai cikin dan mamaki kafin takalli black notebook din dake gefen coffee cup din da aka kawo masa da alama gajiya yay da jiranta yace akawo mai, Ita kanta tambayar kanta takeyi "what is she just doing here with a man? man dinma dabatasan wayeshi ba daga ina yake all she knows about him shine he is a writer marubucin littafin da har yanzun bata karanta ba," Bagpack dinta ta ajje saman daya kujerar tana kallonshi da gwara gwaran idanuwanta,shima kallon nata yake with his grey eyes dasuka ladabtar da nata idon cikin kankanin lokaci takasa cigaba da kallonshi tashiga wasa da kananun fingers dinta dake nan a tsaftace sunji manicure,dasauri yadauke idonshi daga kan hannayenta kafin yabata menu yana dan daga mata gira,yace "order something," kallon menu din tai kafin tace "hot chocolate with whipped cream," waiter yayma signal yakaraso sukai order Ehsaas flat white, Peace hot chocolate with whipped cream,wucewa waiter yay don kawo musu, Yakalleta yana fadin "You came late" "And you came early" Tafada itama tana kallonshi wannan karon, Murmushi yay wanda dimples dinshi suka fito sosai yace "yah I guess I was too excited, I thought you wouldn't come" yafada yana sipping coffee dinsa, Batace komaiba sbd haka kawai taga yamata kwarjini sosai,jin bazatai maganar ba yasa yace "I'm sorry I didn't mean to embarrass you the other day" "You didn't" tabashi ansa shiru yana biyo baya shiya dauka ko haushinsa takeji saboda dariyar da classmates dinta suka mata waccan ranar,kuma be yarda bawai haushinnasa taji ba har yanzun shiyasa yasake cemata "But you walked out," "Because I'm allowed to" ansar data bashi tabashi mamaki kuma yafahimci wani abu atareda ita tabbas bata iya lankwasa zance ba,abinda yafito daga bakinta shi kawai zata gayawa mutum koyaji dadi ko yaji ba dadi ita iya gaskiyarta zata fadama,jinjina kai kawai yay kafin yace mata "but nalura kamar bakison jama'a? do you always fight with your way through attention?

Dede nan waiter yakaraso ya ajje musu abinda sukai order ga mamakinsa se yaga peace tace masa "thank you" beyi expecting tama iya godiya ba yajja ya ganta very rude, Murmushi waiter din yay mata yana fadin "Is my pleasure ma'am" kallon EHSAAS tai lokacin da waiter din yabar gurin tace mishi, "yah only when I don't ask for it," murmushi yashiga yi,kafin yace "karkice nafiya tambaya but sunce ke special ce, ke kinyarda dahakan," fuskarta tasake tamkewa kafin tace "I don't care about what people say akaina and I believe they don't know what to call silence," wannan karon kasa boye mamakinshi yay har seda tagane acikin idanuwansa yajja take fito da kalamanta dalla dalla cikin nitsuwa kamar wacca tagama tsarasu kafin tafada with curiosity yace mata "you write" cikin mamaki takalleshi tace why? "Because your silence sounds like pages," idanwansa cikin nata yafada mata kalmar da tasa heart dinta skipping for the first time seda tai blinking twice tana kallonshi,idonsa akanta yana murmushi, Muryarta kasa kasa tace mai "meyasa kake kallona?" Ahankali yay pouting lips inshi yana fadin "because you look like the start of something that I don't understand," dasauri tadauke idonta anashi sbd he exactly know how to make her heart skip,wani abune akanta yake gaya mata don't forget cewan he is a writer he can easily lie to you,to make you open up don't trust anyone especially someone who is not from your religion muryar mahaifinta yashiga echoing acikin kunnuwanta dasauri tamike tana kokarin daukar bagpack dinta, Muryarta nadan rawa take fadin "I have to go," tafizgi jakar tajuya da sauri zata fice sukaci karo gefen jakarta da be gama zugewa ba ya makale a tray din daya riko jakar tabude,littattafan ta ne suka shiga zubowa,da pens da folded sheets da wayarta da earpods dinta harda wata cross necklace suka zube akasan café din da farin handkerchief dinta dake kamshin lavender,waiter cikeda danasani yake fadin "I'm sorry ma'am," yana kokarin tsugunnawa ya taya ta dasauri ta kalleshi tana fadin "is okay! you can get back to your work," takarasa tsugunnawa tana kokarin kwashe kayanta EHSAAS ma mikewa yay ya karaso yashiga tayata waiter yatsaya yana son ya tayata amman gudun karya taba kuma tunda tace yabari wani abun yafaru shiyasa yabari din,hannunsa ne yasauka akan cross necklace dinda yana dauka yasan da pure white gold aka yishi,yasan cost din pure white gold dasauri tafizge sarkar ahannunshi tana turawa a aljihunta,sosai yashiga tinanin waye baban peace a NURISTAN dayake iya affording mata irin wannan luxury din,pure white gold is very rare musamman a NURISTAN yayan masu mulki kadai zakaga suna ta ammali dashi su kansu bakowa ba,littafan nata yashiga tattarewa,wani black spiral note book daya bude yakifa yadakko yana juyo dashi idonsa yasauka akan red ink din dayake kai fakar idonta yay ganin hankalinta baya gurin yashiga flipping few pages gaba daya bata passing ayyukanta na makaranta