1/20
Subject after subject,kmr wani filin yaki da kullum faduwa takeyi,mamakine ya kasheshi, she's a special student kalmar malaminsu ne yashiga dawo masa so this is what make her special saboda batta gane karatu,kullum faduwa takeyi sosai yaji wani irin nauyi mai girma azuciyarsa kamar wani ubanda yabude takardar makarantar yarsa yaga babu abinda takeyi se faduwa,peace data ankareda abinda yakeyi dasauri tai snatching littafin ahannunsa, idanuwanta sundan kara girma sbd shock din ganin reaction dinshi yadaiyi shiru kawai kuma yana tsugunne beyi yunkurin mikewa ba,seda tagama tattare littafanta tsaf sannan tamike rungumesu tai akirjinta harta bude baki zatai magana se kuma tarufe tama rasa me zatace masa,se asannan yadago yatsaya agabanta yana kallonta ahankali kamar cikin rada for the first time yakira sunanta "Peace..." sekuma yay shiru, "Don't" kawai yaji tace tana dauke kanta daga gareshi,muryar ta tana dan rawa da alama kunya abinda yagani ce ta mamayeta, "But peace," Tace "you see it ai ko, you see how special I am always trying and always falling,just don't say anything that'll make me feel anything more than what I'm feeling right now," Jinjina kai yay yana fadin "I promise I won't say a thing just talk to me," Juyawa kawai tai yana kallonta har fice daga cikin café din beyi yunkurin binta ba amman yaji kamar wani responsibility ya hau kanshi na guiding yarinya bama iya towards religion ba har towards ilimin rayuwa kuma yanason yasan meyasa take da irin wannan dabi'ar da halayyar kuma meyasa take faduwa amakaranta,batai masa kala da yaran da basa gane komai a aji ba, He will make sure she let him in.
Peace na ficewa a café din cikin sauri ta karasa gun datai parking motarta tahau kawai tana mata key ta fice agurin baki daya EHSAAS yafito lokacin yana ganin yajja take tukin yasan she's prostrated,shima hanya yakama zuwa balliol.
Tana karasawa gida nanny dinta tatare ta tana tambayar ta ko tagama aikin inbata gamaba takawo zata mata wani irin kallon data mata ya sanya taja jikinta tai gefe,tasan she doesn't need help kallon yake nufi. Ita abin na bata mamaki peace din kwata kwata ma bata damuwa da faduwar da take is highly possible tasake maimaita senior year dinta indai bata dage tawuce A-level dintaba amman sam hakan be dame taba.
saboda sanyin garin da ruwan zafi sosai tai wanka tafito tana zira winter pajamas ajikinta kasa ta sakko nanny ta jere mata abinci akan dining zama tai taci abincinta ita kadai kamar yajja tasaba seda ta kammala tadawo falo she's feeling lonely sosai ita ba mutum bace me tarin kawaye dazata kira wata suyi hira ko chatting ko su favour sune suke nace mata suna shiga harkarta kuma daman yawanci sunfi nace mata a NURISTAN dake basuda kawaye dayawa acan amman ana dawowa makaranta suna samun friend's dinsu na asali suke watsar da ita kowa yay sabgarshi bazasu sake nemarta ba se antashi komawa NURISTAN don ta biya musu business class suyi fafa dashi ita kuma mutum ce da abin duniyar hannunta be dameta duk abinda take dashi matsawar kana kusa kusa da ita kanuna kanaso baka zatai shiyasa dukda halayenta na miskilanci da shariya kawayen bassa iya zuciya da ita kota musu wulakanci se sundawo.
wayar mamanta tashiga kira aranta tana fatan Allah yasa tadaga,seda tagama ringing batai picking ba,peace dan tsaki taja tana kashingida saman kujerar falon kusan minti biyu tana aikin tinani aranta tana tambayar kome mamanta tatafi NURISTAN yi oho,itafa iyayenta na matukar bata mamaki shekararsu goma da rabuwa amman kullum suna tare waida sunan friendship kamar chewing gum to each other abin yana bata haushi da bakin ciki sannan yana daure mata kai,baban ta despite calling himself a righteous Christian yana leaving under thesame roof da matarsa dasukai divorcing juna shekara goma da suka wuce ita dashi basu taba raba gida ba bare kuma daki kuma they expect her to be okay with it,kuma sunce wai don ita sukeyi for her to be happy,tasan cewa kuma fada suke don suji dadin bakinsu kawai, parent's dinta never considered her not for once acikin rayuwar su komai yaymusu shi suke aikatawa.
mamanta yar asalin kasar England ce, she's from London, dukda itama halfcast ce don mamanta yar Ethiopia ce Addis Ababa,babanta ne mutumin London wanda ya kasance daya daga cikin manya manyan professor's din Oxford kafin yarasu, babanta kuma dan NURISTAN ne iyayensa both a NURISTAN aka haifesu dan asalin kabilar ebira ne kuma komai nashi peace tadakko kama daga kalar fata, kamanni,tsayi kyawun jiki duk nashine don in kaga mamanta bazakace ita tahaifeta don baturiya ce sosai babu abinda tadakko anata,babanta Abraham Zion asali dan Catholicism ne inda anan ta hanyar harkokin addininsa dasuke zuwa kasa kasa yahadu da maman peace me suna Veronica inda suka fara soyayya, Veronica macece yar kasuwa me tarin dukiya sosai domin tana harkar kayan kwalliya da adon matane tanada beauty Parlours a different countries na duniya including NURISTAN inda ake asalin gyaran jiki na mata,The V effect din babu abinda basayi,spa, message Therapy, facials,hair services,waxing, threading,make up dadai sauransu,shiyasa in kaga babarta zakace bata haifeta saboda gayu da ado dayajja take cin uban kudi kwata kwata she doesn't look her age mamanta tabawa babanta shekaru biyar kwarara shiyasa yafita zama saurayi kuma yarone sosai don lokacin data aureshi baida kudi sosai ba kamar yanzun ba daya ke kai daya da ita a arziki koma yafita don shi iyayensa ne masu kudi suka mutu suka barmishi, sabanin Veronica da ita tanemi kudinta dakanta,tataso cikin wani irin chaos home farko iyayenta are on thesame faith lokacin da sukai aure dukda yajja mamanta take mafadaciya amman she's very good towards her,macece me azabar kishi shikuma babanta mutum ne namutane he is very social and wise kullum zaka ganshi zagaye da mutane maza da mata musamman lokacin dayay tsalle yakoma Jehovah witness,sunbashi matsayi me girma acikinsu yazama kamar wani waliyyinsu elder sama elder kasa lokacinne matsalar auren iyayen nata ta gawurta inda baza suyi zaman minti biyarba sunyi fada hakanne yasa maman peace tashiga yiwa Abraham barazanar zata rabu dashi idan bekoma Catholicism dinsaba,ashe shiyama rigata arranging divorce paper din,yace mata why not semeye donsun rabu azahirin gaskiya daman Veronica tafi sanshi akan yajja yake sonta hakanne yasa lokacin dasuka rabu tafishi jinjiki kuma tace bazata bar gidansa dake NURISTAN ba saboda yarta peace dukda alokacin peace da wiyama take ganin daya daga cikinsu kamar yanxun babanta kullum yana cikin hidimar mutane a kingdom halls ko a makarantarsa ita kuma mamanta kullum tana harkar business dinta ashekara zata iya kirga lokacin datake zama tareda iyayenta,daga ita se masu aiki,da farko lokacin babanta yana Catholicism se Christmas Christmas suke zama da ita,dakuma birthdays dinta amman tunda ya koma Jehovah witness yace aiduk abubuwan dasukeyi abaya bidi'a ne yabari kuma yarsama haka,mamanta na kokarin janta Catholic church shima yana kokarin janta kingdoms hall. lokacin da tagama primary a NURISTAN ne mamanta tace zata dawo Oxford sbd kasuwancinta nacan yafara samin matsala,babanta yace tadau peace tatafi da ita donshi baida lokacin kulada peace yana harkokin gabanshi,basu cika damuwa da me yarinyar takeso ba ko kuma menene take bukata sudai kawai insuka fita suka dawo zasu jibgo mata kayan more rayuwa iri iri,kayan wasa kayan kwalliya data fara girma kuma su loda mata kudi a account dinta tai yajja takeso dasu babu shakuwar iyaye da yaya tsakaninsu kowanne daga cikin parents dinta damuwar kansa kadai yasani kuma dawowarsu Oxford bata hana babanta zuwa inyana bukata ba so tari yakanzo yadau mamanta sufita yawan shakatawa susha soyayyarsu tana kallo kuma tanajin duk abinda sukeyi batareda aureba,cikinsu babanta nema yafi damuwa datai addinin su maman ta lokacin dasuka fahimci addinin be damu peace ba be ratsa taba bata wani damuba tace zabtaine inta girma in baban yana mata complaining, dukda murdaddun ra'ayuyyukan Abraham din becika takurama peace tai abinda bataso ba akan addini harse lokacin da taje wani hutu NURISTAN yafahimci tasoma abokantaka da yayan musulman dake zagaye dasu kuma tasoma canza layi bashiri yataka mata burki yataka mata warning mezafi yakuma saka mata strict order duk wanda zata kula seyayi approving duk inda zataje seda izninsa bayan zaman kadaicin datake seya maida ita kuma kamar prisoner don daga school se gida kullum haka take kuma wai ahakan ji suke da ita kamar kwai musamman shi Abraham din domin yace Allah be bashi wani danba bayan peace don haka itace zata cigaba da carrying family name din Zion har karshen rayuwarta,yace duk nemansa da devotion dinsa towards Jehovah saboda wellbeing din peace ne saboda yanason tai leading kyakkyawar rayuwa nan gaba.
Peace wani hawaye medumi taji yana zubo mata lokacin data duba call log dinta taga last time da mahaifinta yakira tun wancan watan kuma shima tambayarta yay akan record book dinsa na evangelism wanda yake marking duk inda yaje yay don karyay ta maimaita gurare daya, shiyasa yake keeping record tana gaya masa ya kashe wayar kuwa,tana tina lokacin datake kokari amakaranta kotazo tadaya babu wanda yake murna acikinsu babu wanda yake appreciating anuna tayi wani abin kirki,amman tun ranar data fara daukar double number hankalinsau yafara tashi domin babanta harsata adaki yake yay mata mugun duka koya kama hannayenta ya daddaure harse yayi taruwar jini tagaske sannan yake kwanceta,har sumar da ita yashayi musamman in tamai taurin kai akan abu. she grew up thinking dakikanci ne yake bata attention na iyayenta se takai takawo donsu bata wannan attention su nuna sundamu da ita suzauna suna mata wannan fadan yasa tadena karatu amakaranta bata note bata classwork bata assignment,sau biyu ana mata repeating class kafin Abraham yagaji yaje yajikasu da kudi yacewa makarantar she's special girl daman tanada wani issue a kwakwalwa battagane karatu,shikenaan suka dena damunshi akan lamarin rashin maida hankalin na peace ko karatu ake a aji zakaga takifa kanta tanata karatun novel kuma bame mata magana ko ce mata danme during lunch time kuwa tana gama cin abincin ta library take wucewa tai zamanta ita kadai kwata kwata zama ita kadai becika damunta sbd tasaba tun tana karama ahaka ta taso,batason mutane sbd gudun tazo tai getting attach babanta ya rabata dasu shiyasa kullum take kaffa kaffa acikin mutanen ko ina za'a zaka ganta akarshe ita kadai.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote [25/04, 17:02] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.