EHSAAS

Chapter 10

by @fatoumspassion

(So close yet so impossible)

Kusan sati kenan da haduwarsu yasha zuwa café din kodan yaga zata sake zuwa amman babu ita babu dalilinta kuma ya fahimci guri indai akace mutane na taruwa tohm bazaka taba ganin peace agurin ba,yau karatu zeyi fitowa yay yana son yadan mike kafa hakanne yasa be tsaya a library din school ba straight yawuce Taylor institution library, sanyi sanyin da ake fama dashi yasa kayan sanyine sunkif ajikinsa har kansa amman dukda haka koh magana yay hucin sanyine yake fitowa daga bakinsa,in few weeks zasu fara final exams dinsu hakanne yasa duk wani abinda yakeso yay yakeson karasawa kafin lokacin yayi.

library din kusan kmr ma empty yake daya shiga yan tsirarin mutane kadanne aciki yajja yawanci yake during late afternoons,dan zagaya wa yay zuwa corner din dayafi jin dadin karatu anan, ga mamakinsa peace ya hango for the first time yaganta sanye cikin kayan sanyin itama to his surprise brand dinsu iri dayane colour ne dai ya banbanta,nata farare ne tas nashi kuma black dasuka haska farar fatarsa sosai itakuma dayake tanada duhu se farin yafiyi mata kyau,wannan round glasses din nata na saman idonta rubutu yaga tana tayi acikin wani littafi Mai kyau ammasa kwalliya da stickers din Barbie zagayawa yay ta bayanta donma karta ganshi ya tsaya yana leka me takeyi. Amman ya makaro tunda ya tunkaro gurin kamshin mayataccen turarensa yacika mata hanci ta ankare da zuwan nashi amman bata nuna masa alamun tasan yazo ba tun haduwarsu tafarko daya cika musu jirgi da kamshin tagane daga jikinsa yake fita haduwarsu tabiyu lokacin daya bata note takara tabbatar da hakan tsabar jinkai da jan ajin peace cigaba da rubutun ta takeyi hankali kwance tanuna bama tasan yazo gunba azuciyarsa yashiga karanta analysis din peom da take handwriting dinnata is very neat sannan sentences dinta ma haka babu spelling mistakes bare grammatical errors, Sonnet 18 shall I compare thee to a summers day? by William Shakespeare yasan komai gameda poem din impact everything na kanshi kuma dede takeyi amman last time aiyaga literature classwork dinta faduwa tai,mamaki yakamasa matuka,kujera yaja agefenta yana zama har zeyi sallama kuma seya tina seya fasa. ya kafeta da ido kawai yana kallonta kamar ta basar karta kulashi sekuma takasa tarufe littafin tana juyowa idanuwansu suka hade acikin na juna yana mata wannan murmushin dimples dinsa nafitowa wanda yakesa zuciyarta tsalle, Rolling eyes dinta tai tana fadin "Mekake yi anan?" Kasa kasa don kar ajiyosu don dokace ba'a magana cikin library, Tagumi yay yana fadin "I'm not here to argue" Aranta ta raya irin ga masifaffiyar nan, kallon gefen ido tawatsa mishi tana fadin "I'm not in the mood to talk to you too," Littafinshi daya dakko yabude yana fadin "Likewise nima bance gurinki nazo ba ai," Cikeda mamaki tajuya tana kallonshi harfa taji dadi ashe bama gunta yazo ba taja guntun tsaki akasan zuciyarta "Then what" tafada tana kokarin cigaba da rubutunta, "Let's study mn peace" Zaro ido tai tana fadin "dawa din?" Dahannu yanuna ta yace "dake mana! ke peace," Cikeda taurin kai tace "ni I don't need your help," Murmushi yay yace "bani zan temaka miki ba aike zaki temaka min," "what?" Tafada tana kallonshi cikin mamaki, yace "eh kodai kinga Allah yabaki ilimi bazaki koyarda wanda be iyaba," dan ware ido tai kafin tace "ni ilimi?" tana girgiza kai "0 nake cifa kullum," murmushi yay yace "I know nima kuma hakan take kinga we don't know anything dukkanmu let's help eachother musan wani abu kenan," girgiza kai tai before tace "your a college student, college dinma balliol is a great deal nikuma I'm just a high schooler,do you think inada abinda zan koya ma," tunda suke betaba ji tayi doguwar magana irin hakaba kuma daman shi burinsa kenan yasata magana me tsayi tayajja zata shaku dashi, "uhmmm" yafada yana tura mata littafinsa cikeda wayo yake fadin "kingani I have to work on my dissertation and I was asked to choose from one of this novels akanshi zanyi aiki, karanta kigani" kamar bazata bude ba sekuma tabude tana kallonshi takaranta afili "Jane Eyre by Charlotte Brontë The great Gatsby by f Scott Fitzgerald" Kallonshi tai kafin tace "atonement, wuthering heights by Emily Brontë," murmushi tafarayi tana fadin "are you sure wadannan ne topics dinnaka?" jinjina mata kai yay irin abin ya mishi wiyarnan,tace "what's your major? English lit?" Jinjina mata kai yay, murmushi na mugun yiwa fuskarta kyau shibe taba sanin tana da kyau kamar haka bama seyau she look very young and adorable,kinga kinamin dariya ko yafada yana nuna ta da hannu ke kin iyasu duk niko karantawa ma banyi ba balle nai analyzing,nazabi topic ciki murmushi tai tace "is not hard, dukansu fa littafan sunada dadi, I think kazaba cikin Jane Eyre da wuthering heights they are one of my favourites," yace "really" tajinjina kai,yace "why?" tace "especially jane Eyre saboda jane is strong willed and independent,you know is about finding self worth and love without loosing yourself," EHSAAS sosai yaji farinciki ya mamayeshi yajja take magana akan Jane Eyre din da alama jane din tana tina mata dakanta ne sosai seeing her talked about it yasa yaji akan jane Eyre zeyi dukda da already yayi choosing atonement amman yafasa sbd ita zeyi amfani da jane Eyre yace "wow ashe peace din tamu genius ce, you know so much about books and literature," se alokacin tatina ma dawa take data zauna tana tai masa bayanin nan dan kauda kanta tai tana murmushi. yanason ya tambayeta meyasa bata participating a aji amman kuma bayason yay overwhelming dinta da tambayoyi hakanne yasa yace "nagode peace I'll use Jane Eyre in sha Allah" sosai taji dadin accepting din dayay yace "kema muga note dinnaki naga kamar kina rubuta wani abu regarding William Shakespeare's shall I compare thee to a summers Day?" rike littafin tai alamar battason yagani girgiza kai yashiga yi yana fadin "wayo ma kenan ni kingama bude nawa kingani ni bazaki bani naki ingani ba pls ban ingani," makale kafada tai like tha seventeen year old girl she is tana sunne kai,yace "uhm uhm nise kinbani" yana biye mata cikeda shagwaba kona karba takarfi yafada cikeda wasa hararar wasan itama tagalla mishi kafin tai sama da littafin alamun tsayinsa baze kaiba dariya tabashi yasan taku daya zeyi yakarbe littafin amman yafison tabashi dakanta. lallabata yashiga yi ita kanta batasan yajja akai tai feeling at ease dashiba ta mika masa littafin ya karba yana mata murmushi budewa yay yashiga karantawa ahankali afili kamar yajja takaranta nasa,kallonta yay before cikin tsokana yace "peace are you sure ba AI kikace yarubuta miki wannan ba,wannan note din is tooo perfect to be human," hararar wasa tagalla mai zata fizge littafin ta yaya saurin janyewa yana mata dariya kafin yashiga budewa page bayan page note ne sosai kuma ba na makaranta bane personal note ne datake analyzing books,poems sannan har essays tana rubutawa,yana gaba yaga har abubuwan other subjects kamar su economics yaga tayi swot analysis nawani company harda example kuma duk tabayar dede ne. ganin yashige inda batasa ya karanta ba yasa taci serious tace mishi "my book," kallonta yay yana rufe littafin,yamika mata yace "so you like failing?" banza tamai tashiga tattara littafanta datazo dasu alamun zata gudu kenan yace "your running away again ko? nanma ba answer" yace "peace I want to be your friend," shikansa seda yafada yaji abin banbarakwai don betaba kawance da maceba, mata dayawa nason suzama kawayenshi amman baya basu fuska yau wai shine yake cewa wata yarinya tazama friend dinsa,mikewa tai tana fadin "Sire I'll take my leave now ayi karatu lpy aidaman kace ba guna kazo ba," tafara tafiya bayanta yabiyo yana barin nasa littafan agurin," "peace wait mana" yafada anitse yana bin bayanta lokacin sunfito waje tajuyo tana kallon shi straight tace masa "meye addininka"dukda har kasan ranta tayi sensing shi musulmine saboda aitaga sunanshi, yayi mamakin tambayar tata amman me baze iya mata karya ko yaki bata answer ba,seyace mata "Islam" tace "you see! we can never be friends kaji,we are two different worlds apart idan babana yasan natsaya da Muslim nayi magana I can get killed for that, can you please avoid me next time koka ganni karka nuna kasanni," Wani irin sanyin dayake kadawa awajan library din yaji yakaru sakamakon kalmomin data gaya masa kamar dirar mikiya atsakiyar kirjinsa, "Peace" yafada ahankali kamar inwani yajishi za ai masa babban hukunci ya karasa daf da ita,rintse idanuwanta tai sosai takeson ta zama kawarshi kodan murmushin dataga yana sata akai akai amman tasan abune wanda yake ba meyuwa bane ba, batason tasaka shi amatsala ko ahalinsa tasan babanta can do anything saboda ita, "Peace I don't care about your religion? peace is not like I'm going to force you ince se kinyi addinina peace we can be friends and respect eachothers religion and choices, I just see you as someone with beautiful mind and I'd like to understand you" Yafada Grey eyes dinshi nadan kankancewa sakamakon kuncin dayake ciki,kafin yadaura da "I saw your note, I saw your fire,you love books the way I do,why does that have to end here?" Ya tambayeta hoping zata canza ra ayinta sbd yasan baze taba iya forcing dintaba, Girgiza kanta tai Tace "sbd you can close a book when it gets too heavy,but you can't close your life Sire,they are things that you'll never understand," ta danja numfashi ahankali tadaura is not about religion kawai,is about culture and family borders you'll never see but they've carved into me like scars, maybe kai you can walk away free amman ni I can't" wani irin daci yaji yazo masa zuciya idanma akwai wanda zeyi paying huge price wa alakarsu yasan shine he have to sacrifice his whole life,his honour, his crown and so much more dan yasan iyayensa bazasu taba amincewa ya shigoda kafira cikin zuriarsu ba shikansa yasan is impossible gidan sarautar NURISTAN gurine da kamar bakin rijiya yake yaro baya wasa agun idan kayi kuma ruftawa zakai shikansa besan meyasa yake wannan tinanin ba. Shikansa yagaza gane dalilin da yasa yake kasa controlling kanshi akan yarinyar yana jin tausayinta bayason tamutu cikin kafircin da aka daurata akai wanda yatabbatar har cikin zuciyarta tasan karyace ba addinin gaskiya bane amman bayajja zatayi ne ayajja ya fahimta iyayenta rikakkun arna ne dasukai nisa basa jin kira, amman ita ze cigaba da kiranta in sha Allah wataran zata waiwayo ta saurareshi, girgiza kai yay yana fadin "your saying we can't be friends kenan koh peace," jinjina kai tashiga yi tana fadin "yes we shouldn't," "But I still want to" yafada yana kallon kwayar idanuwanta data cika taf da kwalla daf take da zuba juyawa kawai yaga tayi tafara tafiya yatsaya kamar gunki yana kallon bayanta maganganunta suka ringa kara maimaituwa a cikin zuciyarsa kamar faifan da ya makale: "If my dad finds out I'm talking to a Muslim, I'll get killed for that." Kamar yanda iska ke kadawa, haka zuciyarsa ke kadawa da kalamanta. Duk wani tsari da ya soma ginawa cikin zuciyarsa, ya rufta tamkar katanga mara tushe,he never taught he will fall for the wrong girl ever,a girl da he isn't supposed to love as a prince har abada.

zubewa yay akan kujerar wajen, da tafin hannunsa ya rufe fuskarsa. Duk da cewa a kullum yana da nutsuwa da kuzari, yau zuciyarsa akarye take. Ba wai saboda tace masa relationship dinsu can't be ba, a'a, saboda irin tausayinta da yakeji, yayi sensing tana cikin kuntatacciyar rayuwa dukda kokarin boye masa hakan dayakeyi, Yakenan mahaifinta ze kasance intana tsoron abokantaka da musulmai idan ita tazama musulmar meze mata, lallai akwai jan aiki agabanshi yafada yana mikewa.

Daga bangaren peace kuwa gida tanufa ba tare da ta sake kallon bayanta ba, zuciyarta na bugawa dasauri dasauri. Tana jin kamar tayi kuskure, amma ta kuma tuna halin mahaifin ta Abraham Zion yasa dole ne tayi hakan,battason wani yay suffering saboda ita. Babanta mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi. Bai yarda da duk wani kusanci da Musulmai ba. Tunanin abinda zai faru idan ya gano tana magana da wani Balliol student kuma Musulmi yasa gabanta keta faduwa.

Tana karasawa gidan ta shige dakinta, ta jingina da kofa tana maida numfashi. Cikin sati daya, wanda batayi tunanin zata sake haduwa da shi ba, ya sake bayyana agabanta. Kuma ba kamar yadda take tsammani ba, wannan karon ya saurareta, ya girmama ta, har da so ya kasance abokinta. Ya zauna da ita a library ba tare da nuna wani irin girman kai ba,nacewar yagirme ta koya fita aji ko kwakwalwa sai ma akasin hakan,ya karbi shawarar ta kan aikin da zai rubuta. Tana jin zuciyarta na son yarda da shi. Amma meye amfanin hakan idan babu makoma? Ta tambayi kanta tana karasawa saman gadon anan tazube,wuni ranar ko ruwa bata iya sawa acikin ta ba nanny yajja takai haka tadawo dashi,da dare ma haka taki cin komai hankalin nanny be sake tashiba se washegari da takai mata breakfast nanma kincin abincin tai tadauka wani abin aka mata amakaranta hakanne yasa takira miss Veronica tasanar da ita halin da peace din ke ciki tasan kalar son da sukema yarsu idan suka zo sukaga wani abin yafaru da ita sbd sakacinta tsaf zasu halakata acikin gidannan, Veronica cemata tai takaima peace waya karasawa dakin peace din tai tana cewa "ga mom dinki zata miki magana" banza peace taimata sanin cewa ko tace tadawo ba dawowa zataiba kuma ita yanzun bawai wanda zatai magana dashi awaya take bukata ba wanda ze rungumeta ya rarrasheta yagaya mata kalamai masu dadi take nema,tanajin maman nata tana fada tacikin waya kan cewar "inbaso take ta kashe kanta ba tadau abinci taci inba hakaba zata hadata da Abraham,ubanme aka mata, tunda ita ta rainata bata jin maganar ta" ta inda tashiga batanan take fitaba bawani lallashi ko tambayarta meke damunta taki cin abinci,kala peace bata cemata ba harta kashe wayar nanny dincema tashiga lallashinta hararar data banka mata nakai gulmarta datai yasa tafito adakin dasauri tana dafe akirji. hardare ba abinda taci,kiranta Veronica tai tambaya ko peace taci abinci nanma tace mata bata ciba aiko nan take ta sanar wa da Abraham,lokacin bama ya NURISTAN yatafi wani taron manyan Jehovah witness America inda anan ne suke basu mazajen kudin dasuke sponsoring yada addininsu da akidarsu wa kauyuka da kasashen Africa iri iri,shiko kirantama beba text yaymata yagaya mata idan bata ci abinci ba idan yadawo gidannan seya canza mata kamanninta kuma ya kone bookshelf dinta tasan Abraham ze iya don ya dade da kullama bookshelf dinta ita da dukane tasaba babu abinda takeji don ya daketa don tunkan takai hakan yake dukanta intai lefi musamman yaganta da yayan musulmai ammaan rabata da littafanta ze iya karasa ta cikin wani mugun depression banda wanda take ciki ayanzun hakan yasa tafito adakinta harwani jiri jiri takeyi takarasa kitchen dakanta tazuba abincin tanaci tana hawaye tanajin inama Allah zedau ranta tahuta bame kaunarta cikin iyayenta bame zama da ita yabata farinciki.

sosai wata zuciyar ke rada mata she should just befriend EHSAAS for the time being ai yakusa gamawa itama kuma haka insuka bar Oxford ba lallai su sake ganin juna kuma dad bayanan aibaze sani ba,dawannan shawarar tamike takarasa tana dire kwanikan data bata tai wucewarta sama,rigar sanyi kawai tadaura saman tracksuit din dake jikinta tadau mukullayen motarta tasakko kasa ko kallon inda nanny ke kallo aparlour bataiba tanaji tana tambayarta ina zataje tamata banza dake weekend ne taja motarta tai ficewarta. Café din da suka hadu waccn ranar takoma A corner table din dasuka zauna wancan lokacin tazauna tana satar kallon entrance kmr mejiran yazo,amman tasan ba lallai ne yazo din ba, kuma inyazo ma me zatace masa nacanza shawara inason mu zama friends yanzun, mikewa tai tana fadin "inaa" acikin zuciyarta kamar tafita kuma seta fasa tadawo tazauna din seda ta shafe awa biyu babushi ba dalilinsa sannan tamike tawuce tashige cikin motarta dan jim tai kafin tatayar tanufi hanyar komawa gida don battason ta dade nanny takira iyayenta donta fahimci gulmar matar kullum gaba gaba yakeyi.

Daga bangaren EHSAAS kuwa yamaida Taylor institution library gurin zuwanshi kullum yana rokon Allah yakara dawo da ita gurin,amman har yagama zaman karatunshi bata zuwa,kalamanta akan jane Eyre yakasa fita a kwakwalwarsa, inda take cemishi finding self worth and love without losing yourself, Yana jin kamar wannan rubutun akansa ne, akanta ne, a kansu ne.

Bayan ya kammala karatu kadan, ya bude laptop ya bude document inda yake rubuta aikinsa na dissertation. Ya goge "Atonement" da ya fara dashi, ya rubuta sabon title:

"Jane Eyre: Finding Love Without Losing One's Self - A Comparative Exploration"

A karkashinsa, ya rubuta: "Dedicated to Peace - the girl who reminded me that even forbidden stories can be beautiful."

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote [26/04, 10:10] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.

Wattpad:@fatoumspassion Arewabook:@fatoumspassion