Chapter 11
(The risk worth taking)
Tun EHSAAS na jimirin jiran peace a library har yagaji yadena amman still tana makale acikin zuciyarsa kuma yasan if they are meant to be ze sake ganinta in sha Allah.
ranar wata Friday bayan yafito daga school wucewa nearby bookshop yay don yanason yasiyo wasu littattafan dayake bukata.
Daga bangaren peace ma yau suna tashi daga makaranta bayan tadawo gida tai wanka taci abinci rasa abin karantawa tai hakanne yasa taiwa babanta text din cewar zataje siyo littattafai,da toh kawai yabata ansa tamike tashirya tafito tanufi Blackwell's bookshop,akafa tai tattaki don yau garin babu sanyi sosai.
Tana tsaye gurin wani dan karamin poetry section na Blackwell bookshop,Tana ta duba wani Neruda collection,kunnenta makale da earpods don waya ta gamayi da favour yanzun da take tambayarta ko tananan zasu zo tace mata battanan, bataji motsin shigowarsa ba amman tajiyo kamshin turarenshi da yasanya da sauri ta daga idanuwanta tana kallon inda take jiwo kamshin,shima tundaga bayanta da yanayin tsayuwarta ya gane itace yanason yaje yamata magana amman kuma yana tsoron crossing boundaries don bayason ya takurawa mace akan abinda tace battaso,wani littafi guda dayane ahannunsa lokacin dasuka hada ido,gaba dayansu murmushi sukai cikeda nutsuwa,kafin sudan dauke kansu daga kallon juna,haka kawai peace ta tsinci kanta dajin nauyinsa sosai,ahankali takarasa tana fadin "It's you again" Murmushi yay yana fadin "Oxford is smaller than it looks," itama murmushin ta mayar masa suka tsaya anan gurin for seconds kamar bazasu ce komai ba, peace tashiga wasa da yatsunta tace "uhm daman I owe you a proper conversation" cikeda mamaki ya waro ido yana kallonta,yace "really," jinjina kai tai tana fadin "I do, because last time I was too harsh and rude and scared too," Murmushi yay kawai yana girgiza kai yace "you have every right to be," Cike da gabunta irinna yarinyar data tashi batasan meye dede da ba dede ba irin sangartattun yarannan da ba'a guiding dinsu zuwa abinda ya dace tace masa "so I don't need to apologize kenan," dariya ya farayi yaga alama yanada jan aiki agabanshi don she's brutally honest duk abinda yazo ranta fada takeyi,yace "peace if you want to, you can, if you don't want to it's okay," gaba tai tashiga duba sauran poems din tana fadin "tohm ni ban iya bada hakuri ba bansan yajja ake bayarwa," yace "really baki taba bawa kowa hakuriba kenan?" jinjina kanta kawai tai, shikuma jinta kawai yake yace "amman bakya lefi kenan shiyasa bakya bada hakuri?" tace "inayi mana" yace "ba sekice sorry ba inkinyi," "hmmm" kawai tace kafin tadora "before ince sorry din ake punishing dina not everyone ake bawa damar cewa sorry," yajja take maganganun acukurkude yana bashi mamaki matuka amman dai bece komai ba,tambayarsa ta shigayi "meyazo yi Blackwell?" yace mata "littafai yazo getting" itama tace masa "itama haka," anan suka bawa juna recommendation yaji mamakin ganin yajja take ta dakko littattafai manya manya kuma first editions masu shegen tsada, bece komai ba har suka karaso gurin biyan kudi ya ajje nasa ta ajje nata katinsa yaciro yamika itama tamika atare suka bayar,kallonta yay yana fadin "rich kid abari ahutarda kudin daddy nizan biya yau," dan daure fuska tai kafin tace "niba sunana rich kid bafa kuma ba kudin daddy bane" yace "nawaye tohm aketa kashewa haka" murmushi tai tana fadin "is mommy's card," dariya yashiga mata yana cewa "Credit card din harda na mommy dana daddy kenan" jinjina kai tai don banki daban daban suka bude mata kowanne yana loda mata nasa kudin ciki,yace "duk sammakal," tsareshi tai da ido wai seya gaya mata meye sammakal,dariya yashiga mata yace "itada ba yaransu ba tayi hakuri da wanda tadan iya cikin jama'a base tace setaji komai ba," ahaka dai yana janta da tsokana dakyar tabarshi yabiya kudin suka fito daga bookshop din delivery dinsu za'a mata zuwa gida don sunada yawa,shine ma yariko nashi ahannu.
Kusada Bodleians stone step suka zauna,gurin shiru se tsirarin dalibai dakan zauna dan jin inuwar yammacin, "gurin feels very peaceful like you peace" cewar EHSAAS lokacin da suka zazzauna murmushi tai tana fadin "I'm not peaceful," EHSAAS cikin tsokana yace "tohm why are you peace then?" Murmushi tai tace "they use to fight alot,very often, suna tinanin giving up akan marriage dinsu when they have me they thought everything will be okay,so they named me peace,they want a peaceful marriage bayan sunsame ni," dukda batai mentioning su wayeba amman yafahimci akan iyayenta take magana he really want to ask her more amman kuma bayason tai feeling uncomfortable, Juyowa tai tana kallonshi jin yayi shiru tace "and you? what is the meaning behind your name EHSAAS? bantabajin irin sunan ba," Murmushi yaymata yana gyara zama, "Sunana na nufin 'feeling', 'emotion'… kamar jin daɗi, tausayi, ko wani abu da zuciya ke fassarawa fiye da baki." Lumshe ido tai kafin tace "That's beautiful… kamar kai, Ina ganin sunan ka ya dace da kai sosai Kana da nutsuwa, kana da tausayi… kuma kanada fahimta fiye da yadda kake tunani." ya zuba mata ido cikin salo yace "maybe nanda wani lokaci kadan ina jin kamar ni ne zanzama Ehsaas ɗinki." Murmushi tashiga yi harda rufe fuska da tafukan hannu tana fadin "stop saying deep things like that," Yace "I'm serious fa irin muzama ride or die friends dinnan dazaki ringa jin you just feel my pain nima inringa jinnaki," lumshe ido tai tana fadin "we will see?" kawai tana dauke kai alamar battason maganar yace "tohm are we friends now?" Yana leka fuskarta, ahankali takalleshi tana fadin "We can be friends sire,but no one can know musamman babana" tadanyi shiru kafin tace "baze fahimta ba," jinjina kai kawai yay kafin yakalleta shima yanason yagaya mata gaskiyar shi waye da circumstances din dake tare da alaka dashi ko kuma yabarshi kawai zuwa nan gaba sukara shakuwa,wata zuciyar cemai tai kar yagaya mata kawai whats the use ze iya kara nesantata dashi idan tasani. kamar tasan tinanin me yakeyi tace masa "whatabout you sire? family dinka ba abinda zasuce in sukaji kana abota da mace da irina," dan murmushi yay yana fadin "don't overthink peace I'm a man so don't worry I can take care of it," "hmmmmm" tace tana fadin "akwai problem kenan just tell me, banson ka boyemin wani abu sire I hate lies ko kunbiya kunbiya a relationship" dan sosa keya yay before yace "are we dating?" Zaro ido tai tana kallonsa dariya yafara mata yace "yes kina warning dina like a girlfriend,and the relationship thing you mentioned...."yakarasa cikeda tsokana, turo mai baki tai tana fadin "do I look like someone datake dating age," "of cause" yafada yana dage mata gira daya "rantse bakida saurayi," yafada yanason jin ta bakinta ya lura batada wani wayo bawiya zaka bugi cikinta tafada maka abinda kake sonji girgiza kai tashiga yi tana fadin "Allah banida shi," "har a NURISTAN?" yatambaya yana mata dariya tace "bawanda yakemin magana a NURISTAN ko acikin estate dinmu everyone is scared of my father," aransa yaraya babannan nata most be very wicked,amman afili se yace "that's good gara kiyi karatu sosai nima banson dating at early age kamar naki" kallonshi tai tana fadin "highschool zangama I'm a big girl I got ny driving licence last year kana cewa I'm young," murmushi yay yashiga tsokanarta "waisu big girl manya," yalura tanada fushi ga saurin hawa ga saurin sauka haka yayta sata surutu har kusan magrib sannan amotarsa ya dauketa yakaita har gidan mom dinta,tafito tana masa bye bye har yatafi.
Tun daga ranar wata irin alaka ce mai karfi tashiga tsakanin EHSAAS da peace domin kullum intatashi amakaranta library take wucewa anan suke haduwa dawayo dawayo yamata harta saki jiki dashi tanuna masa duka littattafan makarantar ta datake faduwa sukasha dariyarsau tare,kuma anan ne take bashi labarin tana faduwane kawai to get her parents attention don tasan sunajin haushi inta fadi fadan dasuke matannan yana mata dadi yana nuna sundamu da ita, murmushi kawai yay yanajin wawta da kuruciya zalla dake tareda ita dukda shima tasa jarrabawar na gaf da gaf amman haka yazauna yake bata lokaci yana temaka mata gurin gane karatun dakyau yakan cemata, "peace your very smart, kidena barin silence dinki yana burying brilliance dinki kidena pretending yout invisible acikin class dinku kinji," inyace hakan takanyi dariya tace masa "maybe she's just dull" cikin tsokana,anan yake kicin kicin da fuska don yatsani takira kanta da dull yace mata "she's not dull, he will help to get everything straight," Tutoring dinta yake sosai duk wata formula ta maths haka yake zama yay mata breaking down, every literature reference ze dauka yabata don sometimes har rubutu shi yake mata in akai a aji tana barci, yafahimci mayyar barci ce tagaske don intaji barci ko a café suke haka zatai kwanciyarta ko na minti gomane setayi,kuma yafahimci yarinyar nada kyauta donko sati biyu basu rufa da fara abota ba tasiya musu wani matching hoodie me kyau ita dashi dukda beso karba ba haka tasaka masa rigima hoodie din designer ne ga shegen tsada yasan kudinsu saboda yanada ire irensu iri iri wani lokacin shiyake picking dinta up a school haka zasuje suna karatun suna hira kamar wani yaya da kanwa,idan battason karatun haka zata lafke masa tace kanta yana ciwo harse yace baza ai karatun ba seta ware sukansu makarantar su peace sunfara lura da canjin da akafara samu a grades dinta yanzun tanayin assignment tanayin classwork, har note ma duk kuma tana ci abin yabawa home room teacher dinsu peace mamaki kuma idan malami yay tambaya a aji dukda har lokacin tana sit din baya indai tasani takan daga hannu tabada ansa. su favour ganin peace tafara kokari yasa suka fara kokarin dawowa jikinta amman me har yau batada sakin fuska cikin jama'a balle susamu damar cewa zasu kulla abota da ita,batada kawaye ko kadan musamman yanzun da kullum tana makale da EHSAAS,bata taba bawa nanny dinta wata kofar zargi ba hakanne yasa hankalinta akwance yake saboda lokacin karatunta a library take amfani dashi suyi karatunsu da EHSAAS sannan in yawo zasuyi ma suyi kwata kwata betaba sanin cewar daga ita se mai aiki suke zaune a cikin apartment din datake zauneba,yadai fahimci kawai babanta na NURISTAN kuma tana mugun tsoronsa da shakkarsa,daga bangaren peace kuwa wani irin burgeta EHSAAS yakeyi musamman insuna zaune iyayensa suka kirashi musamman mamarsa kusan kullum se sunyi waya yakan bata kuma su gaisa yace mata kawai student din da yakema tutor ne,Sunan maama yazauna radau abakinta don idan suna gaisawa da matar sosai take nuna kulawarta agareta peace nason taga ana kaunarta hakan yasa son matar yashige cikin zuciyarta bini bini ta tambayeshi ina maama don ranar nan harcemishi tai wai insun koma NURISTAN zatazo ta gaisheta da tohm kawai ya ansa mata domin yanzun yasoma jin tsoron kalar shakuwar dasuke samu da peace din ko kadan betaba kuma gaya mata shidin waye ba,saboda bama wanda yasan waye shidin ko a balliol. yau Saturday fitowa tai tashirya cikin wata doguwar rigar Ankara for the first time taji tanason tai dressing very traditional ganin garin kamar babu sanyi yasanya tasakko bata wani kware adaurin dan kwali ba haka yasa tadan kwakkwaba tafito tacema nanny ita zata fita tana murmushi,peace dazaka shekara bakaga murmushin ta ba amman this days gani takeyi kamar ma murmushi yawa peace yawa akan fuskarta gashi kullum tadawo daga makaranta takan ganta da kayayyakin ciye ciye iri iri tadura a fridge though tasan peace nada kudin siyayya ko wana irine amman tasan ba dabi'ar peace bane yawo da kawaye aje asiyo irin wadannan abubuwan kuma batama da kawaye bayan su favour wanda ko fuskar zuwa gidansu bata cika basuba tohm mutum zetafi yawo shikadaine? tambayar da takema kanta kenan, ganin peace tana jiran ansarta se tace mata "ina zakije yau Saturday ke kullum bakya gajiya da zuwa siyo littafi ko zuwa library?" dan turo baki gaba peace tai tace "nanny tohm do you want me to sulk and die inside my room, I need air,kema inkina bukatar fita you can go and besides am preparing for my finals so let me study well," aranta tace "yaushe peace tafara damuwa da karatun jarrabawar harda zata damu tana preparing" azahiri kawai seta cemata "sekin dawo," murmushi tai mata tana daga mata hannu har taja motarta tabar gidan nanny hankalinta kasa kwanciya yay kawai tafito already peace tabar street din, daya motar gidan takalla tana komawa ciki tasan duka libraries din da peace kezuwa karatu don haka bin bayanta kawai tai.
Peace straight café din dasuka saba haduwa da EHSAAS tai,tana zuwa yamusu order already waiter na ganinta yakawo, EHSAAS ganinta cikin atamfa ba karamin kyau tai masa dukda bata daura dankwalin dake zame mata sakamakon santsin gashinta dakuma rashin iya daurawar da bataiba, gyalen agefe ta yafa shi,dinkin yakamata sosai yafito mata da hourglass body shape dinta sosai zuciyarsa tashiga skipping,ransa yasoma baci, yana kallon mazan dake zagaye dasu cikin café din wani irin abu yaji ya tokare masa wiya dashi kansa besan menene ba kawai dai bayason yaga kowa yakalleta ahaka,yadan daure fuska yana fadin " let's go," cikin mamaki tabishi abaya tana dakko masa file din daya bari kan table suna fita daga gurin yakalleta yana fadin "gyara gyalenki," dan shiru tai tarasa gane me yake nufi,tadan gyara zamanshi akafadarta shikansa besan meyasa yay hakanba for the first time yariko lallausan hannayenta yadawo da ita gabanshi yazaro mayafin yana warwaresa baida wani girma hakanne yasa ya yafa mata shi yana lullube mata kirjinta da wiyanta yajawo dan kwalinta yashiga gyara mata shi tayajja zezauna sosai akanta don tintini daman ya rigada yahanata fitowa ba hula ko GDST zataje seta saka kodan sanyi sanyin da garin baya rabo dashi. betaba lurada ta iya shigar banza ba don kullum zaka ganta cikin jibga jibgan kayan sanyi da bama kagane komai na jikinta,yaudin daya ganta ahaka bawai kyaune bataiba,amman yana kishin wani yaganta ahaka don tayi bala'in yin kyau cikin traditional clothes din,peace dai tsayawa tai tana kallonsa don tunda suke dashi kodan yatsanta be taba rikewa ba seyau daya kama hannayenta,gurin motarta yanufa yasata agaba kafin yakoma yashiga drivers sit don indai suna tare becika barinta tai tuki dakanta ba,saboda ta iya tukin ganganci na bala'i,ganin kamar ranshi yabaci yasa duk jikinta yay sanyi.
key yaywa motar amman bekaiga fara tafiya ba tace "sire," banza yaymata takara cewa "My sire," dan dafe kansa yay yana jin haushin kansa dayajja yay acting yanzun din, "Sire are you okay? kayan basu maka kyauba ne?" dagowa yay idonshi yadanyi jaa,yadan kalleta yasan arniyace he knows what he is getting himself into don haka he don't have any right yaringa fushi da yar mutane ba gaira babu dalili,amman me seya tsinci kansa da fadin peace "pls kiringa rufe jikinki kinji, I love modesty anything dazaki sa yafallasa baiwar kyawun jiki da Allah yamiki pls be avoiding it,banso kinji babu kyau," dan jim tai tana wasa da fingers dinta kafin tace "is that why your angry?" kallonta yay yadanyi murmushi yace "I'm not angry peace kawai banson wasu su ringa kallon jikinki ne" wani irin dadi taji acikin zuciyarta she feels protected tadan basar tana fadin "tohm nadena bazan karaba," saukin kan yarinya wani lokacin yana matukar burgeshi dukda takan zama stubborn sometimes amman idan dai har yanuna bayason abu har cikin ransa ya fahimci koda ita tanaso takan hakura dashi don farincikinsa, "thank you peace," murmushi tai tana gyara glass din fuskarta tace mishi "tohm smile now" murmushi yaya yafara jan motar kafin tace mishi "kafi kyau inkana murmushi I hate seeing you ka hada rannan kamar wani boss na film" dariya yashiga yi yace "sekace film din take kalla harkina kararwa," murmushi tashiga yi tana fadin "ina kallafa kawai dai denawa nai danai hankali," yace "Au da bakida shi kenan"cikeda tsokana turo baki tai tana fadin "Allah inada shi kawai dai na kara ne," murmushi yakeyi kawai yana tuki yana ganin yajja takunna mai sauti bayason waka ko kadan amman bayason takura mata ita da motarta ya ajje tashi a balliol don yasan ba lallai ita ta iya fitowa ba mota shiyasa, "ina zamuje?" ta tambya tana kallonsa,yace "kanki zan siyar" dariya tafarayi tana fadin "kaina kuma" yajinjina kai yana fadin "senayi kudi kamarki,inzama inada credit card biyu," dariya tafara yi,tace "zanyi tsadakuwa," murmushi yay yace "sosai makuwa" rufe fuska tai kafin tace "ainasan bazaka iya siyar dani ba," yadago yana kallonta silently yace "why? With that cute smile nata tace "because you adore me, I'm your peace right," maganar tata sosai tashige harcikin kirjinsa yashanye ido yanamata kallon da battaso dan yana making dinta tana feeling wani iri iri ajikinta da zuciyarta "kadena kallona," yace "nima kidena kallona," "yaushe nakalleka?" tatambaya tana dauke kai yace "yaushe nima kikaga ina kallonki" dariya suka farayi susu kadai,kafin su karasa kofar wani babban asibiti,mamaki tashiga yi tafara tambayarsa "mesukeyi a asibiti?" yace "banace miki sedake zamuyi ba" lokacin daya bude motar zagayawa yay yana bude mata tace "ni Allah banason asibiti mutafi wani gurin" make mata kafada yay kamar yajja take masa wani lokacin bubbuga kafa akasa tafarayi tana fadin "nidai nidai Allah," yace "kinason indaukeki inshigar dake kenan banson rigima lets go" yafada yana yin gaba badan taso ba tabi bayanshi tana kwala mai kira don ya mata nisa hakanne yasa ya tsayata harta tarar dashi hararar wasa yashiga mata harsuka karasa gaban wani office se alokacin takalli EHSAAS zuciyarta na harbawa ganin anrubuta consultant optometrist Dr Lawrence Johnson, "Me mukeyi anan?" ta tambaya tana kallonshi, "do you trust me peace?" yafada yana kallonta jinjina masa kai tai tana jan numfashi yace "tohm calm down kinji," jinjina kai tai tamai murmushin karfin hali tana fadin "you better not be planning something weird," kwankwasa kofa sukai,dan wani karamin office ne kafin wata kofa wata nurse ce zaune akan kujera tana rubuce rubuce akan wasu takardu dake saman table din tamike tana kallonshi,cikin murmushi take musu barka da zuwa EHSAAS yace mata "sunzo haduwa da Dr Lawrence,shine Mr EHSAAS NASHWAN," murmushi tai tana fadin "and peace Abraham right?" tana kallon peace dake makale abayan EHSAAS dan jinjina kai EHSAAS yay tace "Dr Lawrence is expecting you yadanje yadawo ne you can go inside yanzun zan masa maganar zuwanku," kallon peace yay yana bude kofar office din ita tafara shiga kafin yashigo yakulle kofa,juyowa tai zata fara tuhumarsa ya toshe kunnuwansa kawai irin bama yason yaji me zatace yasamu guri yazauna,cije bakinta tai tana kicin kicin da ido sbd she's very confused kusa dashi takarasa tazauna har kugunta na gogar nasa matsawa yay daga kusa da ita jin office din wa ni irin shiru tsoro yasake kamata takara matsawa gefensa, kara matsawa yay zata matso daidai nan likitan yashigo dattijone he is in his late 40s fari fat dashi kana ganinsa kaga asalin bature yana sanye da labcoat jikin tag dinsa anrubuta Dr Lawrence yakaraso yana murmushi yace "hello young lady,I heard you've been wearing glasses for quite a while now?" Dan gyara zamanta tai tana kallon EHSAAS daya lumshe mata ido alamar tabashi ansa,gently tajinjina masa kai,yace "kamar shekara nawa?" "eleven to twelve" tabashi ansa tana kallon EHSAAS kenan kawota yay aduba mata lafiyar idonta, Dr wasu rubuce rubuce yay kafin yace "that's quite early, do you remember how it started," dan jim tai tana tina lokacin da take yarinya iyayenta basa zama tare da ita idan mommy zata fita ta saka mata kuka seta kunna mata cartoons a TV tai ficewarta,kota bata wayarta data gaji ma tab tasiya mata tadura mata games dase takai dayan dare tana yi bame cemata danme danba kwana agidan suka cigaba dayi ba,kuma inta tashi da safe abinda take fara yi kenan game ko kallo, TV games kuwa tana dasu iri iri,amman ta ina zata fara wannan bayanin agaban EHSAAS Dr yakalli peace data tafi dogon tinani, EHSAAS ne yamatso daf da ita cikin kunnenta yace "peace" dasauri tajuyo suka hada ido kafin tace "uhm," EHSAAS yace "answer honestly kinji" kallon Dr tai kafin tace "I used to stay up watching cartoons, using the phone a lot too. My eyes started hurting and everything got blurry." yace "lokacin da komai yazama blurry wana action kikai taking?" kallon EHSAAS tai da yake jiran ansarta tace "nagaya ma mom dina seta saka nanny takaini asibiti acan NURISTAN anan kawai suka bani glasses shikenan tundaga nan nake amfani dashi," wani irin tausayin yarinyar yaji yamamaye shi kuma sanin cewar iyayen peace nada kudin tsaya mata akula da lafiyarta amman basuyi ba seda nanny suka hadata wai aje aduba lafiyar yarsu wannan wana irin iyayene ya raya aransa amman afili babu abinda yace, Dr kansa yayi mamaki amman kawai seyay mata murmushi yace "Your friend here said he wanted you to have a proper check-up. That's thoughtful of him."
EHSAAS ya yi murmushi kadan, yana boye damuwarsa a zuciya. Peace ta kalle shi cike da mamaki da jin daɗi.
Gwaje gwaje likitan ya farawa peace dawasu na'urori na zamani, yana kallon yadda idonta ke amsa haske da rubutu nesa dana kusa. Bayan kusan mintuna goma, ya ajiye kayan sannan ya dube su duka. Yace "As I suspected. Her eyes were affected due to excessive screen time at a tender age. But the good news is, there's no damage that requires urgent surgery." Murmushi EHSAAS yay yakalli peace yana fadin "mungode allah," kafin yakalli likitan yace " so what's the way forward?" Dr Lawrence yace "zanbaka wasu prescription If you stick to it,eye drops, limited screen time, and some exercises,the eyes may correct themselves over time. If not, she might need minor laser correction, but that's only if there's no improvement in the next year." Kallon peace EHSAAS yay irin kin jidai ko sunkuyar dakanta tai cikeda farinciki da jin kunya don ita kanta saka glasses din ya gundureta,tinawa dacewa iyayenta basu taba considering suyi wani abu akan hakan ba se EHSAAS yana kara sata jin yasamu wani matsayi na daban azuciyar ta,shikam cikeda tausayinta wannan karon yamatso yana rada mata a hankali "I just want to see you happy and healthy, Peace." da murya mai sanyi tace "Thank you, sire. No one's ever done something like this for me before."
It's fatoumspassion EHSAAS
Don't forget to Share Like Comments & Vote. [27/04, 18:45] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.