EHSAAS

Chapter 12

by @fatoumspassion

(My Sire)

Suna fitowa daga asibitin,bayan sun karbo magungunan a pharmacy doctor yayi mata bayanin duk yajja zatai amfani dasu mota suka shiga ta kalleshi tana fadin "thank you sire," turo baki gaba yay yan fadin "you've thank me enough peace, remember no thanks in friendship" dariya ta farayi tace "naji dadine sosai sire shiyasa," lumshe ido yay yana fadin "inason inga kina jin dadi kina farinciki haka " murmushi tashiga yi tace "amman ya akai kai tinanin idona zedawo gani daidai kamar kowa," jinjina kai yay yace "kawai nagaji da ganinki da wadannan glasses dinne, I prefer to see does pretty eyes free, looking independent" dariya tai tana fadin "yanzun kuwa kaga they are dependent glasses dinnan sunyi enslaving dinsu" dagashi har ita dariya sukai kafin tace "sire your the best" tana lumshe masa ido, "where are we heading now?" tatambaya ganin irin kallon da yake mata,yace " Westgate Oxford," dan zaro ido tai tana fadin "I don't need anything sire, mukoma kawai kaga kada yamma yaymana za'a nemeni," kafada ya makale mata yana fadin "ni I need to do some shopping kinga tafiya zakiyi kibarni kina gama jarrabawa so I want us to spend more time together kafin lokacin"

tinawa dacewa NURISTAN zata koma suna gama A-level dinsun yasa taji gaba daya ranta yafara baci ya leka fuskarta yana tambayarta ko lafiya girgiza kanta tai kafin tace "kana ganin balliol xasuyi accepting dina kuwa my grades aren't good kuma bandau wani extra sports daze saka nasamu shiga dawuri ba," dan jim yay kafin yace "why balliol is it because of me bakison kitafi kibarni" dan sosa gira tai kafin tace "uhm uhm" dariya yay yace "just accept it you'll miss me girl shiyasa bakison tafiya," "tohm tohm ka kamani" tafada tana daga hannayenta kamar wacca tai surrender,yace "don't worry, wait for me I'll meet you in NURISTAN just one year kinji,inba dole bama aida MA din na hakura nabi princess dina munkoma tare ko," tasan wasa yake mata hakanne yasa ta turo baki tana fadin "dadin bakine bazuwa zakaiba nasan inka koma NURISTAN kila kama manta dani in kaga fine fine Muslim ladies dake can," dan murmushi yay yace "your fine too amman sun fiki kyau" cikin mamaki takalleshi irin straight ma yay accepting baze dan gaya mata maganar da zatasa taji dadi ba,tace "but why?" yace "saboda suna da hasken musulunci atare dasu wai baki lura duk musulmai kyansu daban yakeba they glow differently matanmu nada kyau saboda they always cover up,kuma Allah yana basu lada insunyi haka" tace "nima ai ina rufe jikina yauma tsautsayine," tana kureshi da ido betaba kushe mata addini ba amman kuma be taba yaba ba samsam ma bataji sun taba hira akan addinan juna bayan yau, "hmmmmm" kawai yace kafi yace "peace basa yawo babu dankwali,suna yin ibada sau biyar akowace rana bayan nafilfili taya zaki zama daya dasu kusancinsu da ubangiji ne yake kara musu kyau da kwarjini," sosai takejin ba dadi aranta yana yabon wasu matan ba itaba dukda betaba fitowa yace yana sonta ba amman aitasan alakarsu is beyond friendship they are just deceiving eachother with so called friendship. jin tayi shiru yasa ya leka fuskarta hawaye yaga yana zubowa sosai hankalinsa yatashi beyi tinanin yar maganar nan dayay zata bata mata har hakaba, "why are you crying peace? meyasa meki nine?" ahankali tashiga shashsheka tana fadin "nima bani nazabi inzo a inda nazoba," "peace pls kibar kuka talk to me," I didn't mean to hurt you with what I say?" Dagowa tai cikeda jin haushi tace "kana tinanin musulmai sune kadai mutanen kirki masu ibada aduniya,kana ganin Islam shine kadai religion din gaskiya, I do have religion too ka tabajin nayi kokarin cin mutuncin addininka ne meyasa ni kake kokarin ciwa nawa addinin zarafi your using beauty indirectly kana nunamin matanku sunfimu daraja da komai," Lumshe ido yay yana dan baya da kujerarsa yakalleta Yace "that's not what I'm trying to do peace,ki fahimceni," Kukanta ta cigaba dayi yana sauraronta kamar ana tsatstsaga zuciyarsa babban bakin cikin ta shine batasan much about addininta ba sef dahar zata kareshi agaban EHSAAS ita mutum ce da bata damu da Christianity ba saboda duk abinda zatai ya burge mahaifinta bata tabayi. amman dukda haka taji haushin maganganun da EHSAAS yafada akan matansu da ita, sunjima ahaka kafin ya tada motar ahankali ganin ya nufi hanyar westgate yasa tace masa "ita bazata je ba karma yasoma kaita," ganin har lokacin fushi takeyi yasa yay parking gefen titi yana kallonta ta dauke mai kai zuciyarta wani irin waswasi takeji domin tanada tambayoyi dayawa da takeso taimasa akan addinin musulunci amman batasan tayaya zata tambaya ba,seda suka jima ahaka sannan tasamu kwarin gwiwa cikin sassanyar mury ta ce, "Sire, why do you think Islam is more truthful than my religion?"

Kallon ta yayi na dan lokaci mai tsawo kafin ya mayar da hankalinsa ga titi "Peace… I won't lie to you. I'm not asking you to change your religion because of me, or because I think I'm better than you. No. But I believe you deserve to know the truth. Because you have sense, you have reasoning. You're not a child. You were born as a Christian, eh nayarda da wannan kince min bake kika zabi inda kikazo ba amman me, that doesn't mean you must die as one. Allah gave us brains to think, to choose what is right when truth comes."

Tayi shiru tana sauraren sa, maganganun sa suna sokar zuciyarta kamar sukan karamin ƙaho.

Ya cigaba, yana fadin, "naji maganganun Ku keda kawayenki… on that flight to Nuristan. I know I wasn't supposed to listen, but wallahi I couldn't help it. You were questioning your own beliefs. You were asking questions even your friend didn't know how to answer,kin ce 'How can Jesus be God and the son of God at the same time?'" Kinyi questioning rabe raben kan dake tsakanin ku Christians" Idonta ne ya ƙara cika da hawaye, amma bata katse shi ba,sema bude kunne tai tana sauraransa

"Peace," ya ce, yana kunna motar a hankali, "how can you convince me that, that very religion you're doubting is from the true God? I'm not judging. I'm just asking. Because even Allah says in the Qur'an:

"There is no compulsion in religion. Verily, the Right Path has become distinct from the wrong path…" (Qur'an, Surah Al-Baqarah 2:256) Yadan tsaya yana tuki ahankali, Kafin yadaura da "And again Allah yafada cikin al Qur'ani mai girma, 'O mankind, indeed We have created you from male and female and made you peoples and tribes that you may know one another. Verily, the most noble of you in the sight of Allah is the most righteous of you.' (Qur'an, Surah Al-Hujurat 49:13)

"Peace," ya ce cikin sigar lallashi da tarairayar da bata taba ganin yana mata ba "Muslims, Christians, Hindus, Buddhists… all of us were created by one God. Ubangiji daya Wllh shine Allah SWT. He is the only one who deserves to be worshipped."

Sannan ya ce da taushi, "Jesus… Isa A.S… is not God.sannan shiba Dan Allah bane annabine kinji peace kidena confusing kanki, He is a Prophet of Allah. A holy messenger. Born miraculously by Maryam bint Imran,without a father,but with the will of Allah. Just like how Allah created Adam without a father or mother."

Peace ta dago kai a hankali. "But why did he do miracles? Why do Christians say he died for us?"

Ehsaas ya juyo kaɗan, yana kallonta da tausayi. "Allah gave every prophet a sign, a miracle. Musa split the sea. Ibrahim walked through fire. Isa healed the sick and brought the dead back to life,by the permission of Allah. It was never by his own power. And as for dying for sins, Allah is the Most Merciful. He doesn't need blood to forgive. He just says 'Be' and it is,and he isn't even death mu anbamu labarin hakan cikin addinin mu"

Ya ɗan yi shiru, kafin ya karasa, "Allah said in the Qur'an:

'Indeed, the example of Jesus to Allah is like that of Adam. He created him from dust; then He said to him, "Be," and he was.' (Surah Aal-e-Imran 3:59)

sauke ajiyar zuciya tai don yajja yake magana kadai cikeda ilimi da nutsuwa duk taurin kanka abin se yashigeka, kuma ta fahimci bawai domin ya raina addininta bane , amma yana son ta fahimci kanta da abinda takeso deep inside ta dade tana sha'awar musulunci amman tana tsoro kuma batada courage din admitting hakan acikin zuciyarta wllh tasan idan harta cika binciken gaskiya wannan abinda EHSAAS yagaya mata zata samu shiyasa takiyi saboda tasan zata jawo yakin da batada army tsakaninta da mahaifinta

"Peace," ya ce yana ɗora idanuwasa cikin nata "you are too special not to search for the truth. Even if it means asking yourself difficult questions. I'm here. I'll never force you. But I'll always pray that Allah shows you the path that brings peace to your heart. True peace is Islam kinji"

Bata ce komai ba. Sai dai hawayen ta suka cigaba da zubowa kamar ruwan sama. Wannan lokacin, ba kukan tsoro bane. Ba kukan ciwo bane. Amma kukan fahimta ne. Kamar zuciyarta ta fara jin wani abu da bai taɓa shigarta ba.

Kallon lokaci EHSAAS yayi yace "mata lokacin sallah yakusa kince bazakije westgate dinba so I think bari na ajjeki agida kawai I'll Trek to balliol," girgiza kai kawai tai tana fadin "let's drop you first zakai sallah,ni I can go home from there aiba nisa tunda amotane," kallonta yay yana fadin "peace are you sure you'll be okay?" jinjina masa kai kawai tai handkerchief dinsa fari tass yaciro daga aljihunsa yamika mata yana fadin "I hate seeing your tears cry cry baby, wipe it off," murmushi kawai tai takarba tana goge hawayenta handkerchief din mugun kamshi yake kamar shidai tadago tana danmai murmushi kadan,ganin tayi murmushi yasa shima yay yana fadin "good girl."

Tukasu yay har zuwa kofar hostel dinsu dake balliol college,fitowa yay yabude mata kofa harda dan bowing dinnan kamar ya budewa sarauniya kofa tana kallon building din takoma driver sit kofar abude take ya tsaya gefenta yana fadin "goodbye my princess take good care of yourself and I'm sorry for today nasan nasa yar karamar gimbiyata kuka" yafada yana mata murmushin dake sanyaya ranta murmushi tai tana fadin "bayanma ko inviting dina zuwa hostel din ba kaiba" dan waro ido yay yana fadin "bakyau mata su ringa shiga hostel din maza, is not good," turo baki tai tana fadin "aiba gurin maza zanje ba gurin ka zanzo" girgiza kai yay yana fadin "your too beautiful zasuyi ta kallemin ke" Rolling eyes dinta tai tana fadin "tohm sekace ba yanzun ka gama kusheni kana cewa banda kyau acikin motaba," dan bude baki yay cikin lallashi yake fadin "ni na isa yaushe nace princess peace bata da kyau nidai fassara aka min mara kyau" dariya tashiga yi tana cemai "Allah yafada," yana girgiza kai waishi lallai befada ba,ganin lokaci naja yasa yace "uhm bari nashiga kar lokacin sallah yatafi Goodbye peace" tace " goodbye SIRE" harze tafi se yajuyo "Sire? Wallahi Peace, you sound like someone straight out of a Shakespeare play. Are you auditioning for Hamlet or something like that? kullum sire, sire, sire, uhmmm! What is this, Shakespeare's England? Why are you calling me that?" yafada yana kashe mata ido daya, ta kalli gefe tana dariya, sai ta ce a hankali "Because… you remind me of someone noble. Not just royal… but kind. Gentle. The type that listens when no one else does. That stands up when I can't even stand for myself. That's why I said sire,out of respect, and a little awe" Tafada itama tana kashe masa ido daya da yasa EHSAAS yakusa loosing control "omg" yafada aransa saboda wani irin kyau da yaga tamasa mgnr ta shigesa sosai wannan yanuna irin darajar da take bashi arayuwarta da respecting dinsa datake without even knowing who he is,a hankali yace "I don't think anyone's ever said anything like that to me before." daga kafada tai cikin salon da only peace ke iyayin tace "Well, get used to it. You deserve it." Yana dan baya baya yana murmshi yace "Thank you… my lady." Tace "Touché, prince."

Motar tafara juyawa a hankali, Peace ta bar hostel ɗin da zuciyarta cike da farin ciki, ba tare da ta san EHSAAS ya tsaya a wurin na ɗan lokaci yana kallon bayanta, zuciyarsa cike da rudani, so, da tsoro.

EHSAAS yana shiga ciki alwala ya daura yashiga gabatar da sallah yana idarwa bayan yagama azkhar rokon Allah ya shigayi da ya temake shi yakarkato da peace kan hanyar dede, Allah ya temaka yasa tagane gaskiya cikin lokaci kankanin yasan shine meshiryarwa, bawa be isa yashiryi wani ba amman yana rokon Allah yasa shi yazama ladder din da peace zata taka tahau tagano gaskiya,sannan soyayyar ta da yake ji aranshi idan ba alheri bace Allah yacire masa ita daga zuciya,idan alheri Allah kakawo mishi komai cikin.

Daga bangaren peace lokacin data koma gida though ta nuna ma EHSAAS she's fine amman kasa komai tai ko wanka kasawa tai tundaga haduwarsu zuwa yau take tariyowa acikin kwakwalwarta babu abinda take tinawa wanda yaymata se alkhairi kama daga temaka mata gurin karatunta, yaye mata kadaicin dayake damunta, yazamar mata tamkar wani dan uwa najini uwa uba yadamu da damuwarta koyaya yaga ta canza fuska yaringa lallabata kenan yana tambayarta me aka mata koda taki bashi ansa haka zeta kokarin tarairayarta yaga ya fitar da ita daga kuncin datake ciki,sannan gashi ya kaita aduba mata idonta saboda yanason tadawo da gani kamar kowa, tabbas yataba zuciyarta don ko iyayen dasuka haifeta basu taba yimata hakanba.

magungunan data ajje saman drower gefen gadonta tashiga kallon kawai maganganunsa kan addininshi na ratsata ba waiyau tafaraji anyi magana akan musulunci ba, amman nashi na musamman ne kodan yazo mata cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,wayarta ta jawo kawai jin kewarsa na da baibayeta tadanna masa kira har seda tagama ringing sannan shi ya kirata tadaga tanayin shiru, "helloo" taji yafurta cikin husky masculine voice dinshi kamar wanda yatashi abarci bayan basu jima da rabuwa ba, "barci kakeyi ne?" ta tambaya tana lumshe iso kamar tana gabanshi "uhm uhm," yafada yana mikewa zaune don kashingida yay barcin na kokarin daukarshi, "tohm me kakeyi?" tatambaya tana jiran amsa, murmushi yay irin overprotective wife dinnan ko girlfriend take tuhumarsa me yakeyi,yace mata "tinanin ki nakeyi," yasan taji dadi don yana iya jiyo sautin murmushin ta ta cikin wayar,amman seta wni maze tace "tinaani na kuma? ba yanzun muka rabuba?" Adan hankali voice dinshi akasa yace "kinsan I can't get enough of you," wani irin dadine ya lullube peace,dasauri tace "tohm ko infito café," murmushi yay don dukkan alamu sunnuna mai peace ma najinshi acikin zuciyarta kamar yajja yakeji,amman dai yasan nasa yafi nata kawai dai saboda ita macece ga kuruciya kuma bata iya boye sirrin dake ranta, she's just straight forward. girgiza mata kai yay kamar yana gabanta yace "ah ah peace, kizauna agida study well kinga gove zaki fara exams so you have revise everything we did together," yakarasa in a voice that shows how much he cares,da tohm tabashi ansa dukda yasan ta turo baki koda baya ganinta don battason tace zatai abu ahanata, "peace are you still here? yatambaya jin tayi shiru tace "uhm sire," yace "tohm oya eat first,and get back to your books, we will talk tomorrow kisha maganin ki kinji use everything kamar yajja Dr Lawrence yace don't touch this phone again, I'll text you as usual kafin ki kwanta" jinjina kai tai kamar tana gabanshi tace "bye bye sire," yce "take care peace" ita tafara kashe wayar se alokacin taji kwarin gwiwar cire kayanta ta shiga wanka kafin tashiga seda taboye magungunan ma don asirrince tashigo dasu gudun kada nanny tagani takai rahoto.

tana cikin wanka taji anbude mata door din dakin tasan nanny bata shigo mata daki kai tsaye hakanne yasa tai mamaki jitai anwuce closet bashiri tashiga dauraye jikinta agurguje tafito daure da wani dan karamin towel tana son taga me nanny kenema take mata bincike mata daki watso kaya taji anayi akasa daga inda take jerawa tashiga closet din afusace, turus tai ganin mom dintace sanye cikin yan guntayen kaya riga da skirt ne rigar budaddiya ce irin wacca battada wiyannan amman tayi zololo tabaya se mini skirt dinda be karasa rufe mata cinya ba kamshin turarenta yacika closet din gaba daya tana kallon yajja take taka mata ko ina da shegen takalminta me tsinin gaske tana taunar chewing gum,seka rantse ko alaka ta abota basu hada da peace ba balle ta haifeta saboda babu abinda ya hadasu ta kamanni ko wani abu, "what are you doing here mom?" Ta tambaya tana karasawa don dakatar da ita daga watso mata kaya don tasan mom din intai haka that means kayanta are outdated, agurin mommy sun tsufa zata zuba mata sababbi da ake yayi,bayan kayanta sababbine wasuma bata taba sawa ba, "baby your clothes are outdated nazo da new levels zan zuba miki,"tafada cikeda gwalli da kwallisa irin nata don Veronica Zion macece yar gayu ta ajin karshe. wani irin bacin rai peace taji tanaji wato bama zuwa tai dan taji lafiyarta ko taji ya take ba kawai ta kayanta take saboda karta fita ace ga yar Veronica tana sanye da outdated kaya. "bana bukatar kayanki" peace tafada tana kokarin tattare kayanta dake kasa Veronica rike kugu tai daman tasan yarinyar zata mata taurin kai ta rainata batta shakkarta shiyasa ta lallabo Abraham tataho dashi, dukda tana tsoron abinda zeje yadawo amman tasan shine zesaka peace tai abinda takeso din. seda peace ta yayimo kayan duka zata mayar taji saukar muryar mahaifinta acikin dakin yana fadin "V are you done? inada abinyi fa" sakin kayan peace tai akasa tana kallon kofar closet dariya Veronica tai don taga tsoron dake cikin idanuwanta lokacin dataji muryar Abraham tadafo yarinyar suka fito tana fadin "ga yarka fa" irin cikin sigar tsokanar nan wa peace batasan haushi suke bata ba duk subiyun.

karasawa Abraham yay dake cikin suit fara kal mekyau yanada tsayi sosai don ze iya kamo EHSAAS atsayi and he looks very young and handsome,baza kace ya haifi peace ba sede kamar da take dashi take tona asirin hakan domin babu abinda tabari nashi that piercing eyes da long nose,dawannaan cute pinkish lips din da doguwar fuska sedai shi yafita duhu dake shi namijine yana gwagwarmayar duniya harta da tsayi nasa ta gado domin tafi mamarta tsayi dukda takalmin dake kafarta, "my daughter" yafada yana jawo peace jikinshi yarungumeta for few seconds kafin yasoma scanning din jikinta irin dubawannan yake ko wani ya gutsirar masa ita da bayanan don yasaba mata hakan kuma tatsani wannan dabi'ar tasa ko kunyar ganinta cikin towel subata privacy basu iyaba,yakalli Veronica yace "naga kamar takara jiki koh,ko idonane,is that okay kuwa, I don't want her to be fat fa" Veronica wata dariya tai tamata yan duniya tana zuwa gefensa abu tarada mai akunne yay murmushi harta da murmushin su iri dayane da peace yana jinjina kai yace "ohhh our daughter is grown up now" yana tabe baki kafin yace "keko gaisuwa baki iyaba mara kunya kina kallona da idanuwannan naki kamar zasu cinyeni baki iya ganin babba ki gaisar ba" tsugunnawa tai har kasa kamar yajja yay mata tarbiyyar inzata gaisheshi tai kneeling kanta akasa looking very sad and helpless take fadin "Good evening sir,good evening ma barka da dawowa," shafa kanta yay yana fadin "my daughter, my daughter" irin yana sake nanata itadin yarsace don taji dakyau, Veronica ce tace "get up peace" karkisa wani yashigo yay tinanin oppressing dinki mukeyi,mikewa tai kan akasa,haryanzun tana mamakin mood din baban nata nayau, Veronica tace "Abraham naga kana wani murmushi meyafaru ne why are you so happy?" Kallon peace yay yana fadin "yatace tasani farinciki daga kasa nake," Veronica tace "me peace din tayi?" yace "naga bagpack dinta awurin nabude and I saw something very surprising," Veronica takalli peace kafin takalli Abraham se alokacin peace tadaga kai tana kallonshi yace "you pass all your classworks and assignment,ina NURISTAN home room teacher ki yakira yacemin your progressing ban dauka yakai hakaba ashedai burina akanki ze cigaba though manyana basuson inbarki kije jami'a because they believe yaran mutane na lalacewa anan peace I fought for you with the governing leaders na Jehovah witness as my daughter na rokar miki alfarma zasu barki ki cigaba da karatu,I want you to be the best leader among them all, peace I want you to pass all your Alevels,study theology be like your father, continue what I start banson inga mutane nabin hanyar shiga wuta ko yaushe I want you to help NURISTAN women basuds knowledge na addininsu,inason kizama jagorarsu, my university will be yours in few years bama iya university komai da nake dashi peace will become yours you'll get much more when you become what they want," yafada yana tallafo chin dinta hawaye yagani daya nabin daya akuncinta,ya tsaya turus yana kallon Veronica dajin maganganun mijin nata tadan ji babu dadi saboda tasan passion din peace na ga literature she knows how the girl want to become a great writer, "menai mata?" yashiga tambayar Veronica "kinga yarkinnan zata batamin rai meye abin kuka acikin maganata nidake tayaki murna" yafada yana watsawa peace mugun kallo bakinta rawa yafara yi ahankali ta runtse ido tana fadin "I don't want to study theology,ni English lit nakeso nayi," cikin mamaki yadago ido yana kallonta duk da bayau tasaba mayar mai da magana inyayi ba amman be dauka peace dabata damu da karatu ba zatai having issue idan yace ga abinda zatai bashine ya haifeta he has every right, "peace nine kike kalla, kike cema bakison abinda nazaba miki okay kinfison inmaidake NURISTAN nazabi miji namiki aure at this young age ko nace kinfison hakan?" girgiza kai tashiga yi tana fadin "ni banason inkoma NURISTAN, I'll get the best grade ever zanyi applying balliol I'll make sure I get in," Abraham dariya ya farayi yashiga tafa hannu yace "ba...me? balliol fa kika peace dawannan banzan kwakwalwarta taki dashi dana jakai babu banbanci kike tinanin balliol zatai accepting dinki wake-up Oxford ba gurin dakikan yara bane irinki,duk wanda kikagani is highly intellect there," "niba dakikiya bace" tafada tana kokarin juyawa tabar mai dakin gashinta yafizgo dasauri Veronica tarintse ido yajja taga yarinya tadan saki kara yayo baya da ita yana fadin "nace nagama dakene zaki juyamin baya kitafi how dare you peace?" Dan kinga ina raga miki this days nabar sha'aninki,oh ko dan kinga kinfara zama macene kike tinanin nazama sa'anki fadamin dududu yaushe kika fara bleeding" dagowa tai da manya manyan idanuwanta da sukenan sak kamar nasa tashiga kokarin fizgewa, ganin tanama da guts din kokarin fizgewa ya sanya yadaga hannu yana kifa mata mari. atakenan gefen bakinta yafashe, Veronica da kenan tsaye ba ita aka mara ba amman seda ta dafe kuncin ta don karar dayay, kallon peace yay yana fadin "peace are you insane ni nake miki magana kina juyamin baya zaki tafi narike ki kike kokarin fizgewa ni ubanki ne fa," kallonsa take da idanuwanta manya kalar tsageru batada alamar risina, yacigaba da bala'i "babu balliol din dazaki, I won't sponsor you indai har kikace bazaki abinda nakeso ba,peace your coming back with me to NURISTAN kuma theology zaki karanta," "bazan karanta theology dinba, English lit zanyi shine nakeso shine ra'ayina,kuma bance kai sponsoring dinaba I'll work hard to get scholarship, I don't need your money" Tabashi ansa tana kallon cikin idonshi, mamaki Abraham yashiga wato rashin kunyar peace har yakai tafara maida masa magana haka yay sakaci yabata yanci, "zakiga wanda ze baki scholarship din da wannan dakikiyar kwakwalwar taki da bansan inda kika gado taba" yakarasa fada yana kallon Veronica da take kallonsu peace ya kewa fadan amman ita take jimata tsoron don peace ta rigada ta kangare mai tasaba da masifar sa,dukansa da zaginsa duka "kuma theology zaki,inba hakaba zanga tayajja zakiyi karatun" yafada yana nunata da yatsa yana sakin kanta tai baya tafadi tana dafe towel din jikinta,har yakai bakin kofa yajuyo yana kallon Veronica yace "harda kema zaki biyoni NURISTAN, you have to choose idan zama anan kika zaba babuni babu ke kuma idan kikace zaki biyewa yarki kusaba min you'll see my other side Veronica," cikeda karfin hali Veronica take fadin "I won't go anywhere,aikai ba mijina ba....." bata karasa ba yajuyo yana watsa mata manyan idanuwansa masu abin tsoron dayasa tai saurin yin shiru tana kama bakinta fita yay yana bugo musu kofa harta nanny dake kitchen akasa seda ta tsorata. da sauri Veronica tai gurin peace ta tsugunna tana kokarin rikota "my baby I'm sooor....." bata karasaba peace ta dago tana fadin "don't touch me" tamike ahankali tana rike kanta Veronica cikeda tausayi take fadin "kidena wa babanki rashin kunya,peace why won't you study what he want? Peace nagama ke karatun be dame ki ba,meye na jayayyar" kallon mom din tata tai cikeda takaicinta tafada bandaki tana kullo kofa wani irin kukane yazo mata da yasanya takasa rikewa tashiga rerawa harcikin zuciyarta take jin zafin iyayenta,dad yamaidata kamar wata dabba arayuwarta batada freedom n azabar abinda takeson tayi bayan rayuwarta ce future din tane batason tai ending up like him har abada, mom dinta kuma masifar son dad dinta ya rufe mata ido bata iya ganin laifinsa duk abinda zeyi dukda tasan ba dede bane amman don kar yarabu da ita duka bazatai magana ba,kotayi maganar bata tasiri don yafi karfinta yanzun daya fara barazanar rabuwa da ita duka duka seta sakko tabada Kai. ta rigada tasan daman batada wani gata na kulawar iyaye aduniya, amman me batason takare rayuwarta karkashin Abraham Zion ko meye kuwa ze faru bazata taba yarda tazama daya daga cikin manya manyan Christians masu evangelism ba, tayaya zata ringa kiran mutane zuwa addinin da ita kanta batasan na gaskiya ne ko akasin hakaba ta tambayi kanta? tinowa da conversation dinsu na dazu tai da EHSAAS ta lumshe ido tanajin wani sanyi yana ratsa zuciyarta for the first time tun bayan da idonta yay tozali da mahaifinta. shower ta sake sakarwa kanta,tagama tana daura towel takalli mirror gurin da bakinta ya fashe saboda marin da babanta yamata ta shafa kadan yadan kumbura Allah ya temaka batada haske yau da ita farace ta tabbatar jajir din da zeyi bazata iya nunama kowa fuskarta ba harse yawarke fitowa tai dakin batai mamaki ba ganin mommy bata fasa kwashe tsofaffin kayanta tazuba sababbi ba. bincikawa tai cikin wadanda mommy tabari nada din tasamu pajamas marasa nauyi taxira kwata kwata battason tafita ta sake ganin fuskar dad din nata hakanne yasa ta haye saman gado tana dukunkune kanta feeling so lonely tarungume pillow.

kwankwasa kofar dakinta taji anayi banza tai sanin cewa nanny ce ko mom dinta bata gama zancen zucin ba taji muryar mom din nata tashigo tana nishi kamar tadakko wani kayan gabas take fadin "my durlin bakici abinci ba kindawo daga makaranta come sweetheart zo, zo babynah kici abinci," dagowa peace tai ta ganta da tray tajero two glass balls aciki se jug akai shine take nishinnan dogon takalminta kamar yakarye takaraso tana ajjewa saman study table din peace, "Abinci peace karyay sanyi," tafada tana washe mata baki kafin takaraso tana duba gefen bakin peace din tace "it most have hurt alot baby, kidena shiga harkar Abraham kinsan cewan he is always violent kinfa girma yanzun so kike duk ya lalata maki kyakkyawar fuskarnan taki da duka,jikinki ma da badan skin products din da kike amfani dasu masu kyau ba aida har yanzun kinada tabbai ajiki thank god aikina kenan,kinga zanta beautifying skin din babynah," tankwabar da hannayenta peace tai sanin mommy din nata batta gajiya da magana kuma bazata fita adakin ba harse taci abincin ya sanya takarasa tajawo tray din tadire akasa tabude tana kallon abincin kafin takalli mom din nata murmushi tai tana fadin "I know you love it, especially the salad din I slide some avocado o the top kici kiji," ture ball din salad tai gefe ta jawo dayan ball din lobster thermidor ne, kallon Veronica dake tsaye tana jiran taji peace tayaba mata tai kafin ta mike takoma saman gadonta tana rufe kanta da bargo Veronica biyota tai tana fada, "kin ma samu nadamu dake nakawo miki abinci,shiyasa wani lokacin in Abraham na miki abu bana cewa kala peace ke wace irin yarinyace you didn't even thank me for bringing food har cikin dakinki," bude fuskarta peace tai tana kallonta kafin tace "thank you for bringing everything that I'm allergy too the great V effect,indai naci avocado I'll be lying agadon asibiti gobe iwal hakannan kinji,and for lobsters I can't even handle the smell, bakisan abinda yarki zata iyaci da baxata iya ciba amman duk wani anti aging skin product kinsani,duk wani kalar fata na duniya kina kallonshi kinsan meye matsalar sa meye yake bukata," Veronica dan shiru tai tasan peace nada gaskiya bata damu da ita kamar yajja ta damu da aikin taba amman tanason yarta har cikin zuciyarta but her career is above everything ita bata taba shirya haihuwa arayuwarta ba,saboda tasan career dinta baze barta kula da dan ba kuma ita baxatai sacrificing dreams dinta saboda yarta ba,peace just happened itakanta batasan yajja akai tadau cikinta ba,amman saboda yajja Abraham keson haihuwa yasa tai keeping din pregnancy na peace bawai don tashirya zama mom bane,tasan peace nacikin kunci batasan yajja zatai ta lallasheta amatsayin mahaifiyarta ba shiyasa taje tadibo mata abinci tana ganin kamar tamata abin kirki ashe bama tacin abinda tadibo din ita wace irin uwace she knows peace is very strong amman abin nasu yafara wuce gona da iri ganin yajja peace din tasoma kosawa da halayensu. "I'm sorry" kawai ta iya cewa peace din kafin tajuya ta nufi kofa, hakadai peace taraya aranta that's all her mom knows how to say she's sorry kuma hakan baya nufin gobema tai neglecting dinta tatafi tabarta itakuma bata iya zuciya da ita dede takai bakin kofa peace tace "mommy" tajuyo tai idonta ya tara ruwa, bude mata hannayanta tai alamar tazo tarungumeta karasowa Veronica tai cikeda farinciki don ta dauka peace din zuciya tai da ita, tarungumeta tana fadin "I'm sorry baby," "mom bazaki sake tafiya kibarni ba cewar" peace tana zubda hawayen kewar mahaifiyar tata datai shiru Veronica tai don batada ansar bata kuma battason tabata musu wannan moment din, "mom pls ko zaki tafi kitafi dani banason zama nini kadai I'm lonely and scared," "shsshsh" Veronica tace tana fadin "don't worry I'll stay alittle bit longer with you wannan karan kinji,banson inringa ganinki cikin kunci haka yata," dagowa peace tai tana mata murmushi kawai anan suka zauna don hirar Veronica kaf akan kayan kwalliyane, latest kaya,latest jakunkuna da kayan shafe shafe dai tanata bawa peace labarin celebrities dake zuwa shagunanta don shiryasu in zasuje wani events din,gulma dai take kawo mata ta celebrities iri iri,daga masu love scandals,affairs dadai sauransu. peace is a very good listener don bata iya surutu ba ita kanta tana mamakin kanta idan taga tana surutu sosai tareda Ehsaas, jin mom din taketa yi har barci ya soma daukar su duka biyun saman gadon suka kwanta peace kasa barci tai tamike don ba taga text din EHSAAS na good night da yake mata ba wayarta tazaro ahankali daga kasan pillow dinta zata duba taji motsin kamar za'a bude kofa dasauri ta maidata kasan pillow takwanta tana pretending bacci takeyi tai luf.

daga takunshi tasan cewa babantane hakan yasa takara mazewa tana jinsa yana tashin mom din nata sama sama, "V baby let's go to bed" yafada mata yana kokarin mikar da ita, ahankali mom din ke fadin "Abraham, peace is sleeping here with me she will feel bad idan tatashi taga bananan," "okay intafi kenan you choose your daughter akaina well, I have many options nima" yafada yana kokarin ficewa adakin tanajin yajja mom din tabi bayansa dasauri batasan me sukai ba sejin karar fitarsu kawai tai ta mike zaune tana kallon kofar dasuka fice cikeda bakinciki,they aren't even married ta sake maimaita abin aranta yana mata ciwo kawai ta fashe da kuka su suke aikata abin amman ita take jiye musu gaba. kusan raba dare tai tana kuka,idanuwanta sun kumbura kafin barawan barci yayi awan gaba da ita washegari daman alarm take sakawa saboda makaranta batason aringa zuwa ana bude mata kofa da sassafe da sunan tashi tatafi makaranta, tana mikewa ta kalli face dinta a mirror she look like hell, idanuwanta sunyi dark cycle alamar bata samu barci ishashshe ba, ga kumburowan da sukayi sakamakon kukan da taci gefen bakinta daya fashe yayi duhu ta manta jiya sam bata shafa magani ba. tinawa dayau zasu fara A level dinsu yasa taji kamar ta kashe kanta she hate mutane su ringa ganinta ahaka suna tambayarta menene yasameta musamman teachers nasu, tohm tace musu me? dabadan jarrabawar bama babu inda zataje agurguje tashiga tai wanka tafito ta shafa maya mayenta,tashirya cikin uniform dinta,karamar jakarta ta rataya don bada wasu littafai zataje ba saboda wayarta ta dauka tafito tana karasa zira takalmanta akofar dakinta taji motsin fitowarsu kamar tai sauri takoma ciki kuma dai sanin dole tafita agidan ya sanya ta kafe kofar tasu da kallo har suka fito,tana ganin yajja mom dinta ke murmushi tana wasa da face din babanta kamar wani yaro tana kiransa da pet names shikuma yana babbasar wa sosai take mamakin rashin zuciya irin na mamanta wllh in itace ko Abraham Zion ne autar maza ta hakura dashi sbd wulakancin dayake mata. "Babyyyy" Veronica tafada lokacin da suka hada ido tana sakin Abraham din ta karaso ta rungumeta hugging dinta back peace tai tana fadin "good morning mom," "har kin shirya ashe" tafada cikeda iyayi don Veronica irin matannan ne yan gwalli da kwalisa, "uhm" kawai tace mata tana kallon dad din daya sake hade rai ganinta dayay, Veronica cikeda concern tace "baby you look like a real mess,oh my god did you sleep well kuwa" tasoma taba fuskarta, peace cire hannun Veronica tai a face dinta tana fadin " bye mom" harta soma taka ma tattakalar benen taji yace "peace" da murdaddiyar muryarsa da zatasa cikinka yakulle don tsoro,amman peace ko gezau bataiba sedai takasa kara taka wani step din har yasakko yasameta a inda take,kallonta yay kafin ya danyi murmushin takaici yana sa hannunsa yamatse bakinta,ta rintse ido don sosai takejin zafi amman taki nuna masa, "yaushe nazama sa'anki dazaki ganni ki kasa gaisheni,peace ni ubankine I'm not a fucking sperm donor kawai, I raised you to become who you are today? har zaki wuceni ki kasa gaisheni sa'o'in kakanninki suka ganni girmamani suke ke kinfi karfin ki gaisheni ko"

yakara matse bakin nata ganin bazatai magana ba yasa ya shake wiyanta ya hadata da bango tagama kaishi karshe cikin tsawa yake fadin "talk ko ke kurmace" tari tafara amman taki gaisheshi Veronica kuka ta farayi takarasa tana fadin "Abraham let her go!meye haka she's a kid, don't kill my child," "xannuna mata cewar nina haifeta bawai ita tahaifeni ba" cewar Abraham yana kara shake peace din, "pls peace greet him kibashi hakuri,kice bazaki sake ba" cewar Veronica tana kokarin janye Abraham amman ko gezau, "peace bakyajin maganr mom dinki,why are you so stubborn" tafada tana kuka "peace pls say goodmorning and sorry to daddy for me baby, koso kike ya kasheki yahuta eh" tafada cikin fada fada se asannan peace ta risina dukda basa shiri da mom din tana jin kaunarta sosai aranta fiyeda dad din,kuma battason taganta cikin bakinciki, "Good morning Sir" peace tafada idanuwanta jajir numfashin kirki ma bata iya fitarwa, "And?" Abraham yafada yana jiran yaji tace sorry, "Sorry Sir" peace tafada ashake sakinta yay tafadi kasa atsugunne tana tari, Veronica tashiga tallafota tana rungumeta shi kuma Abraham yafice abinshi, "I'm sorry baby" Veronica tafada tana shafa bayanta da wiyanta duka,tana dena tarin tamike kawai ga mamaki na ba digon hawaye ko daya a idanuwanta se kwallar da taketa fighting kawai tasoma hada benen bibbiyu daddaya tana sauka harta karasa sakkowa tafice agidan baki daya abakin motarta taga Abraham Zion atsaye koda be fada ba tasan me hakan yake nufi makarantar su zeje donya tabbatar da tacike course din dayace din, Veronica data biyosu tsayawa kallonsu tai ganin Abraham yabude drivers sit yashige,peace turus tai kamar bazata shiga ba se kuma takalli mom din tata dake hawaye kawai seta bude murfin motar tashiga,lip din mom din tai reading tana cemata "becareful pls baby," setaji tafi tausayin mom dinnata akanta dukda baya dukan mom amman dai da wulakanci da barazanar rabuwa da ita gaba daya da yake gara ace dukan nata yakeyi.

suna isa harabar makarantar ya kalleta yana fadin "menace zaki karanta?" kanta akasa tace "theology" jinjina kai yay yana fadin "haka nakeso kisaka a form dinki yanzun zamuje ki cike kinji koh" jinjina kai kawai tai tanajin kunyar fitowa dashi akasari insuka jera mates dinta harda masu cewa suna sonshi don Abraham din bawani babba bane ba don this year zeyi clocking fourty,ga kudi ga iya gayu, kamar dasukeyi sosai cema take sawa ayarda mahaifinta be,shiyasa tatsani yawo dashi gashi he's very gentle and kind to her indai acikin public suke, yi yakeyi kamar ya hadiyeta don soyayya,shi yafara fitowa daga cikin motar seda tadan dau time harseda ya leko yana kallonta sannan tafito tana kafa wani uban black shades sbd battason malamansu suga idonta suyita tambayar meya sameta wiyanta dayay alamun anshaketa tasa scarf tarufe suka jera dashi as usual Abraham always cut ladies attention tundaga gate ake kallonsu wasu ma har gaisawa suke dashi yanata ansawa cikeda fara'a kamar bashi ba har suka karasa office din principal dinsu nan suka gaisa dashi tana mai albishir din dasuka riga sunmai awaya kan progress din peace din beyi tinanin performance dinta yakai hakaba bayan yaga grades dinta hope dinsa yakaru akanta. principal harda cemasa anya baze barmusu peace anan ba kuwa,don da alama tafara copping girgizama principal kai yay yana bata labarin shima yana son yay settling akasar sane duka, amman karta damu peace zata ringa zuwa gaisheta lokaci lokaci daga can, taji dadin hakan dayace sosai, principal dince tagaya mishi peace har tama fara zuwa gurin da ake performing plays tana kallo cigaba ne sosai saboda peace bata shiga social setting kowana iri ne dan murmushi kawai yay yana kallon peace din aransa yaraya "this is not his daughter anya bawanine ke influencing rayuwar yarinyar ba kuwa," cikeda raha yake cema principal ai peace theology zatai acan NURISTAN jami'ar Zion tashi insun koma, principal din kallon peace tai cikeda mamaki tana tambayarta ai home room teacher dinsu yace mata English lit zatai kota canza ra'ayine kallon da Abraham yamata badon tanajin tsoron saba sedon battason yahuce akan Veronica yasa tajinjina kai kawai, principal tadan jinjina kai tana fadin "what a west? peace nada talent sosai gurin rubuce rubuce da karance karance," abraham yace "karta damu zasusan yajja zasuyi da talent din tunda harta riga tacanza ra'ayinta ne," anan peace tabarsu tareda principal batasan me yake gayawa principal dinba tashiga jarrabawar ta babu wanda yay gigin tambayarta meya sameta domin ba wanda yaga fuskar yin hakan cikin lokaci kankani ta tsarge paper yau din sbd kusan komai da aka tambayesu sunyi breaking komai dalla dalla da EHSAAS,tana fitowa takunna wayarta texts din EHSAAS ne rututu tunna jiya da daddare da batai reply ba dana safiyyar yau yana tambayarta lafiya wayanta akashe,is she okay,tambayoyin duk akan yajja take ne tasoma murmushi ita kadai kawai tana rungume wayar ajikinta kamar daga sama taji ance "meye acikin wayar kike dariya?" tsabar tsoro sakin wayar tai akasa tafadi tasan wayar bata wani bugu ba sbd yanayin kararta Abraham dayay maganar tsugunnawa yay yana daukar wayar daga qasa.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment & Vote. [01/05, 12:06] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.