EHSAAS

Chapter 13

by @fatoumspassion

Mr Abraham muryar principal dake bayan sa ce taja hankalinshi daga duba wayar yajuya yana mata murmushi harta karaso. tana fadin "yayi hakuri tatare shi daman tanada wata magana dashine tamanta bata masa a office ba" juyowa yay yakalli peace da gaba daya tai kalar rashin gaskiya,yakalli wayar data fara ringing mom 2 yagani ansa asaman screen din, dukda yaga Veronica ke kira amman jikinsa yana bashi something is off,wayar ya mika mata dai kawai yabi principal gefe inda take sanar dashi "fund raising din dasuke yiwa iyayen wata yarinya da basuda karfi sunyi gobara baban baida lpy sanin Abraham din nada temako take gaya mai koshima zemusu wani abun," bamusu yakarbi account number yazuba musu kudade masu kauri principal se godiya take yace mata "bakomai take sanar dashi da wuri indai irin wannan tataso ko nawane shi ze bayar ba matsala," tace "toh zata ringa fada masa" juyawa yay inda yabar peace atsaye kawai ya nemeta yarasa yadan tsaya yana kalle kalle principal tace "koh ina yarinyar nan tai badai takoma ciki gurin kawaye ba? bari naduba ma Mr Abraham,"

Peace cikin corridor din classes ta koma tashiga goge texts din da EHSAAS yake mata,ga nitai kammar ma basa goguwa da wuri bama tasan sanda suka tara texts haka ba, EHSAAS baya wani social media apart from Twitter,babanta be yarda tai wani social media ba arayuwarta, kuma duka tanayi ba tareda saninsa ba bitai ta ringa uninstalling apps din sbd tasan dole ze karbi wayar wannan karon, baya duba mata waya taraya aranta yanzun tunda yaga she's insecure tashiga uku zeta duba mata waya kenan.

daga inda take tana hango yajja principal keta zuba mai surutu yana sauraro,tashiga call log ma duk tagoge kiraye kirayen EHSAAS din,number shi tadai saving da my sire ma tagoge yau dai daya Veronica tamata rana da badan kiran datai mata ba tasan yau da tata itada EHSAAS ta kare juyawar da zatai se taga kamar principal na tinkaro wa zata shiga inda take dasauri tai clearing abubuwan data shiga recently tasa wayar ajaka dede principal na ganinta, 'peace me kikeyi anan kinbar babanki najiran ki," peace ba abinda tace mata kawai tayo gaba principal nabinta abaya tana sake cemata "tai wa dad dinta godiya akan abinda yabayar waya mutu wayay rai" jin principal kawai take tasan Abraham nada kyauta kyautar ma wacca tacika kyauta amman me tasan bawai dan Allah yake ba yanada manufa,yanayi ne don ace shine don mutane su ya beshi suce shi mutumin kirkine sannan inyazo musu da manufar addinin sa yanuna musu cewar addininsa ne yaymai koyi daya zama hakan, fuska biyun babanta nabata mamaki at times. kallon dataga yana mata tasan na tsantsar zargine kawai suna isa inda yake yamika mata hannu tasan me yake nufi tabude jakarta tana bashi wayar tata gaba yay tabishi abaya har zuwa gurin motarta key din ya jefa mata dede nan ta hango motar EHSAAS tadanno kai zuwa cikin makarantar dake glass dinshi ba tint bane, idanuwansa ne suka sauka cikin nata itama karaf idonta akan nashi suka tsaya suna kallon juna,shi hankalinsa tashi yay sakamakon idanuwanta dayaga sun kumbura sunyi dark circle kana ganinta kasan tasha kuka kuma tana cikin damuwa ga gefen bakinta daya fashe,mutumin dake kokarin shiga gaban motar peace yake kalla,he look very young,don bazefi sa'an yayarsa mimah ba inma bata girme masa ba,he look very neat gentle and handsome amman yajja ransa yake adaure yana danna wata waya data mai kala data peace abin ya bashi mamaki kamannin dayake da peace azahiri yasa yashiga tinanin ko yayanta ne,sekuma yatina tace masa she's an only daughter,toh kodai wannan ne mahaifinta?yatambayi kansa.

peace ganin EHSAAS yayi parking yana shirin fitowa yasa tai saurin fadawa mota jikinta rawa yake tashiga yimata key, EHSAAS niyarsa yafito ya gaishesa yay introducing kanshi,kuma ya tambayi peace meya sameta amman ganin peace taja motar da gudu tayi baya yasa ya tsaya yana tina sharadin ta zasu zama friends amman no one will know especially her father dan jim yay yana tinanin yajja zega peace din dagashi se ita don hankalinsa ba karamin tashi yayba yajja yaganta yasan bahaka suka rabu jiyaba.

motarsa yaja kamar yabisu sekuma yafasa bayason yasake jama peace matsala, makaranta ya koma don lecture yake yi be gama ba yafito hankalin sa gaba daya yayi kan peace din jinta shiru yaudin,ana lectures dinma babu abinda yake tinani se fuskarta wani irin daci yakeji azuciyarsa da take gaya masa kila dukan peace din akai, akai mata haka don fuskarta bata masa kala da wacca tafadi taji ciwo ko makamancin hakanba inkuwa hakane ba uban da ya haifi peace ba ko, ko wayeshi he is ready to fight for the little girl aransa yaraya "tohm adaki peace har adaki me? yar karamar yarinya dabatasan komai ba aduniya,' yana fitowa a lectures yakoma dakinsa tsabar damuwa zazzabine yafara kamashi kawai yajawo wayarsa,yashiga danna mata kira har ta gama ringing ba'a daukaba damuwarsa karuwa tai,mikewa yay jikinsa yayi zafi zau don sam EHSAAS be saba da damuwa ba besan wani abu waishi tashin hankali ba dukda cewa shi dan sarauta ne, peaceful life yakeyi baya barin sha'anin su yadame shi,kayansa ya sauya yana daukar mukullin mota yaji wayarsa tana ringing,dasauri yakarasa ganin peace ce yasa ya daga dasauri yana sauke numfashi irin finally dinnan kamar agabanta yake,jin shiru batace komai ba yasa yace "are you okay?" "And who are you?" Tambayar da kakkausar muryar Abraham ta watsa masa ya sanya yadan dauke wayar acikin kunnansa yana kara dubawa tanata tafiya ya kai yamayar, "nace waye kai din? da kake kiran number minor teenage girl dina kana tambayarta is she okay?" "Do you have a death wish?" Abraham yafada azafafe EHSAAS jin tsawar dayay tadan buga mai kai yasa yadan tabe baki,yana raya lallai dole peace taji tsoronsa mutumin masifaffe ne ko daga yajja yake magana zaka gane,dan jim yay before cikeda nutsuwa sanin peace nagidan ze iya sake mata wani abu yasanya yace "Good day Sir I'm EHSAAS, nine tutor din Miss peace," "what?" Cewar Abraham, "the last time I checked nine uban peace kuma ban daukar mata wani tutor ba shin zakai explaining waya daukeka, kodai kune irin mugwayen samarinnan dake exploiting yaran masu kudi da sunan kuna koya musu karatu ku ringa karbe kudadensu kuna yaudaransu" shi dariyama ya bama EHSAAS amman tinawa da uban peace ne yasanya yace "no Sir, I'm sorry inhakan yabata maka raine,nafara mata karatu ba tareda iznin ka ba the girl need help naga kuma ku iyayenta babu abinda kukai akai naje taron makarantar su......" nan yasoma bashi labari iya wanda yake tinanin Abraham zeji dadin ji nayajja yaga peace din ba walwala batason karatu dayajja ya lallabata dakyar yay convincing dinta ya fara koya mata karatu, Abraham dan shiru yay aransa daman ya raya peace will not come this far batareda temakon wani ba amman afili tsabar girman kai se yace "tohm munji duk abinda kai kuma mun gode,dukda bamu muka sakaka ba, zamu duba zamu daukar wa peace best tutor,bakai da kake student har yanzun ba and for your service katuro account number asaka maka kudin ka Abraham baya karbar sadakar Non believers,nafi karfin wani kafiri ya koyama yata karatu as charity kuma daga yau kasake kiran number nan ba kaiba har iyayenka sesun kuka dakansu" yafada yana kashe wayar EHSAAS sakin baki yay kawai yana kallon wayarsa,yana tambaya "anya mutuminnan kanshi kalau kuwa,shine yakewa kafiri,shi bece masa kafiri ba seshi,yasan suwaye iyayensa kuwa dayake ikirarin sesun kuka da kansu,kuma yama fara zargin kodai bashi ya a haifi peace ba,"

for the first time yaji yanason sanin wacece peace din yanason yasan su waye iyayenta da komai da komai dangane da ita zama yay saman gadonshi kawai ya danna ma Aman kira bugu biyu Aman yadaga da alamun ma daga barci ya tashi, "Uncle prince barka da dare" yafara gaidashi bema tsaya amsa gaisuwar ba yashiga karanta masa "yanason yay bincika masa a NURISTAN akwai wata yarinya peace Abraham tana karatu a Oxford High shekarunta 17 xuwa 18 yaymai background check up mekyau akanta da iyayenta, yana bukatar hakan kafin dare" da sauri Aman dake kwance yamike yana fadin "but uncle prince wacece?" yace "wannan be shafeka ba kamin abinda nasaka kawai" da tohm ya ansa kawai, EHSAAS yakashe wayar yasan indai har mutum a NURISTAN yake kuma yanada katin dan kasa tohm wllh duk inda yake se sun bincikoshi domin yasan Aman gurin state security zeje yana cewa sakon prince ne zasu bari yaduba duk wani information dayake bukata ballema na Peace bazeyi wiyaba tunda hartana fitowa kasashen waje.

Daga bangaren peace kuwa Abraham be tashi bata wayarta ba se da daddare ya kirasu yace tare zasuci abinci nanny nagama jerawa tatafi tabasu guri peace na gefenshi Veronica na table din dayake facing dinsa tanaci tana zuba surutu,tana sanar da peace din abubuwan fashion,turo mata wayarta gaban ta yayi yana kallonta bece mata komai ba illa "I've changed the SIM card, the next time that tutor called....Peace Abraham Zion" yakira full name dinta data mugun tsana yace "I will get rid of him nayi miki alkawarin hakan kowaye shi sena daidaita rayuwarsa," peace rawa jikinta yashiga yi domin ta tsorata sosai da mahaifinta tasan kalar rashin imaninsa ita inze tsaya a ita kadai ba abinda zataji tasan duk tsiya baze kasheta ba amman EHSAAS fa EHSAAS yace mata scholarship ma yasamu a balliol idan babanta yaymasa sanadi yarasa tafa? idan babansa yabisa har NURISTAN yacutar fa? she will never forgive herself babu abinda EHSAAS yay mata se alheri tun haduwarsu don haka she won't be the reason daze saka EHSAAS cikin matsala.

Veronica data kasa fahimtar abinda Abraham din ke cewa yasanya take tambayarsa "waye haka?" murmushi ya shigayi yana daurawa peace ganyayyaki saman abincin ta,peace hate veggies kowana irine yana fadin "eat," kallonsa take cikeda tsoro tashiga dibar abincin tanaci dukda wani irin amai dayake taso mata seda tai rabi taji cikinta najuyawa dasauri tanufi sink,tasoma kwara amai kamar yayan hanjin cikin ta zasu fito Veronica tamike zataje ta temaka mata Abraham yariketa yana murmushi yake fadin "V baby baki gama cin abincin kiba go back to your sit," idonta yakawo ruwa tana fadin "peace hate veggies why did you...." Kallon daya watsa mata yasa ta hadiye sauran kalamanta,murya azafafe yakalli Veronica yana fadin "the next time aka boyemin wani abu ko akaje behind my back ana wani abu, tohm ba veggies zanyi feeding mutum dashiba poison zansa in kashe yaro ba abinda ya dameni kuma nakashe banza" sosai Veronica ta tsorata da barazanar tasa peace tajuyo tana kallonsa da gwara gwaran idanuwanta kawai ta fashe da kuka tana nufar sama aguje,wani iri sanyi yaji aransa finally he won,don indai yaga peace nakuka irin haka tohm bacin ran data shiga yakai kololuwa don sosai ya kejin zafi ingaya yamata abu batai kukaba amman ganin kukanta ransa yay fess,yafice abinsa.

principal yakira yana tambayar ta "waye mutumin dasuka kira yaywa su peace panel talk last two month" dan jim tai kafin tace masa "wani marubucine, me ilimi sunansa Mr EHSAAS," yanajin sunan yaaji yakara tsanar yaron don yasan sunan musulmaine amman don yakara tabbatar wa se yace "dan wana addinine principal? dan jim tai before tace "Islam don nagani a bio dinshi," yace "tohm ki kirashi kigaya masa yarabu da yarinya ta idan ba hakaba, ba balliol ba I'll make sure besake taka kafarshi a Oxford ba har abada" yana karasawa ya katse wayar principal cikeda mamaki da tsoro tashiga kiran EHSAAS alokacin yana kwance yana jinyar kansa don sosai damuwar peace ta lullubeshi har zeki daukar wayar amman tinanin ko Aman ne yasa yadaga yana kallon screen din baida number ta,don haka kmr kar yadaga sekuma yadaga,yanajin muryarta ya ganeta cikeda concern take tambayarsa "ya yake?" yace mata " lpy," tace mai "meye ya hadasa da peace?" dan shiru yay kafin yace mata "meya faru?" nan tashiga yimai gargadi tana cemasa baban peace babbane sosai kuma bayason ana kulamai yarinya, koda temakon nata zeyi da karatu yafara neman iznin Abraham din first Mr Abraham mutumin kirkine ta gayawa EHSAAS amman baya wasa da abinda yashafi peace yace kafita harkar peace inba hakaba he will ruin you EHSAAS" "thank you" kawai yace mata yana kashe wayar yatashi zaune kawai yana mamakin mahaifin peace, "shize aiko akema barazana lallai he is playing with fire,shifa ba tsoronsa yakeji ba kawai ze raga mishi ne darajar haihuwar peace," ganin lokacin sallar magrib yayi ya sanya kawai yamike yashiga bathroom yadaura alwala yafito,anan yatayar da sallar magrib ya idar yafara azkhar seda ya kammala yamike yafada bathroom yay wanka da ruwan dumi,yadauro alwalar isha'i yafito.

wayarsa yaji tana ringing ya karasa yana dubawa number Aman ne, dagawa kawai yay yana tambayar "what's the update?" Aman yace "uncle prince the only peace da muka samu da irin surname dinnan kuma tadace da description dinka itace Peace Abraham Zion yarinyar shugaban Christians na NURISTAN baki daya," "what?" EHSAAS yafada yana dafe kirjinsa da yaji yabuga da karfi yasoma girgiza kai "no ba peace dinshi bace, peace bazata kasance tafito daga jikin arnen nanma,makiyin Allah" har yanzun yana tina maganganun da aman yagaya mai akan mutumin ranar daya sauka a NURISTAN a mota, Aman yace "tohm itace dai kadai akasamu da wannan sunan kuma itace take karatu anan Oxford high school (GDST) sbd babarta yar can ce,itakuma mahaifiyar tata yar kasuwa ce me shahararran beauty Parlours dake all over the world da ake mai take da the V effect,baturiya ce ta asali mahaifiyarta,ance yarinyar is isolated from everyone tun tana karama ma ba'a ganinta,itace only heir wa family din Zion,kuma ita ake expecting zata gaji komai na mahaifinta nan gaba," rasa abin fada ma EHSAAS yay,yakasa gasgata maganar, ahankali yace "Aman bashine kacemin yana batar da mutane a NURISTAN yana sakasu a Christianity ta hanyar basu abin duniya ba bashine kake cemin target na mai martaba ba" yace "tabbas hakane,shida mai Martaba afili basuda matsala sbd mutumin shegene ya iya siyasa biyayya yake sauda kafa amman taciki naciki shifa so yake kowa a NURISTAN yakoma arne, nacema mutuminnan me martaba yace yay nisa baya jin kira yanxun haka mai martaba yana keeping low-key ne kawai akansa sbd dokar kasa data bawa kowa damar yin addinin sa, lefi daya mukeso yayi muruguza duk abinnan daya gina amman shegen kamar yasani yakiyi,Mai martaba ko sunansa yatsani yaji an ambata" duk da haka EHSAAS kasa yarda yay yace masa "ya turo mai da komai da komai ta eMail zeduba" yace "tohm" yana kashe wayar.shiryawa yafarayi aransa yanajin indai hakane aikin dake gabansa bawai karami bane babbane kuma ya daura dammara ta hanyar jawo hankalin peace takarbi musulunci ne kadai zesa mutanen da idonsu ya rufe sukebin pastor din dukda yace ba sunansa pastor ba sauda kafa sugane cewa karya yake musu indai har yarsa zata bijire masa tohm why not su.

sallar isha'ee ya farayi bayan ya idar yajawo laptop dinsa yashiga dubawa Aman yaturo masa duk wasu information daya samu akan peace din harta da elementary school din datai a NURISTAN,da hotunan ta dukda yawanci bata saniba ma akamata su din wasu tareda babanta wasu kuma ita kadai,bugawa kanshi ya farayi daidai nan Noah yadawo daman kwanansa biyu gidan budurwarsa a London se yau yake dawowa, EHSAAS baya barin Noah yakawo musu mace daki shiyasa koda yaushe bayanan don baya iya wuni batareda yarinyar ba kullum yana tafe zuwa gurinta. duk yajja yaso suyi wasa da dariya da EHSAAS din ganin EHSAAS kamar bayajin dadi yasa ya kyaleshi kawai,rnr da ciwan kai ya kwana seda asubah Noah ya ankare baida lpy ganin betashi yayi sallah kamar yajja ya sababa don dukda noah arnene yasan yajja EHSAAS baya wasa da lokacin sallah tashinsa yay da kansa ya temaka mai yashiga yay alwala yafito ya daddafa yay sallah yakoma ya kwanta noah bayajja beyi dashiba suje asibiti yace shi bazashi ba he will be fine soon,har kusan yamma yana zazzabi ga ciwan kai duk ya rikesa ga kirjinsa da kemai zafi se dare noah yakira masa likita ya dubashi har cikin dakin,allura yay masa ya bashi magani,kwananshi biyu akwance Noah yana jinyarsa,yan mata kuwa tunda sukaji baida lpy suka soma jeran kawo mai kayan dubiya,flowers ne cards ne ga sunan iri iri na get well soon dukda inzasu mutu suna buga mai kofa baze budeba har suyi sugama sa arsu daya Noah kan dan basu update kan jikin EHSAAS din.

Daga bangaren peace kuwa gaba daya rayuwarta takoma kamar da saboda presence din iyayenta dukda suna tareda ita amman she's very lonely bame zama da ita yaji matsalolinta acikin su sedai suna zama Veronica tasoma bata labarin beauty levels dinta. shikuma babanta yayta jaddada mata karanta theology da zatai,wanda tinawa da hakan kadai yana sanyaww taji tadena sha'awar cin jarrabawar amman seta tina "She have to do it not for him, but for EHSAAS saboda ita dashi worked hard for it" tasha attempting kiran wayarsa sbd daman ta rigada ta hardace amman bata taba bari tayi dinba sbd tasan Abraham is very smart baze taba dawo mata da waya haka kawai ba tareda yasaka abinda zeyi monitoring dinta ba,hakanne yasa ta caje wayar tsaf tagano inda ya boye spying app aciki batareda sanintaba gashi ba damar tagoge don tana gogewa ze ankare.

yanxun babu inda take zuwa daga makaranta se gida kasancewar jarrabawa suke Abraham kamar yasan fakonsa takeyi taje gun EHSAAS kullum tana gama exams akofar hall take tarar dashi yace "su tafi gida" tasan EHSAAS ya nemeta kila harya gaji,yaudai saura exams daya ta kammalla,kuma tun dare taga mamanta nata hada musu kayan tafiya NURISTAN sosai tashiga kunci da damuwar hakan,hakanne ya sanya tasamu tasaci wayar mom din tana can tana shirye shirye tadanna kiran EHSAAS din harta gama ringing be daga ba tasake kira tana jeka kadawo a bandakin data shiga takulle take fadin pick up! pick up! pick up! dagawa taji anyi amman ba muryar EHSAAS bace ba,muryar wani ce daban, cikeda takaici tasake duba lambar taga dai lambar EHSAAS ce, straight tace masa "ina me wayar yake?" yace mata "barci yake" tace "barci kuma at this time," yace "eh ai beji dadi bane kwana biyu he is sick," dan waro ido tai hankalinta na tashi take tambayar "meya sameshi" Noah murmushi yay aransa yace shegen kaya ashe EHSAAS nada girl yake boyemin,cikin exaggeration yake fada mata "ai ko numfashi ma dakyar yakeyi, he is very sick," "sunkaishi asibiti" tashiga tambayar Noah idonta nacika da kwalla,yace mata "A'ah amman likita yazo yaduba shi amman dai abin ba sauki" peace kuka tasaka kawai, Noah yashiga mamaki she sounds like a kid aransa yaraya,kuka kuma daga yar maganar nan lallai tanason EHSAAS dayawa, "Zanzo inkaishi asiniti dakaina" Tafada tana shashshekar kuka, jin motsin kamar za'a shigo yasa peace takashe wayar da sauri kwankwasa kofar toilet din taji mom dinta nayi a aljihun jeans dinta tasaka wayar tana wanke fuska tabude.

tana kallon mom din dake kallonta tace "peace are you okay? naga kinshiga ciki kinyi shiru" jinjinawa mom din kai tai kawai tazame tadawo cikin dakin mom din cigaba da bata labarin data tsaya tai tana karasa hada kayan nasu ahaka peace ta lallaba ta ajje mata wayar tata bayan tayi blocking number danma karya sake kira ta goge ta ajje,amman hankalinta ko kadan baya kan hirar maman na ta sotake kawai taga EHSAAS. Washegarin ranar wani meeting din gaggawa ne ya tasoma Abraham zuwa London hakanne yasa yace Veronica takaita school ta jirata harta gama tafito, Veronica tace masa tohm kawai,don tanada abinyi bazata tsaya gadin budurwar yarinyar da zatai eighteen this year ba ta raya aranta amotarta ta dauketa takaita har cikin makaranta tace "mata inta gama takirata zata dawo tadauketa" da tohm kawai tacewa mom din tana tinanin yau kam sa'a a hannunta take domin babu abinda ze hanata zuwa ganin EHSAAS sede dad ya kasheta inya gane hakan.

Saboda tsabar son taje taga EHSAAS cikin hour 1 ta kammala jarrabawar tata gaba daya tai sign out tafito wayarta takalla ta kasheta gabaki daya bayan takashe GPS tana fadin "I'm coming to you sire,don't worry, I'll take care of you!"

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment & Vote [02/05, 18:34] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.