EHSAAS

Chapter 14

by @fatoumspassion

(Dorm)

Peace cikin sauri tashiga tafiya ta jawo hular katuwar rigar sanyinta ta rufe kanta sinkif haka tafito kofar makarantar. don tafi sauri ma cab tatare ta kaita har bakin dorm din su EHSAAS dake balliol ta tsaya tana kallon tsohon building din,batasan room number dinshiba ta yaya za'ai ta ganshi?ta tambayi kanta tana ganin student na kai komo damasu shiga da masu fita kuma duk maza ji take kamar takoma amman me bazata iya komawa ba tazo this far dolene taga EHSAAS Kafin takoma, kusan minti goma tabata agurin tana tinanin tashiga ko karta shiga,kafin taji wani matashi daga bayanta yana fadin "hello pretty girl! mekikeyi anan? juyawa tai suka hada ido da wani bature dan guntu don ita kanta tafishi tsayi yana mata murmushi yana kare mata kallo hade ranta tai tana sake damke hannayenta dake cikin aljihun rigar sanyinta tace masa, "EHSAAS! I'm looking for EHSAAS kasanshi ne? dariya ya farayi yace "the prince charming ko? this way kiduba stair XII room 38," yana nuna mata Hana "bansan cikin yan matan nashi ashe harda highschoolers ba" yagama fada yana juyawa, "cikin yanmatanshi?" ta maimaita aranta tanajin wani daci kenan yanmata gareshi harda yan dormitory dinsu suka sheda amman dai she won't judge him not yet kawai tashiga dorm din tafara tafiya tana kalle kalle,kowa sabgarsa yakeyi amman ganin yarinyar cikin uniform yajawo hankalin samarin kanta,se dan kallonta suke data hada ido dasu sesu dauke kai don ya wanci yanmatansu college student suke kawowa bawai kananun yara yan high school ba don su gani suke dating high school girl kamar ma child abuse ne, harda masu labewa don suga inda yarinyar zata shiga akofar tana zuwa benen su EHSAAS room 38 ta tsaya. Ahankali tashiga knocking fitowar EHSAAS daga wanka kenan yana sanye da white bathrobe ajikinsa yana goge kanshi dawani dan karamin farin towel yaji ana knocking kofar gently yasan baze wuce daya daga cikin yanmatan Margaret hall dasuke zaryar zuwa gunshi ba hakanne yasa yay banza don in Noah ne yanada key base ya buga ba,bugawan ta cigaba dayi wani black guy da yazo wucewa kana ganinshi kaga black American,yake gaya mata "ga rama tahakura takoma indai EHSAAS ne baya barin mata shigar masa daki baze budeba," yana karasa yabude dakinsa dake gefen na EHSAAS din tashige, ta danji dadi saboda maganarsa ta wanke wancan wanda dayan guy din yay mata awaje,kara kwankwasa wa tashiga yi kafin ahankali tashiga fadin "sire is me! open the door," kamar daga sama yana ciro kayanshi don niyyar sa yau yaji dadi zeje gidansu peace ayi wacca za'ai kome Abraham Zion zemai sede yay masa amman se yaga peace din, "Is that peace?" ya tambayi kanshi yana kallon kofa yar karamar muryarta yaji ta kara cewa sire aibesan sanda yay saurin karasawa bakin kofaba harze bude se kuma yakalli kanshi, "is not right taganshi ahaka,he us half naked" dasauri yashiga fadin "I'm coming peace 1 min" ya karasa dasauri yana zaro wata farar jallabiya kawai yazira yana bude kofar dasauri ita dince kuwa,itama kallonshi ta tsaya yi har yafada fuskarsa ta kara haske grey eyes dinnan sun dan shige ciki ciki alamar wanda yay jinya ga gashinsa ma yataru he need hair cut sosai don yanada gashi sosai,sire tafada ashagwabe tana karasawa gabanshi daf dashi kamar tashige cikinsa amman dai bata taba shiba fuskarshi take kallo tana dada karemai kallo wani irin kyau yasake mata, "yajikin naka?" ta tambaya tana daura hannayenta saman wiyanshi wani irin yirr dayaji ajikinsa yasa yay saurin kaucewa yana fadin "I'm fine peace! what are you doing here?" "sire I miss you, nakira jiya ancemin bakada lpy, hankali na yatashi meyake damunka uhm?" tatambaya tana tsareshi kamar wata mamarsa ganin mazan na lekowa suna kallon peace ya.sanya ya hade rai yana fadin "come in" juyawa tai taga masu kallon nasu sunyi saurin dauke kansu tashiga yana rufe kofar. tatsaya looking very nervous kana ganinta kasan this is the first time data taba shigowa male dorm,shikuma haushin kallonta da sukeyi yake yakalli jikinta babu inda yafito ko ya dameta a uniform dinta daze nuna ta hakanne yasa ya danji sauki sauki aransa, "peace meyasa kikazo nan what if kika bata or something bad happened I don't want you to be roaming around alone" dan murmushi tai tana karasawa saman bedside drower dinshi kamar wata likita tashiga duba magungunan da aka bashi,tana fadin "babu fa wanda ze cinye maka ni,nasaba da area dinnan is like my second home don't worry bazan bace ba," tana fada hankalin ta nakan magungunan karasawa yay yana fadin "come let me take you back, banson kina zuwa dakina haka is not right peace we are both adults," murmushi tashiga yi tana kasa gane abinda yake nufi tace "tohm ai kaine I trust you nasan you won't hurt me sire" tafada tana tambayar sa "kaci abinci? kasha magani? alamun bama tadau maganarsa serious ba sosai ya kejin zuciyarsa tana tabuwa sbd the kind of trust data bashi yayi alkawari shikuma he will try his best to control kowana kalar feelings dayake dashi akanta harse yazamar mata example dazatai sha'awar shiga addinin daya koyar dashi hakan. "My sire Kaci abinci? tasake tambayarsa tana nufar dan karamin kitchen dinsu,bin bayanta yay yana kallon ta cikin mamaki yake tambayar ta "in banci abinci ba girkamin zakiyi," hannu tasa cikin baki irin tinanin nan se kuma tadan dafe kai tace "matsalar ban iya dafa abinci ba sire, amman nasan kai ka iya guide me sena da fama" dariya yashiga mata shi aduniya bayan hada coffee meya iya,shi ada ko hanyar kitchen ma besani ba komai yimai akeyi zuwansa Oxford yasa yadan iya yin coffee kuma shida espresso machine yake amfani,gashi baya iyacin abincin dining hall na school shiyasa, kullum akwai restaurant din daya biya suke kawo masa abinci har dorm din,inkuma yagaji dacin nasu yafita yanema. girgiza mata kai yay yace "we are equal kinga kitchen dinnan is Noah's nibana komai acikin sa," dariya tafara mai "wai kato dashi be iya girki ba abin kunya," yabude baki yay sekuma yarufe yana jinjina kai kawai yace "ai girki na mata ne ita bemata dariya ba seshine zatawa dariya," kuri tafara mai "wai ita inta girma aizata iya" zagayeta yashiga yi wai wana girman zata kara bayan wanda tai,tace mai "aizata kara tsayi ta kamoshi itafa bata gama tsayi ba," girgiza kai yashiga yi yana cemata "iroko tree kawai zata zama shine yasan tayi tsayi," Dariya shida ita suka farayi yajja kasan basuda wata damuwa aduniya. tace mishi "are you sure your okay" ganin yana murmushi kamar lafiyarsa lau,batasan he is feeling very down ba amman wllh ganinta kawai dayay dinnan yay cheering mood dinshi,yace mata "karta damu he is fine yafa warke wai waye ma yace mata baida lafiya" labari tashiga bashi takira jiya wani ya daga yace "he is very very sick" tadauka zatazo ta ganshi ko tashi baya iyayi,yace "that most be Noah shifa yadage wai se yaga budurwa ta peace yadauka I'm dating you," dariya peace tashiga yi tana cewa "tohm itama fa tanason taga budurwar tashi yanuna mata ita," dage nata gira daya yay yana fadin "really kinason kiganta ta?" jinjina kai tana barin murmushin fuskarta, "zannuna miki ita yanzun,but promise me bazaki kishi ba" yafada yana karasawa gaban wani babban mirror adakin inda suke dressing kansu,turo mishi lips gaba tafaryi irim cikeda rigimar nan duk yana kallon ta tacikin mirror din "come" yafada yana yafito ta da hannu, kamar bazata karasa ba,sekuma takarasa tatsaya agaban shi tana kallonsa yace "look at the mirror" kallon kanta tai cikin mirror din yace mata "this is the reflection of my girl," juyawa tai tana kallonsa dage mata gira daya yay irin yadai dinnan kawai seta sa hannu tana rufe fuska tashiga girgiza kai. shima EHSAAS din murmushi yake yana mantawa da duk wani problem da yake kokarin tinkara akanta,he just knew she's worth it deep inside,bata ankaraba taji saukar muryar sa cikin kunnanta cikin sanyi yake tambayar ta "meya sameta the other day?" Shiru tai tana dena dariyar don tasan ranar daya ganta da babanta a school yake nufi, "peace meya faru waye yadake ki?" shiru nanma tai babu answer, "peace do you trust me?" ya tambaya still cikin kunnanta maganar sa har ratsa zuciyarta take tanajin concern din behind his Voice,jinjina masa kai tashiga yi, "tell me? hakan yana faruwa often yana dukanki akai akaine," girgizawa EHSAAS kai ya shiga yi donta fahimci yagane babanta ne ya daketa, "peace open your eyes ki kalleni" yafada yana dawowa gabanta jitai takasa yamata kwarjini yacika gabanta,tanajin numfashinsa yana sauka ahankali saman face dinta, kamshin daddadan turarensa nashigewa har cikin kirjinta "peace tell me?" Ya sake tambaya,wasu irin hawaye masu dumi taji sunzo mata idanuwa dasauri tashiga kokarin shanyewa tana fadin "I'm okay! is okay,baya faruwa often unless I provoked him,you know how stubborn I can be at times," aransa yaraya being stubborn doesn't mean yaringa dukanki amatsayin ki na diya mace yarinya karama irin haka,mace fa darajane da ita. amman afili se yace mata "he called me!" se asannan tabude idanuwanta dasukai jajir tana kallonshi, "meyace did he scared you off, I'm sorry sire,duk ni najama ka but......" shsshshs yafada yana saka idonsa cikin nata wata irin nutsuwa ce tazo mata "I'm okay, I'm more worried about you peace" yafada yana lumshe ido kafin yace "come" yana yin gaba tabishi abaya gefen gadonsa yanuna mata dakenan very neat kamar ba yanzun yatashi akaiba tazauna yajawo stool din mirror shikuma yazauna akansa,yana fadin "he just warned me nothing more," tasan is not just warning kodai babanta has something to do with EHSAAS sickness ta tambaya acikin zuciyarta? "Don't worry peace your dad isn't that scary" yagaya mata hakan don yaga gaba daya she's tense, "Sire please tell me,what did he said exactly?" tana tinawa da barazanar dayay mata akanshi,girgiza kai yay yana fadin "nothing much kawai yace indena kulaki ne and you know that's impossible I can't breath properly without now," kasa dakanta tai yana ganin yajja hawayen yashiga zubo mata yace "peace don't lie to me,mekika mishi yabuge ki haka," girgiza kai tai tace "is nothing sire,kawai yace inyi theology ne nikuma nace English lit nake so shine yay fushi,nima nai fushi ban gaisheshi ba amman befa dakeni ba kawai dai ya mareni ne se wiyana d...." itakanta batasan lokacin data fara kokarin gayamai yashake wiyanta ba, "me yasamu wiyan naki?" ya tambaya yana kallon wiyan nata dake cikin katuwar high neck rigan sanyin, "open it let me see" girgiza kai tashiga yi tana fadin "yagoge Sir don't worry mom applied the best products for me tabo baya zama ajikina," "Peace let me see it" yasake maimaitawa with a serious tone datasan bazata iya musa maiba ahankali tashiga balle buttons din rigar yadan kauda idonsa gefe don bayason idonsa yacika kallon jikinta, musamman tsayayyun kirjinta dasuka fito nan dass tasaman farar t-shirt din ta,ga kamshin sassanyan turarenta da yake shigr masa har cikin kirjinsa yana neman rikita masa nutsuwa, "sire" yaji tafada ahankali lokacin data gama tai noticing baya kallonta,ahankali yajuyo yana examining din wiyanta daga inda yake zaune har flash ya kunna yashiga duba fresh smooth dark neck din nata,ta rintse ido because she's really feeling it, shikansa don tabbatar da lafiyarta yake hakan bawai don yanaso dinba,jinjina kai yashiga yi tabbon yafita saura kadan,aransa yace shake wiya ana zaune kalau kasheta yakeson yi ko meye lallai Abraham Zion zalincinsa yawuce duk inda yake tinani da hasashe, tohm kodai peace ba yarsa bace amman kamannin dasuke aiduk inda ka gansa kasan shine ubanta. "maida rigarki" yafada yana komawa gurinsa yazauna,yana sauke numfashi yau da wanine yaywa peace haka bawai uban da ya haifeta ba wllh dase inda karfinsa yakare amman shi kansa Abraham wannan ne last time daze sake daura hannunsa akanta shi zeyi maganinsa in yafi karfin kowa zenuna masa shibefi karfinsa ba. "peace kinajina" yafada yana kallonta don yanason tabashi dukkan attention dinta, "never ever allow him to dictate your life,iyaye ance mumusu biyayya amman babu gurin sabawa mahalicci peace kinason ki kara dulmiya cikin Christianity kimutu acikinsa ne?" dasauri tashiga girgiza kai yace "peace I know you like my religion deep inside,but your not very sure, kisani I'll never ever allow you to convert or even force you harse kinzama 100% sure cewan kinaso kiyi peace,saboda la ikraha fiddeen, amman indai harkika amince zaki theology you'll become like your dad kinason kizama jagorarsu ne kema,jagorar batattu" da sauri tashiga girgiza kai,yace "you love literature, I can see the passion you have for it don haka kada kisake kiyarda ki karanta theology is your right to study whatever you want peace, I'll help you get admission in federal open university NURISTAN I'll sponsor you idan shi abaze yiba, I'll take care of everything your admission your tuition fee, everything peace" dan jim tai kafin tace "but sire I can't say no to him," yace "kina tsoron yakara bugarki kome?" Girgiza kai tai tana fadin "bana tsoron dukan shi impact nasaba dashi ammn I can't let him hurt you,he....." seta tsaya kafin tacigaba "he promised me zeyi hurting naka idan har nasake kulaka ko namai wata gardamar," EHSAAS kanshi yashiga shafawa yanajin tsanar Abraham na samun gurbi cikin ransa yanzun wannaan yar karamar yarinyar yakewa barazana akanshi don yaga tana sonshi ta damu dashi yakalleta yana fadin "peace don't worry about me? Baze iyamin abinda Allah bemin ba peace,peace I'm telling you this saboda kada yamiki wata barazana dani ko akaina kidauka," dasauri tashiga girgiza kai tana fadin "bakasan Sir na bane he has power sire all over NURISTAN he has connections he can easily ruin you in yanaso banson family dinka da basu jiba basu ganiba yazo yay musu wani abin," jiyay takara shiga zuciyarsa look at how worried she is for him and his family dabama tasan suwaye ba yarinyar nada zuciya mekyau sosai,he always sees the good in her, "Peace pls don't worry about me? nagaya miki babanki can never and will never ever do anything to me ko anan balle aje can NURISTAN, kawai dai ni yanzun inason kimin wani abune ki kula dakanki do not tell him your not studying theology tinda kina tsoro, you can study literature from home, kiringa xuwa jami'ar daya saki but close your brain karki bari karatunsu yashiga impact zansa miki abubuwan dazaki ringa yi dawaya a ajin in ana karatu,sannan idan yakara tabaki call me, I promise you I'll be there for you koda we are thousands miles away from eachother, I'll go against your father peace thats how much you mean to me," dan zaro ido tai tana kallon shi anya yasan waye Abraham Zion kuwa shidin zewa yi fito nafito dashi,shidinne zatai makaranta biyu yakasa sani, "but yasa spying app acikin wayata he can see whatever I'm doing sire," tafada tana ciro masa wayar murmushi yay yana fadin "I got that covered," wayarsa yadakko yana fadin "take it with you, akwai sim dina aciki bana amfani dashi whenever you have chance ki kirani peace,we will be communicating through this phone" karba tai tana murmushi take fadin "really sire" yajinjina kai yana fadin "karki bari dad dinki yagani kinji," jinjina kai tai tana fadin "what about you? dawanne zakai amfani," murmushi yay yana fadin "I'll get one inna fita anjima, when are you leaving for NURISTAN?" Dan jim tai before tace "probably tomorrow tunda nagama exams yau," sosai yaji babu dadi aransa amman afili se yace mata "have a safe flight hang in there kinji, kijirani harse nazo,and I have something for you," littafan Al Aqidah al wasitiyyah na ibn taymiyyah littafine dayay magana akan prophethood din annabi isa da kuma rejecting concept din din zamansa dan Allah kamar yajja kafirai suke fada,sannan yahada mata da stories of prophet na ibn kathir daya bada tarihin annabawa tundaga annabi Adam A.S har zuwa annabi Muhammad S.A.W,sannan ya hada mata da al sirat al nabawiyyah na ibn Hisham da Al Aqidah al tahawiyyah na ibn tahawi duka masu fassarar turanci ne, yabata yana fadin "make sure you read this kullum kafin ki kwanta barci,inkin tashi dasafe ma kullum kiringa karantawa, acikin wayar mA akwai apps na tafsirin al Qur'ani na ibn jalalyn,anyishi dalla dalla in simple language dakowa ze fahimta akwai na ibn kathir ma peace kiringa dubawa kinji, you'll find all the answers you have acikin littafannan akan addinin musulunci danaki addinin ma, nasan you'll have free time sosai kafin kifara school duk inda kikeda tambaya call me, duk abinda yashige miki duhu zanmiki bayani,inason suzam sune abokan hirarki har zuwa lokacin da zuciyarki zata gama kwantawa da shiga addninin musulunci"

jinjina kai tashiga yi tana kallonsa yadau jakarta yazira mata littafan yana mata murmushi. Jitake kamar karta rabu dashi kamar insuka rabu sunrabu kenan bazata sake ganin shiba ganin time naja yasanya yace mata "she needs to go back now, sbd kar anemeta lokacin gama jarrabawar su yakusa" duk yajja tace mai "zata iya komawa dakanta" kiyay ya hanata,dakansa yadakko car key suka fito ajere sun bala in dacewa da juna sosai. adede kofar hostel din suka hadu da Noah da yatsaya yabude baki yana kallon EHSAAS, EHSAAS din da yabarshi yana barci yanata kudundunewa abargo wato mace tazo har ya tashi yama fito zeyi tuki shegen kaya, yaraya aransa ashedai duk ustazancin mutum mace kan lankwasa shi, "my friend" yafada yana dafo kafadar EHSAAS dayaci serious yana basarwa don bayason ya yarfashi gaban peace din, peace najin muryarsa ta gane shine wanda yadaga mata hankali jiya,itama tai kicin kicin tana kallonshi, "you most be the lucky girl" Noah yafada yana mikawa peace hannu,irin sugaisa dinnan peace da zuciya daya tamika zata bashi ganin abokin EHSAAS ne wani kallo da EHSAAS ya bugama Noah yasa yay saurin dauke hannunsa yana fadin "take care of him well" yay saurin shigewa yanawa EHSAAS dariya don yaga zallar kishin yarinyar atareda shi aransa ya raya shege EHSAAS dole yarikice yaga yarinya karama full option,wannan ya zata kasance in tagama girma kenan don peace akwai dirin jiki tayajja duk namijin daya kalleta seya kara.

Warming motar yay ba tareda yakalli peace ba cikeda taushi yake fadin "this should be the last time da zaki sake kokarin hada any form of physical contact da namiji apart from your dad shishi kadaine muharraminki," dan kallonsa tai looking confused take fadin "but he is your friend,his just friendly and nice," kallonta yay yana buga mata hararar data sa ta hadiye sauran kalamanta, "maimaita abinda kikace?" yafada yana tsareta da grey eyes dinshi girgiza kai tashiga yi ganin fada yakeji tace "bance komai ba nadena tohm," cikeda shakkarsa "wow wllh yana bala'in so yaga yayi fushi ta rikice haka ba karamin burgeshi take dada yiba saboda that shows how much take sonshi da batason bata mai rai,," motar yaja suka fara tafiya yace mata "peace addinin musulunci yayiwa mata hani da hada jiki da wani wanda ba muharraminsu ba,maharim dinki kuwa sune your father,your husband,your uncle,your son ko kuma nephew dinki, peace saboda Allah yakillaceku ku mata abin sone komai naku al aurane,ko jikinki akwai inda maharraman dana lissafo miki bako ina zasu gani ba inkinkai wasu shekarun yanzun dai kamar ke idan ba lalura ba akwai wasu gurare na jikinki dabe kamata mahaifinki ko dan uwanki,ko danki sugani ba amatsayinki na ya mace mijinki ne kawai bashida shinge komai ze iya gani tundaga gashin kanki har izuwa tafin kafafuwanki," dan jinjina kai kawai peace tai alamar taji,yayi tinanin zatamai tambaya se yaga tayi shiru. Dan leka fuskarta yay before yace "My p haushina kikaji namiki tsawa ko?" Yatambaya yana marairaice mata fuska,girgiza masa kai tashiga yi,tana kallonshi da wannan idanuwan nata masu kashesa, "tohm say something kinyi shiru,my pipi" Yafada cikeda tsokana,turo mai baki tai tana fadin "Nibanson pipi,sekace wata alawa kadena fada" Dariya yashiga mata ganin yasata maganar data ki yi "Tohm bakisan kinfi alawa zaki agurin EHSAAS ba,kinfa shige zuciyarnaan kinmamaye har can ciki" yafada yana dage mata gira daya dayasa tai saurin dauke kanta "Nikadena baruwana" Tafada cikeda shagwaba irinta kuruciya "Oh nima menai aibakiji nace komai ba ko" Yafada yana kallon hanya, "Gashinan kana ta wani dage gira kana wani abu da fuskarka ni banson yanasawa inji wani iri" Dariya yashiga mata jin shs can't even express abinda takeji towards him innocence dinta na bala'in burgeshi,kuma yasan batasani dinbane, "Tohm gwadamin inga yanakeyi" Yace mata yana kunshe dariyarsa Kallonshi tai tana fadin "Gashinan kana kumayi,your hair is long muje aski sire" Dan taba gashin kannashi yay da fuskarsa kafin yace "Kinga duk laifin rashin kine,tohm kenakewa kwalliyar dabakinan kuma wazanyi wa" Gani yay kawai takifa kanta cikin cinyarta tana blushing, Shima blushing dinyake yana dariyar yajja take yi din kamar wata budurwar kauye, "Mena kumayi?" Yatambaya yana shan corner,dagowa tai tana mai hararar wasa Taturo baki tana fadin "kana sane kakeyi" tana nuna fuskarshi inda dimple dinsa ke lobawa, "And you love it" Yafada yana biting lips dinshi nakasa, Yana kallon yajja ta harareshi amman yana juyowa seta basar tacigaba da kallon titi yay murmushi kawai yana girgiza kai "Zanraka kafa aski nace,muje amaka fade sire zemaka kyau" Make mata kafada yay yana kallon agogon hannunshi,sarkin son yawo yau ba inda zakije gida zan maidake I promise inna kaiki zanwuce askin,zumburo baki tashiga yi tana fadin "Nidai,nidai kawai bakason kaje danine" Takarasa cikeda bori Tsayar da motar yay yajuyo yazuba mata ido "Meyesa katsayar da motar" Tatambaya tana kallonshi Kwanciya yay saman steering wheel din yana fadin "Ganinai zaki saka mu accident ana zaune kalau" Zaro ido tai tace "Nidin menai" "Shagwaba mana sewani farfara min does angelic eyes kikeyi kina wani buga kafa, I'm not that strong ooo kar akasheni fa" Yafada yana dage nata gira daya,kamar dutse peace sam bata gane meyake cewa ba daman hausar bawani isarta taiba, "Nidai zanje" Tafada tana langwabar mishi dakai Yace "kinsan Allah yout not going banson zuwa gurin aski dake akwai maza dayawa last time ma takuramin kikai haka natafi dake suka ta kallemin ke don haka bazan sake zuwa dakeba fa" Tanajin yafadi hakan tasan bazeje da itaba tana mamakinsa shiwai ko kallonta beson yaga anyi,jin tayi shiru tana kallon taga yasa yatada motar yafara tafiya "Your a jealous freak" Tafada ciki ciki,sarai yajita Yace "I heard that one,kuma sena rama, time will tell nidake waye jealous freak baby girl"

bude glove compartment din motar yay lokacin dasuka isa street dinsu peace akofar layin tace yasauke ta batason wani yaganta ta fito daga motarsa. envelope ciro yamika mata yana fadin "gashi kiyima mutanen NURISTAN tsaraba, karba tai tana budewa taga uban kudin da ita kanta bazata iya kintatar adadinsa ba don pounds ne," tai sauri ajjewa tsakaninsu tana fadin "no sire I can't take your money, this is too much duk dawainiyyar da kake dani," Strictly yace "peace dauki envelope dinnan ko kinaso raina yabaci ne" dasauri tashiga girgiza mai kai yace "we are friends duk abinda nake dashi nakine kinji,if you need anything anything aduniya just ask me don't hesitate," jinjina kai tai kawai tana mamakin inda yake samo kudade haka saboda ta fahimci shima irin tane ya iya spending kudi son ranshi though bawai almabazzaranci yakeba amman baya siyan abu me arha idan yaje guri seya nemo abu mafi tsada yake siya, "but sire...." tafada tana tabe mishi baki cute pinkish lips dinta yay looking very hot a idonshi da sauri ya dauke kai yana fadin *no buts just take it," "tohm sire what are you selling a ina kake samo kudi haka? ko kaima mommy and daddy kake exploiting ne rich kid," girgiza kai yay yana smiling yace "I'm not rich peace! kune masu kudi mu nema mukeyi," tace "but you spend too much," yace "har yanzun koh rabin kudin dana samu a the man ban kashe ba," dan rufe bakinta tai tana fadin "laaaaaaa namanta your the great EHSAAS NASHWAN,a.k.a Creator of Ahmad talal,a.k.a the winner of the famous booker award a.k.a peace's Great sire, Sire kanada kudi next book jirgi zaka siya mana inka samu big sells haka" tafada cikin sigar tsokanar da tasa EHSAAS dariya har hakoranshi na fitowa one thing about her shine duk kuncin da yake ciki wllh moment kadan zeyi spending da ita yajishi acikin farinciki sbd bakinta duk abinda yazo kawai shi take fada gashi ta iya roasting dinsa intaso times without number inta sakoshi agaba seya gaji ya toshe kunnensa tukunna zata barshi.

Yau kamar karya barta tatafi haka yakeji amman tinawa da goal dinsa be kamata Abraham yagane he is still in contact with her ba yasanya yace mata "intagama tsokanar tawuce gida kar afara nemanta" Tabe mai baki ta kuma yi tafara rigimar "daman korarta yakeyi Allah Allah yake tama koma NURISTAN yakoma gurin yan matansa na college" zaro ido yay cikin mamaki yake fadin "waye yace mata yanada yanmata?' labarin abinda guy dinnan yagaya mata tabashi,yace "shikenan nashiga uku wayyo ni yarinyar nan bakison inyi kasuwane ina market fa tunda har yanzun bansamu shiga gurin wacca nake shigewar ba,kuma gashi batason inkula wasu, jealous freak" yamaimaita mata abinda tace mai dazun yana dage mata gira daya wata irin kunyarsa taji ta lullube ta da sauri tashiga kokawar bude kofar motar yana dariya yake cemata "ina zataje tadawo aibe gama bata labari ba" seda tafita amotar da envelope din ahannun ta sannan ta leko ta tagar da yake tana cemasa "itama zata koma nuristan ita da zata shiga jami'a ma yajira yaga kalar samarin da zatai intai turning 18 tunda abin yazama yar haka" tafada tana harararsa tawuce, dariya yafara yi yasan takulu kenan don ya lura tanada masifar kishi,yanzun seyayi aikin lallashi.

Tana shiga gidan suna cin karo da nanny wacca Veronica ta aikata dakko peace din sakamakon meeting din da taje basu gama da wuriba ganin peace din tashigo gidan cikeda annuri afuskarta ya sanya tatsaya tana kallonta, ganin nanny namata kallon tuhuma yasa tadan hade rai tana shigewarta ciki, nanny biyota tai tana tambayar "har an tashine" "Eh" tace mata kawai ta haye saman tana hawa kuwa ta dakko wayar EHSAAS daya bata, tabude "I'm sorry my Queen aikinsan your the only Queen in EHSAAS Life, hope your smiling now as your reading this message"

rufe fuska tai kamar yasan murmurshin take tunda taga text din dasauri ta tura mas reply inshort tace "your pardoned your royal Highness," bagpack dinta da take tafiya NURISTAN dashi tadakko acan ciki tazira wayar bayan ta kasheta saboda she can't risk wani yaganta anan,don gidansu na nan din baida girman na NURISTAN wanda take da part dinta guda na kanta setai sati bata ga iyayenta ba koda suna gari, sometimes she prepared staying there indai tareda su ne don atleast zata samu freedom din yin duk abinda takeso alokacin da take so a part dinta.

Seda daddare iyayen nata suka dawo Abraham yashiga tambayar Veronica "shin tatsaya peace din har tayi tagama" gudun masifarsa yasanya tace mai "eh" kawai yadanji sanyi aransa sbd yayi noticing yaron kamar yaji warning dinsa yarabu da peace din kuma ganin peace din takoma yajja take adacan bawani walwala kuma duk abinda yace tayi tanayi straight yasa hankalinsa yadan kwanta.

tare sukai dinner peace Allah Allah take tahau samanta tai waya da EHSAAS amman mom dinta tama ki barinta ta samu alone time, tace tazo dakinta waita tayata cigaba da hada kayanda tun jiya take hadawa bata gama ba kamar wacca bazata sake dawowa kasarba,tana bata labarin abunda yafaru gurin meeting wanda ba abinda take ganewa cikin hirar da eh, a'ah kawai take binta dashi,har seda dare yalatsa lokacin da Abraham yashigo suka sallameta tadawo dakin takalli agogo tai tsaki tasan yayi barci by now.

Washegari tasamu barcin safe sosai sbd se 11 flight dinsu zetashi se karfe tara suka tasheta tashiga tai wanka tashirya cikin wata English duguwar riga data kaimata har kasa veils dinta tashiga dubawa tana sha'awar tai Rolling dinsa iri yajja taga yaran musulmai nayi amman haryau tana tina lokacin data taba gwada hakan tana elementary school,seda Abraham ya kusa halaka doncewa yay tana koyine da dabi'ar makiyansu non believers. ya yarda tasa mayafi ko wana irine amman be yarda tayafa shi yajja yayan musulmai suke yafawa ba,ganin bazatai kyauba yasa kawai tatube tasaka kananun kayanta data saba sawa tasanya jibgegiyar rigar sanyinta don taga is snowy out there yaudin. tazira airpod kunnanta kamar yajja tasaba duk sanda zatai tafiya,the man da EHSAAS yabata first copy dinsa tadakko tana sawa ajakarta,don shi zata karanta ajirgi tafito sama sama sukai breakfast kafin su kullo gidan gaba daya harda nanny driver Veronica ne yadauke su har zuwa London,SUV din tana tsayawa akofar Heathrow, driver yafito yana bude musu kofa susu biyu agidan tsakiya suka zauna, peace ce agidan karshe ita kuma nanny na front sit itada driver. kamar amafarki ta hango shi jikin wani building cannesa yana kallo su,dasauri tacire glass dinta tana murza idanuwanta don tinaninta gizone yakeyi mata still ta ganshi be baceba. dasauri tafara tafiya zuwa gurin Abraham daya lura peace zatai wani gun hankalinta baya gurinsu ya sanya yariko hannayenta yana fadin "ina zakije ne peace?" se alokacin takalli babanta wani tsorone ya kamata inyaga EHSAAS fa dasauri tajuya tana kallon inda taga EHSAAS yanzun atsaye ganitai babu shi babu dalilinsa kallon gurin Abraham yay ganin peace nakalla,ganin babu komai yasa ya kamata yana fadin "let's go inside ya kusa tashi karki bata mana lokaci," tanata waiwaye ko zata sake ganinshi amman harsuka shige bata kara ganinsa ba.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote. [03/05, 10:03] Fatima Rufa'i Nasidi: It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.