EHSAAS

Chapter 15

by @fatoumspassion

Lokacin da yaga yadena ganin Peace da mahaifinta ahankali yafito daga bayan ginin daya labe yanajin kamar Abraham Zion din ba iya Peace kawai yatafi da itaba,yatafi ne da wani sashe me mahimmanci na cikin rayuwarsa seda yaga tashin jirginsu sannan yahau motarsa yadawo. tsawon ranar jinsa yay gaba daya wani iri kamar zazzabin na neman dawowa jikinsa duk kuwa da yajja Noah yake tsokanarsa yanason yafada mishi wani abu dangane dashi da peace din kasawa yay, agogo kawai ya keta kalla yana Allah Allah kawai su sauka anuristan don yasan inta sauka zata kirasa,har Fulani data kirashi taji muryarsa wani iri data tambayeshi cemata kawai bakomai duk yajja taso taji meke damunsa kin fada mata yay hakanne yasa hankalinta yatashi gaba daya so take ta ganshi dakyar ta lallaba me Martaba yabarta zataje Oxford don duboshi itada mimah suka shirya acikin satin da peace takoma NURISTAN sukuma suka sauka a Oxford, awani apartment na mai Martaba suka sauka seda suka huta sannan suka sanar da EHSAAS yasan gidan aiko nanda nan yazo ya samesu cikin farinciki domin ya mugun jin dadin ganinsu. Don sundaukemai hankali da yajja kewar peace ta mamaye sa gaba dayansa dukda suna makale awaya kusan kullum amman bayajin hakan yana satisfying dinsa so yake kullun yaringa ganinta ta kasance a sight dinshi,sati guda mimah tai tawuce Turkey,tabar fulani da EHSAAS sunsamu lokaci sosai kuma alokacinne yafara jarrabawa,zamansa tareda mahaifiyar sa guri daya yasa ta fahimci akwai mace acikin rayuwarsa saboda ta fahimci duk abinda yakeyi kullum yana makale da waya amman dataxo seya basar yaywa wacca suke wayar sallama kallonshi kawai take batason ta takura mai so take yagaya mata dakansa amman ganin baida niyya yasa tai deciding zata tambayeshi. mai Martaba ne yasoma kiranta yana cewa tadawo dakyar ta lallabashi tacemai ai EHSAAS jarrabawa yakeyi ya daure yabarta har yagama jarrabawar,Mai martaba kuma yayi kewar matarsa mafi soyuwa agareshi fulani ce kadai zatai tafiya cikin matansa kaji yadamu. wasu lokutan Fulani jitake inama haka take rayuwa da danta ko yaushe donko a NURISTAN basa samun lokaci da kusanci dashi haka ba kamar yana nandin ba, Yau dawowarsa kenan daga makaranta yana bata labarin saura exams daya ya kammala,tashiga farinciki tana tayashi murna,lunch din datai masa tajera masa a dining,kamota yay yana fadin "rabin raina maama kixauna ni zanyi serving dinki yau" yana murmushi yashiga zuba mata abincin gently,kafin shima yazuba nasa yazauna agefenta yanaci,suna dan taba hira, ringing wayarsa tafarayi,tana gefen sa inda yakasance gefen Fulani itama shida ita alokaci daya suka kalli screen din POM(peace of mind) se wani kissing emoji. dasauri yadau wayar yana dan kifa screen din cikeda kunya dukda yasan ba lallai ne Fulani tasan full meaning din POM dinba, Fulani murmushi tai irin nasu na manya kafin ta shafa kansa tana fadin "ba kiranka akeyi ba babana" duk da yanason yadauka don yasan peace kira daya takeyi inbe dagaba bazata sake wani kiranba amman kuma bayason yashiga lokacin mahaifiyarsa,girgiza kai yay yana fadin "I'll call back later maama," jinjina kai fulani tai tana daukar tissue tadan goge gefe da gefen bakinta alamar tagama cin abincin tai fixing idanuwanta akan EHSAAS da duka yay feeling atsarge yake har seda yagama yasha ruwa sannan tace mishi "who is she?" Kallonta yay yana dan tsuru tsuru da alamun rashin gaskiya, "EHSAAS yar waye? Kuma a ina take? ta tambaya with a serious tone this time around kuma yasan indai tace mai EHSAAS tohm that means she's not joking. "Maama" yafada yana dan shagwabe mata don bayason yafara gaya mata tukunna harse peace takarbi musulunci,tambayarka nai Fulani tafada tana tsareshi da ido, "maama she's someone I love," yafada yana dan sunkuyar da kanshi cikeda kunya, "nasan you like her shiyasa nake tambayarka wacece ita?" tafada tana shafa kansa, "kasan prince dina ba kowace kalar mata ze kaunata ba nasan prince dina will bring the right lady,a princess kamarshi me daraja mai asali,Mai addini,wacca tafito daga babban gida irin nasa, wacca mahaifin sa zeyi alfahari idan yaga zabin" wani irin bugawa zuciyarsa keyi jin high expectations din da Fulani keda shi ita da yake da hope cewa zatai supporting nasa kan duk abinda yakeso,kuma yanajin tana maganar kamar da gargadi gargadi ne kan inbama takai abinda take fada ba yasan abinda zeyi domin yasan mahaifiyarsa sosai kuma koda wana harshe tai magana yana ganewa dagowa yay yana wiki wiki da ido,jin yaki magana ya sanya tamike tana fadin "don't bring anything less than what I mentioned inba hakaba kadawo gida tsakanin maisoon da jalila kazaba su yan uwanka ne,we know everything about them kasan babu yajja za'ai muzaba ma abinda ze cutar dakai," zata fara taka stairs tajiyo sautin muryarsa cikeda rauni yana fadin "bazan iya rayuwa da wata macenba bayan ita maama, ina kaunarta sosai" juyowa tai tana kallonshi kafin tadanyi murmushi tana fadin "daman Princes never live the way they want to kaji yarima" takarasa tana juyawa sama domin the last thing dazata so aduniya shine EHSAAS yazabo yarinya wacca batakai darajar tazama sirika agidansu ba domin hakan ba karamin tarzoma da bala'i ze jawo atsakanin sa da mahaifinsa ba wanda bata kaunar hakan tafaru ko kadan tasan makiya da dama makusanta jira sukeyi yaron yay mistake guda daya, wanda zasu yi amfani dashi gurun shiga tsakanin sa da mahaifinsa. tun daga ranar Fulani bata sake masa magana kan yarinyar da yake waya da itaba donta fahimci tabbas beda gaskiya yarinyar bata kai bane shiyasa yake boyewa ayajja tasan EHSAAS in yanason abu baya iya boyewa haka zalika in yana ki,don haka ta tabbatar akwai wata matsala tattare da yarinyar datafi bayarda cewa kawai yar talakawa ce shiyasa yake boyeta. bayan yagama jarrabawar ne mai martaba da uwar soro yakawo musu surprise visit zuwa kasar don attending convocation dinsa,sosai EHSAAS yay murnar ganinsu hakan yasa baya samun lokacin waya da peace se dare itakuma lokacin babanta yadawo gida bata iya fitoda wayar daya bata aboye,dagashi har ita asatin sun mugun galabaita saboda rashin ji daga juna,amman haka suka daddafa har akai convocation din aka gama EHSAAS ya karbi lambar yabo matsayin zaqaqurin dalibin da yafi kowa maki a balliol college a wannan shekarar kuma anan suka sake bashi wani scholarship din nakaratu in yana bukata har PhD. mai martaba cikeda alfahari yake tsayawa gefen EHSAAS din ana daukarsu hotunan tarihi,haka zalika mukarrabansa ma washegarin ranar jirginsu yatashi don komawa NURISTAN sukabar EHSAAS cikeda kewa yanajin kamar yabisu yakoma amman kuma yasan indai har yabisu ba lallai mai martaba yabashi damar sake dawowa Oxford don kammala masters dinsa ba. acikin wata uku yay processing komai yafara MA dinsa kuma alokacinne peace ma tasamu admission a Zion university national open university NURISTAN,wanda ta cike batareda sanin babanta ba itada EHSAAS sukai komai online,domin babu yajja za'ai tana yar prof Abraham Zion ta karanta abinda bayaso a jami'ar sa,ba karamin farinciki Abraham yayba yanajin yana alfahari da peace domin tacika masa burinsa akanta babu wanda tafadawa tacike open university daga ita se EHSAAS suka sani hakanne ya sanya lokacin da aka fara registration shine yaymata dakansa ta online shikansa besan abubuwa nawa na rashin dede ze aikata saboda peace dinba yasan boyewa mahaifinta hakan babban kuskurene amman yasan he is not there to protect peace don haka dolene duk abinda zeyi yayi keeping low-key har shekarar takare yakammala yatattara yakoma karatunsa don ya mugun kaguwa kawai yakoma. bayan yagama mata registration Aman ya kirawo yana fada masa "ze sashi wani aiki kuma kada yasake ya tambayeshi komai gameda aikin is highly confidential ko yayarsa mimah bayason tasani" yace masa "ya amince don shi yana mugun kaunar uncle din nasa duk abinda yace masa shi yakeyi" yace masa "zetura masa takardu yay printing out,new student ce a makarantarsu yanason yay mata komai bude files dakomai dakomai ya riga yamata online registration kuma zebashi address din inda ze Kai takardun inya kammala konawane yakashe gurun ganin yayi komai batareda anbukaci zuwan yarinyar ba" Da tohm Aman ya ansa masa yana wondering what uncle din nasa is up to amman yasan EHSAAS nada hankali komai alissafe yake yinsa bazeyi abinda be dace ba,yayi mamaki matuka lokacin dayaga takardun Peace Abraham Zion din ga gulma taf bakinsa amman EHSAAS yadaure mai jijiyoyin wiya.

EHSAAS peace yakira yace mata "tabashi address na gidansu don yanason yaturo mata da sako," turamai tai yace mata "ta tabbatar tafito ta karba karfe shida dede kada tabari wani ya karbi sakon ba itaba ba" tohm ta ansa mishi tunda tasan kila abubuwan makarantar tatane dazata fara online. karfe shida daidai tafito harabar katon gidan nasu me kama da wani babban villa, sa'ar ta daya iyayenta duk basanan se uban security ta ko ina,karasawa bakin gate tai tana kallon yajja security din ke kallonta dake kowa na shakkarta saboda ansan yajja Abraham yake jida ita ko kallon peace yaga kafiya yi agidan sallamar ka yake. har Aman ya iso kofar gidan kiran wayar tata taji anayi bakuwar number data gani yasa ta daga muryar Aman ce yace "nakawo sakon sir EHSAAS ne," karasawa tai gabam motar yafito suna hada ido sanye take cikin wata doguwar riga ta yafa mayafinta akanta bazaka taba cewa ita arniya bace her innocent face look very angelic, she's very pretty Aman yaraya aransa yana mika mata file din da jakar sabuwar laptop dinta da WiFi duk suna ciki, domin strictly EHSAAS yace masa indai yatsaya hira da ita seya mai rashin mutunci yanason yasan alakar dake tsakaninsu amman kuma baya iya take dokar uncle din nasa. murmushi tai masa bayan takarba tace mai "thank you," ganin yana dan yanayi da EHSAAS din yasa tace masa "are you his brother?" Murmushi yay don ba itace mutum ta farko data fara mai tambayar nan ba girgiza mata kai yay kafin yace "his nephew," jinjina kai kawai tai cikeda nutsuwa tace "you most be Aman, guy din dake kiransa kullum" murmushi yay yana fadin "ashe kema kin sheda yajja nadamu dashi nake kaunarsa amman mutuminnaki baya gani," tace "Aman ni cemin yay kai karamin yarone I thought your this small" takwanta tana kasa da hannayenta,bude baki yay sekuma yarufe kafin yace mata "shekara biyar fa kawai yabani," "five is much" tafada tana kokarin bude file din dan haka kawai hankalinta yakwanta da Aman din kuma dan uwan EHSAAS ne duk wani abu daya shafeshi ji takeyi tana sonshi,wayar Aman ce tafara ringing yana ganin EHSAAS ne ya daga yana fadin "nakawo uncle prince," yace "kakoma office tohm," muryar peace yaji tana tambayar Aman wata takarda, EHSAAS strictly yace masa "me kakeyi har yanzun tare da ita," wata irin dariyace tazo masa don ya fahimci uncle din nasa inda yadosa yanzun kishinta yake kishi ma me tsanani kuwa cikin kishin hardashi,yace "uncle kawai fa gaisawa mukeyi," EHSAAS daga dayan bangaren yace "aikoka nai don kai hira da ita eh,zaka bar gurinnan kosena saba maka," dasauri yacire wayar akunnensa yana toshe speaker yakalli peace yana fadin "he is jealous se anjima kar yacinye ni" yakoma mota yana mata bye bye itama cikin mamaki tamai bye-bye tana mamakin what's the rush, EHSAAS meyasa yake hakane nephew dinnasa ma bayason take magana dashi, guards din ta kalla daya bayan daya lokacin data shigo ciki don tasan sarai sunganta dawani,hade rai tai tana fadin "what did you see?" Dayan yakalli dayan suka hada baki sukace "nothing" jinjina kai tai tana fadin "good" tashige cikin gida abinta akasan bed dinta ta ajje file din tana tinanin yajja za'ai tafara makaranta biyu alokaci daya,dukda dai dayar open university ce. Wata iriyar shakuwa ce take kara shiga tsakanin susu biyun kamar wasa har peace taci semester daya dafara karatunta,tadage tana karatunta online batareda sanin kowaba,duk abinda bata ganeba shi take kira yaymata bayani, suyi discussing abubuwa iri iri,A Zion university kuwa babu abinda take zuwa yi se karanta littattafan da EHSAAS yabata bama tasan courses din takeyi acanba har lokacin jarrabawa yazo tazuba iya shegenta ciki tai submitting,babu abinda take ma tsaya taji balle ta fahimta tarubuta, kuma duk abinda yafaru arana daga ita harshi sesun gayama juna ko ruwa tasha seta fada masa shima kuma hakan gaba dayansu ba mutanene masu son magana ba amman idan suka fara hira awaya dayama baya jiran daya yakammala dayan yake daurawa. zuwa yanzun kam tafahimci abubuwa da dama dangane da musulunci ga littattafan da EHSAAS yabata tadage tana karantawa dari bisa dari zuciyarta ta yardar mata tanason tashiga musulunci,amman kuma batasan meyasa ba takasa fadawa EHSAAS haka saboda tana mugun tsoron abinda zeje yadawo tasan Abraham can kill her indai har takarbi musulunci tana karkashinsa,itada EHSAAS wata irin soyayya suke nuna ma juna mai sanyi wanda kai kana kallo zakasan sun mace ajuna amman har yanzun bakunansu yakasa furta hakan amman actions dinsu gaba daya yagama nunawa. alokacin ne kuma akai launching prince publishing dayane daga cikin publishing houses dasukai shura a NURISTAN ayanzun, Prince publishing mallakin EHSAAS ne amman Aman ne ke managing dayawa har cikin masarauta an dauka gurin na Aman ne dukda da dama suna mamakin waye yay sponsoring Aman din yay building babban business haka musamman bangaren family din waziri dasuke ganin kamar cigaban da yazoma Aman din be cancanta yazama nasaba sedai yazama na daya daga cikinsu,mai babban daki duk inda ta tsugunna seta yada cewa Aman jikanta yayi kudi yabude babban kamfanin publishing tana hura hanci tana alfahari tana habaice habaice tana cewa shi zuciyarsa bata mutu akan karatun boko ba yanemo hanyar neman halak dinsa kuma cikin fulani,mai Martaba da gimbiya mimah dasuka san gaskiyar waye owner din babu wanda yay yunkurin yimata bayani kawai aka barta suje ahakan don ba'a son jama'a susan cewar na EHSAAS ne kamar yajja ya bukata cikin shekarar prince publishing tai wani irin boosting tai shaharar da publishing houses da dama dasuka shekara da shekaru aharkar basu yishi ba,sbd buge buge kawai sukeyi akan ruguza tsarin capitalism wanda yagama mamaye NURISTAN din baki daya, jaridar prince publishing bata kaiwa karfe takwas nasafe a market ake siyewa,sbd ragargazar dasukeyi wa manya manyan kasar masu mulki gashi anrasa takameme waye behind the publishing house, Aman amatsayinsa na managing director shine yake ganawa da yan jarida yay komai kuma be taba bude baki yasanar musu cewan tasa baceba times without number dai yakan cemusu meshi yana nan tafe zasu ganshi soon,hankalin su besake tashiba seda tabuga manya manyan littattafai na tarihi guda, fiction daya wanda yake war against capitalism na tarihin tarihin asalin NURISTAN ne tun kafin lokacin zuwan turawan mulkin mallaka,tundaga kan kakan kakansu EHSAAS har zuwa kan sarki NASHWAN maici ayanzun littafin yasamu karbuwa sosai lokacin da akai launching dinsa EHSAAS na shirye shiryen final jarrabawar sa ta MA hakanne yasa manya manyan masu sarauta da masu kudi suka siyi littafin da darajar gaske copy daya inkaji millions da billions da ake ambata gurin siyansa seka rike baki, fiction din kuma labarine tsararre amman kana karantawa kasan da hikima aka rubuta shi ana addressing masuyi tareda gargadinsu kan su dena inba hakaba hukunci na nan tafe,masu kudin sunfi kowa rububin siya saboda kada ace suna adawa da akidar prince publishing din asaka musu ayar tambaya. sells din da akai a shekarar gaba daya prince publishing tai sponsoring matasa guda dubu daya a NURISTAN ta samar musu da abinyi sana'o'in hannu aka koya musu iri iri aka basu jari masu sha'awar karatu aka maidasu makaranta aka biya musu kudin daze ishesu harsu kammala zuwa yanzun sunan Aman duk inda kazaga lungu da sako talakawan NURISTAN shimasa albarka sukeyi agurin masu kudi kuma yazama gembo.

Peace na zaune a parlour itada nanny Abraham yashigo kana ganinsa kasan ransa abace yake yazauna saman kujera yana huci,kawai nanny mikewa tai tana Mai sannu da dawowa banza yay mata kafin yakalleta kuma yace "takawo mai ruwa mai sanyi" daidai nan mom dinta na fitowa daga dakinta, gefen sa takarasa tana tambayarsa "meya samesh? lafiya? kallonta yay kafin yace "kunna TV kigani," kallon peace tai tana mata alama da ido ta kunna TV daman su ba ma'abota kallon TV bane domin Abraham gani yake kamar wani zunubi ne kallon film sedai inshi yana bukata yakunna yakalli news inkaga kayi kallo agidan sedai inbayanan aboye. kunna TV peace tai tana komawa kujerarta tazauna,novel dinta tadauka don cigaba da karantawa taji Abraham yacigaba da masifa "That publishing house is a curse,zan iya rantse miki cewa that so called king of NURISTAN NASHWAN shine yakirkiri wannan publishing house din inba hakaba look tayaya za ace out of all people yaronnan karami da kadan zefi peace shine ke managing wannan big business din wallh someone is behind him,kijifa maganar da yakeyi yanzun kan littafin dazasu saki this month they are just stupid so sukeyi private university su zama wani charity foundation kome,meye amfanin yin private university indai se ance za'a kayyade mana kudin da zamu karba wannan akidar king NASHWAN ne mugu kawai non believer daman burinsa yaga mun durkushe gaba daya yaga shishi kadai keda arziki a NURISTAN inba hakaba taya za'a ce jikanshi ke ayyukannan kuma arasa asalin me rubutun,all the books says about the author shine the prince,the guy isn't using his real name fa," dan dagowa tai tana kallon TV tanajin dadi saboda finally ansamu wani wanda zeyi putting dad dinta back into his senses sbd kudin da yake karba a Zion university is too much,takanji coursemate nata suna complain akan hakan amman tana zuwa gurin se ayi shiru don ansan itadin wacece. idonta yasauka akan Aman yanata ma yan jaridar bayani akan littafin tana tuna inda tataba ganin fuskarsa, "yes nephew din EHSAAS" ta fada aranta, "shine ake cewa jikan sarki taya ze zama jikan sarki,bayan yana running errands ma EHSAAS dinta ai jikan sarki can't do that,to inama EHSAAS dinta yasan jikan sarki" for the first time takalli Abraham tace mishi "Sir,wannan ne jikan sarkin?" kallonta yay yana fadin "ah toh karya zanmiki kenan,kodan kinga surname dinsa babu NURISTAN akarshe dan mace ne, shegen yaro kawai, ina tinanin shize saka heir nasa sbd shiwancan shashashan ma ance he don't have interest,yanacan kasar waje yana karatun banza da hofi ni karatun mezanyi inada kingdom tana jirana so as you can see da alama dan nashi lusari ne shiyasa yadakko jika yasa yake amfani dashi tunda baze iya tunkararmu ayi fito na fito ba.. Hmmmmm, tohm wllh nasan matakin dazan dauka akansa," mikewa kawai yay yana kallon Veronica da jinsa kawai takeyi one interest batta daahi kan maganar tasa, kuma tayi mamakin jin yajja peace yau tasaka mai baki cause usually inyana masifarnan basa saka mai baki har yagaji yatashi yabarsu. yana tafiya peace tamike takalli mom dinta tana fadin "I need to study natafi bangarena," dasauri ta mike tanufi wata kofa dazata sadata da p Flat dinta tana shiga daki ta wuce direct tasoma tinanin "tohm tayaya nephew din EHSAAS ze kasance daga royal family bayan dan yayar EHSAAS ne tasani?" zuciyarta kasa amincewa da abinda take gaya mata tai kawai tadau waya tashiga kiransa alokacin yana tsakiyar depending thesis dinshi gaban manyan balliol college professors hakanne yasa besamu damar dagawa ba harta katse for the first time tasake kiransa nanma ba ansa ta ajje wayar kawai tana feeling restless batason zarginta yatabbata don idan zarginta yatabbata tagama shiga uku,saboda taga yajja rage din wutar tsanar king NASHWAN take tashi a idanuwan mahaifinta. "EHSAAS NASHWAN that makes sense" tafada aranta ta taba tambayarsa last name dinsa yace mata zegaya mata amman ba yanzun ba definitely yana boyewa ne kamar yajja itama bata amfani da last name dinta tana boyewa don kar asani but why would EHSAAS hide such a big thing about himself?ta tambayi kanta tana jawo system dinta, google tashiga tai typing prince of NURISTAN nan take yawatso mata information akan EHSAAS ga hotonshi nan tareda mai Martaba wanda aka musu recently a Oxford lokacin graduation dinsa tanada hotunan amman iya nashi dana Fulani ya turo mata yasan zata gane fuskar king NASHWAN shiyasa be turo da nasaba tashiga babu much akansa da alama yana keeping komai na rayuwarsa private kuma yawanci hotunan dasuke uploading babu wanda yake shishi kadai sede kaganshi tsakiyar taro shida mai martaba ko yana gaisawa da manyan mutane agurin tararraki. dafe kirjinta tai lokacin da taga wani hotonsa da alama hoton yadan jima cikin full shigarsa ta sarauta ya Allah kunga bala'in kyan da kayan suka mishi kuwa fuskarnan tashi ahade babu alamar murmushi akanta rufe laptop din tai tana jin zuciyarta kamar ta yaudare ta dason abinda bazata taba mallaka ba har abada, "why would EHSAAS deceive her like this? yabari tasaba dashi,ta shaku dashi bayan yasan sunfito daga gurare biyu ma banbanta wanda tasan ba tantana idan mahaifansa suma suka gane yana alaka da arniya, arniyar ma yar babban makiyinsu se sunce yarabu da ita tasani.

sulalewa tai saman carpet tanajin EHSAAS be mata adalci ba dayaki gaya mata gaskiyar shiwaye,shiyasa yake cewa babanta ba abinda ze iya mai ashe yasan meya taka no wonder she's very foolish not to understand that, EHSAAS ba tsaranta baneba kwata kwata tasan ko acikin musulmai se anzaba andarje za'a samo masa wacca ta dace dashi yar gidan masu mulki ba irinta ba,kuka tashiga yi na zuci dana fili tana kokarin rarrashin zuciyarta tana gaya mata yakamata tatashi daga mafarkin da takeyi na samun kyakkyawar rayuwa tare dashi nan gaba.

Wani irin bugo kofar dakin taga anyi tadago idanuwanta jajir suna hada ido da Abraham wanda yake huci yana kallonta dawani red gift box ahannunsa,dasauri ta mike don ayajja ta ganshi tasan tabbas tayi laifi ko wani abun yafaru,jikinta har rawa ya farayi ganin yashigo ya sakama kofar lock,ta tsaya tana kallonshi box din daya riga yabude yawatso mata yana fadin "what is this?" Girgiza kai tashiga yi don harga Allah batasan menene ba, "what is this?" yakara daka mata tsawar datasa tai saurin tsugunnawa tashiga bude box din,dake yariga yabude zaro dogon farin hijab din dake ciki tai da sallaya da azkhar da littafin sahih bukhari da chasbaha aciki,se wani kati da aka rubuta congratulations akan rubuta registration number dinta da sunan makarantar. kallon dad dinnata tashiga yi,tana tina daga inda gift din yazo a platform nasufa na online university akeyin quiz kusan dukkansu musulmai ne akan musulunci aketa tambaya kuma anata tambaya ana faduwa akan tauhid ne, littafan da EHSAAS yabata yasa tasan abubuwa da dama gameda wanzuwar ubangiji,siffofinsa da sunayensa tsarkaka,ciki harda littafan data karanta hukunce hukuncen tsarki alwala da wanka anan ta tsaya tohm jin ana tambayar musulman sunata faduwa yasa tace bari tai participating kamar wasa tabada ansa guda uku sukace taci gasar za'a bata kyauta, batasan wannan kyautar ce ba da bata bada ansa ba datasani bata mayi joining group dinba. Abraham ganin peace ma tagama raina mai wayo yasa yakarasa jikin socket inda ta ajje charger dinta yafizgo kawai yana rabbata da kanta yanufota ta rufe ido dan tasan yau bame cetarta agurin sa,saukar bulalar tafaraji abayanta ta dunkule tana kare kirjinta da fuskarta bugunta yake kamar an aikoshi ka rantse bema taba saninta aduniya ba balle su hada jini, "how dare you? Kishigo min da abubuwan non believers cikin gidana peace kafircewa Jehovah zakiyi, peace how dare you kifara wani karatu ba tareda iznina ba peace, I own you ni ubanki ne," yafada yana hankadata da kafarsa tai flat akasa hawaye kawai takeyi amman batta kara bata komai fizgota yay ganinma bata rokonshi for mercy yajawo gashinta yamikar da ita tsaye karar azaba tasaki tana rintse idanuwanta,yadunkule hannayensa yana naushin cikinta yajja kasan yasamu gardi dan uwansa jinine yafara fitowa ta bakinta da hancinta, "Abraham kabude kofarnan kada ka kashemin yarinya open this door pls" tajiyo muryar mom dinta na rokonshi,bugun peace yakeyi kamar besan ciwanta,dede nan kuma yaji wani strange ringing natashi cikin dakin ringing wayar tane da EHSAAS yabata ringing dinsane bata canza ba,yanajin wakar slowly natashi acikin kunnuwansa rangadadau yakejin kalaman I pledge to Islam my religion To be fateful loyal and honest To serve Islam with all my power And I pray......... Abraham rike kanshi yay yanufi wayar dake kan gado daidai nan ringing din yana katsewa yadau wayar yashiga jujjuyawa yasan wannan ba wayarta baceba. buga kofar Veronica takeyi wanda kuka takeyi ba kakkautawa tana rokonshi yakyale mata yarinya ringing dinne yakara farawa, Abraham the wayar yafara jeka kadawo adakin yana kallon yajja tai saving sunan me kiranta da my sire with two kissing emoji, "Jesus" yafurta yakarasa inda take kwance tana rike da cikinta tsabar yajja takejin kamar yafasa mata yayan hanji, yasoma wata shegiyar dariya da kana kallo kasan ta tsantsar takaicine da rasa abinyi. agabanta ya daga wayar ya dokata da kasa yana kara binta ya taka da takalminshi kafin yajuyo kanta yafizgo ta yana mikar da ita, "abubuwa nawa kike boyemin peace,ayaushe kika zama kafira munafuka bansani ba, peace waye yabata miki rayuwa haka bansani ba wayeshiiiii? New phone,New school,who the hell sponsor you,Peace namijine ko,did you open your legs for him, peace did he get into your damned pants" Yafada yana wani sakinta tafadi kasa yay mugun ball da ita tai baya tana dukan gadonta, "yah Allah" yaji tafurta dayasa yakusa karasa zerewa, Ita kanta batasan tafadi hakanba,ko dan sbd zama da EHSAAS ne soda dama in anyi abun mamaki ko abun mamaki ko abu yafaru da ita intace Jesus yakan haneta yace mata sunan Allah ake kira cikin kowana hali kuma kullum shine cikin bakinsa,hakanne yasa itama taji tafurta batareda tasani ba,kuma hakan yay nasarar karasa zautar da Abraham Zion yay kanta gadan gadan jiyake gara ya kasheta dawannan abin kunyar data dakko masa cikin gida ganin bata motsi yasa yaja da baya yana kallon yajja jini yake bin bakinta da hancinta,harta da yar karamar vest din jikinta tayi shatin jini jinin dukan dataci agunsa.

Ba dai ya kashe taba? yatambayi kansa yana jin yajja Veronica ke rokonsa kada ya illata mata ya rinya bude kofar yay Veronica tamatsar dashi gefe tai ciki ganin halinda peace din ke ciki yasa tafasa kara tana karasawa kanta tasoma jijjiga tana ihu tana kiran sunanta.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Like Share Comments & Vote [04/05, 19:44] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.