EHSAAS

Chapter 17

by @fatoumspassion

Kamar yajja EHSAAS yay shawara da gimbiya mimah bayan sun idar da sallar la'asar a babban mosque din dake palace, zama yay cikin masallacin gefen liman har tawagar mai martaba tafita be bisu ba. mamaki Malam liman din yashiga lokacin daya juyo yaganshi,dan karasowa gabansa yay yana sunnar dakai qasa,suka sake gaisawa,yace "yanason magana dashi" Malam liman cikeda concern yake tambayarsa "yarima ince dai ko lpy?" jinjina kai yay yace mai "lpy amman mgn ce dai yake so yay dashi inba damuwa ko zasu fita harabar masallacin" jinjina kai yay yana daukar doguwar chazbaharsa yay gaba EHSAAS yabiyo bayanshi asaman babban carpet din dake harabar suka zauna inda Malam liman yakewa yan matan palace din karatu kullum bayan la'asar yau dake alhamis ce se basu zoba basayi. bayan sun zauna anitse EHSAAS yashiga yi masa bayani ba tareda yagaya mai alakar sa da peace ba kamar yajja mimah tafada mai karyafada din, yadai sanar dashi kawai yana koya mata karatun boko ne kuma ita dakanta dan radin kanta musulunci ya burgeta tai sha'awar shiga ciki, kuma yasanar da Malam liman wanene mahaifinta dakuma azabtar da yarinyar dayay sanadin gane tanason tashiga musulunci da ikirarin kashetan da yace zeyi. dan jim malam liman yay kafin yace "Masha Allah, Masha Allah yarima kace karuwa zamuyi,tunda yarinya ce tai ra'ayi mu zamu tsayamata tsayin daka gurin kwato mata yancinta gun mahaifinta,bantabajin inda wani addinin yabada damar uba dan ya haifi ya yace ze kasheta ba tabbas wannan bawan Abraham yabata,bata mai girma, yarima amman karka samu damuwa zanje insanar da mai martaba base gobe ba in sha Allah yajja ta zabi musulunci mu musulmai bazamu bata kunya ba,zamu nuna mata yajja musulunci yake, cewar tabi tafarkin gaskiya tafarkin dazai sadata da alkhairi na duniya da lahira har zuwa gidan aljanna," jinjina kai EHSAAS yay cikin jindadi Malam liman yace "muje yanzun nida kai, bari nakira mai girma turaki yaymana rakiya saboda shi aikin alheri irin haka yarima ba aimasa jinkiri rannamu ba ahannunmu yakeba." Jinjina kai EHSAAS cikeda jin dadi yanawa dattijon godiya,Mikewa yay yabar malam liman dake kokarin kiran wayar turaki. Aman yakirawo awaya ya tambayeshi "yana ina?" yace "ai yakoma office" yace "Ina sakon dayace yasiyo da wayar da yace yasiyo mai, shin yasiyo? yace mai "eh suna cikin mota," yace "tohm ya samesu a asibitin da aka kwantar da peace" da tohm ya ansa mishi.

Cikin mintinan da basu wuce gomaba turaki yakaraso harabar masallacin yanata bawa EHSAAS hakurin jimawar dayay cewar ya danyi nisane inka ganshi ze girmi me martaba kansa, amman yajja yake dukawa EHSAAS nikaina seda naji wani iri, EHSAAS yadan rikoshi yana fadin "baseka dukaba baba Harees nifa dane agurinka menene don na jiraka" yace "dukda haka yarima ai bekamata in ajjeka nan kana jira ba" murmushi yay kawai yana fadin "bakomai baba karka samu damuwa" waya yay security dinsa suka karaso da motoci,ka'ida baya hawa mota da kowa amman tsabar girman da yake basu, shi ya shiga gaban motar dattawan suka shiga baya,kana ganin convoy zaka dauka mai martaba ne dakanshi ze fita,domin mai martaba yakan bawa EHSAAS fadawa da security ma da suka fi nasa saboda yasan shi yanzun yatura ba lallai ne makiya su hareshi ba amman EHSAAS da yake matsayin magajinsa shine akan layi,daidai zasu wuce ta filin polo na fadar gurin ajje dawakan fadar,kuma nanne suke yin kilisa lokaci zuwa lokaci musamman lokacin bukukuwan al'adar. galadima dake zaune tareda waziri suna shan iskar yammacin yakalli waziri yana kara kallon motocin, "Yaya wadancan motocin ba convoy din mai martaba bane?" girgiza kai waziri yay yana fadin "bashi bane kasan yanzun bayan la'asar lokacin hutawar mai martaba ne, natabbatar wancan shegen tsinannan yaronne,dan iska Dane ganin girman kowa yafita akemai fadanci haka kamar yama riga yazama sarkin NURISTAN baki daya" dan tabe baki galadima yay yana kallon waziri kafin yace "da alama fita mai mahimmanci ce sbd bancika ganin EHSAAS yadau security hakaba I'm curious.." yakarasa yana hura karan cigarette din dake hannayensa,waziri yace "nima jay hankali na be kwanta da fitar nan ba ya za'ayi musan inda yake me?" yace "karka damu bari nakira Ash'ar, daya daga cikin securities dinshine yaronane da kaina nabashi horo seda na tabbatar sunansa yashiga list din amintattun da za'a bawa EHSAAS su," dariya waziri yashiga yi yana fadin "shege jay shiyasa nake yinka kanka yana kawo wuta fa,ya akai kai hakan? kasan fa tafida aka bawa yay screening din dakansa ban dauka yabada kofar saka wani ba aida nima nashigar da nawa" dariya jay yay yana sake busa hayakinsa yace "be bar kofa ba kawai nidin ma kasan na musamman ne indai nai niyyar abu toh ko uban gayyar be isa ya hanani ba" jinjina kai waziri Erfan yay yana fadin "hakane jalal yanzun kirashi muji" jefar da tabar yay qasa yana murjewa da kafafuwansa da sukaji wasu arnayen bakaken cover shoe dake shining kamar yanzun aka gama gogewa yaciro dalleliyar wayarsa yajja yake danna waya ayangance sekace wata macen ce takeyi, cikeda salo yadanna kiran, yanata ringing ba'a daukaba ba,kallon waziri yay kafin yace "kila suna hanya basu karasa ba,amman wayana baya ringing daya be daga ba" jinjina kai kawai waziri yay irin cikeda nagane dinnan, text ne yashigo wayar jay din nan take yabude ya karanta kafin yadago cikin mamaki yakalli waziri,wazirin ma kallonshi yay irin lafiya dinnan yace "EHSAAS nashirya wani abune da bamu sandashi bafa da alama," waziri yace "me yake shiryawa?" yace "yaron dai yamun text cewan Zion university suka nufa kuma suna tareda Mal liman da turaki" zabura waziri yay yana fadin "wace Zion university din," jay kallonsa yay irin kallon kaskancinnan da wulakanci dukda kuwa mugun girmansa da waziri yay karewa waziri Erfan yagirmi king NASHWAN ma yace "ni kake tambaya?" Girgiza kai waziri ya shiga yi don inda sabo yasaba da wulakancin kanin nasa saboda yana bashi kudi makudai,shine mai martaba yayarda dashi yake kulada royal treasure da kuma kasuwancinsa na waje, "tohm get your act together" jay yafada yana mikewa tsaye yashiga gyara rigar kaftan dinsa wacca taji zallar dinkin gargajiya da tambarin asalin gidan sarautar NURISTAN yace "binsu zanyi inason insan meyake yi,kasan bazan taba barinsa ba harse lokacin dana cika burin ummunmu akansa lokacin ne zanyi relaxing," jinjina kai Erfan yay yana tapping gefen kafadarsa yace mai "seya dawo" cikin tafiyar nan tashi ta kasaita yafito daga cikin gurin, yashiga daddana baya in minute driver dinsa yakaraso karbar key yay ahannunsa kawai yafice don bayada bukatar wani yasan inda zeje din.

Daga bangaren peace kuwa barci ta kwanta bayan fitarsu EHSAAS da doctor yashigo yamata allurai yabata magani, ba ita tatashi ba se gurin 4,lokacin hankalin Veronica yasoma tashi ganin har lokacin Abraham be dawo ba bayan yace mata 2 ze dawo tanata kiran wayarsa baya tafiya takira driver sa, se wasa yake mata da hankali,dakyar ta iya lallabawa takai peace bandaki tayo wanka tai brush tafito da ita. maganin tasha mata abayanta da damtsen hannayenta inda duk shatin bulalar yake kumburin idon peace din yasoma saki saboda barcin data samu kuma zafin da cikinta ma yakeyi duk ya daina harta da nauyin da ya danne kirjinta jitai ya daina suna gama shafa maganin tadakko mata sabuwar riga irin ta dazun tabata tazira tana komawa gadon. abincin da nanny takawo Veronica tabude tana tambayar peace mezata ci aciki dan yamutsa fuska tai kafin tazaba,zuba mata tai a plate tamika mata,tazauna tanaci gently bakajin karar taunarta ko kadan,ganin har yanzun EHSAAS bedawo ba yasa takalli mom dinta da hankalinta nakan wayarta gaba daya tana sake kiran Abraham tace "mom karfe nawa," hankalinta sam baya kanta hakanne yasa peace tatsaya da cin abincin ahankali tace "mom" tana dan tabata se asannan tadago tace "uhm kince wani abune peace? "what are you thinking about mom?" peace ta tambayeta cikeda damuwa, Veronica dan shiru tai domin kunyar bude baki takeyi tacema peace waita shiga damuwa akan rashin ji daga Abraham ne mutumin dayay mata dukan mutuwa haka seta kega kamar bata mata adalci ba amman ya zatai zuciyarta na kaunarsa kuma tasan bazata dena sonshi ba har karshen rayuwarta, "mom is it Sir?" Peace ta tambaya ahankali,ranta na jagulewa,abincin da ko rabi bata ciba ta ture yafita aranta sbd ta tabbatar mom tafi kaunar Abraham akanta kam yanxun, Veronica mikewa tai. Ta danyi jeka kadawo kafin tace "since morning yafita be kirani ba kuma yace 2 zedawo bedawo ba I can't reach him, I'm just scared maybe something bad happened to him tunda betaba min haka ba Abraham baya wasa da lokaci ko kadan inyace zeyi abu zeyishi yajja kan time dinda yace," peace cikin gatse tace "tohm mom ko zaki bishi gurin taron ki gani ne," Veronica kallon peace tai tana washe baki tace "really baby will you be fine?" peace sakin bakinta tai tana kallon ta, "okay..... okay your nanny will be here soon, let me call her, if you need anything in case she'll attend to you baby I love you" takarasa tana tattara su handbag dinta da car keys dinta. peace batace komaiba hartazo ta sumbaci goshinta tana mata murmushi tafice in few minutes abin yafaru peace ta tsaya kallon kofar cikeda takaici she haven't even said yes daman kiris take jira Kenan,wani kunci taji aranta da yasa tature plate din abincin gefe kawai tadau ruwa tafara sha ranta yana kara baci sosai daidai tanaji ana knocking kofar dakin. kallon kofar tai tasan mommy won't knock in itace ta dawo sannan nanny beci ace har tazo ba, EHSAAS abinda ranta yaraya mata kenan kofa abude take amman mikewa tai ahankali tana dan dingisa kafar ta, daman ba'a riga anmayar mata da ruwan ba carnular nedai ahannayenta na dama takarasa gaban kofar tana budewa. murmushi tasakar masa,tana kare mai kallo ganin ya saka kayan tradition din da tace yasa ya bala'in yimasa kyau,shima murmushin yay mata yana dan dauke kansa daga kallonta don yaga ita bata damuwa da ganin ta ahakan dayake to kodan sbd banbancin addini da al'ada ya raya aransa wani shopping bag yabata kamar yasan baze tarar da ita da kayan mutunci na kirki ba yace "wear this now,nazo da bakin kiyi sauri sesu shigo," karba tai kafin tace mishi "thank you" yajawo kofar dakin yana bata baya dukda baze iya ganin komai dake cikin dakin ba amman still yabata baya. peace shigewa tai da kayan tabude,wasu irin dogwayen riguna ne abayas wanda kana gani kasan zasuyi shegen tsada guda uku, innalillahi harda set din bra da pant guda biyu,se kwalin waya irinta hannunsa ce sak,se kuma hijabi dogo da sallaya,rufe fuska tai tana murmushi tashiga kallon jikinta so he noticed she hasn't being wearing bra since morning, "shi ko kunya bayaji tohm waye yagaya mishi size dinta?" tafada lokacin data saka taji tamata daidai cif cif, tadauki doguwar riga daya tasaka tahade gashinta atsakiyar kanta tai Rolling gelen kamar yajja taga Arab Muslims girls nayi,wow kunga yajja peace tai bala'in kyau dukda fadawan data danyi tai looking very pale sbd rashin lpy amman yamata mugun kyau hade kayan tai ta maidasu cikin wardrobe din dakin dake VIP ward ne suna dashi, karasawa tai tabude masa kofar tundaga kan yan kananun slippers din dake kafarta da baya tantama bazata wuce cin takalmi 36-37 ba yadakko kallonsa har zuwa goshinta dake daukeda plasta an warware bandage din daya sameta dashi da safe fuskarta tayi yar karama cikin Rolling din tayi kyau kamar ka saceta kamar wata baby doll, "uhum uhum" yadanyi gyaran murya harda shafa wiya yana gyara throat,tadage masa gira irin yajja yake mata tana murmushi wai yagaya mata yatai,dan yamutsa fuska yay kafin yace mata "not bad,be a good girl" bari naje nashigo dasu turo baki ta shigayi wai seyace tayi kyau, "you look more than beautiful girl" yafada with his thick British accent dayasa peace tafara blushing agurin, "koma ciki karki fito kinji" jinjina kai tai takoma tana hangoshi yafice,cikin yan seconds taga wasu guards masu wani irin traditional uniform sunrufe gaban dakinnata.

Hango wasu manyan dattijai tai guda biyu suna tahowa tareda Ehsaas kana ganinsu kasan manyane saboda yanayin shigar alfarma ta asalin gargajiyar NURISTAN dake jikinsu, ahankali tai lowering gaze dinta tana kallon kasa tanajin zuciyarta na bugawa da sauri da sauri wannan shine step data taba dauka mafi girma arayuwarta tana fatan yazame mata haske na har abada acikin rayuwarta,har lokacin dasu EHSAAS suka shigo bata dagoba seda taji yakaraso daf da ita ahankali yace "peace," se asannan tadago tana kallon dattawan dasuka riga suka zauna awata doguwar cushion dake dakin ahankali ta tsugunna tashiga gaishesu kamar yajja taga musulmai na gaida manya sosai sukaji dadin hakan Malam liman yashiga saka mata albarka yana cewa ta koma tazauna itada batajin dadi murmushi tai kawai kanta akasa amman har lokacin tana adurkushe dukda kafafuwanta dake mata ciwo, EHSAAS yace "sit" cikin bada umarni hakan yasa tamike ahankali tana dingisa kafar ta zauna gefen gadon, ga mamakinta EHSAAS stool yadakko yana zama agefenta dukda basuda wani nisa amman dai ba daf da juna sukeba,kamshin turarensa ya cike mata hanci da kirji baki daya yace "peace wadannan suna daya daga cikin iyayena, Malam liman ne babban imam na NURISTAN royal mosque,se baba Harees wanda yake matsayin turakin NURISTAN,kuma dukkaninsu tamkar mai martaba suke agurina sune zasuyi guiding dinki," jinjina kai tai kanta akasa tana sake gaishesu, Cikeda tausayawa turaki yay gyaran murya,yasoma magana atausashe, "we heard what happened, Munzo nanne don mu nuna miki cewa ba ke kadai ba ce, What your father did was wrong, but wallahi, you have a family in us now. In sha Allah, you will never regret choosing Islam."

Malam Liman yana murmushi, yadaura da "Peace, kafin mu ci gaba, I want to ask you again. Do you still wish to embrace Islam, kuma ba wanda ya tilasta miki? Yakarasa idonsa akanta, dagowa tai takalli EHSAAS da shima ita yake kallo duk suna jiran amsarta ta jinjina kai,cike da kwarin guiwa tace "Yes... I'm sure. No one forced me, Na yarda da komai a zuciyata." Malam Liman ya gyara zama, ya kalleta da kyau. "To yanzu, ki fahimci cewa becoming a Muslim starts from the heart. And here are the 6 most important beliefs you should know and accept first." Ya dan numfasa, yana lissafawa da yatsunsa: 1. Imani da Allah (Allah SWT) Yarda da cewa Allah Shi kaɗai ne, ba Shi da abokin tarayya, kuma Shi ne Mahalicci. 2. Imani da Mala'iku (Angels) 3. Imani da Littattafan Allah (Holy Books) Yarda da cewa Allah ne yasaukar da littattafai ga manzanninsa kamar:Attaurat ga annabi Musa, Zabura ga annabi Dawuda, Injila ga annabi Isa shine Bible dakuke cemasa ayanzun,se Al-Qur'ani mai girma wanda aka saukar wa annabi Muhammad (SAW) 4. Imani da dukkan Annabawa - ciki har da Annabi Isa (Jesus), amma a matsayin Annabi ba ɗan Allah ba.Yarda da cewa Allah ya aiko da annabawa da manzanni, kuma Muhammadu (SAW) ne na ƙarshe. 5. Imani da Ranar Ƙiyama (Day of Judgement)Yarda da cewa za a tashi kowa daga matattu kuma a yi hisabi da sakamako na aljanna ko wuta. 6. Imani da Ƙaddara (Qadar - Good or Bad) Yarda da cewa duk abin da ya faru ko zai faru yana karkashin ƙaddarar Allah, ko mai kyau ko mai muni. Peace ta gyada kai cikin fahimta tace "Na karanta wadannan duka ,kuma na yarda da su," Malam liman yace "tohm Masha Allah,yanzu, lokaci ya yi da zaki yi Shahada shine declaration of faith." Jinjina kai peace tai cikeda nutsuwa da fahimta,Malam Liman ya ce da ita, "Ki maimaita kalmar shahadar nan dazan karanta miki da zuciya daya da nufin shiga Musulunci." Da tohm peace ta ansa mishi muryarta na dan rawa,tana kallon EHSAAS dake bata looks din karfafa gwiwa,malam liman yashiga fadin "Ashhadu an la ilaha illa Allah, wa ashhadu anna Muhammadur rasul Allah." Peace da rawar murya tashiga maimaita kalaman "Ashhadu an la ilaha illa Allah, wa ashhadu anna Muhammadur rasul Allah." Idanuwanta sun cika da kwalla amman kwallar farinciki sbd tadade tana sha'awar furta wannan kalmar har cikin zuciyarta amman tsoro da rashin kwarin gwiwa ya hanata, turaki cikeda jin dadi yace "Alhmdlh, alhmdlh,yanzun ke musulmace, welcome to Islam," kallon EHSAAS tai wanda murmushi yakasa barin fuskarsa shima yana mata kallon da take ji har cikin ranta kallon irin yajja yake alfahari da itane, Malam liman yadaura da, "Yanzu ana so kiyi Ghusl, wato wanka na tsarki na shiga musulunci," Turaki ya dora da kulawa: "Bayan haka, zamu koya miki yadda ake sallah step by step, Ba sai kin koyi komai a rana daya ba. Islam is a journey. Slowly, zaki koya yadda ake azumi, bayar da zakka, da karanta Al-Qur'ani." Peace ta share hawayenta, tana kallon su da godiya tace "Na fi jin kwanciyar hankali yau fiye da kowanne lokaci a rayuwata, baba nagode sosai Allah yasaka da alheri" Malam liman murmushi yay yana fadin "Bakomai yarinya mune da godiya,bakisan tagomashin ladan da zamu Samu bane" Ehsaas ya tsaya yana fuskantar ta cikin kulawa yace "One more thing, Peace. Islam does not ask you to abandon your family or culture. Ki kasance mai kyautatawa ga mahaifinki, duk da ba ya fahimtarki yanzu,try as much as possible ya fahimce ki nangaba sbd Islam teaches love, mercy, and patience." Jinjina kai tai ta ce, "Zan yi iya kokarina. Allah ya bani ikon jurewa." "Ameen" EHSAAS yafada yana mata murmushi, Malam Liman yadanyi gyaran murya cikin dattaku yake fadin "Kuma muna tare da ke,Your journey begins today." Turaki ya ce, "We will be your brothers in Islam, your protectors, and your teachers in this new life in sha Allah" Peace cikeda jindadi tashiga musu godiya. (Note this please duk maganar da akeyi da peace da turanci ake mata saboda bata cika fahimtar Hausa ba muna sirkawa da hausane saboda hausa novel muke rubutawa kuma in sha Allah nasamu lokaci zanfara translating dul inda akai turanci a chapters din)

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comments Like & Vote. [09/05, 17:47] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.