EHSAAS

Chapter 18

by @fatoumspassion

Bayan Malam Liman da Turaki sun tafi, dakin ya koma shiru. Peace ta kwanta saman gadon tana tunani, tana ta kallon rufin dakin kamar tana neman amsa a cikin farin ceiling din, Can Ehsaas ya dawo da takarda a hannunsa,ta dauka ma yatafi Kenan ashe rakasu yay yaje yadawo,amman yajima batasan meya tsaya yiba, "Alhamdulillah," ya ce, bayan yatura kofar dakin a hankali yakulle "An sallame ki yanzu daga asibiti. Na karɓo takardar daga gun doctor da kaina." Peace ta dago kai, tana kallonshi da mamaki da ɗan tsoro. "Za a bar ni in tafi?" Ehsaas ya yi murmushi yana zama gefen gadon. "Eh, amma ba gida za mu je ba. I'd like to transfer you to the National Royal Hospital wanda yake cikin palace harse kin gama warware wa tukunna don infi kulawa dake" Peace kasa boye tsoronta tai jiki asanyaye tace "Cikin palace fa kace? Me zai hana na koma gida kawai? I'm okay now " takarasa ashagwabe, Ya kalleta da kulawa, yana magana da natsuwa. "I want you to rest in a place where you're safe, comfortable, and protected. And… I want to introduce you to my father, the King yau bayan sallar Isha'i." da sauri tace, "Toh, amma-what if he doesn't like me?" dariya yay, yana facing dinta yace " karki damu,Malam Liman da Turaki za su sanar da shi komai game da ke. In sha Allah, he will accept you wholeheartedly. Amma I need you to be on your best behaviour, Peace. Show him your true self. The kind, brave, pure girl I know." Ta gyada kai a hankali, tana kokarin danne fargabar da ke damunta. "What if iyayen EHSAAS sukace basasonta what if basuyi accepting dintaba sukace yarabu da ita,zuciyarta bazata iya daukar hakanba" taraya azuciyarta "Yanzu lokaci ne da zaki yi wankan tsarki,domin shigarki Musulunci ya cika" Ehsaas ya fada da kulawa, Peace ta sunkuyar da kai, tana jin kunya. Amma Ehsaas ya ci gaba da bayanin cikin tsanaki, kamar malami mai koyar da ɗalibarsa. "Yanzu," ya fara da bayanin dalla dalla yajja zatai wankan tsarkin,shiru tai tana sauraronshi har yakammala, Yakalle ta yace "kingane? zaki iyayi dakanki? Peace ta gyada kai cikin jin kunya,tace "Zan iya?" "yauwa ki kula sosai kinji" ya ce yana miƙewa tsaye. "I'll wait outside. Take your time. In sha Allah, after Gusul, zaki ji wani irin sanyi da natsuwa. Then prepare for your first prayer, salatil Maghrib, that's approaching." Yana fita, Peace ta zauna na ɗan lokaci tana maimaita matakan a zuciyarta. Sai ta tashi a hankali, ta shiga bayin dakin asibitin, inda aka tanadar mata ruwan dumi. Ta rufe ƙofar, ta lumshe idanu,A zuciyarta, ta furta step one niyya kamar yajja EHSAAS yafada mata tace "Nayi niyyar gusul saboda shiga Musulunci." Tai murmushi bayan tagama hada ruwan,tace step 2 bismillah, bismillah tai acikin zuciyarta kamar yajja ya koyar da ita,tadanyi jim tace step 3 wanke hannaye sau uku,tanajin dadin yajja ta haddace duka abinda yafada,Ta tsugunna, ta dibo ruwa daga cikin bathub din acikin wani babban cup, ta wanke hannayenta biyu sau uku. Step 4 wanke al'aura ta raya aranta sannan dinga zuba ruwa a hankali har ta tsabtace Al aurar ta gabaki daya duk inda ya kamata. Sekuma alwala tafadawa kanta tana tina yajja ake alwalar,dibo ruwan tai tashiga daura alwala wacca tadade da iyata tun zamanta da makotansu shekarun baya anuristan yanzun kuma EHSAAS yadada tinatar da ita yajja akeyi daki daki. tace kafafu zanbarsu sedaga baya right tana ajje cup din,se zuba ruwa akai taraya aranta, tsugunnawa tai tasake dibo ruwa, tana zubawa a kai har sau uku, tana jin yanda ruwan ke ratsa gashinta mai laushi da tsawo,tana jin dumin ruwan na rasa kanta tawanke tass tass ta tabbatar yashiga ko ina da ina,Sannan tafara wanke gefen jikinta nadama ahankali tundaga sama har kasa,tana tabbatar da ruwan yataba ko ina,sannan takoma na hagu shima tayi tunda sama har kasa,Ta koma daga sama har ƙasa tana tabbata cewa ba wani sashi da ya rage ruwa bai shiga.tadudduba gefen kunnen ta da tsakanin yatsunta, tana tabbatar da ruwan ya ratsa,A ƙarshe, bayan ta gama, ta koma gefe ta wanke ƙafafunta da kyau kamar yadda EHSAAS yagaya mata tana murmushi tanajin wani sanyi acikin kirjinta.

Lokacin da ta gama, ta tsaya a gaban mirror tana kallon kanta,wani irin murmushi ta saki tinawa da cewar wai ayanzun tana amsa sunan muslim kamar dai EHSAAS,tajima kafin tadaura towel, Zuciyarta cike take da wani irin kwanciyar hankali da ba ta taɓa jin irinsaba ba. Sai ta kai dubanta zuwa taga, inda rana ke shirin faduwa. "Maghrib is coming. Ta furta a hankali, "Allah, ka karɓe ni." Shiryawa tashiga yi cikin wata doguwar riga mara nauyi akayanta bayan ta kammala tadakko katon hijabin da EHSAAS yakawo mata dazun tazira tana murmushi ita kadai kamar wacca taci kai, hijab din har kasa yake jamata. Daidai nan taji ana knocking sannin EHSAAS ne yasa tace "come in Sire" murda kofar yay yashigo idonsa yasauka akanta, "masha Allah" yafada afili yana kallonta yanajin kamar yacinyeta tsabar sonta dayay masa yawa azuciyarsa wani irin kyau yaga takara cikin hijabin yar karamar fuskarta takara kankancewa she's looking very cute kamar yar baby karancin shekarunta suka kara fitowa ta karasa gabanshi dasauri tana dan dingisa kafar take fadin "kalli nayi kyau," murmushi yay yana kallon kafar tata kafin yace "you shouldn't be roaming around kina tashi tsaye your legs are not fine har yanzun" turo baki tai tana fadin "I'm okay fa," yace "naji but go back and sit," make kafada tai tana fadin "sire naga garin ranar tafa dauke ba yanzun zanyi sallar magrib dinba," murmushi yay sosai yana kallon yajja take so excited tai sallah aransa yace Allah yasa tadaure. amman afili se yace "tohm malama pipi ai lokaci becika ba ko kibari yacika tukunna," jinjina kai tai tana komawa gefen taga ta tsaya tana kallon sama wai tanason lokaci yacika stool yadauka yakai mata kofar tagar yace "tohm zauna sekiyi kallon sosai kar kafar ki tai ciwo" zama tai tana sake gyara zaman hijab dinta tana kallon waje shikuma ita yake kalla,his heart is just beating fast for her,besan meyasa kullum kara kaunarta yakeji ba,juyowa tai suka hada ido tadan zaro mai ido tana fadin "bafa kyau kallon kurilla haramunne," bude baki yay se kuma yarufe yasoma murmushi,tadauke kai itama tana murmushi yace "wato your using my own words against me ba," jinjina kai tai tanna fadin "kasanfa nazama musulma so nima zan ringa maka wa'azi kamar yajja kakemin kullum kabari ma Malam liman yafara biyamin karatu nima zan ringa yin karatu da larabci kamar ka" tafada tana murmushi tana wasa da yatsunta,yace "I'll love that peace inason ma kifini ko hajjajuna," murmushi tai tana rufe fuskarta wai wayaganta itama tana larabci irin na EHSAAS, daidai nan wayarsa da ya saita lokacin sallah tasoma kiran sallah,peace tai zumbur tana mikewa cikeda jin dadi tace "tohm kaji lokacin yacika," dariya yashigayi yana jin dadin ganinta ahakan yace "tohm bari inje inyi alwala mana," ganitai yana kokarin nufar hanyar waje dasauri tace mai "ga bandaki akwai ruwa ai kashiga nan kayi," murmushi yay yanufi kofar toilet din harze shiga seya leko yakalleta yace "you look very beautiful in that hijab I'll get you more of them, inasonshi," murmushi tai tana blowing mai kiss in the air yadage mata gira daya irin zan kama kine yashige ciki. bejima ba yafito yadauro alwala harta shimfida musu sallayar yadau wayarsa compass yanuna masa inda alqibla take ya maida sallayar nan yace ta tsaya abayanshi shi yana gaba, "Ready for your first prayer?" ya tambaya cikin farinciki "Na shirya," tace tana saita tsayuwarta, yace "Zaki tsaya a bayana,ni zan ja sallar. I'll recite everything aloud, just follow me by standing, bowing, and prostrating when I do,kinji" Peace ta gyada kai cikin nutsuwa,Facing alqibla EHSAAS yay yashiga tada kabbarar harama,ya tada sallah,peace na bayanshi tana kwaikwayon duk abinda yakeyi,addu'ar bude sallah yafara karantawa kafin ya karanto suratul fatiha abayyane peace tanutsu tana saurara har ya kammala yashiga karanta suratul gashiyah cikin kira'arsa me masifar dadi kamar wani balaraben saudiyyah sbd zaqi,ahaka taita binshi har suka kammala raka'a uku yay sallama. Azkhar yashiga yi bayan ya kammala,tana kallon yajja yahade hannayensa biyu guri guda ya budesu, ba kamar yajja su sukeyi ba a church,yanata addua batasan meyake cewa ba don larabci taji yanata karantawa,abin na mugun mata dadi akunne kuma itama tanason ta koya,itama kwaikwayon yajja yay tai har ya kammala yashafa itama tai yajuyo suka hada ido tanata kallonshi with alot of admiration, yace "Congratulations,You just performed your first Salah." "Na gode… Allah ya saka da alkhairi." Tafada tana mai murmushi Dan gyaran murya yay yana kallonta kai tsaye, yace " kisani sallar nan zata zamo mafi girman abokiyar rayuwarki. Kamar yadda ke kika karbi kalmar shahada da zuciya daya, salla ce zata karfafa ki kullum." Jinjina kanta tai alamar tana fahimta kafin tace "Na ji wani irin sauki a zuciyata… kamar bana duniya." Ya yi murmushi yace "That's the sweetness of Iman." Knocking din kofar dasuka ji anayi ya sanya hankalinsu ya koma kan kofar ahankali EHSAAS yace "come in" dan yasan baze wuce Aman ba aikuwa shine yashigo yana murmushi yashiga gaishe da peace yana tambayarta yaya jikinta cikin jin kunya ta amsa ganin kato dashi yana gaidata. ledojin take out din daya yi musu ya ajje yana fadin, "abinci nakawo muku aunty kiyiwa uncle magana tunsafe beci abincin kirkiba yanata zirga zirga" dan kallon EHSAAS tai,ya gallama Aman harar wasa yace "kayi gulma kaji dadi ko bakinka baya shiru," dariya Aman yay yace "gara infada mata kila ita zata zaunar dakai tasaka kaci abincin," peace ta jinjina kai tana fadin "ka kyauta kuwa daka fadamin karka damu yanzun zansaka shi yaci" kallon EHSAAS yay, dasauri yace "yauwa aunty,bari naje mota inkun gama ina jiranku" yadau tasa ledar yafice, EHSAAS ne yashiga bude ledar yaciro pack din abinciccikan da Aman yakawo yasa daya gaban peace yana fadin "oya time to eat" karba tai taciro aspoon tadibo tana kaiwa bakinsa "oya time to eat kaima," murmushi yay yana dage mata gira yace "don't worry I will eat by myself" yakarasa yana karbe cokalin tabe baki tai tace "tohm kama samu zan baka abakin nafasa kuma kayiwa kanka," dariya yashiga yi yana tsokanarta ganin ta kulu harda cewa tabude shi yabata itace baby kin karba tai tace "kowa yaci nasa," suka shiga cin abincin ahankali tsaban tsokana irin na EHSAAS kawai seya faki idonta yakwaso nata yatura abaki yana mata dariya tayi kicin kicin da fuska alamar yakaita karshe,tace "ka cinyemin abinci ko zan ramane, don't worry akwai next time" takarasa tana fakar idonsa itama tadauke last piece of meat din dake kan abincinsa ta sanshi dason nama abincin nasafa ko rabi beciba nata yakeci yana cinye namanshi,aiko yahade fuska yana seta biyasa namansa,tashiga cinyewe tana rama dariyar dayay mata. dede nan nanny taturo kofar tashigo dauke da manya manyan hadaddun basket din abincin data shiryowa peace din iri iri tsayawa tai tana kallonsu,kafin takaraso tana gaida EHSAAS domin taga yamata kwarjini sosai kuma tadauka ko visitors ne peace tasamu, amsawa yay fuskarsa ba yabo ba fallasa kamar bashine ke kyakyata dariya yanzun ba,peace ta shiga tambaya yajikinta tana bata hakurin makarar datai wani abune na gaggawa ya tareta peace tace mata bakomai kawai yanzun takoma da abincin tabayar ita tarigada taci abinci,nanny hakuri tashiga bata peace tace mata tabari battason haka taje kawai tagode seda safe,nanny tace "amman Madam Veronica tace mata ta tsaya da ita harta dawo" girgiza kai peace tashigayi tace mata "taje kawai, ai ita tace taje kada tadamu" jiki asanyaye nanny tafice da kaya niki niki ahannu takarasa gaban motar da tazo da ita tamaida kayan bayan tana kokarin shiga gidan gaba taji "ance hello miss," dan juyowa tai suka hada ido da wani mutum bata taba ganinsa ba tunda take gurin babu wani haske hakan yasa bata wani tantance kamanninsa ba,yace "naga kamar daga bangaren da prince yake kika fito, waye ba lafiyane?" Nanny hade rai tai jin yana tambyarta abinda be shafesa ba tace "and who are you to ask me that? kuma waye prince?" Dan murmushi galadima yay yana karasa bayyanar dakanshi agabanta dasauri taji gabanta yafadi saboda tadauka yanzun tabarshi adaki se kuma datamai kallo natsanaki takalli cikin idonsa tagane ba wanda tabari adaki tareda peace bane wannan yadan manyanta kuma wannan idanuwansa bakakene ba kalar mage irin na wancan ba sannan wancan yafi haske sosai amman tsayinsu physique dinsu kusan iri dayane sedai shekaru da wannan ze nunama wancan amman dai baze haifeshi ba, "he is my nephew" galadima yafada yanawa nanny murmushi wanda yasan yana tsayewa mata arai sosai saboda shikansa yasan shidii hadaddan namiji ne me cikar halitta da kyawun fuska,kuma ayajja yakeda lakani babu macen dazata kalli cikin idonta yanemi abu agurinta tahanashi har abada kuwa. nanny daburcewa tai batasan ko tsafi yamata ko wani abun ba kawai tashiga mai bayanin "madam dinta ce batada lafiya sunanta peace ita mai aikintace abinci kuma tashiga kai mata," tambayar ta yay "wacece ita peace din?" kamar radio haka tashiga mai bayanin cewar "ai yar megidanta ce professor Abraham Zion me wannan asibitin da makarantar baki daya," jinjina kai jay yay kafin yace "meye alakar prince da yarinyar?" nanny girgiza kai tai alamar bata saniba tace mai ita bama tataba ganinsa ba se yau amman dai batasan meye dangantakar shi da peace ba. murmushi yay yana fadin "Inason ki ganemin hakan yanzun zanbaki lambar wayata ki bincika min duk abinda ake ciki kisanar dani kinji ko," jinjina kai tashiga yi yace "wayarfa?" dasauri tabude mota tadakko handbag dinta hannunta na rawa taciro wayar tamika mishi yakarba ya danna digits dinsa yana bata,takarba hannayenta still shaking suke don ji take kamar ranta zefita idan bata bi umarninsa ba,mota yakoma yaciro raffar kudi guda biyu yabata yace "ungo wannan kisaka kati" karba tai tana fadin "thank you," yace "your welcome" yana murmushi yakoma motarsa,yana kallon yajja security ke kai kawo akofar asibitin kuma yana hango motar Aman hakanne yasa be karasa ciki ba don samo cikakken bayani, sbd bayason wani yaganeshi itama nanny abinda yasa yagane dakinsu tashiga yaga Aman yamata magana lokacin datake shiga. Aransa so yake yasan me EHSAAS yake kullawa cikin asibitinnan,kuma baze barnan ba harse yasan meyake yi,kiran wayarsa yaga anayi ya dauka ganin waziri ke kiransa ya daga yanna fadin "yadai," Agadarancennan, Erfan yace "jay ina kake mai martaba yace akwai private zama bayan isha iya majalisar dattawa," jinjina kai kawai jay yay yanajin haushin wannan kiran da akai musu kuma yasan dolene ya amsa shi.

Bayan sunyi sallar Isha, EHSAAS ne yatattare kayan abincin dasuka gama ci yazuba aledar da aka kawo,yana kallon peace data cire hijab din jikinta don ya soma damunta da zafi, amman tadaura kanta da mayafin rigar data saka tamata kyau sosai, "Ban ga mom dinki ba tunda na dawo… Ina ta ke ne?"ehsaas yatambaya yana kallonta, Dagowa tai ta ɗan kallesa amma ba ta ce komai ba. Sai ta sunkuyar da kai, sannan ta cigaba da duba wayar daya kawo mata, "Peace? Is everything okay?" ya tambaya, yana dubanta da damuwa. Amma har yanzu ba ta ce komai ba. Kafin ya ƙara magana, ƙofar ɗakin ta buɗe da sauri. Veronica, ce ta shigo, kana kallonta kasan agajiye take, fuskarta cike da damuwa. Ta tsaya cak lokacin da ta hango Ehsaas, sai ta daure fuska tana kallonsa kamar wanda take zargi. "Peace," ta furta cikin gajiya. "ance yabar taron dawuri,naje duk inda zan gansa bayanan, amman kuma dana dawo naji wasu words na yawo cewa sojojin sarki sun ɗauke shi" takarasa tana kallon EHSAAS da shigowar ta aka tareta aka guntsa mata wayeshi da abinda ya wakana tsakaninsu da Abraham, directly tace mishi "Prince, idan hakan gaskiya ne, please… ka sake shi. Ba zan iya rayuwa babu mijina ba. Kuma kaduba relationship din dake tsakaninka da peace just forgive him tunda dai babu abinda yasameka,is just strangling attack… ka dubi wannan alakar a ranka ka yi hakuri da shi." Takarasa cikin gurbatacciyar hausarta, EHSAAS ya danji tausayin maman peace sbd daga gani ta wahala gurin neman mijinta amman bayaji akwai kalaman dazata gayamai yasaki Abraham a yanzun seya gane kurensa tukunna, Peace ta juya da sauri kallon EHSAAS tace "What?! He tried to strangle you and you didn't tell me?" Ehsaas ya ɗan kauda kai,don beso taji abinda ya wakana tsakaninsu ba beson yazama silar kara samun matsalar su, Veronica cikin masifa tace "peace he didn't! baki ganinsa he is fine, stop making it sound like a big deal memakon ki goyi bayan babanki your now showing concern for stranger daya kulle babanki" Veronica tafada tana harararsa, Peace ta miƙe a hankali daga gadon,da dan karfi take fadin "Ya cancanci hakan! Mom,kidena bin bayansa,kinsan Dad ya fita hayyacinsa,he can kill for real bakiga abinda yaymin ba nima ashe be isheshi ba,Ya nemi halaka mutumin da ya taimaka min fiye da kowa, He should learn his lesson!, EHSAAS karka budeshi" Tafada azuciye tana kallo Veronica, Veronica cikin hayaniya da fushi tace "Peace! Yaushe kika fara goyon bayan wasu sama da mu iyayenki,zaki zama ya mara albarka koh? Wannan shine ladabin Musulunci da musulmai suka koya miki kenan? Kinsa ankulle babanki,kina cewa kar abudeshi" Nan take gardama takaure a tsakaninsu Peace na dagewa akan gaskiyarta,cewar baza'a fito da Abraham ba ai inya daketa yaci banza ita yarsa ce,baida right din trying yay harming EHSAAS, Veronica kuma na dagewa tana kare Abraham tana cewa ai mistake ne kuma duk tsiyarta ubantane koso take taga ubanta an kaishi prison ankulle tana jin haushin yajja peace ke bin bayan EHSAAS.

Ehsaas mikewa yay yashiga tsakaninsu ganin daya yaki ragama daya acikinsu,besan peace nada fada haka ba seyau, yai gyaran murya cikin sanyin murya, ya ɗaga hannayensa alamun a saurare shi. Yafara magana ahankali cikin nutsuwa yace "Ma'am ba zan cutar da mijinki ba. I have no interest in that. Amma akwai wasu abubuwa da nake so na kammala da shi, After that, zan sake shi lafiya lau, in sha Allah, ke ke kuma peace this is not the way dazaki magana da mahaifiyarki apologize to her right now" Peace kallon mom din tata tai tana turo baki tace "But sire.." "I said apologize..." Yamaimaita, "Tohm sorry" Tafada akufule, Kafin Veronica ta ƙara roƙonsa don yana ganin girmanta amatsayin mahaifiyar peace baze iya mata more gardama ba, ya katseta cikin girmamawa yake fadin. "kiyi hakuri ma'am,amma yanzu zan tafi da Peace zuwa fada. Zata gana da sarki bayan isha'i, kuma zata zauna a Royal Hospital da ke cikin masarauta har sai ta warke gaba ɗaya," Dan jim Veronica tai EHSAAS yadaura "would you like to tag along with us? Zaki iya zuwa idan kina so." tsayawa tai na wasu dakikoki tana kallonsa. Hannunta a dunkule kamar mai rik'e wani sirri. Ta lumshe ido, sannan ta girgiza kai a hankali. "A'a, ba zan iya ba. Idan Abraham yaji na bi ku zuwa palace... zai ɗauka kamar na ci amanarsa. Yanzu haka, duk da cewa ya yi kuskure, har yanzu shine mijina. And you… you're not just a prince - kai ne wanda ya sa aka kama shi. He'll never forgive me." Peace kawai jinta take yajja taketa hakikancewa mijinta....mijinta jitake kamar tai throwing cewan a ina yazama mijinta agaban EHSAAS amman koda wasa wannan sirrin a iyayenta bazata taba iya tonashi agaban kowaba ciki kuwa harda EHSAAS har abada. Ehsaas ya kalleta cikeda understanding bai ce komai ba sai ya daga kai cikin girmamawa. "Na fahimta, ma'am. I respect your loyalty. Amma ina fatan wani lokaci zaki gane cewa gaskiya dayace, kidena tsoron bin bayanta, especially when it's in the interest of peace, she's your only daughter bakida wani kamarta har abada"

Peace ta dafa hannun mamanta. "Mom.... don't worry. Zan dawo. Kuma in sha Allah, abubuwa za su daidaita. Just pray for us."

Dagowa tai tana kallon peace idonta yacika da kwalla tanajin kamar tabi yarta amman battason Abraham yazo yagane su samu matsala dukda tasan nesanta peace daga gareshi ne karshen gatan dazata taba mata arayuwa amman bazata iyaba zadai tabari wani yayi, Tace "I'll pray for you peace in Jesus name," jinjina kai kawai peace tai takalli EHSAAS daya dauke kai jin Veronica tafara jero addu'ar su ta Christians peace bata nuna mata komai ba tace mata "amen" kawai,tana kallon EHSAAS daya hada few things na peace ajaka yariko mata,yace ma Veronica "Thank you for trusting me with your daughter ma'am," jinjina kai Veronica tai tace masa "yakula mata da peace" tatsaya tana kallonsu har yabawa peace katon hijabin ta tamayar suka fita tare a dakin. bin bayansu tai harsuka shiga mota tana kallonsu seda tadena ganin alamun motarsu acikin asibitin sannan takoma dakin asibitin ta kwaso sauran kayan peace dasuka bari itama tanufi gida zuciyarta nacike da tsananin kewar yarta da Abraham.

Aman ne yake tukasu zuwa palace, EHSAAS ne front sit,peace agidan baya tanata kalle kallen titi peace tunda take arayuwarta bata taba shiga palace din NURISTAN ba duk zamanta akasar tasha wucewa takofar gidan amman bata taba shiga ba ko sau daya,akwai tazara me girma tsakanin Zion university da palace hakanne yasa suka jima kafin su karasa.

Tundaga kofar palace din tasan lallaine tashigo cikin wata iriyar sabuwar duniya da bata taba shigarta ba,Peace ta kasa boye mamaki da al'ajabinta, saboda kyawu da qawatuwar gurin,takalli EHSAAS tana fadin "zan iya zuge glass in kalla dakyau," dariya Aman yashiga yimata, EHSAAS yagirgiza kai yana fadin "nope pipi not now I promise you a tower dakaina banson akallemin ke yanzun," dan turo baki tai dukda taji dadin abinda yafada har cikin ranta,seta bi abinda yace tacigaba da kalla ta cikin glass din motar, kayan ado ne na alfarma iri iri da aka kawaya fentinan, ginunnukan dashi dawasu hadaddun fitilu masu launin zinare da wasu hadaddun woods masu zane da aka kawo daga Turai da Gabashin kasar, harda kalar bishiyoyin dake gidanma bakalar wanda tasaba gani ako ina baneba. Kallon EHSAAS tai tana fadin "Your house is beautiful" Yadan kalleta tacikin Mirror kafin yace " is not mine,but thank you" Aman yadan kalleshi drama nasa da peace tana mai dadi sosai dede nan suka karaso kofar royal private court dogari ne yakaraso yana bude wa EHSAAS kofa yafito yashiga mai kirari ganin yana sake gyara zaman turban dinshi dase yanzun yamaida shi kansa sbd babbar fadar sarki daze shiga, Aman yafito ya zagaya da kanshi ya budema peace kofa,fitowa peace tai tana sake karema gurin kallo da yanzun take dada ganinsa sosai sbd sunfito waje. Kallon Aman yay yace mai "zeshiga ciki tareda peace se anjima zasu hadu a sashensa" "tohm" yace masa yashige motar yay gaba. EHSAAS yakalli peace yay mata murmushi da kyar tasamu tamayar masa saboda yajja taga garadan dogarai na tsugunna mai duk inda suka ratsa sbd da dan tazara kafin su shiga ainahin fadar sirri ta mai martaba sarki NASHWAN din,binsa kawai takeyi abaya tamkar dan karamin yaro dake bin bayan mahaifiyarsa. suna isa wata kofa hadaddiya yakalleta yace "yanzun zamu shiga ciki becalm kinji,my father is like your father,he is very nice duk abinda ya tambayeki answer it honestly kinji" jinjina mai kai peace tai har lokacin atsorace take. dogari yakalla,cikin kakkausar murya yashiga sanarda zuwan EHSAAS din nan danan aka wangale kofar suna zubewa suna gaidashi masu gadin gurin hannu kawai ya daga musu suka shige shida peace wani babban palour ne mai zurfi, wanda kowane gefe ke daukeda manyan maza dattawa ,dukkansu cikin shigar sarauta ta alfarma da natsuwa mai ban tsoro. Wannan shi ne majalisar shawara ta cikin gida ta Nuristan. Sarki NASHWAN na zaune saman wata karaga mai matukar kyau jikinsa sanye da kayan sarauta marasa nauyi ba kamar na yau da kullum da yake sawa inze shiga jama'a ba saboda wannan zama kamar zamane na manyan cikin gida don tattauna abinda ya shafesu,abayan EHSAAS ta labe tana binsa har suka karasa gaban mai martaba sarki kana kallon yarinyar kasan atsorace take,galadima tunda suka taho idanuwansa ya zuba akan yarinyar wacca inda yayi aure da wuri ya haifi kamarta ko wacca tafita amman haka kawai yaji kirjinsa na bugawa da sauri da sauri,jin EHSAAS nakai gaisuwa ga mahaifinsa yasa yadan dauke kallonsa daga kan peace yana maidashi kan batun da za'a tattauna din,cikin sanyin jiki EHSAAS yakoma gefe yabar peace gaban mai martaba ta durkushe itama tashiga gaisheshi kamar yajja taga EHSAAS yayi cikin girmamawa,gashi yabar kusada ita idanuwansu duk akanta suke ji take yi kamar za'a yankata saboda tsoro,ganin tanata rarraba ido alamar tsoronsu takeji yasanya mai martaba cikin nutsuwa da dattaku yace "yarinya matso nan kusa," ahankali takarasa gefenshi kanta akasa kwalla tacika taf a idanuwanta so take kawai tadaga kai koda zataga EHSAAS tadena jin wannan firgicin aranta,Muryar mai martaba taji asanyaye yace "Don't be afraid, my daughter. Daga yau We will protect you ,with everything We have,karki damu da abinda ke tsakanin mu da mahaifinki it's between us, Amma ke kinzama tamu yanzun kuma mun karɓe ki hannu bibbiyu."

Hawaye suka gangaro kan fuskar Peace,sbd yajja kalaman mai martaba suka kwantar mata da hankalinta da yajja kiranta dayay yarsa ya taba zuciyarta. cikin sanyi tace "Thank you... Father." Sosai kiransa da father datai yay masa dadi saboda ko yayan cikinsa mai martaba suke kiransa ze iya cewa rabon da yaji wani ya kirashi da baba tun EHSAAS yana toddler,amman tunda yafara tasawa shima formally yake addressing nashi,that means yarinyar nan tadaukeshi zuciya daya tamkar mahaifin da ya haifeta, Cikin barkwanci yace da peace "Father... I like how that sounds" dan murmushi dattawan sukai domin su kansu ladabin yarinyar ya mugun burgesu kuma sunsan kalar barkwancin mai martaba din,daya bayan daya suka shiga yi mata congratulations tana gaishesu cikin mutunci da mutuntawa,ana zuwa kan galadima bayan ta gaisheshi yace mata "congratulations! meye sunanki yarinya" dagowa tai ahankali suka hada ido kallo daya tamai tai kasa dakanta,wani irin tsalle yaji kirjinsa nayi sbd yajja zuciyarsa ke harbawa tunda yake be taba ganin macen data tafi da imaninsa irin wannan yarinyar ba,kalli idonta kamar ita taiwa kanta, "Masha Allah" yafurta aransa yanajin kila lokacin da zeyi settling down yayi koma a ina EHSAAS yasamo wannan yarinyar rabonsa ce in sha Allah,seta zama mallakin sa,cikin yar karamar muryata yaji tana fadin "peace?" jinjina kai kawai yay yana kallonta tacigaba dagaida sauran. Mai martaba kallon EHSAAS yay da murmushi akan fuskarsa na irin alfahari dashi da yake, yace "You did well, yarima, You protected her like a big brother - even better than many real brothers would do." Peace asace tadan dago tana kallon direction din EHSAAS, amman se taga yayi saurin juyar da kai kamar yana jin kunya. Mai martaba yace "Na ji kince sunanki Peace. Lallai suna ne mai kyau, amma... a musulunci, muna da wasu sunaye masu zurfin ma'ana, wadanda suke da asalinsu daga harshen Alƙur'ani da Hadisi. Do you want to change your name?" Peace ta yi shiru na wasu daƙiƙu. Ta juya ga Ehsaas irin ya temake tannan amman seyay ƙasa dakai yana murmushi,shiya ma manta batun canza sun, ahankali ta ce da siririyar muryarta "Nabar maku zabi Allah ya temakeka duk sunan daka zabamin inaso" Kallon kallo suka shiga yi atsakanin majalisar dattawan,mai martaba yay murmushi irin nasu na manya, domin yaji dadin maganar peace din sosai, Ahankali yace "Your name was Peace,And in Arabic, the very essence of our religion… is ISLAM. A name that means submission to Allah, devotion, and inner peace. It is not just a name - it is a complete way of life,wannan sunan muka zaba miki,kuma ma'anarsa tafi zurfi fiyeda wanda kikedashi abaya,ina fatan zaki karbi sunan nan da muka zaba miki ISLAM" Tafaraddaya peace taji zuciyarta tayi na'am da sunan taji ta karbeshi hannu bibbiyu, Tace "na karba, nagode Allah yasaka da alheri Allah yakara girma da daukaka father" Masha Allah kakeji dattawan suna furtawa atsakankanin su don sun yaba da sanin ya kamatan na yarinyar dukda yajja takeda kananun shekaru banda waziri Erfan dayaji tsanar yarinyar tashiga ransa tafaraddaya batareda yasan dalilin sa ba shikansa EHSAAS besan peace nada zurfin tinanin irin hakaba seyau din, yanajin dadin hakan aransa sbd ayajja yaga mai martaba yana murmushi yasan kalaman yarinyar nayi masa dadi. "Munai miki maraba da shigowa cikin mu ISLAM turaki" yafada mata,cikin jindadi tai masa godiya anan take mai martaba ya umarci sarkin kofa daya kira jakadiyyar Fulani tatafi da peace can bangarenta,sannan ya umarci waziri daya tura babbar royal doctor dinsu mace zuwa can unguwar Fulani acigaba da duba peace din har tawarware yarsa bazata zauna a asibiti ba. EHSAAS jiyay kirjinsa yana bugawa don yasan indai har peace ta zauna akusa da Fulani koda nakwana dayane se Fulani tagane abinda yake tsakaninsu saboda soyayyar dasuke ma juna abayyane take gashi daman yana hadata da ita awaya su gaisa sanda suna Oxford, what if intaiwa peace wayo ta bugi cikinta taji meke tsakaninsu kafin yagama shirya yajja ze tinkari mai martaba da maganarsu? ina lallai baze bar peace tazauna agurin Fulani ba amman yasan be isa ya take abinda mai martaba yace dinba. yana cikin tinani yaji shigowar jakadiyyar Fulani tana mika gaisuwa ta kama peace Ahankali,yanajin yajja idanuwan peace din ke akansa da alama tana jira ya biyosu ne amman betashi ba sbd kunya yanajin har karar rufe kofarsu, bayanai yaji anshiga yi akan harkokin kasa, kwata kwata hankalin EHSAAS baya kansu yanaga peace, "what if they don't treat her right? shifa yafison duk motsi yajita akusa dashi jiyake kamar wani ze gutsurar masa ita,don indai akan peace ne har fulani jiyake baze barmata itaba saboda yasan kalar matar da takeso ya aura ba irin peace bace amman yanada tabbacin mahaifiyarsa is nice bazata taba cutatar da itaba koda kuwa battasonta. "yarima kanaji kuwa" yaji wambai yana tabashi da alama tundazun ake tambayarsa hankalinsa baya kai, dagowa yay yana kallon wambai before yace "Ayi min afuwa,baba mekace?" dan girgiza kai yay yace "tinanin mekake haka kuwa? tundazun mai martaba yay magana bakajiba,waziri yayi ma bakaji ba,seda ni natabo ka," dan girgiza kai yashiga yi yana fadin "aimin afuwa ranka ya dade" yana kallon sarki yace "akwai abinda yadan shamin kaine" mai martaba closely yake kallonsa,waziri cikeda kulawa da izgilanci yace "yarima ai baka saba da zaman fada bane shiyasa kila har kaji kanka nama ciwo,yaro dan madara,ahaka za'ai mulkinnan kuwa?" yafada adan gatsale asiyasance,turaki yace "hattara Erfan kasan mezaka ringa fada agaban mai martba da yarima," jinjina kai yay yana fadin "tuba nake ranka yadade amman yarimanne kwata kwata gani nakeyi hankalinsa baya kan NURISTAN da jama'arta ko kotu becika zuwaba,sannan bayasa hannu akan duk wani abu da yashafi mulki," wambai yace "Erfan" cikin dan fada fada mai martaba daga musu hannu yay alamar ya isheshi sukai shiru baki daya yakalli EHSAAS cikin yanayin da bazaka fuskanci emotions din fuskarsa ba yace masa, "kazoda mahaifin yarinyar can in Allah ya kaimu,xamuyi magana dashi" jinjina kai EHSAAS yay yana amsawa da "tohm in sha Allah ze kawoshi," sallamar sa mai martaba yay yace "yaje yahuta," abin yakara tunzura zuciyar Erfan wato su gasu dutsinaye ko tun dazun sukenan ba ace suje suhuta ba se EHSAAS dan gwal mikewa EHSAAS yay yamusu godiya yana ficewa a fadar baki daya,direct unguwar Fulani yawuce domin yanason yaganta yadubata.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment And Vote.

Fans din Mehtav kuna ina stay tune wannan satinnan zaku jita😂nabaku spoiler team Mehtav.

Wai kuwa yakuke ganin za'a kare jay fa ya kamu,kuna ganin EHSAAS ze rigashi kuwa?

Muhade a comments section. [10/05, 20:04] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.