EHSAAS

Chapter 19

by @fatoumspassion

Ababban parlour ya samu Fulani ta kashingida saman wani tumtum jakadiyyar ta tana dan daddanna mata kafafuwa yakarasa gefenta yazauna yana dan basarwa se rarraba idanuwa yakeyi ko zega peace din amman beganta ba, Fulani tambayarsa ya yake takeyi,tace mai ko yaci abinci cikin kulawa. jinjina mata kai kawai yay,kafin yace "ke kadaice anan ina kawar tayaki hirar?" yana referring ma jalila cousin dinsa,dan murmushi tai irin nasu na manya don tasan be taba tambayar jalila ba tunda yake har yaushema yadamu yake noticing babu wani agurina hunch dinta yazama gaskiya kenan akan yarinyar. "Maama ina take?" ya tambaya cikeda shagwaba,shafa kanshi tai tana fadin "jalila naciki tareda bakuwar mai martaba,ancemin tare kukazo koh?" dan baya yay dakanshi yana jin tsanar palace dinnan over, wato har anzo ankawo mata gulmar yazo dawata. dan jinjina kai yay yace "maama she's the girl danake baki ku gaisa a Oxford is a long story maama,hope she's fine" yafada yana dan sosa keya,tabe baki Fulani tai tana watching dinsa closely tace "aini nadauka sunan yarinyar da kake koyawa karatu peace ita wannan bataimin kala da arna ba impact tacemin sunanta Islam" dan dagowa yay yanajin dadin yajja har peace tafara introducing kanta da sunan da mai martaba yarada mata. yace "she's thesame person, maama labarinta mai tsayine inzaki bani dama zanmiki bayani dalla dalla ayanzun," dan murmushi tai kafin tace "idan har ka kuskura ka boyemin wani abu dangane da alakar dake tsakaninka da yarinyar can, kasani itace dama ta karshe dazan baka, bazan kuma sake sauraronka ba," jinjina kai yay yana fadin "kiyimin afuwa maama naboye miki badon komai ba sedon gudun bacin ranki har zuwa lokacin da zanyi nasarar jawo da hankalinta zuwa ga addinin musulunci," kallon jakadiyyar ta tai tace "tabasu guri" sum sum sum matar tafice daga gurin tana kullo musu kofa seda fulani ta tabbatar tatafi sannan takalli EHSAAS alamar tana sauraronshi. nan yashigaa bata labarin haduwarsa da peace be boye mata komaiba dangane da alakarsu har sonta da yakeyi dayajja itama take sonshi da kuma yajja babanta baya kaunar musulunci da yajja yake azabtar da ita gaba daya halin da yarinyar keciki be boye mata ba. jikin Fulani hajar sanyi yay gaba daya tamike zaune daga kashingidan datake tana fadin "babana, meyasa baka sanar daniba, dani dakaina zan daukota inkawota gabana, tabbas yarinyar nan taga rayuwa, ga kudi ga kayan alatu amman samsam bata cikin farinciki, Allah sarki,ina alfahari dakai nasarar jawota zuwaga addinin gaskiya, Allah yacigaba da baka ikon yin ayyukan alheri iri haka babana, amman ina tsoro banida wani say akan soyayyar ka da ita kasan bazan taba iya sabawa mahaifinka ba kuma banajin ze taba amincewa da bukatar ka ta aurenta ko zaka iya daurewa kacireta daga ranka saboda ita kanta yarinyar zatafi samun nutsuwa da zaman lpy idan akai hakan, tayi kankanta data kasance matar yariman NURISTAN,batada experience kasan meye gidan sarauta kuwa EHSAAS? don baka taso cikinsa bane kake tinanin zama cikinsa ze bawa peace zaman lpy amman kasani ko mace cikakkiya wayayya me ilimin addini dana boko ingantacce tana shan wahalar zaman gidannan balle karamar yarinyar kamarta, for her wellbeing EHSAAS ka kyale musu yarinya natabbatar mai martaba baze barta ahannun daze cutar da itaba nizan iya rike maka itama tareda jalila indai hakan ze saka farinciki" girgiza kai yashiga yi har idanuwansa ya kada yay jajir yarike hannun Fulani yana fadin "nasan hakama zakice shiyasa naboye miki mgnr ta,maama ina kaunarta, jinake sonta ajinin jikina yake bazan taba iya kara kallon wata mace amatsayin mace ba inba itaba,maama ki temaka min I'm ready to do anything,nace anything indai zaku barta tazama matata mallakina inkince tayi kankanta da zama anan I'll take her with me, I'll find another state impact maama zan iya kaita wani kasar in ajjeta don kartai suffering," rungumeshi Fulani tai tana feeling pain dinsa,tasan dawiya EHSAAS ya budi baki yace yanason abu amman indai yace yanaso tohm wllh yanaso dinne da gaske kuma babu abinda zeyi stopping dinshi daga son wannan abun sedai ikon Allah, "I'll help you Fulani tatsinci kanta da fadar hakan amman nasan it'll be hard, lie low for now karka bari kowa agidannan yasan alakar dake tsakaninku inba hakaba wani ze iya amfani da hakan gurin tarwatsa alakar dake tsakaninka da mahaifinka kuma ba zakaso wani abu yasamu yarinyar ba ko?" jinjina kai yay yana fadin "I'll protect her with all my life maaa inasonta," jinjina kai Fulani tai tace "zankula da ita in sha Allah zantayaka riketa," jinjina kai EHSAAS yay yana sumbatar hannayen mahaifiyar tasa sunjima ahaka yana jikinta batareda sunce komai ba,ganin dare nayi yasa tacemai "yaje yahuta" dukda yaso ganin Islam din amman Fulani tace "yadaure kilama sunkwanta yabari seda safe." EHSAAS na ficewa, Fulani tamike,alkyabbar ta tazira kawai tafice zuwa bangaren uwar soro domin bazata iya bari seda safe zata fada mata ba,domin ita kadaice kawar shawararta wacca take tamkar mahaifiyarta take,donta haifi mijinta kuma tasan uwar soro ce kadai zata iya durkusar da mai martaba yay yajja takeso,don haka zataje tanemawa danta farincikinsa.

bangaren peace kuwa tayi jigum tana kallo jalila daketa chatting awayarta tanajin dama batabar tata wayar acikin kayanta dake motar Aman ba,bata dauka mahaifiyar EHSAAS zata karbeta hannu bibbiyu hakaba dukda few words tace mata na welcome ta tambaye ta sunanta kafin ta hadata da jalila amman still she can feel energy din matar bata tsaneta ba definitely. Jalila cema tadanyi mata tambayoyi irinsu daga ina take? wacece ita? sanin basuyi maganar yajja zatai introducing kanta gurin su da EHSAAS ba yasanya kawai tai ignoring questions din jalilan, wanda jalila tai stamping as jinkai da wulakanci hakanne yasa tai mata banza tashiga sha'aninta.

Maisoon mikewa tai zumbur daga kwancen datake tana kallon baiwar data kawo mata zancen, kikace mace fa? Budurwace? Zatai wa? wana irin kallo kikaga yana mata? Jinjina kai matar tashiga yi tana fadin "Allah ya temakeki wllh ance se rawar kafa yakeyi akan yarinyar, batada wani girma don tanada karancin shekaru kuma ance idanuwanta kamar lu'u lu'u tsabar kyau," "dallacan gafara" Maisoon tafada tana bige yarinyar " agabana kike yaban idon wata shegiya jaka,uwar meye sukai afadar tohm? dakuma bangaren uwarsa da ba'a barina inshiga yau ankai wata banza takwana," yarinyar muryarta na rawa tace "wacca tafadamin tace itama bata saniba amman dai ba yar uwarsu fulani baceba don kaf yan uwansu dake zuwa tasansu." "Hmmmmm* Maisoon tafada tana fadin " zakuwa ai tashin hankali agidannan wata jakar aka samo masa bayan wacca take cikin gidannan kenan" fuuuu tafice kamar iska na kadata tsabar siranta da iyayi,dakin iyayenta tanufa straight tana fadin "daddy,daddy daddy" daidai waziri Erfan na bude kofa cikin kulawa yake tambayarta "yar daddy lafiya naji ana kwada min kira haka? "har prince zezo da mace cikin gidannan karasa fadamin uwar wacece ita kuma naji ance har fada taje, bayan kamin alkawari duk wani abu daya taso indai akan sane zaka kefadamin," dan tsaki yaja yana dafa wiyan Maisoon yake fadin "yanzun akan wannan kaskantacciyar yarinyar kike daga hankalinki yar daddy zomuje zo zauna inmiki bayani" yakarasa shigo da ita ciki yay yana zaunar da ita adaya daga cikin manya manyan royal chairs din dake bedroom din kamar parlour,nan yashiga mata bayanin wacece peace dakuma matsayin zamanta agidan nadan lokaci kafin su saisaita da mahaifinta da kuma alakarta da EHSAAS,cewar koya mata karatu yake abaya amman yanzun ba abinda yake hadasu bayan temakon daya mata, tace "shegiya arniya ashema tubabbiya ce shine aka dagan hankali acikin darennan daddy nidai karka manta da alkawarin dakaimin" yace "ni na isa inmanta da alkawarin danai miki yar daddy ai EHSAAS nakine mijinkine ke kadai har abada," murmushi tai tana fadin "ina kaunarka daddy na" yace "nima ina kaunar ki yar daddyn ta" rungumeshi tai kafin tamike tace "natafi," bye bye yamata yanajin relief acikin zuciyarsa don babu abinda yatsana arayuwarsa irin yaga bacin ran Maisoon itace yar autarsa amman tamkar itace jarrabawar rayuwarsa kaf yayansa matane kuma duk ya samu ya aurar dasu, burinsa nakarshe akanta yake ita yake fata zata daukar masa fansar abinda akaiwa mahaifiyarsu acikin wannan masarautar kuma hakarsu bazata taba cimma ruwaba harse ta auri EHSAAS wanda ashirye yake ya aikata koma meye danganin wannan burinnasa yacika.

Daga bangaren galadima kuwa kamar wasa yakasa barci adaren ranar dukda kuwa babu irin abinda baishaba don yaji relief din abinda yakeji akan Islam amman yana kulle idonsa fuskarta yake kallo da kyawawan dara daran idanuwan ta, "fuck" yafada yana mikewa zaune saboda jiyake yana neman zarewa takarfi da yaji, Allah Allah kawai yake safiya tayi agama case din yarinyar da mahaifinta koma nawane ze biya uban don yabashi ita kota halin kakane seya mallaketa, inkuma yaki wllh ze iya kashesa yadauketa yamaidata tashi takarfi dayaji.

EHSAAS kuwa yana komawa bangarensa Aman yasa ya siyawa mamanshi ticket yatura mata,yamata text kawai yace "pls tazo yana bukatar ta" don bayason peace tacigaba da zama a palace dinnan hankalinsa baze kwanta ba harse tabar gidan,mimah da tohm kawai ta ansa mishi don tasan EHSAAS baze taba yimata kiran gaggawar nan ba idan bawai abin gaggawar ne yatashi ba.

Washegari da asussuba jalila tatashi peace tana fadin *ke asubah tayi kitashi kiyi sallah," mikewa peace tai ahankali tace mata "thank you,* tashige tai alwala tafito inda jalila ta idar da sallar takalla takarasa tazura hijab dinta, ahankali takalli jalila tace mata "yazanyi?" cikeda raunin zuciya. jalila tadago ido tana mata kallon irin kimma rainamin wayonnan saboda kwata kwata batai mata kala da arna ba don bata ganta da dogwayen farata ba balle kuma karin gashi kuma bata jita tana wari ba shine take tambayarta ya ake sallah, "kada Allah yasa kiyi indai nice zankoya miki," tsayawa peace tai tayi zuru zuru gashi ba waya balle takira EHSAAS tana ganin jalila tadau al Qur'ani tanata karatu daidai Fulani na turo kofar dakin,tasakar wa peace murmushin dayasa hakoran makanta na gold guda biyu suka bayyana,peace murmushi tamata tadurkusa tana mata barka da safiya,rikota jikinta tai tana tambayar ta yajja takwana sosai taga banbaci akan yajja tai treating dinta jiya,ta tambayeta tace "tayi sallah?" girgiza kai tai Fulani takalli agogo tace "gashi lokaci naneman shigewa ke jalila baki tasheta da wuri bane," jalila ajje Al Qur'an tai agefe tace "ina idarwa na tasheta tayi alwala dan rashin mutunci shine take wani tambayata yajja za'ai taga namata kala da Sa'ar wasanta ne aunty," ran Fulani baci yay cikin fada take fadin "yaushe kika zama mara tinani jalila idan mutum ya tambayeki abu inbe saniba haka aka cemiki wulakanci akeyi eh? ko haka na koyar dake ita wannan ba kamar karamar kanwarki takeba,meyasa baki tambayeta dalilin dayasa tace miki haka ba common bata hakuri yanzunnan," "amman...." jalila bata karasaba kallon da Fulani take mata yasanya tace "kiyi hakuri tohm,* Fulani takalli peace tace "she's immature,kiyi hakuri kinji," jinjina kai tai tana fadin "bakomai," nan fulani tashiga guiding dinta,jalila tai tsuru tana kallon abin mamaki har karatun da zatai se ankoya mata aranta tace "batai min kala da mahaukata ba kodai kwakwalwa taci" ran fulani tai peace tatayar da sallah tana kallonta hartai raka'a biyu tai sallama kuma Masha Allah tanada saurin fahimtar abu don daki daki tai kamar yajja takoyar da ita zama sukai fulani tadako mata littafin azkhar mai fassarar turanci tace ta karanta azkhar din idar da salla da kuma na safiya karba tai tana godiya kuma tashiga karantawa tiryan tiryan Fulani takalli jalila tana fadin "biyoni," fita tai jalila tamike tabi bayanta. Har karamin parlour fulani suka karasa Fulani ta zauna jalila tazauna a gefenta tana fadin "Aunty," fulani cikin fada me kama da nasiha take fadin "ita wancan yarinyar da kikema hayaniya inda kinada kanne zatai kanwarki tanawa eh jalila? kintaba ganinmu muna wulakanta wani acikin ahalinmu eh? girgiza kai jalila tai,tace "tohm treat the girl right she's a new convert,guide her well duk abinda ta tambayeki guide her with love and compassion irin wadannan se kiga ma sunfiki kusanci da ubangiji domin kinsan ayanzun haka batada zunubi ko daya akanta tamkar jaririyar da aka haifa yanzun take don haka becareful" dan dagowa tai tana kallon Fulani saboda taji mamakin abinda fulanin tafada new convert fa,kwata kwata batai mata kala da arna ba amman ahankali tace "in sha Allah bazan sakeba Aunty" jinjina kai Fulani tai tace "tashi kije jakadiya zata kawo mata kaya yanzun, ki bata duk abinda zata bukata sannan seku fito breakfast" jinjina kai tai tana juyawa ta koma ciki akan sallayar ta tarar da peace se duba wasu addu'o'in takeyi don tagama zikirin safiyarta. karasawa tai tana dafata tai mata murmushi tace "Islam kiyi hakuri bansan baki sani bane,in sha Allah bazan kara ba kinji," murmushi peace din taimata tace "bakomai yawuce," zama jalila tai saman katon gadonta tana fadin "yanzun taso kizauna ki fadamin me dame dame kikeda tambayoyi akansu nayi miki alkawarin duk zan ansa" murmushi peace tai amman still taki sakin jikinta da ita tadai zauna agefenta tace mata battada tambaya alhali tambayoyi ne fal acikin kanta kawai dai tafi feeling comfortable tayiwa EHSAAS su. yafi fahimtarta yabata gamsasshshiyar amsa jalila nada ilimin addini sosai saboda kusan tareda EHSAAS suke daukar ilimi agurin mahaifinta hakanne yasa tashiga yiwa peace bayani akan five pillars of Islam,tiryan tiryan tundaga shaidawa babu abin bautawa da gaskiya se Allah,tazo tafara mata bayani akan sallah dalla dalla tashiga fayyace mata anayin sallah guda biyar arana subh,zuhr,asr, magrib se isha,duk tashiga karanta mata raka'o'in da akeyi,tadakko wani note da biro tabawa peace tace taringa taking note din duk abinda take fada ahaka ahaka tun peace bata saki jikinta ba harta dan saki tabude kunnuwanta dakyau tana kwasar ilimi agurin jalila. ahaka jakadiyya takaraso mata da wata trolley wai kayanta ne tasan kayan dasuka dibo basu kai haka ba sannan tace "Fulani tace su shirya su fito karin kumallo hakanne yasa suka tsaya da karatun," jalila tace "peace tafara shiga tai wanka," tace mata tohm abandakin tacire kayanta saboda tanajin kunya bazata iya cire kaya agaban jalila ba,tai wankanta data gama ta daura babban towel din jalila ta yafo karamin akafadarta ta lullube jikinta dashi tafito don batason jalila taga tabbunan dasuke jikinta,jalila tai mata murmushi tace "harkin fito kenan" jinjina kai tai,jalila ta gefen ido take satar kallon yarinyar ashe jiya bata ganta dakyau acikin hijab yarinyar has wani unique aura of beauty da inbaka nutsuba bazaka taba ganiba she has a very beautiful body too,don at her age kalar jikin datake dashi bakowace mace me shekarunta ke dashi ba acike take tako ina batada rama ajikin ta sannan batada kiba,wani irin hourglass body shape ne da ita. jalila dai ta tabe baki tana shigewa ciki,peace bude jakar tai tasoma daddaga kayan duka dogwayen rigunane abayas da irin masu mayafannan yan saudi,babu kananun kaya ko kadan se hijabai,harda underwears duk sababbi,se can kasa kayan da suka taho dasu harda wayarta,wani irin farinciki yaziyar ceta dasauri tadakko wayar tana kunnawa,se kuma takarasa gaban mirror din jalila duk ba irin kalar mayukan datake shafawa bane saboda skin dinta da jalila ba daya bane jalila farace tass kamar EHSAAS itakuma batada haske,amman ahaka tadan shafa saboda kar fatarta tabushe, tadan goga turarrukan ta kadan tunda tace mata she can use everything nacikin dakin innerwears dinta tasaka tadaura sabuwar abayar ta mai kyau daidai ita har tsayin yamata kamar ya aunata. tadau comb tana dan taje dogon gashinta daya dan hargitse, daidai jalila nafitowa murmushi ta mata tana kallon gashin kannata tanada gashi ta mafi peace gashi amman kuma,yajja taga peace nataje kanta straight yana tafiya saboda santsi da laushin kan yasa taji tana sha'awar gashin peace din. tace mata "harkin gama shiryawa" jinjina mata kai tai,jalila aranta wannan dai inda batai magana ba se nace kurmace ba abinda ta iya se body language mgn sekace za'a cajeta,jalila shiryawa tashiga yi peace nazauna tana dan tattaba wayarta,tanason takira EHSAAS amman kuma tanajin kunya,gara dai tabari shiya kirata tafada aranta tana kallon yajja jalila ke zana hadaddiyar kwalliya afuskarta sekace wacca zataje gasar kyau ba breakfast zasuyi ba. juyowa tai tana kallon peace tace "kema kizo kidan shafa powder da kwalli se kinfi yin kyau," murmushi peace tai mata tace "I'm okay like this, amman kinyi kyau fa," murmushi jalila tasaki don tanason intai kwalliya ayabeta tace "nagode peace kin tabbatar dai na hadu ko?" jinjina kai peace tai,cikin zumudi jalila tace "Allah yasa shima yaga namai kyau haka,aitunda naji yazo garinnan nake jiran ranar nan nasan dai dole anan zeyi breakfast tareda mu," tayi expecting peace ta tambayeta waye amman setaji peace tayi shiru domin idan kanajin ana maganar mind your business tohm peace zata dauki tutar yabo agurin. tana daura dankwalin hadaddan lace din data saka tace ma peace "muje ko kar suyita jiranmu," mikewa peace tai tana yafa mayafin abayan saman kanta,atare suka fito,se lokacin peace take kara ganin kyawu da tsaruwar sashen fulanin mansion me zaman kansa kusan parlour hudune da ita kuma kowanne yana wane wancan saboda haduwarsu da irin yajja aka zuba kayan alatu akwai traditional interior akwai modern interior,kana gani kasan kashigo asalin gidan sarauta masu jida kudi da iko babban falon fulanin suka nufa tundaga kofar tajiyo kamshin turarensa mai sanyi da saka kwanciyar hankali ya doketa,jalila ma tajiyo kamshinsa takalli peace tana fadin "da alama yaya yana ciki," da sallama suka shiga falon jalila agaba peace tana bayanta kamar yar kanwarta,dukda tafita tsayi amman kana kallon jalila kasan tagirmeta tafita cika ido,jalila na murmushi takarasa kusada Fulani tana rungumeta tace "good morning aunty, Allah yaja da zamanin ki" murmushi fulani tai tace mata "morning," peace tadurkusa kasan carpet gefen Fulani tana gaisheta Fulani kamo hannayenta tai tazaunar da ita gefenta tana tambayarta yatake,kanta akasa tace mata "she's fine saboda yajja takejin idanunsa na yawo akanta," jalila tajuya tana karasawa gefen dayake tace mai "barka da dawowa yaya yarima fatan kasauka lafiya?" murmushi yay mata yace "thank you jalila nadawo lpy," ganin peace bata gaisheda EHSAAS ba yasa jalila tace "Islam bakiga yayana bane ba baki gaisheshi ba," aranta rayawa tai tohm daman EHSAAS nada kanwa betaba fada mata ba,dagowa tai ahankali idonta ya sauka cikin nashi yana binta da kallo kamar ya hadiyeta tsabar kyan data mishi,tace "barka da safiya," "barka dai" ya amsa yana dan basarwa, "Ftn kin kwana lpy?" Ya tambayeta yana dan kallonta, jinjina masa kai kawai tai, Fulani na kallonsu kuma kamewar yarinyar da nutsuwarta da yajja bata nuna rawar kafar ganin EHSAAS ba yasanya taji hankalinta yakwanta da ita daman anason mace takasance me kame wa akoda yaushe. jalila ta lurada irin kallon da EHSAAS yake bin peace dashi seta dauka kodan betaba ganinta bane don batasan tare sukeba, Fulani tace "tohm mukarasa mu karya ko in bakujin yunwa ni yar tsohuwar ku yunwa nakeji," jalila tsokanarta ta shigayi wai itace tsohuwar aibatai kala da tsofaffi ba,jalila da peace agefe daya suka zauna EHSAAS yana gefen Fulani yana satar kallon peace dake facing dinshi, English breakfast ne,shi kansa table din abin kallone peace tunda take bata taba zama a irin wannan hadadden table din cin abincin ba ahankali tashiga kallon dishes din masu shegen kyau da abinda ke cikinsu, wani three-tiered stand ne idonta yafara sauka akai da aka zuba fresh croissants, pain au chocolat, and almond danishes. Se wasu royal Crystal bowls da aka zuba berries, sliced kiwi, and pomegranate shimmer agefe kuma akwai silver trays dake dauke da smoked salmon, poached eggs,da avocado toast akan artisan bread.Acikin wani porcelain teapots masu kyau kuma Earl Grey and Moroccan mint tea ne,da freshly squeezed fruit juices, irinsu orange, grapefruit,da carrot-ginger aka zubasu a wani dogon cut-glass carafes.

Ahankali jakadiyya tashiga serving kowa abinda ya keso domin tasan choices din kowannensu banda peace wacca tunda tashigo take satar kallon yarinyar tana mamakin matsayin ita wacece da me girma Fulani zataci abinci atable daya da yarima,tana kammala serving jalila tashiga serving peace da thesame abinda tai serving jalila dashi hankalin EHSAAS nakan wayarsa da alama yana wane wani abun mai mahimmanci ne, harta gama Fulani ta sallameta don bata cika son masu mata hidima suna tsayawa akanta ba indai tana tareda prince saboda tasan bayaso,kwata kwatama sashen Fulani ne agidan zakaga bata ajje kuyangu barkatai saboda tanada tsari duk wanda ta ajje asashenta zakaga amintacce ne,abincinsu suka faraci ahankali cikeda nutsuwa peace se kallon smoked salmon din dake kan flat dinta take tasa fork tana dan tabawa amman ko kusa bata kai bakinta don kada ace tafiya iyayi ne amman ita batta iyacin irin kifinnan musamman da safe zuciyarta tashi zatai. Fulani tace "Babana me aketa dannawa ne baza aci abinci ba," dan dagowa yay yana fadin "almost done maama sorry" yakarasa yana ajje wayar gefensa saman table yadau spoon da fork dinshi,idonsa sauka yay akan peace daketa wasa da nata abincin, "oh my god waya zuba miki wannan picky Princess" yafada yana dan murmushi kafin yamike yama manta a inda suke ya jawo plate din gabanta yana tura masa nata sarkin "miskilanci,pipi da aka zuba miki bazaki iya bude baki kice bakya ciba koh,innace your baby kuma kice a'ah," dan kallonshi tai tana satar kallon Fulani da abincinta takeci tanuna bama tasan me yakeyi ba jalila kasa hadiye abinda tasa abakinta tai tana kallon wani irin kayataccen murmushi da EHSAAS kema peace yana tsokanarta kuma yabata abincinsa yashiga zuba mata mint tea yatura agabanta yace "oya inga plate din yanzunnan" jinjina kai peace tai kamar yar yarinyar da aka bawa umarni tashiga ci,yace "good girl," jalila tadauka ko zesa azuba mai wani amman abincin nata data gama jagwalgwalawa da fork yashiga ci yana mata murmushi tasan fa irin kyankyamin EHSAAS wannan cup bada wanda akema kowa amfani akemai ba harda da plates nashi na musamman ne,chokali kuwa koda wasa yafadi kasa anacin abinci yagama dashi kenan har abada muguwar tsafta ce dashi kamar me OCD, amman yakecin abincin da wannan yarinyar tagama jagwalgwalawa. "kambalai" tafurta aranta tanajin tayi loosing appetite gabaki daya,kasa cin abincin tai har Fulani ta lura da ita tace mata "why is she not eating?" girgiza mata kai tai alamun bakomai kawai tadau spoon don kar Fulani ta ankare da halin data shiga tashiga tuttura abincin kamar anmata dole. Fulani ce tafara gamawa tamike tana komawa parlour, EHSAAS ganin Fulani tatafi, yasa yafaki ido yaga dai tayi ciki sosai bazata gansu ba ya dakko plate dinsa yadawo gefen peace yana dage mata gira daya dan zaro ido tai tana nuna mai hanyar falon yaturo mata baki yana daukar cup din tea din datake sha yakai bakinsa yasha,tabe baki peace tai irin bataso dinnan yashiga mata gwalo,jalila hanci da baki tasaki tana kallon yajja yayan nata yazama gaban wannan yarinyar yadawo da shekarunsa dede nata tambayar kanta take wai daman yana murmushi haka arayuwarsa,kasa tashi tai dukda bakinciki dataji tana kwasa acikin kirjinta amman so take tasan meke tsakaninsu,atare suka gama duka yakalli jalila yana fadin " I'll head up,take care of her for me kinji," jinjina kai kawai tai don kwarjininsa baze bari tafadi wata maganar da ba shikenan ba agabansa, Yakalli peace yace "Islam seda anjima ko" irin yajja take fada in zatace se anjima murmushi tamai tana fadin "bye bye" da yar siririyar muryar ta,yace "bye-bye" shima da yatashi harda daga mata hannu yana mata bye bye kamar wanda bayason rabuwa da ita, parlour yanufa yaywa Fulani sallama yawuce. direct Aman na jiransa farmhouse dinsa suka wuce daya daga cikin wadanda mai martaba yake bashi kyauta,akwai wani gidan kasa da yake nan kamar storage ananne suka ajje Abraham dakin ko tafin hannuwanka bazaka iya gani aciki ba kuma tunda aka ajjeshi yace akunna speaker na gurin asaka karatun alQur'ani sbd kawai yaga ko zuciyar Abraham zata dan risina inya kwana yawuni yana sauraron karatun,ko ruwa bece abashi ba balle abinci ga shi gurin sunjima basuyi amfani dashiba kwari sun dabaibaye Abraham se cizonsa sukeyi ya toshe kunnuwansa yanajin karatun kamar dalma akesawa ana kona kirjinsa yana zafi yana sake cin alwashin su Abraham Zion da girmansa da darajar sa yarsa ta hada baki dawani akamai haka tohm wllh baze kyale peace ba ko meye zefaru seya tabbatar da seya rama abinda tamai itada EHSAAS waishi za'a kulle. tun yana saran ganin EHSAAS har yagaji ya dena besan ankwana bama,se can yaji ana tattakowa matattakalar gurin wasu irin gardawan dogarai ne suka karaso suka cemai yataso banza yaymusu zemusu gardama irin ta yayi zuciyarnan suka fizgoshi aka suka daukoshi yanata tsine musu yana gaya musu yajja Jehovah zeyi fata fata dasu sunyiwa makusancinsa haka yana tsine musu. A harabar gidan suka direshi gaban EHSAAS dake kan wata royal chair ya daura kafa daya kan daya da shegen dark glasses dinnan a fuskarsa Aman na tsaye agefensa Abraham muzurai kawai yakeyi yana kallon EHSAAS tsanarsa na karuwa aranshi,ganin Abraham din ajigace da alama beyi barciba idanuwansa sunyi luhu luhu gashi yayi bakikkirin yasa ehsas ya danji sanyi aransa atleast shima yayi bakinciki kamar yajja yasa peace dinsa wllh dabadan darajar haihuwa ba, da idan yasa dogarannan suka fara dukanshi harse yafara suma yana farfadowa amman yaci darajar kasancewa mahaifinta. "kai harni zaka wulakanta irin haka kasam ni waye kuwa?" yafada yana nuna EHSAAS da dan yasa wani dogari guda dayane yataso yana rike dan yatsan yace "karya kake talaka ba'a nuna yarima da yatsa bamu karya ba" yamurde yatsan yana shirin karyawa Abraham yafasa wata karar azaba yana kokarin kwace hannayensa. daga hannu EHSAAS yay yaywa dogarin alamar ya kyaleshi, kyaleshi yay yana faman dungule hannayensa irin Abraham yaci sa'ar nan Abraham yatsansa yashiga shafawa don ya tabbatar akwai yatsan ko kuma babu, EHSAAS yacire glass din yana kallon Abraham cikin bada umarni yake fadin "zamu kaika gaban mai martaba king NASHWAN yanzun inkaga dama kaje kanuna mai rashin sa'ar daka nuna masa yanzun wllh ba yatsanka zasu karyaba wiyanka zasu balla kuma sunballa banza sbd kaiba kowa bane face mutum mara daraja kaskantacce mai dukan mata,harkai kana tinanin kai namiji ne inkai namiji ne ai maxa zakaje katara kuyi gaba da gaba bawai kasaka helpless girl kamar peace agaba kana nuna jarumtar ka akanta ba," yakalli dogaran yana fadin "abeg get this piece of trash out of my sight amai nakeji kuje kumai wanka kusaka mishi sababbin kayan da akazo dasu bekamata sirika yaje gaban mai martaba ahakaba," Abraham tsinewa EHSAAS yashiga yi yana fadin "Jehova yay wadaran sa kuma indai shine sirikin nasa kada Jehovah yanuna masa wannan rnr sbd baze taba bari yarsa ta auri non believer mara tarbiyya kamarshi ba," EHSAAS murmushi yay yana tabe baki kafin yace "breaking news two non believers sunxama yayanka kuwa sbd peace is now ours she's no longer peace, she's Islam sunan yamaka dadi ko daddy" EHSAAS yafada yana dariyar iskanci Aman ya taya shi Abraham kamar mutum mutumi yakasa motsi agurin saboda maganar ta dakeshi haka dogarai sukai gaba dashi kamar yajja EHSAAS ya bukata suka wankeshi tass suka fito dashi baya uhm balle uhm uhm kawai tinanin yajja ze kashe peace yake kullawa aransa da kuma yajja zeyi ko duk duniya zasu hadu kanshi ko EHSAAS ne autan maza baze bari ya aura yarsa ba kuma yasan cewa king NASHWAN ma baze taba bari danshi ya auri yarsa ba, sbd haka idan har EHSAAS yayi nasarar musuluntar da yarsa shikuma yayi ready seya tubure ya yadama duniya EHSAAS bata masa yarinya yakeyi yana bibiyarta ako ina,se yayi dana sanin shiga gonarsa,inyana takama da mulki shikuma zenuna masa karfin dukiyar da yake da ita dan haka bawani musu yabisu cikin mota har zuwa palace din.

Abraham yasha haduwa da king NASHWAN agurin tarurruka amman betaba zuwa palace ba,tohm mema zekawo shi fadar makiyinsa yafada aransa yana tabe baki ya kushe palace din azuciyarsa cikeda hassada,akofar babbar royal court motarsu tai parking aka fito aka budema prince kofa,anata zuba mai kirari seda ya dakatar tukunna. Abraham daura kafa daya kan daya yay, yanajin dadinma wankeshin da akai domin da an daukoshi adakalkale mutuncinaa ze iya zubewa a idon duniya don haka yafara jira shima abude mai kofar,ganin anbude m su EHSAAS wani dogari ne ya leko yana fadin "malam zaka fitone kose munzo mundauko ka" sanin dogaran EHSAAS din basuda kirki yasa yabude murfin motar yana hura hanci yana kallon kowa daddai yabi bayansu EHSAAS din zuwa babbar royal court wacca take dauke da manya manyan dattawan NURISTAN baki daya, murmushi Abraham yay yana raya aransa in EHSAAS yasan wata ai besan wata ba,seda kowa yagama halartar zaman sannan aka sanar da shigowar mai Martaba king NASHWAN bin EHSAAS,gaba dayansu mikewa sukai daga zaunen da suke aka shiga mai fadanci ana rufesa harya karasa kan karagarsa yazauna.

dafarko matsalolin gari da kararraki aka fara saurara, Abraham na gefe yana facing din EHSAAS da Aman dasuke watching dinsa closely domin ganinsa very calm yasa suka fara zargin akwai abinda yake shiryawa,seda aka kammala shari'ar sannan EHSAAS ya gabatar da Abraham Zion agurin mai Martaba amatsayin mahaifin Islam mai martaba tun shigowarsa yagansa ya kalleshi yana cewa yafito fili atsakiyar court din yafito yazauna, mai martaba yabada umarnin agabatar da peace agaban court, Aman ne yafita yakira wayar jalila yace "tazo da Islam babbar court" tayi mamakin jin hakan amman dai tunda taji ance tazo din tasan abune mai mahimmanci amota ta dakko peace din batace mata komai ba sbd jin da tai tana kishinta har cikin ranta bayan abinda taga EHSAAS nayi da safe tasan inta bude bakinta zata iya gayawa peace mgnr da zatazo tai dana sani daga baya hakan yasa bata kulata ba throughout morning din harseda Aman yakirata tace mata "ana kiranta suje kawai," Fulani suka gayawa taimusu izni tatafi kaita,daidai nan motocin dasuka tafi dakko gimbiyah mimah suna shigowa cikin palace din akofar royal court din jalila ta ajjeta tace tashiga,peace kallon jalila tai tana kallon uban security din dake gurin tace "kishiga mana kintsaya kina kallona aibani ake nemaba" tafada akufule don so take tabi bayan mimah kawai tasan a side dinta ake takai mata labarin Islam din din. peace da batason wulakanci bude motar kawai tai tafito tana rarraba ido tana kara jan mayafin abayarta yazo har gaban goshinta don kar gashinta yafito,dogaran dasuka cika mata gaba take kallo gashi ba fuskar tace subude mata ma tashiga daidai nan taji ance Islam daga baya cikin murya mai sanyi tajuyo, idonta ya sauka akan wannan data gani a court jiya me kama da EHSAAS, "me kike yi anan?" ya tambaya cikeda kulawa,kasa dakai tai batace komai ba dan she's not comfortable with irin kallon da yake binta dashi,ko shiga ciki zakiyi yay suggesting yana sake kare mata kallo don jiya beganta sosai ba hijab din data saka ya boye ainahin siffan jikinta ta ya mace tajinjina kai kamar wani maye yashiga hadiyar yawu se kuma yace "okay muje ciki," yana karasawa dogaran suka bashi hanya yace mata "shiga muje ko gaba tai batare da tasan yana bayantaba tashiga tafiya,idanuwansa akan hips dinta yatsaya kem tana tafiya yana shaking ba ita takeyi ba haka jikinta yake is not intentional with every move datai ass dinta seyayi shaking jay jiyay jikansa na daukar rawa lokaci guda saboda kwankwararran dan iskane mayen mata shiyasa yakasa aure sbd yana ganin aure ze hanashi rayuwar da yakeyi,seda suka kai ainahin kofar court din peace tatsaya tajuyo suka hada ido tsabar jaraba idanuwan sa sun kada sunyi jajir tace "munzo" dogaran gurin yaywa umarnin subude kofar suka bude wannan karan shiyay gaba yana saita nutsuwarsa sbd yasan wani ze iya zargin wani abu in aka ganshi abayanta kuma ba lallaine ya iya kama kanshi yaki kallon jikinta ba,bin bayansa tai tana tafiya anitse galadima yaje ya kai gaisuwa yana me isarda aiken da aka mai don shine yasa yay latti. peace ma gaisuwa takai gurin mai martaba ya amsa yana tambayarta "ta kwana lpy badai wata matsala ko?" ta jinjina kai cikin kulawa yace "kafar tayi sauki kenan naga bakya dingisata" jinjina kai tai aranta ta raya ashe jiya ya lurada kafarta shikansa EHSAAS yayi mamakin noticing kafar da mai martaba yayi yace ta zauna agefensa kamar yajja ya sakata jiya,turaki ne ya tashi ya jeroma Abraham tuhumarsa da akeyi na dukan yarsa da kuma hanata yancin shiga addinin da take dayayi. shiru yay yana kallon peace data kasa hada ido dashi saboda sau daya data shigo ta kalleshi irin kallon daya buga mata yasa taji jikinta na rawa sbd tasan inya hadu da ita Allah ne kawai ze rabasu,se taji tafara tsoron komawa gidan, Abraham cikeda ladabin mage da siyasa da duniyanci ya gaisheda mai martaba yana boye kiyarda dayake kafin yace "ranka ya dade tabbas nakarbi laifin dukan peace da akace nayi kuma tabbas nakarbi na dakatar da ita daga shiga addninin ku sbd nasan bata taba ra'ayinsa ba ziga ta kawai akeyi ta bijiremin" yafada yana kallon EHSAAS daya cika da mamaki jin Abraham Zion ya amsa laifinsa kai tsaye, turaki yace "wannan ne dalilin da yasa zaka yiwa yar yarinya yar shekara goma sha takwas irin wannan dukan daya kaita harga kwanciya asibiti," cikeda makirci kamar wata mace yashiga matse kwalla yace "yatace babu wanda yakaini kaunarta kuma har abada ba wanda zai kaini sonta acikinku idan akace yarku nabin namiji yana neman lalata mata rayuwa baza kuyi kokarin daukar mataki akaiba, wasu ma natabbatar zasuyi fin haka," EHSAAS cikin mamaki yashiga kallon Abraham don yasan yanzun inda zancensa ya dosa yanason yabata sunansa dana yarinyar ne, waziri cikeda mamaki da zumudi yace "nifa nace babu dai uban da ze haifi da ace yatsaneshi haka kawai yana bugarsa dole akwai dalili,' Abraham yace "akwai kuwa" cikin daga murya ya nuna peace yace "kunga wannan yarinyar da kuke gani batajin magana ta,bata considering future dinta babu abinda banayi don farincikin ta ciki kuwa harda kaita birnin Oxford tai karatu duk don tasamu kyakkyawan ilimi mai amfani yana cewa Oxford aka shiga kallon kallo domin kuwa kowa yasan yarima acan shima yake karatu," Aman yakalli EHSAAS yana fadin "should I shut him up?" EHSAAS wani irin murmushi ne ya kawo kan fuskar sa sabanin dazu dayay looking confuse yace "no don't aikin da kaf cikinmu ba wanda ze iya guy dinnan Abraham zemana besan waye mai martaba bane ba, barshi yacigaba badai sunana ze bataba indai zansamu peace in the process ya dade be bataba,"

Galadima zuface tashiga karyo mishi yana kallon Abraham yace "kai kasan me zaka ringa fada agaban mai martaba," juyowa yay a fusace yana fadin "harkai waye anan da zaka gayan mezan fada akan yata da wanda bazan fada ba gatanan ku tambayeta soyayya takeyi tareda saurayin,kuma wuni sukeyi tare har dakinsa binshi takeyi,ranakun da bana gari banajin ma tana kwana agida sedai gurinsa zan iya kira muku principal din makarantar su tasheda muku sakon gargadi dana bayar abawa yaron saboda sanin daga inda yafito banason ai tashin hankali dani akan hakan, shiyake zigata akan tashiga sabon addini shiyake zigata ta ringa min rashin kunya tana mayarmin da magana sannan shine bayan nagaji da bibiyar rayuwarta da yakeyi na dakkota nadawo da ita nan gabana nasata ajami'ar ahalina, don nai keeping close watch akanta ya siya mata system da WiFi sbd ban isaba yabiya mata kudin wata makarantar tana karanta wani dan iskan course a online university,kuma inbaku yarda dani ba kubarni naje gida akwai wayarta dana fasa agyara duk akwai record na tabbatuwar alakar ta dashi da irin texts da kiranta da yakeyi itama tana kiransa suna kulla haramtacciyar alaka," mai Martaba kallon peace yay da jikinta yafara rawa tana kallon EHSAAS da kanshi akasa hankalinsa kwance bazaka gane ga irin halin dayake ciki ba,anan take ya soma ganewa amman don ya tabbatar da abinda yake zargi se yacema Abraham 'kai meyasa baka dau mataki akan saurayin ba kanada yanci da power din yin hakan," fashewa da kukan karya yay yace "yafi karfina ranka yadade yafito daga babban gida kuma bana shiri da gidan idan nazo nafada za'a iya karyatani ko kuma intada rigima mara karewa shiyasa kawai da abin yay yawa na hanata fita,amman takasa hanuwa na hanata mu'amala dashi amman takiyi kuma nasan baze taba aurenta ba,nasan bazaku taba bari ya auri yataba don haka yanzun kubani peace intafi da ita nayarda na amince tai dukkanin addinin da takeso zansamo mata mijin kirki in lallaba ya aureta acikinmu," da sauri waziri yace "baza'ai hakaba Abraham aitunda kakawo kukan ka fada tabbas bazaka tafiba se ansharema hawayenka sarkinmu adaline,don haka kafada mana sunan yaron ko a ina yake semun dakkoshi mun gurfanar dashi agaban kotu mai girma mai martaba ya hukuntashi kan abinda yaywa yarka," girgiza kai Abraham ya shigayi irin baze fada ba dinnan galadima cikin son tabbatar da abinda yake zargi yace "Abraham karka ji tsoro kafada kawai ko waye shi se fada ta hukunta" Yakarasa cikin jin zafin kishin koma waye yarigashi nasarar taba jikin peace din, Abraham straight ya daga hannuwansa zuwa direction din EHSAAS yace " is prince EHSAAS bin NASHWAN shine saurayin daya batamin yarinya kuma har yanxun yake bibiyarmin yarinya karama yaki rabuwa da ita kuma ba aurenta zeyiba don haka abinda nake bukata dashi yafita daga harkar yarinyata zansamo mata mijin daya dace da ita in aura mata," salati fada tadauka wani bafade cikin katuwar murya yashiga fadin "karya kakeyi aiko ka akai kasan irin hukuncin da kuto ta tanada ga mutane irinku masu batanci ga yariman wannan daula,tabbas kashinka yabushe arnan banza arnan wofi," Abraham mayar masa yashiga yi dogarai sukayo kansa zasu mai daukar amarya mai Martaba ya dakatar dasu ta hanyar daga hannun sa daya sama shiru court tai kamar babu halitt ko daya acikinta. Mai Martaba cikin dattaku da iya magana yace "munji kukanka Abraham kuma zamuyi bincike akan abinda kafada indai ta tabbata gaskiyane zamu dau tsatstsauran mataki akan yarima domin be wuce kowace irin hukunci ba agurinmu domin yan gaba sugani susan cewa NURISTAN garine mai adalci da yarimanta bazeyi laifi yashaba sannan idan muka gane akwai karya cikin maganarka,zaka karbi hukunci mai tsanani hukunci yiwa yarima kage da diyar da mai martaba yadauka me daraja amatsayin tasa sharri, don haka zabi ya rage naka kana kan bakanka har yanzun ko kuma da ja acikin zancen ka," Abraham sake tabbatar da maganar sa yay yana jaddada EHSAAS na neman peace. Aman dan dafa hannayen EHSAAS yay yasan dole zeshiga damuwa kodan sbd disappointing din mai martaba dayay, "Islam" mai Martaba yafada cikin kakkausar muryar data saka peace dan rudewa,tana amsawa yace "zamuyi miki tambayoyi munason ki amsasu tsakaninki da Allah, ubangiji buwayi gagara musali idan kikai mana karya muka gane hakan zamu hukun taki hukunci mai tsanani," jinjina kai amsawa tai da tohm zata ansa iya gaskiyar in sha Allah, "yaushe kikasan yarima?" Ya jefa mata tambayar dayasa tadago tana kallon EHSAAS be kalleta ba kanshi nakasa,tasan mai martaba baze sake tambayar taba,hakanne yasa tace mishi "last two years," kallon kallo aka shiga yi afada waziri yanajin ransa fess kamar ana wankewa da soso da sabulu saboda da alama karshen EHSAAS ne yazo,mai Martaba yace "meye alakar dake tsakaninku?" muryarta na rawa tace "yana koyamin karatu ne? kuma shi.....shi abokina ne," guntum salati yan fada sukeyi kasa kasa Abraham na murmushi don peace na daure kanta da kantane aransa yace "doluwar yarinya ko karya ma bata iyaba," mai Martaba cikin nutsuwa yace "Islam ko kinsan cewa a addinin musulunci babu wata alaka ta abota tsakanin mace da namiji shida ba muharraminta ba kuma ba aurenta zeyi ba," girgiza kai tashiga yi alamar bata sani ba,yace "meyasa kika shiga musulunci? saboda shi yace kishiga?" dasauri tadago hawaye na zubowa a idonta tace "wllh bashine yace inshiga musulunci ba daman can addinin yana burgeni ina kallon wa'azin malamanku a YouTube during Ramadan inajin alot of muftis kafin EHSAAS yashigo rayuwata I was not a practicing Christian sbd addinin danake ciki din hankalina bai kwanta dashiba Islam is the goal always danake dashi stains, amman banida courage din fighting da babana wanda yake shugabantar mabiya addininmu mahaifina yatsani musulunci da musulmai sannan ko abin musulmai yagani agurina seyay ta dukana yana jamin kunne ina tsoronsa sosai" tafada tana kallon Abraham kasa kasa,cikin rawar murya tace "inada alot of questions akan existence din Jesus amatsayin son of god, duk sanda na tambayi babana baya bani gamsasshshiyar amsa, but when I ask EHSAAS yabani cikakken bayanin sannan yabani misali da existence din prophet Adam da Eve,EHSAAS kawai daurani akan tafarkin gaskiya yay,yana nunamin daidai daba daidai ba amatsayinsa na malamina kuma abokina, EHSAAS has never ever tell me inshiga musulunci dan radin kaina naji cewa nayi na'am da Islam shine tafarkin gaskiya,kuma dalilin hakane yasa nakarba littafan addini gurin EHSAAS ina karantawa,dalilin haka yasaka na shiga wani online quiz na tambayoyin addini naci shine.... shine..... suka turomin kyautar hijab da sallaya d azkhar shine babana yagani yafara dukana yace seya kasheni kafin inshiga musulunci inxubar Mai da mutunci" Abraham cikin daka tsawa yace "peace," dogari ma yatashi yana dakamai tsawa yana gargadinsa peace kinyarda tahada ido da Abraham tai. tana goge hawayenta daya bayan daya da yake binta, sosai mai martaba yaji yayarda da zancen yarinyar domin dukda shida EHSAAS basu cika zama gu daya ba yayarda da danshi yayarda da kalar tarbiyyar dayay mai kilama don ya kwadaitu data shiga addinin yasa ya kusance ta har ya tsamota daga halakar datake ciki amman dai baka shedi dan yauba. mai Martaba yace "Islam bayan abota babu wata alaka dake tsakaninki da EHSAAS tsawon shekara biyunnan," jinjina kai tashiga yi yace "kin tabbatar" dan kallon EHSAAS tai kafin tagirgiza kai, zuciyar jay tsalle kawai takeyi maganganunta kamar tana tamkar Naman kirjinsa sbd kishin ta dayaji yanayi, mai Martaba yace "inajinki!" tace "I..... I.... like him," cikeda kuruciyar da ta sanya mai Martaba sakin wani shu'umin murmushi domin mai Martaba wani irin baudaddan mutum ne da bazaka taba gane gabansa ba balle bayansa, Mai Martaba yace "Islam! why did you like him? Tsakani da Allah peace tashiga bashi answer da fadin "yanada kirki,yana kula dani sosai sannan duk abinda nace inaso yanamin wanda banaso yabari,sannan yanada ilimi sosai he guided me zuwa right part sannan halayenshi nagari sunada yawa bama zan iya mentioning dinsu dukaba yanada tausayi yanada jinkai sannan yana jidani sosai,mai martaba,kuma ni bantaba kwana agurinsa ba,abinda daddy yake fada akanmu ba gaskiya bane ba" yace "kingaya masa hakan?" jinjina kai peace tai tana fadin "eh father" yace "meyace miki?" tace "he said, he feel thesame towards me," salati aka farayi afada daya sanya mai martaba kallon peace yace "tatashi tatafi" mikewa tai anitse tana wa mai martaba godiya tafice agurin ta tsaya aharabar gurin tana wasa da ya tsunta, EHSAAS kallon Aman yay sin..sin ...sin yatashi yabi bayan peace domin yamaida ta. Mai Martaba yay gyaran murya yana kallon EHSAAS inda peace ta tashi yace "yazo ya zauna" ahankali ya karasa kanshi akasa,mai martaba yace "yarima gaskiyane duk abinda Islam tafada," dan jima yay kafin yace "tabbas hakane Allah ya temakeka," mai Martaba yay jim kafin yace "meye niyyar ka dangane da Islam tunda kafita wayo kafita ilimi da hangen nesa kasan babu kyau abota tsakanin namiji da mace meyasa kayi?" EHSAAS anitse yace "sbd ni ba iya abotar ce niya taba koda bata musulunta ba Allah ya halattamin auren ahlul kitabu na yaba da hankalin yarinyar da tarbiyyarta aurenta nakeson nayi in lokaci yayi,kuma idan nace mata inasonta bazata yarda dani ba zataji tsoro taki budemin zuciyarta"

gaba daya fadar seda tashiga shock domin sunsan mai Martaba yadade da fitarma da EHSAAS matan aure, wadanda ze zaba cikinsu suna nan kuma suna jira ya gama karatu ayi yaza'ai ya auri arniya ko ma suce tubabbiya tazama sirika agidan sarautar NURISTAN Mai girma, "aurenta kakeso kayi?" mai martaba yasake tambaya yace "eh Allah yatemake ka," dan jinjina kai yay kafin yakalli Abraham cikeda fikira yace "tohm kaji ai tazo gidan sauki koh daman kace yana binta yana lalatawa tunda yarigada yagama lalata tan bame aurenta seshi ayanzun don haka muna me nema masa aurenta agurinka kuma zamu hukuntashi da daidai abinda ya aikata in sha allahu," "nooooo" Abraham yafurta yana mikewa tsaye yana nuna EHSAAS yace "bazan bashi auren yataba dan meyasa zanbama non believer auren yata wannan dan iskan yaron mara mutunci da in bashi auren peace gwara na kasheta wllh nasan mutuwa tai,yama ci riba akaina Kenan" dogarai zasuyi kansa mai martaba ya hanasu Abraham yashiga fadin, "king NASHWAN ka tabbatar min da cewar kaiba adalin sarki baneba wato saboda dankane shine zakaki hukuntashi kan abinda yaywa yarinya ta ko,tohm bari kaji bazan bayarda aurenta gashi ba,kuma addinin nakuma bazan barta taiba," murmushi irinna manya mai martaba yay kafin yace "inbaka bashi aurenta ba waye zaka bawa yar daka gama kira da lalatacciya anan agaban kotu," Abraham cikin fushi yake fadin "yata ba lallatacciya bace she's as pure as virgin merry nayarda da kalar tarbiyyar da nai mata dankane lalatacce non believer daya zigamin yarinyar tabar tafarkin gaskiya tafarkin addinin Jehovah dan haka ko maza sunkare aduniya bazan bari peace ta auri yaronka ba," King NASHWAN kallon dogarai yay yamusu alama nanda nan sukai surrounding Abraham,yace "kayi magana! ka karyata kanka da kanka ka batawa yarima da Islam suna gaban kotu don haka kasani zaka karbi hukunci mai tsanani ahannun Shari'a kuma amatsayina na shugaba zan tsayama peace gurin ganin na hukunta akan abinda kaimata sannan inkana tinanin mu musulmai zamu kyamaceta sbd kasancewarta yar mutum irin ka kayi kuskure,ranar data furta kalmar shahada tawanke duk wani datti dake cikin rayuwarta,kuma bazamu taba judging dinta donta kasance yarka ba,don haka kutafi dashi kurkuku mafi duhu ku ajjeshi har zuwa lokacin da za'a daura auren yarima EHSAAS da Islam wata mai kamawa in sha Allahu" yafada yana mikewa duk mikewa sukai Abraham yashiga ihu bama ajin abinda yake cewa aka fice dashi mai Martaba yafita ta kofar sa ta musamman, EHSAAS bayanshi yabi saboda yasan yayi hakanne don kare mutuncinsa,Amman har kasan ransa yagano wani irin bacin rai dankare afuskar mai martaba wanda yasan akwai consequences dole mai martaba yay punishing dinsa daidai da abinda ya aikata na soyayya aboye batareda saninsa ba yana fatan dai hukuncin da mai martaba zemai ya iya dauka,yamasa ze iya dauka idandai har ze barshi da peace acikin rayuwarsa.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote [11/05, 20:32] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.