EHSAAS

Chapter 20

by @fatoumspassion

Na dauka duk wani hukunci da mai Martaba zai yanke akaina zan iya karbarsa hannu bibbiyu indai har peace tana gefena,na dauka cewa mallakar peace shine abinda nafi kauna inyi aduniya under any circumstances amman bansani ba ashe Mai martaba yabani peace ne tareda daureni da jijiyoyin wiyana.

I was feeling uneasy throughout the whole day sbd ina shakkar hukuncin daze yanke akaina dukda yajja ake ta zuwa ana tayani murnar saka ranar. saboda nasan waye mahaifina zuciyata tana ta bani akwai abinda yake shiryawa, bantashi sanin abinda mai martaba yake shiryawa ba se washegarin ranar inda yay going through da taron da akeyi na gargajiya na zabar ma yariman kasa mata, it was very grand domin anyi ittifakin ba'a taba taron zabar mata da aka tsara ga kowana yarima nabaya ba irin nawa. gaba daya kaina yakulle lokacin da akai presenting matan guda uku agabana mai martaba yabani umarni cewar sun bani zabina sunmin yajja nakeso nima zanmusu yajja suke so don haka in zabi mata cikin guda ukunnan tafarko diyar sarkin persia ce,wacca ake mata lakabi da Seema,daya daga cikin mata mafi daraja a duniyar sarauta ta lokacin, tabiyu Princess jalila ce diyar yayan mahaifiyata kuma sarkin borno kanem empire na yanzun wanda yake marikina yake kamar uba agurina dukda distance din damuka samu tunbayan da yakarbi mulkin borno da kakana yay murabus yabashi, sbd tsufa da lalurar data sameshi ta zuciya,ta ukun itama cousin sister nace ta gurin uba maisoon bint Erfan diyar kanin mahaifina wazirin NURISTAN na yanzun,cikinsu kaf matane dasuka fito daga tsatso mai daraja da yake dauke da tarihai masu ban mamaki, aka bani dama inzabi daya acikinsu kuma kowacce tana da kyau kamar ita tai kanta, amman bansan meyasa ba zuciyata bata taba kallon kowace nace amatsayin mace ba inba Islam ba nasan cewar duk wacca nazaba acikinsu tabbas na cutar da rayuwarta sbd bazan taba iya kwatanta adalci atsakanin Islam da wata macenba, zuciyata ita take dauki ita takeso amman ya zama dole akaina inbi umarnin mahaifina ko dan gobena tai kyau amman tsayawa nai nayi duba na tsanaki gurin zaben,cikin fikira na yanke shawarar na zabi maisoon bint Erfan diyar kanin mahaifina wazirin NURISTAN,abin ya matukar bawa kowa mamaki saboda kusan daddaikune acikin masarautar NURISTAN basu san kalar rawar kan maisoon ba,kuma kowa yasan cewa candidates guda biyu dana bari sunfita komai da komai sbd su princesses ne amman na tsallake su nadau maisoon shikansa mai martaba yayi mamakin daukar maisoon danai amman dai baice komai ba waziri murna yashiga yi yana tinanin sa'ar da akabashi ce tasa na zabi maisoon.

mai Martaba thesame date dayasa da aurena da peace shine yasaka da maisoon ma'ana rana daya za'a daura auren,abinda ze baku mamaki hukuncin ba iya nan ya tsaya ba mai Martaba saka Aman yay ya ajjemin aikina wai ze koma karkashinsa badon Aman din naso ba, ananne mutane dayawa suka gane cewa prince publishing mallakina ce inda dayawa suka sha mamaki masu bakincikin hakan nayi,Masu taya murna nayi, mai martaba yadaura min kulada southern part of NURISTAN baki daya wani irin nauyine da aka daura min daya kasance bama zanringa samun lokacin kaina ba akoda yaushe sbd mai Martaba yadauramin kamar rabin nauyin garin NURISTAN akaina ne responsibility ne ne daban taba rike irinsa ba tunda nazo duniya,kuma yasa nayi alkawarin aiki tukuru gurin ganin duk arnan dake can south din da Abraham Zion yabatar zandawo dasu kan tafarkin gaskiya,sannan za'a samar musu da ayyukan yi, za'a gida musu masana'antu da dama aikine mai girman gaske, shirin da'awa muka shigayi sbd idan natafi south bazan sake dawowa ba,kila sai lokacin aureba.

Alokacinne yar uwata jalila ta sameni tana kuka take tambaya ta me taimin meyasa na tsaneta meyasa ban zabeta ba dame maisoon da Islam suka fita. inason yarinyar amman baso na aure ba I've always look up to her as my younger sister ina kallonta amatsayin kanwar da banida ita,kuma ina tausayinta sosai kan soyayyar datake min,nuna mata nai itama tamusamman ce kuma basu fita da komai ba kuma na jaddada mata ban zabi maisoon domin tafita ba a'ah nazabi maisoon ne sbd ita kadaice zan iya samun aibu agurinta dazesa mai Martaba ya dakatar da aurena da ita dakanshi sbd bazan iya taba hada soyayyar islam da kowace mace ba bazan taba iya adalci ba,inkuma na zabeta tabbas zan cutar da ita kuma haka ze iya lalata zumuncin dake tsakaninmu nai mata fatan alheri sannan nai mata adduar Allah yabata wanda yafini naji dadin fahimtar datai domin seda nasata murmushi kanta fita daga sashena. bansan wanda yaje ya kaiwa Islam labarin abinda ke faruwa ba,amman dai tadena daga wayata tadena amsa text dina kullum innaje bangaren Fulani bana ganinta,dana gaji navtambaya se akacemin ai uwar soro tadauketa suna tare ashashenta da gimbiya mimah anfara mata gyaran aure,babu abinda nake fama dashi irin kewarta we are so close yet so far, relationship dina da ita is not like normal relationship da zaka dade bakaji daga partner dinka ba kuma bakaji komaiba,we are best friends, bama iya wuni bamuji daga junaba amman yajja peace tai ghosting dina abin seya baku mamaki.

Bantaba sanin peace garwashi bace se awannan lokacin, she's not fire dazata konaka lokaci guda a'ah garwashi ce dazata dafaka ahankali cikin nutsuwa. naje na sameta abangaren uwar soro ashe batada lpy jikinta ya birkice tun rnr da jalila ta yaba mata mgnr aurena da maisoon afuskarta,mimah ce tasanar dani meke faruwa sbd itace ce taketa dawainiya da ita tana fada mata ta kwantar da hankalinta babu abinda ze samu soyayyar da EHSAAS yake mata don ze auresu susu biyu,shidin yarima ne bata ganin matan sarki uku tadena saka ranta cewa da ita kadai ze zauna.

uwar soro kuwa goyawa Islam baya take tana dada zigata kan cewar kada ta yarda ta auri yarima indai har ze hadata da maisoon sbd batasan meyasa ba har ranta taji batason auren yarima da yarinyar bawai don batason Islam ba, amman tausayinta takeyi tasan meye sharrin zaman kishi tareda family din nadra,maisoon jikar nadra ce don haka zasu iya salwantar da rayuwar yarinyar abanza awofi,tasan sunada bin malamai ga tuggu iri iri ita kanta datake tsaye da kafafuwanta iyayenta malamai ne sosai suka tsaya mata awancan lokacin dakyar tasha ahannunsu,tayaya Islam zata iya zaman kishi dasu.

ranar da nazo kulle kofa tai taki barina naganta, kuma uwar soro tahanani spare key din dakin cewarta yarinya tace batason ganina aiba'a dole,karo nafarko danaji inajin haushin kakarta tawa maimakon tabi bayana ta tayani lallaba yarinyar nan amman setake nunamin ma kamar nine nayanke ma kaina hukuncin auren maisoon bayan dantane yay komai.

washegari da sassafe nasake zuwa nai sa'a mimah na dakin abude yake,na zauna agefanta idanuwanta sunyi jajir takaici nake wai sanadina ne take wannan kukan,hakuri nashiga bata ina nuna mata bason raina baneba umarnin mai Martaba bane, nashiga bata hakuri ina karanta mata cewar auren mata biyu ba hakan yana nufin nadena sonta bane har aya nashiga karanta mata inda Allah ya halarta hakan ina fassara mata,nasan weakness din Islam indai nakaranta mata ayah nace Allah yace komenene zata bari kuma zata hakura,amman bansan kishin mata masifa bane se alokacin, cemin tai in tashi infita inbata guri,kuma taji Allah ya halatta amman kuma be tilastawa mata su zauna da kishiya inba saso ba,suna da yancin hakan, straight takalli cikin idona tacemin bazata aureni ba,tacemin ita bazata taba iya hada mijinta da wataba inzaba ko ita ko maisoon polygamy is not for her,wllh yace ze auri wata bayan ita mutuwa zatai. nikuma nace idan ta rabu dani nima mutuwar zanyi,kuka ta cigaba dayimin kamar ranta zefita tana tisa min cewa ni nata ne ita kadai kuma bazata rabani dakowa ba.....tunda ganan nagane cewa ni mijin mace dayane sbd Islam batason kishiya kuma duk abinda ze bata mata rai gudunsa nakeyi har abada bazan zamo sanadin batuwar rannata ba. Ni natane ita kadai haka nai mata alkawari cewar har abada bazan zauna ea wata bayan itaba.

Islam tana kawo nan gurin kawai ta fashe da kuka tana tina irin yajja ta azabtar dashi da silent treatment ashe yanata fafitikane gurin ganin yasamo abinda ze hana aurensa da maisoon bata saniba,irin yajja tai mishi take tinawa ashe shiba me tsawon rai bane ba, she shouldn't have maltreated him that way inama zedawo yanzun tayarda ko mata dari zai zauna dasu baruwanta indai har zata ringa ganinsa akusa da ita. Hawayenta ne yasoma jika littafin dasauri tashiga kakkabewa tana rungume littafin littafin akirjinta kamar wani ze rabata dashi.

kiran sallar magriba dataji anayi ne ya sanya ta mike ahankali,kuyangar ta tashiga nade shimfidar da akai mata, sashensu takoma taje tadaura alwalar magrib ta tayar da sallah bayan ta idar tayi azkhar tadakko al Qur'ani tashiga karantawa cikin zazzakar kira'ar data koya gurin mijinta seda aka kira isha'ee ta yi sannan bayan tagama jera mishi addu'o'in samun rahmar ubangiji.

for the first time takeji kamar da gaske yamutu din baze sake dawowa ba seda tasha kukanta sannan tamike takoma daki wayarta tadakko da tsawan watannin batta ma ko kallon inda take bama charge, charger tashiga lalubowa bata ga tataba se atashi tasaka tatsaya tana kallon charger din. tana tuno yajja take tsokanar sa tasaka charge a charger dinsa duk randa tata tak spoiling yayita mita kenan yana cewa inta bata mai seta biyashi,"He is the best husband ever" tafada aranta tana goge kwallar data kawo mata haka kawai takeji gabanta yana faduwa,takalli agogo kusan tara saura ba'a dawo mata da EHSAAS junior ba me hakan yake nufi? tasan cewar duk inda magrib tai uwar soro ta goyeshi takawo mata shi har nan dakanta amman yau shiru takeji tayi karane yasa bataje cigiya ba, amman kuma dare nahi tana bukatar jin dumin danta ajikinta.

mikewa tai zumbur tana jin idan wani abune yasamu junior dinfa? dasauri tashige makeken closets dinsu taciro wani dogon hijab tana daurawa akan kayanta,ta zaro daya daga cikin makullayen motocin EHSAAS tafito. kuyangarta nabin bayanta,don sufi sauri mota suka shiga tai driving dinsu har unguwar ta soro, parking tai tafito rike da car key din,tawuce ciki.

Acan cikin turaka tasamu uwar soro ana mata tausa harta kwanta,cikin mamakin Islam tashiga kallan dakin ga gadonsa nan nadakin kwalam babu komai,shigowarta tasa uwar soro dan bude ido tana kallonta,tace "yadai Islam baku kwanta bane har yanzun?" dan girgiza kai tai tana karasawa gefenta tace "Allah ya temaki grandma hutawa akeyi haka" jinjina kai uwar soro tai tana fadin "kinga kafatace take damuna zirga zirga shiyasa nace sudan daddanna min," jinjina kai Islam tai tana mata sannu cikeda kulawa tace "kidena zuwa daukar maigidan naki dagayau da kaina zanringa kawo miki shi ana mai wanka har inda kike sannan dakaina zanringa zuwa ina daukarshi" murmushi uwar soro tai tana fadin "keda kike jego Islam kinmanta me likita yace kihuta" Islam tace "nafa warke shikansa tabon ya hade yashafe gaba daya grandma karki damu," tace "tohm Islam Allah yakara sauki,Allah yayi albarka, ina kika baromin angon nawa da darennan ko yayi barci ne dazun yanata canyara min rigima bashiri nace akaima uwarsa shi yayi wayo bayamin kara yasan babarsa," wani irin ras gaban Islam yabayar tashiga kallon uwar soro kamar wata sokuwa tabude baki se kuma takasa magana uwar soro ganin halinda tashiga yasa tamike tana tambayar "Islam me yafaru dashi? baida lpy ne naganki haka?" girgiza kai tashiga yi, tamike jitake zuciyarta kamar zata buga "not her child,her child,......."abinda take fara aranta Kenan, "Islam kimin magana" cewar uwar soro, "ba'a.... ka....wo min shi....ba,uhm....zuwa nai.....don in dauke shi" tafara muryarta na rawa,salati uwar soro tashigai tana fadin "takamba? ina takamba takai jaririn?" "Kekuma da baki jishi ba dan me yasa baki kirani kin tambaya ba" Jin an ambaci sunan takamba yasa islam tadanji dama dama don itace amintacciyar jakadiyyar Fulani hajar,Amman kuma har cikin ranta bata taba yarda da dattijuwar ba tun lokacin data taba kamata tana barbada wani abu cikin abincin mijinta,alokacin ne ta sakata taci abincin don tinaninta ko gubane tasaka yariman sbd attempting kasheshi datasha kamawa anayi tahanyar gubar amman ba abinda yasamu takamba koda taci abincin data sanar da Fulani da yarima cewa sukai she's just being over protective ko kowa ze cutar dasu acikin gidannan banda takamba domin itace baiwar Fulani tunta aure,kuma tareda ita aka raini EHSAAS yace da takamba zata kasheshi da tini ta aiwatar da hakan saboda babu abincin wanda yakeci agidan bayan na Fulani se nata. Islam cikin son bawa kanta karfin gwiwa take fadin "tohm kila Maama takaiwa shi, grandma bari naje naduba," cikin tashin hankali uwar soro tace "kuban mayafi na" aka miko mata tabi bayan Islam da in minutes takarasa gaban mota hannun ta yana rawa ta bude tashiga. uwar soro tana fitowa tai saurin fadawa baya tareda kuyangar Islam din,awani irin mugun speed taja motar xuwa unguwar Fulani.

ko gama parking bataiba tafito se dogaran kofarne suka shiga suka kashe motar Islam shigewa tai,uwar soro da jikin tsufa da sauri take binta abaya, babu kowa ababban falon hakanne yasa Islam ta haye sama inda turakar Fulani take direct tana fadin "maama maama," tunkan takarasa kofar dakinta Fulani tafito sanyeda kayan barci don taji muryar Islam din kuma dukannin alamu sunnuna na lafiya ba. karasawa tai tana rike hannunta tana fadin "maama junior yana nan ko,?" tana kallonta cikeda wani irin hope dinda burinta ace danta na ciki tashiga ta rungume shi, "maama yana nan ko?" tasake tambaya tana kallon Fulani, Fulani da kanta yadaure tace "ba dazun nabaroshi sashen uwar soro ba,yanata rigima ba'a kawo min shiba," sakin hannun Fulani Islam tai tashiga baya da baya da badan uwar soro data hayo yanxun tana nishi ta tareta ba da wllh se ta fada benen, "Islam yana nan ko?" uwar soro ta tambayeta,tana kallonta, girgiza kai tashigayi wasu irin hawaye masu dumi suka shiga fitowa a idonta,cikin ficewa daga hayyaci take fadin "shima sun daukeshi,my son dana meyay musu he is innocent, don Allah sudawo min da dana," tafada kamar zararriya tana kokarin fixgewa daga rikon da uwar soro tai mata Fulani da hankalinta ya tashi sama dana kowa dasauri tashige daki ta dauki waya direct mai Martaba tasanarwa aka kulle dukkanin wata kofar shiga da fice na palace din,yace "gashinan zuwa dakansa," dogarai aka baza tako ina da wasu mahaukatan securities kanajin masarautar NURISTAN din kasan babu lfy,babu shiga babu fita, kasarma baki daya acikin daren aka rufe dukkan hanyoyin fita ciki kuwa harda tsaida hawa da saukar jiragen sama dana kasa da motoci.

Kamar almara babu takamba babu jariri zuwa tsakiyar dare ba iya Islam ba har uwar soro da Fulani neman zarewa sukeyi, uwar soro najin sakacinta ne data bari ta kamba tana daukar jaririn bayan duk sunsan harin ransa akeyi,kusan duk wani mai ruwa da tsaki afadar yana bangaren Fulani aranar har zuwa safiya ana jajanta abinda yafaru,neman takamba akeyi babu kakkauta wa har gidan iyayenta akaje inda aka tarar da babanta wani kyamushashshen tsohon da yakusa shekaru tamanin aduniya tahowa dashi akai fada bama ya iya tafiya dakansa tambayar duniya ina takamba take yace musu shi yakusa shekara uku ma rabonsa dayasata acikin idanuwansa. Waziri da mai babban daki sunfi kowa nuna damuwarsu akan rashin jaririn, galadima kuwa Allah yakyauta kawai yay yazauna dai jigum ana taya su jimami. seda akai asubah aka watse wani irin mahaukacin zazzabine ya kama Islam,dakyar tai alwala tafito dakyar ta daddafa tai sallar asubah tazube kan daddumar tana hawaye tanajin she failed as his mother data kasa protecting dinsa, tasan da EHSAAS yana nan ko kwaro baze bari yakusanci inda danshi yakeba balle mutum dan Adam,tasan yajja EHSAAS ke kaunar cikinta ze iya bada rayuwarsa saboda shi,ita wace irin uwace data kasa protecting danta take fada aranta.

mimah ce taturo kofar dakin tashigo,ta tsaya akanta tana fadin "Islam indai ba ciwo kikeso kijawa kanki ba,toh kibar kukannan haka ya isa tashi kinji" dagowa tai tana kallon mimah da firgitattun idanuwanta kafin ta risinar dasu tana sake fashewa da kuka wllh durkusawa tai kafafuwanta akan gwiwo yinta tashiga hada hannu bibbiyu cikin roko take fadin "gimbiyah mimah dan girman Allah dan soyayyar dakikewa Allah da manzansa,kidawo min da yarona na rantse da Allah bazan sake fada ba bazan sake pointing finger akan kowaba bazan sakeba dan girman Allah karku cutarmin da yaro wllh I will let everything go, dan Allah kidawo min da junior shine rayuwata," mimah tsayawa tai tana kallonta tana son ta sheke da dariya amman kuma tafasa aranta tace "ashe karamar yar iska ce Islam din tunda harta risina tunkan afara wasan," amman me ita kanta yanzun zata iya bayar da duk abinda ta mallaka don abata junior din kodan tai amfani dashi gurin cuzgunawa Islam amman me batasan wanene yaymusu irin wannan shigen ba. "Islam" mimah tafada tana kallonta "Banini kadai kike kokarin tarwatsawa agidannan ba, banini kadai kakai pointing kikace nakashe miki mijina, sannan banini kadai kikaima rashin arziki ba,kisani EHSAAS nada tarin makiya acikin gidannan kuma ke kina kokarin tonosu ne tayaya kike tinanin danki ze zauna lpy bayan ansan shishi kadaine weak point dinki, abu daya dazan gaya miki shine, junior baya hannunmu ban cutar da EHSAAS yana karami ba, meyasa zan cutar da dansa in cutar da junior ince nayi me,nida iyayensa nakeyi, ke kinsan nafi karfin inkara da dan tayin jariri_ Islam muryarta na rawa take fadin "dan Allah kidawo min da dana nasan yajja kika tsani EHSAAS kuma nasan tsanarsa ce zata shafeni nida junior dan Allah kidau fansarki akaina ba akan dana ba," "hmmm" gimbiyah mimah tafada tana neman guri tazauna tace "garama kitashi kije kinemi danki agunsu domin duk tsanar da naiwa EHSAAS, kintaba ganin na nemi in cutar dake?' Ta tambaya girgiza kai tashiga yi tace "tohm ni laifin dan uwana baze shafeku ba,dan haka kinemi danki awani gurin banan ba" tafada tana kwanciyar ta,azabure Islam tamike tana ficewa adakin mimah tashiga dariya tana fadin "saura kadan kwakwalwarki takwance,zuciyarki tabuga don bakinciki kibi dan iskan yaroncan lahira nahuta shegiyar yarinya se bakin masifa chai chai chai irin zuciyata tai sanyinnan ko,tohm wllh koda nasan inda yaron yake baxan fada mataba balle daga baya tanemi tonamin asiri shegiya kafura tubabbiya."

Daga bangaren su Mehtav kuwa da daddare iyah ta tattarasu suka koma gida ba wanda ya iya barci cikin Abeey da Mehtav saboda damuwa da tinanin halinda Islam din keciki alwala sukai suka ringa mai addu'ar samun sauki.

washegari da asussuba Mehtav ta tashi ta shirya kyakkyawan breakfast datasan Islam din naso ta zuba a basket din daza'a tafi dashi asibiti incase koda yatashi. se kusan goma inna tafito tayi mamakin ganin Abeey da Mehtav har sunyi wanka sun shirya ita suke jira,jabiru driver ne ya dauke su har zuwa asibitin doctor kafaya har lokacin kuma Islam din be farfado ba,amman dai ta tabbatar musu he is fine now.

suna ta jiran tsammani ne kawai,karfe hudu nayi inna ta saka jabiru yamaida su Mehtav gida saboda tasan dolen dole engineer Habib yakusa sauka akasar koma duk inda yake kilama yana cikin Nigeria,kuma tasan asibitin zefara zuwa. Abeey da Mehtav da suka koma gida gaba daya jikinsu asanyaye yake bayan sunyi wanka Abeey cema takwanta tana rama barcin da bataiba jiya da daddare Mehtav kasa barcin tai kawai tatafi kitchen,girki tashiga yi kala kala na tarbar paa dinnasu dashi, saboda tason yanason abinci mai dadi atleast idan yasamu abinci me dadi ready, kila yadan rage hukuncin daze yimusu itada Abeey.

Seda akai sallar magrib ta kammala takoma daki tatada Abeey tai sallah,sannan suka dawo parlour sukai zaman jugum jugum, Abeey takalli Mehtav tana fadin "Yah Mehtav waiko yan makarantar kauyennan suna jin turanci?" Mehtav kallonta tai irin karki damenin nan,tace "dagaske fa kinga gwara insani sbd can paa yace ze maidani inmuka sake rashin ji," "tohm waye yaja? duk bakece kika jaba tsabar toshewar basira kintaba ganin inda mara lafiya ya warke babu shan magani" Mehtav tafada cikeda fada, Abeey kasa dakanta tai tana fadin "aidai nayi nadamar abinda nai kuma bazan sakeba, I did it for you yah Mehtav,sbd inason kisamu wanda kikeso" "did I ask you to?" mehtav tafada tana jan tsaki kasa kasa tana jin tausayi da kauna da jin haushin Abeey din duk lokaci daya tasan Abeey has a good intention behind abinda tai amman kuma still ba daidai bane tunda gashi hakan na neman saka rayuwarsa cikin hadari, "wai bazaki ci abinci ba? Mehtav ta tambayi Abeey tana kallonta, "banajin yunwa cewar Abeey" tana zumburo baki ashagwabe, "kindaisan yunwa batada hankali ba'a mata iyayi inma xakici kije kici nise paa yadawo zancike" Abeey tace "nima" haka daidai nan sukaji horn din dakeyi akofar gidansu, mikewa sukai don sungane motocin babansu ne suka karaso nan danan sukaji zuge gate ana shigowa,Abeey dasauri tai bayan Mehtav tana cukuikuyeta Mehtav tace "dallah cikani,aiduk ke kikaja bazaki fito ba," "dan Allah kiboyeni I can't face paa pa" tashiga rokon Mehtav daidai iya na kwada sallama acikin dakin gidan,ita tafara shigowa bayanta engineer Habib bai,dan dattijone da akalla zaikai shekaru hamsin aduniya,amman tsabar yajja boko da wayewa ya ratsashi zaka dauka befi 40 ba, idanuwansa sanye da medicated eye glasses irinna Abeey sak sak,kana kallon shi kasan shi ya haifesu sbd kammanin dasuke da yaran musamman Abeey,sedai yafisu duhun fata sbd shi namiji ne,mamakine yacika Mehtav ganin Islam abayan sa,sanye da wasu sababbin kananun kaya bakake dasukai bala'in mishi kyau,dukda yadan fada yayi duhu amman kamar bashine yay doguwar suma haka ba,he looks so happy. kasa dakanta tai ganin idon paa din akanta,yakaraso falon yazauna.

da sauri Islam yakarasa yana fadin "Abeey, Abeey,Abeey my friend are you playing hide and seek sbd" yagano dan karamin hannunta data zagaye Mehtav dashi,jin muryar Islam yasa Abeey tamanta ma tareda paa suke tafito tana fadin "handsome Islam katashi? Yajikin naka, I'm so sorry" "Natashi Abeey I'm fine" yafada yana mata murmushi rungumeshi tai shima yay hugging dinta back yana fadin" "That man there wancan yacemin sunashi papa and he is nice,yacemin shima anan gidan yake kuma shine babanmu duka wai dagaske ne?"yatambayi Abeey yana nuna mata babansu, Abeey satar kallon paa din tai dasauri tamaida kanta gurin Islam tace "yes he is our paa" Murmushi Islam yashiga yi cikeda zumudi yashiga bata labari "papa yasiyamin kaya sababbi sannan yasiya min wannan" yashiga nuna mata agogo mai waya ahannunsa yana dannawa yana kawo wuta seyay dariya Abeey tayashi dannawa tashiga yi suna dariya kamar wasu tababbu. Mehtav simsim takarasa gaban paa tana tsugunnawa tashiga gaidashi tana mai sannu da dawowa be amsaba kawai ya mike yana fadin, "kubashi abinci," Yana referring to Islam "zanje inwatsa ruwa indawo" bin bayan paa din da kallo tai tana dafe kirjinta yajja yake bugawa kamar ze faso, "yah Mehtav kinga agogona" taji Islam yana fada yana nuna mata,kallonsa tai tana galla mishi harara don haushinsa takeji duk shine yasata cikin wannan halin tana dari darin ma kula babanta inda dane yajja yadawo dinnan itada Abeey rige rigen zuwa su rungumeshi sukeyi amman yanzun tsoron ma hada ido take dashi sbd tasan tamai laifi,islam shima hararar ta yashiga yi,kamar wata mace harda farfara ido,daya mugun bata dariya tace "ko kyau ma agogon beyiba" tana ture hannunsa daga gabanta,kallon Abeey yay yana fadin "kinganta ko," Abeey tace "rabu da ita Islam kasan halin ta ciki abun take maka," yace "meye ciki abun?" dariya tai Abeey tashiga mai bayani daman itace malamar sa tace "tohm bakinciki takeyi," yace "and whats that?" Yana dan yamutse fuska Dafe kai Abeey tai tana fadin "haushi takeji ita paa besiya mata ba sekai ya siyawa," dariya ya farayi yana kallon Mehtav data mike tai dinning,tana jinsa yana cewa "kuma papa baze siya mata ba tunda ita batada kirki masifaffiya ce," spicy stir fried rice with chips and chicken tashiga zuba mishi daidai yajja tasan zeci tazuba, amman tacika mishi naman kazar akai saboda tasan yanaso,tana gama serving ta kalli inda suketa wasa da agogon kmr irin yan kauyennan dasuka shigo birni dagashi har Abeey,tace "Islam time for food zokaci abinci," makale mata kafada yay yana cigaba da danna agogonsa,fitowa tai tana karasowa gurinsa tace "tashi muje kaci abinci" tana hade rai kamar yayarsa, Abeey sum sum ta wuce saman table tazauna,don yunwa take ji daman, "zanyi ceasing agogonnan in baka tashi bafa," kallon dataga yawatsa mata da wadannan grey eyes din nata yasa tadan sha jinin jikinta,bece mata kalaba ya cigaba da danna dannan sa daman suncire agogon ahannunsa shammatarsa kawai tai tana warce agogon ahannunsa. dasauri yamike taboye agogon abayanta tana fadin "you won't get it back harse kagama cin abincin," "I don't want to eat" yafada sounding very serious "And give me back my clock" juyawa tai daniyyar tafiya dining inya gaji aize bita kawai taji ya fizgota tafada saman faffadan kirjinsa,kallonta yake ranshi ahade da alama bayason raini kirjinta sama da kasa yakeyi tsabar tsoro don tunda take inba shiba namiji be taba mata irin wannan rikon ba "my clock" yafada yana hade hannayenta guri guda abayanta yakarbe agogonshi kafin ya tureta ajikinsa yana fadin "I'm not your mate, Abeey tace I'm the big brother" kirjinta dake bugawa tarike tana kallonshi kamar ma besan abinda yay mata yanzun ba,yazauna yana danna agogonsa,Mehtav kamar mutum mutumi ta tsaya tana maida numfashinta,muryar inna tana sallallamin uban naman data gani saman abincin abeeda ce tadawo da ita hayyacinta.

ta karasa dining tana jan kujera, Abeey abincin da aka zubama Islam takeci tana zuge kazarta hankali kwance,inna tace "kedai yarinyar nan ko yar gidan mayu ce se haka inda ba habibu ya haifeki ba aida nafara tantama sekace kura,duk namannan ke zakici ke kadai," Abeey gwalo takema inna tana cin kayan ta hankali kwance, ba'a jimaba paa yafito sanye cikin pajamas dinshi masu kauri,yazauna saman table Abeey satar kallonshi takeyi ya hade girar sama data kasa yaki basu fuskar kulashi balle subashi hakuri, Mehtav ce tashiga serving dinshi daidai abincin datasan ze isheshi,batareda ya kalleta ba yace "mara lafiyan yaci abincin?" ahankali tace "yace baze ciba tundazun nake fama dashi," hankalinsa nakan agogon kallon inda yake zaune paa yay kafin yace "uhm yama?" yana kallon inna dasauri tace "Islam sunansa," yace "Islam son, come, zokaci abinci kaji" yana murmushi, Islam juyowa yay yana kallon paa yashiga girgiza kai yace "I'm not hungry," paa cikin lallabi kamar yana magana da Abeey yace "nasan bakajin yunwa but you need to eat to gain your strength back, yajja zakaje kaita danna agogonka baza kagaji ba," dan shiru Islam yay kafin yataso yaja kujerar kusada paa yana fadin "tohm zanci" ya ajje agogon agefe yana kallon Mehtav dake gefen hannun sa na dama, alamar tazuba mishi harara tagalla masa kasa kasa take fadin "seka samu yar aikin dazata sake zubama abincin," sarai yaji me tace yakalli paa yana fadin "tace wai insamu yar aikin da zata sake zubamin," dasauri tazaro ido tana fadin "kai nina fadi haka sharri zakaimin," zaro mata ido yay kamar yajja tai masa yace "aihaka kikace," kafafuwansa dake cikin socks ta take irin don tai shutting dinshi up dinnan, amman ina se yama fasa karar jin zafin dayay,paa yace "Islam lafiya kuwa?" nuna Mehtav yay yana fadin "she's wicked, tabugarmin kafa na" Yakarasa ashagwabe ya tsugunna yana taba kafar, "Mehtav" paa yafada with authoritative voice yana kallonta,dasauri tace "sorry paa" don tasan bayason hayaniya inyana cin abinci,abincin tashiga zuba mai dayawa kuma tana sane take xuba iya gun abincin banda naman se uban chips ta loda mai. tai mai murmushi tana tura mai plate din tace "here is your food," kallon abincin yay yashiga kallon na Abeey da paa sannan yakalli nata farantin dako tabawa bataiba, straight yajanyo farantin ta yana tura mata nashi yake fadin "wannan nakeso kekici wannan," Yatura mata nashi, Mehtav kamar wata Abeey ta tabe fuska tana fadin "karka cimin abinci, aiba naka bane ga naka nan" tatura mai nashi xatai canjen yarike farantin yana fadin "ni wannan nakeso shine zanci," Abeey kallonsu tashiga yi with much admiration tana dariya kasa kasa,inna tace "Mehtav nikam mezan gani abin kunya kinsan yaronnan ba lafiya gareshi ba ki biyemai kuyita rigima kamar wasu kananun yara, meye hakanne wai bazakici girma kibarmai wanda yakeso ba," kamar Mehtav zatai kuka haka ta hakuri tashiga cin nasan,gashi ba daman ta mike tarage tazuba naman paa zesan mugunta Mai, shikuma yanacin nata harda yi mata gwalo, engineer Habib duk yana lura da abinda sukeyi. tunda yake be taba ganin Mehtav tana acting so childish tun bayan rasuwar mahaifiyar ta ba se yau koda kuwa agabansa ne,she always acted like a woman, abig sis and a mother to Abeey, amman ganinta gefen islam suna murmushi ya tuno da Mehtav is not that big she's just a 22 years old little girl dake bukatar kulawa da soyayya. abinda sukai tabbas ba dede baneba amman yafijin haushin kansa fiyeda komai cikin wannan abin yana ganin kamar yayi failing as a father dahar yaransa zasu shiga trouble irin wannan su boye mishi suki gaya masa tsoronsa dasuke ji yadara shakuwar dake tsakaninsu wanda yay alkawarin gyara hakan kuma deep down yana alfahari dasu da temakon yaron dasukai, ze tayasu aikin ladan tahanyar kula dashi kuma ze binciko iyayensa ko a ina suke afadin duniyarnan ze samesu yamaida musu da dansu cikin aminci, amman kuma tabbas baze kyalesu hakaba don idan yabarsu kamar yace gobe su sakene amman dai he will not be harsh kamar yajja inna tabukata,ze hukuntasu da barazana cikin ruwan sanyi.

peacefully suka gama cin abincin daren nasu,inna tace da Mehtav da Abeey suje su gyara dakin baki anan EHSAAS ze koma da zama cikin jindadi suka shiga daman komai agyare yake kawai sharewa Abeey tai, Mehtav tagoge shi tas tas ta chanza beddings din,tawanke mishi toilet.

duka su ukun suka hadu suka kwaso kayanshi daga dakinsu suka dawo dashi dakin bakin, Abeey takalli Mehtav lokacin dasuke jera kayan tana fadin "yah Mehtav wai kodai paa ya hakura ne? kingafa bece komai ba kuma anbawa Islam dakinnan kina ganin yanzun baze koreshi ba kuma baze maidamu kauye ba," girgiza kai Mehtav tashiga yi tana fadin "tunda kikaji paa yayi shiru wllh akwai abinda yake shiryawa nafi tsoron shirunsa akan maganar sa," Abeey tace "kumafa hakane yah Mehtav, tohm nidai duk abinda zefaru gara yafaru amman dai banason akori Islam" tace "nima haka saboda kinga bashida kowa bayada inda zeje,naga kuma kamar paa nasonshi," Abeey tace "nima haka kina ganin dazun yanata magana a dining aida mune da tini ya koramu koya mana fada amman shibe cemai komai ba," Mehtav tace "eh Abeey nima nagani." Suna kammalawa fitowa sukai. Islam har yafara hamma saboda magungunan sa da yasha akwai mesaka barci aciki yay kwanciyarsa saman doguwar kujerar falon idonsa akan TV but he looks super cute yajja idanuwansa ke lumshewa yana kokarin fara barci ,paa ma yana falon yana kallon news, Abeey nason zuwa ta hau jikinshi amman tana tsoro tasan tayi ba daidai ba dukda haka kujerar dayake zaune taje tadan xauna tana satar kallonshi,dagowa yay suka hada ido da sauri tai kasa dakanta,miko mata hannayensa yay alamar tazo dasauri takama tana fadawa jikinsa kamar tayi shekara dari bata ganshi ba,cikin shagwaba take fadin "papa," yace "don't papa me, ashe kema kin iya karya kina biyema Mehtav kuna boyemin abu ko," Mehtav dasauri takarasa kusa dashi tana kama hannunsa, Abeey tace "we are sorry papa bazamu karaba ko ya Mehtav" jinjina kai Mehtav tashiga yi kafin tace "and is not my idea, I swear papa Abeey ce tace karfa mufada maka tunfarko" Abeey ta zaro ido tai tana fadin "papa you know me right, ni ba'a sirri sena fada ma yah Mehtav convince me not to tell you kasan bazan boye ma ba" takarasa tana fici fici da ido da kallo daya yaymata yasan karya take dukkanin su yasansu ciki dabai yasan duk abinda kowacce zata iya yana mamakin yajja Abeey kewa Mehtav wayo duk girmanta,yawanci Abeey ke influencing dinta suyi rashin ji se kuma tazo tabarta aciki tace ai ita karama ce Mehtav ce tasaka ta, sedai taita rantse rantse tana kokarin kare kanta abanza. shiyasa ya yanke hukunci yasan Mehtav will never find any trouble indai Abeey bata gefenta don haka boarding school zaikai Abeey kunnansa yahuta kawai. "Paa believe me Allah banice nace mu boyeba" Mehtav tasake maimaita masa,jinjina kai yay yana fadin "niba ruwana dukkan ku kukai colliding kuka sabamin don haka dukkan ku zanyi punishing,you abeey boarding school zan kaiki session na karewa kekuma aidaman kin kammala semester daya ta rage miki don haka zanbaki zuwa lokacin kifara tsayawa damasu nemanki kifito da miji kiyi aure aikin isa tunda har kin iya taking care of things alone," dasauri Abeey tamike daga jikinsa kwalla na cika idonta, Islam da sama sama yakejin hirar tasu dan bude idonshi yay suka sauka cikin na Mehtav data fashe da kuka jin paa yace zemata aure.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Send Comment & Vote [15/05, 19:31] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.