EHSAAS

Chapter 21

by @fatoumspassion

Ahankali yaji idanuwan sa na budewa sosai saboda sautin kukan nata daya sauka har cikin kwakwalwarsa haka kawai yaji bayason yaji tana kukan. zaune ya mike yana kallon yadda Mehtav tashiga bawa paa dinnasu hakuri tareda alkawarin bazata sakeba don Allah yajanye maganarsa, Abeey tayata kukan tai suna rokonshi,dan yamutse fuska Islam din yay yana mikewa yazo inda suke hannayensu both yakama yana fadin "stop crying pls" dagowa sukai duka suna kallonshi,Abeey cikin kuka take fadin "Islam kacema paa bazamu sakeba don Allah kada ya rabamu," Mehtav dasauri ta janye hannayenta daya kama tana dunkulesu ajikinta,tana saita kanta tama manta agabansa suke aida batai kukaba karya rainata. Islam paa yakalla cikin tuhuma irin babban yayannan yace "why are you making them cry? Your bad I don't like you," yakarasa fada yana janyo Abeey daga jikin paa din ya dawo da ita kusa dashi yashiga lallashinta yana cewa "tadena kuka,zeyi chasing paa away from them tunda kuka yake sasu," leka face din Mehtav yashiga yi yana fadin "you lo ugly in kina kuka pls stop mn," harararsa tashiga yi kasa kasa,yasa hannu yana dungure mata kai da sauri takalli paa dake kallonsu tace "haka fa yake innace yabari baya bari," Takarasa cikin son kare kanta paa tsaki yay yana mikewa yace "inshi bashida lafiya besan meyake ba? ke ina hankalinki yake? kar insake ganin irin haka kutashi kuje ku kwanta seda safe" mikewa tai tana fadin "paa pls I'm...." Bata karasa ba taga yanuna mata kofar dakinsu,alamar yayi dismissing dinsu kenan. mikewa tai sum-sum tana bin hanya, Abeey ma tamike agefen Islam tana mai bye bye tareda mai alkawarin "tadena kuka tatafi takwanta" tabi bayan Mehtav. kallon paa Islam yay yana hade rai, ya gallama paa harara irin yanajin haushin sa dinnan yay gaba zebi bayan Abeey dasauri paa ya rikoshi yana fadin "ina zaka?" yace "don't touch me your a bad Person your making my Abeey and yah Mehtav sad," girgiza kai paa yay cikeda hikima yake fadin "ba haka za'ai ba kaifa abokinane yadafo kafadarshi" yana fadin "zauna muyi magana man to man," zama yay yana turo mishi baki, Paa yace "kaga mu mazane ba mata ba bekamata mu ringa biye wa shirmensu ba ko,laifi sukamin shine na hukunta su, shine suke koke kokennan karka damu zuwa safiya zasu dena," kallonshi yay yana fadin "meye laifi?" Paa yashiga mai bayani yace "nace musu karsuyi abu, kamar kaidai yanzun innace maka karka kunna wannan TV din seka je kakunna batareda nasani ba tohm kaga kayi abayan idona,don haka dole sena hukunta ka,don ka saba dokar dana gindaya maka" dan zaro ido yay yana fadin "shikenaan yanzun bazan kalli TV ba seka sani?" yakarasa yana rike bakinsa kamar yajja Abeey keyi in aka gaya mata abu tai mamaki. girgiza kai paa yashiga yi before yace "not like that abinda sukai yafi mere kunna TV, they lied kasan meye karya ko," jinjina ki yay yana fadin "Yes! Abeey told ne" yace "kuma kasan babu kyau ko" jinjina kai yay yace "tohm they lied to me shiyasa nikuma nai punishing dinsu yanzun suke kuka," "too bad" cewar islam yana girgiza kai kafin yace "that means aure is punishment" yakarasa yana jinjina kai irin yagane dinnan paa can't help it kawai yafara dariya saboda yajja Islam din yafada, Islam hade rai yay yanawa paa kallon dariyar fa tamenene girgiza kai paa yay yana fadin "ba punishment bane, but nayi amfani da hakanne don Mehtav tasan ta girma kuma tayi laifine kuma is high time daman in aurar da ita din,tanada manema bawai bata dasu ba, nine daman ban bata damar tsayawa da kowa ba," Islam yace "so what's this aure thing? Manema?And so on da yasata taketa kuka,is it that bad?" paa yace "union ne na man and woman like..." pa yay shiru don besan yajja ze fara bayanin yadda kwakwalwar Islam din zata dauka ba. se kawai yace "union ne na mace da na namiji suke coming together as one suzama husband and wife," murmushi Islam yay yace "so they become one like how?" Paa yace "like they will be a couple," Islam yace "kamar kaida old zombie witch din can?" yana nuna mai direction din dakin iya,paa yace "kaji ja'iri babar tawace witch?" turo baki islam yay yana fadin "banine nafada ba Abeey told me" girgiza kansa yay aransa yana fadin "yarannan uwar tawa suke cema witch zan gamu da sune" afili se yace "not like that kaga ita she's my mom,itace ta haifeni! come let me show you something" yafada yana janshi zuwa dakinsa wani tsohon photo albums ya ciro mai, don haka kawai yaji yanajin yaron har cikin zuciyarsa shiyasama yake jansa ajiki, budewa yay yana mika mai hotunan shine tareda mahaifiyar su Mehtav lokacin bikinsu, yace "kaga wannan nine! wannan kuma itace mom din Mehtav da Abeey," Islam kallo yake, yashiga shafa fuskokinsu yana murmushi "cause they look so happy" yashiga budewa page bayan page harzuwa lokacin haihuwar Mehtav tambaya yashigayi "waye wannan aka cemai Mehtav ce" yace "she looks so tiny" paa murmushi yay yace "aihaka jarirai suke kayanta yar karama ko but kalleta yanzun all grown up" shiga mai bayani hutunan yay tun daga haihuwarta har zuwa lokacin datai shekara goma yana mai bayanin yajja akai da sanda akai hotunan da inda sukai susu uku. yace wa paa "tohm ita ina maman take yanzun" dan jim paa yay before yace "she passed away while delivering Abeey," girgiza kai Islam yay cikeda jimami don yasan meye mutuwa yace "sorry paa,karkai kuka" paa murmushi yay yana dafashi irin is okay dinnan. Islam kallon hoton Mehtav yashiga yi kafin yazaro guda daya daga cikin photo album din yace "can I have this one," paa kallon hoton yay yana fadin "why?" Yace "uhm she looks so cute I wanna keep it" yafada yana shafa fuskarta, jinjina mai kai kawai paa yay, Islam yagyara zama yana fadin "ka nunamin hoton kowa banda nawa ni ina nake?" Paa tsuru-tsuru yay domin sam ya manta Islam din ze iya tambayarsa wani abu gameda hakan,yace "kuma kace kai da wannan yanuna hoton mamansu Mehtav kune kuka haifi yah Mehtav and Abeey nifa? Abeey tacemin I'm her big brother ni ba kumin hoton bane ina karami," girgiza kai paa yay kafin yace "lokacin da aka haife.ka zamani be zoba babu camera na daukar hoto duka shiyasa" dan jim Islam yaay kafin yace "so you got me before getting married right?" paa rudewa yay gaba daya yana fadin "I'm... I'm..." Islam ya kafeshi da ido yana jiran amsarsa,se yace "Islam is complicated kabari gobe zanbaka wannan answer din I promise," dan murmushi Islam yay kafin yace "and one thing kace kanason kaima Mehtav aure nima inaso inyi aure zan aureta kawai,we will look good together just like you and mom look at this picture" yafada yana nuna mai pic dinsa da matarsa,paa yace "muje inrakaka ka kwanta Islam naga alama kafara jin barci koh" dan murza ido yay yana fadin "barcin fa ya washe fa, yanzun amsa kawai zaka bani zaka bani ita,ka auramin ita," paa mikewa yay yana fadin "ka kwanta yanxun first da safe ma karasa maganar," jinjina kai yay suka fito shida shi har kofar dakinsa yarakasa yana mai bye bye yashige ciki paa yace "yau Allah ya hadashi da rigimmamen yaro shirmenshi baya karewa sekace Abeey,ina shi ina wani aure awannan halin dayake ciki dabema san kanshi ba", yanzun yafara ganin kokarin su Mehtav da suka iya handling dinsa tsawan wannan lokacin. Daki yakoma yasake shirin barci yadakko wayarsa, cikin sa'a yaga text dinda taj yay masa,cewar "sun fara bincike akan case din Islam din in sha Allah cikin satinnan zezo mai da labari mai dadi," murmushi paa yay don yayi trusting aikin tajuddeen indai ya sakashi aiki tohm seyayi completing yake samu yahuta,tun a asibiti bayan yaji cikakken bayanin lalurar data samu Islam din daga Dr kafaya da yajja su Mehtav suka kawoshi yadau alkawarin ze cika aikin alherin da yaransa suka fara ze sada yaronnan da iyayensa shiyasama yanemi taj jami'in tsarone na sirri,yana aiki akarkashin hukumar DSS takasa,kuma tajuddeen shine da daya tilo ga yayar mahaifiyarsu Mehtav da itama Allah yay mata rasuwa shekarun baya tun kafin rasuwar mamansu Mehtav don haka taj din kusan gurinsu yatashi hannun mahaifiyar Mehtav din lokacin da suka haifi Mehtav ne dangin mahaifinsa dake can Maiduguri suka nuna suna bukatar daukar yaronsu, hakanne yasa suka hakura suka barmusu shi sbd suna kaunarsa sosai suma, sunmusu kara kuma suna matukar kula dashi. tohm tunda yaje dakin Islam din yay introducing kansa matsayin paa dinsu Mehtav din ya dauki hoton yaro asace ya turama Taj kuma yasan duk inda yafito seya nemo koshi waye indai har a kasarnan yake,koda ba'a nan yakeba as far as akwai information akanshi a yanar gizo gizo dole zasu sami inda yake nan bada jimawa ba.

Washegari da asussuba paa ya bugama Islam kofa yace "yafito zasuje masallaci" yana turo baki haka yashige toilet yakama ruwa ya dauro alwala yafito paa ya bashi wata sabuwar jallabiyya cikin siyayyar dayayo mishi adazun ya saka yana kama hannunsa suka fice zuwa masallacin dake can farkon layinsu.

asahun gaba akoda yaushe paa yake sallah saboda himmarsa gurin zuwa mosque dawuri haka kawai Islam yakeji kamar this is not the first time daya taba ganin kanshi a irin wannan gurin musamman yajja aka jere a sahu, yasa yake kokarin tina wani abu daya shude cikin kwakwalwarsa amman duk yadda yakaiga so yatina kasawa yay,sema kansa daie kokarin fara ciwo, har aka tayar da sallah,anitse sukai sallah suka idar suka zauna azhkar,paa sosai yaji yana alfahari da yaransa ganin yajja Islam din ke jero addu'ar bayan gama sallah yana gamawa ya daura da addu'ar safiya,he felt proud irin uban da kasan kabawa yaranka ilimi mekyau kuma kana ganin amfanin sa.

seda rana tafara fitowa sannan shida paa suka fito Islam mood din sham kamshin ne suka dawo yana ganin yajja paa yatsaya yana gaggaisawa da mutane yaja gefe yanuna ma kamar baisan da wanzuwar suba,se lekensa suke suna tambayar paa "ko bako akai don basu taba ganinsa ba?" amsawa paa yay da "eh bako yay shidin kamar danshi yake" seda paa ya yafito shi sannan yadan mika musu hannu suka gaisa sama sama se Masha Allah suke cewa suna kallon sa da duk yaji ya tsargu, shikansa paa se yanzun yalura da tsantsar kyawun Islam din suke yabawa suna fadin "Masha Allah, Masha Allah" din.

Tare suka dawo gida, paa be barshi ya koma barci ba gym dinsa dake cikin garden din gidan da Mehtav bata taba barin sa ya fitaba suka je. Islam se wow wow! yake fada yana tambayar paa "ai betaba zuwa nanba kuma anan gidan yake?" paa yay murmushi yana fadin "ai baya barin su Abeey zuwa don lalata mai kayan amfani sukeyi," kamar wani da da uba haka suka shiga tare ya nata nuna mai yajja ake amfani da abubuwan, shikansa paa was a bit surprised da yaga nandanan Islam ya iya komai ya dauke cikin dan kankanin lokaci. good 1 hr sukai cikin gym din kafin sufito gaba dayansu sunyi zufa musamman Islam da yake yadade beyi ba, wata skin tight black vest ce ajikinsa data kamashi tafito da duk wata kyakkyawar murdadden jiki da Allah yay masa, yadaura wani white mini towel awiyansa yana tsane gumin da yake jikinsa. suna shigowa paa ya wuce daki don yana bukatar watsa ruwa, Islam har ze bude dakinsa yaji wani irin kamshin abinci da yasa yaji wata irin yunwa da kishirwa na damunshi lokaci guda, hanyar kitchen ya nufa, Mehtav daketa aikace aikacenta hankali kwance bataji shigowarsa ba sejinsa tai abayanta yana leka kaskon datake suya,saura kiris spoon din dake hannunta yafadi tai saurin saita composure dinta tana fadin "Islam what are you doing?" Hannayenta yakama dake rikeda abin juyawan yazare ahankali yashiga jujjuya mata jitai numfashinta na seizing yajja yake very close to her, she could feel breath nashi har cikin kirjinta, "Islam please stop..." tafada tana zamewa daga gabanshi juyowa yay yana kallonta da idanuwansa dasuka dan kankance sbd beyi barci ya ishesa kamar yadda yasaba. kasa hada ido tai dashi sbd yajja jikinta ke wani vibrating intai hakan ahankali yanufi inda take kmr ze chafkota rintse ido tai,tana fadin "I said stop plzzzzzz" Takarasa tana jan wani dogom numfashi sejin hucin sanyin fridge tai agefenta da alama gurin fridge din yazo ba gurinta ba, ruwa taga ya dauka mai sanyi yana maida murfin fridge din ya rufe tadago ido suka hada ido tashiga kallon manyan murdadden muscles dinshi da broad chest dinshi kamar ya faso tacikin riga da shafaffen cikinsa da tsabar yajja rigar ta kamashi ana iya ganin six packs lines dinshi. shan ruwan taga ya farayi hungrily irin yaji qishi sosai dinnan ruwan harna biyowa ta gefen bakinsa zuwa wiyansa,da Adams apple dinsa ke motsawa zuwa kirjinsa yanabin jikinsa ga zufan da yakeyi har yanzun he looks super hot da yasanya Mehtav jin ta daskare agurin tana hadiye wasu irin yawu daya makale mata amakoshi tana kallon irin yajja yake binta da kallo har ya gama shan ruwansa, ya ajje goran ruwan da yabar sauran kadan yafice daga kitchen din bece mata kalaba. kasa motsawa tai agurin batasan minti nawa ta daukaba sejin muryar inna tana sallallami tai tana fadin "wai kaurin me take ji ne,wake kona abinci?" dasauri takarasa gaban gas din tana kashewa daidai inna na karasowa kitchen din tana fadin "mezan gani Mehtav abin karin kika kona mana sekace wata yar koyon girki tinanin me kikeyi haka?" dasauri Mehtav takarasa inda ya ajje sauran ruwan sanyin tabude tana kwankwada tanajin sanyin yana ratsa kirjinta da yake cida wutar sonshi har zuwa cikinta. ba ita tai training dinna amman zufa itama takeyi,inna tace "ke yarnan lpy kuwa?" dasauri tagirgiza kai tana fadin "inna dan Allah kidanyi breakfast din zanyi wani abu yanzun" bata tsaya jin amsar inna ba tafice a kitchen din kafafuwanta na hardewa har zuwa cikin dakinsu,ganin Abeey har lokacin bata farkaba yasa tashige bathroom haka tasakarma kanta ruwan sanyi aka tana dafe bango batareda tacire kayan barcin dake jikinta ba. kawai seta fashe da kuka tana durkushewa agurin wannan wace irin masiface takeson saka kanta aciki tayaya zataso mutumin da shikansa besan waye shiba? tayaya zuciyarta zata yaudareta taso wanda ako yaushe ze iya barin rayuwarsu? anya kuwa bata dakkowa kanta ruwan dafa kanta ba? seda ta gama kukanta sannan tamike tacire kayan tai wankanta normal tafito daureda karamin towel tawuce closet. se alokacin Abeey tatashi daga barcin tana jinta tana tambayar ta "wai yau baza taje makaranta bane ba? tai mata banza tasan intagaji da tambayar zata dena dan kanta, Jin budewar kofarta tai alamar tafice adakin duka. Abeey straight dakin Islam tawuce tatarar dashi yafito awanka ya kammala shiryawa, Murmushi tai tana hayewa saman gadonshi tace "hi handsome hows your night?" Murmushi yay mata yace "is great full of sweet dreams," tace "awwwwwnnn really? tohm mafarkin wa kayi? hardani dai aciki koh?" dan Rolling eyes dinshi yay kafin yace "uhm tohm akwai ki aciki, amman ba sosaiba nayi mafarkin ranar aurena ne da yah Mehtav,kuma kema kina gurin kinsaka beautiful gown kamar irin na Cinderella," dan waro ido Abeey tai tana fadin "really" yace "yes,ainacema paa ya.bani aurenta jiya kuma nasan zebani tunda so yake yaymata aure," Abeey cikeda son jin gulma tace "gist me everything kaban labari karkabar ko detail guda daya," nan yashiga bata labari dukda inyay sentence daya se yagama shamata kamshi yake cigabawa haka har yagama bata labarin Abeey farinciki kamar ya kasheta take fadin "ai in sha Allah mafarkinnan seya zama gaskiya kaga shikenan inka aureta anan gidan zaku zauna base kowa ya dauketa yatafi da itaba" tafada tana tsallen murna, yace "of cause nima banason adauketa kinga dukda she's wicked amman ni inasonta kince insota sbd tana bani extra meat din abinci kullum," Abeey tace "exactly yanzun abinda zamuyi mufarai wa paa list din abubuwan bikinnan kaga dole mufara shiri da wuri koh kar wani yazo yariga ka Islam" cikin gamsuwa da maganar Abeey yace "yes your right amman ni bansan komaiba dangane da wedding me kike tinani xamuyi?" dan jim tai tana fadin "we will have a simple wedding tunda kaga Islam bakada kudi, baka aiki amman don't worry I'll use my servings muyi hidimar bikin duka dashi kawai," tafada cikeda yaranta da zuciya daya,yace "yes it does not matter wana kalar wedding za'ai as far as me and yah Mehtav zamuyi uniting muzama abu daya, kuma zanfara aiki to get money inringa baki keda yah Mehtav" Murmushi Abeey tai tana fadin "Shiyasa nake yinka islam over and over" littafin koyon karatunsa tadakko da pen dinshi suka shiga rubuta list duk shirmen abubuwan cartoons din Abeey ne,tagama ta karanta mai yashiga jinjina kai cikeda farinciki yana fadin "zan auri yah Mehtav soon," Abeey tashiga hyping dinsa tana fadin y "You will be the most handsome groom ever,angon yah Mehtav," murmushi yakeyi yanajin tana fasa mishi kai duk wannan budurin Mehtav batasan ma sunayi ba.

Daga bangaren Islam kuwa kamar wasa babu junior babu labarinsa wani irin ciwon kirjine ya kwantar da ita sbd ji takeyi gangar jikinta baxata iya daukar mugun nauyin da kirjinta kemata ba awannan lokacin. tana bangaren Fulani har lokacin kuma babu labari domin har yanzun garin arufe yake an karade ko ina lungu da sakon NURISTAN babu junior babu dalilinsa, inkaga Islam seka tausaya mata,sbd yadda take azabtuwa ita kanta fulanin dauriya kawe takeyi tana tsaye akan kafafunta sbd batason tanuna rauninta afili yarinyar ta karaya tasare baki daya, uwar soro ma akwance take tun bayan abun da yafaru saboda tasawa ranta cewar sakacinta ne yajawo aka sace junior din.

Yauma kamar kullum tana kwance saman babban royal bed din dakinta na bangaren fulanin tana aikinta na tinani wanda tasaba domin ko yaya tarintse ido fuskar danta take ganin that beautiful cute face irinta babanshi yana mata dariya,inta fara barci koyaya kukanshi takeji yana karade kunnuwanta yana nema zautata tasan duk inda danta yake yana tsananin bukatarta,ita wace irin uwa ce haka,tana cikin irin wannan tinanin taji anturo kofa anshigo daga idon da zatai suka hada ido da Fulani ta kalleta dakyar ta iya kakalo murmushi tana fadin "Islam yajikin naki? rintse ido tai tana girgiza wa Fulani kai sbd bakinta baze iya furta irin pain din da take cikiba, "Islam kinga galadima ne tunjiya yake zuwa dubaki ana cewa barci kike,ajiyan sau biyu yana zuwa yauma yadawo nasan bazaki so kiganshi ba amman ya dage ko ince masa yashigo kawai?" kallon Fulani tai taga irin hoote din dake idonta tasan tana jin kunyar jay intace bazata gansaba Fulani bazata ji dadi ba sbd yajja take kallon jay din matsayin mutum nagari wanda yadamu da damuwarta,jinjina kai kawai Islam tai tana fadin 'maama yashigo kawai," Fulani murmurshin yake tai wanda ake cema yafi kuka ciwo tana fadin "nagode Islam," fulani bata jima da sauka ba taji ana kwankwasa kofar ahankali ta mike zaune hannunta me dauke da karin ruwan da ake mata ta gyara tana saka hannu tajawo babban cashmere gele data idar d sallah dashi ta daura tana rufe jikinta baki daya dukda cewan mijinta ya mutu tana matukar mutunta kanta da mutunta shi tahanyar suturce jikinta akoyaushe kamar yajja yake matukar kauna. "shigo" tafada asanyaye dabata tinanin nawajen yaji me tace amman me se taga anbude kofar ahankali aranta tace "maye wannan ko azuciya nai magana dole seya jini indai shine," ahankali yazauna saman kujerar dake dan nesa da ita,yana kallonta kamar ze cinyeta ko kyaftawa bayayi,dayasa taja tsaki tana kara lullube jikinta Dan gyaran murya yay Yana tambayarta, "Peace yajiki?" Dagowa tai da dara daran idanuwanta dasukai jajir suka kumbura tana mai kallon sama da kasa irin ita yake tambaya yajiki, Girgiza kai yashigayi yana kokarin durkusawa kasa amman be karasa ba tace burinka yacika you've made my life miserable don haka katashi kafita,kuma dakinnan dakaga kashigo darajar Fulani kaci amman inba hakaba ganin fuskar azzalumi dan ta adda fasiqi irinka amai ma take sani" Tafada cikeda fitsara tana nunamai kofa, "Peace pls kisaurareni wllh kinyi misunderstanding abinda kikaji nace wancan ranar,wllh narantse miki da Allah,na rantse miki da Al Qur'ani izu sittin babu hannuna cikin abinda yafaru da mijinki EHSAAS pls ki yarda dani" Wani irin kallon kama rainamin hankali tashiga yi dayasa yadan daburce yana fadin "Nayarda wancan ranar nasan cewa,yaya Erfan yana planning something akan EHSAAS amman wllh bankawo kisan kai baneba,the real plan din was to drug him a Nigeria muyi kidnapping dinsa and get him to sleep with my niece maisoon sbd yarinyar tarigada tazare taki daukar kaddarar rabuwa dashi, Islam you know I'll never lie to you" Cikin mamaki take kallonshi tana fadin "Mijin nawa zakusa yakwanta da waccan kazamar yarinyar karuwa" Takarasa cikeda takaici dawani zafin kishi daya taso mata Yace "yes,and I swear to you wllh bansan sanda suka canza plan nacewa kasheshi za'ai ba" Tayaya kake tinanin zan yarda dakai tafada tana mai kallon tuhuma tadaurada "Maganganun ku nawancan ranar is still clear acikin brain dina kuma daman kayi alkawarin daukar fansar abinda yamaka" Yace "Peace pls I know deep down kinsan bazan iya kashe dan dan uwana da muka fito ciki dayaba I admit cewan ni mutumin banzane I was such a bastard danake bibiyar matarshi,nasan ni mashayine kuma mazinaci amman wllh niba makashi bane ba shiyasa nazo nagaya miki wannan maganar domin na wanke kaina agurin ki,"dakyar tasamu tamike har tana kokarin faduwa yay kamar zetareta wani irin matsiyacin kallon data watsamai yasa yay baya yana rike kanshi kofa tanufa tabude tana nuna mai hanya, Tace "get out" Karasowa yay jiki asanyaye kafin yakalleta dayazo daf da ita kamar rada rada yace mata "Ju...nior" cikin yar rawar murya,jin ya ambaci sunan danta yasa tazaro ido tana kallansa cikeda rudewa take fadin "ku...kune koh jalal kafadamin inda dana yake dan sanka da Allah daya halicceka" Takarasa tana fashewa da kuka Cikeda tausayi yake fadin "Yana cikin palace dinnan haryanzun sbd antoshe duk wata kofa tafita dashi,tsaron da mai Martaba yabawa palace dinnan tun bayan rasuwar EHSAAS babu wanda ze iya fitada crown prince batareda ansani ba,peace innace miki banine nadau junior bazaki yardaba," Dasauri tashiga rawar murya tana fadin "wllh zanyarda I won't say anything,bazan fadawa kowaba kokai ka daukeshi dan Allah kadawo min da dana takarasa tana durkushewa agabansa," Shima tsugunnawa yay agabanta yana fadin "She's very dangerous tadade a underground tunnel na palace dinnan batareda kowa yasani ba,peace is our mom ko ince mom din Erfan,uwar data raineni tun bayan rasuwar tawa mahaifiyar,is the great exiled Queen nadra" Awani irin gigice peace tadago tana fadin "Nadraaaaa"numfashinta na kokarin daukewa don haryanzun bata manta kalar wahala da azabar datasha lokacin da Queen nadra taso kasheta ba "My baby,my innocent child, wayyo Allah na me nai mata I've always being very careful and mindful of what I do tunda nashigo gidannan bantaba fada dakowa na meyasa suka tsaneni meyasa basa sona" Takarasa tana shashsheka, Jay yace "Uwace agareni peace bazan iya juya mata baya ba,kuma zanyi fito na fito da duk wanda yajuya mata baya,inkinason ki karbi junior agurinta karki fadawa kowa koda Fulani ce kuwa wannan maganar da muka tattauna dake tazama sirri karfe shabiyu na dare nayau, disguise yourself as a maid kada kibari kowa yasan kinfito,kisameni abayan garden zamuje mukarboshi we should beg her maybe tabaki shi batareda tacutar dashiba tunda EHSAAS ne makiyinsu bawai junior ba" Islam dagowa tai tana kokarin karantar fuskar jalal amman takasa saboda yajja yake nuna yana tareda ita, da kuma labarin danta na raye daya kawo mata cikeda wayo take fadin "Tayaya zan yarda junior na hannunta,kar naje wani trap kashiryamin,kuma danmeyasa bazan fadawa Fulani ko mai Martaba ba,sune kadai zasu iya maganinta" Jay girgiza kai yashiga yi yana fadin "she's dangerous peace ita uwace agareni, I know wacece ita, peace da manyan aljanu take aiki wllh ze iya yiwuwa duk wanda zeje gurinnan bazema gantaba harse in ita taso taganshi kuma inkikai hakan zakiyi provoking dinta tacutar da danki kinason hakan?" Girgiza kai tashiga yi bakinta narawa sbd tarasa ma me zatace tarasa dawa zata yarda dakuma waye bazata yarda ba yakalleta yana fadin "12 pm sharp karki wuce lokacin indai kinason ganin junior araye" Jinjina kai ta shigayi tana binsa da kallo har yamike yafice akofar dakin yanajin taturo kofar kasa karasa fitowa yay yacije lips yana fadi "yes, finally yau Allah zekai damo ga harawa" Wani dan iskan murmushi yashigayi yana fadin "Jay your the best".

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote. [16/05, 21:04] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.