EHSAAS

Chapter 23

by @fatoumspassion

Tajuddeen qure paa yay da ido ganin yadda gaba daya jikinsa yake rawa ya firgice ya gigice lokaci guda ganin sunan EHSAAS da inda yafito. dakyar paa ya iya controlling shock dinsa yasaita kansa yana rufe file din gaba daya don yaga abinda yake bukatar ya gani din,Yadago yana kallon Taj yana jiran karin bayani Taj gyara zama yay yana fadin "Paa fatan dai komai lpy,naga kamar karasa nutsuwa lokacin dakaga sunan EHSAAS," jinjina kai yay yana fadin "is a long story tajuddeen amman dai bantaba sanin cewar yaron king nashwan ya girma yakai har haka," taj cikin dan mamaki yake fadin "kasan king NASHWAN of NURISTAN ne?" girgiza kai yay yana fadin "bashi nasani ba matarsa nasani," cikin dan mamaki taj yace "matarsa kuma,wacce daga ciki?" memakon ya bashi amsa se paa yashiga tambayarsa wacece mahaifiyar EHSAAS cikin matan king NASHWAN din, Taj cikin mamaki yace "Fulani hajar of borno," cije labe yaga paa yayi kafin ya saki wani murmushi yana kallon Taj yace mai "yanzun shi EHSAAS din menene yafito dashi daga NURISTAN," dan jinkiri Taj yay dukda kasancewarsa jami'in tsaro amman yanayin paa din yagama rudashi yace "alabarin dana samu dai wani taron sirri yazo can wani kauyen dake wajen Abuja,kuma tarone wanda manya manyan masu sarauta suke gudanarwa aka'ida king NASHWAN ke zuwa,amman wannan shekarar kawai se yace EHSAAS dinne ze wakilce shi,kuma kasan yadda masu sarauta keda tarin makiya," paa yace "yanzun sunacan sunata nemansa kenan" dan girgiza kai taj yay yana miko masa jaridar NURISTAN ta waccan watan yace "kaga anan dai sunyi official sanarwar mutuwarshi, sbd ance antsinta gawarsa ta kone," cikeda mamaki paa yake fadin "gawa kuma, bayan gashi yana rayuwa cikin gidanmu," Taj yace "abinda nakasa ganewa kenan cikin dayan biyu kodai makiyan da sukai yunkurin kashesa sunsan yana rayene sukai haka ko kuma suma kansu sunyi tinanin ya mutune don su gamsar da jama'a hakan sukace antsinta gawarsa takone,banajin idan king NASHWAN yasan danshi na raye zebarshi yacigaba da zama anan," jinjina kai paa yay yana fadin "tajuddeen kana ganin har yanzun akwai masu bibiyarsa?" yace "tabbas baza arasaba don dai baya fitane kawai you should be careful with him harse mun mikasa zuwa NURISTAN cikin aminci,idan babu damuwa nizan sanarda shugabanmu maganar nan inyaso hukumar kasa da kasa setai magana da NURISTAN su se su aiko da mutanensu don su tafi dashi cikin aminci," girgiza kai paa yay yana fadin "befa san inda kansa yakeba tayaya kake tinanin zamu maidashi, insukai kokarin kara cutar dashi fa," anitse taj yacema paa "namaka alkawari ba wanda ze cutar dashi kuma maganar danake maka zamansa anan din kamar cutace agareshi domin babu wanda yake awaccan rayuwar tasa don haka ba lallai yataba tina komai dangane da rayuwarsa tabaya ba," jinjin kai paa yay kafin yagyara zama cikeda dabara sbd yasan kota tsiya kota tsiya tsiya baze taba bari su tafi da EHSAAS ba tareda yacika burinsa akansa ba yana ganin kamar wata damace tazo masa har cikin gida, daman Allah ba azzalumin bawanshi bane,sungama boye dannan tun yana karami suna kareshi daga makiyansu da magauta yau Allah yakawo masa shi asama don haka dole yay amfani da damarsa yadama tayajja bashine ze nemi NASHWAN ba NASHWAN me zenemeshi yaraya acikin zuciyarsa amman afili se yace da Taj "EHSAAS ba mutum ne gama gari ba da za'a iya barin sa a hannun hukumar kasa da kasa, Sannan mu ba za mu iya mayar da shi ga su iyayensa ba... har sai mun tabbatar da cikakken tsaronsa, kuma ni so samu yadawo cikin hayyacinsa" Taj ya zaro ido yay domin yasan hadarin dake tattare da barin prince EHSAAS ahannunsu amman kuma baze iya musu da paa ba yasan baze taba yin wani abu daze cutatar da EHSAAS ba yace "So, what do we do now?" "Yanzu dai... zai cigaba da zama anan, a matsayin guest kamar yajja yake, kuma a hankali... zamu shirya komai,ze cigaba da shan magani, sannan Mehtav zata taimaka wajen kula da shi" Taj gyaɗa kai kawai yai,dukda zuciyarta bataso hakan ba yace "Just be careful Paa. Kingdoms like Nuristan don't joke with their heirs. I have a feeling someone out there is already searching for him, musamman criminals din karku barshi yana fita" Paa kara kallon hoton EHSAAS da ke cikin file din yay, sannan ya ce "Karka damu tajuddeen in sha Allah zan kuladashi sosai,nagode da dukkanin taimakon dakaimin kuma inason maganar nan tatsaya a iya nida kai koh Mehtav banason tasani" Dan jinjina kai kawai Taj yay batareda yasan dalilin paa naboye hakan ba.

Sallamar Mehtav sukaji, dasauri paa ya daura pillow saman file din EHSAAS yana murmushi ya amsa. tunda tashigo Taj yazuba mata ido kamar ya cinyeta yajima beganta ba seyaga tagirma ta kara kyau tray din dake hannayenta ta ajje tana karasawa gefen taj tana murmushi take fadin "sannu da zuwa yaya Taj ashe rai kangarai baka nemanmu kaboye," tafada cikin tsokana murmushi yay mata yana fadin "kinsan yanayin aikin namune se ahankali amman yanzun ba gashi kinganni nazo ba," dan hararar wasa tawatsa mishi tana fadin "da yake paa yadawo ba shine ake ganinka" murmushi ya sakar mata yana fadin "da yake kekuma bakya afuwa Sarkin complain ceke ko," dariya tai tana komawa ta zuba mishi juice mai sanyi a cup tana mika mai still dariya takeyi kamar gonar auduga don tanada Fara's sosai yashiga tambayarta ya suke? ina mutuniyar tashi? tace " aitana ciki bata jika bane danasan yanzun tuni ta taho nan," yace "najima paa yace tamin kishiya ai," dan sunkuyar dakai Mehtav tai tana kallon paa before tace "eh amman aikasan tsakanin ka da Abeey bata baci kar aji kanku mana," murmushi yay yana kurbar lemon ahankali suka shiga hirar zumunci irinna andade ba'a gamunnan ba. sunjima suna hira kafin paa yace suje cikin gida anan suka barshi suka shige cikin gidan tareda Taj sa'ar ta daya Islam ya kwanta barcin safe,Abeey kawai suka tarar datai farincikin ganin Taj kamar ta hadiyesa don suna da mugun son mutane suna so suga anzo gidansu sudai, kasancewar sunyi nesa da yan uwa da abokan arziki yasa suke dadewa basuga kowaba,bayan sunkaishi yagaida innarsu aka shiga hira, rabin labarin duk na Islam ne ake bashi seda ya tambaya waye islam Mehtav tagaya mishi sannan ya gane ai prince EHSAAS ne,kamar yace musu ba sunanshi hakaba amman dai ya tina yaddaa sukaida paa se kawai yakyalesu. Abeey ta shiga dakin EHSAAS yakai so uku tana fitowa taga be tashi ba har lokacin tafiyar Taj yay saboda yanayin aikinsa sallama yay musu kawai,tareda pa suka fice agidan gaba daya.

Afirgice ta tashi, wata irin xufa ce take karyo mata tana jin kirjinta yana nauyi vividly take tina kalar mafarkin datai,ta rintse ido tana kallon fuskar EHSAAS data gani yana mata murmushi yana daga mata hannun kamar meyi mata bye bye yana baya baya da ita,fashewa da kuka tai tana rike kirjinta dake mata zafi kamar garwashi haka takeji what does this mean? yamata bye bye dagaske kenan yatafi yabarta bazata sake ganinsa ba. jitai kamar numfashinta yana neman daukewa saboda zafin da kirjin ta yake mata kawai ta mike tana kallon gadon yara da junior ke kwance yana barcinsa hankali kwance. toilet tanufa kawai ta sakarma kanta ruwan sanyi tanajin zafin kamar karuwa yakeyi hawaye takeyi babu ihu ko gunji ko kadan saboda ita kadai takejin me take ji da kalar kewarsa datai arayuwa babu wanda zata iyawa explaining ya gane, she's now just leaving sbd yaronta tasan cewa badan junior ba batada karfin zuciyar iya tinkarar rayuwar da babu EHSAAS acikinta batasan adadin lokutan data diba cikin ruwanba kafin ta kashe ruwan ahankali tai normal wanka tai brush tai alwala tafito ganin lokacin sallar asubah ze wuce yasa agurguje ta tayar da sallah, tai sallarta cikin nutsuwa tana tina hukuncin da Fulani tayanke jiya itakanta zuciyarta tafi aminta data bar NURISTAN din duk kuwa da sanin cewar mutan borno bakowa yay accepting dintaba har yau,hakanne yasa EHSAAS betaba kaita gurinsu ba ita tunda takema ko inda Nigeria din take bata taba zuwa ba, balle borno.

bayan ta kammala addu'a tajawo wayarta,kan number mahaifiyarta ta tsaya, tana tinanin takira ko karta kira,se kawai tai clicking kamar yadda tai expecting line busy aketa gaya mata alamun ta rigada tayi blocking layinnan nata shima batasan sau nawa ta sanja layi ta kirata ba amman duk sanda taji itace katse wa takeyi tai blocking batasan wana abu mahaifinta yay wa mahaifiyarta, ko wace kalar barazana yay mata haka ya rabasu ba, amman dai abu daya data sani shine tabbas mamanta ba asan ranta take hakaba,zuciyarta keta ingizata ta kirawo Abraham koshi zata sameshi koba komai mahaifinta ne yanzun da babu EHSAAS kila ya jikanta yabarta takusancesu sbd tasan duk duniya susu kadaine jininta, se ayanzun take jin inama taji maganar EHSAAS tun wancan lokacin tayi making peace da mahaifinta duk korar daze mata tacigaba da zuwa da ayanzun bazata rasa jininta wanda ze zame mata makama arayuwa ba. number Abraham din ta kira tanata ringing be daga ba harta katse tasake kira awannan karon bata jima tana ringing dinba ya daga yana fadin hello! hello! toshe bakinta tai kuka na zuwar mata amman tahadiye tana rasa ta inda zatai magana, hello! tasake ji Abraham yay magana yana tambayar waye cikin wannan dakakkiyar muryar tashi me ban tsoro data sanshi dashi,muryarta na rawa tashiga fadin "sir....sir it's me," dan jim yay kafin yace who? Anitse,tasan fa Sarai yagane muryarta amman se tace da rawar murya "peace Sir, waye peace?" taji yafada irin be.santan nan ba,tace "sir I'm sorry pls ka yafemin is peace your daughter," cikin fada yashiga fadin "karki sake kirana, peace yata ta dade da mutuwa karki kuma kiran layinnan imba hakaba ranki zeyi mummunar baci," "sir I'm sorry" tashiga rokonshi,yace "for what bansan ki ba a'ah kawai mutane su ringa kiranka suna maganganun banza" ya karasa yana kashewa,sosai taji dacin abinda yay saboda tasan sarai yasan itadince,tashiga kokarin sake kira setaga lin busy alamar shima yaayi blocking dinta.

tadade agurin tana rasa inda rayuwarta ta dosa, jitai ana knocking kofar dakinta da sauri ta dago kai tana goge hawayen dake fuskarta don tasan baze wuce Fulani ba,kwankwasa kofar ta karayi ahankali kafin tabude tashigo rikeda chazbaharta ahannu alamar itama bata jima da gama lazumi ba,tace "yata kintashi?" jinjina mata kai tashiga yi ta karasa ta rungume ta tana fadin "barka da safiya maama na abar alfahari na," "barkanki dai diyata fatan kintashi lpy," "alhmdlh maama na kefa?" tace "mungode Allah Islam, ya kuka kwana?" tafada tana karasawa gurin gadon junior tai tana fadin "enyee mutumin yanata barci be tashiba" ta shafa kanshi tashiga karanto mai addu'o'in neman tsari iri iri Islam tana kallonsu don sun birgeta sosai. Fulani ta kammala tashafe mishi jikinsa dashi har lokacin be tashi ba,tadago tana fadin "kinsan saraki ne ba'a tashinsa abarci, Yayo gadon barcin me sunan da" dan murmushi kawai Islam din tayi, wanda zaka fi kiransa dame ciwo tana tina irin barcin EHSAAS wanda bako yaushe yakeyi ba amman inyafara duk sanda tai gigin tashinsa tohm se sunyi fada kuma wuni zeyi yana daure fuska yana mitar tashinsa datai, Fulani zama tai a gefen gadonta tanawa Islam alamar tazo ta zauna ganin kamar tinani takeyi, karasowa tai ta zauna agefenta,kama hannunta Fulani tai tana fadin "nagode sosai da duk abinda ki kaimana arayuwarmu Islam kama daga auren EHSAAS da kikai,giving up family dinki for him, everything naki kin sadaukar saboda shi soyayyarki agareshi babu macen da zata iya masa ita har abada, Islam har rayuwarki kinsaka cikin hatsari saboda shi harta da abinci baki yarda yaci batareda ke kinci ba sbd incutarwa ce tafara zuwa gareki kafin shi wanda koni dana haifeshi bantaba yimai irin wannan gatanba sedai nasaka bayi suyi, duk cuzgunawar da ake miki acikin gidannan ina sane dashi da hakurin ki duk ina kallo, nasan cewar ke din kincika matar rufin asiri gaba da baya, Islam kisani banida diya mace da ina da diya mace zanso takasance tamkarki,kuma har abada ke yatace duniya da lahira,duk abubuwannan dake faruwa damu jarrabawace daga ubangiji Allah yana gwada imaninmu ne ya dauke EHSAAS daga cikin rayuwarmu sbd yafimu kaunarsa inaso kisaka aranki EHSAAS yana gurinda yafi dacewa ya kasance kicigaba da rayuwarki kamar kowace mace zakije borno cikin yan uwana da ahalina nasan wasu nasonki wasu kuma basa sonki amman nasan bazasu taba cutatar dakeba, don haka ina me rokon ki kisaki jikinki kibar rayuwar dakikai anan tatsaya anan,be happy kinji munada yan mata sa'annin ki iri iri, I'm sure you'll enjoy being there," jinjina kai Islam tai tana fadin "thank you Maama," Fulani murmushi tai tana shafa kanta kafin tadan nisa tace "Majlis Al Adl xamu wuce za'ai first hearing wanda gaba daya NURISTAN zasu kasance agurin don ganin kalar hukuncin d mai martaba ze yanke, Karkice zakizo kinji,kizauna anan ki huta ki kula da junior in sha Allah justice shall be served muna dawowa zamu fara shirin tafiyarki ba zanso kiga abinda ze wakana acan gurin ba," dan jim Islam tai saboda duk duniya babu abinda take kauna irin taga an hukunta mutanen dasuka zalinci EHSAAS da ita da danta amman kuma bazata iya musu da Fulani ba tasan tafita hikima da tace kartaje din kodan saboda lafiyar danta, "ko kinaso kije?" Fulani ta tambayi Islam dake bata iya karya ba seta jinjina kai alamar eh murmushi Fulani tai kafin tace "tohm ni zan zauna tareda junior ke kije kawai,sbd kinsan bazamu iya barinsa da kowaba se mu biyu kuma kakar ku ma nayi nayi da ita tazauna tacemin se taje taga yajja za'a hukunta nadra kinsan rigimarta," Islam ta danji ba dadi saboda tasan kila Fulani ma nason taga yadda za'a hukunta wanda suka zalinci danta da sauri tace "maama kije kawai zan zauna in lura dashi bakomai Allah," girgiza kai Fulani tai tana fadin "nasan kinason zuwa don haka kije kawai babu damuwa kawai I insist....." jinjina kai islam tai tana rungume Fulani sbd tana jinta har cikin zuciyarta. Daidai nan sukaji motsin junior Fulani tajuya tana fadin "ya.tashi," murmushi Islam tai ta karasa tana dakkoshi se ya mutsa farar fuskar sa yake yana lakwasa hannaye yana kokarin sawa abaki kamar yadda yara sukeyi ta mikawa Fulani shi ta karbeshi tana dariya tashiga yi mishi wasa tana lakace mai hanci "wai wa yabiyo itadai hancinta ba irin wannan baneba," shikuma ya kure Fulani da ido irin yanajin metake cewa dinnan Islam kawai tatsaya tana kallonsu cikeda sha'awa don kana kallonsu kasan sun hada jini. wannan kenan.

Majlis Al Adl cike take makil da mutanen NURISTAN maza da mata manya da yara tsofaffi da mata domin tunjiya aka yada shelar shari'ar da za'a gabatar ayaudin bayan zaman sirri da mai martaba yay da counsel dinsa baki daya da doguwar shari'ar da akayi jiya acourt tacikin gida shiyasa aka yanke shawarar yankewa masu laifin hukunci a Majlis Al Adl.

wata katafariyar harabar fada da ke tsakiyar birni, inda tagwayen statue na dokuna wanda akayi da zallar zinare ke tsaye agurin manya manya agefen karagar sarautar NURISTAN. Babu abinda kakeji ayaudin se Ƙarar ganguna da bugun kaho da yacika sararin samaniya. Al'umma na qara taruwa tako ina, masu ruwa da tsaki, malamai,manyan dattawan qasa, da talakawan da suka zo kallon irin adalcin da basu taɓa gani ba cikin shekaru masu yawa,domin indai akace maka a Majlis Al Adl za'a yanke maka hukunci tohm taka takare ba karamin laifi kaiba.

Manyan manyan motoci ta manyan mutane da jami'an tsaro sekai kawo suke sakamakon manyan kasa daketa taruwa yan jarida rututu dako ina suna daukar shirin ana watsawa live,domin ansan kalar adalcin sarki NASHWAN.

Matan kasar NURISTAN matane masu daraja da ba'a bari camera ta haskasu bare ta ya dasu a idon duniya, shiyasa duk inda zasuje irin wadannan tarukan fuskarsu arufe take sinkif da wani nikab mai matukar kyau wanda babu ma me amfani dashi akasar se yayan sarauta.

Da lambar motocin su da ma'aikatansu ake gane zuwan kowacce daga cikinsu kuma tana sauka jami'an tsaro zasu da baibayeta harseta shiga can cikin ainahin court din can sama inda akai musu hawa na musamman tayadda zasu kalli shari'ar cikin aminci batareda kowa ya gansu ba.

Seda kowa yazo sannan kafin zuwan mai Martaba sannan motocin Princess Islam suka Karaso shi kansa security din da aka bata na musamman ne, da motocin prince take amfanu hakan yasa taja hankalin Al umma sosai, su nata ambatar sunanta saboda alheran mijinta agaresu se addu'o'i suke mata ana saka mata albarka tunma kafin tafito daga motar.

Lokacin data fito daga motar tsayuwarta kaɗai ya wadatar da mutum da tabbacin cewa ba kowace irin mace bace gabanka saboda yanayin siffarta da haibarta da kwarjininta macece wacca ta cika mace me nutsuwa,babu abinda suke gani ajikinta kofuskarta face kyawawan idanuwanta masu matukar kyau da daukar hankalin mai kallo.

domin a NURISTAN din inba yan cikin gida ba babu wanda ze iya cemaka yasan ainahin fuskarta saboda yadda dokar NURISTAN take akan matansu. Amman shigar dake jikinta kadai ta rikita al ummar dake gurin bama iya talakawa ba harda masu mulki sbd shigace mai girma da daraja kayane wanda aka kashe millions of dollars gurin yinsu asalin kayan sarautar NURISTAN ne tunna zamanin farko wanda akayisu da zare na alfarma wanda aka kera shi daga raw silk mai launin jade emerald, wanda ke bayyana asalinta na daula da launin aljannar da ke kewayen tsaunukan Nuristan.

An ɗinka kayan daga hannun manyan masassaƙa, kuma kowane ɗinki na dauke da threadwork na gwal tsantsa da aka ɗora lu'u lu'u masu launin ruwa da zinare a tsakiyarsu.

Gyalen wanda ya lullube kanta da bayanta har kasa, an kawata shi da zare na azurfa da gwala-gwalai da aka jera a gefensa. Ya rufe kanta da kyau. Wuyanta na ɗauke da wata sarka mai tsawon gaske da aka qera da zinare zalla, wanda adanananniyace tun zamanin sarki EHSAAS. asalinta ta mahaifiyarsa ce, tabawa sirikarta Queen Aisha(uwar soro)itakuma tabawa tata sirikar Fulani,itakuma tai passing dinta zuwa ga princess Islam domin babu macen da take iya kai hannunta kan wannan sarkar har seta haifawa NURISTAN magaji, sarkace datake symbolising cewar wacca take dauke da ita zata zama Queen mother. Hannayenta dauke yake zobuna guda huɗu masu nauyin tarihi da mai Martaba ne dakanshi ya mallaka mata su amatsayin kyautar aurenta awancan lokacin zobunane masu daraja da ko yayan sarki bakowane yake mallakar irinsaba. Se wasu manyan manyan diamond bracelet wanda kyautace ta musamman data mijinta shikuma.

Takalmanta kuwa, An ɗinka su ne daga fata na musamman daga dabbobin tsauni na Nuristan,jikinsu an jera wasu duwatsun gwal da pearls masu daraja.

Dakyar jami'an tsaro suka kakkare jama'ar dake kokarin ganin sun isa gareta ta kowace hanya harta shige cikin ainahin court din. shigarta ahakan ta tafasa zuciyoyin masu mata hassada dayawa domin ko kalar kallon dataga mai babban daki tana mata tundaga kasa har sama seda taji ajikinta yes sako ya isa zuwa gurin da ake bukata. gefen gimbiya mimah takarasa inda aka tanadar ma fualni kujerarta tamusamman batare da takalli kowaba tai zamanta tanade kafa daya kan daya batareda ta juya ta gaida kowa daga cikin su ba,saboda fulanin ce tabata umarnin zama a mazauninta,kuma hakan yakara tunzura zukatan wasu daga cikin manyan dasuk is ganin kamar ita yarinyace karama batakai tahada kafada da kafada dasu ba kuma ita bakowan kowa baceba, banda manyan dattawan data hadu dasu afarko ta gaisar babu wanda ta daga kai takalla sema ita da ake zuwa ana kawowa gaisuwa burin kowa daga cikinsu yasamu gurin zama azuciyarta kallonsu kawai takeyi. mimah jitai haushin Islam din ya tirnike ta cikeda bariki tanason taga kayan jikinta na gaskenne kokuwa na karyane da aka kwafo a kasar waje,dafa kafadarta tai cikin wasa tashiga murza yadin tana fadin "kimfa yi kyau yau giwar yarima matacce," dan dago kai tai suka hada ido sarai taga abinda takeyi tasa hannayenta mai daukeda zoben gadon gidansu da aka bata tadan janye hannayen mimah tana fadin "kuma uwar yarima rayayye me jiran gado point of correction" tafada tana sakar mata dan iskar murmushin daya kusa rusa rugujajjiyar zuciyar mimah,tashiga kallon hannayenta tana tina irin yadda takewa babanta naci akan zobunan nan be bata ba se matar EHSAAS yabawa itada ba yarshi ba,idonta yakasa dena kallon zobunan,kamar tafashe da kuka takeji, Islam ta kalli yadda take kallon zobunan tace "oh gimbiya mimah kodai baki ganesu bane kinga wannan ma?" tadan matsar da mayafinta tana nuna mata dankwaleliyar sarkar dake shimfide asaman tsayayyun kirjinta take fadin "sunyi kyau kuwa?" tana dage mata gira daya dayasa mimah saurin kokarin dafa sarkar kallon kyankyamin da islam take mata yasa takasa kai hannayenta jikinta.

Islam ta dauke kai tana kallon cikin babbar fadar court inda aka sanar da zuwan mai Martaba sarki NASHWAN bin EHSAAS gurin shiru ya dauka gaba daya,dake an rigada anshigo da masu laifin,maga takarda tashi yay yashiga karanto tuhume tuhumen da ake musu kamar haka.

"Ana tuhumar tsohuwar sarauniya Nadra, wacca aka kora daga masarautar NURISTAN shekaru da suka wuce saboda babban laifin data aikata na batawa yarima suna, tareda bada tsatstsauran hukunci kan cewa duk sanda aka ganta a NURISTAN tadawo a kasheta har lahira, ankamata ta dawo ta boyayyen hanya tare da taimakon galadima na NURISTAN Jalaluddeen bin Ehsaas, ba tareda sanin masarauta ba suna zaune a underground tunnel dame Martaba yadade da bayar da umarni ga galadima arufeshi ashe bebi umarnin yarufe dinba,sannan Sun haɗa kai da Maisoon karamar jikarta kuma diyar wazirin NURISTAN, da kuma wasu jakadu daga fadar giwar mai Martaba Fulani hajar da wasu ma'aikatan waje suka sace Yarima Ehsaas bin Ehsaas bin NASHWAN bin Ehsaas na uku, Baya ga haka, Jalaluddeen ya yi ƙoƙarin yi wa Gimbiya Islam fyaɗe."

Nan kotun tadauki shiru ana kallon masu laifin kowa na tsine musu acikin zuciyarsa,sunyi wujiga wujiga musamman Queen nadra da take tsohuwa tanajin kamar ta kashe kanta da irin wannan tozarcin da NASHWAN ke mata agabaki dayan kasar NURISTAN.

waziri da shigowarsa kasar kenan yasamu wannan mummunan labari kasa karasa shiga kotun yay domin baze iya shiga ciki yaga abinda za'ai wa mahaifiyarsa ba tabbas yasan tasu takare shishi kadaine ze iya daukar musu fansa don haka baze shigaba ballantana zuciya ta dibeshi yayi wani yunkurin dazesa asirinsa yatonu. Juyawa yay don yasan jay ze iya tona mai asiri don haka wannan ce damarsa tabarin kasar NURISTAN gaba daya kuma ta hanyar nemo EHSAAS a Abuja ya kasheshi ya aikoma da NASHWAN kansane kadai ze bashi kwanciyar hankalin da yake bukata yanzun.

Daga cikin court kowa shiru yay yana jiran jin abinda mai martaba zece bayan shirun dayay cikeda nutsuwa da kamala da dattijan taka da izza irin ta mulki ya kalli daya bayan daya daga cikinsu,dan uwansa na jini mafi soyuwa agareshi da yar dan uwansa da kuma matar mahaifinsa sun hada kai donsu cutar da jikansa, Cikin kakkausar murya yake fadin "Nuristan bata taɓa barin zalinci ba, NURISTAN kasa ce mai adalci a koyaushe,kuma ko kai wanene,ko ke wacace, ko yaya nane,ko yan uwanane, ko abokaina ne,gurin adalci bama duba alaka tajini, idan ka saba, dole ka fuskanci hukunci,mai tsauri kamar yadda za'ai ma kowa,sbd kafin in karbi wannan kujerar Na rantse da Allah, zan tsaya akan gaskiya."

Gurin tsit yay sbd yadda lafuzzan king NASHWAN ya ratsa zukatansu, Mai Martaba ya bada umarnin ashigo da ma'aikatan dasuka kamasu suna kan wannan aikin. daya bayan daya harda su Aman dasu turaki suka shigo suka bada shaida kan duk abinda yafaru aranar wanda ya girgiza al ummar NURISTAN baki daya harta da allurar kanjamau da nadra tai kokarin yima yarima seda aka fada,peace da suke can sama, aka kaimata mic ta bada tata shaidar,da jama'a suka ringa Allah wadai da halayen su jalal da Queen nadra da Maisoon.

Bayan da aka gamane mai Martaba ya kallesu daya bayan daya tareda basu damar kare kansu, Maisoon aka fara tambayar abinda yafaru cikeda rawar murya tashiga rokon king NASHWAN tana cemasa "yay mata rai ta rantse da Allah sharrin kakarta ne ita ta sakata komai ita batasan ma andakko shi ba seda taje tagansa shine tace ba shi yakamata adakko ba ita ga barta da iyayensa takeyi wllh kakarta ce tashirya komai" Queen nadra kallon takaici da tsantsar tsana tashiga yiwa maisoon ganin yadda take tona musu sirrika afaifai sbd tsoro,juyin duniya akai da queen Nadra taki cewa uffan waiko taroki sassauci ko wani abu taki, jakadiyya kasa hada ido da mai martaba tai domin ita kanta tarasa dalilin dayasa tai hakan ana tambayarta kawai jay tanuna tace "shine yasaka kuma ita batasan dalilin dayasa tai hakanba," jay da zafin kai da taurin zuciya yadago yana kallon King NASHWAN,yace "nine na sakata kuma ko yau kasake ni sena kara sakata domin nasan karkari kace zaka kasheni kamar yadda ka kashe mahaifiyata, kaidin bakowa bane face makashi azzalumin sarki da yake boyewa abayan adalci yana cuzgunawar Al'umma" wani irin bugu da wani gardin bafade yakai masa yasa ya hantsila tabaya yana buguwa da kasa hancinsa ya fashe ya dago yana kallon king nashwan dake kallonsa shima bafadan takobi yasa awiyansa yana fadin "kalma daya tak mara dadi ka kara fada dangane da adalin sarkinmu sena fille kanka," kallon bafaden yake wanda ada kallon inda yake be isa yay ba wai yau shine yake dukansa lallaima. Gyaran murya king nashwan yay yana kallon jalal,cikin zafin rai yake fadin "Kabani kunya Jalaluddeen,Ka watsar da zumunci, ka wulakanta amana, ka nemi ƙasƙantar da matar Yarima, yarima tamkar danka ne na cikin ka sbd na dauka dana dankane, kuma duk wanda yay yunkurin wulakanta iyalin yarima tamkar NURISTAN baki daya ya wulakanta,sannan kahada baki gurin sace karamin yarima mai jiran gado don haka dokar kasa bazata kyaleka ba,ko keta haddin mace da kai yunkurin yi kadai ya cancanta ahukunta ka hukunci mai tsanani wanda shine hukuncin kisa ta hanyar rataya ba Kace ni makashi bane ayau bayan karbar azaba mai tsanani tawata shida agidan kaso,ni sarkin NURISTAN na goma sha uku NASHWAN bin Ehsaas na yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya," gaba daya fadar rikicewa tai ana fadin "Allahu akbar" jay yadago agigice yana kallon dan uwan nashi da idonsa yay jajir yay yasan ba.wasa atattare dashi rawa jikinsa ya.dauka sbd yasan idan har NASHWAN ya furta hukunci agaban jama'a babu yadda za'ai yakoma yacanza sbd kalar murdadden ra'ayin da yake dashi,yajuya ga Queen Nadra cikin kasaita yake fadin "Ke kuma, Nadra, mun kore ki daga wannan ƙasa bisa babban laifin sharri abaya, Kin dawo ta boyayyar hanya ta boyayyar hanya,sannan kika kara wani laifin kan wanda kikai abaya kuka sace Yariman wannan kasar,wannan wace iriyar wautace da rashin lissafi,bazan cemiki komaiba illa Hukuncinki yana nan, kamar yadda muka ambata abaya duk sanda akasakd ganinki a NURISTAN za'a kashe ki a bainar jama'a" Kabbara gurin ya dauka domin daman ka'idar NURISTAN duk sanda aka ambata hukunci akanyi kabbara don nuna goyon bayansu akan sarkinsu.

Maisoon ganin hukuncin kisa kawai king NASHWAN yake yankewa yasa ta durkushe kan gwiwo yinta hannunta bibbiyu cikin roko take fadin "dan girman Allah mai Martaba ka te makeni aimin afuwa na tuba nabi Allah nabika wllh bazan sakeba kaimin rai karka kasheni bannason inmutu,wllh sune suke zigani suke cewa zansamu EHSAAS zandau fansata akan duk abinda yaymin nakin aurena dayay wancan lokacin, ka temakamin," Girgiza kai king NASHWAN yay yana kallonta seda tagama sambatunta sannan yace "Maisoon, kin bi zigar datazata kaiki ga halakar, kin zubar da mutuncinki da zuriyarmu. Za ki kare rayuwarki har abada agidan yari tareda horo mai tsanani,ita kuma jakadiyya da sauran wadan da suka temaka musu gurin sace yarima bada son ransu ba mun yanke musu shekara goma goma, agidan yari tareda horo mai tsanani suma,"

kabbara aka shigayi ana salati, dogarai suka karasa suna kakkama masu laifin fadawa suka tashi suna bude manya manyan rigunansu don kare mai Martaba ya mike yasakko yana kokarin fita ta kofar da yashigo. "NASHWAN bani kadai bane ba wannan wana irin rashin adalcine Erfan, kujerar dakake kai bataka bace tashice,shine babban dan mahaifinmu shiyay deserving yazama sarki ni tayashi adawa nake yi, nace Erfan fa shi bazaka ce komai akansaba tohm bari kaji ingaya maka shine ya kashe danka EHSAAS danka daya aduniya gudan jininka kabinciki Erfan tareda......." wukar da aka yanke masa maqogaransa dashine ya sanya yakasa karasa abinda yake niyyar fada. Abin kamar kiftawar ido kotun ta kacame king nashwan yajuya cikin tashin hankali yana kallon inda dan uwansa jay yazube jini na kwarara a makoshinsa idonsa na farfari alamun rai na fita ajikinsa dawani irin sauri da zafin nama yay kansa fadawa suka chafke daya daga cikin dogaran daya yanka masa wiya yana muzurai yana kokarin guduwa daga gani ba acikinsu yakeba sbd kayansa sababbine fil basaja yay yashigo.

rungume jay nashwan yay ajikinsa yana fadin jalal jalal Jalal yana taba wiyansa yana kokarin tare jinin dake zuba, "nash nash nash......" jay ko sunan kasa karasawa yay rai yay halinsa gurin yadau wani tsit mai martaba ya kame agurin kamar wani statue duk jarumtarsa seda yaji wani abu yadaki kirjinsa,kamar bashine yanzun yagama yankemai hukuncin kisaba,koda ya yankemai hukuncin kisa ya bashi wata shida gidan kurkuku domin yagyara laifukansa idan yatuba,yaroki gafara, shime iya yafe masa ne. amman wanene yakeda zarar kashe masa dan uwa abainar nasi,acikin daya daga cikin kotunan musulunci da ake jidasu aduniya gaba daya bama iya NURISTAN ba. dagowa yay yana kallon yaron da baze wuce shakara ashirin aduniya ba, idanuwansa kamar garwashi ya cire takobinsa yana daurawa saman wiyan yaron, Yaron ya durkushe agurin, "waye ya aikoka?" Tambayar da king nashwan yay mishi kenan babu abinda yakeyi se zare kwala kwalan idanuwa yana kallonsu "nace zakai magana kose na yanke maka wiyanka," bude baki yay yana kokarin magana amman me? Bashida harshe,harshensa aguntule yake alamar an yanke masa shine bada dadewa ba,sauke takobin king NASHWAN yay yana kasa dakansa kawai cikin jin ciwon rasa jay dayay kawai yace "kutafi dashi," domin baida nutsuwar zuciyar hukuntashi haka sbd yasan dole akwai wanda ya aikoshi, idanuwansa suka sauka akan Queen nadra dake murmushi cikin annashuwa "take them away king NASHWAN" yafada yana wucewa,gaba daya al ummar gurin jikinsu yayi sanyi don basu taba ganin irin wannan kisan gilla kamar yadda akaiwa jay agabansu dinba, Islam kanta jikinta rawa yakeyi domin batai tsammanin zasu iya kashe jay na cikinsu makusancinsu hakaba,gaba daya kasar taji tafita aranta baki daya.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment & Vote. [22/05, 18:37] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.