EHSAAS

Chapter 24

by @fatoumspassion

Acikin garden din gidan da wani yammaci rana na shirin faɗuwa, Iskar yamma mai matukar dadi na kaɗa furannin gurin da suka zagayesu . Paa yana zaune akan daya daga cikin plastic chairs dake gurin yana karanta wani littafi, yayin da Mehtav ke gefensa tana mai bayanin yadda tai jarrabawar ta tayau din, kallon littafin yake amman gaba daya hankalinsa yana kanta yana mai sauraron duk abinda take fada masa.

Abeey ce ta fito da robar ice-cream tana ta dariya,daga cikin gida take

"Paa," ta ce tana shan ice-cream, "yaushe zaka yiwa Mehtav da Islam auren ne? Gashi can kasa yay barci yanata fushi yace baka dau maganar sa da mahimmanci ba?"

Paa ya dago kanshi ahankali yana kallonta, kafin ya ɗora littafin a gefe guda yana fadin "Hmmm... I've been thinking about that too o," yakarasa yana murmushi da yasa zuciyar Mehtav tashiga bugawa don ta dauka ze tsawatarwa da Abeey akan maganar ne,ido tadan zuba mai ganin yana cigaba da kallonta yana murmushi, ta dake tace "Paa please... not now."

Amma sai yagirgiza kai yana dariya yace "A'a, yanzu fa. Tell me Mehtav... what do you think about Islam?"

Cikin firgici da mamaki, Mehtav ta ce, "Islam? Why?"

Ya ɗan gyaɗa kai. "He's respectful, calm, has good eyes. And for someone who doesn't even remember himself... he still has kingly aura, kuma yana sonki sosai, besan komai ba se wanda zaki koya masa don haka idan kika aureshi kinga kamar kece ma kike da akalar mishi tarbiyya, se yadda kikai dashi" Yakarasa yana dan basarwa don yasan mata nason ace se yadda sukai da maza.

Abeey cikin murna take fadin "Exactly! Islam is sooo handsome! Wallahi he's better than all those your suitors, duk wanda suke cewa suna sonki babu wanda yakaishi haduwa fa"

Mehtav ta ɗan sunkuyar da kai, zuciyarta na bugawa kamar ana buga drum. She couldn't believe her father was actually suggesting it. The very man she thought would never allow her to love a man without identity was now encouraging her to consider the only one who truly made her heart restless.

Paa ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya matsa kusa da ita. "Look Mehtav... I know you well. You're my only daughter. I won't force you into anything. But I've never seen your eyes light up like they do when you're around him."

Sai ya kalleta da kyau yace "I just want to know… if he asks for your hand for real this time bawai da wasa ko barkwanci ba… would you be able to say yes?"

Mehtav ta ɗanyi kasa da idonta, dukda yadda taso basarwa amman seda wani murmushi ya bayyana akan fuskarta kafin gently ta daura hannayenta saman fuskarta cikin jin kunya, tana cewa cikin siririyar muryata, "If... he asks... I don't think I could say no."

Paa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. Abeey kuwa ta fara tsalle da murna. "Yessss! Wedding bells loading!"

Amma a cikin zuciyar Paa, wasu mugayen lissafi ne ke ƙaruwa: "Once the marriage is done... and they become one, even if he regains memory, he can never walk away from her. And the kingdom that mocked me, will call my grandson heir. Allah na, ka taimakeni wannan burin nawa yacika..."

Muryar Abeey dake ihu tai cikin gida tana kiran sunan Islam tadawo dashi daga dogon tinanin da yake.

yakalli Mehtav dase wani sunkuyar dakai takeyi agabanshi alamun kunyarsa takeji yace mata "Mehtav I'll be waiting for ra'ayin both of you akan mgnr nan, because I'm serious banason adau lokaci kan ayi abinnan," dagowa tai tana kallon paa wanda kullum lamarinsa ke bata mamaki amman kuma batason ta cika mai tambayar kwakwa kan abinda ya sanja masa ra'ayi domin me batason ace ga abinda ze kawo sanadin daze ce wannan burin nata data dade tana dannewa acikin kirjinta, Allah ya kawo mata lokacin cikarsa ta faraddaya tabarar da damarta. jinjina kai kawai tai tana mikewa kafafuwanta har rawa sukeyi tabi ta kofar da Abeey tai tashige cikin gidan.

tana isa ta tarar dashi daga shi se farar singlet da three quarter daman daga barcin yamma yatashi domin sometimes har mamakin yawan barcinsa take amman ta lura yafiyin barci da rana akan da dare be cika yin barci mai nauyi da daddareba. hada idanuwa sukai dashi wani irin kyau taga ya kara mata da cika ido idanuwansa da suka dan tasa sbd barcin dayay me tsayi looks so damn sexy, yasakar mata murmushin da yasa both dimples dinsa suka lotsa yana daga mata hannu biyu alamar takaraso gurinsu aibatasan lokacin data falfala dagudu tashige cikin dakinsu ba tana kulle kofa ta dafe kirjinta dayake bugawa takejin kamar ze faso kirjinta. tanajin duk duniya babu macen dazata kaita sa'a idan ta mallaki Islam, saman gado takarasa tana kwanciya ta rungume pillow ta lumshe ido harta fara fantasizing kalar zaman auren da zasuyi, tabakin paa dinne she will be his everything,kuma se yanda tai dashi babban farincikin ta shine indai harta auri Islam suna dai tareda Abeey don tasan paa ze iya cewa su cigaba da zama agidansu tare tunda baida gida bamashi da komai da kowa,tausayinsa taji tanayi kuma amman tayi alkawari zata zame mishi komai na rayuwa.

Ranar kiri kiri ba irin kiran da Abeey bata mata ba akan tazo suyi dinner tace ace kawai ta koshi. sbd kunyar zama table daya taji tanayi dashi tareda paa da inna,daga karshe Abeey kyaleta tai har suka kammala bata fitoba,se bayan da ta tabbatar kowa yashige ciki taga Abeey tazo tai wanka taja bargo ta kwanta tamike, don gobe Abeey nada school don haka dawuri zatai barci itama wankan tafesa.

bayan tagama tafito bayan tagame shafe jikinta da maya mayan fatarta masu matukar saka fata taushi da santsi, turarrukan ta najiki tashiga gogawa iri iri bayan ta kammala tanufi closet pants kawai tasaka tadakko wata silky night gown data tsaya mata a iya gwiwa tazira tana dakko tasamanta data kenan kamar kimono tadaura gashinta tadaure atsakiyar kannata tafito da shirin kwanciya. kwantawa tai tashiga juyi wata irin yunwa taji tanaji kawai tamike tana tsaki ita kadai tazira slippers dinta tafito ko ina duhu ankashe komai takarasa kitchen tana budewa. bata kunna fitilaba tanufi fridge tana budewa,idonta ne yasauka akan sauran cookies din da sukai da safe taciro shi tana hadowa da yoghurt mai sanyi, cikin ta har wani motsi yake tsabar yunwar dataji don ita ba mutum bace me iya jure yunwa,takulle fridge din tanufi bakin tagar kitchen din hasken dake wajen gidan ne daya haskonan kawai ya isheta tashiga cin abinta hankali kwance tana lumshe ido. takusan rabi kamar daga sama taji hannunsa kannata wanda yake rike da bottle din yoghurt din tadan juyo afirgice tana shirin kwalla ihu domin ko kadan bataji motsin shigowar mutum ba hannunsa daya daura saman bakinta ya hana ihun da take kokarin yi fitowa, tazaro idanuwanta tana kallonsa shima itan yake kallo fuskarsa adaure bama alamar wasa ko murmushi atattare da ita,ganin tanutsu idanuwanta sun rusuna ya sanya ya janye hannunsa daga jikin bakinta yana fadin "What are you doing here?"

Bakinta har dan rawa yakeyi tashiga motsasu kafin tace "uhm....ahm.....am eating," takarasa tana tura cookies daya abakinta tana kallonshi ta cikin yar fitilar da take hasko kitchen din,tabe baki taga yayi daya mugun ma kyau yana fadin "ashe gulmane anajin yunwar ake jamana aji daman Abeey tafada" yakarasa yana jan stool yazauna adaf da inda take tsaye yana kallonta,murguda mishi baki tai tana fara masa ido cikin wasa take tambayar "atleast ni banciba kaifa? what are you doing here ko kari kazo nema?" "hmmmmm" kawai yace kafin yace " Here rudy niba abinki nazo ciba, I just couldn't sleep kuma naji motsin fitowar ki shiyasa nafito," adan mama kance take kallonshi kafin tace "why can't you sleep?" yace "I just couldn't this days inna kwanta barcin dare, I suffered alot I have bad nightmares kamar akwai abubuwan dana keji namanta dasu arayuwana da wannan nightmare din yakeso ya sanar dani," Mehtav dakyar ta iya hadiye cookie din bakinta data gama taunawa tai sak tana kallonsa jikin ta na mugun mutuwa take tambayarsa "mekake gani acikin mafarkin naka?" Yace "is just so strange,I keep seeing blood… water… a sword… and then a woman crying, calling a name I can't hear. Then... I wake up, restless."

Mehtav hada kalmomin daya fada take kokarin yi amman takasa gane ma'anar abinda mafarkin ke nufi straight yace mata "Mehtav" karon farko daya kira sunanta batareda yace mata yaya ba, hannayenta yahada biyu guro guda cikin nasa yana janyota ya tsayar da ita atsakiyar kafafunshi yana fadin "is there something dana manta arayuwana dayake da mahimmanci danake bukatar sani Mehtav pls kifadamin," hawaye ne ya cika idonta sam batason tai mishi karya amman kuma tana tsoron abinda ze biiyi baya idan yasan dacewa shiba nasu bane karewa ma tsintosa sukai kuma yamanta komai acikin rayuwarsa. what if they end of losing him baki daya? girgiza kai tashiga yi tana fadin "noooooo" afili batareda tasan tayi hakan ba because no din datace na irin bazata taba bari wani abu ya sameshi ba sabanin yadda EHSAAS ya fahimta ajjiyar zuciya yay yana fadin "alhmdlh amman dai suna hunting dina sosai I think idan doctor ta sake dawowa zanfada mata ko zata bani wani taimakon haka ko" yakarasa yana dan matsa hannunta dake cikin nasa jinjina masa kai kawai tai tana mai murmushin ya qe tanajin aranta kamar she's being selfish sbd takasa fada masa gaskiyar shi wanene, "Mehtav kinyi tinani akan mgnr auren namu?" taji yajefi mata tambayar da tasa tai saurin fizge hannayenta cikin nashi tana dan ja dabaya, murmushi taga yayi yana fadin "I'm I that bad?" girgiza kai tai tana kasa iya hada ido dashi yace "fadamin meye matsalar if is not me?" Yakarasa yana nuna kanshi,dagowa tai tana kallonsa kafin gently tace "because you don't love me Islam,you just think you do" dan kallon ta yay yana yamutsa fuska kafin yace, "Abeey told me I love you. And I think… she's right."

Mehtav ta daure duk da yadda zuciyarta ke fada mata it doesn't matter even if he doesn't love her tunda dai ita tana sonshi amman se tace mai "That's the main problem ? Why do you love me? Amsar shine sbd Abeey kawai tace maka hakan seka yarda"

Shiru yadanyi yana kallonta kamar maison karanta wani abu acikin fuskarta kafin yace "is not just Abeeys ideology nima inaso, Because you're kind. You take care of me… not because you have to, but because you want to. And whenever I look at you… I see peace. I want that peace forever. With you."

Shikansa besan ya akai ya iya wadannan kalaman ba amman se jiyay kamar yataba furtasu abaya,amman ya rasa gane gawa ya furtasu din amman dake Mehtav ce agabansa tinaninsa da imaninsa gaba daya akanta yake yana binta da kallo kamar ya hadiyeta sbd yadda yake jinta aransa, jitake kamar numfashinta ze rabu da kirjinta tsabar yadda takejin kalaman nasa masu sanyi na tasiri har cikin kirjinta, takasa cemasa komai "Mehtav… will you be mine?" taji yafada yana leka fuskarta datai kasa da ita cikin tsananin jin nauyi. arude ta dago tana kallonsa ganin yadda yake magana bawasa looking very masculine and matured,batasan sanda tabashi ansa da "Yes. I'm already yours." Jitai kawai ya janyota jikinshi yana rungumewa kamar yadda yake wa Abeey yana fadin "yes yes,thank you Mehtav," vibrating sosai takeji jikinta nayi yana daukar dumi saboda yanayin da suke ciki amman se taga da alama ko ajikinsa kamar ma he doesn't have any romantic feelings towards her shiyasa yake da qumarta duk lokacin da yaga dama. jitake kmr numfashinta ze dauke kuma takasa hanashi,dan kansa ya raba hug din yana kallonta ya dago da fuskarta yana saka idonsa cikin nata yake fadin "I love you," kalmomin taji suna ratsa ta suna shigewa ko ina na jikinta ahankali tasaki wani kayataccen murmushi tana fizgewa tabi gefensa tafice akitchen din dasauri.

seda ta tabbatar ta karasa daki sannan ta dafe kirjinta tana fadin "I love you more Islam."

Ranar kusan barci tai mai mugun dadi mai dauke da mafarkai iri iri nashi da irin rayuwar da zasuyi nan gaba. Da asuba paa ya buga musu kofa bayan sun dawo daga mosque don yau makara su Mehtav din sukai duk nauyin barcin Abeey yau itace tafara tashi ta tashi Mehtav din sukai alwala sukai sallah bayan sun idar ne Abeey ta kafeta da ido don wani irin blushing taga tanayi lokacin da take addu'a which make Abeey curious tana kuwa ganin tashafa takaraso gabanta cikin sonjin gulma take fadin "Whats up? Ya Mehtav any good news naga se wani murmushi kikeyi," murmushin Mehtav ta cigaba dayi dake Abeey dince kawar sirrin nata amman tanason taja mata rai kafin tafada mata se cewa tai "sarkin gulma,baza kiji ba," dasauri Abeey ta rike hannunta tana fadin "pls haba aikinsan nidake batta baci I promise bazan fadawa kowaba not even Islam," Mehtav dariya tai jin ance Islam yasa annashuwar fuskarta takaru nan take Abeey tadau haske tana fadin "is it him? meya faru,danai barci wani abin yafaru ne tell me pls..." tafada cikeda zaquwa don tanason taji labarin.

Mehtav cikeda shan kamshi take fadin "sirrin mune ni dashi baza kiji ba,ai kuma in kunayi bakwa sani aciki," dasauri Abeey tamike,domin Abeey tasan yadda takesa Mehtav tai mata abinda take so asanda takeso sbd tasan duk wani weak points dinta tace "bari inje in tambayeshi shikam nasan baze jamin kamshi ba" riko hannayen ta Mehtav tai tana fadin "ke meye haka ba'a sirri dake salan ma kije kigama zubarma da mutane aji agabanshi ko ban aikeki ba," dariya Abeey tafarayi tana fadin "yah Mehtav shifa Islam dakike gani besan wani abu wai wani aji ko makamancinsu ba in ma zaki sake kusha love kiyi saboda bature ne baruwansa he's very open minded," tace "aiko naga alama" tana murmushi kafin tace "kinsan meya faru last night," girgiza kai Abeey tai tana jiran karin bayani "yace fa yana Sona" takarasa tana fadawa saman gado harda wulla kafa, Abeey mikewa tai tana tayata murna tana dada zigata tashiga bata labarin duk abinda yace mata tana wani blushing kamar wacca akasa a aljannah. Abeey se dadi takeji domin duk duniya babu abinda tafiso irin taga yar uwarta Mehtav tana farinciki kamar haka.

Ranar dai ba maganar komawa barci don ahaka inna da tazo tashin Abeey makaranta ta samesu sunata juya yadda akai yau ba fada ba komai Mehtav ce ma ta temakawa Abeey tai shirin yau dakanta tai mata komai ta rakata har gaban school bus tashiga tana mata bye bye duk da taso suyi sallama da islam kafin tatafi amman kuma Mehtav ta hanata tashinsa daga barcin daya koma bayan asubah sbd tasan be wani samu yin na daren ba. deep down tadamu sosai akan mafarkan da yakeyi hakanne yasa takira kafaya bayan takoma ciki tana tambayarta akan hakan,kafaya cikeda farinciki take fada mata "ai hakan na nufin ansamu haske akan lamarin nasa tunda yana iya tina rayuwarsa tabaya ta siffar mafarki tun yanayi ararrabe idan yacigaba dashan magungunan zefarayi daki_daki komai yaringa dawo masa ahankali dan kansa batareda anyi pushing dinsa gurin tina hakanba,"

sosai Mehtav taji dadin bayanin don duka burinta ayanzun shine duk abinda ze inganta rayuwar Islam din nata domin tasan duk yadda zasuyi zama me dadi bakamar idan yasan suwaye iyayensa ba,don haka cikeda farinciki take bama paa labarin hakan lokacin daya fito,amman se taga paa kamar baya farinciki da hakan,ba abinda yace mata se kawai "Allah yakara sauki" hakan yasake daure mata kai,se kuma ya daura mata da mgnr aurensu da yadda sukai da Islam din,dan shiru tai kwakwalwarta tagaza fahimtar abinda paa din ya aikata just now,kawai tace mai "ta amince zata aureshi amman so samu tagama final exams dinta tukunna," tambayarta lokacin da zata gama yay,tace mishi "next month" dan jim yay kafin yace "Allah ya kaimu" kawai yacigaba da karatun jaridarsa.

Se kusan karfe 10 EHSAAS ya farka daga barci bayan yayi wanka yafito ya tarar gidan bakowa shiru Mehtav ce kadai. inna tafita yin kitso acan wani saloon dake babban titi, Abeey tana school,paa yatafi sabgoginsa, hakanne yasa tashirya masa breakfast na musamman cikeda nuna kauna mai sanyi sukaci suka gode Allah kafin tafara Shirin makaranta don tanason taje akoya mata wani aiki wanda zasuyi jarrabawar sa gobe,tana fitowa ta kalleshi yana kwance saman doguwar kujera yana kallon cartoon dinsu dasuka saba kalla da Abeey tacemai "zata tafi school." mikewa taga yayi yana fadin "ze bita" dan kallon gidan tai jin shiru babu kowa yasa tace mai tohm don batason tabarshi shishi kadai,kadaici ze dameshi kuma itama zataso ya kasance a side dinta,hakanne yasa suka fito tare jabeeru yadaukesu zuwa makaranta.

seda suka karasa ciki tafara dana sanin fitowa dashi domin duk inda tai dashi se ankalleshi sbd yanayin kalar farar fatarsa dake kama data larabawa da doguwar sumar kanshi da beard dinshi daya mugun cika sbd rashin aski,don gashin kansa yakusan tsayin nata.

inka gansa zaka dauka original Arab blood ne irin na era din farko dinnan ne ga kyawawan idanuwansa dasuke kara dada jan hankalin jama'a babu mata ba maza,har class rep din nasu daze musu tutorial din kasa shiru yay seda ya tambayi Mehtav inda tasamo wannan balaraben,dukda EHSAAS na jinsu cikanku bece musu ba sbd baida sakin fuska kuma bata gane hakan se yana tareda mutanen dabe saniba seka dauka betaba dariyaba sbd wani irin kwarjinin isa da kasaita da Allah yazuba mishi. wayarta ta bashi yashiga buga game har aka kammala musu karatun two hours basu cikaba suka fito daga school din.

tanason suwuce gida amman kuma tanason dama takaishi amasa aski don gashinsa ya soma damunsa sosai talura da hakan. hakanne yasa tasa jabeeru ya kaisu gurin aski mai kyau, Casablanca luxurious barbing saloon ya kaisu dake gwarimpa,har ciki ta rakashi sbd yaki yarda sam jabeeru yay mishi jagora se ita dole.

dayawa sun dauka mata da mijine saboda yadda EHSAAS din ke makale da Mehtav duk inda tasa kafa yana bayanta hannunsa cikin nata tun tana jin kunyar hakan har seda ta hakura ta kyaleshi se wani basarwa yakeyi,shi kansa barber din seda yagama sha mishi kamshi sannan ya yarda yataba gashin nasa tana gefensa tana tamai videos masu kyau awayarta tana mai gwalo se kace wanda in aka taba kan za'a gutsiri fatar jikinsa.

Sosai ake dan satar kallon EHSAAS din dukda yadda kowa kejida kanshi agurin amman shidin ba irin mutanen da suka saba gani yauda kullum baneba,dakanta tazabi irin askin data keso ai mishi, iri dayane sak da wanda tafara ganinsa dashi aka masa kuwa sajensa dake hade da lallausan gemunsa takalla tace "shima surage masa," tsaf tsaf yafito bayan da aka gama kamar ka lashesa barber din kansa se yabawa yake yadda doguwar fuskarsa ta bayyana sosai sabanin dacan da gashin ke yawan rufeta.

daga nan jabi lake mall suka wuce sun jima suna siyayya agurin itace takeyin siyayyar amman komai nasane da Abeey su biyu taiwa siyayya da duka monthly allowance dinta da paa kenata,kaya take zabar masa masu kyau sosai daga tace yaje yagwada wannan se tace a'ah wancan.

Ba inda bata shiga dashi ba cikin Zara, Lacoste da Hugo boss yana biye bayanta don jabeeru jiransu yay amota ganin yawon nasu bame karewa baneba,tanata snapping dinshi domin drama yake mata sosai yana nuna shifa yagaji donta takura mishine.

bayan sunfito kafin sutafi sallar azahar suka tsaya sukai daga nan suka fada Nkoyo restaurant dake gefen tafkin jabi sukaci abinci mai rai da lpy suka koshi,bayan sungama cikin recreational park din jabin suka tsaya EHSAAS nata kalle kalle saboda abin Kamar sabo yake agurin sa don betaba gani ba bata tashi ankarewa dasun bata lokaci sosaiba seda taji ana kiraye kirayen sallar la'asar.

Anan sukai sallar daganan jabiru yadakko su zuwa gida suna hirarsu mai sanyi mai cikeda shakuwa susu biyu abayan mota harta da jabeeru dake tuki yana kallonsu ta glass bazece ga abinda suke fada ba sbd yadda yaga Mehtav nawa EHSAAS magana kasa akasa kmr rada acikin kunne don yalura baida surutu kusan duk hiran Mehtav ke mishi, harsuka karaso gida.

batai mamakin ganin motar paa a harabar gidan ba EHSAAS ne ya riko musu shopping bag din niki niki har suka karaso ciki,tanata mai dariya tana tsokanarshi wai kodai yamai nauyine tazo ta tayashi, hararar wasa yake watsa mata ahankali irin tama raina shinnan yashiga nuna mata muscle dinsa dake cikin t shirt dinsa.

dede inda sukai turus da sukaci karo da paa daketa kai kawo afalon kamar wanda yaywa sarki karya,wani mugun kallo daya watsa musu yasa Mehtav tasha jinin jikinta tai saurin kamewa agurin tana kokarin fara gaida shi ya dakatar da ita tahanyar daga mata hannu yake fadin "da iznin wa kika dauki yaronnan kika fita dashi kuku biyu kacal Mehtav," dagowa tai sbd tsawar dayay mata abune dabe cika yiba,muryarta na rawa tashiga fadin "paa...." don tanason takare kanta ne,amman takasa magana, "Mehtav wai meyasa kike abu kamar karamar yarinya ne kinsan yaronnan bashida lpy idan kika fita wani abu yafaru dashi fa kokuma inkika fita aka cutar daku fa banason sakarcinnan da kikeyi kingirma amman bakisan kingirma ba,kodan kinji nace zan aura miki shi shine kike tinanin kinsamu license din yin yadda kikeso alokacin da kikeso tareda shi," "but paa..." tafada tana yarfar da hannayenta cikeda borin shagwaba don ita a iya saninta batai laifi ba daze sata agaba ya ringa fada haka yamaki sauraranta. EHSAAS calmly yake kallon paa don mugun haushinsa yaji yanaji yana dagawa Mehtav murya haka, "kika min kuka anan sena bubbugeki, this should be the last time dazaki sake fita dashi daga gidannan kinji ko" yafada cikin gargadi da yasa EHSAAS cikeda gadara yace "inta karafa me zakayi" Ba paa ba ita kanta inna dake fitowa daga daki da hayaniyar datakeji tayi yawa seda taji kirjinta ya buga saboda yadda yay magana cikeda da mazan taka bazaka taba cewa kanshi wai ajuye yakeba with a serious tone yacigaba da fadin "nace mezaki inta kara din? why are you being so harsh on her, for god sake nine nabita muka fita nine yakamata kaiwa tsawa ba wannaan yarinyar ba, and I'm not sick I'm perfectly okay" yakarasa yana kallon paa don ji yakeyi kawai yatsani yaga namiji babba ko yaro kowana irine yana dagawa mace murya. paa cikeda mamaki yanuna kanshi yana fadin "Islam ni...nikake fadawa haka," Islam cikeda izza irin ya isannan yabude baki yana fadin "Yes you, wicked anga....." bekarasa ba kawai yaji Mehtav ta rufe mishi baki hawaye yana sakkowa a idonta tashiga girgiza mishi kai alamar yabari, "pls stop it he is my father" tashiga fadi tana girgiza mai kai dayaji zuciyarsa tacigaba da tafasa fuuu ya juya yanufi dakinsa bayan ya dire shopping bags din be sake kallon inda paa yakeba. Mehtav takalli paa dake tsaye kmr statue yana kallonsa aransa yana raya, lallai kamar kumbo kamar kayanta in beyi takama da wannan izzar ba aiba ace iyayen sane suka haifeshi ba amman duk jijida kansa yanajin lokacin sauke masa yakusa yi,ammaan kuma he won't push karyaje burinsa yaki cika.

Mehtav karasowa gabansa tai cikeda ladabi take fadin "Allah ya huci Zuciyar ka paa kayi hakuri da duk abinda nida Islam mukai maka in sha Allah bazamu sake ba, wannan ma kuskurene shima xansa yazo yabaka hakuri bada niyya yaymaka rashin kunya a" kallonta yay yanajin tausayin yarinyar tasa deep down yana me tsanar kanshi da amfani da ita dazeyi gurin cuzgunawa Fulani hajeer, amman anya ze iya kuwa anya ze iya sacrificing Mehtav dinsa gurin biyan bashin gabar daya riga yashude shekaru da dama dasuka wuce baya hada son yayanshi da komai kuma tsoronsa shine kada ace masu farautar ran EHSAAS su ganshi tareda yarsa idan tana daukarsa suna fita haka barkatai su cutar mishi yarinya zuciyarsa bazata iya daukaba duk kuwa da kwadayinsa nason hada zuria da royal family din NURISTAN.

Rungumeta kawai yay cikin kunnenta yake rada mata "I'm sorry for raising my voice too, my dear forgive your papa" kankame shi tai tanajin matukar kaunar mahaifin nata tana ratsa ko ina na jikinta. kafin ahankali ta raba hug din tasoma kwasar kayan tana nufar dakinsu dashi.

inna kallon paa take yi kawai domin tabbas tasan be saba yiwa yaransa hayaniya hakaba kuma ayadda tasan Habib dinta ba yadda za'ai yabari yaronnan dukda haukarsa yay disrespecting dinsa yaci bulus haka toh kodai Habib yasan wani abu dangane da yaronnan wanda su busu saniba ganin Mehtav tatafi yasa takarasa tana zama daya daga cikin kujerun falon, tai mai nuni da shima ya zauna zama yay yana dafe kansa don yamanta rabon da kanshi yadau irin wannan pressure din haka,kafin ma inna takai ga magana taji yace "Inna don Allah karki tambayeni komai zanmiki bayani daga baya yanzun dai inason afaraiwa Mehtav wannan abin da kukeyi naku na mata su dilkane kome.....uhm dukdai abin gyaran jikinnan inna aimata ko nawane aimin bill zanbiya sannan gobe da daddare kishirya jabeeru ya kaiki Augusta's ko Dr bint AJ's pls afara hada mata kayan kitchen inason ayi komai on time,sannan kiyiwa auntynta zainab magana kinga ita tasan kayayyakin zamani irin nasu,seta zo itama tadauketa suje su hado lefe," inna sakin baki kawai tai tana kallon paaa domin batasan sanda Mehtav tafara zance bama dahar ta tsayyar da miji kuma dahar ya aiko akai magana kuma akabashi aka saka ranar biki,lallai kenan rashin amfaninta har yakai Habibu yabada yarsa ba tareda tasani ba ta raya aranta, batasan yafito fili ba dasauri paa yadago kanshi yana fadin "wllh inna bahaka baneba abinne yazo bakatatan kuma ba'ayi ko daya daga cikin abubuwan dakike zargin anyi dinba," tace "kafadamin uban waye mijin dakake min wannan lissafin mara kunya fitsararre kake zaune kana tsarani wai har kana cemin inwa yarka yar fari gyaran jiki koh,koma kara baka da ita habibu" dan shiru yay saboda yasan idan tasan cewar Islam ne mijin tabbas za'ai daru da ita koma dai taje ta hadashi da kawunnanshi akauye azo su hanashi abinda yake da niyyar aikatawa kawai badan yaso ba yace mata ai dan abokinsane kuma zece yazo yagaidata bada jimawa ba, tayi hakuri don Allah inranta yabaci,tace "Ba maganar hakuri abinda nakeson sani yanzun shine ita Mehtav din ta amince ne ko auren dole zaka mata Habibu" dan girgiza kai yay yana fadin "inna don Allah kiyi hakuri abinne yazo baka tatan kinsan sha'anin aure ta yarda karki saka tazo tace tafasa kuma kinsan halin yarinyar taki butsuwa ce," jinjina kai inna take kawai kanta yana kwance wa domin Mehtav yadda idanuwanta ke atsaitsaye bata mata kala da yaran da za'a zabawa miji su karba hannu bibbiyu ba, amman dai kawai se tace "tohm" don seta fara magana da yarinyar tukunna taji ta bakinta don duk irin zaman doya da manjar da suke agidan tana matukar kaunar yan jikokin nata.

Adaidai Farkon daren wannan Rana lokacin gari yayi duhu saboda kiraye kirayen sallar magariba da ake tayi daidai Private jet din mai Martaba sarki NASHWAN daga Nuristan ya sauka a Filin Jirgin Sama na Maiduguri.

Airport din acike take dam da jami'an tsaro masu dauke da wasu manya manyan mahaukatan makamai ahannayensu, motocin tsaro tako ina sun zagaye gurin, da kuma jami'an diflomasiyya. An tanadi securities na musamman domin karɓar bakoncin zuwan matar marigayi crown prince EHSAAS da current crown prince EHSAAS karami tareda Queen mother mahaifiyar sarki NASHWAN bin Ehsaas domin tabbatar da lafiyarsu akai hakan, yadda garin maiduguri yacika da manyan jami'an tsaro zaka dauka wani shugabn kasarne ze sauka,ita kanta Islam seda tasha mamakin kalar mahaukatan jami'an tsaron da aka zuba agurin,dakuma yadda suke kaffa kaffa dasu suna tattalinsu, ga manyan dogarai daga fada da wakilan mai Martaba sarkin borno dasuka zo tarbarsu cikin girma da mutun tawa.

junior na jikinta barci ma yakeyi,se uwar soro dake gabansu tana tafiya tana dan dingisa kafarta saboda zaman jirgin dayasa kafarta yin tsami dukta addabeta cikin aminci da girmamawa aka tarbesu, sallar magariba suka farayi acikin airport din, sannan aka kaisu cikin katafariyar motar dazata daukesu zuwa ainahin palace din mai Martaba sarkin borno na yanzun mahaifin jalila kenan kuma yaya ga Fulani hajeer tare da rakiyar motocin tsaro masu siren, Islam haka kawai takejin hankalinta yakasa kwanciya dukda ta tabbatar tabar NURISTAN amman se take ganin kamar ko ina taje kawai she's not safe,dukda kawai intuition ne kuma tana kore hakan daga cikin ranta,duk da darene amman hakan be hanata fara kalle kallen jahar ba, sam sam gine ginensu da kalar suturar mutanen data hadu dasu batai kala da wacca ta saba gani a NURISTAN da kasashen waje datake zuwa ba.

wannan looks abit local amman abin yaburgeta yakuma kayatar da ita,uwar soro cikin barkwanci take fadin "anan garin dakike gani ananne mijinki yafara dabo gashi munkawo danshi ma ze fara, Allah dai yasa inada rabon ganinsa yana takawa kinsan shekarun namu sunja" murmushi tai tana dawo da attention dinta kan uwar soro tasan cewa ta gaji sosai saboda amatsayinta na babba wacca shekarunta sukaja be kamata ace tana irin wannan tafiyar da zirga zirga hakaba, tasan kaunace ta tsakani da Allah da take mata tasa takasa yarda dakowa akanta tace lallai lallai seda ita za'ai wannan tafiyar, Islam ta dan kama hannun uwar soro tana fadin "Grandma in sha Allah bama iya da bonshi ba har aurensa zaki gani" takarasa tana murmushi ta kwantar dakanta akafadarta jaririn kuma nakan cinyarta. uwar soro murmushi tashigayi tana shafa kan Islam take fadin "Islam aiko kikace inga auren junior bakimin gataba so kike sena zame muku jidali kenan," jinjina kai islam tai tana murmushi tace "uhm bamu gaji da ganinki ba.....kuma..." kasa karasa abinda zata fada tai sakamakon fashewar wani abu mai kara da sukaji dayasa har motar da suke ciki seda ta girgiza gaba dayansu cikin tashin hankali suka dago suna kallon juna. wata karar suka ji data sanya junior dake barci canyara kuka da sauri Islam ta rungumeshi tsoro na cike kirjinta don tunda take a NURISTAN bata tabajin irin wannan karar ba da alama ita ta firgitar da yaron yake kuka haka.

uwar soro cikin tashin hankali takalli sojan dake tukasu tana tambayar "me yake faruwa?" over over dinsa ya dauka yashiga magana da motocin gabansu, In minutes yataka burki yana kokarin yin reverse da yaja ya sanya hankalinsu yadada tashi kokarin baya da motar yakeyi don ya juya amman motocin dake bayansu da suka faraci da wuta ya sanya yakasa hakan.

"innalillahi wa inna illahirrajiun" uwar soro tashiga furtawa ga junior yaki dena kuka kamar ansaka mishi remote ana cewa yakara volume, "Madam we need to get out of this place bomb ne yatashi agabanmu kadan kuma ana zargin set up ne mune target dinsu,yanzun....." aibegama rufe baki ba sukaji karar harbe harbe ta gaba tabaya tako ina dawasu irin mahaukatan machines dasuke sauke wasu maza cikin bakaken kaya ko ina na jikinsu arufe harda fuskarsu daya sanya Islam karasa gigicewa.

musayar wuta suka farayi da jami'an tsaronsu kafin su sakar musu wani abu me hayakin masifa da yasa jami'an suka fara tari suna kokarin tare hancinsu daga shakar abin sbd ceton ransu, amman sun kasa haka daya bayan daya suka shiga fara musu kisan gilla da makamai manya manya da yafi ma na jami'an nasu. sojan bude kofar motar yay yana ce musu karsu fito,yashiga shima aka fara fafatawa dashi,uwar soro kallon Islam tai tana fadin "Zaki ita tukin yanzun" jinjina kai tashigayi tace "bani dan, kiban dan kidira kija motarnan tabaya tagefe kota inane mufita agurinnan ran yaronnan suke hari bamu ba, dolene mu ceci ran yaronnan koda zamu rasa tamu rayuwar islam at all cost"

ita kanta batasan lokacin data mikawa uwar soro yaron ba,ta baya tadire ta koma driver sit daman ta kware atukin ganganci aguje taja motar tana yin gaba dashi kafin yan bindigar su an kara sufara harbin motar tako ina jikake tas tas suna harbin motar uwar soro tana "karki tsaya Islam kiyi gudu kozasu kashemu dome ki tseratar da rayuwar yaronnan, kiyi gudu... kiyi gudu" tana juyawa tana kalle mata baya wani daga cikin yan bindigan ne yay nasarar saita glass din motar yana harbawa ciki akokarinsa na kashe me tukin uwar soro cikin karaji take fadin "Islam durkusa kanki kasa....nace kiyi kasa.. kasa" da sauri tai kasa dakanta tanajin saukar harbin yawuce wani sharp pain taji akafadarta ammam tsabar tashin hankalin datake ciki ko dubawa bata tsaya yiba.

taka motar kawai takeyi suna cigaba da harbi wani irin dogon numfashi da uwar soro ta jane yasa taga ne cewar wani abu mara kyau yafaru da ita,ga junior dake ihu asaman cinyarta yaki denawa, Grandma Grandma Grandma tashiga furtawa da karfi jikinta yana jijjjiga yana kakkarwar tsoro jin babu motsin uwar soro kwata kwata acikin motar se wani irin kuka da junior ya keyi kamar ana zare ransa.

sharara gudu kawai takeyi acikin motar amman jin tana sake kiran sunan uwar soro bata ansaba yasa ta tsaya chak agefen titi gurin tsit kamar anyi ruwa an dauke babu abinda kakeji se kukan tsuntsaye fitowa tai tana bude bayan motar uwar soro dake jikin kofar biyo kofar tai rigif zata zube Islam ta tarota tana tattabata "Grandma Grandma Grandma" tafada da karfi tana kankameta ajikinta junior yana kuka tana kuka tana kiran uwar soro da babu alamar zata amsa mata tattabata takeyi ga gurin duhu babu alamar haske ko alamar jama'a. jin wani abu kamar ruwa ahannun ta lokacin data taba wiyan uwar soro tadago tana kaiwa hancinta babu tantanma tagane jini ne yake zuba daga jikin kakar tasu kuka takara fasawa tana fadin "don't leave me please Grandma, Grandma kitashi Grandma kema tafiya zaki kibarni ko Grandma ya kikeso inyi da rayuwa ta inkika tafi kika barni, Grandma pls pls I can't protect this child alone Grandma I need you" takarasa tana shashsheka numfashinta na neman daukewa da sauri tashiga gyara zaman uwar soro junior dake kuka akan cinyar uwar soro ta dauka tana ciro babban gyalenta me dauke da wata irin kwalliya da abuga ajarida ta sakashi abayanta tadaureshi tigijim jim, kamar kuma ance yay shiru duf kukan nashi ya dauke ya lafe abayanta.

takulle kofar don ta koma ta cigaba da tuki ko zata samu asibiti akusa da zata kai uwar soro wanda za'a bata temakon gaggawa hannunta har kakkarwa take tashiga yiwa motar key amman me se tace tasheni inda kika ajjeni motar datayi kiii seta mutu, "not now not now pls" tashiga fada tana dukan steering wheel na motar jikinta na rawa hannayenta duk jini, motsin tahowar ababen hawa dataji yasata saurin bude kofa tana kokarin zaro uwar soro da take baya amman takasa saboda nauyin datai mata,gashi se kara kusanto su motsin yakeyi dagudu tai can cikin dajin gefen titin tana labewa bayan bishiya. yan bindigar taga sun karaso ababur wani yare sukeyi da bataji ma kwata kwata, se zagaye gurin taga sunayi sunata dube dube da alama ita suke nema basu ganta ba,tanaji tana gani taga daya daga cikin su ya shiga motar,cikin fulatancin dabata gama tsintar na kirki gurin EHSAAS da Fulani ba taji dayan yana cewa dayan "ya zasuyi da gawar tsohuwar?" gawar dataji ya ambata takara rikitata gaba daya tanajin kamar tafasa kuka "kenan Grandma dinta tamutu dagaske itama tatafi tabarta," batasan me sukaiwa motar ba se gani tai sun bude gaban motar hayaki yana ta fita suka dan tattabata dayan yana kunnawa dake tabar key ajiki takama. biyu suka shiga motar taga sunyi gaba da ita harda gawar uwar soro dake ciki,batasan iya adadin lokacin data dauka agurin ba,hawaye keta ambaliya afuskarta zuciyarta nawani mugun radadi kamar zata fashe haka takeji.

motsin junior abayanta yasa da sauri tasakkoshi da alama yunwa yakeji don rabonsa da shan mama tun acikin jirgi Ahankali jikinta na rawa tashiga feeding dinsa dukta bata jikinsa da jinin hannayenta,harbin daya wuce ta gefenta se yanzun take lurada ma ya gogi kafadarta da take ta zubda jini. tana cikin feeding yaron taji wani abu medan karan azaba ya gallara mata cizo batasan komeyi ba,cizon be mata kala da wanda karamar dabba kamar su cinnaka zasuyi ba hakanne yasa tamike zumbur tana zare junior daya fasa kuka alamar be koshi ba wani irin azaba takeji tanabin kafarta daba tantama tagane kila kunamace ta harbeta,mayafinta data goya junior dashi tayage kasan ta daure don kada yay spreading dukda azabar da takeji seda ta tsaya tagama shayar dashi harya fara barci sannan tamaidashi bayanta.

tashiga fitowa bakin titi da sauri da sauri tanayi tana kalle kalle don tabbatar da babu wanda yake ganinta, dawani irin sauri take tafiya kamar zata kifa ga kafarta dake tsananin zafi alamar dafin yafara tsananta,bataji motsi ba kawai se ganin wani mutum tai agabanta bata lurada sanda yasauka daga kan babur dinsaba,babu ko alamar kukan abin hawa. ai dagudu ta yunkura zatai daji taji an rikota dasauri ihu tafarayi tana kokarin fizgewa domin tagudu taceci kanta da danta don yamata kala da masu machine din dasuka farmakesu dazu saidai shi nashi machine din baya kara, "let me go kasakeni zan kasheka let me go" tashiga fada tana tuttureshi amman dake karfinsu ba dayaba,tattareta yay guri daya yana hadewa yake fadin "keh who are you?mekike anan" Tsawar dayay mata ya kara gigita ta tashiga kurma ihu tana neman te mako hannu daya yasaka yana toshe bakinta, tashiga gartsa mai cizo da iya karfinta da yasa dan dole yasakin mata baki, "do you think I'll let you harm my son,babu wanda ya isa ya tabamin dana acikin ku sena kasheka katabamin yarona se alokacin ma ya lura da danda ke abayanta," yasan area dn datake nufa bayby lafiya indai hartai gurin tohm wllh ko burbushinta babu me sake gani amman da alama batasan da hakanba shiyasa take tunkarar halakar ta kai tsaye, "karki je can gurin akwai yan ta'adda area dinnan babu lafiya me yakawo ki nan? Kinsan inane nan kuwa harda goyo anan gurin," kuka ta fashe dashi tana fadin "karka yaudareni nasan your one of them,bazan yarda dakaiba kasakeni" fizgota yay ganin zata gudu yana ciro ID card dinsa daga aljihu yana dodanawa afuskarta yake fadin "I am Assistant Director Tajuddeen Bashir, Maiduguri Command," kallon ID card din tashigayi dukda babu abinda take ganewa ajiki bayan DSS da batasan meye ma'anar saba jitai takasa katabus saboda wani irin jiri dayake dibanta,cikeda rauni da rashin sanin madafa take fadin "take me away from this......place help me.......protect my...... son" tashiga fada idanuwanta na rufe taro ta yay ganin ta sume. kalle kalle ya shigayi ganin babu kowa daze iya temaka masa ya sanya yashiga kwanto babyn dake bayanta yana rasa yadda zeyi dashi tsintar kanshi yay da raba gyalen biyu yadaure babyn asaman faffadan kirjinsa ya sun kuceta ya daurata saman machine dinsa mara kara yasa rabin zanin yana daureta ajikinsa tayadda kosun fara tafiya bazata fadi ba, yajuyar dakan machine dinsa yashiga bin hanyar da yasan bazasu taba haduwa da yan bindigar ba, domin yasan tunkararsu ayanzun baze haifar masa da da me idoba don kwata kwata ba ashirye yakeba,be kuma zo Maiduguri dan wannan aikinba shi operation dinsa daban yake nasirri wanda yariga yagama gudanar dashi adaren yau yake shirin komawa Abuja kuma se wannan tashin hankalin ya bullo yaritsa dashi.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Send Comment & Like.

[23/05, 20:31] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.