EHSAAS

Chapter 25

by @fatoumspassion

Ahankali take bude idanuwanta dasukai mata wani irin mugun nauyi ta saukesu asaman ceiling din dakin fari tass dabata taba ganin irinsa akasarta ba. tun tana gani dishi dishi har idanuwanta suka bude tarwai akan wata farar fitilar dake cikin ceiling din tana haskata, kanta ya mata wani gingirin tsabar yadda takeji aciki hatta da duka jikinta jitake ya mata tsami. se kuma alokacin hankalinta yasoma dawowa jikinta ta tina acikin wana hali ta sume, Agigice ta mike zaune tana fadin "junior" cikin ranta tana dafe kirjinta dayay mata nauyi. motsin dariyar yaron dataji ata wajen kofar ya sanya tajuya daidai taga wannan saurayin daya temaketa yashigo rike da junior ahannunsa yabashi abin wasa me kacau kacau se kadawa yakeyi yana dariya kamar ya dade da sabawa da mutumin. lumshe ido tai wani irin hawaye masu dumi yashiga fitowa a idonta takoma ta xauna tana dafe kanta tana kuma tina yadda yan bindigar suka tafi da gawar kakarta,wani irin ciwo mai tsanani takeji acikin kirjinta tanajin anya zata iya cinye wannan jarrabawar dake bibiyarta daya bayan daya tana ganin kamar itace bad luck dake jefa duk me kaunarta cikin hadari daga EHSAAS yanzun kuma ga Grandma dinsu matar data nuna nata kauna wadda babu wanda yataba nuna mata shi, furucin mahaifinta lokacin daze tafi daga palace din bayan ta nuna bazata bishiba take tinawa inda yace mata "he curse her bazata taba albarka acikin rayuwarta ba,yatsine mata ya tsinema duk wani wanda ke sonta kuma yace rayuwarta har abada seta tagayyara," haka kawai taji tana furta "I'm sorry father I'm sorry," Bata nadaman shigowarta musulunci har wayau sbd bata taba daura laifin kaddarar da Allah yadaura mata akan kowaba se akaran kanta,tanajin inama itama Allah zedau ranta kamar yadda yadauke EHSAAS da Grandma masoyanta dabazata taba samun kamarsu ba har duniya ta nade.

mutumin tsayawa yay yana kallonta daidai lokacin ya karaso saman madaidaicin gadon datake kai ya kwantar da junior agefenta,bece mata komai ba se gani tai ya tsugunna yaciro wata katuwar bagpack akasan gado wasu kayansa da yagama ninkewa yazaro yana yimusu guri acikin jakar ya zuge yana kallon ta kafin yace mata "sannu ko, Gashi har safiya tayi bazaki sallah bane?" dasauri takalli taga inda rana tafito sosai dasauri tamike tana kallon kafarta dawani fari farin abu mai maiko data gani ajiki da alama magani ne nadafin kunamar aka shafa mata, gefen hannun tama se yanzun ta lura anyi treating dinshi ganin irin kallon datake mishi yasa ya nuna mata bathroom da sauri ta wuce tashiga ya tsaya kawai yana kallon weirdness din matar yana kallon yaron kwata kwata batai kala da danba,sbd yarinyace karama danya sharaf musamman daya kare mata kallo,tayi kankanta data haifi wannan bouncing babyboy din kuma kalarta dayaron yayi parallel sosai. aransa yaraya "toh kodai ba danta baneba" se kuma ya kore hakan daga ranshi sbd yana tinawa vividly yadda take rokonshi yay protecting yaron tan adaren jiya kafin ta sume yataho da ita nan, dakin hotel din da yake zaune acikine nasirri saboda baya iya staying a family house dinsu irin gidan yawannan ne da bashida private space nashi da zasu barshi yay aiki dakyau shiyasa yake zama anan din. kuma ajiyan ya kawota nanne sbd nan din zefi tsaro akan family house dinsu dake tsakiyar cikin gari,yana nan zaune tareda junior daketa wasanshi tafito ta dauro alwala,sallaya ya shimfida mata,yakawo mata wani babban abin rufa da baya amfani dashi ta yafa yanuna mata gabas tatayar da salla. isha'ee da batai ba jiya tafarayi bayan ta idar tayi asubah bayan ta idar nanma zama tai saman sallayar tashiga addu'a tana rokarwa kakarta rahamar ubangiji tanata mata addu'o'i iri iri harseda taji hawaye nabin kuncinta, Taj se kallon agogo yake domin tana bata mishi lokaci bayason yay tukin dare kwata kwata kuma yanada ayyukan dasuke jiranshi a Abuja dan gyaran murya yay hakanne yasa ta shafa addu'ar tana dagowa suka hada ido dashi yana kallonta, fuskarsa ba yabo ba fallasa yake cemata "sannu" jinjina mishi kai kawai tai dayaga alama kamar batajim hausa da kyau seya juya zuwa turanci yana tambayarta "inane unguwar su ya kaita donshi yanzun akwai inda ze wuce," kallonshi tai tana tinanin yadda zata fara cemishi ya kaita gidan sarkin garin amman kuma tana tsoro don batasan waye shiba kartai exposing identity dinta ya cutar dasu.

kawai se tace mishi ya ara mata wayarsa bamusu yaciro wayarshi yana mika mata,karba tai tashiga danna number Fulani direct tana kaiwa kunnenta amman abin mamaki kwata kwata kiran bama ya tafiya,hankalinta soma tashi yay saboda batasan kowa agarinnan ba Fulani take saran takira tasaka akawo mata temakon gaggawa amman kwata kwata layinta baya tafiya sam tamanta cewar lambar manyan kasa irinsu Fulani hajar bakowace number ce kiranta ke shiga wayoyinsu ba musamman daba lambar kasar NURISTAN baceba kuma su basu da ita atasu wayar.

jitake har zufa tana karyo mata domin bayan lambar mijinta da iyayenta babu lambar wanda ta haddace seta Fulani da grandma dinsu wanda duk su biyun jiya sunrasa wayoyinsu a abinda yafaru kuma grandma tarasu,hawayene yashiga zirya akuncinta takalli Taj cikeda rauni tace mishi "baya shiga" kallonta yay ganin yarinyar da alama bakuwace kuma tana cikin mawiyacin hali yake tambayarta "lambar inda kika zone baya shiga" jinjina mai kai tashiga yi bakinta nadan rawa,yace "kinsan sunan unguwar?" dan kallonshi tai ganin danta na hannunsa kuma tun jiya beyi kokarin yimusu komaiba yasa tace mishi "Kawaidai yana kusa da gidan sarki ko zaka kaini ka nunamin gidan sarki maybe daganan kozan gane" dan jim yay kafun yace "ba matsala give me few minutes inazuwa" ficewa yay daga dakin se gashi yashigo da wasu ledoji guda biyu da alama yanzun akai mishi delivery dinsu ya ajje mata yana fadin "freshen up kici wani abun se mutafi" kallonsa tai cikeda nutsuwa tace mai "thank you" murmushi yay mata yana fadin "your welcome" wucewa yay ze dau junior sufita dasauri ta tsaya abayansu yajuyo yana kallonta yace "lpy?" yana dan zaro mata ido alamar ta tsorata shi dan girgiza kai tai tana fadin "leave him here kawai" tana fidgeting fingers dinta alamar she's nervous kuma bata gama yarda dashi ba dan dage gira yay yana tabe baki yafice adakin yana barinta. Agurguje tashiga toilet tabar junior tareda abin wasan daya siya masa tai wankanta shaf shaf tafito tana bude ledar daya ajje mata wata brown doguwar rigace mai kyau,abayace mai matsakaicin kudi mai kauri daidai tsayinta tazira kawai tana daukar kayanta data cire ta cusasu acikin ledar ta bude dayar ledar, breakfast ne mai rai da lpy amman kwata kwata batajin appetite abakinta amman kodan saboda junior yasamu abinda zesha daga jikinta yasa ta tuttura abincin tanayi tana hawaye badon tana jin dadinsa ba harta kammala be dawo ba, lokacin junior yayi barci secan sannan taji yana kwankwasa kofa iznin shigowa tabashi, yashigo yana kallon ta yadda tai kyau dark skin dinta yay fresh her babyface looking so angelic kamar ba itaba daya gani jiya ajigace. dan murmushi yay mata kafin yace mata "shall we?" jinjina mishi kai tai,se yaga tajawo gelenta tana rufe rabin fuskarta dashi besan dalilin dayasa tai hakanba,kuma tayi hakanne saboda bata saba fita babu niqab ba tunbayan aurenta da EHSAAS sbd kamar wani mugun laifine kina Princess kifita azahiri cikin jama'a ana kallon face dinki, takarasa tana daukar junior da barcin ya kwasheshi agurin akafadarta ta daukeshi suka fito atare yana gaba tana binshi abaya har suka fice daga reception din hotel din gaba daya. bayan ya ajje musu katinsu karasawa parking lots sukai dake anan yake ajje motar sa don be fiya yawo da ita acikin garin ba,don indai cousins dinshi mata sukasan yazo da mota sunringa takura mai kenan akan seyakaisu yawo da dare. bude mata gaban motar yay tashiga rungume da junior kafin shima yashiga amota ba yadda beyiba yabugi cikinta yaji daga inda take kuma meya fito da ita amman setai ma kamar bata gane kalar tambayoyin da yake mata ba dukda wayon dayake mata matsayinsa na jami'in tsaro amman tsabar miskilancin Islam uffan batace mishi game da komai akanta ba. tundaga wuraren babban titin gidan sarkin shikansa yasha mamaki dayake ganin wasu mahaukatan securities nakai kawo agurin kamar ma anhana zirga zirgar ababen hawa tawajen da alama wani gagarumin abinne yafaru amman kuma yasan da wani abu yafaru baze rasa jin labari ba don koyau ya saurari labaran safe da baya wuceshi. wani black policeman ne ya taresu yana me tambayarsu ina zasuje? gurin wa sukazo? dan kallonsa Taj yay aka'idar aikinsa be cika bayyana asalin shiwaye agaban kowaba sbd aikinsa yana bukatar sirri yakalleta yana tambayarta "inane zataje?" daburcewa tai tana kallon police din bakikkirin dake binta da wani irin kallon zargi da tuhuma ganin yadda ta rufe rabin face dinta kawai jikinsa yabashi itace princess din da ake nema kuna yaron dake kwance ajikinta dukda arufe yake yasake tabbatar da zarginsa, "baiwar Allah kice wani abu mana inbakiyi magana ba fa bazasu bari muwuce ba," Mgnr Taj ta katse mai tinani. bakinta rawa ya shigayi kafin tace " ka..... kasauke ni anan kawai zanje dakaina" tashiga kokarin bude kofar,shikuma haka kawai Taj yaji be yarda da irin kallon da policeman din kemata ba kawai seya datse motar yashiga yin reverse. kallonsa takeyi cikeda mamaki take tambayarsa "meyake shirin yi haka?" yana gama juyar da motar ya nufi wata hanyar daban da tunda yafara tafiya ya lura da wasu motoci nabinsu.

cikin daburcewa tafara mai bala'i akan meyasa ze juyo da ita ita ya sauketa tatafi aitasan hanya, ayadda take maganar kadai yagane karya takeyi don da tasan hanya da tafadi inda tazo din. jin tacika mai kunne da hayaniya yasa yace "kalli bayanmu," wata katuwar bakar jeep data gani tana bin bayan sun yasanya jikinta yahau rawa take fadin "mezasu min sunganeni ko," cikeda son kwantar mata da hankali yake fadin "nothing will happen trust me kinji" yakarasa yana bata assuring look kafin yataka motar amugun guje akokarinsa na guje musu, rungume danta tai tana hawaye me zafi karar guje-gujen nasu na kokarin taba mata kwakwalwa don har canciki takeji.

sun kusan awa daya suna tuki kafinnan taji Taj ya tsagaita da gudun da yake har tanajin sautin dariyarsa yana fadin " this state is my territory bame iya cimmini anan din shashashu kawai" yakarasa yana dawo da hankalinsa kanta ganin yadda ta kankame junior kamar zata ballashi yasa yace mata "are you okay?" dan girgiza mishi kai tai tana bude idonta tagansu awani titi faital babu jama'a ko daya se zirga zirgar manyan motoci daidaiku dataga suna wucewa agurin,tace "inane nan?" dan kallonta yay kafin yace "Maiduguri mana" yana daga mata kafadarsa,kallonshi tai tana fadin "ka aramin wayarka dan Allah" kamar bazece komai ba ya dakko wayar yamika mata dasauri zata karba ya janye wayar yana mata murmushi cikin sigar wayo da tsokana yake fadin "da sharadi you'll tell me your name and why are you being followed domin wa ancan mutanen kece target dinsu bani ba,da alama that police man ne yabada information akanmu yagane fuskanki dakike wani bobboyewa," girgiza mishi kai tai kafin tace "niba wanda yasan fuskata anan sedai in description dina yagane,kuma ba abinda zanfada maka akaina" Taj yace "Ple just tell me who are you tahaka ne kadai zan iya temaka miki intseratar da rayuwarki dana yaronnan agarinnan," dan jinjina kai tai kafin tace "tohm kafara aramin wayar naka ai zanfada maka," kallonta yay irin ta tabbata dinnan ta jinjina mishi kai mika mata wayar yay yana ganin yadda tashiga zuba numbers din awayarsa tana gamawa tai dialing tana karawa akunnenta still wayar fulani bata shiga hakanne yasa tajuya akalar kiran zuwa wayar mom dinta, tanata kira baya reaching kwata kwata,cikeda rashin sanin abunyi tashiga kiran Abraham,saida takira sau uku tasamu tai ringing ana ukun. Taj duk yana kallonta wayar na ringing amman jitake kamar da bugun zuciyarta yake tafiya, Tanajin andaga tafashe da kuka Abraham Zion dake sauraronta ta daya bangaren shiru yay dukda yadda tsigar jikinshi da zuciyarsa ke tafasa da jin kukannata don kwana biyunnan yana yawan mafarkai iri iri marasa dadi akanta kuma yana alakanta hakan da kafircewa Jehovah da taine yasa take haduwa da tashin hankali iri iri, dakewa yay yana sauraronta "please help me Sir, forgive me bazan sake bata maka ba nayi alkawari just protect my son Sir,they want to kill us pls Sir, I need youuu" takarasa tana shashsheka numfashinta nasama da kasa kamar zata shide daga ta dayan bangaren kawai taji Abraham yana tambayarta "peace where are you right now? cikin daburcewa take fadin "I don't know somewhere in borno Nigeria father....wani.. ..wani mutumine ya temaka min ina tare dashi yanzun bansan ina nake anan ba,"

Abraham cike da nutsuwa da saita kirjinsa dake bugawa yake fadin "bashi wayar peace," mikawa Taj wayar tai hannunta yana rawa take fada mishi "my father needs to talk to you," karbar wayar yay yana sallama Abraham be ansa ba don bema san yadda ze ansaba kawai se yace mishi "thank you for helping my daughter,your such a.good Samaritan, yanzun akwai wani alfarma na keson na rokeka kaji," Taj yace "bakomai ai da na kowane" yace mishi "baida visa din Nigeria zeyi kokari yasamu akan lokaci,idan besamu bama zeyi kokari ta niger ne yashigo seya karaso amota yariketa agurinsa har yazo Nigeria se yamai kwatancen inda yake kar yabarta take fita ko ina," dan jim Taj yay se kuma yace mishi "shi ma'aikatacin tsaro ne kuma aikin daya kawo shi Maiduguri ya kare don haka yanzun Abuja ze koma anan yake main work dinshin sedai yatafi da itacan inba damuwa" da sauri Abraham yace mai "badamuwa it'll be more safe ma idan akabar garin Maidugurin da ita take her far away I'll pay you konawa ne just take care of my child kaji yaro" Abraham yafada cikeda muryar da inda peace zataji alokacin zata fara wondering anya inshine kuwa, Taj murmushi yay yace mishi "bakomai seyazo din kawai" yana mikama Islam wayar karba tai tana kallon Taj takara akunnenta Abraham yace mata "peace!" tace "yes Sir" yace "we have no other option bayan muyi trusting wannan mutumin dukda bamu sanshi ba be sanki ba kince ya temaka miki danhaka follow him, I trust Jehovah will take care of both you and my grandson har inzo in daukeki daga wadannan azzaluman mutanen kinji," dan jinjina kai kawai tai don taji ba dadi sbd tasan dangin EHSAAS yake referring to azzaluman wanda tasan not all of them are that bad. addu'a yashiga mata da tasa peace tadan zame wayar akunnenta don jin waken addu'an nashi takeyi yanzun kamar wani surutan banza mara ma'ana amman kuma tasan babu wanda ze temaketa awannan halin datake ciki yay protecting yaronta se shidin don batada wanda yafishi. godiya tamai tana katse wayar ta mikama Taj ta kalleshi tana fadin "thank you," karba kawai yay yana fara tada motar yana kallonta yace mata "it'll be a very long drive, get ready" dogon numfashi peace taja tana kallon yadda yasaita motar akan hanya har lokacin kuma junior barci yakeyi kamar wanda akama allurar barci. hanyar Abuja suka dauka tunda peace take arayuwarta bata taba tafiya amota koda na awa biyu ba balle wannan nakusan awa goma sha metsayi irin wannan, zatace wannan shine the worst traveling experience data taba samu arayuwarta,dukda mahaukacin gudun da Taj yakeyi seda suka kwana ahanyar inda babu abinda yake tsayar dasu seyin sallah da cin abinci da yawanci Taj kecin abinsa domin yawancin abincin titin da yake siya ita bata tabawa ganin irinsa ba ko dandana kalarsa batayi, gani take idan taci tamkar mutuwa xatai,don mugun kyankyami gareta kamar me OCD.

haka in junior yay kuka zeyi parking abakin hanya yafita yabata guri tai feeding dinshi seta gama sannan ze dawo su cigaba da tafiya,har amai seda tai sau biyu ahanya jikinta gaba daya ciwo yakeyi ga uban zazzabi dake kokarin lullubeta sbd kalar wahalace wacca bata taba shanta arayuwarta ba shikansa Taj seda ya tausaya mata.

se washegari suka karasa Abuja kuma ahakan babu abinda yatsinta dangane da ita se sunan da take gayama danta junior ko sunanta taki yarda tafada mishi niyyarsa yakama mata hotel ta xauna harse babanta yaxo amman me ya kashe kudi sosai azuwansa maidugurinnan kusan duk albashinsa ya tattare yabawa cousin sister dinshi dake shirye shiryen bikinta akeyi tai demanding wasu kudade masu nauyi ahannayensa shikuma sam baida rowa domin abin hannunsa be taba rufe masa ido ba, ganin kudaden hannayensa bazasu isheshi ba yasanya bayan sun shiga garin Abuja yatsaya awata private hospital likita ya duba mishi ita akai mata allura aka bata wasu drugs tana dan hutawa yasamu yafita yana danna number din Engr Habib. bata jima tana ringing ba ya daga gaisawa sukai cikin raha da mutunci da shakuwar da take tsakaninsu kmr da da uba yake cemishi "yaushe ze shigone yaji shiru har yanzun" anan yake sanar mishi wani dan aikine yarikesa amman yadawo yanzun haka yashigi gari,dan gyaran murya yay don yanason karyar da zema paa tashiga paa din don ya sanshi da tausayi da jinkai da kuma temakon wanda ke bukata yace mishi "idan babu damuwa yana da wata friend da take neman gurin da zata fake for two days, ba yar gari baceba tana da yaro kuma sunsamu matsala da mijintane ya koreta kaga ba'a sasanta ba papa ba'a yi hanzarin barinta tatafi gidan iyayenta cikin halin datake cikiba batada lafiya ma sosai" paa abin yatabashi don yatsani yaji namiji na wulakanta mace cikin fada fada yake fadin "ai irin wannan bama seka tambaya ba Tajuddeen kakawo tanan nizan zame mata uba kabar dan iskan zezo ya samemu har inda muke abokiyarka ai yarmuce," murmushi Taj yay jin karyar shi tashiga kuma paa ya amince ya kawota yace "paa ba matsala ba takurawa daiko tana da yaro fa" yace "Tajuddeen mukabar barema wanda bamu saniba yazauna tareda mu balle kuma abokiyarka daka santa ainasan bazaka kawo abinda ze cutar dani da yarana ba," wani iri iri Taj yaji saboda yasan kalar kirki da kyakkyawar zuciyar paa se yakejin bekyauta ba da yamai karya akan yarinyar amman shikansa haka kawai yakejin yarinyar har cikin ranshi she looks very young and fragile kamata yay ace wannan tanama makaranta tana daukar darasi kamar Mehtav dukda yana kallon wannan yasan cewa Mehtav xata girme mata nesa ba kusaba.

Komawa yay ciki yatarar da nurse din se dambe suke da junior yana yan koke koke wai bazata mai wanka ba dan babyboy din dan lukutine and he is very energetic, itakuma uwar ma barci takeyi, murmushi yayma nurse din yana karbarsa daga hannunta he is very good with kids don kusan tare dashi ma sukai rainon Abeey cikin wasa ya karbeshi ahannun nurse yanamai wasa yaron yay shiru ya fara kyalkyala dariya ahaka da wayo da wayo ya wanke shi tastas yanayi yana satar kallon Islam dake barci peacefully kamar wata sleeping beauty she looks so innocent with her baby face. suna gamawa ya barma nurse junior tashiga shiryasa asababbin kayan daya fita yasiyo mishi yafito tsaf tsaf abinshi like the prince he is, wannan madarar kyawu da haske daya gada daga mahaifinsa ya saka duk inda nurse tadan zaga dashi se kaji ana kai Masha Allah tubarkallah don yaron yashiga ranta har goyashi tai harzuwa lokacin da Islam tafarka. wanka tai tafara feeding dinshi sannan dakyar ta iya shan tea mai kaurin da nurse takawo mata sbd harwani ji take da ita don Taj yamata alheri duk tinaninta matar shi cema amman kuma mamakinta baiwuce yadda jaririn baya kama da kodaya daga cikinsu ba. duk yadda taso Islam tasaki jikinta da ita kitai don ita ba mutun bace mai saurin sabo kuma tama lura da yarinyar tunda tafarka ta karbe danta ahannunta kamar batason aringa taba mata yaron hakan yasa ta barmata shi har zuwa yammacin ranar aka sallamesu. ita tabata kyautar zani tace mata tagoya shi abayanta,goyon da tamai kanshi kana kallo kasan bata saba goya yara ba don jiya tafara ma iya dabaran tagoya junior don kusan rainonshi da komai nashi uwar soro ce take yimata hakanne yasa ta sangarce babu abinda ta iyama yarin sedai tashayar dashi kawai. nurse dince tashiga gyara mata shi abayanta ta kammala tamata godiya ta rakosu har bakin mota tanawa junior bye bye Taj wani kudin ya kara mata tanata godiya harsuka bar harabar asibitin tana musu bye bye.

hanyar gidan paa yanufa yana dan satar kallonta batareda tasan yanayi ba,sai can yace mata "gidan uncle dina zan kaiki amatsayin friend dita banson kije ki fada musu something otherwise" dan kallonshi tai da gwara gwaran idanuwanta masu ladabtar da mutane yasa yadan daburce yana fadin "wai banson muyi musu magana biyune," dauke kanta tai akanshi tacigaba da kallon titi cikin son janta da magana yake fadin "atleast karnaje gidan uncle dinnawa su tambayeni sunanki infara zare ido ko baiwar Allah," batareda takalleshi ba yaji tace "I'm not your friend," murmushi yatsinci kansa dayi don tunda yake arayuwarsa be taba ganin mace me attitude irin nataba wai itafa yake temakawa amman ita ke basar dashi tana wani jajjamai aji da alama zatai jinkai ya raya aransa kafin ya kalleta tagefen ido aransa yace "with this beauty ai kadanma tai" saikuma yashiga a'uxiyya domin be sani ba ko matar aurece gata dai da yaro ko ina mijinta yake? ya tambayi kansa yana raya wana mijine zebar tsaleliyar yarinya irin wannan karama tana gararanba akan titi,amman dai don yakawar da shakkun dake cikin ransa bayason yake eyeing matar aure seya dake yace "where's your husbad? I mean juniors father?" Mugun kallon data bugamai yasa yasha jinin jikinsa kafin yace "no offense I just wanna know naga baki kirashi ba ko kun rabune, uhm?" shiru tamai babu ansa yace *can't you trust me for a bit mom junior bazaki iya amsamin ko daya daga cikin dumbin tambayoyin danake miki ba kikasani ko inada abinda zan taimaka miki dashi" "ISLAM" kawai tace mishi kanta akasa tana wasa da yatsunta daya lura kamar dabi'ar tace yin hakan "Islam" yamaimaita yana kallonta ba tareda yasan me hakan kenufi ba, "thats my name isn't that one of the questions da keke tambaya" dan sosa kai yay da yaga duk wayonshi yarinyar nan tafishi wato don karta ansa tambaya akan mijinta yasa tafada mashi sunanta, "nice name" yafada daidai suna shigewa gate na estate din gidan Engr Habib dake magrib yayi already gari yayi duhu amman ko ina da fitilu dake area dn masu dashi ne, haka kawai takejin heart dinta ya.fara beating faster in abnormal way tadafe kirjinta tana feeling restless kamar wani abun zefaru da ita,tadai daure sbd she have a very bad feeling towards abinda takeji ayanzun din,horn din daya fara dannawa akofar gidan paa ne yasa taji ciwon da yake kirjinta yakara tsananta daidai nan dan liti mai gadi ya zuge gate, Taj yadanna hancin kan motarsa zuwa harabar gidan da haske ya kenan tarwai kamar rana saboda fitulin dake ata ko ina na gidan.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote. [24/05, 19:22] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.