EHSAAS

Chapter 26

by @fatoumspassion

Adaidai kofar shiga main house din Taj yay parking, Abeey ce ta fito da gudu don sun san da zuwan shi, paa ya sanar dasu bata ma gama jira ya fito daga motar ba takarasa tana bude mai kofar murmushi takeyi kamar bakinta ze yage. Ahankali yakashe motar yana fitowa tafada jikinsa tana fadin "oyoyo brother Taj nayi missing dinka," dagata sama yay chak kamar yar tsana dake batada wani girma yana wulwulata tana ihun ya sauketa tana dariya tukunna yadireta yana Jan cheeks dinta yana gyara mata zaman medicated glasses dinta yake fadin "I miss you more Papa's Abeey," murmushi tai hannayenta tasa cikin nashi take fadin "ya hanya brother Taj, kazo muje ciki yah Mehtav cook something very delicious for you" se asannan yadago dede fitowar Mehtav daga gidan sanye da wata doguwar rigar atamfa da aka mata dinkin A shape datai matukar amsar jikinta,tadan daura karamin mayafi asaman kanta tana mai murmushi.

ba su lurada Islam dake gaban motar tayi shiru tana kallonsu ba, "The great Assistant director Taj is here" Mehtav tafada sanda ta tsaya agefensa hannu ya miko mata alamar su gaisa ta makale masa wiya cikin tsokana da raha take fadin "haram mijina ya hana bakasan ni matar wani baceba," jan kumatunta yay da yaketa kyalli yana wani glowing kamar wata amarya ga wani uban hasken da yaga tayi kamar wacca akema wankan inji yace "Mehtav waiko bleaching kika fara bansani ba, fadamin meye sirrin? naga skin dinki se wani sheki yakeyi" yafada harda dan murzawa kautar da hannunsa tai tana hararar shi dake sun saba wasa irin haka take fadin "mijinane sirrin" shida Abeey suka hada ido suka sheke da dariya yace "Abeey fadamin da alama dan kauye dai yayi agogo shiyasa lungu lungu yakebi yanata daga hannu" Abeey dariya tashiga yima Mehtav yadda yayan nasu yake mata tsiya taturo baki tana fadin "haushi dai kakeji ankasa abokinka ehen" dariya suka sheke mata dashi shida Abeey yace "Mehtav kanki akeji yanzun dai kunbar bakuwata acikin mota but later za'a fadamin who's the lucky guy" yakarasa yana zagayawa gurin mazaunin Islam bude mata kofa yay yana fadin "muje ciki kihuta ko maman Jr," Idanuwan Mehtav gaba daya suka koma wajen suna jiran ganin kawar Taj dazata fito daga cikin motar.

Ahankali ta fito daga motar, cikin wata iriyar nutsuwa kmr wata sarauniya, yaronta yana goye abayanta iskar datake kadawa aharabar gidan taja dan karamin gyalen abayar dake kanta yay baya. Mehtav dai tuni ta tsaya cak, kamar wacce aka dasa agurin, Hankalinta gaba daya yayi kan Islam, idanunta sun makale a jikin Islam din tamkar bata taba ganin wata halittar mutum irin taba aduniya. "This is beyond just beauty, this was art in human form." Wata murya take fada mata acikin kanta,kokarin gyara gyalenta takeyi already Dogon gashinta bakikkirin ya sauko ya baje har ya rufe jaririn dake bayanta don idan idonta ba gizo yakeba yakusa kaiwa har bisa cinyoyinta, yana wani irin sheki mai matukar kyau tsabar yawan dayay mata se fama takeyi dashi. Fatar jikinta kuwa ba irin bakace ko fara data saba gani ba, melanin ce amma irin melanin din da ke haskakawa kamar wanda aka saka diamond cikin duhu. irin fuskarta ba irin wacca zaka iya kalla sau daya ka dauke kaice ba, hakan yasa idon Mehtav yakasa barin kallonta,kallon kurilla tacigaba da mata tundaga fuskarta harzuwa hourglass body shape dinta kama wacca tai kanta, binta take da kallo ko zataga wani alamun cewa plastic surgery tai tasamu kalar jikin amman dake abayan jikinta yarufe ko ina na jikinta kasa ganewa tai,amman abayar ta lafe ajikinta batareda tasani ba tayi shaping dinta tana nuna duk wata baiwar diri da Allah yay mata ajikinta. Mehtav bata tabajin ta raina kanta agaban wata ya mace ba se yau gaba dayanta bazata wuce kafadar Islam ba saboda doguwar macece me cikar zati da haiba. Hada idon da sukai da ita yasa ta tsaya karema idanunnata kallo "ya Allah." Mehtav tafada tana kokarin saita kanta they are Big, almond-shaped, angelic eyes masu wani irin magnetic aura, kamar idan tana kallonka har da cikin zuciyarka take gani. Wanda bahaka bane kawai dai yadda sume atsaitsaye ne yake firgitar da marasa gaskiya agabanta.

Mehtav kasa motsawa tai daga inda take atsaye duk da tana jiyo muryar Taj yana mata magana amman samsam kasa gane me yake cewa tai saboda wani irin abu dataji yadanne mata kirji gameda kyawun Islam din, ahankali taga yarinyar tafara takowa zuwa gurinta, amma ba ajin takun takalminta ko kadan saboda tsabar nutsuwar ta, kamar walk of a beauty goddess being announced by the wind itself. Mehtav dai ta kasa motsi. Ta ji jikinta ya kame kam, Tana jin wani abu da bata taba ji ba tunda take arayuwarta kmr kishi, kmr tsoro,wani irin feeling ne na raina kai da ajin da ya wuce tunanin mutum.

Abeey kuwa zaro ido tai,cikeda exeggeration take kallon Taj tace "Wait… is this real? Taj dariya ya farayi donshi kanshi jiya kwana yay yana yaba beauty din yarinyar nan,yace "a'ah is fake" cikin gatse, Abeey tasaki murmushi tana fadin "Kai yah Taj… friend dinka ce? Kafadi gaskiya Ko dai angel ka dauko daga heaven bamu saniba?" Taj ya dariya ya fariyi yana daga girarsa yana cewa, "kice antashi kanki mutuniyar," Jinjina kai Abeey tafarayi takarasa gaban Islam da Mehtav da suka tsaya daf da juna yanzun tana fadin "hey I'm Abeey" tana mika mata dan karamin hannunta tana murmushi, murmushi itama taima Abeey din tana mika mata nata hannun suka gaisa tace "I'm Islam," dan waro ido Abeey tai tana kallon Mehtav jin sunanta iri daya da Islam dinsu amman ganin Mehtav bata wani nuna zumudin hakan ba yasa jikin Abeey ya danyi sanyi tace "nice to meet you Islam, muma munada Islam anan gidan amman namiji ne zaki ganshi nan bada dadewa ba suntafi masallaci tareda paa" takarasa cikin surutu irinna fadi ba'a tambayeka ba na Abeey, jinjina kai kawai Islam tai don batasan mezata sake cemata ba,bata wani iya magana da yara ba,takalla Mehtav da bata cemusu cikanku ba kawai tasakar mata murmushi,wanda haka kawai Mehtav taji is not fair just murmushi yay mata kyau haka,jin siririyar muryata tai tace mata "Hi" Murya ce me cike da nutsuwa mara hayaniya,gatanan very soft, bold, seductive dakuma class. Mehtav kasa amsawa tai da fari ta dan jinjina kai, sannan cikin karamar murya ta ce: "You're… beautiful." Ita kanta batasan hakan yafito daga bakinta ba seda tafada dake Islam bawannan ne karon farko da ake cemata tanada kyauba seta dan mata murmushin yake kawai dayay looking a idon Mehtav kamar wani sexy smirk me cikeda nuna isa da jin kai, tace mata "So I've heard, thank you" Tana mika mata hannayenta alamun su gaisa. Don ita kuma haka kawai taji Mehtav din ta kwanta mata mika mata hannunta tai suka gaisa idanuwanta suka sauka akan wani diamond ring dake hannayen Islam din, with infinity shape dayay matukar amsar hannayen ta masu tsayi marasa girma sosai,se asannan tadago tana kara kallon fuskar Islam tace mata "barka da xuwa,sunana Mehtav," "Mehtav" Islam ta maimaita acikin ranta tana dan mata murmushi kadan, Abeey tace "tohm yanzun kinga yah Mehtav tayi kawa, kawai kuzo mu shige cikin gida tun kafin papa yadawo ya tarar damu anan, yace munbar bakuwa awaje" Taj yace "exactly Abeey, kuma tagaji she needs some rest" nan gaba dayansu suka rankaya zuwa cikin gidan. Mehtav se satar kallonta takeyi da suka shigo main parlour din gidan cikin nutsuwa. Abeey tana taiwa Taj surutu tana bashi labaran makaranta da shirye shiryen bikin dasuke yi,yana sauraronta, Mehtav jefi jefi take saka musu baki,islam dai tayi shiru abinta bata cewa komai she just had that silent grace, irin wanda ke speaking fiyeda words. Inna ce ta taresu, fuskarta cike da annuri da farin cikin ganin Taj datai, ta bude hannayenta da farin cikin gaske tana cewa: "Lale marhabun! Ashe Tajuddeen ne agarinnan, ina bakuwar taka da ake tamin zancen zuwanta tun dazun?" Takarasa tana kallon Islam data tsaya daidai gefen Taj, ba ta ce komai ba,don bata cika gane hausar da tsohuwar takeyi ba.

Mehtav taja numfashi irin hmmmmm dinnan aranta tana raya ina Taj yasamo wannan yarinyar me dan banzan girman kai kawai don taga tanada kyau taketa jama mutane aji,saboda yadda take kallon iya ya kular da Mehtav din kamar wacca taga dodo.

Itakam inna ba abinda ya dameta donta fahimci yarinyar kawai akwai rashin saurin sabo atattare da ita,da kanta takarasa wurin datake tsaye, da murmushi akan fuskarta ta kalli Islam cikeda kulawa tace "Ke yar kyakkyawa… sunanki fa?" Islam ta sunkuyar dakai kadan donta fahimci sunanta data tambaya, ba tare da murmushi ko karin magana ba, ta ce a hankali "Islam." Inna ta dan kalleta cikin mamaki tana kallon Abeey da Mehtav tace "kunji abin mamaki sunanta daya da mutuminku dan rigima? Abeey tace "nima inna nayi mamaki fa sosai sunansu iri daya yanxun tayaya zamu ringa banbancesu"

Inna cikeda farinciki don ita jaririn bayan Islam takeson dauka don akwai su dason yara tace "Ah tini za'a banbanceta ai ita se muringa kiranta da maman baby macece ko namiji ma mugani,bari inga kyakkyawar fuskar sa…" Ta karasa gefen da Islam take tana kokarin kwanto jaririn dake bayanta, amma Islam seta dan janye jiki a hankali,saboda kwata kwata batada yadda ko kadan, kanta akasa cikeda girmamawa tace " uhmmm....Yana bacci… and he doesn't like it in aka tasheshi rigima yakeyi." "Ohhhh" inna tafada tana dan leka fuskar junior tace "a'ah dan balarabe da alama za'ai rikice kace,kasha barcinka anjima na daukeka" tafada tana dan shafashi,da yasa Islam tadan kara matsawa daf da Taj don kar inna ta cigaba da tabashi. shishi kadai yafahimci cewan batason ataba mata yarone,yalura batara yarda kwata kwata akan danta. Ya dan lumshe ido yana murmushi kadan, aransa ya raya He should've warned them about it.

Cikin son bagarar dasu kada su gane hakan yace "Bari dai tafara hutawa ko agajiye takefa munsha hanya, But wait Ina Paa?"

Abeey ce tai caraf tana fadin "bakaji nace Sun je masallaci da handsome Islam dinmu ba, sun ce zasu dawo bayan Isha'i."

Taj ya jinjina kai, sannan ya kalli Mehtav yana fadin: "Please Mehtav, take her to your room, let her freshen up and rest small. I'll go get her things from the car."

"Okay," Mehtav ta amsa da murmushi, takalli Islam tana fadin "muje ko," jinjina kai Islam tai Mehtav tai gaba tana binta abaya, Mehtav da taji bataji takunta ba seta dauka ko bata taho bane tadan juya kuwa takusa cin karo da ita don tana biye da ita, murmushi tamata kawai tana juyawa zuciyarta na tsananin bugawa tana mamakin yadda someone can look this beautiful, Ba makeup, ba lashes, ba wani show off clothes, amma every inch of Islam was glowing. Tsantsar kyau. Kyau mai nutsuwa. Kyau marar hayaniya. Kyau wanda koda mace ce ta kalla, zuciyarta seta buga kuma tasake kalla din.

Mehtav ta bude kofar dakin sannu a hankali, tana mai juyowa tana cewa "Please feel at home, wannan dakinmu ne nida Abeey and this will be your room too, paa yayi deciding Abeey zata ringa kwana gurin inna har lokacin da zaku sasanta da me gidan"

Takarasa cikin son janta ajiki don dukda abinda taji tanaji akanta duk seta kore shedan daga zuciyarta saboda batason takejin kishi ko hassadar kyawun wata yar uwarta mace ba tareda ta taba mata komaiba arayuwa, amman me se taga Islam ba ta ce komai ba, kawai ta dan daga kai da wani murmushi mai kyau wanda ba kowa ke iya yi ba.

Se taji Dakin ya cika da kamshi, kyakkyawan scent na vanilla da clean linen. Amma wani sabon kamshi ne ya shigo dakin da zuwan Islam, irin kamshin da ba perfume ke fitar da shi ba,but aura ce.

kawai ta tsaya daga gefe tana kallon yadda Islam ta janye mayafin rigarta a hankali, gashinta yazube gaba daya abayanta, tashiga kwanto jaririn a nitse tana kara nannade shi da zanin ta yadda Mehtav bazata ma iya kallon fuskar saba ta kwantar dashi saman gadon Abeey data fara gani afarko har lokacin kuma barci yake be tashiba tadan kara gyara mai kwanciya, sannan ta zauna a gefen gadon, Sai kuma ta juya da kanta kadan,da daddad'an muryarta tace "Thank you."

Mehtav ta daga kai kawai tana jinjina mata,itafa tasan tanada kyau, amman ba za ta iya musanta cewa akwai wani kyau da class da Islam ke dashi da ba za ta taba iya kaiwa ba. Kamar wacce ta tsara kanta da kantafa take ganinta, Skin dinta ba kawai melanin bane ba, it's polished obsidian, flawless. Ba za ka iya cewa African ce kai tsaye ba, amma kuma ba za kace ba itan bace. Wani irin shape gareta, hourglass na asali, ba surgically enhanced ba. Tsayayye,kuma Cikakken figure. Amma hakan ma ba shine babban abin kallo ba…

Idanunta sune, they are Angelic. Shineless. Calm. Amma idan suka kalle ka sosai, sai ka ji kamar kana tsaye gaban alkalin wata supreme court.

Mehtav ta goge goshinta da bayan hannuntan jin gumi na tsatstsafo mata,dukda sanyin AC dake dakin se kawai tace "bari na kawo miki towel da sponge"

Islam ta gyada kai kawai.

"Ko menene wannan yarinyar take da shi… it's beyond beauty. It's power, anya mutum ya Taj yakawo man kuwa" Mehtav tashuga rayawa aranta sanda tanufi kofa.

Tana fitowa, ta ci karo da Abeey dake shirin shiga, sai ta janyo ta gefe cikin murya kasa kasa don karta jiyosu tace

"Abeey… wait, please... waiko kinga abinda nagani dake tattare da matarnan kuwa? This Islam?"

Abeey ta kalleta da dariya, tana cewa: "Wai me kike nufi ya Mehtav? Metai kuma?"

Mehtav ta kad'a kai tana fadin: "No. I've seen many beautiful women in my life… models, celebrities, makeup artists… but this girl? She's another thing. Ba kamar mu bane. Ko dai nice nake ganin haka,kamr fa tafi Islam dinmu kyau kawai hasken fata ze nuna mata…" Takarasa suna leken cikin dakin tana zaune inda tabarta tanata kallon danta dake barci Mehtav tadaura da "kinsan me abeey For the first time, I feel like my own beauty is just ordinary."

Abeey dan tabe baki tana fadin "Ayyah yah Mehtav ki gode Allah kema da kyan dayay miki anyi ittifakin kaf fa estate dinnan ba budurwar data kaiki kyau kuma ke kanki kinsan kina da kyau mutane dayawa suna fadan hakan,kuma kinfita haske."

Tsaki kawai Mehtav taja ganin Abeey takasa fahimtar inda tadosa kawai se tace "bazaki gane bane,Abeey ni nace miki ban gode Allah da yadda yayi niba, kawai dai ina mamakin nata kyawunne da bantaba ganin irinshi ba da kalar attitude dinta kamar wata queen nina gode Allah ma da matar aurece da bazan yarda tafito agaban fiancée dina hakaba," dariya Abeey tafara tace "yah Mehtav magana dai tafito kice kishi kikeyi, karfa ki damu da Islam shifa abinda kike tinanin ze kalla baya taba kalla tohm mutumin da bama abinda yasani har tayaya ze iya banbance tafiki kyau ke kadaice azuciyarsa pls kicire duk abinda kikeji shi nakine ke kadai har abada kinji,"

dan murmushi Mehtav tai tanajin dadi kalaman Abeey din sosai kafin tace "nifa amman ina mugun kishinsa banason inyi sharing dinsa da kowa nafison kawai it should be me & him,just us" Abeey cikeda tsokana take fadin "inyeeee love manya," Mehtav takama hannayenta tana fadin "karki shiga bare ki takura mata da fadi ba'a tambayeki ba zo muje"

anan suka wuce Abeey tai gurin Taj Mehtav tawuce dakin Islam don ta dakko mata sabon towel da sabon sponge don yanada su dayawa tasiya mai a shopping din dasukai, bata sameshi adakin ba ko ina tsaf tsaf se kamshi yakeyi haka ta tarar da dakin saboda ita dakanta take gyara mishi kullum bata wasa da duk abinda ya shafesu kuma hakan nakara mata matsayi na musamman azuciyarsa saboda shi mutum ne data lura yanada tsafta baya kaunar kaxanta ko kadan,tana dakkowa tafito takoma dakinsu a inda tabar Islam anan ta tarar da ita.

"Here… I brought a fresh towel and sponge The bathroom is clean too. I can warm some water if you want," ta faɗa tana ajiye komai a bakin gado. Islam ta kalli kayan a hankali, sannan ta ɗan ɗaga kai tace "Thank you."

Wucewa bandaki Mehtav tai dakanta tahada mata ruwa mai dumi a bathtub tafito tana fada mata, godiya ta sake mata batareda tamike ko tayi yunkurin shiga bandakin ba don jira take Mehtav tafita tabata guri domin ita sam sam bata saba da sharing room dakowa ba inba mijinta ba,tunda tataso bata taba kwana daki daya ko tai sharing bathroom da kowa ba seshi,don haka kawe sharing ma kyankyami yake bata sedai a situation irin haka da babu yadda zatai.

Mehtav ta tsaya ganin Islam bata motsaba,taki barin dakin sai satar kallon jaririn dake kwance agefen islam din takeyi "He's adorable… Is he still sleeping?" Ta tambaya tana kallonta, Islam ta gyara zamanta kadan, bata ma kalli Mehtav ba, sai tace da wani irin salon nutsuwa "Yah! Let him sleep." Mehtav jinjina kai kawai tai tana mamakin attitude din yarinyar wacca ta tabbata ta girme mata,amman take basar da ita haka ita kuma masifar son yaran datake dashi baze barta tai zuciya tabar mata danta ba,seta karaso daf dasu tana dan kallon kafafuwansa da suka fito daga cikin zanin farare kal tace "Zan iya ɗaukar shi? Just to help while you go freshen up…karki shiga toilet yatashi yay kuka" Takarasa cikin tausasawa, tana fatan samun yardar Islam. Zuciyarta na ɗokin daukar jaririn burinta kawai taga fuskarshi don da alama zeyi kyau kmr babarshi.

Islam ta juya kai a hankali, idanunta suka tsayawa kan Mehtav kamar wadda take nazarin wani abu Sai kawai tace da murya mara hayaniya: "No. I can handle him."

Mehtav ta tsaya cak. Tana kallon yadda ta tsaya ba tare da wani Jin kunyar idon taba tace mata no,aranta tace tayi kala da me cinye jariraine data hanata daukar shi "Okay…" ta faɗa a hankali tana duban jaririn da ke cikin zanin Sai ta ce: "At least, what's his name?inba damuwa" Takarasa adan hasale saboda taji haushin hanata daukarsa datai.

Islam ta ɗan juyar da kai kamar wadda bata da sha'awar amsa tambayar. Sai tace: "Junior." Mehtav ta ɗan rufe baki da hannunta cikin yar dariyar rainin hankali tace "Junior kawai? C'mon… he must have a proper name." Islam ta nisa, ta kalli jaririn na ɗan lokaci kamar wadda ke tinanin wani abu acikin ranta, Sannan cikin sanyi ta ce: "His name is… EHSAAS." Da sauri Mehtav ta kalleta, tana maimaita sunan "EHSAAS?" Ta murmusa, tana jin yadda sunan ya taɓa zuciyarta. "That's so unique… it sounds like something deep." Islam ba ta ce komai ba. Sai kawai ta miƙe, ta ɗauki towel ɗin da Mehtav ta ajiye, sannan ta ce da ita kai tsaye "Excuse me. I'll just freshen up."

Ta wucewa ba tare da tasake mata magana ba, har ta shige cikin bandakin,se take ji kamar kawai taje tadau yaron duk abinda zefaru ma yafaru se kuma tatina gara dai karta daukar mata yaro tunda tanuna battaso kartai disrespecting din wish dinta.

ficewa tai tawuce kitchen tana kara duba dinner data kammala shiryawa tuntuni shirya table din tashiga yi tanajin Taj yabawa Abeey wani shopping bag yace "takaima Islam din" Abeey tawuce cikin dakin batasan zaman me Abeey tayi ba don har su paa suka dawo bata fitoba,se juyo muryar paa tai yana fadin "Look who the cat dragged in… my Taj is home." Taj ya miƙe cikin girmamawa, ya rungume Paa cikin ladabi da ɗan dariya: "Paa. I missed you." Daidai nan idanunsa suka sauka akan EHSAAS dake bayan paa cikeda dan mamaki saboda se yanzun yake ganinshi dakyau afili a zahiri ba'a hotoba har zece EHSAAS kuma seya fasa ya tambaya "Is that… Islam?" "Yes," Paa ya ce yana juyowa, yana kallon EHSAAS da hankalinshi gaba daya yayi kan Mehtav dake jera abinci don haka yake, baya gajiya da kallonta wata irin soyayya sukeyi me sanyi Paa ganin abinda EHSAAS din yake ya dafashi yana fadin "Our Islam," ya ƙarasa yana murmushi, sannan ya juya yana cewa: "Taj, meet Islam. Islam, this is Taj, my boy, the assistant director himself." Taj ne ya miƙa mai hannu domin suyi musabaha, EHSAAS ya karɓa amma idanunsa ba akan Tajuddeen suke ba… sai kan jaririn da yaga Abeey tafito rike dashi har dan nishi nishi takeyi don ya mata nauyi gata ba wani karfi ba amman don karambani seda tadakko shi. Mehtav tagwalo ido tana mamakin yadda akai waccan mara mutuncin matar tabar Abeey tadakko mata danta, ya tashi daga barci idanuwansa tangararau abude masu kalar grey ga kumatukansa subu subu kamar ansaka abu aciki,yan kananun bakinsa gasunan jajir dasu harta da gashin kansa kalar na larabawane akwance yake luff saboda hularsa data zame garin daukarshi da Abeey tai. dasauri Mehtav takarasa tana fadin "keh Abeey wayace kidakkoshi ita tabaki shine da zaku dauko mata yaro," Taj yace "Abeey maman Jr tasan kin dakko mata yaro?" "nace matafa xanyi wasa dashi tacemin tohm kuma munata wasa kawai se naga tayi barci shine nafito dashi kawai," Mehtav tai dariya tana fadin "nifa ince nasan dai bazata baki danta ba dazun ko innama hanawa tai balleke jitake dashi kamar gwal," "Masha Allah" inna tafada tana karasowa tasa hannu ta karbeshi daga gurin Abeey tana fadin "tubarkallah Masha Allah dole taki bari akarbeshi ai wannan se baki ya cinyeshi irin wadannan yayan daman iyaye kewa yara kashedin boyeshi kila itama anmata ne," takalli Abeey tana fadin "kidena dakkoshi haka bata saniba karkije ki kadaku gaba daya kinga yamiki girma," inna tashiga mai wasa da rawa yana dariya.

Mehtav se take ganin kamar ita kadai take ganin dimple din dake cheeks din yaron yana lotsawa irin na EHSAAS tadan murza idonta tana kara kallon yaron kafin ta juyar da idonta kan EHSAAS aranta tace "ikon Allah," Paa yace "masha Allah wannan shine yaron abokiyar taka Taj" jinjina kai Taj yay yana fadin "shine" yace "tubarkallah da alama dai mamar tashi balarabiyace dubi da jajir sekace Islam namu" yafada yana dafo Islam daya kure yaron da kallo yanajin kirjinsa na bugawa kamar ze faso kirjinshi, Abeey ce ta kyalkyale da dariya tana fadin "badai balarabiya bace don nima nafita fari sedai in babanshi" takarasa tana wucewa dining, Paa yace "Taj mujeko kaci abinci nasan ka kwaso gajiya," Taj yakalli Mehtav yana fadin "ita taci abincinne?" girgiza kai Mehtav tai tana fadin "bata ciba, bakaji Abeey tace tayi barciba ko in tasheta" tafada cikin fushi fushi yace "calm down Mehtav" ya dafota cikin rada yace "naga kamar kishi kike da ita I'm all yours fa, karki damu" yafada yana mata murmushin rainin hankali da yasa takaimai naushi a ciki da sauri yakauce yana fadin "bani nakar zomanba rataya aka bani kardai kije kitasar mana maman junior tafi karfinki, ta ratayemu mundauko mata da batareda tasani ba" dariya suka shiga yi ita dashi domin da alama shima yagane weirdness din bakuwar tashi sosai. suka zauna saman dining se alokacin ta lura da EHSAAS dake tsaye gefen inna mutumin dake tsoron inna intana gabas kudu zeyi intana arewa yamma zeyi, yaushine agefen inna se leka jaririn yakeyi yanason yace tabashi amman kuma besan yadda ze rike shiba,inna tajuyo tana kallonsa tace "a'ah, malam Islam ko zaka daukeshi ne?" dan jinjina kai yay yana sakin murmushi tace "toh kawo hannunka" ahankali yamika mata hannunsa nadama tace "a'ah bahaka akeyi ba biyu zaka hada, toh zauna karka yardashi" dasauri yazauna saman kujera yana hada hannayensa aguri guda ta daura mishi yaron wani irin annashuwa yaji yanaji har cikin ransa idanuwansa cikinna yaron dake kallonshi yana dan kifta ido yana motsa baki, "dan baby" EHSAAS yafada yana dan girgiza junior daya fasa mishi ihu alamar rikon da yamai bemishi dadi ba. gaba daya EHSAAS rikicewa yay yana kokarin sashi akafadarsa amman besan yadda akeyi ba,inna tana kallonsu cikin al ajabi yadda kasan da da uba domin da ace islam da Mehtav sunyi aure ta tabbatar zasu haifi wannan dan, jin yaron yaki shiru yasa inna ta karbeshi Mehtav closely take watching dinsu tana mamakin irin wannan resemblance din,inna tace mishi "Islam jekaci abinci zan kula dashi," yamike yana kallon babyn daya lafe jikin inna yadan shafa kansa harya juya ya kuma juyawa ya tabashi sekuma dai yakoma yazauna kusa da Mehtav. kallonshi Mehtav tai yana grinning ear to ear,ganin tana kallonshi yace "his cute" yafada yana nuna mata junior tace "yes he is kana sonshi ne?" dan jinjina mata kai, tashiga murmushi aranta tana fadin "xan haifa maka irinsa in sha Allah nanda shekara daya," cikin nutsuwa sukaci abincin su inna kuwa tasamu da, don dakinta ma tawuce dashi, Abeey tabi bayanta donji take kamar abarmusu junior na har abada, EHSAAS yaso yabisu Mehtav ta tareshi da batun shirye shiryen bikinsu dake gabatowa sunata zabar interior design na gidansu da Paa yabasu a maitama amman hankalinsa gaba daya yana kan junior. Islam daman allurar da aka mata da magungunan da tasha akwai nabarci shine yasata taketa barci har Taj yabar gidan bata saniba,innace ta goye junior haryay barci se wurin 12 ya farka aka kaishi gurin Islam aka tayar da ita daga ita se Mehtav adakin already tasaka daya daga cikin riguna guda uku da Abeey takawo mata wanda Taj yasiya mata,tai feeding dinshi takara lallashinsa yay barci,kasa komawa barcin tai don alluran sun saketa data kwanta se tashiga mafarkan Grandma iri iri tana tina abubuwan dasuka faru dasu awaccan ranar,ga yunwar da takeji duk Mehtav na lura da ita cikanki bata cemata ba, taga tamike tashiga toilet ta dauro alwala tafara kiyamul layl,tun tana iya kirga raka'a nawa tai harta bingile anan tana barci Islam nata Sallah. data kammala tazauna tashiga bitar haddar karatun Qur'ani datai acikin zuciyarta tana taiwa grandma da EHSAAS addu'ar samun rahmar ubangiji tana kuma rokon Allah yakare mata danta yatsare mata shi.

da asubar fari taji wata irin iska me karfi tana shigowa cikin dakin dake tagar dakin abude take kwankwasa kofar dakin taji anayi taji muryar wani dattijo yana kiran "Mehtav, Mehtav lokacin Sallah yayi," kallon Mehtav dake barci dafa'an tai kanta karasa kusa da ita tana dan taba kafarta ahankali kamarfa zata taba wuta sbd ita batason body contact dakowa arayuwarta se selective people data saba dasu, dake batada nauyin barci tabude idonta tana dan kallonta sama sama jin muryar paa yasa tamike tana cemishi tatashi se asannan shida EHSAAS suka wuce mosque.

Islam ce tafara komawa toilet ta sake daura alwala tafito kafin Mehtav ma tashiga tayi,kafin tafito tasaka hijab dinta kusan tare sukai sallar asubar suka zauna kowacce tana azkar dinta acikin zuciyar ta.

iskar da akeyi mekarfi tana bugo tagar dakin tasa junior fara motsawa da sauri Islam tamike tana nufar tagar don ta kulle labulen na biyo ta yana rufe fuskarta tasa hannayenta tana yaye farin curtain din kamar amafarki kawai taga giftawar wasu maza guda biyu wanda ko asume aka tasheta aka tambayeta waye ya wuce da bayansa kadai tasan waye din tsaf dukda bataga fuskarshi ba figure din mijinta take gani saboda ginannan kafadunsa ba kowana namijine yake dashi ba. tashiga leka wajen babu kowa,sosai kirjinta yake bugawa irin bugawar da intaga EHSAAS ne kadai takeyi she's feeling restless haka kawai, ganin kamar gizo yake mata saboda irin kewarshi datai ya sanya kawai takulle tagar tadawo dakin tazauna saman gadon Abeey gefen danta tana zuba tagumi, tana kallon Mehtav ta nannade sallayar datai sallah takoma saman gadon takwanta da alama barcinta zata koma be isheta ba.

Islam gaba daya babu barci ko daya a idanuwanta kirjinta fass fass kawai yakeyi,kallon agogon dakin tai batasan har lokaci yaja hakaba taga karfe bakwai wai hartayi, ahankali taji ana knocking kofar dakin kamar ba'a son kowa yaji,kwankwasawa taji ancigaba dayi kamar tatashi Mehtav se kuma tafasa tamike takarasa jikin kofar bugun zuciyarta na tsanantawa, "open the door yah Mehtav" taji yana fada kasa kasa, kunnuwanta tadan bubbuge saboda tanason ta tabbatar da muryar wanda takeji din amman ganin kamar baji take dakyau ba yasa kawai tamurda tana bude kofar dakin yana kai hannayensa ze sake knocking. idanuwanta ne suka sauka akansa yana sanye da wata jallabiya mai maiko brown colour datai matukar amsar kalar fair skin dinshi vividly take kallon cikin grey eyes dinshi dashima ya jefa nasa idon cikin nata yana kallonta cikeda confusion,jitai numfashinta yakasa wucewa ta kirjinta,kirjinta yatsaya chak tana kallonshi cikeda abinda ta kasa fassarawa tana tantamar anya wannan ba irin daya daga cikin mafarkan data sabayi bane ba. shikuma wani irin blackout yasamu acikin kwakwalwarsa nadan lokaci dara daran idanuwanta dayake kallane suke dawo masa cikin siffofi da shiga iri iri dakallo kala kala wanda ta tabai mishi irin wannan abaya,those Angelic eyes baze taba iya mantawa dasuba.

hannayenta narawa bakinta yakasa buduwa ma bare tai magana takai hannayenta saman fuskarshi daya qame kamar wani statue yana kallonta,tashafa fuskarsa abinda betaba bari tayi acikin mafarkan da takeyi ba,wani irin lumshe ido taga yayi saboda wani irin sanyi dayaji ya sauka acikin kirjinsa.

amman kwakwalwarsa juyewa takeyi cikin zafi zafi take wani irin masa forwarding wasu irin abubuwa da suka shude acikin rayuwarsa muryarta na rawa kamar zata shide tama kasa fitowa take fadin "my sire" bata ankaraba kawai se ganin zubewar mutum tai agabanta yafadi babu numfashi, Abeey dake bayansu wanda fitowarta tana kunkuni tana sanye da uniform agabanta komai ya wakana tafasa kara tana kiran sunan Islam. itakuma Islam kasa motsawa tai kawai tazuba mishi ido yadda ya sume agabanta kmr ma yamutu baya numfashi take gani kuma takasa gasgata gaskiyane ko mafarki amman ihun da Abeey tacika gidan dashi tana karasowa tana jijjigashi yasanya tafara gane wannan ba mafarki bane wani irin reality ne dabata taba tinanin ze iya faruwa arayuwarta ba. fitowar Mehtav wadda ta bangajeta saboda yadda tatsaya abakin kofa takara dawo da ita hayyacinta Mehtav kokarin dagoshi take tana fadin "Islam Islam wake up meya sameka? Abeey me yasameshi?" tafada dakarfi cikin karaji tana kallon Abeey,daidai paa da inna suna karasowa don babu wanda ihun Abeey din be.taso agidan ba, Abeey tana kuka tashiga nuna Islam tace "itace, he was fine standing there tanuna bakin kofa,she just touched him and he fainted"

takarasa tana fasa ihu tana jijjigashi "Islam katashi pls karka mutu kabarmu I can't leave without you," Mehtav cikeda rage na fushi ta juyo dama kuma gashi hankalinta be kwanta da yarinyarba take fadin "what did you do to him?" Are you a witch? mekika mishi nace mekika mai?" takarasa cikin masifar data gama dawo da Islam hayyacinta, da sauri tai kan EHSAAS zata tabashi Mehtav tarike hannayenta tsam tana fadin "don't you dare touch him ina ruwanki dashi, meye ya hadaki dashi zaki fadi mekika mai anan gurin koh sena miki abinda kikamai kasheshi kikeso kiyine," hawayene kebin kuncin Islam ita bata Mehtav takeyi ba ta EHSAAS dinta dake kwance takeyi ta fizge hannunta cikin na Mehtav tana sake kaiwa gurin EHSAAS wannan karon duka hannayen biyu Mehtav tarike tana hankadata baya "don't you dare touch him again," tana fadar haka takoma kanshi tana kiran sunansa takalli paa tana fadin "let's take him to the hospital paa baya numfashi fa" muryarta na rawa gaba daya tarikice paa yace "no bari mu kira kafaya aibanajin komunje yanzun tafito a asibitin" Yakarasa yana nufar dakinsa don dauko wayarshi, inna ba abinda take maimaitawa se innalillahi wa inna illahirrajiun tana kallonsu. Islam da rarrafe takaraso zata kama EHSAAS Mehtav zata sake tureta tadago tana watsa mata gwara gwaran idanuwanta dasuke ladabtar da mutane da Mehtav takasa iya turata,cikin rawar murya take fadin "don't touch Islam again inba hakaba zakiga other side of me,"

Islam watsar da hannayen Mehtav daga kokarin taba jikinta datake tai tana nunata da yatsa cikeda fushi da damuwar halinda EHSAAS yake ciki take fadin "do not cross your limit, inba hakaba cikinmu zakiga other side din waye is the worst and you don't even know him to even start with, shidin EHSAAS ne, nice Islam his other half" takarasa tana rungumoshi cikin wani irin kuka dawani iri emotions wanda bazata iya fassarawa ba ta daurashi saman kirjinta tana sakin wani irin maraitaccen kukan da duk wanda ke sauraronta indai da imani akasan zuciyarsa seya tausaya mata.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote [25/05, 20:18] Fatima Rufa'i Nasidi: It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.