Chapter 27
Kiran da Taj yaji ana yi masa babu kakkautawa ya sanya yay saurin bude ido daga barcin gajiya daya koma bayan sallar asubah. da dan hanzari ya mike zaune yana daukar wayarsa dake gefen gadonshi akan drower mamaki ne ya kamashi ganin director general ne dakansa yake kiranshin. harta katse, cikin hanzari yabi kiran da ba'a wani dau lokaci ba ya daga, kamar yana gabansa cikin girmamawa suka gaisa,yana tambayar sa ina yashige anata kiransa baya picking? yace mai "barcine yadaukeshi tun bayan dayay sallar asubah" ta dayan bangaren yaji director general yana fada mishi "akwai wani aiki mai mahimmanci da yake bukatar ya saka shi kuma da akwai bukatar yakoma maiduguri yau yau dinnan makuwa" dan zaro ido Taj yay kamar yana gabanshi domin be cika son sha'anin zuwa borno ba saboda hadarin dake tattare da aiki agarin kullum cikin tashin hankali suke musamman a yan kwanakinnan. jin Taj yay shiru yasa director general yace mishi "aikin sirrine don haka shishi kadai yayarda dashi daze mishi wannan aikin ba tareda manema labarai sun saniba, yace anraba aikin wa duk wata hukumar tsaro datake Nigeria harda external forces ma, yazo office don ba maganar da za'ayi awaya baceba," ansa masa yay da "gashi nan zuwa kawai" domin ba ze iya mishi musu ba yasan kuma tunda ya bukaci yaje din abune mai mahimmanci.
minti talatin kacal yanbashi yashirya yay reporting to work a gurguje Taj yamike ya fada toilet yay wanka da ruwan sanyi yafito yashirya kansa cikin black suit mai kyau wacca ta matukar amsar siririn jikinsan da babu rama kwata kwata ajiki amurde yake saboda kalar training din daya samu matsayinsa na jami'in tsaro.
be tsaya ko yin breakfast ba yafice 10min drive ne ya kaishi asalin office dinnasu dake daman basuda wani nisa da gidajen ma'aikatan, tunda yashiga yake amsa gaisuwar juniors dinsa har ya karasa office din DG straight akaimasa iznin shigowa da yake ansan dashi yakarasa yana sara mishi murmushi director general yay yana fadin "I like how responsible you are.." yana kallon agogonshi yace "cikin 30 min din dana baka ko minti daya baka karaba sema rage two minutes dakai AD Taj Bash have a sit pls" yakarasa yana nuna mai ma zauni dake kallon kujerarshi.
zama yay yana dan mai murmushi wani blue file ya ajje agabanshi yana mai masa iznin budewa Taj yasa hannu yana budewa hoton Islam yafara cin karo da ita cikin wata irin shiga ta alfarma wanda kana kallo kasan sarauniyar wata shahararriyar daulace hannayenta cikin na EHSAAS da dan madaidaicin ciki a jikinta, yadam tallafota tafiya sukeyi da alama bama susan andau hoton ba,don shine hotonta babu nikab kadai dasuka iya samu. cikeda rudewa ya dago ido yana kallon director general wanda be lura da yanayin saba y ashiga masa bayanin cewa "sirikar sarkin NURISTAN ce kuma sirikar sarki Abdul Aziz,sunanta Princess Islam bint Abraham ta bata kwana uku da suka wuce a jihar borno Maiduguri saukarta kenan daga NURISTAN, zuwanta na farko aka farmaketa akwai jaririn danta atareda ita da kakar mijinta wacca aka tsinta gawarta,sannan jaririn yaron masarautar NURISTAN bata taba bari camera tadau hotonshi ba amman dai yarone da baze wuce wata uku zuwa hudu ba namiji, annemesu anrasa ba'a son manema labarai susamu labarin hakan don ze iya taba mutuncin masarautun guda biyu musamman borno dasuka kasa protecting dinta," Yadora mai da "amman yafi zargin garkuwa akai da ita dukda ance bata san ko ina agariba tabbas da tana free da tayi yunkurin neman temakon backup daga masarautar borno amman har yau shiru," yace "Taj wannan aikin da kake gani idan harka zama successful ze iya canza rayuwarmu nidakai baki daya, za'a kara mana matsayi sannan zamu samu tarin alherai masu yawa daga dukkan masarautar guda biyu banason ace police ko military sun rigamu samun wani information dangane da yarinyar da dannata saboda magana ake maka tacewar jaririn shine current crown prince na NURISTAN baki daya tun bayan rasuwar mahaifinsa,"
wata irin zufa Tajuddeen yaji tana tsatstsafo masa kawai abinda ya aikata yake tinawa yana tina request din paa na kin bari kowa yasan EHSAAS na karkashinsa har se lokacin daya dace "what did he just did? yadau matarsa kaco kam yakai gidan innalillahi wa inna illahirrajiun yake furtawa acikin ranshi. director general dayaga Taj kamar is tense yace mishi "AD lpy kuwa?" dan girgiza kai kawai Taj yay cikin kokarin tattaro da nutsuwarsa yacema DG "lpy lau kawai dai labarinne ya bashi mamaki dahar yanzun manema labarai basu samuba," DG yace "aisu dakake ganin masu mulkinnan se abinda suka ga dama suke bari asani kuma idan har maganar nan ta tsallaka kasar NURISTAN tayadu akwai kura mai girma saboda ana zargin ma jin abinda yafaru sarkin yayi collapsing kasan kuma inbaida heir what can happen irin jinin sarautar nan basuda imani ba karamin aikinsu bane sukarasa shi," dan jinjina kai kawai Taj yay.
Allah Allah yake kawai yayi dismissing dinshi yatafi gidan paa ya gyara kwabar dayay don ya tabbatar zuwa yanzun kila Islam taga mijinta. bayanai masu mahimmanci wanda yake da bukatar sani DG din ya babbashi ya kuma cemai sauran information din duk suna cikin file din inya dudduba,ticket din zuwa borno yabashi yace gashinan zuwansa da dawowarsa za'ai sponsoring kuma inyaga dama yahada team din dayake bukata dazeyi aiki dasu jinjina kai kawai Taj yay yana mai godiya abisa yarda dashi dayay yadora shi akan wannan aikin me mahaimmaci kuma ko kadan be nunama DG cewar yasan inda Islam takeba har ya sallameshi,bawai don beyarda dashiba sedon yanason yafara tackling issues din dake agidan paa yanzun.
tafiya yakeyi amman gaba daya hankalinsa bayya gurin attitude din yarinyar since day one yake tinawa she doesn't look like a common girl, rashin yardarta, kaffa kaffarta duk wannan bayanin ya amsa mai komai, so she's a Princess no wonder. seyaji kuma yana tausayawa rayuwar karamar yarinyar he wonder how she coped with it ta boye komai acikinta batareda tayi sharing any of it dashiba,lallai tanada wayo da experience.
yana shiga motarsa ya ajje file din agurin me zaman banza straight yanufi gidan paa yana me rokon Allah yasa the worst doesn't happen don besan idan suka ga juna abinda ze faruba musamman EHSAAS da yake baida lpy se yanzun kuma yake hada fuskar junior data EHSAAS no wonder they look so much alike ashe shine ubanshi.
Daga bangaren su Mehtav kuwa dakyar suka iya daga EHSAAS susu hudu itada paa,da Islam se kuma inna daba wani karfin kirkine da itaba suka dai jajjashi har zuwa cikin dakinshi,domin doctor kafayat tace tana hanya.
A cikin mintoci kalilan kafayat ta shigo da sauri dauke da emergency box dinta, nurses biyu na biye da ita, tana kallon EHSAAS da sauri tafara duba shi.
Ta karɓi stethoscope, ta saka a kunnenta, sannan ta dora a kirjinsa. Kallon da tayi musu cike da ɗacin rai da damuwa yakara hargitsasu duka,sbd kallone na irin kun kara dinnan koh musamman Abeey da Mehtav da su taiwa warning last time
"Who talked to him last?" ta tambaya ba tare da kallon kowa ba, tana ci gaba da aikin dubashi
"Islam, Maman junior... itace..." Abeey ta fada tana nuna Islam wacce ta takure a jikin bango tana kuka.
Kafaya ta juyo da sauri, murya cike da ƙarfi da gargaɗi saboda batasan waye Islam din da ake fadaba kawai dai tasan sun sake saka EHSAAS cikin hadari,cikin fada fada tace, "Do you people understand what you just did? This is not some film set! His brain is literally shutting down because of what you caused!"
Kowa yayi shiru,tsit kakeji bame iya bata ansa saboda tsananin tsoron ganin halin da EHSAAS din ke ciki, "Paa yace kafaya me faruwa ta riga tafaru kiduba yaron please" Kallon da kafaya ta watsawa Mehtav yasa bata san lokacin da ta ja baya ba, don gani take kamar itace taja hakan. Paa dai yana dafe da kansa, gaba daya hankalinsa atashe yake kana kallonshi kasan yana cikin mummunan damuwa.
"Ina mamakin yadda zaku zo ku tayar masa da hankali like this. His condition is fragile. Very fragile!" Kafaya tacigaba da fada tana ƙoƙarin sa mishi injection.
Ta juyo da kulawa tana duba karfin bugun zuciyarsa, tana cewa, "He's in critical danger. The brain is trying to access everything at once, his memories, traumas, buried thoughts and it's not strong enough to take it, Hmmmmm Allah ne kadai ya temake mu dasauran kwanansa, da yanzu he's gone completely."
Islam durƙushewa ƙasa tai domin ta gaza gane meke damun EHSAAS din amman daga abinda likitar nan tafada tasan rayuwarsa na cikin hadari kuma ganinta ne yakara assasa ciwon nashi, ta dora hannun ta a kanta tana kuka,irinta shiga ukunnan ga samu ga rashi duk alokaci guda "Ya Allah... ka kare min EHSAAS...Pls don't let me lose him again" tashiga furtawa tana kama hannayensa tasaka cikin nata,kowa kallonta yake musamman Mehtav data kejin kamar taje tafizge hannayen islam dinta acikin na wannan matar sa ita tajawo dukma abinda yafaru, yafaru ko uban meye tace mishi oho,kasa jurewa tai kawai takarasa gefen inda yake ,"can I sit next to him?" ta tambayi kafayat Amma Kafayat bata saurare taba, saidai ma ta ɗaga kai tace, "Everyone OUT! He needs total peace and rest. He has been injected with a sedative. If you love him, leave this room!"
Takarasa tana nuna musu kofa, tana kallon yadda sukai carko carko akanta tai,dukkansu ba haka suka soba musamman Islam da Mehtav amman don dole suka fice. Islam ce karshen fitowa saboda gani takeyi kamar intabar kusa dashi zata nemeshi tarasa koya bace,ko tatashi taga mafarki takeyi.
Zaman jigum jigum suka je sukai a falon, Islam dai ta takure akasa tahade kanta da cinyoyinta tana rasa irin abinda takeji aranta sbd wani mix emotions ne na farinciki da kuma bakincikin halin dataga EHSAAS din yashiga daya ganta, amman kuma tasan kome ze biyo baya farincikinta shine asama da bakincikin saboda kasancewar yanada rai yana numfashi kadai ya wadatar mata cigaba da rayuwa mai inganci.
zaman jiran fitowar doctor kafayat din haka suke jinsa kamar akan kaya suke domin sekai kawo Mehtav takeyi tana dan kallon hanya dakin don taga ta inda zata fito nurses dintane suka fara fitowa sukai musu sallama suka wuce, se can gata tafito rike da labcoat dinta ahannayenta da box dinta ta ajje gefen kujera tana zama akujerar dake facing paa kusa da Abeey daketa aikin shashshekar kuka. Shafa kan Abeey tai cikeda lallabi take fadin ,"don't worry Papa's Abeey your handsome friend will be fine kinji," "Really aunty doctor" jinjina kai kawai kafaya tai tana maida kanta zuwaga paa dayake jiran jin karin bayaninta.
dukkansu ma hankalinsu yadawo kanta, Mehtav cikin azarbabi ganin kafayat din kamar ma bazata musu bayanin asalin halin da EHSAAS din kecikiba tace "Doctor... me zai faru idan... idan ya farka yanzu? Wai meye ma ya sameshi?" Ta tambaya cikeda damuwa. Kafayat tadan nisa kafin tace "kuzan tambaya kun sakeyin wani hayaniyar agabanshi ne?" dasauri Abeey tashiga girgiza kai tana fadin "Aunty doctor tun waccan rnr bamu sake fada agaban Islam ba, bamu bane muka mai komai is this new Islam itace kawai nafito daga dakin inna na ganshi atsaye akofar dakinmu yana knocking seta bude taita kallonshi se tace mai wani abu kawai senaga yafadi yasuma,"
Abeey takarasa tana hararar Islam don ita gani takeyi kawai Islam witch ce tazo zata shanye masu jinin handsome Islam dinsu, daman she doesn't look like human beings. gaba daya hankalinsu yay kan Islam datake kallonsu daya bayan daya amman ruhinta da tinaninta kaf yana can gurin EHSAAS, "Wacece wannan?" Doctor kafayat ta tambaya tana kallonsu tana jiran karin bayani ba wanda yace mata uffan innace kawai tace mata "kafaya karki biyeta abeeda itafa yarinyar nanma bakuwace karku daura mata wani sharrin,daman can shi wancan rigimamman yaron lafi lafiyane,ita wannan fa abokiyar Tajuddeen ce da suka samu sabani da mijinta shine tazonan tadan kwana biyu kafin komai yadaidaita,"
kafayat kallonta tashigayi domin ba yadda za'ai ace EHSAAS kawai yaga bakuwar fuska dabe taba gani yasume ba, amatsayinta na likita tasan dole sedai inwani abin yataba shiga tsakaninsu abaya gently tace "baiwar Allah kinsanshi ne abaya,"
Islam wasu hawaye masu dumine suka shiga bin kuncinta tashiga jinjinama kafayat kai ganin ita kadaice ta fahimceta kuma take tambayarta cikin tausashsshiyar murya, kafayat takallesu duka yadda sukai tsuru ana jiran jin ina ta sanshi,kafayat tace "a ina kika sanshi kuma wayeshi agurinki?" Islam muryarta na rawa tashiga fadin "I know him sunanshi EHSAAS ba Islam ba kuma nidin matar shice shi mijinane," Paa ya tsaya chak. Zuciyarsa ta fara bugawa da sauri. EHSAAS? Mijinta? Sunansa na ainahi fa ta ambata,that means tajuddeen lie to him,to meyasa yay hakan, Ihun da Mehtav tai tana fadin "karyane" yadawo dashi hankalinsa daga dan shock din daya shiga, Ta nufi Islam da sauri, kamar wata guguwa. "What did you do to him?! Karki mana wani karya dacewar ke matanshi ne kiyi tinanin zakici bulus" Ta fasa ihu, muryar ta na rawa tana amsawa a falon gaba daya, "What exactly did you do to my fiancé?! Who the hell are you?! A witch datake sucking blood din kyawawan maza kamar mijina"
Islam ta zaro ido tana kallon yadda Mehtav take dirin masifa da bala'i acikin gidan, ja da baya tafarayi kamar wata karamar yarinya. Kukan da take ƙoƙarin hana kanta yi ya ƙara ɓarke wa, amma Mehtav ta cigaba da masifa.
"This is the last time zamu tambayeki, Wacece ke?! Kuma me ya haɗa ki da Islam har kika zo ki jefa shi cikin irin wannan halin? Kuma kika sake kikamin wani karyar cewar mijinki ne sena mammareki ko yah Taj baze iya kwaceki ahannuna ba, idan da mijinki ne na gaske aida bakiyi kokarin kasheshi irin hakaba" Takarasa cikeda borin kishi da jin she can't really open her head tayarda ma da maganar wannan strange girl din daman tunjiya tagane take taken behaviours dinta be kala da normal people ba.
Islam rintse idanuwanta tai, ta dafe kanta, tana rawar murya tanajin kamar duk duniya bata taba jin tashiga tsaka mai wiya irin yau ba wai ita ake cema zata cutar da EHSAAS, mutumin da batasan adadin lokutan data saka rayuwarta a cikin hadari danta ceceshi ba she can give up her whole life for him, tace "Wallahi... wallahi ban san yana da matsala ba. I didn't know! I'm sorry! I never meant to hurt him...his my sire,shidin EHSAAS dinane tayaya za'ai in iya cutar da mutumin dana keso fiyeda raina"
"Sorry?! Would you just shut up" Mehtav daka mata tsawa da karfi tana rike kugu sbd bala'in kishin yarinyar da takeji "Ki tsaya kiji kuma ki daina kiransa EHSAAS. Stop calling him that name. His name is Islam, and he's mine! Shiba mijinki baneba"
Takarasa tana durkushewa agurin tana fashewa da kuka kafayat gaba daya kallonsu take don tsaf tagane masifaffen son yaron can Mehtav takeyi daya haifar mata da jarababben kishinsa amman in banda karfin halima keda kika tsinceshi yanxun anzo anyi claiming dinshi memakon kiyi murna seki fara bori. "hmmmmm" kawai tace tana kallon paa wanda yafara tausayin yar tasa yanajin kamar this is just the beginning of watching her in this pain don se yau yake gane kalar mugun zurfin son datake ma wancan yaron. "Will you please all calm down" kafayat tafada tana kallon su duka biyun Islam dai babu abinda takeyi se hawaye ta takure kanta agefe guda, Paa cikeda damuwa yace "doctor kigaya mana memory dinnasa yadawo ne koyaya, hankalina yakasa kwanciya kwata kwata" Ta girgiza kai, sannan tace, "One of two things will surely happen, ko dai zai tashi ya tuna komai, every memory, every person nacikin rayuwarsa ze tinashi and he'll come back to you fully, or..."
Ta tsaya, ta kalli Mehtav da paa, sai ta ci gaba: "Or... he loses everything. Including you all. Including himself. Because the brain might not be able to handle that shock. Kuma yiwuwar wannan second scenario din is far more than the first."
Paa ya dafe ƙirjinsa, Mehtav ta mike tsaye jikinta na rawa jin ance ze iya sake manta komai ciki harda ita kenan harda soyayyarsu, what if takasa building sabuwar soyaya dashi? what if kuma yatashi yatina komai yaji bayason ta? rasa me ma zatayi tai ko kuka za ta yi, ko ihu. Islam dai na can nesa, tana kallon su.
se yanzun take fahimtar ainahin abinda yafaru da EHSAAS din no wonder shiyasa be dawo gareta ba shiyasa bai waiwayo su ba ashe total amnesia ya samu donta tabbatar da kalau yake da tini ya koma gida garesu,yanzun shikenan ya manta da ita everything they shared all those good memories their marital life, his home, grandma, Fulani, NURISTAN ya manta komai har junior ma dayake burin yaga yazo duniya yarikeshi da hannunsa,don lokacin datake da cikin junior harcewa yakeyi he's jealous of her saboda tana carrying babyn bashiba, saboda tana feeling each and every movement nashi acikinta bashiba yace duk seya fanshe inyazo duniya baze barta tana rikeshi ba seya rama duka 9months din datai dashi shima,jin cewar duk yamanta da waannan ta saka fuskarta cikin cinyoyinta tashiga raira kukan wanda ke tafarfasa mata kirjinta tanajin kamar mutuwa zatai domin tana kallon EHSAAS araye ace yamanta da ita abune wanda zuciyarta bazata iya dauka ba,she will lose him wata zuciyar tagaya mata,se kuma tatino maganganun Mehtav akanshi da kasancewarsa wanda zata aura, yanzun har EHSAAS ze iya mantawa da ita cikin lokaci kalilan haka yafara son wata mace, dayar zuciyar ce tashiga fada mata "What if you already lost him Islam...?" Tayi tambayar cikin zuciyarta, sai kuma hawaye suka cigaba da gangarowa daga idanuwanta dasukai jajir suka soma kumbura tsabar hawaye, domin duk sanda tatina cewar EHSAAS dinta,mijinta, Best friend dinta,kuma teacher and mentor dinta, namijin da bata taba kallon wani bayan shiba, uban danta,kuma soulmate dinta, wanda sukai sacrificing alot of things tare don su kasance cikin inuwa guda, yanzu yana kwance ba tare da ya san ko ita waye ba. Kuma mai yiwuwa... bazai ƙara tunawa da itadin wacece ba abin na sake dagargaza zuciyarta ne tanajin gara tamutu akan tai witnessing irin wannan jarrabawar, wasu irin suicidal thoughts take fama dasu acan kasan kirjinta.
Abeey ce ta kama hannun doctor kafayat cikin shashsheka take fadin "aunty doctor pls make him remember me banason yamanta dani" jawota jikinta kafayat tai tana fadin "don't worry baby Abeey ze tinaki insha Allah lets think positive okay" takarasa tana kallon su duka.
Islam ce ta dago da jajayen idanuwanta dataci uban kuka ta rarrafa tana karasawa gurin likitar ko zata roketa kamar yadda Abeey tai itama tai duk mai yiwuwa tasa ya tinasu domin zataso taga murmushin daze kasance afuskar Fulani ayayinda tagama bada amanna tarasa danta na har abada ta ganshi tadawo mata shi agabanta. kama hannayen kafayat tai tana hawaye tace "Your a doctor right?" jinjina kai kafayat tai tana kallon innocent face din yarinyar mekyau tace "EHSAAS has always being healthy, he hardly get sick doctor, he us to joke about having a healer gene koyayi ciwo da wuri yake warkewa yadawo normal, doctor please do all what you can namiki alkawari inkikasa yatina mu family dinsa ba iya career dinki ba your whole life will change NURISTAN will forever be grateful to you,yanzun ba iya mu zaki ceta daga rasashi ba kisani dubban al umma out there will leave the best life ever idan har kikai nasarar saka EHSAAS ya tina komai daga cikin rayuwarsa because he has responsibilities, please do something for EHSAAS,"
Mehtav mikewa tsaye tai, tai kanta kamar zata kai mata duka, amma paa ya riketa. Ya kasa magana, ya kasa motsi, saboda zuciyarsa tagama amincewa da maganar yarinyar saboda babu yadda za'ayi tasan duk wadannan abubuwan dangane da EHSAAS inbata sanshi ba, Sosai yarike Mehtav dake kokarin karasawa tanason tadan faffasama Islam baki ko zata dena magana tana fadar maganganun dasuke sake tabbatar mata itadin matar shice kuma hakan ke dada yaga zuciyarta tanajin kamar Taj yakawo mata masifar rayuwarta har cikin gida. tanaji inama paa ya daura mata aure da Islam kawai da itama tasamu kwarin gwiwar bugar kirji tacema wannan yarinyar itama matarshi ce, Inna tamike tana tafa hannu cikin sallallami take fadin "ke Mehtav bazaki nutsuba ance miki kishi haukane ita datake matarshi ma harda da batayi shirmennan dakike yiba se ke, inzaka infika kinga yaro asama aidaman zura muku ido nai keda ubanki nasan duk daren dadewa irin wannan ranar zatazo da wani daga cikin ahalin yaronnan zasuzo nemansa amman kukai kunnen uwar shegu kuka cigaba da shirinku,toh ga irinta nan"
Kallon inna Mehtav tai cikeda takaici ganin bayan bakuwar nanma takebi banata ba,itakanta kafaya mamakin bala'in Mehtav din takeyi saboda ayadda tasan Mehtav tanada mugun hakuri da kauda kai amman daman ba'a shedar mata agurin kishi, Kafaya takalli Mehtav tana fadin. "Kikwantar da hankalinki kidena daga hankalinki akan maganar nan Mehtav meye ribarta intazo tamana karya tace shi mijinta ne eh,ribar mezataci Mehtav?"
Cikin karyayyar murya Mehtav take fadin "zata ci riba mana, he's a good man,he is handsome, intelligent, sexy, hot and very romantic,he is the best lover ever,babu namiji kamarshi" Takarasa fada cikin rufewar ido donta manta ma agaban iyayenta take, Islam ta share hawayenta da hannun rigarta, tana kallon Mehtav da kallo mai cike da tausayawa da kuma taurin rai,saboda yadda Mehtav tai describing nashi just make her believe mijintane kuma har yanzun he is thesame be canza ba, takarasa gefen Mehtav din wannan karon tana kallon cikin idanunata dake cikeda masifar kishi tace
"You just described him well... he's my husband, kuma duk abinda kikace game dashi haka yake he's more than what you even mentioned" takarasa cikin murya mai sanyi data aikama Mehtav sako har cikin kwakwalwarta tana shata mata layi tahanyar nuna mata eh nawane nafiki saninsa,islam tadan nisa kafin tace "Shidin fa mijinane nasake maimaita miki... kuma mahaifin ɗana junior.dalilin rabuwarmu shine mun rasa shi watanni da suka wuce a wani hadari. Mun yi tunanin ya mutu... sai yau da na gan shi nan, cikin wannan gida, cikin wannan hali..." Takarasa muryarta na rawa tanata kokarin fighting hawayen dasuke so sudawo kan fuskarta, "ban zo da niyyar cutar da kowa acikin gidannan ba, Na zo ne domin neman mafaka sbd rayuwar dana datake cikin hatsari,bansani ba ashe fate ne yakawo ni cikin gidanku domin inga cewar EHSAAS dina be mutu ba,cewar dana ba maraya bane ba,kuma maama Fulani bata rasa danta ba"
Takarasa cikeda wani shauki tana fadi "idan iyayensa suka ji cewa yana raye... za su yi murna sosai. His mother hasn't smiled for real since we lost him...fake smiles kawai maama takeyi I wanna see her smile widely idan taga zuciyarta gaba daya yadawo EHSAAS shine zuciyar ta"
Mehtav ta girgiza kai da karfi kamar wacce kwakwalwarta ke toshewa bata fahimtar maganganun islam tace "No... no... hakan ba zai yiwu ba. Ki tsaya...munji kinada miji me suna EHSAAS, what if he just looks like your husband? What if he's just a lookalike? This is my Islam. My fiancé!"
Islam ta kura mata ido na wasu dakiku,ganin kamar Mehtav din kawai gaskiya ce bataso, dogon numfashi taja kafin ta tattara nutsuwarta guri guda tana kallon Mehtav,cikeda basira da hikima da salon iya magana wanda tariga ta kwarance akai saboda gogewar datai acikin manyan mutane da manyan mata da wayayyu masu ilimin addini dana zamani tashiga tambayarta
"To Mehtav nayarda shidin fiancé drinking, but just answer this few questions dazan miki... ina kika san shi? A ina kuka hadu? Su waye iyayensa? Inane garinsu? Menene tarihinsa kafin ki sanshi?"
Mehtav ta yi shiru. Hannunta na rawa, zuciyarta na karaya. Idanuwanta sun cika da hawaye taf. Ta juya gefe guda tana dafe kirji, kamar wata me shirin shiga panic attack
"Please... stop..." ta furta da ƙyar. "I don't know his past. I don't even know his family. But I know I love him. I love him deeply. I don't want to lose him... please... please don't tell his family you saw him yet. We're getting married soon..."
Kukan da Mehtav ke yi ya tsinke zuciyar Islam. Tunanin irin radadin da ta sha lokacin da suka rasa EHSAAS take, radadin da ya taba ranta har itama takusa binsan, ya sa ta fahimci wannan yarinyar sosai, tasan yadda so yake kuma tasan me akeji idan kaga xaka rasa masoyinka amman babu yadda za'ai ta iya sacrificing EHSAAS after all they went through tabarma wata stranger shi but she truly understand Mehtavs emotions.
Ahankali ta rungume Mehtav cikin karfin hali tana danne duk wani azabar radadin dake tasowa a kirjinta "Shhhh..." ta ce tana shafa bayanta. "Na fahimce ki. Nasan me kike ji... because I've been there. And wallahi I'm not here to take him away from you."
Mehtav ta riketa sosai kamar yarinya da ke neman mafaka daga hadari.
Islam ta cigaba "Let's not rush anything, Mehtav. Abinda ya fi muhimmanci yanzu shine lafiyar sa. Let's focus on EHSAAS waking up... and when he does, let's see what he remembers. Maybe fate will decide where his heart belongs."
Kallon mamaki Mehtav tashiga yi mata, da zuciya mai nauyi, wanda tasan idan itace a position din Islam baxata taba iya yin hakaba,yaza ayi yar karamar yarinya haka takeda wisdom irin wannan hartana gaya mata kalamai masu dadi haka after being so rude to her. anya kuwa batasan abinda tataka baneba,dan dagowa tai tana kallon Islam se kuma aranta ta raya ko hala auren hadinnan ne da akeyi shiyasa taga Islam bata wani saka mgnr aurenta da EHSAAS din acikin ranta ba.
Sallamar Taj ce ta.katse Mehtav daga overthinking din data tafiyi, Abeey ce takarasa dagudu tana welcoming dinsa tun daga kofa tasoma narrating mai abunda ke faruwa,ganinsu carko carko yasa Taj yaji gaba daya gwiwarsa ta sage because that shows cewan me faruwa tarigada ta faru ga labarin Abeey dinma ba duka yake ganewa ba don arude take gaba daya. akan Paa idonsa ya sauka wanda kemai kallon da yakasa gama ganewa domin irin kallon weldone dinnan yake mishi irin kayi abinda kaga dama dinnan.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote [29/05, 20:26] Fatima Rufa'i Nasidi: *** Not edited It's Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.