EHSAAS

Chapter 28

by @fatoumspassion

Falon tsit yay bayan fitar Doctor Kafayat saboda akwai wani emergency da ya tashi a asibiti, kuma ta tabbatar musu kada wanda ya shiga dakin EHSAAS har se ya samu 48 hours of sleep, ya huta, kwakwalwarsa ta huta tukunna. Paa kallon Taj yay yana mai alamar ya sameshi, ya waje, ya mike yana ficewa abinsa. Gaba daya hankalin Taj a tashe yake. Ganin kowa yayi jugum-jugum da jan ido, bin bayan Paa din yay.

Islam ma mikewa tai tana nufar daki domin a jikinta kawai taji junior ya tashi. Aiko tana shiga suka hada ido. Ba dai yiwu kuka ba, se wasa yake da 'yan hannayensa. Ta dauke shi tana mai murmushi tana dan jujjuyashi, da yasa yaron ya fara dariya. Kamanninsa da mahaifinsa ya kara fitowa sosai. Haka kawai taji wannan nauyin da kirjinta yake mata yana sauka, domin tana jin kamar damuwarta ta duniya kuma ta kare. Tunda Allah ya dawo mata da EHSAAS dinta gareta bayan cire rai da tai, ga hakan na har abada, abu ne wanda ba ta taba tsammanin zai kasance haka ba har abada.

She's just looking forward da ganin ya samu lafiya, domin a jikinta take ji ko wane irin ciwon da yake kan EHSAAS, ba zai fi karfin soyayyar da yake mata mai karfi ba. Tasan koda brain dinsa ta kasa ganeshi, tabbas zuciyarsa za ta ganeta, saboda tayi imani da soyayya mai karfi wacce suke wa juna - tafi karfin wata amnesia.

Daidai nan Mehtav ta turo kofar, ta shigo dakin. Feeding din junior take, amma tsabar kame kai, jan gelen gefenta tai tana rufe kirjinta. Domin bayan sanin abinda ke ran Mehtav din, dole ne ta san kalar zaman da za ta yi da ita - ba wai ta saki jiki a gabanta ta taita kare mata kallo ba, tana matsayin budurwar da take son mijinta.

Mehtav duk da abinda take ji a ranta, ta danne. Itama a kokarinta na son taga ta nuna komai ba komai bane kamar Islam din. Ta karasa tana tambayarta: "Ya tashi?"

Jinjina mata kai kawai tai, cikeda dan rawar jiki, saboda ganin cewa dan masoyinta ne. Take tambayar Islam ko za ta mai wanka yanzu. Jinjina mata kai Islam tai tana dan basarwa. Zuwa yanzu ta gane nature din yarinyar - na bada answer da body language - ba wai wulakanci ba. Kuma Mehtav tayi mamaki sosai ganin bayan ta gama bashi, maman ta miko mata shi da kanta ba tare da ta tambaya ba.

Mehtav jiki na bari ta karba tana dada kallon kamannin yaron da Islam dinta. Jitayi tana mugun son yaron. Kwata-kwata bata ji kishin da take yi akan uwarsa ya shafe shi ba. Ta dan murmusa tana fadin: "Tubarkallah, Masha Allah. In mai wanka?"

"Na iya wa yara wanka," ta fada tana dan kallon Islam da take kallonta itama yadda take dan tarairayar yaron. Dayake baida kiwa ko kuka, be mata ba.

Jinjina kai Islam tai. Don sam ita bata iya wani wankan yara ba. Kodacan kakarsu ce ko Fulani suke yi mai. Iya kaci dai ta shiryashi. Wani bin shirin ma duk su suke mai da sauri.

Mehtav ta mike tana fadin: "Na tafi gun Inna. Ina kayansa? Zan mai a can don tafi guiding dina."

Jinjina mata kai kawai Peace tai. Kafin can ta mike tana dan dube-dube cikeda miskilanci, tace: "Uhm pls, ina ledar da sister dinki ta kawo jiya? Akwai kayansa da AD Taj ya bayar a saka mishi."

Jinjina kai Mehtav tai kafin tace: "Na saka a closet. Bari na dakko."

Wucewa tai da junior a hannunta. Ta dakko ledar, ta dawo da ita dakin. Ta bude ledar tana fadin: "Wanne za a saka mishi?" Don kala biyu tagani.

Islam tace mata: "Kowanne zeyi."

Daukar wanda yafi kyau Mehtav tai tana fadin: "Bari mu baki guru, kema ki yi wanka ki shirya ko dan..."

Jinjina mata kai Islam tai tana fadin: "Na gode, Mehtav."

Mehtav tace: "Duk abinda kike bukata, just ask me. Za a kawo maki in sha Allah."

Kan ta jinjina kawai again kamar wata kadangaruwa. Mehtav dai tana mamakin kalar jan ajin matar har ta fice a dakin tana waiwayenta. So take ta dan shige jikinta ko ta samu ta dan bugi cikinta, ta gaya mata kalar rayuwar da suka yi da EHSAAS. So take lallai-lallai ta sani auren hadi aka musu ko na soyayya, ta yadda ita za ta san ta inda zata kafa nata gwamnatin in ya farfado.

Dakin da ta wuce Abeey dai, jikinta duk a sanyaye ta tarar da ita. Inna na famar lallabata. Ta sha tea din da ta hada mata, don tun safe ba wanda yaci komai a gidan. Sam Abeey ta ki - wai ita se Handsome Islam dinta ya tashi. Amma ganin junior se ta shiga murna.

Wata karamar roba Inna ta samo musu cikin sababbin kayan da ta taho da su daga kauye - tsaraba a ciki. Suka hada ruwan wankan. Mehtav duk ta mamanta yadda ake yin wankan. Iyace ta tuna mata. Abeey na watching dinsu.

Junior se jin dadin ruwan dumin yake yi. Seda aka zo wanke fuska tukunna, yasa hannayensa yana kutufar Mehtav da shi, yana bare mata baki, don daman can haka yake - ba ya son a taba mai fuska. Da kyar aka wanke fuskar. Mehtav ta na dashi cikin towel ta shiga lallashinsa.

Ba su da baby oil kwata-kwata a gidan. Kuma maya-mayan da suke shafawa yawa fatarshi. Karfi Inna ce ta dakko man kadanyar ta mai kyau, tana fadin: "Kawo a shafa mishi wannan, ingantaccen maganin sanyine, kafin a siya mai wadancan maya-mayan baturen da kuke so."

Mehtav ba don taso ba, ta bawa Inna ta shafa masa. Don ita personally ko kamshinsa bata son ji bare ta taba.

Inna ta gama shiryasa. Lumi. Abeey don rigima wai a goya mata shi. Mehtav dai ta dan barta, ta rikeshi for some minutes kafin ta karbeshi a hannunta tana sakashi a baya da wani wankakken zani da Iya ta bata. Ta shiga goyashi. A ranta tana jin: "Yes, ai duk mai da wawane, in Islam taga tana son danta, za ta saki jikinta da ita, ta bata labarin yadda ta san EHSAAS har suka hadu suka yi aure. Inna hadine? Taji. Inna soyayya? Nema taji. In kuma na zumunci ne ma duk zata ji."

Tana dawowa ta tarar da Islam har ta gama shiryawa. For the first time Mehtav ta ga ta mata murmushi tana tambayarta: "Harda wahala haka? Kar yasata ciwon kirji. Yanada nauyi fa."

Mehtav tace: "Ai babu komai. Kawai tanason ta goya shinne."

Godiya Islam ta mata. Mehtav ta sha mamakinta. A ranta tace: "Ashe dai ba wai wani girman kai gareta ba."

Junior barci ya koma, domin baya gajiya da barci.

Mehtav ta dakko tsintsiya da mopper, zata gyara dakin su. Ta shiga karkade bedsheets din gadonta da ta kwanta. Islam ganin tana aiki, itama ta tashi, ta hau tayata, saboda ta iya gyaran su gado da shashsharen daki da wankin toilet, saboda bata bari kowa ya shiga yayi wa mijinta. Don dole ta koya, itace ta share dakin. Mehtav tai mopping tas.

Tace mata, "Me kuma za a yi?" Daga nan parlour suka fito. Tace su shirya lunch tunda gashu har rana tayi, babu wanda ma ya nemi breakfast. Binta kitchen kawai Islam din tai tana ganin yadda Mehtav ke fito da komai a tsanake tana aikinta cikin kwarewa. Ta shiga kallonta with admiration, don har yau ita bata wani iya girki ba. Koda suka yi aure, EHSAAS kuma ba wani nuna mata damuwarsa akan hakan ba. Ita da shi kullum gun Fulani suke cin abinci. In ma basu shiga ci ba, za a aiko musu da shi ko su fita outing su yi ciye-ciyensu. Sam sam ko ta shiga kitchen da niyyar koya, haka zai samu hanya ya shashantar da ita yana zigata wai ba fa dole bane seta iya girki zata siye zuciyarsa. Shi yake dada spoiling dinta yana riritata. Shi yasa har yau, bayan dafa ruwan zafi ko shinkafa fara, bata iya dafawa ba.

Satar kallonta Mehtav tai ganin bata ce zata tayata ba. Tasan yadda taganta mace cikakkiya me aji, haka ai ba za a ce bata iya girki ba. Tadan juya tana fadin, "Maman Junior, ko zaki gwada mana girkin mutanen garinku ne yau a gidan muci? Kin gama baki fadamin sunan garin naku ba?" Ta fada cikin wasa.

Islam ta kalleta, wani silly smirk tai domin she can see right through Mehtav. Ta saba da kalar wannan faran-faran din da makircin jokes na bugar ciki a gidan sarauta. Amma don ta nunama Mehtav kamar ita wawiyane, se tace mata, "NURISTAN ne sunan kasarmu. Kinsan da ke mu ba anan kasar muke ba. And mind you, I'm a Princess. Mijina baya bari ko wuka na rike bare nai girki."

Dan zaro ido Mehtav tai cikin mamaki take fadin, "In this generation kuwa ai duk macen da bata iya girki ba, sunanta fa 'sorry'. Maman Jr, kinaji kina gani husband dinki zai yi second wife da me abinci a waje."

Murmushi Islam tai kafin tace, "He is a Prince. He doesn't eat outside."

Tace, "Nikam dazun kamar naso na ji. Taj nacewa ku yan gidan sarautane. Yaya abin yake ne, Maman Jr?"

Da dab lumshe ido Islam tai. Bata cika son dogon jawabi ba, amma taga alamar yarinyar nan Mehtav zata samata ciwan kai da yawan magana. Tace mata, "Uhm, hakane. Shine dan gidan sarauta. Ni ba 'yar gidan bace, auroni akai."

Mehtav tadan juyo tana fadin, "Kice kema princess din wani kingdom din ne. Is it Indonesia, or Ethiopia? Don naga kin fi min kama ma da yancan garin. Da alama auren hadi aka muku - na power da power - tsakanin masarautu ko?"

Murmushi Islam tai kafin tace, "Ko daya. Have you ever read Romeo and Juliet?"

Girgiza kai Mehtav tai tana fadin, "No. I don't read novels, especially fictions."

Da fata taga Islam tayi kafin tace, "My bad. That's your fiancé's favourite. Kinsan shi marubuci ne, he is a hopeless romantic. But when he found me, I become his hope. Search for his works. Ya rubuta littattafai masu dama akan soyayya. Anan zaki gane auren hadi aka m ai ko na soyayya. His full name is EHSAAS bin NASHWAN bin EHSAAS NURISTAN, the only heir to King NASHWAN bin EHSAAS."

Wani irin bugawa zuciyar Mehtav ta shiga yi domin sosai abin ya bugi kirjinta. Ya shiga bata mamaki domin tana mugun jin shakka da kuma tsoron shiga gidan sarauta. Kuma tasan cewar Islam ta fita experience. Duk yadda ta so ta sake bugar cikin Islam kan ta gaya mata wani abu dangane da alakarta da EHSAAS, ki tai. Daga karshe ma ficewa tai, ta barta a kitchen din.

Asace ta nufi dakin da EHSAAS yake. Duk da yadda aka shata musu warning kar wanda ya shiga, hala ta lallaba. Tunda tasan ba wai hayaniya zata mishi aka yi ba. Tai shigewar a hankali cikin sanda. Ganin babu kowa a falon, saboda tana son taganta a kusa da shi. Karasawa tai ta zaune a gefen gadonshi tana kallon face dinshi dakenan - very fresh da shi. Sai dai taga yayi dan duhu. A hakan, wai da su Mehtav suke ganinsa jajir, kuma bata raba daya biyu canjin ruwa da kayan shafa shine ya janyo haka. Saboda tasan yadda suke kulawa da komai nash tsaf-tsaf, basa wasa da duk wani lamari na tsaftar jikinsu da kalae maya-mayan da suke shafawa.

Shi da ita saman gadon, ta hauye ta shiga shafa mai doguwar sumarshi da har ta soma kara taruwa. Wani irin shaukin sonshi ke fizgarta. Babu abinda take yi sai godiya ga Allah daya bata wata dama ta biyu a rayuwarta - ta rayuwa da EHSAAS dinta.

Hannayensa ta kama ta saka a cikin nata. Daman kuma jiya bata samu tai wani barci da daddare ba. Ga sanyin AC dakin na busowa da daddan kamshin da dakin ke yi - wanda Mehtav ce ke tsaye tsayin daka akan duk wani tsaftar cikin dakin nashi. Bata san sansa barci ya kwasheta anan gefensa ba.

Kana kallonsu, duk da cikin barci, amma ba karamin burge ka zasuyi. Yadda ta kwanta a saman jikinsa cikin barcin, ta kwakubeshi kamar zai ma data ciki. Shi ma ya sa hannayensa yana rungumeta sosai duk da baya cikin hayyacinsa. Amma tun tabashi na farko da ta yi, yake jin abin har bargon jikinsa.

Mehtav data ji Islam shiru, ta dauko ko 'yan miskilanci ne suka tashi. Ta tafi daki ta zauna, sai da ta gama jere komai a dining sannan ta nufi dakinsu don ta kwantar da Junior. Ita kuma ta samu tayi wanka. Mamakine ya kamata ganin babu Islam, babu dalilinta. Ta karasa toilet, ta dan bubbuga, taji shiru. Closet ta nufa, nan ma bata ganta ba. Da sauri ta kwance Junior tana kwantar da shi saman gadon. Abeey tayi saurin ficewa, dakin Inna ta nufa, taga Abeey ma barcin ranar take yi, Inna na zaune tana ta fitar da kayan da zata bayar don tana son zuwa kauye wannan satin, ta jima bata je ba.

Inna ganin Mehtav ta shigo kamar an jehota, take tambayarta, "Ke lafiya? Ina maman Jr take?"

Mehtav ta tambaya a dan rude tana kallon dakin. Inna tace, "Oho, Islam tohm, ina zata je? Ki duba dakinku mana."

Mehtav tace, "Inna daga can nake fa."

Inna tayi jim, sai kuma tace, "Kila tana gurin babanku da Tajuddeen. Tun dazun na ga sun fice. Ai kila suna tattauna yadda za a mayar da rigimamman can naku gida tunda Allah ya sa an san daga inda ya fito."

Da sauri ta juya ta fice, don ta san balallai Islam din taje gurin su Taj. Ta tagar kitchen ta shiga, leka garden din, paa! kawai ta hango da Taj suna ta tattaunawa. Ranta ta ayyana, "Wato wayo ta yi min, ta bar ni a kitchen bayan tace mu bari ya warke, ita ta tafi gurinsa ko?"

Da sauri ta juya ta wuce dakin EHSAAS. Tana bude kofar kuwa, ta gansu a yadda suke. Kana ganinsu ka san they are a match made in heaven, kuma akwai tsantsar soyayya da shakuwa a tsakaninsu. Wani tukukin kishi taji yana zuwar mata cikin zuciya. A fusace ta nufe su da niyyar ta tashe Islam daga barcin, sai kuma ta tuna da warning din kafaya karfa tai wani abu da zai saka rayuwar EHSAAS cikin hadari.

A hankali ta karasa tana huci, ta shiga dan tapping kafafuwan Islam a hankali. Daks barcin ba wani nisa yay ba, sai ta bude ido a hankali. Idonta ya sauka akan Mehtav dake mata wani mugun kallo, da ta gane na tsantsar kishi ne. Mikewa zaune tayi tana dan gyarama EHSAAS kwanciyar shi.

"Out," ta fada a hankali tana nuna mata kofar waje tana dan harararta. Sai taga Islam tana nuna kamar ma ba ta san me tayi mata ba. Ta juya ga mijinta, babu komai a fuskarsa, amma sai taga ta shiga dan shafa mai saje kamar mai dada kwantar da shi. Tayi pecking goshinsa tana mikewa. Mehtav ji tayi kamar ta gaura mata mari. Ta sakata a gaba kamar uwarta. Suka fito a parlour, kafin ta karasa daki, Mehtav tayi saurin shan gabanta tana fadin:

"What was that?"

Dan dage gira Islam tayi tana fadin:

"What?"

Mehtav, cike da masifa da jarabar kishi tace:

"What you just did? Ai inace kina ji a gabanki doctor tace kar aje inda yake ko? And you sneaked into his room kika wani lafe kina barci a gefensa. What if something bad happened to him? Bayan kince ai a jira ya warke, but kina karya alkawarinki."

Islam dan kallonta tayi kafin ta dan harde hannayenta a kirjinta tace:

"Yes, na ji me doctor tace. We shouldn't disturb him with any hayaniya, that is why I sneaked silently. Saboda Inna tambayeki, I know you'll react this same way, Mehtav. And by the way, danace ki bari ya warke, kin ji labarin nace miki bazan kula da mijina bane in the process? Ko kin ji labarin nace miki I'll neglect him saboda kawai baida lafiya? Yamanta ni uhm?"

Mehtav's muryarta na dan rawa tace:

"But you said... you said fate will decide where his heart belongs."

Tabe baki Islam tayi kafin tace:

"Of course, and I'll do everything in my power for that fate to be in my favour."

Kallon mamaki Mehtav ta shiga mata, don ta dauka wata sokuwa ta samu da za ta mata wayo, ashe kar take kallonta.

"Kin gama abincin?" Islam ta fada tana juyawa, ta nufi dining. "Kinsan fa yunwa nake ji, abinki da lactating mother."

Ta karasa ta soma bubbude food warmers din da Mehtav ta jera. Mehtav ta tsaya tana kallonta, "Wato gama yar aikinta ta gama mata girki zata zo taci." Mehtav ta karasa tana rufe warmer din da Islam ta bude, tace:

"Hmmm, amma dai kinsan baki ajjeni ba ko? Ko kuma ba don ke nai girkin nan ba, tunda dai baki biyani ba kuma baki kawo kayan abincin da za a girka ba. Ai seki bari masu gidan su zo su fara zubawa," ta fada cike da gori.

Tabe baki Islam tayi before tace:

"Karki damu, fiancée dinki is a multi-billionaire. He owns one of the best publishing houses in NURISTAN and he is the best crypto trader in our country. Ki bari in ya warke, he will pay you. Kinsan baya wasa da duk abinda ya shafeni."

Ta karasa tana janye hannun Mehtav, cike da wani matsiyacin jan aji da yanga, ta shiga serving kanta. Kafin ta bude baki tace:

"In kuma kinaso yay fushi, kin hana mamar danshi abinci, tohm kinsan se naci. Junior ze samu shima daga jikina."

Ta karasa tana kai spoon din hadaddiyar fried rice din bakinta. "Uhmmm wow Mehtav, you're a great cook. I bet EHSAAS loves your food so much. Kinsan be wasa da abinci, musamman in akwai nama."

Ta karasa tana soma tsame dunkulellen namomin da ke ciki tana kaiwa bakinta.

Fuuuuu!

Mehtav ta wuce don ta ma rasa abinda za tace. Ganin Islam yarinya ce ta dauka zata mata zarra gurin siyasa da iya bariki, amma ba ta san yarinyar ta shallake kanta ta zauna da manyan mata da suka yi shaping din brain dinta da mind dinta gurin iya cakka bakar magana da nuna ma mutum komai ba komai bane ba, koda ya bata mata rai. Saboda abu na farko da Grandma ta fara koya mata bayan aurensu shine yadda za ta mastering emotions dinta duk abinda wani ze mata don ya bata mata kai. Ta nuna ranta ya baci? Instead, se dai ma ta cinna mishi hauka. Dalilin hakan yasa suka fara samun matsala da 'yar uwar mijinta, Mimaah, don so tayi ta zame mata puppet kuma ladder din da za ta rinka amfani da ita gurin cutar da EHSAAS.

Anitse ta shiga cin abinci, ba ta wani jima da farawa ba Paa da Taj suka shigo suna kallonta. Gaida su tai, suka amsa, fuskokinsu babu yabo ba fallasa, musamman Taj, da fadan da Paa din yay masa ya chafe mai a zuciya. Duk da yasan ya mai ba dede ba, amma ba taba dauka Paa ze dau issue din personally ba, da har yake gaggaya mishi abubuwa marasa dadi akai, yana ce mishi daman burinsa ya ba shi shi ya kaishi ga danginsa don a kara mai matsayi. Toh gashi nan, gashi shima ya gaji, tunda dai matarsa tazo ya hada ya tafi da su. Ba ze cigaba da rikesu ba tunda yanzun yasan EHSAAS nada mata, babu amfanin da zasu mishi. Kuma he is sure cewa idan King Nashwan yasan cewa EHSAAS yana gurinsa bayan yasan cewa ya gane waye shi, ze iya shiga gagarumar matsala da babu wani mahaluki da ze iya cireshi aciki, saboda kalar connection din da yake da shi a duniya baki daya.

Duk bashin bakin da Taj yay yana me gaya mishi, ba san Islam tana da alaka da EHSAAS ba. Kin yarda yay, yana ce mishi lallai, lallau yasan yadda zeyi dasu, ba zasu cigaba da zama a gidansa ba balle su ja mai bala'in da be ji ba, be gani ba. Taj ne yayanke shawarar cewa tunda mahaifin Islam din yakusa zuwa, su bari yazo kawai, shi ze san yadda zeyi ya fitar da su daga kasar nan ba tare da idon makiyansu ya kai kaiba. Don yanzun in aka ce za'a sanar da Masarautar Borno, ma wani sabon tashin hankali ne ze faru. Zasu iya cewa ma shi yay ma EHSAAS haka, musamman King Abdul Aziz, da Paa yasan yafi kowa tsanarshi kaf cikin yan uwan Fulani Hajar, don yadda yaki jinin hada jini da bare kuma talaka.

Paa shigewa ciki yay, ya bar Tajuddeen a gurin Islam. Zama yay yana tambayarta ya take, tace mishi Alhamdulillah. Ya dan yi jim kafin yace mata: "Maman Jr, baki kyautamin ba. Kin min karya. Meyasa baki sanar dani ke wacece ba tun farko?"

Dan jim tai tana kallonsa kafin ta ajiye abincin gabanta, domin ba ta iya cin abinci a gaban wani namijin ba mijinta ba. Tsareshi da idon da tai yasa ya sha jinin jikinsa, ya shiga inda-inda. "I mean, if you had told me..." tace. "AD Taj, I'll forever be grateful to you for duka abubuwan da ka min tun zuwana kasar nan. Nagode da cetona da yarona da kai, amma kasani ba na taba maka wani karya ba. Kawai dai na boye maka gaskiya ne, saboda nasan ba zata amfaneka da komai ba, face ma ta saka rayuwarka cikin hadari." "But at least, Islam, if you did, I'll avoid this situation we are in," ya karasa yana nuna mata gidan baku daya.

Dan murmushin gefen baki ya ga tayi kafin tace: "Da ba zaka kawo ni nan gidan ba, ko ba shakka."

Ya shiga jinjina mata kai, tace: "That means kun san waye mijina, kuka rikemana shi anan. Ba ku yi alerting kowa he's still alive ba?"

Dan jim yay kafin yace: "Munayin hakan ne don kare lafiyarsa Islam, ba wai don san ranmu ba."

Dagowa tai tana kallonsa cikin wani irin shakkarta, ya shiga dauke idonsa akanta. Tace: "Kare lafiya kace? A wanan irin fannin kare lafiya ake kokarin yi ma mutumin da ba ma iya gane sunansa ba aure? Ka taba jin inda akaiwa mutum mara lafiya aure bayan an san cewa raje dyk daran dadewa? What is your motive behind aura mishi yarinyarku AD?"

Dan shiru yay, don shi kansa ya ga ganganci da kuskuren Paa akan wannan niyyar tasa da ba san dalilinsa na yin hakan ba, kuma baida amsar bata, don shi ba daya tambaya Paa fada ya haushi dashi. Yana ce masa shi ze gayawa meye dede da ba dede ba. "Shi ne ya haife su ko su suka haifeshi?"

Jin ya mata shiru yasa tai murmushi kawai tana fadin:

"That's not right. Komeye ma motive dinku, you are not being fair. Kun cutar da waccan yarinyar because she truly loves him with all her heart."

Ta karasa zata mike tsaye ta bar gurin, da sauri Taj yace: "Islam, ta tsaya."

Chak, tana kallonsa kafin yace: "I'm sorry. Ba zan iya miki explaining abubuwan da suka faru ba. Amma nasan Paa will never hurt your husband. Shi din ba mugu bane. Ki sani, soyayyarsa ga EHSAAS ce ta saka blindly yake son ya aura ma yarshi ita. Maybe yana ganin hakan ze iya taimaka mai ta wani gurin."

Tace "Taimako fa kace? Wane kalar taimako? Wanda ya bata yake nema? He is lost in a strange land. Baku taba cigiyarsa ba, kuke magana da taimako?"

Ya ce: "Na ji Islam, nasan munyi kuskure, but ki zauna ki saurare ni, kin ji? Zan baki labarin duk abinda ya faru, da yadda yaran suka tsince shi."

Zama tai, tana kallonsa. Ya shiga mata bayani tiryan-tiryan kamar yadda ya ji daga bakin Paa da Abeey, yadda suka fita da motar mamansu asace, da yadda suka ganshi cikin jini. Everything be boye mata ba, har kokarin cigiyarsa da Mehtav tai, duk ya fada mata da yadda Paa yace a bari ya warke tukunna a maidashi cikin yan uwansa.

Jinjina kai ta shiga yi, tana jin Mehtav da Abeey suna samun gurbin zama a zuciyarta. Domin da ba dan su ba, yanzun da tuni mijinta baya wannan duniyar. She will forever be grateful to them. "Islam, yanzun zaki iya yarda dani? Zaki iya sanar dani menene ya faru a Borno, da kuma dalilin da yasa EHSAAS ya bar gida a wancan lokacin?"

Dan jim tai kafin tace: "Amma se ka min alkawari zaka taimaka min gurin maidamu NURISTAN."

Dan jim yay kafin yace "Your dad is probably doing everything possible wurin ganin ya iso Nigeria akan lokaci, so nasan he will help you gurin komawa NURISTAN."

Dan jim tai, se yanzun ma take tunawa cewa fa ashe ta nemi taimakon Abraham Zion. Dan dafe kanta tai kafin tace: "My dad should not meet us here, Taj, saboda ze rabani da shi ta karfi da yaji."

Dan waro ido yay yana kallonta, tace mishi: "Yes, babana ba taba son aurena da shi ba. Ba ya son EHSAAS, in fact he hates him. Abinda yasama ya yarda ze taimake ni, na tabbata saboda yasan bani da way out sai shi. Yasan EHSAAS ya mutu, shiyasa."

Taj cikin mamaki yake fadin: "Islam, wane uba ne kuwa ba za so yarsa ta samu miji kamar Yarima EHSAAS ba?"

Tace: "Babana, shi shi kadaine title din Prince ba taba burge shi ba. Impact, baida wani makiyi sama da mijina. Ko ince ni da mijina. Because he thinks EHSAAS snatched me away from them." "Taj, labarina da EHSAAS yana da tsayi sosai. Sannan koda na baka, ba komai zaka fahimta a ciki ba. Yanzun fatana guda daya ne: EHSAAS ya tashi, ya tuna dani, mu bar kasar nan baki daya mu koma inda muka fito."

Taj yace: "Karki damu Islam, na miki alkawari. Ni dake ne zan taimaka miki gurin ganin kin koma gida tare da mijinki cikin aminci."

Tace: "Kafin babana yazo?"

Yace: "In shaa Allah kafin babanki yazo."

Mehtav da ta gama jin maganar Taj da Islam, da sauri ta juya, sādaf-sādaf tana komawa ɗaki. Dawowarta kenan da niyyar ta maida ma Islam baƙaƙen magana kamar yadda ta gaya mata. Sai dai ta tarar da su suna magana. Kamar ta nuna ta ji, sai kuma ta fasa, ta kasa, ta sa kunne ta saurari duk abin da suke cewa.

That means idan EHSAAS bai tashi ba, baban Islam zai zo, za ta sa ta a gaba su tafi. Idan Islam ta tafi, matsalarta ta tafi. Koda EHSAAS ya tashi ya tuna, she can convince him to marry her, ta yadda za ta tafi da ita garinsu itama a matsayin matarshi. Kome zai faru, ya faru.

Wani tunani ne ya shiga zuwarta. Amma deep down, ta san ba daidai bane. Amma kuma ta san shi ne best abin da za ta yi wajen ganin ta tsayar da tafiyar Islam, har sai babanta da ke ƙin aurenta da EHSAAS ya dira a ƙasar Nigeria, ta yadda duk tsarin shirin Islam ɗin zai wargaje.

Ta kasa zaune, ta kasa tsaye. "Hmmmmm... hmm," kawai take faɗa. Kafin kawai ta ƙarasa, ta saka key ɗakin, hannunta na rawa, ta shiga laluben wayarta. Can ta hango ta a ƙasan bedside drawer dinta, ta ɗauka. Kirjinta bugawa yake yi, kwakwalwarta na faɗa mata abin da take shirin yi ba daidai bane, amma zuciyarta na ingiza ta.

Don a yadda taji yarinyar nan take zuzuta soyayyarsu, ta san lallai idan har EHSAAS na sonta kamar yadda take faɗa, ba zai iya haɗata da komai a zuciyarsa ba. Koda ya aureta, za ta zame masa second option ne-she hates being second best a rayuwarta. Tana so ta kasance ita kaɗaice a rayuwarsa.

Don haka kawai ta shiga danna lambar Kafaya. Tana jin: "Everything is fair in love and war." Kawai ta fanna-ba abin da ya dame ta da zai je ya dawo.

Saidai da ta gama ringing, sannan Kafaya ta ɗauka, tana tambayarta: "Lafiya? Ko dai jikin EHSAAS ne?"

Mehtav ta girgiza kai kamar suna gaba da juna. "Tohm, ina jinki Mehtav. Lafiya kike kirana?"

Kafayat ta tambaya, domin dama haushinta take ji-dalilin abin da Mehtav ta musu. Engineer ya daina bata fuska saboda ƙaryar da ta yi supporting akayi masa da yadda ta karɓi kuɗade a hannun Mehtav.

Straight, Mehtav tace mata: "Doctor Kafayat, I know how to amend your relationship with my father. Kuma har aurenki za mu saka yayi. In dai har kin min abin da nake so yanzu."

Doctor Kafayat, cike da mamaki take faɗin: "What? Mehtav, are you high?"

Mehtav tace: "Please, don't pretend as if we don't know what you're after. Na san kinason Paa tun ba yau ba, so let's do this. Ina son ki yi wa EHSAAS allurar da zata mantar da shi komai, ta ƙara juyar da kansa ya zama brain dinsa ta dawo 'empty' kamar yadda muka same shi a day one. Sannan ina so koda ya tashi kada kowa ya san ya tashi, har sai nanda kwana biyu."

Kafayat, cike da mamaki, ta ce: "Mehtav, kin san me kike faɗa kuwa?"

Ta ce: "Eh nasani Doctor. Ko ba za ki taimaka min bane? Zan nemo wani likita. In kuɗi kike so, zan siyar da bracelet ɗin Mommy na, in baki duka kudin. Just make him forget that woman. Ni kuma na miki alkawari: we will make you our new mommy. Dama saboda mu kika ce Paa ya ƙi aure, tohm mu za mu saka shi ya aure ki. Kin san za mu iya ko?"

Kafayat ganin ga koshi, ga kwanan yunwa-ta kasa amsawa. Ta san irin influence ɗin da yaran suke da shi wajen babansu. Ko yau suka sa shi a gaba da rigima, zai aureta, ya maida ta gidansa. Amma kuma magana ake yi ta Yariman ƙasar Nuristan. Yanzu idan ta yi masa wannan allurar, abu ya je ya dawo-if anything went wrong, ta san ba ita kaɗai ba: her entire family will be wiped out. Kilama daga ranar ba za a sake jin ɗuriyarsu ba har abada.

Muryar Mehtav ta ji tana kuka: "Nifa ba kashe shi nace ki yi ba Doctor. Ce miki nake kawai ki masa allurar mantuwa for the meantime, har sai waccan matar ta tafi. Tukunna sai ki ɗaura shi kan magani."

"Hmmmmm," Kafayat ta faɗa kafin ta ce: "Mehtav, zan zo gidan gobe kafin ya farka. We will talk in person. Banason mu yi taking any rash decision cikin sauri. What if in ya tashi bai ma tuna ta ba? Ba ki ga in muka masa allurar mantuwa zata ƙara damaging kwakwalwarsa ba?"

Mehtav tace: "I don't care! Just do it. Ni kuma ya za a yi na zauna da shi? Allah!"

Kafayat tace: "Mehtav, ba ki san me kike faɗa ba. Sai nazo dai kawai."

Bata jira me Mehtav za ta sake cewa ba, ta katse wayar.

Mehtav ta kifar da kanta a gurin-image sleeping position ɗin su yake dawo mata fresh a kwakwalwa. Da kuma yadda Islam ta sa Taj a gaba tana ma yi mata faɗa akan a aura mata shi-da za su yi.

Take take, take jin wani irin tsanarta yana shiga ranta. Tana jin kome ye ma za ta yi, don ta yi getting rid of her daga rayuwar EHSAAS-baki ɗaya.

© Fatoum's Passion EHSAAS 🩷 Kar a manta: Share • Comment • Like [30/05, 21:05] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

Follow me on Instagram@fatoumpassion

Not edited

It's Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.