EHSAAS

Chapter 28

by @fatoumspassion

Mehtav tunda ta gama waya da Kafayat, kasa wani motsin kirki tai. Deep down, tana jin cewar she's not right, amma kuma baƙar azabar kishin Islam da ke a ranta ya sa take jin kamar dede tayi.

Motsi taji kamar mutum, sai ta ji kuma sassanyar sallamar Islam ta shigo. Ba ta amsa mata sallamar ba saboda yadda ta nisa cikin tunani. Islam ɗin ma ba ta ce mata wani abu ba, kawai ta nufi ɗanta dake barci. Ta ƙarasa tana dauko ta rungume shi a jikinta har ta nufi ƙofa zata fice, sai kuma ta juyo tana kallon Mehtav kamar wadda ta tuna da wani abu. Ta ce mata:

"I'll forever be indebted to you, Mehtav. Thank you for saving him."

Tana ƙarasa faɗar hakan ba ta jira jin reply ɗin Mehtav ba, wadda ita Mehtav ba ta yi niyyar kulata ba. Dama har ta fice ta bita da kallo. "She's not this wicked," ta furtawa kanta tana riƙe kanta da kanta. How can she even think of hurting her beloved? In ta yi hakan, sunanta kenan zasu zama ɗaya da mutanen dake hunting rayuwarsa. Ta ayyana a ranta tana jin jikinta gaba ɗaya ya mutu murus kamar an zare mata duk wata laka. Gashi Abeey ce kaɗai abokiyar shawarar ta a duniya, kuma tun jiya taga daga dukkan alamu ba zata goyi bayanta ba, saboda ba ta san meye kishi ba. Ba ta san meye ma zama da kishiyar da ka san ta fika komai da komai ba.

Ta jima a gurin zaune tana riƙe da kanta tana jin kawai she needs someone to talk to. Amma waye zai fahimceta ya saurareta ba tare da ya yi judging ɗinta ba?

Kwankwasa ƙofar ɗakin nasu taji ana yi. Wanda mutum biyu ne kacal ke kwankwasa mata ƙofa irin haka, saboda kasancewarsu mazan gidan ba sa shigo musu ɗaki direct ba tare da sun yi knocking ba - it's either Paa ko kuma Islam. Da sauri ta dago tana kallon ƙofar, muryarta cike da rauni ta je faɗin:

"Come in."

A hankali Paa ya turo ƙofar ɗakin yana shigowa, jikinsa sanye da wata black jallabiya mai maiƙo, wadda tayi wa jikin sa na dattijai taka matuƙar kyau da tsari. A hankali ya je faɗin:

"Can I come inside, Mehtav?"

Da sauri ta shiga ƙoƙarin saita mood ɗinta. Ta jinjina masa kai tana ɓoye hawayen da yake kan fuskarta. Karasowa yayi gefen ta ya tsaya akanta yana karanta yanayinta. Duk yadda ta so ta ɓoye masa ƙuncin da yake cikin zuciyarta, ƙasawa tai. Ta fashe da kuka ganin yadda yake binta da kallon da yafi kama da na tausayi.

Zama yayi a gefenta, bai hanata kukan ba. Sai da taci kukanta ta koshi, har da shashsheƙa, sannan ya kamota zuwa jikinsa yana rungumeta. Yana jin tabbass yana da hannu wajen karya zuciyarta, domin da be bata hope na samun EHSAAS ba, ya yarda da yarsa ba zata taɓa zurmawa cikin son yaron nan haka ba. Zata rinƙa tunanin me ze je ya dawo, amma go ahead ɗin da ya nata shine ya gama lalata komai. Tunda gaskiyar wacece Islam ta bayyana, yake dana sanin abinda son zuciya ya kaishi ga aikatawa da kuma ƙwadayin haɗa zuria da jini mai daraja kamar jinin Fulani Hajar.

Yaso Fulani Hajar kamar ransa zai fita tun kafin ma ya san da wacece ita. Ba zai taɓa mantawa ba, a ƙauyensu shishi kaɗai ne mutumin da yayi nasarar samun scholarship yayi makarantar turawa dake cikin birni - makarantar secondary ɗin da ake kira da Teachers College a wancan lokacin. Yaya mata ba a fiye barinsu suna zuwa makarantar boko ba, sai yayen masu mulki da suka waye.

Anan ne kuma zuciyarsa ta faɗa da soyayyar Fulani Hajar. Love at first sight kuma love ne da ba a taɓa mai reciprocating ba. Soyayya ce wadda tayi kusan ajalinsa. Soyayya ce wadda gaba ɗayan rayuwarsa ya ƙwallafa rai akanta. Ya jure cin mutunci, zagi, hantara da tozarci daga dogarai da kuma 'yan uwan Fulani Hajar har sai da ya tabbata ta san da zamansa a wancan lokaci. Amma ba ta taɓa mai wani kallo sama da na head boy ba - dalibin da yafi kowa ƙwazo a makarantar. Tana JSS 3, yana SSS 3, kuma yana daya daga cikin sanadin da yasa aka cire Fulani Hajar daga makarantar sakamakon yayanta Abdul Aziz dake aji daya da shi a wancan lokacin. Da ko kallo ba su isheshi ba, yan group ɗinsu Abdul Aziz ba sa ma mu'amala da yaran talakawa kamar shi.

Sanda suka gane ya ƙwallafa rai ya daura ido akan Fulani, lokacin suka yi mai cũne. Daga gidan sarautar Borno aka kama shi har gaban giwar Sarki aka kaishi. Mahaifiyar Fulani Hajar lokacin tana da rai, inda ta sha ta masa layi da yarta aka saka mai dokar tabaci kan cewa in dai har ya ƙara daura ido akanta - ba iya makaranta ba - sai an tsireshi a bayan gari.

Har yanzu yana tuna kalaman da matar da ɗanta Abdul Aziz suka faɗa masa - cewa "Ba kai ba, kuma ba zai taɓa kaiwa ba. Kuma har abada jininsa da nasu ba zai taɓa gauraya ba. Shi din ba kowa bane face talaka, fakiri, ɗan ƙauye kuma kaskantacce."

Ya dan runtse idanuwansa, yayi domin har yanzu yana tuna yadda aka cireta aka mata aure a sanadin sa. Yake kuma yana tuna yadda yake cikin jama'ar da suka halarci daurin aurenta da Sarki Nashwan, mutumin da ya kusan haifarta. Ya ninka shekarunta yana kallo lokacin da aka ɗanƙawa Nashwan ita a matsayin matarsa a bainar jama'a inda ya ayyana babu abinda zai raba shi da matarshi bayan mutuwa.

Duk wani arziki da yake takama da shi a yau, rashin auren Fulani Hajar ne yayi motivating ɗinsa yayi shi - domin wata rana idan ya samu haɗuwa da family ɗin Fulani, ya bugi kirji, ya nuna musu cewa yes, he made it. Shi din multi-millionaire ne yanzu, wanda yake neman halal dinsa kuma wanda yayi making a rayuwa ba tare da taimakon kowane mai mulki ba. Ya ɗauka yin kuɗi shine zai zame masa key na zama mai arziki a idanuwan masu sarauta. Amma bai san ba haka abin yake a fannin dangin Fulani Hajar ba. Don ba zai manta ba, ya taɓa haɗuwa da Abdul Aziz a Umrah da ya je tare da mahaifiyarsu Mehtav a wancan lokacin. Irin kallon kyama da tsanar da yayi masa abin ya ba shi mamaki.

Sannan a gaban idanuwansa yaga tawagar mijin Fulani Hajar tazo da ita kanta Hajar ɗin. Dayake masu mulki ne har ɗakin Ka'aba mai tsarki aka buɗe musu. Yana kallo aka hanashi shiga shi da matarsa da tsohon cikin Mehtav - wanda abin yayi mata matuƙar ciwo saboda yadda mahaifiyarsu Mehtav ta ƙwallafa rai - itama tana so ta shiga ciki. Ya saukar da kansa, yabi tawagarsu da niyyar neman alfarmar Fulani Hajar tunda ta san shi. Amma me? Suna fita daga Harami yana ambatar sunanta, yaga an zagaye shi da manyan bindigu kamar wanda yayi laifin kisan kai. Already sun shigar da Fulani Hajar cikin manya-manyan motocin da suka zo da su a wancan lokacin.

Yana ji yana gani aka kama shi aka kai prison da shi - wanda ya kusa dimauta matarsa a wancan lokacin. Sai da yayi kwana bakwai ba ci ba sha, sannan aka gabatar da shi a gaban King Nashwan - wanda shi ya ma riga ya manta da shi. Ya tambaye shi dalilin da yasa yake kira Sarauniyar da mace, matarsa, iyalinsa mafi soyuwa a gare sa a cikin bainar nasu. Abdul Aziz ne yayi caraf, ya sanar da King Nashwan cewa ai tsohon masoyin Fulanin ne.

Ga mamakinsa, kamar wani clown, haka King Nashwan ya maida shi - shi da makarrabarsa. Aka ikaice aka sha masa layi da gargaɗin kada ya sake, ko da tunanin Fulani Hajar a ransa balle ya kira ta, saboda ita da shi ba abu ɗaya bane. Sama tawa yaro nisa.

Abdul Aziz ya sake jaddada masa: su da gauraya jini da shi har abada. Wannan abin ya fi tsayamai a rai, kuma bai taɓa mantawa da wannan wulakancin ba - dede da rana ɗaya.

Shi yasa lokacin da ya gane waye EHSAAS ɗin, yaji kamar damar ce tazo gurin sakawa - ya auri yarsa su gauraya jini. Ta yadda za su gane cewa babu abinda ya fi ƙarfin hukuncin Ubangiji. Duk da tozarci da suka mai, shi din ya iya riƙe musu da cikin aminci, kuma har ya ba shi auren yarsa. Kuma shi - kaskantacce - yarsa zata haifa ma masarautarsu jikanta.

Wannan shi ne kadai burin Paa akan EHSAAS. Amma ko kaɗan bai taɓa da nufin cutar da EHSAAS ko Mehtav in the process ba. Amma gashi, garin son zuciyarsa yarsa ta zama victim ɗin unrequited love. Domin kukan Mehtav din har cikin ransa yake ji.

Da ƙyar ya samu ya lallasheta tai shiru. Shi ma ya rasa da wane baki zai buɗe yace mata tayi haƙuri da maganar EHSAAS har abada. Domin sai yanzu yake gano illolin da ke cikin auren kamar zai fi alheran da yake ganowa. Kuma rayuwar yarsa tafi fansarsa mahimmanci.

Paa tafurta a hankali tana dada shigewa jikinshi. "Ina sonshi, Paa. What if ya tashi yace baya sona? Matarshi yake so kawai?" Ta karasa fada tana kankameshi.

Dan shafa bayanta ya shiga yi yana fadin, "Shhhshhhshhh, Mehtav, kisani everything that happened and what will happen next is already written. Let's just pray for the better. Kisani idan Allah yayi, zaki auri EHSAAS. Kome ze faru, ko mata hudu ne dashi, Allah ze kawo kaddarar da zesa yarabu da daya ya aureki, kin ji? Amma ina son ki dago ki kalle ni yanzun muyi wata magana, kin ji diyata?"

A hankali ta dago tana shashshekar kuka tana kallonsa. Hannayensa yasa ya shiga share mata hawayenta cike da lallabi da kaunar da yake mata mara sirki irin ta da da uba. Yake fadin, "Let's try and focus on Mehtav alone, kin ji? EHSAAS is someone that entered our life, Mehtav, ba tare da munsani ba. Kuma Allah ne daya jefoshi cikin rayuwarmu. Yafi kowa sanin dalilin yin hakan. Kisani, komeye ze faru is for the better. Inason ki fara kokarin fighting wannan feelings din da kike ji a ranki towards him. Nasan yarinyata is a fighter. Mehtav is very bold and pretty. She can overcome any heartbreak in this world. Mehtav is the best girl a duk duniyar nan. Itace fa yarinyar da mamanta ta rasu, ta fara da jaririya karama danya bata san komai ba. She managed to take good care of her. Mehtav tayi overcoming rasa mom dinta at early stage. Toh, menene kuma Mehtav ba zata iya overcoming a duniyarnan ba?"

Yafada cike da wani irin so da tattali da yake ma yayan nashi da ba zaka taba gane hakan ba har se daya daga cikinsu ya shiga matsala.

Cike da shagwaba take fadin, "I'm not strong, Paa. And Mommy fa? Nasan barin duniya tayi. Shi kuma yana duniyarnan. How can I let him choose another woman over me?"

"Shhhshhhshhh," ya fada yana dada jawota jikinsa. "Stop saying such things, kin ji? I know you can do it, Mehtav. Kuma itafa wannan matar da kike fada, she knows him before you, my daughter. Let's not be selfish, kin ji? Mehtav din da na sani is always considerate. She's pure-hearted. Kyakkyawar zuciyarta is beyond pure diamond. Dago, yanmata, ki fadamin wace kasa kikeso in kaiki ki yi Master's dinki. Forget about auren nan and everything, and forgive Paa for putting you in this situation. Let's focus on Mehtav alone."

Dagowa tayi tana kallonshi cikin mamakin jin furucinshi, shi da ba taba yarda ya kaisu waje karatu ba. A cewarshi, yara suna lalacewa, su koyi dabi'ar banza iri-iri. Amma yau shine yake cewa ze kaita karatu waje.

Yace, "Ina jinki, fadamin wacce kikeso-John Hopkins, Princeton, NYU, WSU, ko Harvard kikeso? Duk ki zaba, I promise duk inda kikeso nan zan kaiki."

Tace, "Paa, cin hanci ne fa wannan. Ni duk nafison EHSAAS akan makarantun nan. Ni ba son karatu ba, aurenshi kawai nakeson yi."

Cike da fahimta yace, "Nagane. Aiba EHSAAS kadai ba, NURISTAN duk ma zan bawa princess dina. Ni dai burina ta daina kukan nan. Allah yahuci zuciyarta."

Se a lokacin tayi murmushi don tasan wasa yake mata. Ta dan dago tana kallonshi kafin ta sake komawa jikinsa tana fadin, "I love you, Paa. You're the best. But let's wait a bit. I promise I'll teach him how to love me again."

Ta fada tana reassuring kanta cewar indai har ya taba sonta, zeke raji yana sonta, koda ya manta komai da komai ne na rayuwarsa.

Sun jima da Paa a haka kafin ya fita, kuma se da ya tabbata ya ga tana murmushi, kuncin da ke ranta ya ragu sannan ya fito daga dakin, yana jin gaba daya laifinsa yafi yawa a wannan al'amarin.

He shouldn't be that greedy.

Dakyar ta iya shiga, ta yi wanka ta fito ana kiran sallar Asr. Dama ta dauro alwalarta, ta shiga closet, sai da ta zaba ta dirje cikin kayanta. Ta zabo wasu hadaddun riga da skirt na Swiss lace dinta wanda yake matukar amsar jikinta. Ta saka, ya yi mata cif-cif, yana fitar da duk wata baiwar kyan jiki da Allah ya bata. Domin itama ba daga nan ba bangaren kyau. A gaban mirror ta tsaya. She's moderate, ba ta da wani girman jiki kamar Islam, kuma ba ta da wata rama. Komai nata dan chass chass daidai da jikinta. Sai da ta gama kare ma kanta kallo, ta san yes, ta hadu. Sannan ta fito da sallayarta da hijab. Anan cikin closet ta yi sallarta. Tana idarwa, ko addu'a bata tsaya yi ba, ta zauna gaban mirror, ta shiga tsantsarawa fuskarta kwalliya mai daukar ido. Sai ka yi tunanin gasar kyau za ta je. Kwata-kwata fa, make-up is not her thing, amma ji take yi ai yau in ta yi make-up dole za ta fi Islam din kyau.

Powder da ta shafa tai daidai da farar fatarta mai matukar taushi da kyau da sheki. Ta saka, ta kara wani irin haske mai daukar ido. Ta dau kusan minti 40 tana lailaye fuskarta. Ta gama, ta dakko jewellery set din mom dinta na gold da ta barmata. Ta shiga jerawa a wuyanta, da kunnenta, da hannayenta. Kawai so take taga ta fi wancan yarinyar kyau yau dinnan, tunda taga ba ta zo da wani kayan kirkiba. Yan dogwayen rigunan da Taj ya kawo kawai take sawa.

Tana kammalawa, ta sako takalminta, me dan tsayi. Ta dauro dankwali, ture kaga tsiya tana baza kamshi. Tako ina, ta fito falon, ba ta ga kowa anan ba. Hakan ne yasa ta nufi dakin EHSAAS a dan hanzarce. Ta dauka ko nan Islam ta koma. A hankali ta tura dakin. Wani irin shock ta shiga ganin idanuwansa a bude yana kallon saitin kofar, amma da alama allurar da aka mai ce ta kashe mai jiki ya kasa motsi. Kamewa tai chak saboda ta tuna tsaf Kafayat tace "senan da 48 hours ze farka." Tohm, garin yaya ya tashi kasa da 24hrs? Ko dai yana da karfin jinjina?

Kallon kurilla taga ya kureta da shi. Da sauri ta karasa, taga yana mata wani kallo kamar ba ta taɓa ganinsa ba a rayuwa. Zuciyarta har ta fara skipping. Tana jin wani irin sanyi ganin this is the same kallo da ya yi mata sanda ta fara ganinsa. Tana jin ba ma sai Kafayat ta mai allura ba kenan, ya manta komai da komai. A hankali ta zauna a gefensa tana murmushi, tana jin dadin itace mutum na farko daya fara gani. Don haka duk abin da ta fada da shi za a yarda, kamar yadda ya fi yarda da Abeey akan kowa a wancan lokacin.

Kama hannayensa tai, ta saka a cikin nata. A hankali, cike da tsantsar sonshi da nuna damuwa a kanshi take fadin:

"Ka tashi? Ya jikin naka?"

Kallonta taga ya cigaba da yi, bai bata answer ba. A ranta tace:

"Ba ya tuna komai ba. Wayyo Allah, na tare da ni. Ba ma sai na yi komai ba. Me kake tunawa dangane da past dinka? Ya sunanka uhm?"

Ta tambaya tana tsareshi da ido itama. Dan janye hannayensa yayi cikin nata yana lumshe ido amma ya kasa motsi. Mikewa tai a hankali tana fadin:

"Kankane yake ciwo?"

Dan jinjina mata kai kawai yayi. Tace:

"Sannu. Anjima likita zata dawo. Ya sunanka?"

Dan kallonta yayi cike da mamaki kafin yace:

"EHSAAS of course."

Wani irin daram dam kirjinta ya bayar. Ta zaro ido tana kallonsa kamar taga wani zombie. Ta kasa motsi tana kallonshi. Yana dan yamutse fuska irin kallon nan da yake mata farkon ganinsa da ita, ne irin kallon waye ita nan yake mata. Cike da rawar murya tace:

"EHSAAS kuma?"

Sai saita kanta tayi kafin tace:

"Kila abin da yake iya tunawa kenan."

Ta nuna kanta tana fadin:

"And I... ni wacece? Ya sunana?"

Gani tayi ya dage gira daya irin like seriously din nan kafin ya bude baki a hankali yace:

"Mehtav... go and call my wife for me."

Jikinta rawa ya fara yi, ta shiga nanata:

"Innalillahi wa inna illahirraji'un."

So the worst scenario never happened. Ya tuna komai - everything, komai da komai. Ta shiga uku:

"Meyasa kuma yake neman Islam din yanzu bayan gata a gabansa? Ita da ta ceci rayuwarsa, kamata yayi ya rungumeta ya soma yi mata godiya."

Ƙoƙarin tashi ya shiga yi amma ya kasa gaba daya. Allurar ta sagar mishi da gabobin jikinsa.

"I need to see her right now, please Mehtav. Akwai abin da nake so na fada mata mai mahimmanci," ya fada with serious commanding voice, wanda tunda take ba ta taba jin Islam dinsu da irin ta ba. This is EHSAAS a gabanta, ba Islam dinta ba. EHSAAS din Islam. Shikenan, ta shiga uku, ta lalace.

Gan in kamar ba zata ce komai ba yasa ya shiga sake kokarin tashi. Da sauri ta karasa gabansa tana maidashi kwance. Cikin mastering emotions dinta take fadin:

"Sannu EHSAAS. I'll get her right away. Kadan ka kwanta kafin nan, kaji? Karka tashi."

Rike kansa da ya ji yana sara mishi yayi kawai, ya koma ya kwanta, bai mata musu ba. Domin so yake ya sanar da Islam wata muhimmiyar magana, koda bai sake tashi ba. Yana jin ya gama mata maganin abubuwan da za ta fuskanta a cikin gidansu bayan bashi.

A hankali Mehtav ta fara fitowa a dakin tana waiwayonshi. Tana karasawa bakin kofar ta faki idanuwansa. Kawai ta zare key daga ciki, ta fito tana kulleshi ta waje. Jikinta har rawa-rawa yake yi. Ta nufi daki, gelenta kawai ta zara, ta fito waje. Tasan allurar ba zata taba sakinsa ba balle ya yi kokarin fitowa. Hakan yasa ta nufi waje. Taj da Islam ta gani sun zauna kasan wata bishiya saman wasu fararen kujeru. Junior yana hannun Taj suna ta wasa. Da alama wata muhimmiyar magana suke tattaunawa.

Da sauri ta karasa, bata nuna kwata-kwata damuwar da take ciki ba. Ta ce ma Taj:

"Can you please borrow me your phone? Zan dan yi wani kira mai mahimmanci ne. Wayata ba kati."

Dan kallonta yayi kafin yace:

"Bari nai crediting layin naki. MTN dinnan ne ko?"

Da sauri tace:

"Pls ban da lokaci. Network ne ke rawa, shiyasa nima ban saba kaban. Pls."

Cikin mamaki ya dau wayar yana danka mata. Ta matsa can gefe inda suna ganota amma ba sa ganin abin da take yi. Call logs din Taj ta shiga bincike. Ta soma mai country code kawai take dubawa a cikin kiraye-kirayen da yayi satin, sabo da ta san dole Baban Peace sun yi magana. Ba ta wani jima da fara scrolling ba ta ci karo da lambar NURISTAN din. Ta dan kallo inda suke, akanta kawai. Ta kwashe lambobin ba bata lokaci don kada Taj ya yi zargin batai wani kira ba. Yasa ta saka kiran lambar level coordinator dinsu. Yana dagawa, ba su yi wata doguwar magana ba. Ta ce mishi dama tana son taji wai yaushe za a yi final paper ne, ta manta. Abin ya ba Doctor Kamal din mamaki, amma sai ya fada mata. Godiya kawai tayi mishi, ta katse kiran tana mayar wa da Taj wayarsa.

Fita tayi bakin gate, taga Dan Liti da Jabeeru suna shan mangwaro. Ta kalli Dan Liti tana fadin:

"Muje, zaka rakani unguwa."

Da sauri ya mike yana fadin:

"Tohm, Hajjaju Mehtav."

Parking space ta nufa don ya tsaya wanke hannayensa sosai. Kirjinta ke dukan tara-tara. Tashie bayan motar dake bude take. Number Kafayat ta shiga lalube. Ba ta jima da fara ringing ba, ta dauka tana fadin:

"Ban ce ki bari sai gobe in na shigo ba?"

Bakinta yana rawa, tace:

"Doctor ya farka kuma wallahi ya tuna komai da komai. Har sunansa da sunan matarsa da ni kaina!"

Kafayat cikin mamaki take fadin:

"Ke Mehtav, karki raina min hankali. Ban taba ganin mutumin da na yiwa irin wannan allurar barcin ya tashi kafin awanni 48 ba."

Tace:

"Wallahi Doctor, da gaske nake miki. Yanzun ma nemanta ya aikoni yi wai in kira mai ita. Amma dai na kulleshi a dakin. Na san ba zai iya motsin kirki ba. Waidan wajanki zan taho. Na ma shigo mota-"

"Stop!" cewar Kafayat kamar tana gabanta take fada mata.

"Karki zo nan! Ke kin fiya azarbabi. Yanzun ki koma kiga na tabbata kawai. Cikin sambatu ya farka, zai koma barcin in less than 5 minutes. In kuma bai koma ba, a cikin side drawer dinsa na ajiye drugs dinsa da allurai. Akwai wata allura nan."

Ta shiga gaya mata sunanta da amount din da za ta zuba a syringe tai mishi a cikin drip din da aka daura mai. Tace allurar barci ce. Mehtav, iya amount din da nace miki zakiyi. Karkiyi sama da hakan, ba zai sake farkawa ba sai bayan kwana biyu. Kafin nan kuma mun nemo abin da za mu yi. Don ni gaskiya idea dinki ta juyar da kanshi bata kwanta min ba.

Tace:

"Amman doctor, in bai yi barcin ba fa? A gabansa zan yi allurar. Ya san fa ni ba likita bace ba."

Tace:

"Mehtav, it doesn't matter. Ba ki ce everything is fair in love and war ba? Zabinki ne ba nawa ba. Ni iya taimakon da zan iya baki kenan. Gaskiya ba zan ja wa kaina masifar da ba zan iya dauka ba."

Jinjina kai Mehtav tayi. Daidai nan Jabeeru yana shigowa motar da bismillah a bakinsa, yana kokarin mata key. Mehtav kawai ta bude kofar ta fice fiiiii kamar wata iska. Su Islam suna hangota daga inda suke din har ta shige cikin gida.

Taj yace:

"Ikon Allah, Islam, Mehtav is not like this. Ban san sanda ta zama mai saurin fushi irin haka ba."

Murmushi kawai Islam tayi tana fadin:

"Is not her fault. Mijinta ne sanadi. Shiyasa bata son ganina anan."

Dan murmushi yayi yana fadin:

"Ke wai ba kya kishin ne? Ita da ta je budurwarshi, so-called budurwa ma zance tana wannan azababben kishin a kanki. Amma ke ko damuwa ba ki ba."

Dan jim Islam tayi before tace:

"Taj, kishina yafi na Mehtav zafi. Danneshi shine mafi a'ala akan bayyanashi. Kuma har abada ba zan taba iya bayyanashi akan macen da ta ceci rayuwarsa ba. Mehtav is a good girl. When she gets to know who EHSAAS really is, zata dena ne."

Yace:

"How sure are you?"

Kallon kofar inda Mehtav ta wuce kawai take yi. Haka take kamar me jinnu, instincts dinta ne yake bata tabi Mehtav saboda kamar a fusace ta ga ta fito kuma ta koma cikin gidan. Bama taji yadda Taj din ke sake maimaita mata. Zumbur ta mike ta juyo tana fadin, "Inazuwa," ta nufi cikin gidan da sauri. Taj ya rufa mata baya yana rikeda Junior a hannayensa.

Mehtav na shiga gidan da sauri-sauri ta karasa ta saka key ta bude dakin EHSAAS. Tanayi hannayenta yana rawa saboda a lokacin hankalinta ya gushe kawai, tsantsar kishine ke dawainiya da ita da wata irin soyayya da ba zaka iya cemata love ba, face obsession. Tana shiga dakin, idonshi a lumshe ta tarar da shi. Motsin shigowar ta ne yasa ya dan bude idon eyelids dinsa. Kana gani kasan nauyi suke mai saboda barcin da ke kokarin sake daukarshi.

Ganin ta shigo ba tare da Islam ba, ya bita da kallo. Tsabar rudewa ko kofar dakin bata yi yunkurin kullewa ba. Ta shiga bubbude bedside drawers dinsa. Cikin sa'a, tana bude ta biyun taci karo da ruwan allurar da syringe. Duk yana kallonta. Tai marmaza ta shiga hadawa. In few seconds ta gama, ta zuke ruwan allurar duka tana kallonsa, hawaye na kwarara a idonta. Ta karaso gabansa, hannayensa me dauke da cannula ta riko. Instead of ta mai cikin ruwa, saboda tsabar azarbabi tana tsoron kada wani ya shigo ya tarar tana mai. Kawai ta cir is mishi ruwan tana barin iya cannula din.

A hankali yake kokarin zame hannunsa yana fadin, "Islam..." Ta shiga juyemai ruwan allurar a jijiyar hannunsa tana fadin, "I love you, pls forgive me, it won't hurt you. Barci kawai zakai for few days." Tana zare ruwan allurar, kiram da Islam dake bakin kofa tai mata, yasa ta firgice tana wurgar da allurar a kasa. Taj da ne bayanta shima yaga allurar da Mehtav ta wulla. Da sauri ta karasa tana yin kan EHSAAS din da idonshi ke bude yana rufewa.

Saman gadon tahaura ta tallafo face dinshi tana fadin, "Sire! Sire!" Sosai yake kokarin daga ido ya kalleta, amma allurar da ta mai daya kamata ta shiga gradually lokaci daya ta zuba mai ta fara cin karfinsa.

"Sire pls wake up, kana jina?" Islam ta fada tana sake riko face dinsa cikin hannayenta. A hankali ya shiga bude baki yana kokarin fada mata wani abu amma kamar ya kasa. Wani irin raunataccen kuka Islam ta saki tana fadin, "Sire, you'll be fine, kaji? Don't worry." Ganin bakinsa na motsawa ta saka kunnenta saitin bakinsa ta yadda bakinsa ke gogar kunnan nata.

"Mims, Islam... Mims..." taji ya shiga fada yana sake maimaitawa. "Na sani..." Ta dago tana kallon shi. "Na san Mimah ce behind everything, Sire. I know her true colour already." Wani kayataccen murmushi taga ya sakar mata. Yana sake motsa bakinsa ta maida kunnenta tana fadin, "Hang in there."

"Taj pls, ka kira mai likita!" Mehtav jikinta rawa yakeyi, ta kasa motsawa daga inda take. Gashi bata jin me EHSAAS ke fadawa Islam din kwata-kwata. Taj kuma ya tsugunna ya dau allurar da yaga ta yarda wacca ba tantama da alama yiwa EHSAAS tai. Ya zaro wayarsa ya shiga wani app nasu nasirri yana scanning kwalbar allurar daya gani shima a yashe a kasan dakin. Ta shiga zubo mishi bayanai akan allurar. Mehtav tayi tsuru-tsuru tana hawaye, wani irin dana sani yana flooding mind dinta.

"1st June..." abinda Islam taji yana maimaitawa kenan, har idonshi ya rufe baki daya.

Sai a lokacin ta dago tana kallon Mehtav. Idanuwanta sun yi wani irin jajir kamar wuta. Sosai Mehtav taji jikinta na kadawa kamar tafalle a guje. Domin ta san Islam din ta ga abinda tai. Gani tai ta gyarawa EHSAAS kwanciya tana mikewa daga kusa da shi bayan ta tabbatar da barci yay, ba suma ba. Karasowa tai ta kamo hannayen Mehtav tanufi hanyar waje da ita. Kawai Taj ya mara musu baya. Bata sake hannunta ba, sai da ta karasar da ita falo ta tsareta da gwala-gwalan idanuwanta da yake firgitar da mara gaskiya.

"Allurar me kika mai?" Ta jefa mata tambayar. Don haka kawai taji a jikinta Mehtav din ba zata taba cutar dashi ba saboda taga irin son da take masa. Amma kuma idonta ya gane mata abu daban. Mehtav shiru tai, taki cemata komai.

"Kee Mehtav nace allurar me kika mishi?"

Da sauri Mehtav tace, "Barci..." Saboda tsawar da Islam din taimata har cikin kanta ta jita. Kuma guiltiness ya baibayeta.

"Ke likitace?" Islam ta tambaya tana tsareta da ido. Girgiza kai tashiga yi. Ta kalli Taj tana fadin, "Call that doctor pls. Karmuje yay mishi wani illar a jikinsa." Taj yace, "Right away," ya soma kokarin kiran doctor. Da sauri Mehtav ta karasa tana fizge wayar a hannayensa cikin in-ina take fadin, "Ba abinda zatamai ai... Ai kwana biyu kawai zeyi yana barci har se sanda babana ze zo ya tafi da ita daga gidannan."

Cike da mamaki Islam take kallon Mehtav. Don ta san batai maganar da ita ba. Ta juyar da idonta ga Taj. Ganin kamar tana zarginsa yayi saurin, "I did not tell her anything."

"You sedated him to sleep for good two days!" Islam ta fada tana rike kanta. A fusace ta juyo kamar zata yi kan Mehtav din, kuma seta damke hannayenta tana nunata da yatsa kafin tace, "You're mad!" Tana sauke hannu, ta zube a kasa. Mehtav binta kasa tai tana kokarin fara bata hakuri. Islam ta daga mata hannu tana fadin, "I'm very, very disappointed. Is this the type of love dake cewa kina mai? Kinsan illar barinsa cikin wannan halin kuwa? You're very selfish, Mehtav!" Ta fada tana tureta daga gabanta.

Mehtav ganin reaction din da tai, tunanin peace zata bashi take ba. Ya kara sagar da gwiwarta gaba daya, cikeda nadama da dana sani take fadin, "I didn't mean to hurt him. Kawai banason ki kwace shi daga gurina ne, don Allah kiyi hakuri."

Girgiza kai Peace ta shiga yi tana fadin, "Hakuri? Hakuri fa kikace? Definitely kinsan cewar yatashi ya tina komai na rayuwarsa. Shine for your selfish interest kika maidashi barci. Kina tunanin EHSAAS zeso mace mai son kanta irinki?"

"Kinsan mission din daya kawo shi kasarnan kuwa? Toh bari kiji. Ingaya miki: ya zo ne don ya ce ci ran yankin guda dake NURISTAN. He is fighting a war against his own sister."

"Aikinjishi ko? Definitely you must have heard him yana kiran sunanta Mims, and some date that nikaina bansan mehakan yake nufi ba. Kifadamin tsakani da Allah, daya tashi meya fada miki? Did he ask for me?"

Mehtav kuka ta cigaba da yi, ta girgiza kai se kuma ta gyada kai alamar eh.

"Talk!" Cewar Taj daya fizgota kamar yadaketa. Tose kunnuwanta tai domin tun da take a rayuwarta, yayanta Taj ba taba mata irin wannan tsawar me shiga kwakwalwa ba.

"Yes, he did ask for her. Sunanta kawai yake kira fa, ba ko min kallon kirki ba. That made me angry."

"Angry?" Taj ya fada sarcastically. Daidai Paa yana karasowa falon saboda hayaniyar da yake ji sama-sama. "Meke faruwa anan ne?" Taj ya kalli Mehtav yana nunata da hannayensa yake fadin, "Paa, gatanan, ta maka bayani. She just injected Prince with sedative hypnotic drug."

A mamakance Paa yake kallonta. Ta fashe da kuka tana zubewa agurin, "I'm sorry pls. Nayi dana sani." Paa yace, "Mehtav, maganar da na ji just now gaskiyane?" Da sauri ta mike ta je gurinsa tana rike hannayensa, "Paa, bazan sake ba, dan Allah ku yafemin. Inace mungama wannan maganar dake dazun a daki..." "Mehtav, this is not you. Mekike tinani kika aikata irin wannan danyan aiki haka? Ku kiramin Kafayat ta dubamin yaron nan yanzun!"

Mehtav kara damke wayar Taj da take hannayensa tai. "Bazaki ban wayar ba?" Taj yafada yana karasawa, ya kamo hannayenta, ya shiga kokarin cire wayarsa a hannayenta. Ta damke, "Zan gaura miki mari in baki bani ba!" Ya karasa yana fizgewa don karfinsu ba daya ba.

Ya shiga dialing. Da sauri tace, "Ai, ai... Itace! Tace in mai wannan, babu abinda ze sameshi fa." Mehtav ta karasa fada cikeda rashin wayau.

Paa yace, "What? Ita wa?" Hannunta ta shiga yarfarwa tana labarta mishi duk wani abu da suka tattauna tare da Kafayat a waya ba tare da ta boye mai komai ba. Saboda dan banzan tsoro ne da ita. Dama kawai kishine ya rufe mata ido.

"Innalillahi wa inna illahirraji'un!" Haka Paa yashiga fada. Islam kawai tsayawa tai tana kallon Mehtav, cikeda takaicin halin rashin tunaninta.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment & Vote. [31/05, 20:36] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.