EHSAAS

Chapter 29

by @fatoumspassion

Gaba dayansu jugum jugum sukai a falon har zuwa lokacin da Dr safwan ya fito daga dakin EHSAAS din domin tunda paa yaji abinda Kafayat ta goyawa Mehtav baya sukai yaji baze sake kara dada yarda da ita arayuwarsa ba har abada, hakanne yasa yatura dan liti ya bugawa makocinsa Dr safwan kofa gidansa yana kallon gidansu shima likita ne amman ba mazauni bane kamar dai paa.

Aiko cikin sa'a aka sameshi agida kuma yazo cikin gaggawa don ya duba EHSAAS din, dake professional Dr ne yanada kusan duk abubuwan emergency da zeyi attending to EHSAAS din.

Zaman jirannasa sukeyi haka Abeey da inna sukazo sukai joining dinsu duk da basusan kan labarin me yafaru ba tundaga farko sunga dai Mehtav ta rakube guri daya tanata kuka babu kuma wanda ya kulata bare kokarin rarrashinta.

Abeey ce takarasa tarungume ta tanata tambayar ta "me yasameta?" takasa ma bude baki tai mata magana kawai kallon kofar dakin EHSAAS din takeyi.

fitowar Dr safwan din yasa dukkansu suka mike kamar zasu karasa su taroshi don tsabar yadda suka damu da sanin condition din EHSAAS din,

Dr. Safwan ya tsaya a gabansu cikeda nutsuwa sbd dattijone sosai ze iya girmar paa ma, yana kallon yadda Mehtav ke jan hanci da hawayenta dake zuba kamar ruwan damina. Abeey ta rike hannunta, tana kokarin ba ta karfin guiwa. Taj kuma yana gefen Islam da bata mike tsaye ba saboda junior dayay barci ajikin ta.

Doctor ya ce a hankali, da kwantar da murya: "Ku kwantar da hankalinku… EHSAAS ba zai mutu ba. A cikin gaggawa na yi masa emergency reversal injection wadda aka fi sani da Flumazenil, domin karya tasirin waccan allurar sedative-hypnotic da aka masa."

Islam ta dago da idonta da suka kumbura,tace "Dr ze farka ko?"

"Insha Allah, zai farka," yabata answer cikeda assurance "Yanzu haka jikinsa yana mayar da martani ne, Na saka shi a karkashin kulawa ta musamman. Mun daura masa oxygen domin taimaka masa da numfashi. Duk da yana unconscious har yanzu, alamu sun nuna cewa jikinsa yana kokarin dawowa daidai amman dai gaskiya duk likitar data mai wannan allurar da akwai ganganci alamarin wannan ze iya sashi cikin mummunan hadari da Allah besa anyi tackling cikin sauri ba kuma dadin dadawa yanada lafiya sosai ga karfin zuciya he is fighting hard to live da wata mgnr ake yanzun ba wannan ba"

Paa yajuya yana kallon Mehtav irin kinji dinnan ko,sake fashewa da kuka tai tanason ta tambayi Dr yaushe ze tashi amman kunya takeji da tsoro haka dai yace musu subashi zuwa awa 24 in be farkaba zedawo kawai suwuce asibiti direct godiya paa yashiga yimasa ya rakashi har waje yay masa sallama tareda alheri mai tsoka ya wuce gida don daman yana cikin hutune.

Acikin falon kuwa Islam duk yadda Mehtav taso ta kulata banza tai mata ta tashi tai shigewar ta dakin EHSAAS din tai zamanta.

Abeey se tambayar Mehtav takeyi takasa bata answer inna tace "oh ni yanzun daga wannan se wannan kutattara yaro kumaida shi gaban iyayensa kunqi aiga irin tanan inya mace muku karku sake ku sakani acikin wannan batu" tamike tana nufar dakinta domin ita inta tata za'a bi kawai asallami su EHSAAS da Islam sutafi kasarsu can su karata.

Se can bayan sallar magrib sannan Taj yayi musu sallama yabar gidan, kuma cikinsu ba wanda ya sake cema Mehtav ko cikanki kuma silence dinsu ba karamin cimata rai yakeba yana cimata tuwo akwarya don tafison sumata fada, su zageta, koma sudaketa atleast zataji sanyi akan wutar dana sani da azabar datake cin zuciyarta, tana jin inama bata biyewa dokin zuciya ta aikata abinda ta aikata dinn yanzun dawana ido ma zata sake kallon EHSAAS.

tayi attempting bin Islam dakin yakai sau goma tana kasawa, daga baya se Abeey ta lallaba ta aikata ta dubo mata ita lokacin tace mata "ai sallah ma takeyi," tareda Abeey suka zauna jugum a parlour se da kyar sannan tafara labarta mata abinda ya faru sosai Abeey tasha mamakin Mehtav bata dauka zata iya wannaan haukar da rashin wayon akan kishiba ita data tambayi shawarar ta aida ta hanata yin wannan danyar aiki saboda lafiyar EHSAAS din gaba daya ta saka cikin hadari kuma damacan Abeey tasan Kafayat is up to no good itada mutuniyar kirkice aida ta hanata amman saboda son zuciya da alkawarin da Mehtav tamata yarufe mata ido seta biye mata.

rungumeta Abeey tai tazama kamar itace yayar, Mehtav kuma kanwar tashiga lallashin Mehtav tana cemata "is okay tunda tariga tai nadama aishikenan karta sake kawai, everyone is not above mistake,that is what makes us human" ta soma dan nusar da ita akan yadda take da da kuma yadda tamata fada lokacin data dena bashi magani.

sosai Mehtav taji dadin magana da Abeey domin Abeey badai wayo ba ga wisdom intana magana seka rantse wata babbar macen ce takeyi se bayan da sukai sallar isha'ee sannan suka ga Islam tafito daga dakin EHSAAS din ta nufi can dakinsu Mehtav din da yaron ta ahannunta.

acan tashiga tamai wanka don yau tashin hankali be saka ammasa na yamma ba, wankan mafa dakyar ta lallaba tanayi suna kokawa da junior dayake kokarin fin karfinta sbd girman jikinsa. Tana gamawa tazaunar dashi tana hada mai yan tarkace agabansa tashiga bathroom yadda za'ai ta farama wanke kayanta da nasa take tinani ta jima kafin tafito seta tarar da Mehtav harta shigo tadauki Jr din daga inda ta zaunar dashi tana mai wasa bata kulata ba kawai tafice adakin. afalo tasamu Abeey tace "ta bata detergent din da ake wanke kaya" mikewa Abeey tai tabi bayanta suka dawo toilet din tace "inwa ya Mehtav magana kuje bayan gida akwai washing machine ta iya amfani dashi" girgiza kai tai tace mata "aitasan da Mehtav din ta tambayeta" Abeey tabe baki tai tana dakko mata detergent din ta ajje agabanta tafice tabata guri, Mehtav duk tana kallonsu.

tara ruwa tai a bucket kusan cikin bucket din saboda arayuwarta bata taba wanke wani abu samada pants dinta ba shi kadai ta iya wankewa shima kuma seda ta auri EHSAAS ta iya. nanny dintace take wanke mata komai agidansu har innerwears, data aureshi kuma se yadaura be wani damuba in sunyi wanka da kanshi yake wanke mata dukda yana kokarin koya mata amman bata wani iya wankewa din sosaiba, wata irin sangartaccen reno da aka mata agidansu bewani damu da yagyara matanba.

kayan yaron ta saka tajuye kusan rabin bigsize detergent acikin ruwan tafara cudawa takai kusan rabin awa datayi datayi seta dan dago wai taga koya kara fari se nishi takeyi kamar wacca take aikin gabas kuma duk ta guggurje tsintsiyar hannayenta da detergent din, Mehtav jinta shiru shiru yasa ta zaunar da junior asaman gadonta takaraso tana kwankwasa mata kofar, "Islam kina jina? are you okay? Do you need some help?

Tanaji tamata banza, hakanne yasa Mehtav tadauka ko wani abunne yasameta tabude kofar ta tarar da ita tana wannan danyan aikin inda normal day ne da dariya zata mata amman sanin cewar Islam din na mugun fushi da ita saboda danyan aikin data aikata seta shiga tana kallonta kawai kafin tace "let me help you" bata jira amsarta ba kawai ta janyo bucket din zuwa gabanta tana zubarda rabin ruwan da Islam din ta loda tabar dan kadan daidai wanda ze isheta ta zazzaga omon in minutes ta cuccuda kayan yaro dake ba wani datti sukai ba ta daurayesu. tadakko dogwayen rigunan Islam din guda biyu tana fadin "bari na wanko miki su awaje akwai washing machine bata kulata ba harta fice a bayin da bucket din data gama dauraye kayan yaron tazuba aciki. se alokacin Islam ta danji sanyi tashiga wanke bayin tass tass sannan ta cire kayan jikinta tai wanka tadauro alwala.

bude inda suke ajje wankakken towels tai daya daga cikin guntayen towels din Mehtav tadakko tadaura tafito, mamaki ne ya kamata ganin an ajje mata sababbin pajamas marasa nauyi saman gadon Abeey data kwana jiya, batai kokarin tabawa ba tadai karasa closet dinsu tadan murza maya mayan Mehtav kadan shima sbd kada fatarta tabushe tai hakan. tasako katon hijab din data bata jiya Mehtav bata ji dadiba datazo taga kayan yadda ta ajjesu, tadan saci kallon Islam data idar da sallah se tace mata "uhmmm kinga islam wannan kayan barcine nadade da siyansu amman summin yawa bantaba sawaba shine na dakko miki kozaki amfani dasu kafin kutaai inba damuwa nabaki," shiru Islam tai kamar baza tace komaiba se kuma tace "toh" fuskarta babu yabo babu fallasa takarasa tadau kayan don daman tagaji da zama da dogwayen rigunan nan musamman inzatai barci takura mata sukeyi ita da take using transparent lingeries yawanci gurin kwanciya EHSAAS yasabar mata da saka irin lalatattun kayan barcinnan iri iri shiyasa takasa sabawa da barci da normal kaya. a closet tasako kayan kam cif cif jikinta harma yadan kamata kamar dan ita akayisu wandan nema yadan dage mata sbd yanayin tsayin daidai na Mehtav ne ita kuma tafita tsayi,tana fitowa ta dauke danta dake kan gadon Mehtav takarasa saman gadonta domin tana mugun bukatar barci ko kwakwalwarta zata samu nutsuwar gano me EHSAAS yake nufi da date din 1st june daya fada mata.

rungume Jr tai dayay lamo akirjinta amman bawai barcin takeyi ba tayi nisa cikin tinanin yadda akai gawar da aka kawo tai daidai da DNA din EHSAAS. muryar Mehtav dake kiranta ahankali cikin sanyi azatonta kotayi barci tafargar da ita daga tinanin datakeyi Islam, Islam

shiru tamata kamar bazata answer ba sekuma tajuyo tana kallonta tacikin dim light din dakin alamar tana jinta,tace "dan Allah kiyi hakuri nasan banida kalmar da zanyi amfani da ita gurin cemiki kiyi hakuri I know I messed up,amman wllh ba halina baneba bansan meya hau kaina alokacin ba, I will never ever forgive myself for what I did today Islam"

dan shiru Islam tai tana sauraron yadda Mehtav ta cigaba da bata hakuri tana cemata aisharrin shedanne da fushin zuciya shine yasakata ta aikata dukma abinda ta aikata dun. Ahankali Islam tagyara kwanciyar junior asaman kirjinta tana kallon saman dakin, silently tace mata "Mehtav inna ga irin kishinnan da naivety dinki akan son EHSAAS kina tinamin dani lokacin kafin nasan ya rayuwa take a irin gida nasu EHSAAS, amman Mehtav tunda nake shirmena bantaba koda kuskuren sakashi acikin hadari makamancin wanda kika sakashi ayau ba,ansha attempting amfani dani gurin cimmasa amman ba'a taba nasara ba, kina ikirarin kinason shi memakon kizama mutum na farko da zata kareshi daga tarin makiyyan dayake dasu amman se kika kasance mace tafarko data fara amfani da kalmar soyayya ta tafka kuskuren da is irreversible," takarasa tana jan dogon numfashi Mehtav tace "nasani wllh amman namiki alkawari bazan kumaba kuma shima inya tashi zanbashi hakuri kuma zan rungumi duk abinda ya yanke zan karbi kaddara koda yace baya sona bazan yi kokarin yin komai akan hakanba in sha Allah,"

Islam tadan saci kallon Mehtav batareda tasan ta kalletan ba because she looks so innocent, pure hearted and beautiful at thesame time tana wannan kukan kamar karamar yarinya ko ita da batakai shekarunta ba batajin zata tsaya tana koke kokennan har tana bawa matar wai wanda takeso hakuri haka.

dan juyo wa tai wannan karon tana shafa bayan junior tace "Mehtav I understand your feelings, your hurt sbd kin dauka keke kadaice macen da zata kasance acikin duniyar EHSAAS kwatsam segani nazo namiki babakere koh, nima hakan ta taba faruwa dani Mehtav"

kina jina alokacin da zamuyi aure mai Martaba that's sires father, nasan yanasona amman bayason nasabar dana fito daga cikinta zanbaki wannan labarinne sbd inaganin kin cancanci kisan inda zaki kai kanki kisaka kanki zanbaki wannan labarin bawai don na yarda dake kirike min wani sirri ko amanata ba zanbaki labari saboda I know your curious kisan yaya akai nazama matarshi at the first place da harkike ikirarin ko auren hadine,zance miki na hadine amman hadin bana iyaye ba na ubangiji saboda alakata da EHSAAS kainuwace dashan Allah duk yadda makiya sukaso su girgizata kasa girgizuwar tai.

ambashi aurena tareda auren cousin sister dinsa Maisoon bint Erfan ta danyi murmushi tace Mehtav babu irin borin da banyi ba alokacin aiki zetafi south south of NURISTAN aurenmu da wata daya amman dagamai hankalin danai akan maganar gaba daya ya dimautashi ni nace nafasa aurensa indai harze hadani da wata, banbancin kishina da naki kenan ni bantaba tunkarar maisoon don ko mata barazana ko wani abinba hasalima ni sau daya nataba ganinta bayan ansaka musu ranar, sodayan ma agurin taron gifting ceremony dinmu, nasan you'll be surprised innace miki I was taken aback by her beauty, family dinsu EHSAAS yadda kika ganshi jajir balarabe duka haka suke musamman Maisoon kamar yar aljanu haka takeda mugun kyau da haske sedai yar siririya ce irin matannan ne masu slim figure me mugun daukar hankali, Kuma akan min habaici ana cemin wai ana yayinsu maisoon din sosai awannan zamanin wai mace mejiki irinnawa bata fiya farinjini ba maza sunfi son sirara kuma nadau maganar nadaura acikin Raina.

Maisoon looks like an angel, ga iya kwalliya Mehtav ko kece aka hadaki kishi da wadda kike ganin tafiki kyau,da asali mai kyau hankalin ki dole ze tashi.

da sauri Mehtav ta daga kanta so yadda dai takeji akan Islam itama Islam din tataba kasancewa a thesame situation irin nata gyara zama tai tana fadin "that is what I feel lokacin dana fara ganinki nima your presence intimidate me alot," dan murmushi Islam tai tana fadin "haka muke mata,musamman kan namijin damukeso, amman baki saniba su fa maza babu ruwansu da wannan indai suna sonki kawai suna sonkine, namijin dabe san kanshi baneba yake barin beauty yana defining kalar standard dinshi amace I was too naive back then I even confronted EHSAAS da mgnr se yace min wai aishi idonshi nafi duk matan duniya kyau,kuma jikina yanason shi ahaka harcemai nai zanyi slimming budar bakin bawan Allah nan cewa yay wai innai beyafe ba cutarshi zanyi. memakon maganar taimin dadi senama kara hawa sama nakejin duk duniya yama gama rainamin wayo, nayi kuka nayi fada babu abinda banyiba amman kullum inya bude baki se yacemin nikadaice zan kasance matarshi har abada kar indamu baze auri Maisoon ba.

hakanne yasa natattara kayana nabi yayarshi gimbiya mima kasar turkey inda ta cigaba dayimin shirin aure nagani nafada ina matukar son mimah saboda kaf gidansu EHSAAS babu wanda yanuna min kauna kalar tata kanwarta take cemin sama da kasa. kuma itace take lallabani awancan lokacin tana cemin inyi hakuri ai idan ya auremu mu biyu ni yakeso ba Maisoon ba don haka idan inaso zan iya maida Maisoon hoto acikin gidan,hakan yasa nasaki jikina muka cigaba da shirye shiryen bikina al'adar garinsu Fulani anawa mace lefen kaya kafin aure wanda baya cikin al'adun NURISTAN amman tasaka EHSAAS yayi mana nida Maisoon inda komai aka bawa mimah tayi dani ake zuwa ana zabar komai tun anan nagane cewar mimah na mugun sona batason maisoon intasamu abu original zata dau fake dinshi tasaka a akwatin Maisoon. I felt good at first but deep down nasan is not right,amman kishi yasaka nai shiru ina nunawa mimah what she is doing ai gaskiya ne. idan EHSAAS yakirani se tace kar indaga innuna mai indifference kamar bandamu dashi ba inya kira damun gama gaisawa zatace inkatse se kuma wata goben bansan hakan yasaka mijina cikin tsananin damuwa ba, I thought gata takemin tana koyamin jan aji ashe sotake tasamu control ne over me,cewar infi yarda da ita akan EHSAAS.

Yana cikin tsakiyar arna a south south,sunki bashi hadin kai yayi abinda ya kawoshi yadawo gida donya magance matsalar datake tsakaninmu dakuma aurensa da maisoon, garin yanada mugun hadari sbd anyi ittifakin kaf NURISTAN babu garin da aka tara thugs da top drug dealers kamar nan din ga garin gaba daya adabbace suke rayuwarsu, yasha wiya sosai kafinma sufara sauraronshi da jikinsa da aljihunsa da komai daya mallaka yake amfani da gurin ganin ya janyo hankalinsu to cut the story short nidashi bamu sake ganin juna ba bamu sake saka ido acikin juna ba se asatin da za'a fara bikinmu muka dawo NURISTAN.

Dadi daya shine yagano bakin zaren matsalar garin sannan yadawo da information me girma inda yay zazzafan rubutu ya fallasa asiri wadan da sukeda ruwa da tsaki gurin safarar kwaya yankin inda sunayen manyan kasa da dama yafito kuma king nashwan beyi kasa agwiwa ba gurin sakawa akamasu gaba dayansu aka yanke musu tsatstsauran hukunci da yasaka EHSAAS yasamu popularity da kauna me tarin yawa acikin jama'a domin har kamfanunuwan dasuke sarrafa kwayoyin seda yasa aka binciko da masu seda gurbatattun magunguna a asibitoci. sannan EHSAAS yasake bude wani foundation din inda wannan karon yay sponsoring marasa karfi million daya a NURISTAN aka koya musu Sana'ar hannu wasu kuma aka maidasu makaranta duk inda kika shiga a NURISTAN sam barka zakiji anawa yarima, ana yabawa da halayensa, Amman wannan shine mafarin saka rayuwarsa cikin hadari kwata kwata bandauka cewar yacigaba da bincike akan case dinba bayan ankama wadannan mutanen yadda yatara masoya haka yatara makiyya cikin manyan kasa dalilin wannan case din,kuma yayi alkawarin kawo karshensu bali daya daga kasar NURISTAN.

Ranar dana fara dawowa NURISTAN gimbiyah mimah ta kaini bangaren Fulani nagaida ita bata barni nawani zauna da Fulani ba setaacemin intashi mutafi sbd ba'a sakewa agurin suruka, Ashe shakuwa bataso nayi da Fulani kwata kwata.

Gurin mom dinta takaini donna gaisheta se alokacin nasan cewar mamanta ma tana da rai sbd nasan dai Fulani tayi kankanta data haifi mimah duba da shekarunta amman bantaba tsammanin mamanta nada raiba jin cewar bata taba min magana ba an karbeni cikin girma ankarrama ni mai babban daki tana ta haba haba dani har fiyema da Fulani kuma naji dadin hakan sosai sbd nafahimci fulani najin kunyar doguwar magana dani itakuma wannaan mamar mimah din batayi sejana ajiki take.

mimah ce take laburta mata wai ai naki sakin jikina sbd maganar auren maisoon duk na addabi kaina da kishi,maman ce tagyara zama tacemin kar indamu ai indai ina tsaginsu babu yadda za'ai inkuka akan kishiya, kishiyar ma wacca itada banza agurin mijinnamu duk daya haka tacemin inshirya gobe kafin aimin first ceremony na wanke amarya zanrakata unguwa zata kaini gurin wani malami daze ban wasu lakani da addu'a wai in mallakeshi zezama atafin hannuna ko sakinta nace yayi zeyi sosai naji dadin bayaninta. nakalli mimah ina tambayarta shin dagaske ne tajinjina min kai tacemin ai itama danake gani tana zaune da mijinta ai ta sanadin wannan malaminne, inba hakaba maza nada mugun son mata inbata tashi tsayin dakaba seya auri uku bayanta harda kwarkwara.

nace mata amman aunty mimah aishi bayason yayi aurenfa mai Martaba ne yakeson yaymai, kenan yanzun inmunje semu mallake mai Martaba kawai,mimaah tai dan jim kafin tace toh bari mugani amman me iya mallake me martaba akasarnan aise shahararran malami domin tsarin dake jikinsa bame iya karya shi gashi kujerarnan dayake hawa kullum kadai babbar kariyace agaresh.

banida wani ilimin addini I was too childish na dauka ai mallakar wani abin kirkine kuma naji ance malam nasan kuma malamai ai mutanen kirki ne kuma addu'ar su tafi karbuwa ayadda mimah ta nunamin. sunbani abinci nazauna naci nai nak sunata tambayata ya shirye shiryen bangaren su Fulani babu abinda ban fada musuba har kalar turarrukan da Fulani ta siyamin tabawa uwar soro tabani, sbd duk miskilanci na bana iyawa mimah kamar tsafi duk abinda ta tambayeni sena fada mata.

don ina gani kamar duk duniya banida masoyiyar data kaita main while bansan so take tai amfani dani gurin reaching EHSAAS ba,adaren ranar koda mukai waya d EHSAAS atsaitsaye bance mishi komai akan hakanba kuma raina fess yake don ina ganin matsalata ta kawo karshe.

washegari da sassafe daman ina bangaren grandma bayan angama min gyaran jiki nayi wanka na shirya nafito ina sauri sauri don mimah tace insameta awaje acikin mota mom dinta zata rakani gurin malam amman acan zamu hadu, kuma karnacema grandma zanfito kawai nasato hanya don zata iya hanani tace za'a fara biki.

satar hanyar kuwa nai saidai banyi sa'a ba ina fitowa mukai kacibus dashi sosai nai mamakin ganinsa saboda becemin ya isoba jiya da mukai waya dukda kewar sa danai hakan be saka na sakar mai fuska na nuna nayi kewar tashiba sema hade rai danai saboda hudubar gimbiya ta rigada tagama zama akwakwalwa ta kancewar idan na fiya sakarmai fuska ina nuna ina sonshi rainamin wayo ze cigaba dayi.

asanyaye yake kallona dawani irin shauki na kewa ta dayay ban ankara ba kawai naji ya jawo hannuna muna dawowa ciki,kamar yadda na saci hanya nafito haka shima ya saci hanya yadawo dani har cikin dakina na bangaren kuma nakasa cemai komai saboda yadda zuciyata take azalzalata in tambayeshi me yasameshi yarame yay duhu haka amman kuma tsabar jan aji naqi.

kallona yake from head to toe, kamshin jikina gaba dayw yagaba ratsa ko ina na zuciyarsa yana mai haifar mishi da wata kasala wacca yasan shibe fito da itaba, doguwar rigace ajikina ruf se dankwalinta dana yafa,amman hakan be hanashi ganin irin kara cika ido dana dada yiba sbd yadda ake kula dani, nakara zama wata hamshakiyyar mace tako ina bazakace min yarinya yar shekara goma sha takwas ba.

"Pipi where do you think your going looking beautiful like this?" yawatsomin tambayar yana kallona,turo mishi baki nai cikeda bori na nufi kofa zan bude ya wani janyoni na fado saman kirjinsa. tunda muke dashi in kunga yatabani cene is necessary ko lalura ko wani abin kwata kwata be saba tabani ba hakanne yasa kirjina yashiga bugawa saboda yadda nakejin zuciyarsa na harbawa saman kirjinsa kamar zata faso. kamshin turarensa gaba daya ya baibayeni ya gauraya dana jikina yana bada wani sihirtaccen kamshi na musamman. "let me go" nafada silently ina kokawar raba kaina dashi amman dake karfinmu ba dayaba kasawa nai ya kankameni ajikinsa kafin yasauke kanshi agefen wiyana yana shinshinar yadda fatata take fitar dawani kamshi dake neman rabashi da nutsuwarsa, inajin yadda jikinshi yay mugun dumi kamar ma bashida lafiya, "sire" nafada ina kokarin dago dashi daga jikin,hankalina ya soma tashi "are you sick menene ya sameka?" Natambaya da damuwa amuryata "Islam, menai miki yaushe kika dena sona bansani ba uhm, I never thought a day like this will come inda za'a ce Sire dinki yaywata bai ganki ba kuma baki taba daga waya kin kirashi ba sedai idan harshi ya kiraki, baby innakirama minti nawa kike bani 3_4 kin kashe, what are you up to? Inkin dena sonane kifada min, Kodai da gaske bakison auren nawane uhm araunace nake fadin "uhm uhm, ainidai bance nadena sonka ba bakaine ba dan meyasa zakace zaka aura wata bayan ni,aikasan I hate the idea of sharing you with any woman,"

"Baby kinsan cewa inda zabi nane I'll never ever allow that to happen, kuma nace miki I have plan amman kinki yarda dani ya kikeso nayi na bijirema umarnin iyayena Allah yayfushi dani"

girgiza mai kai nai cikeda yaranta take fadin "aikasan da option kaki bi yanzun ba gashi ni mama mai babban daki da big sister mimah zasu kaini na nemo mana mafita ba," yace "baby menene option din tell me, Kinsan I'll do everything in my power to do it indai ze hana ai aurena da wata nakeba"

ringing din danaji wayata tanayi yasa nadago dake tana aljihun jeans dina yasanya nadan tureshi daga jikina nadago rigar sama, Ina kallon yadda yabi cinyata da ido yana kallon yadda rubber jeans din yabugun dame min cinyoyinnawa, yawani kefani da ido harna ciro wayar na sauke rigar baibar kallona ba duk senaji natsargu sbd besaba min dan iskan kallo irin hakaba. "kaga tana kirana" Na nuna mai screen din wayar zan daga wayar ya zameta ahannuna ban ankaraba naga yakalla kawai yatura aljihu cikeda bori nashiga turamai baki harda buga kafa "kagafa tana jirana kabani wayata zamu tafi kada su gaji tatafi tabarni," Yace "uhm bama ki damu dani ba koh shiyasa keta fita yawo kike yi da mims bama taniba," Yakarasa fada yan wani cije lips dinshi idanuwansa nasauya kala kamo face dinshi nai kamar wani baby because he looks so cute and angry at thesame time cikeda nutsuwa nake fadin "saboda nadamu dakaine yasa zance kaga nasamo mana option din dakai bazaka auri wancan me idon magenba kuma bazaka sabama iyayenka ba,sunce indai malam yamin addua ya mallake min kai kawai duk abinda nace zaka ringtone, amman nafasa yanzun kawai cewa zanyi amallake mana Mai Martaba ta yadda kaga inkace bazaka auri Maisoon ba he won't say anything and mama mai babban daki tace in aka mana adduar nan ta mallaka se yadda mukai da mutum," amamakance yake kallona yasan bana karya and yadda na hakikance ina fada kmr wani abin kirki yasan wani ne yazuba mun mentality din a brain dina shiyasa fa bayason zamana acikin gidannan dalilin da yasa yabarni natafi turkey gurin mimah kenan amman me kamarfa yaji nace mimah dincema zata kaini yace "Kikace me pipi mallaka fa? Nace "Yes mallaka ai gurin malam zamuje" yace "ita mimah dince tafada miki hakan?" Nace " eh mama mai babban daki ce tafada and I asked your sister tacemin itama tawa mijinta," Yace "mimar" cikeda mamaki Nace " mima biyune agidannan ne bayan wadda kasani" dogon numfashi kawai yaja yana kama hannayenna saman gado ya zaunar da ni yana zama gefenna yakamo zuwa jikinsa,yace " bandai san me mims take nufi da nata form of mallakar ba but I just know you don't need it sbd kinriga kingama mallake wannan zuciyar tawa," Yakarasa yana daura hannayena asaman kirjinsa dake beating very fast I could even feel it, Nadan tureshi ina fadin "Stop touching me kacefa babu kyau" "Hmmmmm" kawai yafada yana dan dauke kanshi akaina yace "kuma abu nabiyu dazan fada miki duk wanda zece kizo yaraki ki gurin wani dan Adam don yabiya miki bukatar ki ta duniya ba daidai baneba,inaganin dai itakanta mimah ta manta amman maganar addu'a ai zaki iyayi da kanki agida ina littafan addu'ar dana baki? Nace "yananan ina biyawa kullum amman banga ansaka akwai adduar mallaka acikiba,' dan murmushi yay yarintata kam actually pays him alot sbd duk abinda kafadamin sena fadamai yace "baby kinsan meye asiri?" dan jim nai kafin nace "uhm uhm" yace "sorcerer ai you know what that means ko?" dan zaro ido nai ina fadin "babu kyau" yace "exactly so there are alot of fake malams out there dasuke ikirarin su malamai ne suna temakon jama'a but they do sorcery ne gurin yiwa mutane abinda sukesu,they work with jinns, kuma kinsan shirkane hada Allah dawani agurin bauta duk wata bukata taki ta duniya da lahira Allah ne kadai ze iya biya miki ita ba wani mahaluki ba don haka zanja kunnenki ba mimah ba daga yau koda fulanice tace kizo ki rakata gidan Malam wai zaku mallakeni ko wani karki sake kije inba hakaba Allah zeyi fushi dake se kinyi kwana arba'in kina sallah ba'a karba" zaro ido na shigayi ina fadin "nadaina bazan jeba aibansan babu kyau ba" yace "good! ina karatun da nace ku ringayi da mimah tana koya miki kuwa izunki nawa?" Nace "nidai bansan meye izuba nasan dai ta tsaya min Wassama'i' wattariq," yace "takasa kuka faro kenan?" k"unyi sabbi hisma rabbikal a'ala" jinjina mai kai tai yace "what about tauhid tana koya miki?" girgiza mai kai nai yace "fiqhu fa?" nanma nagirgiza mai kai yace "dorin take miki kadai kenan, amman baby yaci ace kinyi izu koda biyune nasan capacity din brain dinki ba kullum kukeyi ba ko?" dan jinjina masa kai nai " hmmmmm" kawai yace before yace "I'll handle it myself, yanzun dai ki kwanta kifara hutawa nasan later bazaki samu lokaci ba and ba inda zakije here is your phone" Yakarasa yana ciro wayata daga aljihun da yana mikomin, jinjina masa kainai kawai,shafa gefen face dina yay kafin yace "take care baby" ze juya na riko mishi hannayensa,yajuyo yana dagemin gira daya irin yadai dinnan "kaifa meya sameka bakacin abincine dakyau a south din uhm?" jinjina kai yay yana fadin "I don't like their food," Nace "tohm kaci abinci yanzun daka dawo?" yace "Maama is busy kinsan banacin abincin kowa se nata kuma" dasauri namike nadan kalleshi kafin nace "nizan maka girki ina zuwa" dan waro ido yay yana fadin "karma kifara so.kike ki konamin amaryata amin bakincikin daga angwancewa inkoma jinya," Batareda nafahimci meyace ba nace "zanfa iya bazan koneba" Nafada ina kokarin nufar kofa dawo da ni baya yay yana fadin "no need zansa Aman ya kawo daga waje," "uhmmm uhmm nidai zan dafa" Nafada batareda na saurareshi ba nacire hannunsa anawa na nufi waje few maids na samu sunata aikace aikace da shirye shirye. Na nufi dakin kakarmu da akema gyaran gashin biki, uwar soro ganina nashigo ko sallama babu yasa tace "toh toh lpy yar rigimar kishi,nida nace kifasa auren kika watsan kasa a ido yau kuma meya faru" karasawa nai na zauna akusa da ita ina dan sunkuyar dakaina cikeda jin kunya bawai tataba a'ah tamai gyaran gashin " menene fatan komai lpy" uwar soro ta tambaya cikeda kulawa dan jinjina kai nai kafin nace "yunwa fa yacemin yanaji basu bashi abinci ba kuma kinsan bazeci na masu aikiba and maama is busy kuma ni ban iya dafa abinci ba," uwar soro tai saroro tana kallona kafin tace "yanzun kuma nice less busy se intaso inbar kwalliyar bikin tawa inmai girki tsabbar iyayi da tsirfa irinta magaji shi bazeci abincin chefs dinmu ba aise yaje uwarsa data saba bashi tabashin donni be ajjeni kukaiba atoh," kama hannunta nai ina fadin "tohm ki koyamin yadda zan dafa koda instant noodles ne inkaai mishi," Dan jim uwar soro tai kafin tace "Karfa ki kone magaji yacinyeni danya kintabbatar zaki iya" jinjina kai nai nace " zan iya mana" nan danan tashiga bani instructions daki daki yadda zan dafa simple instant noodles tina gyada kai kamar abin yana shigar min kwakwalwa sosai tana gamawa Tace "Kardai kishiga kitchen ke kadai kishiga da cook donta lura da abinda kike karki kone, Turo baki nai cikin shagwaba nace " nidai ai zan iya, thank you kawai" bantsaya sauraron me zatace ba domin ita namayar kakar dabani da ita saboda itama nata tabamin kallon wacca ba jinin taba Nabude kofar nafito ahanya mika hade da EHSAAS yabiyo sahuna don yaje kitchen beganni ba, " I'll cook for you" Nafada ina riko hannayensa yana ganin yadda idanuwan ma'aikatan yake akasa dukda yasan suna satar kallon yadda na rikemai hannu ko ajikinsa harmuka karasa babban hadadden kitchen din sama na sashen uwar soro da bame amfani dashi se in itace tai ra'ayi zatai girki dakanta wa mai martaba kullum sashen tsaf tsaf yake kamar ka lashe don tsafta. stool na jawo masa nace " yazauna" be musa mataba yazauna yaga na bude drowers din kasa na kamfato wata katuwar kitchenware dazata dafa abincin mutum goma wai ita zan dafa instant noodles din da sauri yamike yana karbar tukunyar yamayar yace "wait fadamin yadda grandma tace kiyi I'll help you" Yana dakko yar karamar pot, daki daki nashiga mai bayani karshe dai nice nakoma yar zaman banzan shikuma kallo daya yaywa bayan instant noodles din ya kwashe yadda ake dafawa beyi mata wani iyayi ba ya dafa mana guda uku nida shi.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to share Comments Like & Vote. [01/06, 22:16] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's Fatoumspassion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.