Chapter 30
Cikin nutsuwa yake komai nasa. Idan zata zo gaban tukunyar, sai kaga ta labe abayansa tana leƙe, wai ko zataga tana ci. Aiko da taga tana yi, ta juya cikin murna tana nuna mai. Bayan abayansa ta labe gaba ɗaya, ji yay da damuwar da ya dawo da ita akanta ta sauka, saboda she just instantly shifted his mood from being sad to happy, super cheerful. Kuma yaji daɗin ganin ba ta da wata matsala da kowa a gidan, rayuwarta take freely.
A kitchen ɗin suka zauna. Shine me jin yunwa, amma ita ce me zumuɗin cin indomie kwan da aka soya ne dai ya ƙi ciwuwa, saboda dan banzan gishiri da aka zabga masa. Ba albasa, bare wasu veggies. Aka ajiye shi gefe. Da kanta take bashi abinci a baki, yana bata itama. Suna yi yana dan briefing ɗinta kan tafiyar tasa da yayi, da kuma littafin da za'a sake saki.
Kwankwasa ƙofar kitchen ɗin sukaji anayi. Duk da a buɗe take, amma baiwar da take bakin ƙofar bata yi gigin shigowa ba. Daga inda suke suna kallonta, Islam ta kalleta ba yabo ba fallasa. Ta shiga tambayar ta, "Lafiya?"
Kanta a ƙasa take ce mata, "Ai Gimbiya Mimah ce take ta nemanta tun dazun."
A kasa kallon EHSAAS tai. Shina ya kalleta kafin yace ma matar: "Taje, tace tana zuwa, ta jirata a falon ƙasa."
"Da tohm, Allah ya temaka ka," ta amsa tana juyawa ta bar gun.
Islam ta kalleshi tana raurau da ido. "Yanzu me zan ce ma Aunty Mimah ɗin?"
Dan ture plate ɗin gabansa yayi, da dama sun kusa cinyewa. Ya ɗau glass ɗin da ta zuba mai ruwa kaɗan, ya sha. Yace, "If you're done, ki wuce ɗakinki. Zan yi magana da ita, kinji ko?"
Jinjina masa kai tai kawai, don bata iya wani musu da shi ba.
---
Sauka falon ƙasa yayi, amma ganin yadda maids suke kai kawo yasa bayan sun gama gaisawa da Faras, take faɗin: "Magaji, ai ban san ka dawo ba. Da na shigo mun gaisa."
Duk jikinta kana gani kasan yayi sanyi da irin cold treatment ɗin da EHSAAS ya bata. Yace, "Uhm, na dawo Mims. In dan ganki manna," yay gaba. Tasan ba yadda za'ai ta iya mai musu, duk da kasancewarsa kaninta, amma girma da darajarsa da ɗaukakar da Allah ya bashi ta lokaci ɗaya ya sanya yake mata wani irin bala'in ƙwarjini.
Suna fita, motarta da tayi parking a waje yashiga. Bata cire key ba, da kanshi ya tuka ta zuwa sashensa. Tana kallon ɗaya da tfkeken ginin da ake masa. Wani irin mahaukacin fili aka shata masa a kusa da asalin unguwar Mai Martaba. Don ya gina inda matansa zasu zauna, amma kallo ɗaya ta mai, ta gane cewa ginin gidan mace ɗaya yake yi. Domin tsarinsa da yanayinsa kwata-kwata ba yayi kama da wanda za'a saka mata biyu a ciki ba, kuma ko ƙoƙarin daura bene bai yi ba. Amma gama coming finishing kawai akeyi yanzu.
A ranta tace, EHSAAS ɗan gata, kalli wannan part ɗin - komai yay, da za'a ce ba za'a kawo matarsa nan ba, sai an yi sabo.
Yana parking, ya juyo ya kalleta. Suna haɗa ido, ta sakar mai murmushi tana faɗin: "Nayi missing ɗinka ɗan kanina."
Murmushin gefen baki yay mata, daya sa dimple ɗin na bari daya ne kadai ya bayyana. Sai ya dan yi shiru kafin yace: "Mims, what's this things about mallaka da nake jin kuna gayawa Islam? Kuma inane zaku rakata - ke da Big Mummy - dake haka kike cema mai babban ɗaki? Ba tare da kun nemi iznina ba? Uhmmm. I thought zaman na take a gidannan, ba zaman kowa ba."
Dan jim tai kafin ta rintse ido. Bata taba expecting yarinyar nan zata yi exposing ɗinsu haka ba. Ta dauka tanada wayo - after all irin brainwashing ɗinta da ta ringa cewa kada ta yarda da EHSAAS, ta ringa fada mai komai - ashe seda ta fada.
"EHSAAS," Mimah ta fada tana tattaro hankalinta guri guda, cikeda yadda ta kware a gurin displaying role na Big Sis. Take faɗin, "Ka san bazan taba kai Islam inda za'a cutar da ita ba. Ko mallakar da kake tunani ba ita nake nufi ba - ni da Mummy. Tayama in bands, abinka na rasa wanda zan kai a mallake sai kai, dan kanina. Da ita da kai da waye nafi kusanci? Eh?" Ta ƙara sa tana kama hannayensa. "Am doing it for you. Ka san yarinya ce, akwai wani gyaran jiki ne na sirrin 'ya mace da muke kira da mallaka. Shi nake so nakaita a yi mata saboda ina son komai na kanina ya fita daban, ya yi fess, ya yi shara. Ina son lokacin da zaka samu Islam, ka tabbatar da cewa yes - ka yi dacen mata. Ka samu mace. Kuma taki yarda ati. Shiyasa na mata wayo da hakan."
Dan zame hannayensa yayi cikin nata. Ba don bai yarda da ita ba, a'a. Shi har gyaran jiki ba so - ba kwanta maiba.
Yace, "Mims, ni ba don jikinta nake sonta ba. I love her for who she is. Ki daina kai min mata inda za'ai ta tattaba min ita, ko da mata ne kuwa. Ina kishi, bana son hakan. Kuma ba tsari bane ba. Kuma duk sanda zaku sake fita a rinka sanar min. Dan Allah."
Ya ƙare da girmamawa. Amma deep down, Mimah felt disrespected. Tace, "Uhm, ɗan soyayya kenan Alh. EHSAAS. In sha Allah, an dena. Gaka - ga matarka. Ba me sake tab'a ma ita. Mace dai sai da gyara da ado a koyaushe."
Ba ya tanka ta ba. Yasan neman magana take. Ya buɗe murfin motar yana faɗin, "Let me get some rest. Ki gaishe da mutanen gidan kafin na shigo."
Tasan da maman ta yake kuma ba ta raba. Ɗayan biyi already - yaje ya gaida tasa uwar. Man tata, sai ya gama hutawa.
A fili, sai tace: "Tohm, ranka ya dade. Sai ka tashi."
Cikin raha da wasa yake cewa: "Ke koh?"
Ya girgiza kai kawai, ya fice. Yanufi sashensa. Kwafa kawai tai tana komawa ɓangaren driver, tace: Lallai ma yarinyar nan. Dani kike yin zance daga temako, bakin ki baida linzami?
A haka za'ai wannan abin?
Da key tayi wa motar, ta soma analyzing abubuwan da suka faru. Ji take kamar taje tai wa Islam din tas tas. Amma kuma tana tsoro kada ta sake kwashewa ta fada wa EHSAAS - tunda taga ba ta da wayo bare sirri. Hakan ne yasa kawai ta wuce ɓangaren mahaifiyarta don ta labarta mata abin da yake faruwa din.
Daga bangaren Islam, yana fita ƙasa, iya ƙarasa cin abincin tayi. Biyo bayansa tayi, amma ta kasa sauka ƙasa. Kawai ta wuce dakinta tana ta tunanin dalilin da yasa Mimah zata ce su je su yi sabon Allah. Amma kuma se wata zuciyar tace mata kila itama Mimah ɗin ba ta san sabo bane, shi yasa. A yadda taga Ehsaas, ta san tabbas ranshi ya baci duk da ƙoƙarin ɓoye mata nake yi. Ba ta son ace yau ya samu matsala da 'yar uwarsa tãlli ɗaya ƙwal. Saboda ita tayi jigum, anan hadaddun manyan matan da zasu shirya ta zuwa ceremony na farko na bikin suka same ta tare da uwar soro. Ta zauna a gefenta tana kama hannayenta, tace:
"Islam, a yau Mai Martaba ya bada damar a fara gudanar da bukukuwan al'ada na aurenku ke da Ehsaas. Kinsan da hakan ko?"
Da jinjina mata kai tayi. Uwar soro ta numfasa tana faɗin:
"Islam, ina son ki sani kece macen prince ta farko. Je za a fara wankewa da ruwa mai tsarki kafin maisoón and that shows Mai Martaba ya amsheki a matsayin uwar gidan Ehsaas. Ina son ki toshe kunnuwanki ki kama kanki, know, kiji, ki kiji, ki gani, ki ƙi gani. Ki sani, ayanzun ne zaki haɗu da ainahin family ɗin prince, dangin ta bangaren uwa da uba. Kuma nasan akwai kace-nace da zé gudana sosai akan zabarki da yayi. Kar ki saka duk abinda kunnanki zé ji har cikin zuciyarki. Kin ji yar albarka?"
Jinjina kai Islam tayi, jikinta yana fara sanyi sosai.
"Ina son ki kame kanki, zan kasance tare dake a kowanne hali. Waɗannan gasunan, kin gansu nan, su ne suka fara miki gyaran jiki tun farko kafin Mimah ta tafi dake. Base nasake introducing dinsu ba. Wannan ita ce Hajiya Jannat of Persia, wannan kuma Hajiya Azeeza of Morocco. They will be with you throughout your journey, and maybe Hajiya Noora will join too before the wedding. Zasu kasance har se an kaiki dakin mijinki. Ko da ban ƙusa, su ne kawayena na amana, su ne zasu zama tamkar iyayenki. Nasan matsalar da aka samu da mahaifinki, babu lallai ne ya bari 'yan uwanki su zo ko mahaifiyarki. Amma try and call her, kiji ko zata zo. Domin idan da akwai wani naki a gurin, zakiji daɗi sosai."
Jinjina mata kai Islam tayi, kanta a ƙasa. Ta shiga mata nasiha sosai, mai ratsar jiki. Kafin tace ta bata minti goma tayi duk abinda take buƙata kafin su fara shiryata don taron. Hajiya Azeeza ta shafa kanta tana faɗin:
"Masha Allah, Allahumma barik fiki."
Dayar tajin amsa mata da wani yaren da bata iya ba. Da alama ba ma su cika jin wani yaren ba banda nasu da Turanci. Don ta fahimci duk sanda zata yi mata magana da Turanci take mata.
Wayarta ta lalubo, ta shiga kiran mom ɗinta. Sai da ta kusa katsewa ta ɗauka. Dayake ba ta san lambar ba, amma tana jin peace ɗin ce. Ta fara mata kuka tana roƙonta akan cewa ta fito mata da mijinta. Ita wace irin 'yace marar albarka da zata rasa wanda zata saka a jefa a kurkuku se uban da ya haifeta? Ta inda take shiga ba nan take fita ba. Sai da ƙyar ta bawa peace damar faɗa mata:
"Ai aurenta za a yi, yanzun haka tana gayyatarta ne."
Tun da suke da Veronica bata, tana zagewa, ta zazzageta irin yau ba. Har da kiran auren nata tsinannan aure. Tunda dai ba da yawun ubanta zatai ba. Kuma tace:
"Allah ya kiyaye! Tatako ƙafarta zuwa wannan palace din wai da sunan halartar bikinta."
Sannan tace mata:
"Tafito mata da mijinta da gaggawa, in ba haka ba ita zata yi disowning ɗinta."
Peace ta katse wayar ganin masifar Veronica ɗin ba ta karewa. Tayi shiru tana tunanin kamar ta ce ma da Ehsaas su sakeshi haka kawai. Amma kuma tana jin kunyar idon Mai Martaba. Saboda ta san don ita yayi wa Abraham haka. Kuma ɗin ya ganar da shi kuskuren da ya aikata ne, ba don wani abu ba. Kuma ta san Mai Martaba kaifi dayane, tunda yace se da biki za a sakeshi. Ta san is close, tunda duk zanga-zangar da mabiya addinin Abraham Zion suka ringa a cikin garin, ba ta sa King Nashwan ya sakeshi ba. Sai ma saka dokar ta-baci da yayi kan duk wanda aka kama da sunan ya fito zanga-zanga a fito da Abraham Zion, to a cafke masa shi.
Hakan ne yasa ta shiga ƙoƙarin zare maganar Veronica a ranta. Ta faɗa toilet, ta ɗauro alwala, ta zo ta shimfiɗa, tana cikin salla ta jiyo kamshin turarrukan matan da ba sa rabo da shi. Domin hadaddun matane, 'yan gayu, wanda kana ganinsu ka san sun waye makura. Kuma ga su da tarbiyya, wayewarsu ba ta sa sun watsar da tarbiyyar da addinin Islama ya daura su akai ba.
Tana idarwa Hajiya Azeeza ce ta saka ta takwabe, ta shiga toilet ɗin kanta. Ta dirjeta tass, tayi mata wanka da wani ɗan uban sun haɗe-haden turarrukansu na gargajiya. Da Peace tana shigowa gurin, se ka san ta shigo yadda ya kamata. Jikinta suna fitowa, ta ɗau wata hadaddiyar royal pink bathrobe ta bata. Domin daga nan za a wuce da ita gurin ainahin inda za a mata wankan Noor, tsohuwar al'adar ƙasar Nuristan ce, wacca duk matar da prince zé aura se an mata wannan wankan, ta yadda iyayensa zasu dubata tsaf, don ganin ko tana da wata illa, tabo ko wani malkwada a jikinta tun kafin a kai ga ɗaura aure.
Bayan sun saka mata bathrobe ɗin suka rufe jikinta da wata irin alƙyabba ta alfarma mai nauyi. Babu wanda aka bari ya ƙara ganinta, har aka wuce da ita wani ɗaki na musamman a gidan wanda ake kira da Zaure Al-Khayal, ɗakin da ake shirya kawai don wankan amarya. Tun zamanin kaka da kakanni, duk amaryar da prince zé aura, se an kawo ta wannan ɗakin, an wanke ta.
Ɗaki ne mai matuƙar kyau, an kawata shi da fitilu masu launin rawaya, ga wasu furanni masu kamshi irin su jasmine da rose, da kuma labulen da ke lilo cikin iska mai sanyi, wanda yake da tambarin asalin gidan sarautar Nuristan ɗin.
A ciki suka tarar da wasu dattijan mata guda uku, wanda 'yan uwan King Nashwan ne. Tsofaffi ne tukuf amma se bala'in jida gayu da jida mulki da ke cikin jininsu. Da wasu tsofaffi uku daga bangaren Fulani Hajar se mai babban ɗaki da Sarauniya Hassana, Fulani bata halarta ba, saboda kunya da ƙarar kasancewar Ehsaas ɗan tane.
Kuma haka Hajiya Azeeza da Hajiya Jannat suka sa ta gaisar da su duka cikin girmamawa da mutuntawa kamar yadda suka koya mata. Wani irin kunya take ji sosai, ganin wai anan za a mata wanka, a bude mata jiki a gaban duka waɗannan mutanen. Gaba ɗaya al'adun she's finding them weird, ba irin wanda aka saba yi bane a normal weddings. Duk da ita ba me shiga mutane ba ce, amma dai ta san cewa ba kowacce amarya ake yiwa hakan ba.
Kasan dakin a shinfide yake da wani silk NURISTAN rug a kasa, an jera manyan tuluna guda uku masu dauke da: pure rosewater daga Damascus da Shiraz, se madara mai dumi da saffron soak, da na ukun medauke da ruwan Zam-Zam da itacen sandalwood for the final rinse. Daya daga cikin dattijan tsofaffin da tafi kowa tsufa, da sanda ma take tafiya, da taji ana cemata Mother Fariha, ce ta yi mata umarnin shiga wani hadadden marble bathtub da aka cika da ruwan rosewater da madara mai dumi. Dayar ta shiga ta taimaka mata, ta zare alkyabbar jikinta da kuma bathtub dinta, daga ita se wata 'yar figigiyar half-vast mara hannu da Hajiya Jannat tasa ta saka kafin ta fito. Se pants suka barta, ta shiga cikin ruwan tana rintse ido, amma wani irin dadi da kamshi da dumin da ruwan yake yi, ba ta san sanda ta saki jikinta aciki ba. Mother Fariha ce ta shiga ta yayyafa mata ruwa a tsakar kanta tana wanke mata jiki da wata auduga mai laushi da furannin da suke wayo a saman ruwan.
Wasu irin addu'o'i taji Mother Fariha tana yi tana tofe mata kanta da su. Addu'ar neman tsari daga shedan da shedanun cikin mutane take mata, da kuma addu'ar samun albarka a cikin aure. Duk matan sun yi tsit saboda sun san Mother Fariha ba ta wasa da kowa a cikinsu, tana daya daga cikin tsofaffi mafi daraja wanda suka rage a masarautar, duk da ba a cikin palace take zama ba. Kuma ba za ka taba ganinta a guri ba se irin wannan tataso din. Ita kanwar baban King EHSAAS na farko ce, that makes her great-grandmother din EHSAAS.
Seda ta dau lokaci tana wa Islam wankannan inda take jin hatta da fatar jikinta yanayin laushi da sulbinta ya canza salo, kafin nan tace ta mike ta fito. Aka zaunar da ita akan wani tumtum ne, mugun laushi kamar fatar mage. Sannan Queen Layla, uwar gidan King Abdul Aziz of Borno, ta shiga ta shafe mata jikinta da turarruka masu daraja irinsu musk, amber, da sandalwood paste, wanda ke nuni da tsarkakke jikinta da suka yi, da kuma ganin ba ta da wata illa da sabuwar rayuwa da take shirin fara a gidan masarautar.
A karshe Sarauniya Hassana da Mai Babban Daki suka lullube ta da silken robe mai launin shudi mai haske daya rufe jikinta ruf. Aka yafa mata veil na crystal-net, sannan aka fesa mata pure oud oil a goshinta, da kunnenta, da wuyanta. Sannan taji tsofaffin sun hada baki suna fadar Masha Allah, ana juyawa ana rungume juna. Ita dai kamar yadda Uwar Soro ta fada mata, ta kame tsaf, kuma tun da aka fara bata dago kanta tace zata kalli direct cikin idon wadannan matan ba.
Mother Fariha ce ta kalli Azeeza da Jannat tace, "Ina kuma masu karbarta? Ma'ana representatives dinta daga danginta?" Hajiya Azeeza ce ta dake tana fadin, "Mune, Mother." Dan kallon ta tayi a mamakance, amma dai ba tace komai ba, domin gulmar maganar ta dade da shiga kunnanta. Ta mika musu ita.
Hajiya Jannat ta kamata, se ashe Queen Layla ta bude baki tana fadin: "Na san mahaifiyar mijinki ba zata iya zama ta sanar dake wannan ba, amma ni zan fada miki, tunda ni kamar uwar daki nake a gurin EHSAAS, don zancensa yafi rayuwa a gabana akan Fulani. Don haka ki sani, wannan wankan da aka yi miki na nuni ne da cewa kin tsarkaka. Ki ajiye duk wata rayuwa da kika yi a baya a matsayin past. Kin shiga sabuwar rayuwarki taya yanzu da rikon amana. Kuma daga yau ki zama kamar furannin nan masu kamshi. Ki rike martabarki a matsayin ki na uwargidan gidan sarautar NURISTAN. Ki nuna mana daraja da kamala. Ki rike girmanki. Kada ki sake ki yi going astray har abada kamar wasu."
Ta karasa fada cikin salon gasa magana ga Mai Babban Daki da ta ci magani. Dan durkusawa Islam tayi cikin girmamawa tana fadin, "In sha Allah zan kiyaye, My Lady." Shafa kanta tayi tana fadin, "Stay blessed."
Fitowa da Islam akai wannan karon a cikin wani haɗadden golden palanquin aka ɗauketa don mayar da ita sashen uwar soro, wanda taron ne da aka haɗa nata da na Maisoon a guri ɗaya. Za a musu zarposh inda ake bawa matar sarki mayafi mai daraja, sannan kuma gifting ceremony.
Tuntuni 'yan uwansu Maisoon sun hallara a gurin, gasu da dangi gaba ɗaya babu masaka tsinke. Har ta da Maisoon ɗin tazo, kuma su ba su san an yi wa Islam wankan Noor ba har sai da tamakara ake tseguntawa Maisoon ɗin, wadda take zagaye da kawayenta. Ta ci wani uban kwalliya ta alfarma wanda za ka rantse wani gagarumin taron sarauniyar kyau zata je-abin da ko shiga cikin bikin ba a yi ba tukuna. Abin ya tsaya mata a rai kenan, Islam aka tsarkake ita fa, dan meye yasa ba a yi mata wannan wankan ba?
Da wannan kudurin suka ɗau aniyyar sai sun kuntata mata matuƙa a gurin bikin, sun nuna mata nan din territory ɗinsu ce-ita ba kowankowa ba, bad face, kaskantacciyar armiya kuma talaka.
Lokacin da aka sauke Islam ɗin, wata irin busar sarewa ce aka shiga bugawa da ganguna, ana tambura. Ya ƙara hassala dangin Maisoon da yadda manyan mata suka mata rakiya. Domin har da su Mother Fariha sun bi bayanta a motoccinsu. Ana sauke palanquin ɗinta, Hajiya Azeeza ta karaso tana buɗe mata labulen. Kafafuwanta da suke sanye cikin wani haɗadden flat shoe wanda yana daya daga cikin kayayyakin da uwar soro ta yi mata na fitar bikin, da doguwar kafarta ya ja hankalin jama'ar gurin. Dake gurin a bude yake, an yi decorating ɗinsa, ya yi kyau sosai.
Kamar ta san jiran ta ake yi, sai da ta ɗau lokaci kafin ta fito da kafafuwanta gaba ɗaya. Mayafinta ya lulluɓe mata kanta baki ɗaya, amma sharara ne. Kana iya gano nitsattsiyar fuskarta, da ke nan very natural-ko kwalli ba a saka mata ba saboda taron ne na cikin gida, iya mata.
Maisoon wani irin bugawa taji kirjinta yana yi saboda yadda ta ga Islam ɗin tana wani taku cikin nutsuwa tamkar wata dawisu. Ga yadda idon kowa ya koma kanta-har da danginta. Wani irin kishinta taji tana yi.
Islam ko sau ɗaya bata ɗaga kai ta kalli kowa a gurin ba, har su Hajiya Jannat suka kaita zuwa kujerarta da aka tanadar mata a kusa da ta Maisoon. Wata ƙaramar ce mai siffar crescent moon, an rufe ta da zannuwa na silk blue da wani crown na gold a bayanta.
Mayafinta har yanzu a lulluɓe yake ita, fuskarta mai sheƙi na haskakawa daga ƙarƙashinsa. Bayan an zaunar da ita, aka kira manyan mata guda bakwai daga ɓangaren dangin Fulani Hajar domin su yafa mata mayafin zarposh na alfarma kafin a buɗe mata fuska.
Ga mamakin Maisoon, tun dazun taje a gurin amma cikin 'yan uwan Fulani babu wanda ya yi attempting fara event ɗin har sai da Islam tazo. Dukkaninsu sha'anin kansu suke yi.
Gimbiya Mimah ce ta karaso da mayafin a saman wani tray na azurfa mai kyalli, ta karaso gabanta da su Queen Layla da sauran 'yan uwan Fulani Hajar cikin mutunci da mutuntawa. Queen Layla ta ɗaga mayafin tana haɓawa a saman kan Islam. Nan gurin ya ɗauki kabbara, ana Masha Allah saboda mayafin Fulani Hajar ce da kanta ta dinka shi-dinkin hannu ne da wani zare mai daraja.
Sai da aka gama guda da kabbara, sannan aka shiga turareta da wasu irin ɗadaddan turaruka irin na mutanen Maiduguri, domin dangin mahaifin Fulani Hajar Kanuri ne na asali. Kafin wata kanwar baban Fulani Hajar ta ɗaga mata mayafi a kai tare da karanta mata addu'o'i da fatan alkhairi.
Sai Subhanallah da Tabarakallah ake cewa. Idon Islam a ƙasa, zara-zaran eyelashes ɗinta na ƙara wa fuskarta wani irin ƙwarjini da haiba.
Queen Fariha ce ta juya tana kallon Maisoon kafin ta yi mata umarni da ta karaso ta gaishe da 'yar uwarta. Maisoon kamar tayi hauka haka ta ringa ji, saboda ta san cewar ko a shekarun tagirma ma wannan yar iskar yarinyar-amman wai ita za a ce taje ta gaidata!
Ta ganin ido gaba ɗaya ya yo kanta, gashi ko arzikin lulluɓin fuska bata yi ba. Sai ta karasa cikin ƙaudi da kwaikwayen da shanye duk wani bakin ciki da take ji. Ta durƙusa a gaban Islam tana kare mata kallo.
Gimbiya Mimah tace, "Islam, gafa Maisoon-amaryar EHSAAS ta biyu. Maisoon, ga Islam."
Da ɗan dafa cinyar Islam, Maisoon tayi tana ƙara kare mata kallo. Kyan dai fuska, babu abin da zata nuna mata, domin a kallon zahiri ma, tafi Islam kyan fuska, tako ina. Maisoon dan fara, idanuwanta tai wanda suka sha eyelashes masu kama da na mage.
Ta ce mata: "Barka da shigowa cikin zuriyar mu da addininmu. Peace. Allah ya sa tubanki karɓabbe ne... Tubabbiya."
Ta faɗa a cikin muryar da ba wanda ya ji sai ita da ita.
Sai alokacin suka haɗa ido, don Islam bata taɓa jin kalmar Tubabbiya a baya ba-sai daga bakin Maisoon. Ita ta fara jifanta da wannan kalmar a masarautar, wanda da dama suka ɗauka cikin maƙiyyanta suke kiranta da shi.
Ba tace ma Maisoon komai ba. Maisoon ta miƙe tana dan rungumeta a jikinta amma bata yarda sun haɗa jiki ba. Tace: "Kidan rage weight ɗinki. Ba ki san yanzu ba a yin mata irin ku ba. Ki haka, mijin zeyi dan maliyo maliyo dake. Kin zama ɗauki da nishi."
Ta ɗago tana mata murmushi kafin tace: "God bless you yayata, uwargidana." a fili yadda kowa zai ji.
Wannan karon sai mamakin Maisoon ɗin ake yi. Islam kasa shanye kukanta tayi, sai hawaye zirr ya biyo fuskarta, saboda taji haushin zagin da Maisoon tayi mata.
Hajiya Jannat da ta lura kamar abin da Maisoon tace ya bata wa Islam rai ta faɗa mata: "Master your emotions. Control everything. Duk wanda ya bata miki rai da bakar magana, kar ki nuna ranki ya ɓaci. Instead, give him the biggest smile you can ever give."
Wani irin hadiye kuka Islam tayi tana jin kamar Maisoon ta soka mata wani abu a makoshinta. Shi yasa kwata-kwata ta kasa jin daɗin taron, har aka koma kan Maisoon itama aka yafa mata mayafi mai daraja kafin a fara basu gifts.
Mayafinta aka buɗe saman cinyarta. Kowacce mace da abin da take da ƙaura musu: wasu gwal-gwalai, wasu envelope ɗin kuɗade, wasu turarruka, wasu har da makullin mota, wasu harda takardu da dabino da zuma da gold-plated Qur'ani da azkar da calligraphy da sunayensu. Ba karya, ta samu kyaututtuka na ban mamaki, amma da yake Maisoon ce ta zo, sai suka fi bata kyaututtuka iri-iri na alfarma musamman dangin babarta.
Hakan ne yasa aka shiga tambayar: "Ina dangin Islam?"
Kasa-kasa taji ana ta ƙananun maganganu, amma tunawa da nasiha da uwar soro ta yi mata yasa duk ta shanye. Amma deep down, tana jin auren EHSAAS ya fara fita a ranta baki ɗaya.
Sai bayan magrib sannan aka tashi daga taron.
A wasu irin mahaukatan convoy aka kawo, aka ɗauki amaren kamar ba a gidan zasu kwana ba. Haka aka mayar da kowacce inda take-taro ya watse.
Islam kuka kawai take yi a cikin motar da aka ɗauketa. Hajiya Jannat tana ta bata baki tare da mata faɗa akan me zata bari maganganun mutane su ringa shiga kanta.
"Ita dai ba dasu zata zauna ba. Mijinta na sonta. Iyayen mijinta ma suna sonta. What is she looking for apart from this?"
Hajiya Azeeza ma tana mata bayani cewar: "Ai wannan kaɗan ne daga cikin kalubalen aure a gidan sarauta. Musamman da yake EHSAAS is the only prince kuma Maisoon 'yar uwarsa ce. Don haka kada ki sake ki nuna ma su Maisoon ta karaya ko kuma ranki ya ɓaci da abubuwan da suke miki. Ita dai ta rike mijinta a hannunta-shine priority dinta."
Daga bangaren EHSAAS kuwa, se daf da magrib ya tashi a barci yana feeling kansa fresh, don rabonshi da barci irin haka me tsayi tun yana Oxford. Jikinsa yaji dadinsa sosai, ya mike ya shiga ya watsa ruwa mai dumi, ya fito. Dake sashen nashi, daman baya bari a zuba masa wasu ma'aikata bayan masu gadi, wanda suke gyara mishi ma, amintattune ne. Wanda se ya fita suke shigowa su yi share-sharensu da goge-goge se su tafi kafin ya dawo.
Shiryawa cikin wani farin yadi mai laushin gaske, yana gyara sumar kanshi. Kafin ya kammala, ya fesa jikinsa da turarrukansa masu kamshin gaske as usual, ya sauko kasa don tafiya mosque. Ya ci karo da Aman akan system dinsa, se dariya yake yi. A hankali cikin takunsa na isa da kasaita ya karaso.
Aman, kamshin turarensa ne yasa ya ankara da zuwan nashi. Ya juyo yana fadin, "Barka da fitowa, Uncle Prince."
"Barka dai," ya amsa mishi yana kallonshi kafin yace, "Me kake kalla haka kake ta dariya?"
Wata irin dariya ya cigaba da kyakyatawa yana fadin, "Amaryarka nake kallo, Uncle Prince. Pardon me," ya karasa yana kokarin rufe bakinsa da dariya.
Dage gira daya EHSAAS yayi, yasan dole Aman ba normal abu yagani ba, yake wannan kyakyata dariyar data fi mai kala da mugunta. Karasowa yayi, ya juyo da system din. Kallo daya yayi wa video, ya dauke kai yana basarwa.
Aman ya cigaba da kalla yana fadin, "Hot! Mais your newly bride!"
Kallon da EHSAAS ya watsa mai yasa ya dan tsuke baki. Still yana dariya yake fadin, "Uncle Prince, ban sha wani wahala gurin digging all her dirts ba. Daman nasan bata jin magana, amma ban dauka wawancinta ya kai taringa social media tana matsayin princess a kingdom dinnan ba. Ko dan taga bamu wani damu da social media bane shiyasa. She use to share contents about beauty & sex, kaganta coach ce ma guda me bawa mata shawara akan yadda zasu ji dadin rayuwarsu. And she thinks she can be our future queen? Impossible! She's not modest at all. Wannan kadai ya isa yasaka mai Martaba ya dakatar da auren nan."
Dan jim EHSAAS yayi, karin yace, "Is not enough. Ina gwajin jinin danasa? Ka kai ta amata?"
Dan shiru Aman yayi kafin yace, "Yana mota. Ai baka bani damar bude wa ba tukunna."
Yace, "Muje. I need to see it saboda I'm sure I'll find something on her ta wannan hanyar."
Mikewa yayi yana nufar waje. Aman da sauri ya tattara laptop din, ya rufe, ya bi bayansa. Daman yayi alwalarsa shima. Ya bude mishi gaban motar, ya shiga. Shikuma ya shiga driver seat. Abaya ya sa hannu ya dauko file din yana mikawa EHSAAS.
Ya tayar da motar yana nufar babban masallacin Kamsus Salawat dake Palace din EHSAAS. Gently ya shiga budewa. Shidai hope dinsa guda daya - genotype dinsu kar ya matching. Saboda yasan shi AS ne kuma babanta ma AS ne, ba dai san mamarta ba. Shiyasa tun Peace tana asibiti yasa aka mata gwajin jini asace, and everything is compatible about them - genotype dinta AA ne, blood group dinta O+ ne. Sannan bata da wani STS, daman kuma ba yayi expecting ze samu ba.
Amman Maisoon ya tabbata bazata fito clean ba. Report din farko ya nuna mai itama AA ce. Yaji kirjinsa ya wani buga. Ya shiga karanta na biyun wanda ya kusa juyar mai da kai.
"Wait!" ya fada yana kallon Aman daya tsayar da motar nan take.
"Ka tabbata wannan report din gwajin jinin Maisoon ne?"
Jinjina masa kai Aman yayi yana fadin, "I'm very sure."
Rike baki EHSAAS yayi kafin yace, "Thank you, Aman. You have no idea cewa you just saved my life with this report. Ko mai Martaba ba zai sake cewa in aureta ba."
Yace, "Uncle Prince, meye a cikin report din?"
Dan kallonsa yayi kafin yace, "Karka damu, ba sai ka sani ba. Bani flash din daka cire videos dinta duka aciki. Daga mun fito a sallar Isha'ee, se mu wuce private sitting din mai Martaba."
Aman yace, "Amma dazun ka ce min gurin Aunty Islam zamuje. You know she must be scared right now. Kasan tsofaffin nan fa ba zasu bita da sauki ba."
Yace, "I know, but wannan yafi mahimmanci. Is for her too - she will be very happy intaji maganar nan. Just make sure Mims na tare da ita. I know she will take care of her."
Yace, "Okay, Uncle Prince."
A masallaci suka hadu da mai Martaba. A sahu daya suka yi sallah. Yana tambayarsa, "Ya shirye-shirye?"
Yace masa, "Komai lafiya, alhamdulillah."
Ita kanta masarautar, wata iriyar kwalliya ake mata tun farkon satin - akai wa ko ina sabon fenti. Kana gani kasan za'ayi wani gagarumin taro ne.
Bayan sun idar, as usual, shida mai Martaba suka zauna karatu, basu bar mosque din ba se bayan Isha'ee.
Tunda mai Martaba yaga EHSAAS na bishi bamba to bamba, yasan cewa akwai magana a bakinsa. Ba ma bari dogari ya bude wa mai Martaba motaba - da kanshi ya bude mishi. Ya kalleshi yana dan murmushi yace, "Magaji, fatan dai komai lafiya, ko akwai magana?"
Jinjina masa kai yayi yana kasa da kanshi. Cike da fahimta irinta da da uba yace, "Mai toh," ya shiga motar su je.
Karbar laptop yayi daga hannun Aman bayan mai Martaba ya shiga cikin motar, ya bi bayansa. Ganin zasu yi tattaunawar sirri yasa Jay saurin karbar key din motar daga hannun driver, saboda yana son yaji me EHSAAS ze ce ma babansa.
Ya shiga, ya fara tukasu zuwa ainahin private fadar mai Martaba. EHSAAS shiru yayi ganin Jay a gaban motar, saboda daman cam jininsu ba ya haduwa.
Mai Martaba yace, "Magaji, kayi shiru kuma, bayan nasan akwai magana a bakinka."
A hankali EHSAAS yace, "Allah ya temake ka. Mu karasa can kawai sena fada."
Yace, "Ka tabbata? Akwai fa su kawunnanka acan, karka kasa magana."
Yace, "Zan iya, Allah ya temake ka, in sha Allah."
Shafa kansa mai Martaba yayi kafin yace, "Yasha'anin bikin. Ina diyata? Fatan tana samun kyakkyawar kulawa daga gurin iyayenka mata ko?"
Dan jinjina kai yayi yana fadin, "Allah ya temake ka. Ni gani nake yi ma Grandma ta dena sona, ta koma kanta."
Murmushi yayi yana fadin, "Nima dai naga alama. Garin yaya kai sake haka sosai."
Jay yaji haushi jin sun koma wata maganar barkwanci mara mahimmanci daban. Bayan ya ajiye su, da sauri ya bawa driver makulli, ya bi bayansu.
EHSAAS ba ya tsaya wata doguwar magana ba. Dake ba su da wani yawa a gurin - daga shi se Aman dake rike da laptop da file dinsa a hannu, se Waziri, Turaki, Wambai, Jay Galadima, se Tafida.
Aman ne ya sanar musu akwai abinda yarima ze nuna musu. Dake tsabar ya iya, ya saka video din Maisoon tana raye-raye a gaban camera da guntayen kaya.
Gaban Waziri ya fara turawa yana fadin, "Allah ya temake ka, gashi."
Ya bude baki ze tambayi waye, kawai yaji yawun bakinsa ya kafe kaf saboda ganin Maisoon da yayi marabarta da tsirara kalilan. Wani irin harbawa zuciyarsa ta shiga yi, yana tunanin irin miliyoyin kudaden da ya riga ya karba daga gurin mai Martaba don shirin bikinnan.
Innalillahi, kardai yarinyar nan tozarta zata yi - tai wannan abin kunyar. Tunda suke da ita, ba ya taba tunanin tana social media ba. Yasan dai tana yawo kuma bata ji.
Zare ido ya fara yi yana kallon Aman. Kafin ya kara jawo system din gabansa ze rufe, Tafida yayi saurin fadin, "Miko nan mana. Ai naji kamar yace dukanmu mukalla ko?"
Ba san sanda Tafida ya karbe daga hannayensa ba. Jikinsa ya mutu murus.
Tafida, "Nagani!" ya fara salati yana fadin, "Wacece wannan yarinyar? Yar dibar albarka kamar gimbiya Maisoon fa nake gani!"
Wambai yace, "Wace Maisoon din? Matar da yarima ze aura?"
Yana lekawa, yarintse idonsa - don ba zai bari idanuwansa na tsufa su kalla wannan barnar ba.
EHSAAS ya basar kamar ba shine ya bayar ba, yana jin tsofaffin sunata, "Allah wadai!"
Waziri ya kasa cewa komai.
Wambai ne ya shiga yi wa mai Martaba bayanin video din - cewa Maisoon ce, yar gidan Erfan, take raye-raye a yanar gizo-gizo.
Mai Martaba ya kalli EHSAAS yana fadin, "Menake ji haka, yarima?"
Yakalli Aman yana fadin, "Wannan irin shashanci ne?" Aman ya gyara zama yana fadin, "Allah ya temake ka gani mukai. Ya kamata kusan da wannan boyayyar dabi'ar ta Maisoon. Ita din tuni tajima tana yada videos dinta ire-iren wannan a kafafen sada zumunta irinsu Instagram, TikTok da Facebook. Tanada mabiya sama da miliyan goma, kuma ba iya a fadin NURISTAN ba har kasashen ketare suna ganin wadannan vidiyoyin da take yi tana watsawa. Zaku iya shiga wayoyinku ku yi searching sunanta 'Hot Mais'."
Jay kallon EHSAAS yake yi cike da mamaki, domin ba taba dauka EHSAAS zai iya coming up da wannan trick din don ya hana aurensa da Maisoon ba. Bayason ace koda yaushe EHSAAS na samun yadda yakeso. Wayarsa ya ciro kafin yace, "Kukasani ko wanine yake impersonating dinta? Ta yaya zami yarda daku bayan mun san duk hanyar hana auren nan kuke nema?"
Yana searching Hot Mais, kuwa, sega hotunanta nan iri-iri da ballagazar shigar da take yi ita da kawayenta. Wasu a clubs, wasu a hotels. Jay dagowa yayi yana kallon Waziri dake da dan hope din cewa Jay zai kare yarsa, amma sai ya ga jikin Jay din yayi sanyi.
Yace, "Uhmmm, munji wannan Yarima, amma hakan baya nufin saboda wannan video din da aka yi wata da watanni zaka yanke mata hukunci. Mun san yaran yanzun duk mun haifesune, bamu haifi halinsu ba. Ai za a iya kiranta ta saukesu duka ba. Shikenan ba auren da ake magana za a daura jibi. Mun buga katin gayyata zuwa ko ina kake. Tinanin zaka sa a fasa saboda san ranka, eh? EHSAAS!"
"Da Yarima fa kake magana, ranka ya dade," tafida ya timaimai yana mai gargadarsa.
Jay yace, "Mu ajiye title a gefe. EHSAAS, ni kanin mahaifinka ne. Kar ka yi tunanin zakazo ka raina mana hankali. Bayan mun maka yadda kake so tun farko. Mun barka ka auri wadda ma bata cancanta ba, shine yanzu zaka kawo wannan wasan gabanmu? Idan rashin tarbiyya ake magana ai duk abinda Maisoon zata yi, zatakai arniya. Ba wadda take tubabbiya. Ita a kasa da abinda ta yi a baya - suda zina kafin aure - ruwan sha suka maidata. Ita zaka ce tsarkakakkiya ce?"
Wambai yace, "Galadima ya isa haka, kar ka manta a gaban wa kake?" Ya fada yana timaimai mai martaba na gurin. EHSAAS bai tankashi ko kadan ba saboda kulawa ma ya bawa ce, kuma yasan duk abubuwan da zai fada akan Peace karya ne.
Aman yace, "Uncle Jay, dan Allah kayi hakuri, bata kai ga haka ba. Amma mu munada shaida ne mai karfi." Ya karasa bai yi wata-wata ba, ya ciro file din medical report na Maisoon. Yana budewa, mai Martaba ya mika mai da kamar ba zai karba ba, sai kuma ya karba yana kai idonsa kan takardun anitse. Ba zaka ce ya karanto wani abu na daga hankali a ciki ba.
Yana kammalawa ya kalli Waziri. Da sauri ya karasa gabansa, mikamai takardun yayi. Waziri hannunshi na rawa ya karba, bai san wane sharrin kuma suka kulla masa ba. Kasam ba gane abinda aka rubuta a takardar yayi ba, ya dago yana neman wani ya mai bayani.
Jay ya taso yana karbar takardar. Kallon EHSAAS yayi kafin yace, "Kasan cewa idan har wannan takardar ba gaskiya bace ba zaka ja wa kanka bacin ran fada, cikanka."
EHSAAS bai ce mai ba.
Wambai yace, "Me ke faruwa? Ai mana bayani mana!"
Mai Martaba kallon EHSAAS yayi kafin ya kalli Aman yace wa sauran dattawan su basu guri, kawai aka bar 'yan family.
Waziri yace, "Wallahi duk ma abinda tayi zammata fada. Bazata sake ba. Zan sa ta goge, zan karbe wayar ma."
Jay yace, "Hakane Yaya Nashwan. Dan Allah kar ka dakatar da auren nan. Zuciyar yarinyar zata karye."
Mai Martaba yayi jim kafin yace, "Ba a auren tsakanin mai lafiya da mara lafiya. Jalaluddeen ko a Musulunce babu kyau." Yace, "Yaya Nashwan, EHSAAS ba ya son Maisoon tuntuni. Yaya za'ayi mu yarda da wannan report din? Yaushe ma yake gari da har ya dau Maisoon a kai mata gwaji?"
Yace, "Shine nima abinda nakeso in tambaya."
Aman ne yayi saurin amshewa yana cewa, "Allah ya temake ka, nine nakaita da kaina."
Jay yace, "Bakinku daya ai. Ni duk ban yarda daku ba."
Waziri yace, "EHSAAS, kai wa Allah, kai wa Annabi. A bar tone-tone. Maisoon 'yar uwarka ce. Duk abinda zata yi ba zaka iya rufa mata asiri ka aureta ba. An gama gayyatar kowa fa. Kasan cewa in ka fasa a wannan lokacin ba me aurenta."
Sai a lokacin EHSAAS ya dago cike da nutsuwa yace, "Kawu, nima ba yadda zanyi ne. Maisoon tana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV. In na aureta zan shafa. In shafa ma, daya yarinyar itama da bata ji ba bata gani ba..."
Waziri yace, "EHSAAS! Maisoon 'di tawa. Ka ji tsoron Allah. Idan ba ka sonta ba, ba se ka mata irin wannan sharrin ba."
Gyaran murya mai Martaba yayi. Duk suka nutsu suna sauraronshi. Ya kalli Jay yana fadin, "Inason ku je ka da Aman, ku dakko yaran da za su aura duka. Su su biyun a kaisu lab. Inason kafin goman dare a kawo min results dinsu gaba daya, har da na shi Yariman."
Jay yace, "Tabbas haka ya kamata ayi, ranka ya dade."
Ya kalli EHSAAS yana fadin, "Bazan karbi report din kowa ba sai na Abdul Rahman."
Jin ance sai na Abdul Rahman, jikin Waziri yayi sanyi gaba daya, don yasan babu yadda za'ayi Abdul Rahman din ya ci amanar mai Martaba. Shi din amininsa ne tun da kuruciya, tun kafin ma ya zama sarki. Kuma sanadinsa yake aiki a babbar lab din cikin palace din. Babban lab scientist ne. Hakan yayi ma EHSAAS dadi sosai.
Wambai a kasa ya kira Abdul Rahman din, ya sanar masa da zuwan su EHSAAS directly. Mai Martaba ya basu umarnin su je.
Suka fito su su uku, duk da Waziri yaso zuwa, amma kasa wa yayi saboda yadda yaga Jay ya tsaya tsayin daka.
Jay kallon Aman yayi da EHSAAS yace, "Ku kuje ku dakko Maisoon, ni zan je in dakko dayan matar da za a aura din."
Wani irin dan iskan kallo da EHSAAS ya bishi dashi sai da yayi mamaki, kafin silently yace, "Kai din muharraminta ne? Mais din dai itace taku."
"Ban ce in dakko matana ba," ya karasa yana kallon Aman wanda yake kumshe dariyarsa, don ya gano ragowar idon Jay din. Ya mika mai a gabansu ya shige yayi mata key, yayi tafiyarsa.
Aman yana dariya kasa-kasa ganin Jay ya kasa motsawa yace, "Kawu, ko dai mu bishi ne?"
Juyowa yayi yana cije lebe kawai kafin ya shige tasa motar da aka kawo mai. Aman ya bishi a baya.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comments Vote & Like [01/06, 22:16] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.