Chapter 31
EHSAAS yana karasawa aka mai iso gurin kakarsa. Tayi mamaki matuka ganin shi a wancan lokacin don tasan yadda palace ɗin ta cika da baƙi ko'ina. Bai kamata ace yana shigowa sashen Islam ɗin take ba, ko da saboda 'yan bani na iya ransa. Fess yay mata bayanin abinda ke faruwa, tace mishi "shikenan," ta aika a kira mata Islam ɗin dake ɗaki a kwance. Tun da suka dawo, zazzabi yake son ya rufeta. Tayi shirin barcinta ma, ta dauro katon hijab dinta akan kayan barcinta ta fito.
Sosai tai mamakin ganin EHSAAS ɗin. Ta karasa gefen kakarsu, ta an turo baki tace, "Yauwa ma, ga hijab a jikinta se ku wuce kawai." Ta dan kalleshi, ganin ya mike ya fita. Tace, "Grandma, ina zamu?" Tace, "Ke dai bishi, ai ba sede ke zai ba, zai miki bayani a motar. Umarnin wancan ɗan ne." Tun da taji ta ce "wancan ɗan," tasan mai martaba take nufi. Don kunya bata kiran sunansa, seta zama dole.
Fitowa tai, yana tsaye kofar ɗakin yana jiranta. Tun daga ƙasa ya ɗakko yana kallonta har sama. Ya dan lumshe idonshi kafin yace mata, "Go and change, ina son ki saka complete kaya."
Dan turo baki tai gaba tana fadin, "Tohm, ina zamuje? Na fayi shirin barcina, barci nake ji." Yace, "Nasani. Ba zamu jima ba. Just do as I say." Dan girgiza kai tai kafin tace, "Hijab dina har ƙasa ai, ba abinda ake gani a jikina." Dan matsowa yay daf da ita kamar zai hade jikinsa da nata, sai kuma ya tsaya chak yana kai lips ɗin shi dede kunnanta yace, "Go and wear your bra first."
Jitai kamar ta nitse a gurin don kunya. Da wani irin sauri ta tagefensa, ta nufi ɗakinta. Ya jingina da bakin ƙofa kawai, idonsa a rufe yana jiranta.
Can segata ta fito, yana kallonta. Yasan she's fully dressed, ba kayan barci ne a jikinta dake nuna komai na jikinta. Ta canzo ma hijabi, amma duk da haka wani irin kyalli take yi. Tana mai kyau. Da zai san yadda zai yi ya kasance shi shi kadai, zeringajin wannan ɗan banzan kamshin da take yi da kuma kyawun fuskarta da zai yi. Saboda kwata-kwata ba ya son wani namiji ya kalleta. Kamar yace ta saka niqab, sai kuma ya fasa don ba ya son ya cika takura mata.
Kawai ya karaso inda take yana fadin, "You look more pretty, babyyyyyy." Ya ja biii ɗin yadda ta jita har cikin tsigar jikinta. Gaba yay tana binshi a baya har suka fito. Ya buɗe mata gaban motar ta shiga. Yana kallon yadda dogaran bakin ƙofar suke satar kallonsu har ya zagaya shima ya shiga. Yayma car ɗin key. Kamshinta gaba ɗaya ya dagula mai lissafi. Yana tuki, idanuwansa na juyawa suna kallonta. She's focused tana kallon irin kwalliyar da aka yi ma fadar wanda yay mata. Tana nuna mai.
Hannunsa taji cikin nata, ya daura a saman cinyarta yana murzawa kaɗan. Ta juya tana kallonshi kamar ma ba shine yake mata hakan ba, saboda idonsa yana kan titi, ɗayan hannun nakan steering wheel.
"Ina tohm zamuje?" Ta fada feeling a bit uncomfortable yadda yake murza lallausan hannayenta.
"Zuwa zanyi incinye ki," yafada yana mata murmushin gefen baki dake ƙara wa face ɗin shi mugun kyau.
"I'm not food da zaka cinyeni ai," tafada tana turo mishi lips.
Yace, "Uhmmm, aiki nfi abinci baby. Ko baki saniba, ana gajiya da cin abinci. But I'm sure I'll not get tired of eating you." Yakarasa maganar cikeda nutsuwa yana cizon lips ɗinshi na ƙasa.
"Nidai I don't get what you're saying. Ka fadamin inda zamu kawai."
Daidai nan yay parking a ƙofar asibitin. Juyowa yay yana kallonta. Bai kunna fitilar motar ba, hakanne yasa hasken parking space ɗin ne kawai ya ishesa. Yake kallonta, yace:
"Na taba fada miki kinada kyau kuwa?"
A wani irin basata, ta saki murmushi tana jinjina kai alamar eh.
Yace, "Tohm, zan ƙara fada miki kuma kullum zan ci gaba da fada miki: You're the prettiest woman da EHSAAS ya taba gani, pipi nah."
"Sire," tafada tana kokarin boye fuskarta a kujerar mota. Gashi ya rike mata hannu yaki saki.
"Toh, ka sake min hannu," ta karasa fada cikeda shagwabar dake ƙara dagula mai yar nutsuwar da yake da ita.
Yace, "Sedai da sharadi ɗaya."
Ta dago tana kallonshi. Yace, "Kinyarda."
"Meye sharadin? Tell me first," ta tambaya tana kallonshi.
Yatsansa taga yasa a saman cute red lips ɗin shi, yana dage mata gira ɗaya. Dan zaro ido tai, tana me girgiza mai kai. Ya tabe baki irin abin tausayin nan, yana sake nuna mata lips ɗin.
Fizge hannunta tai cikin nashi, tana rufe tafukan hannayenta biyu.
"Hmmmm," taji yace kafin ya daura da, "Okay, tunda baby ba zaki rageni wani abu ba, don't blame me. I won't spare you on our first night. Kwana biyu kacal ya rage."
Yi tai kamar bataji me yace ba.
Setaji kuma yana tambayarta, "Wai yau dawaye-dawaye suka kalla miki?"
"Wai me dama aka ce mata?" Dagowa tai tana kallonshi, don ya tuna mata kalar abubuwan da suka faru gurin Zarposh ne. Kuma gashi ba ta son ta fada mai don kar ya samu matsala da danginsa akanta.
Ganin face ɗinta ya canza, yace, "Baby me ya faru? Are you okay?"
Daidai nan yaji ana kwankwasa mai glass. Jay ne, domin ya fi minti biyar suna jiran EHSAAS a gurin. Gashi da suka ga ya zo yay parking, maimakon su ga ya fito, sai suka ji tsit kamar ma baida niyyar fitowa.
Kallo ɗaya yay wa glass ɗin, ya juya, ya ci gaba da tambayar Islam, "Meya faru?"
Hawayene suka fara saukowa kamar famfo a fuskarta. Hannunsa yasa ya kamo face ɗin yana fadin, "Pipi me aka miki? Are you okay? Please tell me, meya faru a gurin?"
Girgiza kai ta shiga yi tana dan kokarin stopping hawayen, tace, "Is okay, ba komai fa."
Yace, "Da komai. Na san you won't cry over nothing."
Bude kofar da yaji anyi be saka yasaketa ba. Jay ya tsaya chak yana kallon yadda EHSAAS ke ta lailaya fuskar Islam da hannunsa. Bema lura da kuka take ba. Abu ɗaya ne yazo mai rai - sumbatar ta yake. Wani irin mugun kishi ne yaji ya caka mai zuciya.
Yashiga bala'i yana fadin, "Kai malam, mu yaran ka ne da zaka bar mu munata jira tun dazu?"
Dan dagowa EHSAAS yay suka haɗa ido, kafin yace, "Stop shouting. Can't you see akwai baby anan? Karka firgita ta." Yakarasa yana kokarin fitowa. Jay ya basu hanya.
Zagayawa yay, ya buɗema Islam, ta fito. Ya shiga gyara mata hijab dinta ɗaya dan zame gaban goshinta, mai laushi da lallausan gashi ya fito. Suna gamawa, be kula Jay ba, ya kama hannayenta zuwa cikin lab ɗin. Sun rigada sun tashi, hakanne yasa babu kowa aciki. Shima Abdul Rahman, saboda request din Mai Martaba, yasa be tafi ba. Su Jay suka biyo bayansa, shi da Aman da Maisoon wacca tana cikin ƙawayenta. Ana live taji kira daga sama, ba tasan me za'ai ba don ba wani cikakken bayani aka mata ba. Hakanne yasa ta biyosu ba wani gardama.
EHSAAS da Islam ne suka fara shiga ciki. Jininta aka fara ɗauka kafin a zo za'a ɗau nata. Ta cije lips, ana zukan jininta. Don dauriya kawai take yi, kar ta kuka a gaban Abdul Rahman. Ana yi, EHSAAS na lallabata yana bata baki. Abdul Rahman se kallonsu yake yi cikeda sha'awa. Da aka gama, yasa mata auduga, EHSAAS ne ya rike yana danna mata. A haka suka fito, suka zauna a ƙofar gurin.
Islam sarai taga Maisoon tun fitowarsu a mota, amma ganin ko kallo bata ishi EHSAAS ba, yasa itama ta basar. Kallon da taga Maisoon na musu, yasa ta tsinci kanta tana cigaba da narke mai wai zafi. Shikuma yana lallabata kamar wata ƙarama yarinya. Jay jiyakeyi kamar ya shake shi. Haka har Maisoon ta shiga, aka ɗau nata jininta itama, ba tare da tayi musu ba. Saboda ita kanta ba tasan tana ɗauke da cutar ba.
A cikin minti 20 report ya fito. Aka bawa Jay a hannunsa suka taho. Ba wani tsaya budewa ba, don be taba expecting Maisoon ɗin rashin jinta har yakai haka ba. Shi da Aman da Maisoon suka wuce gurin Mai Martaba. EHSAAS kam yajuya ya tafi kai sarauniyarsa unguwar Uwar Soro.
Straight gurin Mai Martaba aka kai report ɗin lafiyar tasu. Waziri jiyake yi kamar ya jawo takardar ya duba da kansa. Mai Martaba yana gama karantawa ya nannade, yana mikawa Jay, shima ya shiga dubawa sosai. Jikinsa ya ɗau rawa, ya juya a fusace yana cafko Maisoon, mari ya sheƙa mata a fuska yana faɗin, "Abin kunyar da kika jawo mana kenan?"
Ihu ta fasa tana ambaton sunan babanta, idanuwanta yayi zuru-zuru. Waziri ya miƙe cike da tattali da so da yake wa Maisoon, yake faɗin, "Jalaal, kayi a hankali. Mu tambayeta dalilin ta."
Ƴa juya yana faɗin, "Wane dalili fa kace? Wane? Ka taɓa jin wani a cikin zuriyar mu da ya kamu da cuta mai garkuwar jiki?"
Waro ido Waziri yayi yana faɗin, "Cuta mai garkuwar jiki kuma?"
Yace, "Eh yaya! Maisoon zinā take yi. Gashi nan ta haɗu da jaraba. Ba dai a gidan nan ba, ball da ita zeyi."
Mai Martaba ya ɗaka masa tsawa yana faɗin, "Jalaal!"
Jay ya ɗago, idanuwansa sun yi jajir. Yace, "A gabannan ka kake dukan mace? Sakinta!"
Ƴa yay yana durƙushewa a gaban Babban Takaicinsa. Yanzu shikenan EHSAAS zai mallaki Peace, shi shi kaɗai. Ita kaɗai kuma za su ci duniyarsu da tsinke. Shi fa…
Maisoon kuka ta saka, ta fara rantse-rantse, "Ita ƙarya ake mata!"
Mai Martaba bai ce komai ba, kawai ya miƙe yana faɗin, "Sai da safe."
Aiko yana ficewa, Jay ya juya kan Maisoon da gudu. Ta rarrafan ta gun babanta. Yace, "Kin cuci kanki, ba mu kika cuta ba. Ki sani, ke da EHSAAS har abada." Ya ƙarasa faɗa yana wulla musu takardar, yay ficewarsa.
Kuka Maisoon ta cigaba da yi a jikin babanta. Domin ita kanta ba ta san tana da cutar ba. Gashi an ce EHSAAS ba zai aureta ba.
Da ƙyar Waziri ya lallabata suka tafi gida. Suma a daren ranar suka je suka samu Queen Nadra a underground passage ɗinta. Ita kanta hankalinta yayi kololuwar tashi. Inda suka saka Maisoon a gaba suka fiffirgita ta har sai da ta gaya musu yadda take zuba rounds dinta da kuma saurayin da take zargi ya saka mata ciwan.
A daren ranar suka sa aka kamo shi suka kashe shi, don ma ƙarya je ya yada abin ga wasu a san yana kwanciya da ita. Anan suka sa tahau ta yi deleting ɗin duka social media accounts dinta. Sannan Queen Nadra tahau buɗe tsafinta saboda so take ta toshe bakin Nashwan ko ta halin kaka, don ƙarya ce anfasa aure nan.
Sai dai, kash! A ranar, King Nashwan - tsabar takaicin abin da ƴar ɗan uwansa ta yi - kasa barci yayi, kuma yana dakin Fulani. Bayan ya labarta mata abin da ya faru, ta ba shi shawarar ya cire abin a ransa. Ba laifinsa bane. Yayi iya ƙoƙarinsa akan duka yaran gidan - ciki kuwa har da Maisoon ɗin - domin ka hanasu fita, ka hanasu ƙawayen banza. Amma iyayenta suna barinta tayi duka a ɓoye.
Tace masa ai addu'a ce ta saka hakan ta bayyana kafin auren. In ba dan haka ba, haka za su je su ɓata EHSAAS da matarsa.
Ranar kwana suka yi shida Fulani suna sallolin neman tsari daga sharrin shaiɗan, suna roƙon Allah ya tsare su, ya tsare zuriyar su daga shiga irin wannan halin. Suka riƙa roƙon Allah ya sa albarka a cikin auren ɗansu da Islam idan ita ce mafi alheri.
Washegari da sassafe, ƙarfe 9, Mai Martaba ya fitar da sanarwar dakatar da daurin auren Yarima EHSAAS na biyu till further notice. Abin da aka riƙa yawo da shi a cikin masarautar kenan.
Don Islam tana tashi daga barci, ta soma jin kishin-kishin wai an dakatar da auren Yarima. Dake ba ta ji gulmar da kyau ba, hankalinta ne yayi mummunan tashi. Gashi jiya an je an yi gwajin jini. Ko dai ita da EHSAAS are not compatible? Haka ta shiga jeka ka dawo.
Gashi tana ta kiran wayarsa baya ɗauka. Da alama yana can yana barcin safensa na ƙa'ida, ya sa ta a silent.
Wanka ta fesa, ta fito tana sane, ta sauko ƙasa ko za ta ji ainihin maganar. Amma bayin suna ganinta, suke kasa da kansu suna yin gum, don suna jin tsoron kada ta kama su suna gulma.
Ta basar kawai, ta zauna tana daddanna wayarta. Hjy Azeeza ce ta fara zuwa. Tace mata wayace ta fito ne? Ita da take amarya, ai ba kamata ba ne yanzu ana ganinta a falo.
Ta tasa keyarta zuwa ɗaki. Wani irin sabon gyara ta fara mata kafin zuwan Hjy Jannat.
Tun daga fara'arta za ka san ta shigo da farin ciki. Hjy Azeeza tana goge jikin Islam, take tambayarta lafiya kuwa taga tana ta nishadi?
Tace, "Uhm... ai da gulma a bakina ne."
Islam sarakan kishi! Be happy an dakatar da auren Yarimanki da wancan figalalliyar yarinyar."
Islam ta ɗan wara ido irin da gaske nan?
Tace, "Of course. Ban san me ya faru ba, ba ma wanda ya sani. Amma an ce wai saboda rashin tarbiyyar Maisoon ɗinne. Ni dama yarinyar can ba ta min ba. Idanuwanta a tsaitsaye yake. Ban so innocent soul ɗinnan ta yi kishi da ita."
Ta faɗa tana riƙo chin ɗin Islam dake blushing ear to ear.
Hjy Azeeza tace, "Amman na tayaki murna, Islam. He's now all yours. Kinga kuwa semu kara zage damtse gurin gyara, ko? Everything da zamu miki kamar sharar fagene. Islam, kinga biyayya, kinga respect, kinga kulawa-kirikesu dakyau, dakyau. Yaron nan kowa yasan yana mugun sonki. Shidin jinin sarautane. Koda nan gaba za'a iya mai wani auren, amman in kika daure kika zama jaruma, jajirtacciya akan mijinki, duk sauran biyi bayanki zasuyi."
Nan suka shiga mata nasiha iri-iri, bawai Islam bata kwashewa wani abin ma insun fada. Ita kunya take ji tana jin bama zata iyaba don kunya. Suna gama gyaran jiki kuwa suka fita sallar zuhr, ita kuma ta shiga tai wanka da ruwan turarrukan da suka hada mata.
Karin ta fito ta dauraye jikinta, tai alwala. Cike da nishadi take yin komai sanin cewa yanzun EHSAAS mijinta ne ita kadai.
Tana dauko wayarta, miss calls dinsa ta gani. Bata bi ba seda tai sallah tukunna sannan ta kira shi. Dagawa yay yana fadin, "Babyyyyyy!" cikin muryar da tai sending chills ma jikinta gaba daya.
Tace, "Uhm."
Yace, "Good afternoon."
Tace, "Afternoon Sire, ykk? Kaci abinci?"
Girgiza mata kai yay kamar yana gabanta, "Uhmmm, uhmmm."
Tace, "But why? Baka son cin abinci, ko?"
Yace, "A ina fada miki kece bakya bani?"
Tace, "Kayi hakuri. Aizan iyo girki, sena ringa baka. But for now kace adafama, kaji?"
Yace, "Ni baby, ba irin wannan abincin nake so ba faaaa. Na girma, irin shi baya burgeni."
Dan jim tai kafin tace, "I don't get you."
Yace, "Video call baby, ganinki nake so nayi."
Ba taji mezata ce ba, yamaida kiran video call. Dagawa tai tana kwanciya saman gado, ta daga wayar sama tana dariya.
"Baka gajiya da ganinane, Sire?"
Girgiza kai yay yana fadin, "Bana gajiya, pipi nah. Zaki bani abincin?"
Tace, "Aini banida abinci."
Yace, "Kina dashi mana."
Dagowa tai tana fadin, "Nidai you should be talking da irin yaran da zan gane. Stop talking in riddles."
Yace, "Yunwa ne yasani haka. But kinsan I'm innocent. I don't do dirty talks. Jinake kwana daya nan kamar shekara daya, pipi. Kuma nasan in kuka fara abin lallen nan naku na mata, bama zaki tuna dani ba-mantawa zaki da wani EHSAAS."
Tace, "Allah bazan manta dakai ba. Abinda duk sbd in maka kyau za'ai."
Yace, "Tohm. Make sure kin rubuta sunana ba a ayi hannayenki ba-har ciki n zuciyarki."
Tace, "Done, Your Royal Highness." Tana mikewa zaune.
Yace, "Pipi, inason kiss. I'll love to kiss you. Zan zo anjima. Make sure you're ready, 'cause I won't take no for an answer."
Dan wado ido tai tana kallon dakin, don ta tabbatar ba me jinta kafin tace, "Babu kyau fa, ka bari a daura."
Sire yace, "Tohm, yout now the preacher ko? Aiba damuwa-zaki shigo hannu ne."
Basuyi wani jima suna wayar ba. Ganin yaud'in gaba dayansa ya kwance mata duk abinda ya fito bakinsa fada mata yakeyi, yasa kawai ta katse wayar. Bata ce mai komai akan fasa auren da aka yi ba, shima kuma be ce mata komaiba.
Tare da uwar soro sukai lunch tukunna. Hjy Azeeza da Hjy Jannat suka shiga suma fara mata shirin hannabandan din. Event ne namata zalla da suke taruwa: ai raye-raye, ai wake-wake, inda amarya zata saka traditional red gown mara hannaye da zata zauna a yi mata hadaddiyar red henna da initials din mijinta a hannayenta da kafafuwanta tare da iyayenta da jama'ar ta gabaki daya.
Sosai ta farin ciki a wannan taron-ba kamar na jiya ba. Kuma an fi taruwa a yau saboda bakin 'yan uwa da suka zo daga wasu garuruwan da kasashen saboda auren da za'a daura gobe.
Bata gama farin ciki ba, seda taga mamarta Veronica din ta sako wata bakar jallabiya ta zo. Ba zakace mata arniya ba, amman kallon farko zakai mata kasan baturiya ce. Se kus-kus akeyi: "Wannan daga ina?"
Bata san yadda aka yi ta yarda tazo ba, amman tayi mugin jin dadin ganinta. Seda aka gama tarin, EHSAAS ke tambayarta, "Yaya taga surprise dinta?" Har kuka ta ringa mai don tayi mugin jin dadin ganin mahaifiyarsa duk da bata wani saki jiki ba, amman dai ta yarda har lalle ammata a hannunta guda daya.
Seda aka gama taron tsaf sannan Aman ya maidata gida, kuma ta kawo wa Islam gifts masu tarin yawa daga bangarenta.
Lallen Islam sosai yay jajir. Ya hadu matuka, da duk wanda ya kalla seyaji ya burgeshi.
Tun dazun EHSAAS yake makale da ita a waya, yaki barinta ta sarara. Se da akayi Isha'ee suka rabu da waya. Hjy Jannat ce ta shigo dakin ganin Islam na ta hada-hadar bude kyautukan da ta samu.
Tace mata, "Me kike yi har yanzun? Batai wanka ba dan kallonki."
Kafin tace mata, "Sotake se zatayi barci tukunna."
Tace, "Wait, ta manta akwai Oath of Devotion," wanda suke kira da Songand e Sarbedari. Shi din al'adar mutanen NURISTAN ne inda adaren da za'a daura wa ma'aurata aure, zasuje long night walk tare da rikiyar elderly woman, inda za'a yi holding dinsu a moonlit royal garden. Daga amarya se ango akeyi, inda za'a ajiye kujeru guda biyu da table wanda ake daura bowl da madara aciki.
Za'a musu lighting 3 candles-one for the past, one for the present, and one for the future. Se amarya da ango su saka hannayensu na dama acikin bowl din, suyi personal vows a zukatansu akan auren. Se ango ya bawa amarya kyauta me daraja, se itama ta bashi tukuicin kyautar da duk abinda ya tambaya daga gareta. Se su rike hannun juna ko su rungumi juna ko su sunbaci juna-ya danganta da ra'ayin couples din. Wannan elderly woman din ta karanta musu addu'o'i masu daraja.
Jin wannan bayani na Hjy Jannat yasa Islam ta mike, ta shige bathroom. Ta dau lokaci ta wanke jikinta tsaf yadda suka koya mata lungu da sako na jikinta. Ta lailaye shi kafin ta kammala, ta daura alwala, ta fito, sallar Isha'ee tai.
Hjy Azeezat ta kawo mata wani farfesun naman kaza da akamai hade-haden magungunan su na gargajiya. Ta zaunar da ita seda ta tabbatar ta cinye tas, sannan ta umarceta taje ta wanke bakinta. Brush tai, ta kuma kurkure bakinta da mouthwash mai kamshin gaske. Ta fito, Hjy Jannat da Azeezat suka shiryata cikin doguwar gown na Persian chiffon da lace mai launin baby pink da cream. An zane duk jikin rigar da hand embroidery na furanni masu kama da orchid. Suka rufe nata kai da veil mai laushi dake dauke da wasu diamonds masu kyalli farare.
Suka shafe mata jiki da turare na musamman oudh da rose attar wanda aka yi importing daga Oman da Iran, domin wannan ranar kawai. Wani irin kyau tai, mai sanyin gaske. Hjy Azeeza ce ta riko hannayenta har suka karasa gurin uwar soro. Ta shiga saka mata albarka, ta kama hannayenta ta saka mata wasu awarwarayen gwal guda hudu - biyu dama, biyu hagu - tace mata, "Allah ya kiyaye hanya."
Hjy Azeeza din ce ta raka har kofar babban sashen na uwar soro inda EHSAAS ke jiranta tare da Mother Fariha, wacce ita ce zata yi musu rakiya. Har gaban palanquin dinta Hjy Azeeza ta kaita, inda Islam ta gaisheta cike da girmamwa da daraja. Ta shafa kanta tana saka mata albarka.
Kafin ta kira EHSAAS, ta saka hannunta cikin nashi, domin ita a palanquin zata bisu, su kuma da kafarsu za su taka don su fi kallon taurari da kyau. A hankali suke tafiya, masu dauke da palanquin din Mother Fariha suna bin bayansu da ita. Islam kanta a kasa yake, don duk a tsarge take sanin cewar duk jama'ar gidan - duk da ba wai kowa suke gani ba - sai daidaikun masu gadi, amma ta san sarai ana kallon nasu.
Ya kankame hannayenta kamar wasu za su kwace mai ita. Long walk ne suka yi har zuwa Moonlit Garden din, cikinsu ba wanda ya ce ma wani kala, domin presence dinsu kusa da juna kawai ya wadatar da zukatansu.
Suka shiga cikin garden din, su su biyu. Mother Fariha ta zauna cikin palanquin dinta don tana son ta dan basu privacy, taga kamar sun takura da ita. Dogarai guda biyu ne a gurin. Da sauri suka ja musu kujera don su zauna. EHSAAS sai da ya jira Islam ta fara zama, ya gyara mata gyalenta sannan shima ya karasa ya zauna yana kallonta yana smiling.
Kad'an yayi ma dogaran wani kallo, daya suka juyar da keyarsu daga kallonsu. Dage mata gira daya yayi, yana sa hannayensa ya kamo duka hannayenta. Kasa-kasa yake magana kamar za a cajeshi, yace:
"Wai Oath of Devotion za mu yi anan din? Ba su san wannan zuciyar is already devoted to this perfect lady sitting across me ba?"
Sunkuyar da kanta tayi tana blushing cike da jin kunya. Kafin ta sake dagowa, idon shi akanta yake, yana fadin:
"But for their sake, let's do the formalities, ko? Tawan?"
Ya karasa yana dage mata gira daya.
"Ladies first," ya fada yana daukar hannunta. Nadama ya zira a cikin ruwan tare da nashi hannun, yana rike da hannunta daya yake ji kamar karya saki har abada, yana fadin:
---
Islam… From the moment I saw you, I knew. I knew that no crown, no kingdom, no title would ever matter without you by my side. Today, Allah should be my witness, I vow to be more than a husband to you. I vow to be your home. I promise to listen to your silence, to guard your peace, and to hold your heart with both strength and tenderness. I promise to lead you with mercy, not pride. To protect you with honor, not power. To love you in secret du'as and in loud laughter, every single day. I vow to be the reason you smile after tears… the warmth you feel when the world turns cold… And when trials come - because they will - I will not walk ahead of you, I will not walk behind you… I will walk beside you. As your shade, your shield, and your soulmate. I will serve you with love, with faith, and with the vow that… no matter what, this heart belongs to you and only you.
---
Ya karasa fada idanuwansa a cikin nata. Ko sau daya ba su yi breaking eye contact ba. Idonta a kasa, tace:
"It should be silent vows, Sire. Why are you saying them out loud?"
Tana murmushi ta karasa fadi.
Yace, "Who cares about the formalities, baby? I just want you. That's all I know."
Ta dago ido tana kallonsa kafin ta fara fadin:
---
Sire… I vow, in the name of Allah, that my love for you will never be seasonal. It will not be swayed by riches or weakened by time. I vow to be your calm when the world storms you… your light when darkness falls… your silence when words fail. I vow to obey Allah through loving you - with loyalty, with shyness, and with complete honesty. I will love you with all your perfects and imperfections. I will speak well of you in your presence and in your absence, and I will fight anyone who tries to steal the joy we built. I vow to guard your heart like a sacred amanah. To respect your leadership, and to make you proud to call me your wife every single day. EHSAAS… I may be new to love, but I promise to learn you - deeply, slowly, and forever. You may be a prince to the world, but to me… you're the one my du'as have whispered for in the dark.
---
Wani iri dago da hannayensu yayi daga cikin bowl din madarar, ya kai knuckles din hannayenta yana kissing deeply. Wani irin yar jikinta yake bata ba tare da yayi breaking eye contact da ita ba. Ya mike yana zagayowa gurinta, kafadunta ya kamo yana tsayar da ita. Da kyar ta iya tsaya, saboda yadda kalamansa da idanuwansa suka kashe mata jiki baki daya.
Hannayensa ya sa, yayi curving face dinta.
Slowly ya dago kanta, ya daura lips tun daga forehead dinta, ya fara kissing zuwa kan idonta. Sannan yayi pecking both cheeks dinta zuwa lips dinta. Yabi da warm and soft tongue dinsa yana licking kusan rudewa tayi sosai, ga wani iri irin yarr da take ji na binta ta ko ta ina.
Tanaji ya sakko da lips dinsa, ya tsaya daidai saitin bakinta, sannan ya cafke karamin bakin nata, yana wani irin kissing dinta - slowly and passionately - kamar wanda zai zuke mata numfashi. Jikinta ya gama mutuwa sosai, banda wani fitinnan nishi da take fitarwa.
Kasa katabus tayi balle yunkurin hanashi abinda yake yi din, saboda har kwakwalwarta take jin sa.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment & Vote [04/06, 22:12] Fatima Rufa'i Nasidi: *** Follow me on Instagram@fatoumspassipn
It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.