EHSAAS

Chapter 32

by @fatoumspassion

The kiss was so deep and intense da ita kanta ba tasan minti nawa suka dauka a tsayen a cikin wannan halin ba. EHSAAS is just kissing her lips kamar rayuwarsa gaba daya depend on it. Daga ita har shi ba susan lokacin da Mother Fariha ta karaso gurin ba, sai jin gyaran muryarta suka yi. EHSAAS gaba daya jikinshi ya mutu, haka zalika ita Islam ɗin. Kuma ya kasa zare lips ɗinshi cikin nata, hakan ne yasa ta yi ta maza ta dan janye fuskarta a tashi kanta a ƙasa tana ƙoƙarin bada tazara a tsakaninsu. Da sauri ya wani wawurota yana kankamewa a saman kirjinshi, idanuwansa a lumshe.

Mother Fariha ta tsaya kawai tana kallon iya gudun ruwansa. Sai da ya dau lokaci sosai kafin ya iya sakin nata, amma duk da haka hannayenta suna cikin nasa. Da sunkuyar da kai yayi a gaban Mother Fariha sabõda ka'idar Nuristan ce, Prince baya tsugunnawa kowa sai sarki. Ita kuma Islam ta tsugunna ta shafa kawunansu ta shiga jero musu addu'a iri iri ta neman albarka wa union ɗin nasu.

Kafin ta kammala, ta umarcesu both su dago. Dagowa suka yi, ta ciro wani moonstone pearl da aka raba, guda daya ne amma aka raba biyu. Ta bawa EHSAAS daya, ta bawa Peace daya. Ta yi musu umarnin su haɗa shi tare a guri guda. Yadda tace haka suka yi, sai gashi kuwa ya bada haɗaɗɗan full moon. Anan ne take yi musu nasiha tana fada musu su zama kamar wannan moon ɗin wanda is never complete in babu other half ɗinsa.

Sosai Islam ta yi mamakin yadda Mother Fariha take musu nasiha akan hakuri da forgiveness a cikin aure da kuma yadda zasu tattalin soyayyarsu ta yadda babu wani evil eye da zai iya zuwa ya rabata. Ta kai kusan 30min tana musu nasiha kafin ta basu umarnin wucewa. Tace ai ceremony ɗin is over, itama zata wuce. Ita ta fara gaba, suka bita a baya. EHSAAS yana ji inama daren bai yi ba da za a raba shi da Islam haka. Amma ba yadda ya iya. Tunanin kanshi ya shiga yi-just one night kafin ya ja dogon number.

A cikin motocin alfarma, Mother Fariha ta saka EHSAAS kafin ta riko hannayen Islam cikin palanquin ɗinta ta saka ta. EHSAAS kamar yayi kuka don yaso shi aka bari ya kai ta da kanshi. Sai da carriage ɗin nasu ya wuce sannan ya tafi.

Cikin palanquin ɗin kuwa tsit kake ji. Babu abinda Mother Fariha tace mata, itama kuma haka har suka karasa katafaren sashen uwar soro. Sannan Mother Fariha ta dago kai tana kallon Islam. Kalaman da ta fada mata wacce har yau ba zata taba mantawa da ita ba, saboda tayi matukar taimakon ta gurin gudanar da rayuwar cikin gidan yadda ya kamata:

"Islam ki zama mace mai sirri. Ki sani sirrinki da mijinki naku ne ku biyu kadai har abada. Duk closeness ɗinki da mutum, koda iyayenki ne, fadar wannan sirrin zai zama barazana wa rayuwar aurenki. Duk abinda ya shafi mijinki ki rinka tattalinsa da jida shi kamar wani abu da ke kusa da zuciyarki."

Ta karasa tana shafa kanta. Godiya Islam tayi mata tana ce mata in sha Allah za tayi aiki da wannan nasiha tata. Ta jaddada mata idan tana bukatar wani abu ko wani ya takura mata kada ta yi kasa a gwiwa, ta fada mata. Tace in sha Allah za tayi. Kafa da kafa ta rakata har cikin sashenta. Ta dan kama hannunta ta miƙa mata Hajiya Jannat sannan ta barta.

Dama yau anan za su kwana saboda shirye-shiryen daurin auren da za a yi. Kakarta Islam ta fara tambaya, Hajiya Jannat ta sanar mata tayi barci already. Bata tasheta ba, suka sata a gaba har cikin dakinta. So take tayi wanka kawai ta ɗau waya. Sun fara magana da EHSAAS amma me? Sai taga bathrobe akan gadonta. Dama tana ganin hakan tasan wani wankan za a kuma mata. Kallon Hajiya Azeeza tayi tana marairaicewa alamar ta gaji.

Hajiya Azeeza tayi murmushi tana fadin:

"Daga yau ne, karki damu. Ba me sake maki wanka sai mijinki."

Sosai maganar ta ba Islam kunya. Tayi saurin ɗaukar bathrobe ɗin tana nufar bandakin. Da ita ta tube tana sakawa ta fito. Hajiya Azeeza ta shiga tana haɗa mata wani haɗin tsumemmen madara da ta ji wasu sinadarai masu gyara jikin mace, taushi da glowing.

Tana kammalawa ta fito, ta sameta Hajiya Jannat tana daure mata gashinta cikin hular leather ta yadda ba zai sha fa ba. Tana mamakin yadda suke treating ɗinta kamar wata ƙwai. Kyakkyawan motsi ba su cikason su ga tana yi ba, sai dai ta ba da order. Komai yi mata suke yi wai don tasaba, kar ta zauna a zube mata. Baya komai tana yi da kanta, suraina ajinta.

Haka suka shiga, aka dirjeta tass tass. Ita kanta in ta taba fatarta ta kalli kanta a mirror tana wondering wai dama haka take da kyau bata taba sanin ba. Duk da ko da can ba wai ba ta yin gyara bane, amma mamarta tafi ta allaka da yin gyaran irin na bature, saboda shi ta iya. Amma wannan traditional gyaran jikin na ƙasarsu da ake mata, ji take kamar yafi amsar fatarta da cikin jikinta ma baki ɗaya.

Bayan sun gama aka daura mata wani haɗaɗɗen ruwan turare. Suka fito. Wedding dress ɗinta dake nan a tsaye cikin closet ɗinta suka saka. Ta sake gwadawa don tabbatar da komai chass chass. Ai ko wa suka ga komai fess. Sannan suka cire, suka ce ta kwanta tayi barci mai daɗi, saboda fuskarta tafi kyau in ta samu isasshen hutu.

"Da toh," ta amsa musu. Suka mata sallama suna ficewa. Ta kashe wuta ta hau saman gadon tana jawo wayarta. Kuwa, miss calls ɗinshi ta gani rututu tare da messages ɗinshi:

> I still feel your lips on mine. Are you sure we can wait until tomorrow?

Dan waro ido tayi tana rungume waya a kirjinta kamar wani yana tayata karantawa. Ta saki murmushi, because EHSAAS is being naughty kwana biyunnan. Look at what he is saying.

Kafin ta ɗago da wayar ta karanta saƙonshi na biyu:

> Baby pick up mana. Ko dai kunya kike ji? Uhm don't worry, I'm all yours. If one kiss did that to me… I can't imagine surviving the honeymoon.

Bata karasa karantawa ba wani kiransa ya shigo. Kasa dagawa tayi saboda wani irin kunyarsa da nauyinsa da ta ji tana yi. Yana katsewa, ta shiga typing:

> Go to bed, naughty boy.

"Babyyyy," ya turo mata with crying emoji kafin taga yana typing:

> Be honest, were you trying to behave, or was that you holding back?

Jin tsokanar ta kawai yake son yi ya hana ta barci. Yasa ta maishi typing:

> Good night.

Ta saka waya a silent, ta ajjeta ta kwanta, fuskarta cike da annashuwa da murmushi. Za ta iya cewa yau tana daya daga cikin ranakun da ta fi kowace rana kasancewa cikin farinciki a rayuwarta.

Gaba ɗaya daren EHSAAS kasa rintsawa yayi, saboda yadda yake anticipating zuwan wannan ranar. A kan sallayarsa ya kwana yana sallah, yana addu'ar samun dawwamammen farin ciki cikin aurensa, yana mai kuma roƙon Allah ya kade fitina da duk wani sharrin mai sharri-mutum ko aljani-wanda yake da niyyar zuwa ya yi ruining marriage ɗinsa.

Ba tashi daga kan sallayar ba, sai da aka yi kiran sallar farko. Bathroom ya shiga, ya ɗaura alwala, ya fito yana sauya jallabiyar jikinsa zuwa wata milk colour mai matuƙar kyau, wacce ta amshi ginin jikinsa. A waje ya samu Aman, already ya fito da mota yana jiransa. Dakeshi ɗin ba mutum bane mai tara abokai, hakan ne yasa duka groomsmen ɗinsa 'yan uwansa ne na jini, wanda Aman ne ma ya tara musu su bashi. Ba haka samarin suka rufa mai baya a nasu motocin zuwa masallacin da yayi makil saboda bakin da suka taru damkam. Suka cika masarautar NURISTAN daga kowane sassa na duniya saboda halartar daurin auren yarima mai jiran gado EHSAAS.

Kowa haba haba yake yi da shi har aka shiga sallah. Shi Mai Martaba ya sa aka gaba don ya jagoranci su sallar ta yau. Ya tada kambarar harama, zazzakar kira'arsa tana mai ratsawa ko'ina na cikin masarautar NURISTAN da kewaye nata.

Islam tana barci, tada kambarar haramar ya tasheta. Domin zuwa yanzu ta saba da tashi sallar asubah saboda babu yadda za ayi-indai kai ba kafirin ƙarshe bane kana masarautar NURISTAN-ka ce an yi sallar asubah baka ji ba. Saboda yadda ko'ina zaka ji kiran sallah yana tashi kamar a tsakiyar harami kake.

Mikewa tayi lokacin har ya shiga karanta Suratul Fatiha cikin zazzakar kira'arsa. Murmushi ta shiga yi tana rufe fuskarta, don ta gane kira'arsa sarai. Ta miƙe tana karanta addu'ar tashi daga barci da ta riga ta haddace, ta nufi bandaki. Nan ma sai da tayi addu'ar shiga tukunna ta shiga, tayi fitsari, ta ɗaura alwala, ta fito tana shimfiɗa sallaya. Tayi sallar asubah, ta zauna tana jero azkhar ɗin da ake yi in an kammala sallah. Tana kammalawa ta ɗaura da azkhar ɗin safiya.

Sai da ta kammala sannan ta nade sallayar tata, tana jin ranta yana so ta kira mahaifiyarta yau ma, ko zata kasance da ita a wannan ranar mafi daraja a gareta. Kwankwasa ƙofa taji ana yi, hakan yasa ta bada izinin shigowa.

Sai ga su Hajiya Azeeza nan da Hajiya Jannat. Gaishe su tayi, suma suka gaidata, ta amsa. Hajiya Jannat na zolayarta wai murmushinta yau na musamman ne saboda za a mata aure. Ko rufe fuska tayi da hannayenta tana jin kunyar su biyun matuƙa.

Suka ce ta tashi maza su fara shiri, domin anjima nayi, ba samun daman kimtsa ta da kyau za su yi ba. Suma suna son su dan fito su yi kyau. Hajiya Jannat ce ta haɗa mata haɗaɗɗen ruwan wankan turarrukanta. As usual, yau bata ce zata mata ba; ita da kanta ta shiga.

Hajiya Jannat tana jaddada mata: idan bata fita ba, zata fito ta mayar da ita. Tana murmushi ta shiga. A ranta tana ta zulumin ko mommy ɗinta zata zo ko ba zata zo ba.

Daga ɓangaren EHSAAS kuwa, yana fitowa daga mosque, jama'a suka mamaye shi. Kowa na son gaisuwa da shi, ana fatan Allah ya sanya alheri. Da ƙyar dogarai suka cire shi daga cikin ɗumbin al'umma da suke masoyansa na hakika. Ya faɗa mota suka wuce ainihin sashensa.

Ba taɓa yarda a rayuwarsa wani ya tayashi shiryawa ba, amma yau, da ke ranarsa ce ta musamman kuma Mai Martaba ya aiko da masu tayawa a shirya shi ɗin, bai yi wani musu ba.

Haɗa masa shima ruwan wanka aka yi da wasu irin furanni masu kamshi na asalin Larabawa. Daurin auren ƙarfe tara ne, kuma ya san tunda Mai Martaba yasa tara-taran ne prompt, ba African time.

Wanka ya fesa irin wanda ya daɗe bai yi a rayuwarsa ba. Babu inda bai kalkale a jikinsa ba. Ya fito da babbar white bathrobe a jikinsa. Yana shiga closet, a babban mirror dinsa ya tsaya yana kallon kansa tun daga sama har ƙasa.

Gani yayi dawowarsa har wani irin haske yayi da kumari, kawai don yana tare da Islam. Ya dan yi murmushi yana baza sumarshi, wacce yaki yarda a aske masa. Daman yace sai ranar, saboda yana son ya bata surprise of her life. Don low haircut zai yi kamar yadda take muradi a koyaushe.

Aman ne ya shigo directly, da ke ya bashi permission ɗin shigowa, yana mai sanar da shi ai ya ɗakko maman Islam ɗin har ma ya kai ta sashin Uwar Soro. Murmushi yayi yana fadin, "Ya aka yi ta yarda ta zo?"

Yace, "Kamar dai wancan ƙaran na bata tabbacin cewa yau dai da mijinta zata koma gida."

Yace, "Kasiya duk abubuwan da nace, kasiya ku taho da shi a matsayin kyauta?" Yace, "Eh, duk an yi."

"Uncle Prince ya sha Masha Allah. Shi wancan mutumin fa?" Aman yace, "Tun jiya Mai Martaba ya aika Jay gurinsa. Amma dai ba mu san yanda suka yi ba. Ya bada tabbacin zai halarci daurin auren."

Yace, "What?" yana ɗan juyowa don bai yi tsammanin Abraham Zion zai sauko da wuri haka ba. Ya kalli Aman yana fadin, "Kace Jay ne ya mai magana?" Ya jinjina kai yace, "I'm sensing something. Inason ka ƙara security a duk wata ƙofa ta entrance na palace ɗinnan. Duk wanda ba shi da entry IV, kada a saki a barshi ya shigo palace ɗinnan-kowaye shi."

Aman yace, "Kowaye kace?" Uncle Prince yace, "Eh kowaye. Bana son wani problem. Everything can wait. Kuma ko da ba gurina aka zo ba bayan jama'ar da aka riga aka gayyata, bana son kowa ya shigo yau ɗin."

Jinjina kai Aman yayi yana fadin, "Angama, Uncle Prince. Amma me yasa kace haka?"

Yace, "Saboda ban yi trusting babanta zai yarda ya zo auren nan kai tsaye ba. Kuma ka ce min Jay ne yayi convincing ɗinshi. Banajin Jay zai yi convincing kowa akan farin cikina. Kai ni, ka sa ma Jay ido. Sai fa ka bari ya yi amfani da power ɗinsa ya shigo da kowa cikin gidan nan ba tare da sanina ba."

Jinjina kai Aman yayi yana jin daɗin wannan doka da order ɗin da EHSAAS ya bashi.

Yace, "Na'i. Zai iya cewa masu shirya sa su shigo."

Kansu a ƙasa, domin babu wanda yake iya daga kai ya kalli EHSAAS ɗin. Su dinnan high professional fashion designers ne da makeup artist na maza da professional barbers wanda aka haya su na musamman saboda wannan ranar.

They took two hours cikakke gurin shirya EHSAAS ɗin. Don da aka gama gyara masa sumar kanshi da beard, sai da ya shiga, ya sake wanka, ya fito.

Suka shiga shiryasa cikin haɗaɗɗen royal wedding custom ɗinsa-made Sherwani by Sabyasachi Mukherjee, hand-embroidered with 24k gold thread.

Sherwanin shi yana da deep midnight blue base me matuƙar kayatarwa. An sa pure Zari gold embroidery a gefen wuyan rigar har zuwa gaban faffadan kirjinsa. Buttons ɗin rigarsa kuma wasu real sapphire stones ne masu daraja, a kasaka ɗaya bayan ɗaya. A bayansa aka shimfiɗa mai wani royal shawl made from Kashmiri pashmina, pure white with golden calligraphy da aka rubuta initials ɗinsu. Wani royal turban suka ɗaura mai a saman kansa made from fine ivory silk, yana da brooch na white diamonds in a crescent shape, wanda yake nuni da cewa shi ɗin Crown Prince ɗin ƙasar NURISTAN ne. Kafarsa sanye take cikin gold-threaded juttis, embroidered with patterns of Nuristan's royal seal, da wani slim, ancient ring a hannunsa na hagu, damansa kuma zobunayensa ne na gold wanda ya gada daga gurin kakansa King EHSAAS na farko. Wani irin kamshi na musamman ne yake fita daga jikinsa wanda kai tsaye ba ka isa ka ce ga turaren da ya fesa ba. It was a personal blend of rare oud, sandalwood, and saffron musk, unique to the royal family of Nuristan. A single whiff of it was enough to let you know: this is not an ordinary man. This is the chosen prince. Su kansu masu shirya sa'an satar kallonsa suke yi saboda wani irin kyau da yayi wankan ya amshe sa nagaske, ga wani aura of happiness da yake bayyana a tattare da shi. Wayarsa ya ɗauka ya danna kiranta. A lokacin suna tsakiyar yin makeup, taji ƙarar wayarta, kuma ta san babu me kiranta sai shi ɗin, mom ɗinta da ita ta karɓi ragamar yi mata kwalliyar, ɗake daman field ɗinta ne nan din, ta cire komai dangane da damuwar Abraham a cikin zuciyarta. Ita dai burinta kawai taga yarta ta fito, tayi ta wuce raini a idon kowa. Kallon screen ɗin wayar tayi, ta kalli Islam da take ta ƙoƙarin hangen wayar, tace, "Stay still, ba zaki ɗaga wani kira ba har sai na gama." Raurau tayi da ido kamar za ta yi kuka. Hajiya Jannat tace, "Ai kinga wannan Miss Veronica, in dai ya kirata kamar mazari haka take jikinta, na rawa take ɗauka kamar zai gudar mata." Hajiya Azeeza tace, "Haba ku kuwa, abinta da mijinta. In ba tayi rawar kafa a kanshi ba wa zai yi? Ni ku barmin yarta, ku dena mata irin haka, ba mu so." Ko Islam kallon Hajiya Azeeza tayi tana mata murmushi. Aka cigaba da mata kwalliya ba tare da tayi picking call ɗin ba. Shi ma da ya san ta shiga hidima, bai sake kira ɗin ba. Sai ya maida akalar kiran zuwa ga 'yar uwarsa Mimah da itama tana can sashen mamanta. Sun ɗauko haɗaɗɗun makeup artist, kamar beauty parlour haka suka zauna ana shirya su, ana musu kwalliya da dressing, ita da mai babban ɗaki da Sarauniya Hassana, domin so suke su ga sun ɗau wanka, na kece raini su fi kowa kyau. Amman tsabar zumudi, Mimah na ganin EHSAAS na kiranta, ta dakatar da me kwalliyar tata tana ɗaukar wayar. Gaisawa sukayi, tana tsokanarsa da Ango, ango. Yace mata, "Ai su ne masu biki, yayun amare." Cike da raha da barkwanci da suka saba su su biyun, yake tambayarta, "Ya ina amaryar tasa?" Because yana expecting ta kasance da Islam ɗin a wannan babbar ranar. Ita kuma bata san me ya saba ba, tunda Islam ta faɗa wa EHSAAS abin da suka ce mata dangane da mallaka, taji kamar kusantar yarinyar zai yi exposing abin da ta dade tana boyewa dangane da halayyarta. Hakan ne yasa tayi baya da ita kafin ta san ta ina zata biyo mata da wani salo na daban. Amman kuma bata son EHSAAS ya san tayi baya da ita saboda abin da ya faru. Sai tace masa, "Ai tabar Islam, anata shirya ta a ɗaki." Cike da zumudi yace ta shiga, ta ɗan sato masa hoton kwalliyar ta, because he can't wait har sai an zo gurin daurin aure ya ganta. He is eager. Tace mai, "Ana wa," cike da raha. Yace, "Mims you know ke ta wace, so don't worry. Anything you want." Cikin rawar jiki ta mike a gurgunce, ta saka a ƙarasa mata kwalliyar, domin ta san in EHSAAS yace anything, yana nufin anything, kuma daman akwai kuɗaɗen da Mai Martaba ya hanata, take so ta amshesu gurin EHSAAS ɗin, ta fitar da kayanta da aka taresu a Nigeria watan daya gabata. Shiryawa tayi cikin ɗakakkun kayan sarautarta da ya fito da ainihin heritage ɗinta na kasancewa gimbiya kwalli ɗaya a ƙasar NURISTAN. Duk da yadda girma ya fara kamata, amman tsabar gayu da jida kyau, ba zaka gane hakan ba. Driver ta ne ya tukata zuwa unguwar Uwar Soro, duk da yadda mai babban ɗaki tayi mata tass akan rawar jikin da take yi kan yarinyar da ta riga ta gama kwance musu zani a kasuwa. Sanda ta je, ita kanta bangaren ya cika dam da manyan baƙi, mutanen Grandma ɗin nasu, dangi da abokan arziki duk sun hallara. Duk girman sashen nan, sai kana gafara-gafara zaka wuce. Shigowarta yasa duk tsoffin nan aka hau yaba kwalliyarta, ana mata addu'o'i da yasa taji yes ta haɗu sosai. Da ƙyar ta samu ta hauro saman kakar tasu inda tun daga wajen ɗakin Islam ɗin take jin wani masifaffen kamshi na tashi wanda ya ratsar har cikin kirjinta. A hankali ta murɗa ƙofar ɗakin, ta ji ta a rufe gam-gam. Ta shiga kwankwasawa cike da nutsuwa tana kiran sunan Islam ɗin. Hajiya Azeeza ce ta ƙarasa ta buɗe. Islam jin muryar Gimbiya Mimah ɗinta yasa da sauri ta mike wai zata buɗe, Veronica ta riketa tana faɗin: "Where do you think you're going?"

Jin Hjy Azeeza tana cewa Mimah ba za su ga amaryarsu ba har se lokaci yayi ya saka ta dan ji babu dadi. Ai ba komai, ita ce uwar dakinta. Tana jin Mimah na cewa ai ita ba a dangin ango tazo ba, a yayar amarya tazo. Hjy Jannat tace, "Toh, se ta biya zata ganta." Dakyar dai se da suka gama wahalar da Mimah suka barta ta shigo.

Aiko tun daga bakin kofa ta soma santin kyawun da Islam ɗin tai, tana ta yabawa tana cewa ai kaninta se ya rikice in ya ganta. Islam murmushi kawai tai har ta karaso tana kallo, ana karasa mata. Duk yadda ta so ta ɗau hoton tsofaffin, sun hanata wai ai ba za a ga kwalliyar ta ba se gurin daurin aure.

Se da aka kammala tsaf sannan Hjy Jannat ta jagoranci Islam ɗin zuwa closet ɗinta don ta saka kayanta aciki, ta barta ta fito. Suka cigaba da yarfirar su ta manya, suma suna ɗan ƙara goge fuskarsu. Mommy na kasa buttoning bayan rigar cewar Islam daga ciki. Veronica kallonsu Hjy Jannat tai don ta san ita ba ita ce tai mata fitting ba balle ace zata je ta gyara mata. Kuma don ta dan musu ƙara yadda taga suna kulawa da Islam ɗin sosai, hakan ne yasa ba ta ce komai ba.

Kan Hjy Azeeza ta motsa, Mimah tai caraf tana fadin, "Ni bari na je na duba. Ai in dai dress ɗin da aka sa a lefenta ne, nasan issue ɗin." Ba su ce komai ba suka barta don an san Mimah is a dignified woman.

Tana shiga tai ido hudu da Islam ɗin da taga dress ɗin ya mata wani irin bala'in kyau. Tun daga ƙasan kafarta ta shiga kallo har zuwa wuyanta inda rigar tabi ta zauna a tsayayyen jikinta. Rigar kana kallo kasan an kashe billions ne gurin ɗinkinta. Don kallo ɗaya tak mata, tasan hakan. Kuma ba ita ce wadda ta saka mata a lefe ba.

Karasowa tai, Islam ta dan shagwaba tana fadin, "Anty Mimah, na kasa taimaka min."

Dakyar ta iya haɗiye wani abu da ta ji ya tsaya mata a ƙirji. Tana zagawa ta bayan Islam ɗin, kallo ɗaya tai taga ta inda button ɗin ya makale. Cirewa kawai zata yi ta gyara, amma saboda abinda ta shirya se ba ta ce komai ba. Ta shiga ƙici-ƙici kamar so take ta gyara, tace, "Islam, wannan rigar taki wa ya matse miki ita haka? Ko ba a gwada ki bane wa ya baki?"

Dan turo baki Islam tai tana fadin, "A jikina ma aka gama ta. Maama ce ta saka a kamin ita."

Jin Fulani ce ta saka aka mata yasa wani bakin ciki ya cakkaketa. Wato duk wani abu mai daraja da shegen tsada daga gurin Fulani ake gani kasan koh?

Ba ta san lokacin da ta sa ƙarfen jikin zoban hannunta tana jan button ɗin ba - ta fizge, ya fice daga jikin rigar baki ɗaya. Irin mistake ɗinnan tai, ta shiga nuna Islam tana fadin ta yi hakuri.

Dan zaro ido Islam tai, tsoro yana kamata. Saboda Hjy Azeeza strictly take gaya mata kar ta bari komai ya taba dress ɗinnan kafin bikinsu, amma gashi yanzun wannan abin ya cire. Ta shiga uku. Wani ruwa taji yazo idonta amma don kar ta bata makeup dinta ta ka sauri ta shanye tana fadin, "Anty Mimah, yaya zamuyi yanzun?"

Hjy Jannat da ta ji shiru-shiru, leƙasu da tai taga me ke faruwa, ta fara salati, ta kira 'yar uwarta. Rasa yadda za su yi sukai. Veronica ganin abinda ke faruwa yasa ta shiga tana dubawa. Tana ganin yadda aka fizge dress ɗin, ta san cewar da ƙarfi aka cire, saboda aikinta ne. Ta girgiza kai kawai, domin in dai Islam ta saka a haka, an rage darajarta.

Dakin ta koma, ta shiga bude gifts ɗin kayan da Ehsaas ya bata, ta kawo wa Islam ɗin a matsayin ita ta kawo. Cikin sa'a kuwa ta samu har da kayan aure. Shiga tai, tace su basu guri tana kallon Mimah sama-sama, ba dai tace komai ba kawai.

Suka fito jikinsu duka a sanyaye. Gashi sun san Gimbiya Mimah ɗin ba zata taɓa yin hakan da gangan ba. Mimah looks so worried a fuska, amma deep down wani daɗi take ji don ta san in this short time ba zata taɓa samun dress ɗin da zai kai wannan haɗuwa da tsada da kyau ba.

Tsabar ta ma gama abinda take so, se ce musu tai ita zata fara wucewa. Akwai bakinta dangin mijinta da za su zo gurin taron suna jiranta. Cike da makirci ta shiga rokonsu kan a tabbatar komai na Islam ɗin ya tafi daidai kafin time ɗin fitowar ta. Amsarta kawai sukai, har suna tunanin kiran Fulani don su sanar da ita abinda ya faru da dress ɗin, amma dai suka fasa don su bar mahaifiyarta tai iya nata itama.

Fitowa tai tana dariyar mugunta, tana kallon wayarta na ringing. Seda ta karasa mota ta masa. EHSAAS ya shiga tambayarta ina kwalliyar, ko akwai wani abu ne? Har yanzu bata gamaba. Tabe baki tai tace mai, "Komai normal, kawai dai sun hanata daukar hoto, sun gane aim dinta." Girgiza kai kawai yay, yana mata godiya, ya kashe wayar do already yana cikin motar da zata kaishi zuwa gurin daurin auren, saboda ka idar. Daman shine ze je yajirata, ita kuma tareda mahaifinta zata sauko. Addu'a kawai yakeyi kada mutumincan ya batawa Islam ranar farincikinta ta duniya baki daya.

Aman ne yakaraso shima, ya shirya cikin shigarsa ta alfarma, yashiga bayan motar EHSAAS kusa da shi. Rada ya mai a kunne kamar wani zejisu, shima kawai ya jinjina mai kai, yana bashi order akan duk abinda yazo, ya gaya mai yawuce kawai.

Yana ganin wucewar dawakan mai martaba da tawagarsa, yadan gyara shawl ɗin dake kafadarsa, yana kara duba kansa a mirror din motar kafin yadan saki murmushi ta one side. Dimple dinshi na wani irin mugu fitowa saboda yadda ya saisaye bakikkirin din beard dinsa. Seda ya tabbatar visitors din sun gama zuwa, saboda babu wanda za a sake bude ma kofa, yashiga. Indai amarya da ango suka zo, ya sanya ya bawa driver order kan time yayi.

A wani irin slow suka fara tafiya, don tacan gate na uku na cikin palace din katafaren gurin taron yake. Gurin taron da yafi kowanne gurin taro girma da haduwa a kasar Nuristan baki daya. Royal weddings kawai ake yi a ciki na princes da princesses. Ko ina na cikin palace yadau harama, har da bayi, sunyi shigar sababbin uniforms din da aka dinka ma kowanne daga cikinsu. Darajar wannan biki mai daraja, ita kanta hanyar da zebi an gyarata da real rose petals da aka zuba daga tun daga farkon sashensa har zuwa ƙofar babban dakin taron bikin.

Ana tunkaro gurin suka fara jiyo sautin karar Royal Trumpets da African drums da suka cika masarautar baki daya.

Yana hakimce a daya daga cikin motocinsa wacce kyauta ce daga mahaifiyarsa Fulani Hajar - Bugatti La Voiture Noire da aka yi custom specially for this wedding. An yi covering dinta da dark royal matte finish, with 24k gold rims, and the royal crest of Nuristan engraved on both doors.

Bayan motarsa, akwai wasu motocin guda goma sha biyu dake binsa abaya. Wasu irin arnan limousines ne masu royal insignias, wanda suke dauke da mahaifiyarsa da kakarsa har da su Mother Fariha da matan babansa duka.

Gefe da gefen motar kuma akwai horses with white coats, kowane doki an daura masa royal tassels a wuyansa, da miniature flags of Nuristan.

Wani irin kamshine ke tashi tako ina a palace din, saboda turaren sandalwood na asali wanda aka fesa daga royal censer a gaban palace din ya cika ko ina.

Lokacin da motarsu ta karaso ta tsaya adaidai ƙofar dakin taron, seda 'yan uwansa gaba daya suka fito, kowa da kowa ya fito, sannan aka masa signal da shi kadai ake jira tare da mahaifiyarsa, wacce zai shiga da ita gurin taron.

Seda ya gama jan ajinsa tukunna ya bada dama aka bude mai kofa. Nan ma seda ya dau mintina kafin ya saka kafarsa akan kasan royal green carpet din dake shimfide har zuwa cikin dakin taron. Flutist sai aikin busa sukeyi, masu kada drums na yi.

Sanda ya fito gaba dayansa, wani iri kirari aka dauka aka fara mishi, cikin tsayuwarsa wacce take nuna shi a matsayin cikakken namiji mai cikar kamala da haiba. Kafin ya fara takun nasa, wanda kallo daya zaka yi masa kasan cewa shidin dan sarautane gaba da baya, tsabar daraja da girma.

Dayake bawa mahaifiyarsa har gaban motarta ya karasa, ya dan yi vowing kadan saboda ita da babansa kadai zai iya wa hakan. Yana mika mata hannunta, ta kama tana murmushi, hakoran makanta na gold na bayyana cikin net half cover niqab din dake fuskarta. Duk haskensa senaga ya dishashe a gaban Fulani Hajar. Kana kallonta kasan mahaifiyarsa ce saboda yadda suka yi matukar dacewa da juna da dibar kama da juna. A hankali suka fara takowa har cikin katafaren dakin taron, hannun mahaifiyarsa cikin nashi. Daga ita har shi, farinciki yana cike zukatansu, domin wannan itace babbar ranar da suka dade suna jira a rayuwarsu.

Shigowarsa tare da Fulani Hajar ba karamin tunzura zukatan wasu tai ba, saboda yadda suka haska suka wani irin bada kala. Abin yayiwa sauran matan sarki ciwo, da suke ganin kamar EHSAAS ya nunawa duniya bambanci - cewa mahaifiyarsa mahaifiyarsa ce, su din ba kowa bane face matan babansa.

Cikin manyan da suka halarci taro, musamman manyan matan, kowa burinsa ya samu damar magana da Fulani Hajar. Don yanzun an riga an gane itace star, itace taci gida baki daya, saboda dantane zai zama sarki, su basuda yaya.

Wasu kuma abin ya kayatar dasu ba kadan ba, musamman King Nashwan da yake ji kamar ya maida iyalansa ciki. Saboda tsabar kauna, yau bai zauna akan crown ko kadan ba. Yace ranar EHSAAS ce, ba zai yi stealing mai spotlight din ba. Yana zagaye da manyan dattawan kasar Nuristan, da kusoshin shuwagabannin kasashen ketare da suka samu halartar bikin.

Ehsaas be saka hannayen Fulani ba har seda ya kawo ta kujerar kusa da Mai Martaba, wanda daman is meant for her. Cikeda tsokana ya dau hannayenta yana sawa cikin namijinta, ba tare da ta ankara ba tai sauri da kasa da kanta. Mai Martaba kuwa ya rike kamkam yana murmushi. Manyan suka dauki kabbara yana dan jujjuya Ehsaas hannaye, alamar shi ko. Kana kallon salon nasu kasan ba karamin you kaunar juna suka ba, se kace su su kadai ne iyalinsa. Saboda soyayyarsa a garesu ta musamman ce.

Mimah dake daya gefen na mahaifinta wani irin abu taji ya cake mata a zuciya, tana jin kamar babansu ba taba daukar kowa da ba kamar yadda ya dauki Ehsaas.

Daga bangaren Islam kuwa ta wata kofar sirri suka biyo da ita aka dakkota cikin palanquin ta musamman, aka shigar da ita ta bayan dakin taron zuwa saman benen. Kanta a kasa, manyan matan ke tafiya da ita. Amma kasancewar mamanta na gefe nata yasa taji duk wata dar-dar da take ji ta samu confidence din tararsa. Suna karasawa saman benen ta jiyo muryar Aman yana gaisheta yana kuma yaba kwalliyarta yana meh. Bata dago ta kalleshi ba amma dai tace mai "tagode" kasa-kasa. Ba ta san waye aka hada hannayenta da shi ba amma dai taji yadda kirjinta ya soma beating fast. Bata gane waye ba seda taji Aman cikeda muryar iya shege yana fadin:

"Daddy ba kace tayi kyauba?"

Da sauri ta dago ido, aiko caraf idonta ya sauka akan Abraham Zion wanda ke kallonta irin kallon nan da tasan na tsanane da tsantsar bakin ciki, kuma ya rike hannayenta tsaf. Jikinta rawa-rawa ya fara yi seda Hajiya Jannat ta lura da haka tace:

"Islam, lafiya kuwa?"

Kara matse hannayenta yayi. Bai jira ta basu amsa ba kawai ya jawota suka fara walking down stairs din. Wani irin harbawa kirjinta yake.

Tun lokacin da ya fara saukowa da ita idon kowa yayi kansu. Abraham sanye yake cikin wata arniyar Tom Ford suit fara tas - irin dai shigarsa ta koyaushe daya saba yi. Sosai yake ji kamar tafiyar kai kansa wuta yake yi yadda yaga idon kowa akansa. Tunda yake programs dinsu na addini yana tsayawa gaban jama'a bila adadin, yayi bayani, amma ba taba jin kamar a tsaye yake akan wuta a gaban mutane a rayuwarsa ba kamar yau.

Wani irin daavi yake ji - yana jin ba zai taba iya yafewa Peace wannan tozarcin da ta jawo masa ba. Kasancewar sa sananne mutum ya sanya aka fara kallon kallo a gurin amma ba wanda ya ke da zarrar tankawa.

Ehsaas ya kafe ta da kallo saboda bala'in kyan da shigar tata ta masa, kuma ya mugun ji dadin ganin kayan da ya saka aka mata da hannayensa - ya rubuta abin da yake so ayi a jikin dress din don kuma yaji dadi ta saka a ranar aurensu. Wani irin unique modest custom ne made by Elie Saab x Zuhair Murad gown.

Islam ta hade ta fito kamar wata hasken lunar eclipse. Gown ɗin is very modest yet commanding, with diamonds & dusted silk, real silver thread embroidery, da moonstone lace da ke walƙiya kamar wani wata a sararin Samaniya.

A-line ne, ya rufe jikinta gaba daya, long-sleeved, high-necked, tight at the wrists, with pearl droplets falling like divine tears from the sleeves.

Rabin fuskarta was veiled daga bridge din nose dinta har zuwa chin dinta. An yi covering dinsa in soft, shimmering chiffon veil.

Idanuwanta da brows dinta were visible, rimmed in bold kohl that echoed mystery and fire - eyes that could silence a thousand courts. Saboda idanuwan Islam sun kasance babban magnet din da suke jawo mutane zuwa gareta bayan dan banzan hourglass body shape dinta.

Wani irin veil ne aka yafa mata mai kama da hijab wanda aka yi daga layered lace da crystal-trimmed chiffon, flowing to her waist, crowned with a diamond tiara in the shape of a crescent moon.

Ehsaas kwata-kwata ba san lokacin da suka yi walking akan royal green carpet din ba har suka karaso zuwa gabansa. Gaba daya ya mace a tsaye yana godewa Ubangijin da yayi masa kyautar wannan halittar a matsayin mata.

Prince yaji Aman ya dan tabashi - hakan ne yasa ya dawo hayyacinsa yana sakin wani kayataccen murmushi. Idonsa ya sauka akan Abraham wanda yaga ya rame ya kara duhu. Murmushin keta yayi mishi irin gidan kaso wasane, hade rai Abraham ya sake yi kafin yayi lining daidai kunnen Islam yace mata:

"My daughter, you can still back up. Kice kin fasa and daddy will fight the world for you - koda hakan zaiyi sanadin mutuwata."

Islam dakewa tayi kamar ba ta san me yake cewa ba. Idanuwanta a kasa, zuciyarta na wani irin bugawa.

"Back out now," ya sake maimaita mata, amma ba tama nuna alamar ta saurare shi balle tayi yadda yace din.

Hannayen da Fulani Hajar ta bata yasa Abraham ya kara matse hannunsa cikin nata. Da taji kamar zai balla mata kashin fingers dinta, ba shiri ta mika ma Fulani hannayenta. Ta kama kuwa caraf - ba yadda Abraham ya iya. Haka ya saketa yana jin cewa ya wanke hannayensa daga lamarin Peace baki daya. Kuma mamaki yana kamashi ganin har lokacin kanin baban Ehsaas da suka ce zai kawo masa mutanensa da zasu tayashi hana auren - bai zo gurin taron auren ba. Baki daya a ransa ya raya kodai yaudararsa yayi?

Fulani ta kama hannayenta tana murmushi sosai mai kayatarwa duk da ba a ganin cikakkiyar fuskarta. A hankali ta kama Islam tana karasarda ita gurin da aka tanada domin zamanta, inda aka saka babban labule mai sharara daya raba tsakanin bangaren mata da na maza - inda Ehsaas zai tsaya a bangaren maza ita tana na mata.

Saboda aiki da lokaci ya sanya Mai Martaba yayiwa Malam Liman alamar a fara proceeding domin daurin auren. A hankali yayi ma Ehsaas nuni da shima ya karasa ya zauna. Zama yayi kamar yadda aka zaunar da Islam, ya tankwashe kafafuwansa yana wani iri kallonta duk da rabin fuskarta a rufe yake - idanuwanta da girarta cikakkiya yake gani. Da ta zanu ya wani lumshe ido, yana ji kamar ba zai iya jira a gama daurin aurennan ba.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote [12/06, 11:35] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's Fatoum's Passion: EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.