EHSAAS

Chapter 33

by @fatoumspassion

Malam Liman ya hau wajen da aka tanadar masa, cikin nutsuwa da ƙwarjini ya soma magana:

"Innal-ḥamda lillāhi, naḥmaduhu wa nastaʿīnuhu wa nastaghfiruhu, wa naʿūdhu billāhi min shurūri anfusinā wa min sayyiāti aʿmālinā. Man yaḥdihillāhu fa-lā muḍilla lah, wa man yuḍlil fa-lā hādiya lah. Wa ash-hadu an lā ilāha illallāhu waḥdahu lā sharīka lah, wa ash-hadu anna Muḥammadan ʿabduhū wa rasūluh. Amma baʿdu: Fa-inna aṣdaqal-ḥadīthi kitābullāh, wa khayral-hudā hudā Muḥammadin ﷺ, wa sharral-umūri muḥdathātuhā, wa kulla muḥdathatin bidʿah, wa kulla bidʿatin ḍalālah."

Ya karanta Khutbatul Haajah cikin nutsuwa yana mai buɗe taron da sallama irin ta Musulunci. Ya fara tunasarwa akan cewa aure ibada ne, kuma sunnah ce daga Annabi Muhammad ﷺ.

Sannan ya fara jawo aya daga cikin Al-Qur'ani mai girma:

"Wa min aayaatihi an khalaqa lakum min anfusikum azwaajan litaskunoo ilaiha wa ja'ala bainakum mawaddatan wa rahmah; inna fee zaalika la aayaatil liqawmin yatafakkaroon."

Malam Liman ya shiga fassara ayar yana musu bayani dalla-dalla akanta.

Abraham se zare ido yake kamar shege 'Arabon gado saboda dayawa daga cikin abubuwan da ake cewa ba ji yake ba, don larabci suke jefi-jefi suke yin turanci. Bayan an kammala,

Malam Liman yace "zasu shiga siga yanzu kamar yadda addini ya tanadar da kuma bisa tsarin al'adarsu." Kallon Aman Malam Liman yayi yana mai magana ƙasa-ƙasa, da yasa Aman ya wuce zuwa gurin Mai Martaba. Ƙasa-ƙasa yayi masa magana, sega Mai Martaba ya tashi da kansa-abin da yasa ake ta mamaki kenan saboda an san EHSAAS is present-he doesn't need any waliyyi, zai karɓi aurensa da kanshi.

Basu gama rufe baki ba, daidai Mai Martaba ya ƙarasa gefen ɓangaren da Islam take zaune. Shima EHSAAS kallon babansa kawai yake yi. Malam Liman yace:

"Ina waliyyin Amarya ya matso kusa."

Mai Martaba yayi murmushi yana fadin:

"Gani nan. Allah ya gafarta Malam."

Murmushi Malam Liman yayi yana kallon Abraham da yake ta fici-fici da ido, don a tunaninsa shi zasuce ya tsaya mata a auren. Yayi musu rashin mutunci don ko zasu kashe sa ba zai ba.

Malam Liman yayi gyaran murya yana fadin:

"Allah ya temake ka. Babu wani dangi na kusa da ita, kai zakai jinjina kai?"

Mai Martaba ya dan jinjina kai yana fadin:

"Babu! mahaifinta, ba zai iya karɓar aurenta ba saboda shi din ba Musulmi bane. Duka 'yan uwansa na kusa ma haka. Hakki na ne a matsayina na shugaba a wannan ƙasar kuma Musulmi ɗan uwanta in aurar da ita."

Murmushi EHSAAS ya shiga yi saboda duk da ƙasa-ƙasa suke yi yana jiyo abin da suke faɗa.

Malam Liman yaji daɗin abin da Mai Martaba yace sosai kafin yace:

"Toh, me za a shar'anta sadakinta?"

Kallon EHSAAS yayi yana murmushi kafin yace:

"Shi fa yarshi me tsada ce, don haka yana buƙatar 2 billion grams of pure 24K gold."

Babu wanda bai ji wannan magana ta Mai Martaba ba, don wannan karon ya kunna speaker ɗin da aka makala masa a jikin kayansa-wanda yasa jama'a da yawa buɗe baki-saboda sadaki ne wanda ba a taɓa ba wa wata mace a tarihin ƙasar ba. Sadaki ne mafi daraja wanda zai mayar da ita multi-billionaire a tashin farko.

Wani irin abu ya danne zuciyar Mimah tana jin shekararta nawa a tare da Mai Martaba amma bai taɓa bata wannan tsantsar dukiyar ba, kuma sadakinta, ita a matsayinta na 'yar sarki ko kwatan wannan ba a ba ta ba. Pure 24K gold fa shine gold mafi tsada a duniya kuma ya buƙaci a ba ta 2 billion.

Kwafa kawai ta shiga yi tana jin lallaima an gama raina mata wayo.

Malam Liman murmushi yayi kawai ya kalli EHSAAS yana fadin:

"EHSAAS bin Nashwan bin EHSAAS, an bayyana maka cewa za ka auri Islam bint Abraham, akan mahr ɗin da ya kai kimanin 2 billion grams of 24K pure gold. Shin ka amince?"

EHSAAS yayi murmushi yana fadin:

"Na amince."

Nan take aka fara fiddo gwala-gwalan daga cikin wasu irin akwatuna na alfarma, ana ɗaura wa saman gram ɗin da aka tabbatar sun cika cif cif.

Malam Liman ya juyo yana fadin:

"Alhamdulillah!"

Ya kalli Mai Martaba yana fadin:

"A matsayinka na waliyyin Islam bint Abraham, shin ka amince da wannan auren tsakanin diyarka Islam da ɗan sarkin masarautar Nuristan, Prince EHSAAS bin Nashwan bin EHSAAS, wanda ya biya mahr ɗin da ka amince da shi?"

Dan jinjina kai Mai Martaba yayi kafin yace:

"Na amince."

Kabbara! Aka ɗauka.

Malam Liman yayi gyaran murya yana kallon labulen da aka raba tsakaninsu da Islam, dashi yana kallonta saboda shara-shara ne sosai. Yace:

"Ke kuma Islam bint Abraham, kin yarda a aurar da ke ga EHSAAS akan wannan mahr ɗin da waliyyinki ya ambata?"

Dan shiru tayi tana matuƙar jin kunya. Veronica dake bayanta ta dan shafa kanta tana fadin:

"Islam, ana magana."

Don ita so take tace "a'a" kawai su ɗauketa su tafi da ita gida.

Sannan ta dan jinjina kai, muryarta na rawa tace mishi:

"Yes, I do."

Kabbara gurin ya ɗauka.

Malam Liman ya dubi crowd din cikin farin ciki yace:

"Alhamdulillah! An daura auren EHSAAS bin NASHWAN bin EHSAAS da Islam bint Abraham akan mahr 2 billion grams of pure 24K gold. Allah ya sanya albarka. Mun shaida. Mun shaida. Mun shaida."

Kabbara! Aka kara ɗauka kafin gaba ɗaya crowd ɗin su ɗauka, aka shiga karanta Suratul Fātiha da Suratul Ikhlās a matsayin addu'a ga masoyan da suka zama mata da miji.

Ana kammalawa aka bada umarnin a yaye labulen dake tsakaninsu, aka zarge shi. Wata irin farin ciki da annashuwa ce ta dabaibaye zuciyar EHSAAS, yana jin kamar yau yafi kowane namiji sa'a a duniya. Binta yake da kallo kamar bai taɓa ganinta ba a rayuwarsa. Kamar ya cinye ta haka yake ji sabo da tsabar so.

Mai Martaba ya kamo kafadunta suka taho tare slowly, yana karasowa da ita gaban EHSAAS a matsayinsa na waliyyinta. Ya kama hannayenta ya saka cikin nashi yana fadin:

"Ga ta nan. Na baka diyata amana. Babu abin da zan ce maka se ka ji tsoron Allah. Ka ji tsoron Allah. Ka ji tsoron Allah. Allah ya baku zaman lafiya. Kariketa da kyau."

EHSAAS yayi bowing gaban Mai Martaba. Islam ma ganin yayi haka yasa tayi. Ya dago su, ya haɗasu, ya rungume su yana shimusu albarka.

Malam Liman ma yasa musu albarka, ya karasa gurin Kawu Erfan dake gefe yana ta cika yana batsewa, bayabo ba fallasa, shima yace:

"Allah yasa albarka a auren."

Suka juya ga Abraham suna karasowa. EHSAAS saboda yadda yake farin ciki, bai ma lura da yanayin yadda fuskar Abraham ta dauke rahma duka ba. Ya wani rungume shi yana fadin:

"Bless us, Daddy."

Peace da take shakkarsa bata yi gigin taɓa shi ba, amma sai EHSAAS ya dan janyota suka rungume shi tare. Yace:

"Ba zaka yi blessing ɗinmu ba, Daddy?"

Bakinsa ya saita daidai kunnuwansu yana fadin:

"Allah ya tsine ma wannan auren" daga Islam har EHSAAS.

Wani irin abu suka ji ya cakar musu kirji.

"I curse this marriage! and I curse you peace bazaki taba albarka acikin rayuwarki ba, you will forever be in pain and agony tunda kika zabi ki tozarta ni haka yadda kika wulakanta ni kema Allah ya wulakanta ki,yasa aurennan shine ze zamo ajalinki"

dasauri EHSAAS ya janyeta daga jikinshi ganin jikinta ya soma rawa maganganun nasa nashiga kwakwalwarta, gently yake kallonta hawaye har yafara zuba daga idanuwanta. wllh da badan ranar farincikin shi bace kuma Abraham mahaifin Islam ne da babu yadda za'ai yakasa zubar mai hakoranshi agurin nan.

Abraham be jira meye zasuce ba yawani karasa yana jawo hannun matarsa da itama yanada tashi da ita ganin ta shishige anata wani komai da ita yashiga jan hannayenta babu wanda su kaiwa sallama suka fice ahall din daman he is free to go tunda aka rigada aka daura aure.

Akofar fita yaci karo da jay da yake shigowa wurjanjan don dakyar yasamu Maisoon tashigo dashi tawata kofar sirri shida bakin daya kawo mutanen Abraham ne wanda yabashi contact dasu turawane kuma suna daga cikin jiga jigai mabiya addininsa an aiko sune daga can sama donsu dakatar da Auren bayan ya kaima Abraham waya yayi asirrince dasu ajiyan.

yau suka dira akasar tun kafin adaura auren amman sbd dokar tsananin da EHSAAS yasaka aka hanasu shigowa dagasu har jay din daya kwaso su Abraham yashiga kallon jay cikeda takaici kafin yakalli mutanensa dayake dada jin ya muzanta agabansu dawana baki ze kallesu yace yarshi ta auri musulmi, strictly yakalli jay yana fadin "useless non believer kawai daman ni mema yasa nayarda dakai you guys are all in competent" yakarasa yana yiwa mutanenshi rada akunne sbd baze taba shiga ya kunyatar dakansa ba peace ba, ya yafe ta duniya da lahira kuma yatsine mata.

gani yay sunjuya sunbi bayan Abraham yarasa gane meke faruwa har seda yaji busa da bugun ganguna na al'ada alamar har andaura aure ango da amarya na shirin fitowa besan meyasa ba wani irin kishin EHSAAS ne yadanne zuciyarsa yama kasa karasawa hall din agabansa dogarai suka fara zuba fararen furanni masu kamshi da taushi akasa wanda ma'auratan zasuke takawa har su karasa saman horse dinsa. Fari kal na EHSAA wanda yake kiransa da Raehan.

jay nanan tsaye yaga fitowarsu, duk mutane an rakosu ana watsa musu flowers abin gwanin burgewa har gaban dokin, Islam dukda yadda zuciyarta take nauyi akan abinda Abraham yace amman hakanan tahakura ya daurata saman doki kwata kwata bataji tsoron hawan ba don ba yau tasaba hawan ba takan hau idan taje guraren shakatawa.

shima hawa yay yana riko mata siddin ya rungumeta tabaya yana shakar daddadan kamshin tururrukan da suke tasowa daga jikinta ya lumshe ido yana fadin "are you ready for the journey habibty?" kasa cemishi komai tai. setaji yadan taba gefen cikin yana fadin "uhm?" alamar yana jiran ansa jinjina kai tai yafara tafiya da dokin ahankali al umma nabinsu akasa ana sunata hailing dinshi cikin harshen larabci Ya Amirna Ehsaas! Fakhr al-qalb wal-nass! Al-laylah farhatna bik, W'il-shams tighar min zifafak! Allah yihfaz zawajak, Wa yihfaz malikna al-'aziz! Suna watso musu roses, Cikin kunnanta taji yana mata rada yana kwantar mata da hankali akan kartasaka abubuwan da Abraham yafada mata cikin ranta in sha Allah babu abinda zefaru da ita ko aurensu, zebata farinciki fiyeda wanda take sha awar samu arayuwarta kuma in Abraham yasakko daga fushi zasuje su sake bashi hakuri don shidin mahaifintane har abada batada kamarshi,sosai taji dadin kalaman EHSAAS din sbd abubuwan daya fada mata sun mugun daga amata hankali amman yadda EHSAAS ke kwantar mata da hankali cikin murya mai sanyi yasa kawai tabirne abin akasan zuciyarta.

ahaka har yakarasa da ita sashen Fulani inda abisa al ada daman gurin mahaifiyar sane zata fara zuwa amata shirin grand royal reception din da akeyi na mata daban na maza ma daman domin basu cika hada bikin maza dana mata ba.

akofar sashin suka tarar da Fulani da duka yan uwanta suna jiransu harsun karaso dake su mota suka hawo.

da kanshi yasakko da ita daga saman dokin yana fadin "bismillah wife," gimbiya mimah ce tazo tana karbarta daga hannunshi cikin nuna farincikinta tashiga congratulating dinsu har tana tsokanarshi wai buri dai yacika zasuji shiru murmushi kawai yay mata yana kallonsu.

har aka gama wanke mata kafafafu da madara aka bata wani abu taci suka shigar da ita sannan shima yajuya yana nufar nashi sashen da abokansa suka cika makil ko kuma yace abokan da Aman yay masa.

sosai yashiga busy domin yana zuwa wanka yay yafito aka shiga shiryasa cikin wasu kayan daban na alfarma. suna kammalawa suka wuce gurin reception din dame Martaba ke jiransa shima da tashi ta wagar anci ansha anyi barin Kudi sosai domin irin kyaututtukaan dashida Islam suka samu awannan tarurrukan ze isa yamaida kai wani mai kudi hamshaki.

komai yatafi adaidai bisa tsari ana kammalawa kuma aka shiga sallamar baki bashi yasamu kansa badai se kusan karfe goma na dare kuma yasan daga bangaren Islam ma haka, koda ya kirata yaji switchup be wani damuba sbd yasan tagaji amman yakira mimah tatabbatar mai taro yatafi atsari yanzun hakama amaryarsa gajiya tayi liqis da ita takwanta barci. murmushi yay yana fadin "yagode sosai, tacigaba da kulamai da ita" kafinnan yakashe wayar yana fadawa saman gadonshi kamar wani karamin yaro yashiga birgima yana fantasizing irin rayuwar da zasuyi shida Islam din.

Islam tunda tai sallar asubah bata tashi tashiba se kusan karfe sha daya na safe.

tamike tana mika domin kwana biyunnan bata wani barcin kirki amman yau datai ta mugun jin dadin jikinta sosai tayi mamaki sosai da bataji su hjy jannat da azeezat sunzo sun tasheta ba tamike ahankali tana zira slippers dinta dake gefen gadonta tawuce toilet tayi tinanin kila sbd tana sashen Fulani ne basuzo ba. brush tafara fasawa sabo gal tasaka toothpaste tanayi tana kallon kanta amadubi har wani irin kyallin kyau taga takara kawai tafara murmushi ita kadai waifa yanzun tazama matar aure kuma matar sire dinta, kamar yana gabanta tashiga sunkuyar dakanta tana murmushi ita kadai tana kammalawa ta ajje komai a inda yake.

sosai tai mamakin ganin an ajje mata kwalaben turarrukan wankanta datake amfani dasu abangaren uwar soro tai murmushi aranta tace "Kenan sunzo sunga ina barci se suka tafi," hada komai tai daman tuntuni sun koya mata tafesa wankanta tsaf tafito daure da karamin pink towel dinta daidai nan taga jalila data shigo don an aikota ta ajje mata kayan da zatasa yaudin tana Allah Allah kada taganta tafice amman gashi tafito sunga juna din sbd batason tatsani yarinyar akan laifin daba nataba, kuma ita dabadan mamanta ta matsaba babu abinda ze kawota auren EHSAAS. "jalila" Islam tafada tana kallonta kasa murda handle din tai tana rintse ido don bala'in haushinta takeji,ta juyo tana kallonta,seda ta tattaro dukkan karfin gwiwarta sannan tace "sannu amarya se yanzun kike tashi,"

Islam karasawa tai sbd batasan tsakaninta da EHSAAS ba kuma tasan EHSAAS nasonta kmr yadda yakeson mimah gashi hjy jannat tace mata intanason takara samun gurbi aransa sosai taso yan uwanta taringa kyautata musu tana kuma yi musurmushi tadena yimusu uban miskilancin nan nata, Islam sosai taji dadin ganin jalila daman gidan dukse manya ba yara yara dukda jalila ba sa'ar tabace amman she prefers her company akan nakowa sbd atleast age gap dinsu bawani meyawa bane ba.

"sannunki jalila daman kina nan bantaba ganinki ba?" basarwa jalila tai kafin tace "aijiya nazo" Islam takarasa tana zura hijab dinta sbd bata saba zama gaban mutane da towel ba koda mata kuwa. tace "meyasa baki zoba duk anyi abubuwa bakyanan?" tace "kinsan exams nakeyi shiyasa" tana kokarin kara bude kofa tafice Islam tace "ina zakije bazaki zauna mu danyi hiraba," aranta tana raya " yaushe yarinyar nan ta koyi surutune last time I checked magana ma yi take kamar za'a cajeta" jalila tace "sorry I can't ina abu akasa ne! daganan tafice tanajin ba dadi har cikin ranta sbd tasan ba laifinta baneba amman zuciya batada kashi,ita anyama zata jira gobe agama walima ita dai tatafi kawai take so.

Islam tadau lokacinta sosai ta shirya cikin gown din da Fulani ta aiko mata da ita tai mugun karbarta tana cikin shirin sega su hjy jannat nan sune suka karba suka karasa mata simple MakeUp suka nade mata kanta da babban gyalen rigar.

sunayi ana fada mata ethics din cin abinci da surukai,sbd wannan ne first meal dazata fara having itada mother in law dinta da father in law dinta. har kasa suka rakata inda suka tarar da fulani tareda gimbiyah mimah a private dining din Fulani na musamman islam ta gaidasu cikin girmamawa suka zaunar da ita. Bayan sun kai gaisuwa gurin Fulani da mimah din suka wuce mai Martaba ne ya fara zuwa kafin EHSAAS se tambayar Islam ya keyi yata kwana fatan bawani matsala ta amsa masa da "eh babu" Kwata kwata dining din sit din mutum hudune ne kacal,sbd daga shi sai Fulani da EHSAAS se mimah ne kecin abinci akai. Inkaga sunhau dining dinnan toh family bounding zasuyi amman ajiyan aka karo kujera daya sbd ita don taxama part of them.

EHSAAS tunda yashigo idonshi yake akan islam din yakasa dauke ido daga kanta mimah na murmushi kasa kasa tana tabo Islam din da idanuwanta ke kasa sbd tana matukar kunyar mai Martaba,karasowa yay ya gaggaisheda iyayen nasa yaja kujerar dake kusada matarsa daman ita kadai ya rage yazauna yana satar kallonta.

Mai Martaba ne yabude zaman da addu'a kafinnan yafara musu nasiha akan zaman aure da hakuri da kyautatama juna da soyayya har yana buga musu example zamanshi da fulani da yadda babu wanda yataba jin kansu da rike sirrin junansu. cikeda hikima da dattaku, kafinnan yace "fulani ma tace wani abu." Tace "ai yariga yagama fadar komai kawai abinda zatace musu shine surike ibada domin ita makarin mumini ce karsuyi wasa da ibada in sha Allah babu wani abu daze taba cutar dasu arayuwa," godiya sukai musu shida Islam din kafinnan mimah ma tacema Islam "tazama kamar yar uwarta ita kadaice yar uwar EHSAAS guda don haka baida kamarta da ita kadai zata yarda agidan duk abinda yashige mata duhu ita zata ringa fadawa bama seta tunkari Fulani ba su sisters ne don haka sune zasu ringa jin damuwoyin juna suna temakawa juna" murmushi tai sosai tana jin dadin kalaman mimah EHSAAS closely yake watching dinta harta gama suka mata godiya.

amintacciyar kuyangar Fulani ce ta shigo zata fara serving dinsu Islam ta dakatar da ita domin yana daga cikin abubuwan da su hjy jannat suka koya mata cewar she should always serve her parents in law abinci kar taga ko sunada servants dayawa hakan kyautatawa ce me girma duk sun koya mata irin abubuwannan girkine dai taki yarda su koya mata sbd gogan da yake zigata cewa bata bukatar girki donta siye zuciyarsa.

gently tashiga serving dinsu se saka mata albarka sukeyi mimah aranta tace "ji kinibibi" ta zubama kowa kafin ta xubama kanta tazauna.

tana zama babu kunya taji ya daura hannayensa saman cinyarta yashiga shafawa ahankali yana cin abinci dan zaro ido tai tana kallonsa setaga he is focused abincinsa yakeci hankali kwance kmr ma besan meyake yiba. ahankali takai hannayenta kasan tana kokarin dauke hannayensa daga gurin sbd yanayin yadda yake matan dukda akwai barrier din riga tsakaninsu sosai yake tasiri ajikinta gani tai yacafke hannun yana wani murzawa.

fizgewa tai aikuwa yamayar saman cinya gudun kada kusur kusur yayi yawa yasa kawai ta maida hannayenta cikin nashi sbd bazata iya cin abinci yana yawo mata da hannu saman lap dinta hakaba.

seda suka kammala sannan Fulani ta tambayi gimbiya "yashirye shiryen walimar?" EHSAAS dagowa yay yana dan hada rai sbd shifa yagaji da al'adunnan matarsa kawai yakeso akawo mishi ya dauka yau zasu bashi ita. tace "maama yana tafiya kan tsari mun tanadi komai," fulani murmushi tai tana fadin "make sure is the best sbd yata tamusamman ce" takarasa tana kallon Islam datai murmushi tana kasa dakanta EHSAAS be san sanda yace "mims I thought dukhool(consummation night) is first before walima," kallon dasukai mai yasa yagane meyay agaban iyayen nasa da sauri yay kasa da kanshi yana sosa keya mai Martaba kawai ya girgiza kai yana murmushi irin nasu na manya Fulani kuwa mamakin bakin nasa take sbd tasan yadda yake da muguwar kunya takin karawa. Amman da kanshi yau wannan mgnr,mimah tace "EHSAAS kace me?" harararta yashigayi kasa kasa, Mai martaba yakalli mimah yana fadin "ku kaimishi matarsa duk abinda zakuyi aizaku iyayi tana dakin mijinta banason shiga hakki kinji ko" jinjina kai kawai mimah tai tana mamaki wai mai makon amai fada yayi rashin kunya agaban manya sema ace amai abinda yakeso ga EHSAAS dan gwal.

Tace "In sha Allah za'a kaita Allah yatemake ka" daganan basu jima suna hiraba mai Martaba yatafi kafinnan Fulani takalli EHSAAS tace mai "shima yatafi se anjima kuma karta kara ganin kafarsa asashenta yau" dan sosa keya yay yan fadin "tohm maama" sbd shikam mai martaba ya biyashi yakalli Islam suna hada ido yawani kashe mata ido daya.

lips dinshi kawai takalla tagane me yace mata "see you tonight babyyyy," wata irin kunyace tamamaye ta don tinanin ta suma sunga me yace din yana fita kuwa mimah tace "tataso suje sama kawai," Fulani tace "a'ah tafara zuwa ta gaggaishe da manyan bakin da basu tafiba kuma suna nan sashen" sunji dadi sosai su Queen laila,mother fariha da dai sauransu duk taje ta gaggaishe su tai musu bangajiya. ba haka mimah taso ba amman ba yadda zatai don yadda tsofaffin kewani ririta Islam ana nan nan da ita kular da ita yakeyi.

sama takaita tana kallonta tace "kinji dai rashin kunyar da mijinki yayi agaban Mai Martaba ko?" Islam tadan zaro ido domin kwara kwata batasan meyayba tace "meyayi," tace "sekace bakyaji bakiji yace wai ba dukhool za'a farayi ba kafin walima," Islam looking confused tace "whats that," mimah tace "wai baki saniba tohm dukhool shine consummation night ranar da ango ze fara kusantar ki yay having sex dake" dan zaro ido tai tana kallon gimbiya mimah sbd jin tana fadar maganar gangan kamar wata mara kunya.

tai kasa da kanta tana kasa magana gimbiya mimah cikin ziga take fadin "kina ganin yadda yake rawar kafarnan akanki aikina bashi kanki shikenan kinzama sorry..... zema iya dena sonki bakisan maza ba they just want to get into your pants kuma ina mai tabbatar miki kika bari EHSAAS yatabaki gobe akazo walimar nan kowa se yagane abinda kukai harda Fulani sbd bazaki iya tafiyaba kilama tafiyar ki ya canza har abada,idan nafara baki kalar wahalar da abinnan yake dashi sekin tausayamin kuma haka zasuyi dake sukara auro wata suma suyi da ita,"

Islam jitai wani amai nataso mata sbd the thought of her husband touching her sannan yaje yataba wata gaba daya yanasa tai feeling nauseous, ta inda gimbiyah mimah take shiga batanan take fitaba cikin fada fada take fadin "ga ke dinnan ba yar goyo bace, nan nan nazo daniyyar in temakeki, mom dina tace zata rakaki gurin malam kika kwashe komai kika fadama EHSAAS sbd ke yar dadi miji dadi saurayice bakida sirrin kanki,shiyasa nafita daga lamarinki peace gaki ga EHSAAS nan duk abinda yamaki karma kice kinsanni gobe,"

ruwane yakawo idon Islam tashiga girgiza kai tana fadin "don Allah kiyi hakuri aunty mimah bazan sake fada maiba daman fa shine ya tambayeni inda zanje kuma mexanje inyi kinsan karya babu kyau shiyasa na fadamai kuma yacemin zuwa gurin malamin shirkane babu kyau haramunne Allah zeyi fushi damu,"

harararta gimbiyah mimah tai kasa kasa afili se tace "dake na cemiki gurin boka zan kaiki ko aike baki mai bayani daidai ba shiyasa yay misunderstanding yazo yana titsiyeni kika karamin irin haka sena fita asha'aninki kinsan dai su grandma da maama duk old school ne basusan yadda mazan zamanin nan sukeba zanga wanda ze ringa koya miki abubuwa,"

hakuri Islam tashiga bata har tana kuka tana cemata tayi hakuri bazata sake fadawa kowaba. gimbiyah minah tashiga dariyar keta aranta sbd tasan yadda taji tsoronnan bazata fadawa EHSAAS dinba ta rungumeta tana fadin "is okay ni kinga ina kaunar kine peace shiyasa duk wani abinda ze amfane ki nakeson inkoya maki wanda zai cutar dake kuma in haneki kinga ina shiga sabgar sauran yarannan kamar yadda nake shiga taki?"

girgiza kai Islam tashigayi alamar a'ah tace "tohm kinyi sa'a nashiga don haka kiringa jin magana ta" jinjina kai tashigayi tace "me zanyi yanzun," tace "farko dai yanzun ina sadakinki?" dan jim Islam tai kafin tatina jiya Fulani tace mata ga sadakinta fa tace abawa Grandma ta ajjemata. Tace "yana gurin Grandma," mimah cikeda takaici take fadin "Grandma ko wato Grandma kadai kika yarda da ita waye yake zuwa yaymiki siyayya dacan inba niba meyasa bakice abaniba," dan jim tai kafin tace "kina cikin hidima jiya banason na takura mikine shiyasa," jinjina kai mimah tai tana fadin naji "tunda kinriga kinbata wannan sauran kyaututtukaan kudi duk da aka baki in ankaimiki gidan zanzo mu lissafa se inkarba inmiki investing acikin business dina na south kinyarda, zuwa daga baya inya cigaba da habbaka semu karbi sadakin naki ko" dan jim tai kafin tace "intambayi sire first yace inringa tambayarsa duk abinda zanyi," tace "kinga ko fadamasa zakiyi nafasa tunda kince haka kinsan dai dan kudin da aka baki befi chicken change din danake kashewa ba dakike tunanin zancuceki harse kinfadama EHSAAS wannan maganar" Dasauri tace "nafasa fadamai aunty mimah karkiyi fushi" tace "yauwa kokefa yanzun wadancan matan zasuzo su shiryaki zamu rakaki har sashen EHSAAS,kuma nasan bayan muntafi zezo kuma zenemi yataba ki kada kisake kiyarda kibashi kanki sbd kina bashi kanki ze dena sonki darajarki zata ragu a idonsa amman inkika ja ajinki kika hanashi gobema yadawo yay begging kika hanashi jibima haka wani martabarki ce zataita da duwa acikin zuciyarsa," Islam tace "really?" tace "yes mana ke kina abu kmr ba wacca tataso akasar wajeba haba."

Daganan ta cigaba da bugar cikinta duk wasu gifts data samu seda tafada mata su da wadanda suka bata anan su hjy jannat suka samesu suma sukai joining dinsu amman da yake batason susan motive dinta seta shiga kwada Islam din agabansu tana cewa aitayi goshi gifts din data samu ai tun zamaninta ba'a taba aurar da wanda yasamu irinsa ba. hjy jannat nacema Islam "aitazama alaja yanzun biyayya zata fara mata dama kuma gata princess yanzun ga kudi" hjy azeeza tace "kudaiyi kugama ko sile bazamu bakuba duk nagane neman gurin zama kukeyi" Akasha dariya, anan sukai la'asar anan,kafinnan asaka islam tai wanka kuma anan uwar soro ta samesu aka shiryata acikin wasu dakakkun kayan sarauta.

aka baza mata wankan gwala gwalai na alfarma ana mata wankan turarruka iri iri zuciyarta tacika da tsoro sbd abubuwan da mimah tacika brain dinta dashi ya mugun daga mata hankali tashin hankalinta ace yau EHSAAS ya dena santa ko ace yau EHSAAS tabashi jikinta ya koma ya karo wata macen, abinda take tsoro kenan dukda wani sashe na zuciyarta nafada mata her sire is different bawai iya abinda ya keso ajikinta ba kenan.

uwar soro sosai tagyara ta tsaf ana kiran sallar magrib sukasa tai sallah suka fito da ita an lullubeta cikin wata dakakkiyar alkyalla me thread na gold suka sakko.

sallama sukasa taiwa Fulani taita saka mata albarka dasu Queen layla dake su din iyayen angone yasa bazasu rakata ba, mother fariha ganin uwar soroce zatai rakiyar dake basa wani shiri yasatace ta fasa zuwa.

aka fita da ita cikin wata hadaddiyar palanquin ta musamman aka saka ta ita da uwar sorone kadai aciki tana rungume ajikinta har suka karasa shashen da yakenan tsit domin daman EHSAAS baya barin kai koman jama'a aduk inda yake zaune ko dayan sashen nasa ba'a bi ta wajen koda baya gari balle yanzun da yake nan tareda iyalansa.

wani irin huge flat ne me dan banzan kyau tundaga farfajiyar su hjy jannat ke santi sbd babu wanda aka taba bari yashigo ana ginawar se yau.

Farfajiyar farko na sashen shi kansa wata duniya ce ta alfarma da kyan gani da babu wanda yake da kwatan kwacin irinta a palace din, da zarar ka shigo, za ka ga driveway mai faɗi wanda aka lulluɓe da white Italian marble, yana haskawa kamar wani glass.Se wani hadadden fountain mai ƙirar Alhambra architecture da ruwa ke fita daga bakin golden lion heads guda huɗu. A cikin tafkin akwai fararen royal swans da ke shawagi cikin natsuwa, daya kara kayata gurin. Tsakar gidan kuwa an tsara shi da salon Andalusian-style da Moorish arches. Tsakiyar gidan akwai babban waterfall wall da ruwa ke gangarawa a hankali bisa black obsidian stone, Ko'ina cikin courtyard ɗin akwai golden brass benches, da Mughal-styled lanterns da suke ba da haske mai sanyi da launi. Adaidai kofar shiga suka ajje palanquin din ahankali aka fito da Islam dake lullube,tanajin hjy jannat nacemata "itafa anan zata hado kayanta tadawo taga gurin xama irin wannan aljannar duniya haka aiko sashen mai Martaba se haka," Uwar soro tana fadin "su kyale mata yarinya haka fa batason fitina"

Daidai suna tsayawa gaban double arched mahogany doors din gidan da aka yi da real Spanish wood, aka sa musu gold-plated handles masu zubi irin na zamani. A saman kofar akwai wani engraved royal crest na gidan sarautar Nuristan da aka tsaga, ahankali cikin bismillah uwar soro tabude sashen ta umarci islam "tafara bismillah tashiga da kafar dama" aiko bismillah tai tashiga da kafar dama kamar jira suke suka shige sunayin gaba uwar soro ta girgiza kai kawai.

ai tini mimah ta xaga takira mom dinta da sarauniya hassana don suzo suga katafaren sashe da mai Martaba yaginama EHSAAS din kar abasu labari,aiko cikin mintina kalilan se gasu tareda tawagarsu sun karaso,a Main Lounge Area suka tsaya wanda yakeda vaulted ceiling mai fitilu na Swarovski Crystal Chandelier,an rataye shi a tsakiyar falo. Fitilar tana da zare na azurfa da diamonds, dake walwali kamar rana da dare.

Wall panelings ɗin bangon falon an yi su da white Italian marble mai launin gold, an lullube kusurwoyi da mother-of-pearl inlays.

A gefe daya, akwai Velvet tufted armchairs masu launin royal blue, da kuma babban gold-leafed Victorian sofa da aka tsara da custom embroidery of the royal initials "E.I."

A tsakiyar falon kuwa, akwai onyx coffee table mai nauyi da tsada sosai, wanda aka kawo kai tsaye daga Greece. Akan tebur ɗin kuwa, an ajiye Versace tea set mai adon gold shima.

Har shafawa mai babban daki ta ringayi don ta tabbatar gold din na gaske ne tana jin kishin irin kayan dakin da aka zubawa Islam din dukda duk abinda yazuba ya zubawa mimah irinsu harma da finsu lokacin aurenta amman sam bataji dadin ganin yayiwa watama irin kayan yarta ba.

Hjy Hassana kam itada batada ma yar daza'a mata irin haka se hmmmmm hmm kawai take cewa. mimah tsabar gulma takarasa gurin grandama tana fadin "muje akaita dakin ko kar yazo ya sameta anan" Girgiza kai Grandma tai kafin tace "babu wanda ze shiga main bedroom dinsa and karku manta shidin prince ne but you sure can check all the other section nagidan,"

mimah bahaka tasoba amman dake ambasu iznin ganin ko ina se taja zugar tata su hjy jannat sunce sunga enough suka zaune gefen Islam suna bata karfin gwiwa yan kallon gida kam sun kalla iya san ransu sun kashe kwarkwatan idonsu,

Domin daga private library da media room dinsa suka fara, dake gefen main lounge area din cike yake da first edition leather-bound books, daga littattafan su Shakespeare har zuwa su Ibn Khaldun duk akwai. An saka automated rolling ladder domin hawa saman shelves din. A bangare ɗaya kuma, akwai soundproofed cinema room, da recliner leather chairs, kuma TV ɗin ciki 8K OLED curved screen ne, haɗe da surround sound by Bang & Olufsen.

Se jinjina kai sukeyi masu ya bawa nayi wanda hassada ta cikema rai sunayi Suma suna fita suka wuce private living room din islam din yana dauke da custom-made furniture da aka yi da danyar gold da walnut wood, an ɗora kujeru na royal velvet da aka sa tambarin sarauta a jikin su. Akwai babban fireplace da aka yi da gold da sardonyx, da kuma LED touch control panel da ke sarrafa komai daga temperature zuwa curtains har da ƙarar waƙoƙi masu taushi. Se kuma wani bangare da aka ware ake kira da "Royal Leisure Lounge" inda prince ze ringa kallo ko taro da abokansa. An sa 4D Home Cinema, billiard room, da virtual reality room. Saman bangon wannan wing din akwai hotunan kaf sarakunan NURISTAN nabaya har suwa kan king NASHWAN, wanda yake nuni da Nuristan heritage wanda aka zana daga hannun mashahurin artist daga Spain.

Suna gama kallon nan suka wuce grand dining hall,the hall is 80-foot long dining table da aka yi da rare Black Forest wood daga Germany, wanda gold ta ratsa tsakiyarsa kamar rawaya ta rafi. An yi chandeliers da Swarovski crystals guda 11, kowanne zekai aƙalla kilo 300. Kowane kujera da ke zagaye teburi an yi ta da silk brocade fabric daga Paris. Ganuwar dakin sun kasance anyi sune da hand-painted murals da ke nuna tarihin Nuristan da zuriyar sarautar.

Daga ciki, akwai gold-plated robotic serving arms da ke kawo abinci kai tsaye daga kicin, cikin glass-walled warmers. Gimbiyah ta rike baki wato donma kada akawo kowa sashensa shine yasaka akai ajje masa robotic arms, "tohm aizega wacca zata ringa mai girkin" tafara dariyar keta tana shiga kitchen din domin tasan dai islam bata iya girki ba ko kadan.

Kicin ɗin yana da babban marble island na Italian Calacatta Oro da ke tsakiyar ɗaki, tare da soft gold inlay. An lulluɓe dukan ganuwar da handmade walnut cabinetry daga Switzerland, da gold leaf trimming. Appliances ɗin kuwa, Kowane na'ura da ke ciki na Sub-Zero ne,da La Cornue Château da Gaggenau, musamman customized for Islam kadai. Akwai smart induction hobs, steam ovens, walk-in cold room, da kuma hidden non alcoholic wine cellar wanda ke karkashin kasa, ana buɗewa ne da biometric fingerprint din EHSAAS kadai dana Islam duk yadda mimah taso tabude kinbuduwa tai. tai kwafa kawai tana cemusu su wuce next section kawai bangaren dakunansu na barci suka nufa, akwai private spa da aka tsara da Thai bamboo walls, onyx lighting da kuma crystal ceilings da ke motsawa da hasken ruwan tabarau.

Akwai Moroccan hammam da ke fesa ruwan zafi da rose essence se Massage beds guda biyu na heated Himalayan salt base. Akwai ice room, infrared sauna, da kuma jacuzzi infinity tub da ke kallon wata yar rana artificial a cikin ceiling dome. Ana watsa custom music therapy daga real-time orchestra recordings na Vienna Symphony.

Wani irin abune ya danne kirjin mimah shd tasan dole ko iya kayan Mai Martaba yakashe millions gurin zubasu balle ahada d gwala gwalai dake jikinsu that is customized kawai fitowa tai bata jirasu mai babban daki su gama ba tai ficewarta agidan tanajin kome zefaru dolene tatara arzikin dayafi na EHSAAS da babanta.

Uwar soro da taga kallon nasu bame karewa bane gashi dare nakara yi yasa tarike Islam takaita har cikin main bedroom dinsu da yake akulle se itace tabude da pin dim daya bata.

ko ina se tashin kamshin dadadan turarrukan da aka kunna a humidifier din gidan yakeyi itadai islam babu abinda take gani dakyau har lokacin sallama tai mata,se alokacin tafara mata kukan shagwaba wai bazata tafi tabarta ita kadaiba,dakyar ta lallabata suka rabu, tace mata ai dole sutafi haka ka idar take ta ajje mata personal maid din EHSAAS zata kasance apalour harse prince yashigo tukunna zata tafi bangarensu,tasanar mata EHSAAS baya bari bayi nashigo masa sashi barkatar so duk wands tagani anan din is well choosen by him me amanane.

duk abinda take bukata na kayanta turarrukan ta,komai da komi suna closet na daya dakin wanda shine nata an ajjesu. tana gama mata bayanin nan da nasiha ta zame tafice tabar islam na matsar kwalla,tattara kan kowa tai har lokacin basu gama kallon gidaba amman sbd bame iya saba umarninta yasa duk sukatafi daniyar gobe zasu dawo su karasa ganin gidan dakyau.

Tsit Islam ta zauna bayan tafiyarsu tai jigum ganin zaman ya isheta kuma gashi batai sallar isha'ee ba yasa tamike tana yaye lullubin alkyabbar nata. tatsaya tana karewa babban gari guda din da ake kira matsayin dakin EHSAAS din aranta tace "this room is too huge for just the two of us tunda take bata taba ganin daki me girmansa ba,Fentin bangon dakin anyi shine da white satin paint mai ɗaukar ido, tare da hand-carved gold leaf moldings da aka kawo daga Florence, Italy. Ceiling ɗin kuma yana da 24-karat gold detailing tare da chandelier na Baccarat crystal wanda aka rataye a tsakiyar dakin, wannan chandelier ɗin yana dauke da fitilu fiyeda dari da ke canza launi gwargwadon yanayin dakin.

Tsakiyar dakin wani babban California King-size bed ne da aka ƙera da Italian mahogany wood da aka zana da hannu. An rufe gadon da hand-stitched Egyptian cotton sheets (1,500 thread count), tare da lafiyayyun goose-down pillows masu sanyaya jiki. Headboard ɗin gadon na da built-in massage system, da kuma voice-activated mood lighting a cikinsa wanda zasu iya sarrafa ta da muryarsu.Kasan dakin an shimfiɗe shi da Italian white marble with underfloor heating, sannan a tsakiyar dakin akwai wani babban Persian silk carpet wanda aka ƙera na musamman don Ehsaas da tambarin kasar Nuristan a jiki.

Bangaren wardrobe kuma ya kasance wani walk-in closet ne mai girma da aka raba gida biyu: ɗaya don kayansa na alfarma na yau da kullum, ɗaya don royal regalia da kayan yaki. Shelves ɗin da drawers ɗin an gina su da rosewood and ivory finish, sannan suna da automated rotation system don sauƙin zaɓi. Dakin yana da floor-to-ceiling soundproof glass walls da ke kallon farfajiyar Garden din sashen nasu. Balconynsa an zagaye shi da onyx stone balustrade, tare da heated outdoor sofa da ke kallon ruwa na infinity fountain. Sannan bangaren kamshi kuma Ana amfani da automated scent diffusers da ke fitar da oud, rose damascena, and sandalwood, da kuma LED underlighting da ke bada soft ambience. "Wow" Islam tafurta lokacin data bude bathroom dinsa. Shikanshi bayin abin kallone gashinan kato gari guda shikansa bangon an yi shi ne da onyx marble walls, wanda ke haskakawa da fitilar cikinsa. onyx marble ɗin yana glowing softly musamman yanzun daya kasance darene, yana baiwa bayin wani kamannin dreamy spa sanctuary. Ceiling ɗin kuma yana da skylight da za a iya buɗewa da rufewa domin shigar da hasken rana da iska mai sanyi. A tsakiyar bayin akwai custom-made solid gold freestanding bathtub da aka kawo daga Paris, a one-of-a-kind piece.An kewaye shi da petals na furanni masu ƙamshi da scented floating candles. Gefe guda kuma akwai 7-nozzle jacuzzi mai hydro-massage system, tare da aromatherapy mist release, da kuma underwater LED color lights waɗanda ke daidaita launin ruwa bisa yanayin zuciya da motsin jiki. An ɗora wani babban rainfall shower a tsakiyar wani sashe na bayin wanda ke zubar da ruwa kamar ruwan sama daga saman gold-plated panel din. Bayan bangon shower ɗin akwai private steam room da aka saka Eucalyptus-scented stone walls, domin nitsuwa da fitar da gajiya.

Gefe guda kuma an gina double vanity sinks da aka ƙera daga Italian Carrara marble. Faucet ɗin suna da touchless gold sensors, da kuma LED smart mirror da ke bayyanar da weather, time, skincare reminders, da kuma voice assistant domin bawa EHSAAS shawarwari.imagine duniya tana gurin masu kudi fa da masu mulki,shikansa part din Wurin zama domin yin bayan gida ba irin na kowa ba ne, Japanese smart toilet ne, wanda ke da heated seat, automatic lid, self-cleaning system, da kuma built-in fragrance diffuser. An sakaya shi cikin wani private alcove tare da art wall da digital call button incase idan yana buƙatar wani abu.

Se kuma storage da extras inda aka ajje towel warmer drawers cike da Turkish cotton robes da luxury towels. Se Sashin perfumes & skincare station wanda ke da tarin Oud, Creed, Amouage, Tom Ford Private Blend da sauran turarruka masu daraja.

Bata tsaya wani kauyenci ba dake tazazzauna akasashen waje tasassan yadda ake amfani da ire iren abubuwann alwala kawai ta dauro tafito asaman lallausan carpet din dakin ta tayar da Sallah tun kafinma ta idar tajiyo kamshin turarensa yacika mata hanci yana shigewa har cikin kirjinta. Anitse ta cigaba da sallarta harta idar,tashiga karanta azhkar zuciyarta na bugawa sanin idanuwansa na kanta gashi tama rasa ta inda zata iya hada ido dashi sonshi nafizgar ta kalleshi amman kuma tana tsoron kada tazake abinda mimah tafada ya tabbata. jinsa tai yasakko ya zauna akusada da ita harta kammala tashafa bata dago takalleshi ba tacigaba da kallon kasa abinta. cikin murya mai sanyi yace "mata muyi nafila raka'a biyu baby" bata musa mishiba yamike dake carpet din sabone galgal yauma aka shimfida sa be wani damuba yajata suka yi sallar. cikin nutsuwa suna idarwa tanaji yana jero addu'o i afili tana ansawa da Ameen acikin ranta dukda batasan me yake cewa ba yadau lokaci mai tsayi yana adduar kafin ya kammala yajuyo yana facing dinta kasa kallonshi tai. se taji karar sautin murmushin sa cikeda nutsuwa kafin yace "wannan new peace ce haka nidai babyana dana sani mijinta yazo zuwa zatai ta rungumeshi tana mai oyoyo ba taita durkusar dakai kasa ba"

shiru tai bata cemai komaiba jin haka yasan kunya takeji,yace "nibari namata oyoyon ko come here baby sit on my lap" yawani jawota yana hadawa da jikinshi, yadaura ta saman lap dinshi. wani irin nishi suka sauke daga shi har ita, ta kife kanta akirjinsa wllh tana mugu mugun son ya ringa mata irin wadannan abubuwan amman abinda mimah tace mata yaki barin kanta,cikin kunnanta taji yana fadin "pipi na yau rowar fuskar akemin baza'a bari ingani ba uhm?" jinjina mishi kai tai tanason taraba jikinta dake gogar nashi daya haifar mata da wata mahaukaciyar kasala,tasoma kici kicin kwacewa dagata yay cancarakas yana mikewa tsaye don baya jin nauyinta kwata kwata.

saman gadon ya ajjeta yana fadin "pipi naga alamar baki kewana kamar yadda nai kewarki ba ko, come on help me remove this clothes kinjiiiiiiii "yakarasa cikin wani irin slow voice dake sending chills jikinta yana mika mata hannunshi kin karba tai tana wani kifi kifi da ido. seyay rolling eyes dinsa yana mikar da ita tsaye kamar wata yar tsana bata ankaraba kawai taji yafara cire mata alkyabbar jikinta ta rintse ido,har yagama takasa hanashi sexy hot fitted gown din dake jikinta yabi dukkanin shape din jikinta ya kebi da kallo kafin yay gyaran murya yana matsowa daf da ita trying hard su hada ido sbd yasan kalar yadda idanuwansa keda mugun tasiri akanta amman taki kwata kwata.

ganin kamar gaba daya atsorace take yasa ya kamo hannayenta suka dawo saman couch din dake ta dayan gefen dakin mai mugun laushi ya janyota jikinshi ta gefen kujerar taga ya danna wani abu in few seconds taji kofar na announcing zuwan personal maid dinshi Aarah. mikewa yay yadan ja hancinta kadan yana fadin "I'll be right back baby," kicin kicin tai da ido sbd tasan sunan Aarah na mace ne kuma ita battason duk wasu bayi mata a inda yake," dan wara ido yay se kuma ya saki murmushi kafin yace "is traditional warm milk ne takawo da dates nakine nakeson inje inkarba kinga ke amaryane bazaki je da kanki ba yau ke tawace ni kadai bame kallar min ke kidena kishi mana" yafada yana hada goshinsu guri guda yana murmushi kasa kasa,turo baki gaba tai yana jinta tana kunkuni ciki ciki amman dai beji komaiba ya mike ya karasa bakin kofar duk yadda take leka wiya taga wacece Aarah din batai nasarar ganinta ba saboda daga inda take zuwa bakin kofar akwai tazara.

tahowa taga yayi walking majestically da wani hadadden glass da madara aciki mai kauri da wani small bowl da yake transparent me dan murfi ta hango dates din aciki samanshi se wani small cup.

ajjewa yay agabanta saman wani haddden table yana fadin "My royal Highness nadawo" kasa tai da kanta yashiga zuba mata warm milk din a cup kuma har lokacin be bar kallonta ba duk tabi ta tsargu. "come" yafada yana matso da ita jikinsa yace "baby haaa," kin bude bakin tai yace "dura kikeso inmiki koh" dan fara mishi ido tai daya kara daskarar dashi agurin yace "uhm sake abinda kikai yanzun just now pls," kmr batasan metai ba innocently tawani ce "ni menai," yace "Holy fuck that thing you just did with your eyes, just do it again baby" kinyi tai,tace "niba abinda nai," dage gira daya yay sama yana fadin "Zanrame tohm tunda karya nai kenan koh?" cikin sigar tambaya murmushi tai tashiga girgiza kai kamar wata kadangaruwa tana fadin "nidai banfa ceba uhm," "have some milk" ya fada yana kai madarar bakinta yar kadan tasha ta ture cup din,yace "kinajin yunwa" girgiza mishi kai tashiga yi "uhmmm uhmmm" yace "kin tabbata" Ta jinjina kai date din yadauka yasaka abakinsa yasoma taunawa ahankali bata ankara ba kawai taji ya hade bakinsa da nata cikin wani irin salo yana juye date din daya gama taunawa abakinsa cikin nata duk yadda taso ya saketa kiyay harseda ta hadiye dates dinnan tanajin jikinta baki daya yadau rawa lokaci guda.

Se dayay me isarshi sannan ya saketa yana zame royal scarf din dake kanta,gashinta me tsayi mai laushi baki sidik dashi yabayyana an nade mata shi cikin wani dan karamin net a keyarta zare net din yay yana jefarwa agefe, yazube agadon bayanta. ahankali yadebo sumar gashinta da hannunshi yakai saitin hancinshi yashaki kamshin da yake fitowa daga jikinshi da ya dada kunna shi kafin gently yasaki gashin, yay cupping face dinta gently yadaura goshinshi kan nata wani kalan kwarjini na musamman yau yake mata she couldn't bring kanta takalli kwayar idanunshi, runtse idanunta tayi gam gam dasauri tareda fashewa da wani kalan helpless kuka mara sauti, sbd tafarajin tsoro "what if in mgnr mimah ya tabbata in EHSAAS ya gama da ita yadena sonta?" ganin tana kuka ya dago Ahankali cikin dan mamaki da tashin hankali yake fadin "Why are you crying, baby? Did I hurt you?"

Ta girgiza kai cikin rawar murya tana shashsheqa "No... No, you didn't hurt me. I just...." Sai kuma ta shige cikin kirjinsa tai burying face dinta aciki, muryarta na rawa, "I love you more than my life, Sire... but I'm scared."

Scared of what, love?" Ya tambaya yana shafa bayanta da hannu daya,cikeda kulawa "What if... what if after tonight, after you have me, you realize I'm not enough? What if you fall out of love and marry someone else... like they all do?"

EHSAAS ya yi shiru na kankanin lokaci,kafin ya dagota daga jikinsa ahankali yana tinanin waye yafada mata wannan mgnr yasan wannan ba kalar tinanin da peace dinshi zatai bane ba, "Who told you that nonsense?" ya tambaya cikin sanyi, yana kokarin kallon cikin idonta. sanin bazata iya fada masa wacca ta sanar da ita hakanba yasa ta kau da kai don tasan intai karya yana ganewa, hawaye suka ci gaba da zubowa,cikin shagwaba tace "No one… it's just… my fears." Yadda tafada kadai ya tabbatar masa dacewa wanine yakeson brainwashing dinta tabbas se yasa ido akan wadanda zata ringa mu' amala dasu acikin gidannan,don kwata kwata bema kawo yar uwarsa mimah zata iya wannan aikin ba. Daura goshinsa yay saman nata yana fadin "Tell me baby waye yafada miki?" Ya sake tambaya cikin lallabi Make mishi kafada tai tana sake jaddada mai ita bakowa,sanin bazata fadaba din yasa yace "Islam… listen to me. You're not here to be used. You're here to be loved, honoured, protected… forever. I didn't choose you for a night. I chose you for a lifetime." Ya kamo hannunta duka biyun yana fadin: "You are the only woman I want to see when I wake up and the only one I want to hold at night. You are my forever."

Islam ta kai kallon gare shi cikeda kuruciya, tana kokarin fahimtar gaskiyar sa,tace "You promise me you won't leave me… even when I'm no longer beautiful… or when I annoy you?"

EHSAAS ya dan murmusa, yana kamo fuskarta yashiga goge mata hawayen da daya kebin daya yana fadin

"You'll always be the most beautiful woman to me. Even with gray hair, even when you frown. I love you for your heart, Islam… not for your skin. Your beauty is eternal to me."

Yasake rungumeta yana kai bakinsa sama kunnanta,ya ce: "Wallahi, I swear by Allah who made you and brought you to me, you will never know the pain of loneliness, because I'll never leave you. Never..Sedai idan babu rai ajikina"

Islam ta jingina da kirjinsa, numfashinta na sauka da ahankali ahankali saboda nutsuwar da kalamanta suka haifar mishi,Sai ta ce cikin murya mai sanyi

"I trust you Sire,… I just don't want to be hurt."

"And I'll spend my whole life proving you never will be." Ya ce yana sakar mata kiss a goshinta, sannan ya matseta cikin kirjinsa.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote [13/06, 13:01] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

Follow my Instagram page @fatoumspassion It's fatoumspassion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE