Chapter 35
Mehtav ce a gaba, Islam ta makale a bayanta tana satar kallon Abraham da ya kafawa Jr ido dake hannun Mehtav ɗin. Ita kanta Mehtav sai da ta dan girgiza da kallon Abraham ɗin saboda yadda fuskarsa da yanayin zubinsa suka nuna cewar babu wasa a tattare da shi. Kuma he looks very young, bata yi expecting zai kasance kamar haka ba.
Ganin sun yi turus, babu wanda ya karaso, gun sa ya kalli Islam, fuskarsa a dan hade yace, "My grandson" yana nuna Jr dake hannayen Mehtav yana ta wasansa da dankwalinta.
Jinjina kai Islam tayi tana jin kirjinta na bugawa. Wani irin murmushi yayi wanda rabon da taga yayi sa a rayuwarta har ta manta. Ya tashi yana karasowa gurin Mehtav, karbarsa yayi. Duk suka tsaya suna kallonsa. Ya dagashi sama yana dan jujjuyawa, kafin ya kalli Islam for the first time ya ce, "He's so cute, hasken grandmother dinsa ya ɗauko." Don ya kasa admitting a zuciyarsa cewa kamannin yaron da na EHSAAS ne - makiyinsa.
Jiyay yana son yaron kuma zai riƙe shi, tunda dai jininshi ne. Kuma yadda EHSAAS yayi nasarar kwace Islam daga hannunsa, shi ma zai kwace ɗan nan daga masarautar NURISTAN. Kuma ya taso a matsayin babban malamin addinin Kiristanci - shine kudurinsa, sannan sai ya maida 'yarsa addininsa.
Jr ba mai wani kiwaba because Abraham is good with kids. Saboda in ya je evangelism yakan siye zuciyar iyaye ta hanyar yayansu.
Mehtav ganin ya koma ya zauna da Jr a hannunsa, ta kalli Islam alamar kar ta damu. Tana nan, babu abinda zai yi mata. Kallon agogo Abraham yayi yana cewa mata, "They have a flight to catch, taje ta haɗa musu kaya ta fito." Ita da tasan bata zo da wasu kaya ba, komawa ɗaki tayi Mehtav don kar ma ya tafi da yaron kawai. Ta samu guri ta zauna a falon.
Har Islam taje tayi wanka a gaggauce ta fito, duk yadda Mehtav ta ce da ita ta sha ko tea ne da ta haɗa mata, ƙasa tayi. Hankalinta kawai yana kan ɗakin EHSAAS.
Ganin haka ya sa Mehtav ta ce ma Taj ya zauna anan tare da Abraham, za su je su dawo daga ɗakin EHSAAS. Suka shiga a tare.
Mamakine ya kama su duka ganin shi zaune, Abeey a gefensa tana ta zuba mai surutu, amma da alama hankalinsa gaba ɗaya ma yayi wani gurin, ba ya jin me take cewa. Gaba ɗayansu kallonsa suke cike da shauƙi da ƙaunarsa da ta rigada ta gama kashe musu zuciya.
Mehtav ta kasa yarda ta haɗa ido da shi. Bata san ya farka ba. Da tasan ya farka ba zata shiga ba saboda kunyar abin da tayi masa.
Da gudu Islam ta ƙarasa inda yake tana faɗawa jikinshi, ta fashe masa da wani irin raunaṭaççen kuka tana kiran sunansa. Shafa kanta taga ya shiga yi ba tare da yayi hugging ɗinta back ba. Bata damu ba, ta dago tana cupping face ɗinsa cike da damuwa ta fara faɗin:
"I thought… I thought I lost you. Sire, please don't leave me again, I'll die without you."
A hankali ya shiga kallon cikin idonta for the first time yau. Ta kasa karantar impression ɗin da ke fuskarsa. Kallon cikinta taga yanayi kamar me neman wani abu kafin a hankali ya buɗe baki yace mata:
"Is she okay?"
Da sauri ta jinjina masa kai tana wani irin murmushi wanda tun da Mehtav da Abeey suke, ba su ga tayi shi a gidan ba.
Yace: "And the baby?"
Kallon Mehtav tayi. Da sauri Mehtav tace:
"I'll bring the baby,"
Saboda wani iri-iri take ji a ranta - farin ciki na reunion ɗin couple ɗin da kuma daɗin rasa EHSAAS da tasan tayi har abada.
Amma me? Mamakine ya kama ta ganin EHSAAS ya riko hannunta a hankali yana hanata tafiya. Ya kalli Islam yana kasa haɗa ido da ita yace:
"Bring the baby, zan yi magana da ita."
Cikin Mehtav ne ya ɗuri ruwa sanin cewa ya ganta tana dura masa allura. Ba dai ya tsaneta ba? Ba dai zaginta zai yi ba?
Yace: "Ta rabu da shi da iyalinsa ba."
Itakam ta shiga uku.
Islam sakatoto tayi tana kallonsa, ta ma kasa motsi a gurin. Mehtav tayi saurin girgiza kai tana faɗin:
"I'll bring the baby."
Wannan karan fizgota yayi ta zauna a gefensa na hagu, inda Islam take a gefensa na dama. Ya juyo ga Islam yana faɗin:
"Bring the baby," with authoritative voice din da tasan in yayi magana, ba da wasa yake ba.
A ranat tunani ta soma yi - ko dai ba ta ne ba? Ko dai ya sake manta wani abu ne a cikin kwakwalwarsa?
Haka ta miƙe da waswasi, sanin Abraham ba lallai ya ba ta yaron ba. Ta fito falon tana kallon yadda yayi focusing akan Jr.
Cikin wayo tace masa ai zata je ta canza masa diaper ne, ya cika. Abraham ba don ya so ba ya bata Jr. Ta nufi ɗakin EHSAAS cike da zulumi.
Abraham ba don ya so ba ya bata Jr, ta nufi ɗakin EHSAAS cike da zullumi - anya kwakwalwarsa ba ta tabbu ba kuwa? Ita yake wa magana haka?
Kofa murnar ganinta bai yi ba, and he didn't hug her back data yi hugging nasa. First time da ya tashi, ai ita ya fara nema. Yagani ko allurar ta bugi brain dinsa ne again?
Abeey kawai ta gani a ɗakin tana ƙoƙarin karkaɗe gadon da ya tashi yanzu. Ta tsaya, kirjinta na bugawa tana tambayar Abeey:
> "Ina yake?"
"Toilet," ta nuna mata.
Kasa-kasa take jin motsi, kirjinta na bugawa. Ta ƙarasa toilet ɗin da ba su gama rufe wa ba. Tatura, bathrobe ce a jikinsa saboda rashin ƙarfin jikinsa har yanzu. Mehtav tayi supporting dinsa, ya dafa kafadarta yana brush.
Kallonsu ta tsaya yi, zuciyarta na bugawa kamar zai fito. Gani tayi ya kafa ma Jr ido, ya ƙi ɗauke kansa daga kan yaron har ya gama brush dinsa. Ita kuma idonta ya kasa ɗaukewa daga yadda ya riƙe Mehtav. A iya saninta ita ce matarsa, don haka idan freshening up yake buƙata, ita zai saka ba Mehtav ba.
Tabbas ta ƙara gasgata cewa kwakwalwarsa ba ta daidai.
Dan sakinta Mehtav yayi, yana dan taku a hankali yana dafe bango. Ya ƙarasa gurin Islam ba tare da ya kalleta ba, ya sa hannu yana karɓar Jr. Wani irin lumshe ido yayi, yana buɗewa - taga idanuwansa sun yi jajir kamar garwashi. Ta kasa karanta impression dinsa kwata-kwata.
Kiss taga ya manna mai a goshinsa, ya rungume shi a kirjinsa na tsawon mintuna. Mehtav dai ta wuce ta haɗa mai ruwan wankan da ya buƙata kamar yadda ta saba.
Ganin ta gama, yasa ya miƙa wa Islam ɗan tayi mamaki, ba be tambayi sunansa ba.
Wata irin ƙwalla ce me ɗumi ta zo mata fuska. Ganin ya juya gurin Mehtav ya mata alamu da hannu akan ta cire mai bathrobe ɗin, kallon Islam tayi. Ita kanta she's confused akan abin da yake yi. Ranta kuma na ta raya mata ko dai kwakwalwarsa bata dawo daidai ba ne?
Tana tsoron tai wani action ɗin da zai saka shi a haɗari. Ganin ta ƙi ta taimaka masa, ya sake langabewa yana faɗin:
> "Plsss…"
Kallon Islam tayi da tayi saurin ficewa a bathroom ɗin ta bar su.
Ɗakin ta bari baki ɗaya, ta wuce ɗakinsu Jr. Kawai tayi masa wanka, ta sa Abeey ta ɗauko masa kayan da aka wanke, ta saka masa, ta shirya shi. Ta goye shi kamar yadda Nurae ta goya mata shi wancan ranar a asibiti. Ta fito tana kallon Abraham ɗin da ya gaji da shige da ficen nasu.
Inna ta kawo masa 'yan snacks, ya ƙi cin komai - shi dai yana zaman jiran ta gama tafito su tafi. Abinda yasa ya ɗaga mata kafa, ma'anar flight dinsu na yamma ne, ko sun tafi yanzu, sai sun jira sosai a airport.
Inna ba wani turanci kirki ta iya ba. Tana daiji kuma tana son ta yi wa Abraham magana, ba fuska. Ta zauna tana ta kallonsa kamar gunki. Lokacin Azahar ya yi, Taj ya fita mosque. Tace masa:
> "Kai bawan Allah, ba ka sallah ne ba? Ba za ka fita ka yi ba?"
Banza yayi mata, kamar ma bai san me take cewa ba. Tace:
> "Ikon Allah, kato da kai, ka ji kiran sallah, sai a ce maka ka je ka yi!"
Nan ma banza yayi mata. Ta miƙe tana bambami, ta tafi ɗakinsu Mehtav inda ta tarar da Islam ta idar da tata sallar, tana goye da Jr, ta kafa kai da gwiwa, se kuka take kamar ranta zai fita.
Cike da kulawa Inna ta shiga tambayarta:
> "Meya same ki?"
Girgiza mata kai kawai tayi tana goge hawayenta. Tace:
> "Ba komai."
Tace:
> "Yar nan, ya za ki ce min ba komai? Ko dai tafiyar ce ba kya son yi? Ki bar mu? Na san akwai sabo, amma ai dai kin san duk tsiya sai kin koma ƙasarki, ko?"
Jinjina mata kai Islam tayi. Tace:
> "Don haka ki cire damuwar komai a ranki. In dai mu ne, za mu riƙa kawo miki ziyara akai-akai. Habibu na da kuɗi, zai iya biya mana kuɗin jirgi duka. Kuma… kuma in kun je, kada ku manta da alheranmu a gare ku."
> "A toh, na ji an ce kuna da sarauta - a kirani a karamta ni."
Sai a lokacin Islam ta yi murmushi, tana faɗin:
> "In shaa Allah, ba za mu manta da ke ba."
Inna ta washe baki tana faɗin:
> "Tohm! Taso mu je. Da ma karar wancan mutumin mai kama da ke na falo na kawo miki ba fa ya sallah. Ana ta sallah a masallaci, nayi-nayi ya je yayi, ya maidani yar iska yaki tashi."
Sosai Islam taji kunyar bude baki ta ce mata mahaifinta ba Musulmi bane. Sai tace mata:
> "Ki yi haƙuri, zan yi masa magana - kila ko ba da alwala bane."
Fitowa falo suka yi. Abraham ya miƙe yana faɗin:
> "Thank God. You're done, right? Shall we?"
Ya faɗa yana ajiye wani envelope mai ɗauke da cheque da ya rubuta wa Tajuddeen - wasu jahilan kuɗade kyauta, a matsayin taimakawa yarsa da yayi.
Inna tace:
> "Kaiko ɗan nan, ai ka tsaya, ka bari maigidan ya dawo ku yi sallama. Kuma ina za ka kai ta? Shi mijin nata fa?"
Bai tsaya sauraron Inna ba, ya ƙarasa yana kama hannayenta, ya sa cikin nashi yana faɗin:
> "Thank you for your help, mam. Zamu wuce kawai."
Taku biyu kacal suka yi, Islam ta caka ta ƙi yarda ta haɗa ido da shi. Ya juyo yana ba ta wani banzan kallo, daidai Taj da paa suna shigowa daga masallaci. Yace:
> "Peace… let's go."
Hawaye ne suka soma sauka a idanuwanta kafin ta soma girgiza masa kai. Tace:
> "I'm sorry Sir. Ba zan iya zuwa ko ina ba tare da mijina ba."
Cike da mamaki da kaɗuwa yake kallonta, tunanin ko ta haukace. Yace mata:
> "Wane mijinki kuma?"
Kanta a ƙasa, tace:
> "EHSAAS."
Wata irin bazawarar dariya yayi yana tambayarta:
> "Ko kabarinsa za ki bi ne?"
Girgiza masa kai tayi tana faɗin:
> "He is not dead, Sir. Akwai misunderstanding. Al'amarin yanzu ma haka yana cikin gidannan, Sir."
Sakin hannayenta yayi, ya juya ga Taj alamar yana neman ba'asi. Taj da bai san maganar da suka yi ba, bai ba shi amsa ba.
Abeey ce ta fara fitowa daga ɗakin EHSAAS tana faɗin:
> "Tadaaaaa! Inna! Paa! Taj! Ga babban surprise! Munkawo muku mun shirya muku handsome Islam ɗinmu cikin native attire da aka ɗinka mai na biki!"
Mehtav ce tare da shi suka fito. Yana takowa a hankali saboda kansa da yayi masa nauyi. Yasoma tai supporting dinsa, kitai - don tana ganin hakan kamar cin fuska ne ga Islam ɗin.
Abraham Zion ware ido yay yana kallon EHSAAS, dashi ma ya kafeshi da ido yana kallo. Da sauri Islam ta ƙarasa ganin kamar tafiyar da ƙyar yake yi, zata taimaka mai. Dan ɗaga mata hannaye yay alamar ze iya, tai turus tana kallonsa har ya ƙarasa ya zauna saman sofa.
Aura ɗin shi ta yau daban take domin shi kansa paa yaga yayi mai wani irin mugun ƙwarjini cikin yadi mai laushi da ya saka. Ya haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana fadin:
> "Kowa ya zauna."
Basu musa masa ba, kowa ya samu guri ya zauna. Abraham kasa zama yay, yana kallon yaron da aka ce ya mutu a gabansa kenan.
> "Bala'in rayuwarsa be kare ba wannan, wane iri shegen yaro ne da ba ze barni in huta ba?"
Ya raya a ransa.
EHSAAS cike da nan aji da miskilanci yake fadin:
> "Daddy ko ka fi son tsayuwar banza?"
Yay masa yana kallon Islam yace:
> "I don't care about him being alive, abu daya nasani yadda kika daga waya kika kirani kika hanani sakat, baki san hanyoyi da nabi gurin samun shigowa kasar nan ba, kike tinanin zan barki? Baki isa ba. It's either ki biyoni ta cikin sauki ko kuma da karfi zan kwace jikata a hannunki domin ba zan bari shima ya taso a gurin non-believer ba."
Yafada yana nuna EHSAAS da yatsa dayake mai wani irin kallo da ba zaka iya fassarawa ba.
Islam dake gefen EHSAAS ƙara shigewa gefensa tai tana makaleshi alamar ba zata bishi ba.
Abraham, cike da bala'i yake fadin:
> "EHSAAS bar ganin prince ne kai, Nigeria ba NURISTAN ba ne. Baka isa ka hanani tafiya da yata ba da take wani makale maka anan. Ko ki biyoni ko kiga otherside of me a yau ɗinnan. Yarinya ta kirani tana kuka zaku kasheta sanda tana bukatarka, ina kake? Sai yanzu ne zaka dawo don kaga zata gyara alakarta da mahaifinta? Kai wane irin sheda ne ne EHSAAS?"
EHSAAS, dan yamutsa fuska yay yana kallon Abraham, yanun mai Islam, yana dan matsawa daga kusa da ita yace:
> "Come and take her, ko ni na hanaka ne?"
A zabure Islam ta dago tana kallonshi. Yajuyar da kansa yana fadin:
> "She's your daughter and the baby is your grandson. Babu wanda ya isa ya hanaka daukarsu, amman kuma nima kasan matata ce da dana ko."
Abraham yace:
> "I don't care about your marriage, akwai wani aure daman tsakanin zuriyata da known believer."
EHSAAS yace:
> "For the first time nima I agree with you, nima I'm tired. Just take her and go far away from NURISTAN."
Abraham kanshi sakin baki yay yana kallon EHSAAS saboda beyi expecting that kind of answer ba.
Yace:
> "Kace in dauketa?"
Yace:
> "Of course, I don't wanna see her again saboda zan kara aure ne. Look at my would-be wife."
Yafada yana nuna Mehtav dake gefen hannun kujerar paa da birkice ta dago tana kallonshi. Magana yake amman kwata-kwata bazaka dauka daga bakinshi tafito ba.
Abraham yawani tafa hannu yana kallon Islam yace:
> "Peace did you just hear abinda yace? In dauke ki, mu tafi. He is re-marrying. Did you just hear that? Ya tashi daga mutuwa memakon ya nemeki, ya koma ga iyayensa. Ashe shi aure yakeso yayi. Shiyasa ya ki nunawa kowa yana da rai. Did you see what I've been telling you akan Muslims kika ki yarda?"
Jr ne yasoma kuka abayanta, jitai gaba ɗaya kunnenta ya toshe kamar ma ta daina sauraron komai tun da EHSAAS yafara gargaɗawa babanta magana, kancewar ya tafi da ita, shima ya gaji.
Sakko Jr tai, ta rungume shi a kirji, ta shiga lallaɓinsa, hawaye na bin idonta. Ta kalli Mehtav tana faɗin: "He don't remember me… just call the doctor."
Ta sake dubashi, ta ƙarasa tana miƙewa zata bar gurin, taji EHSAAS ya rikota, yana miƙewa tsaye. Facing juna sukai, idanuwanta cikeda tsoron abinda zefito daga bakinsa take faɗin: "Sire, you're sick. Ka daina magana haka, kanka zeyi ciwo. I'll pray for you. Allah zey baka lafiya, don't worry kaji."
Tasa hannunta ɗaya tana shafa gefen beard ɗinsa cikeda son kwantarwa da kanta hankali take faɗin: "I'll wait for you okay? Harse kayi recovering ka tuna wacece ni. I'll take you to Maama - she will be the most happiest in tasan kana Raye."
Seda ta gama sannan ya ciro hannunta cikin nasa, idanuwansa sunyi jajir yace mata: "I remember you. I remember everything about us. You are Peace - the girl I met in Oxford, the confused girl with piercing eyes, the gentlewoman I loved with my whole life. I still remember everything Islam - our friendship, our marriage, our life, the pregnancy and even the accident."
Cikin tsawa ta fizge hannunta cikin nashi tana faɗin: "And how dare you speak like that? Ka ce in bi babana? Kaima kagaji? Ka ce zakai aure? Do I even care about your marriage? Sire, this is not you! Why on earth won't you fight for me? And if I leave you here, what about Maama? What about NURISTAN?"
A nitse yadago yana faɗin: "I wanna move on from my past and start afresh. This is my new home, my new family. And I'm not going back to NURISTAN anywhere soon… maybe after my marriage." Yafada yana ɗauke ido daga kanta.
Wani irin suka kirjinta yake in ta jishi yana cewa marriage ɗinnan, cikeda baƙar zuciya da taurin rai tace: "Fine. Congratulations on your wedding, prince. Enjoy."
Hanya tanufa zata fita, Mehtav tashiga gabanta tana faɗin: "No, don't go pls. Karki yanke hukunci cikin fushi. Nima nayarda he is not okay."
Don't forget to Share Comment Like & Vote. [20/06, 21:02] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
Not edited
It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.