Chapter 36
"Then help him," kalmomin da suka fito daga bakina kenan, bayan Mehtav ta gama rokona kan cewa itama ta yarda ba kalau yake ba. Ni nasan kalau yake, saboda babu yadda za a yi ya iya manta rayuwar da muka yi a Oxford kuma a ce min ba kalau yake ba in yarda.
Ban san yadda aka yi na fice daga falon ba. Ban san yadda na sauko daga stairs ɗin gurin ba. Amma na san na fita da Jr a jikina, zuciyata na min wani irin nauyi da radadi wanda tun da nake a rayuwata ban taɓa jin irinsa ba - wani irin ciwo ne da ba zan iya fassara muku shi ba.
Kafafuwana tafiya suke kawai, ba tare da nasan ina nake jefasu ba.
Wai yau my Sire, my EHSAAS, my husband, and my best friend - wanda a ba ce min ni ce "peace" ɗinsa ne - ya kalleni yana faɗa min he's marrying someone else. Ya ce he's staying here. Ya ce I should go with my father.
Kijina'i kamar nauyin duk duniyar nan aka ɗaura min a saman kirjina. Kishinsa na neman halaka, duk suna wani ƙwarin gwiwar da nake dashi a kansa.
Ina jin tafiyar babana a bayana yana mita, trying to prove his point cewa he was always right about EHSAAS from the beginning. Muryarsa ta karade ko'ina yana masifa:
"Na gaya miki Peace! Na faɗa miki tun farko cewa ba zai kare da kyau ba. Kin ƙi ji. Kin tafi kin auri ɗan sarki saboda soyayya! Kin raina shawarar mahaifinki! Yanzu ga shi-ya kore ki kamar wata mara daraja!"
Kalaman Abraham Zion jinsu take tamkar ana soka mata wuka a kirji. Ta kasa iya maida mai da martani saboda ba ta san me za ta ce mai don ta kare EHSAAS a karo na ba adadi a gabansa ba.
Zuciyata na ta kawo dalilai da dama da EHSAAS zai ce in tafi tare da babana don kareshi, amma ta kasa kawo dalili ƙwarai wanda zai sa ya min irin wannan ƙorar a gaban macen da yake iƙirarin zai aura.
Why would you say that to me, Sire? Why would you look me in the eyes and say you're marrying someone else-without telling me why?
Wadannan tambayoyin su suke yawo a cikin zuciyar Islam tana girgiza kai kamar wacce ta soma zarewa.
Muryar Abeey ce ta katseta daga doguwar tunanin da ta tafi yi:
"Islam! Islam, please wait!"
Abeey ta shiga ƙwala mata kira tana tahowa, hakan ya sa Islam ta ƙara sauri tana karasawa gurin motar da taga Abraham ya buɗe mata gida baya. Ta saka Jr a ciki.
Sa'da ta ɗago taga ashe tare da Mehtav suke, idanuwanta yayi jajir kamar wacce ke shirin fashewa da kuka. Kwata-kwata ji tai ba ta son ganinta a gabanta.
Zata shiga mota taji Mehtav cike da rauni ta fashe da kuka tana faɗin
"He didn't mean it, maybe he is still sick!"
Saboda ta san EHSAAS ya farka lafiya, ta san kalmomin da ya faɗa ba cikin hauka ba ne. Amma zuciyarta ta kasa amincewa da maganar, ya zabe ta akan matarsa da ta sha gwagwarmaya a kansa. Tana jin kamar ita ce ta jawo wannan ruɗanin duka, amma kuma ta san cewa ko da EHSAAS zai aure ta, ba za ta taɓa jin daɗin wannan auren ba at the expense of another woman's happiness. She's not that cruel. Ta yaya za ta fara rayuwa da shi bayan ta san irin son da Islam take masa ya fi nata?
"Please… don't go!" Ta faɗa tana ƙoƙarin ta riƙe mata hannu.
Amma me? Islam jan hannunta tai baya kamar wata wutace za ta tabata.
Mehtav tai saroro tana kallonta. Ta san dole dama Islam za ta tsaneta; abin zai mata ciwo.
"Ki saurare ni dan Allah, kar ki tafi a haka!"
Mehtav ta shiga kara rokonta wanda ta san ba lallai ne ta saurara ba, don ta lura Islam na da mugun taurin kai.
"Yana da kyau ki bar ni, Mehtav. Just go and focus on your wedding," Islam ta faɗa sarcastically, da wata irin dakakkiyar murya da ita kanta ba ta san tana da ita ba. "I'm sure EHSAAS will make a great husband. Just make sure he doesn't get into any more accidents."
Mehtav riƙe bakinta tai da hannu ɗaya tana kallonta, saboda ta gane irin maganar nan ce wadda ake gwabawa mutum tamkar cikin jin zafin abin da ya faru da ita. Hawaye ne suka soma bin idonta, don sosai taji tana tausayin Islam ɗin.
Abeey da sauri ta riƙe Islam tana faɗin, "No, no! Don't say that. Please don't say that! He loves you. Everyone knows that. There must be a reason. Yana tashi sunanki fa ya fara kira. I was with him, amma ke ya fara tambaya. Har nai kishi nace ai yah Mehtav ke kula da shi, me yasa me tambayeta? Ba se ke ba. Sai ya ce min wai ke ce rayuwarsa ce duka. Na ce masa 'Yah Mehtav fa?' and he said… he said… she's his wife."
Abeey ta karasa tana stammering. Kalmar wife ɗinnan ta ƙara dugunzuma zuciyar Islam. Wannan karon, kasa riƙe hawayenta tai - sirara masu ɗumi suka biyo kuncinta.
"Reason?" Ta murmusa da wani irin sarcastic smile mai tafiya da hawaye da Mehtav ba za ta taɓa mantawa ba. "Oh yes, there is always a reason. Sai dai wannan karon, it came with a bride. Congratulations again."
Ta karasa tana kallon Mehtav daidai lokacin da Abraham Zion na karasowa ɓangaren da suke yana kallon Mehtav da wani irin raini da tsana a fuskarsa.
Ya ce, "Ke, you better stop trying to convince her ta koma mai, because hakan ba za ta taɓa faruwa ba. If he wants her back, he should be here begging instead of ya turo ki, ke ma ɗaya shashsheƙar."
Ya karasa cikin daka-tsawa. Ko kaɗan Mehtav ba ta ji tsoronsa ba. Ta buɗe baki za tai magana cikin son mai bayani a kan me ke faruwa:
"Sir-" amma ya katseta da yatsansa a sama.
"Don't 'sir' me. You stood beside him. You helped him hide. You want to convince my daughter to believe in a man who has no dignity again? A man who threw away his wife like she was a mistake he regrets? Ke ma turn ɗinki na nan zuwa barnan ƙonai, ball dake."
Ya karasa faɗa yana juyawa kan Islam.
"Ke kuma, za ki shiga mota ne ko na tafi da jikina na bar ki anan gurin darling prince ɗinki, princess?" Ya faɗa da mocking tone da yasa Islam ba ta ce komai ba. Ta buɗe bayan motar, ta shiga, ta zauna a gefen da ta kwantar da Jr, wanda ya fara barci. Tai shiru kamar wata dolled corpse.
Tana ganin yadda Abraham ke wa Mehtav masifa, ba ta san me za ta ce mata ba, sai ganin Mehtav tai fuuuu, ta juya don komawa ciki. Abeey ce ta tsaya tana mata bye-bye, fuskarta duk ba daɗi. Da ƙyar ta ƙakalo murmushi, ita ma tai mata.
Daidai lokacin da Abraham Zion na shiga mota, driver ɗin da yazo da shi yay saurin tasowa daga gurin su, daga liti ya shiga, ya tada motar. Abraham sai mita yake yi har driver ya ja motar suka soma ficewa daga harabar gidan. Islam na jin kamar an rabata da rayuwarta ne baki ɗaya.
EHSAAS yana tsaye daga window ɗin falon, tare da Paa da Tajuddeen. Kallo suke yi kamar suna kallon drama. Amma EHSAAS shi kaɗai ya san me zuciyarsa take ciki. Yana ji a ransa, ko da ace Islam ta yafe masa wata rana kan abin nan da ya yi mata, shi ba zai taɓa yafewa kansa ba. He will make it up to her in dai Allah ya ba shi tsawon rai da zai ƙara kasancewa tare da ita.
Shi kansa ba ƙaramin rauni wannan furucin ya haifar masa a cikin zuciyarsa ba, amma abu ne da ya zama dole yayi, domin matsalolin da suke jiransa a NURISTAN ba za su bar shi ya zauna lafiya da ita ba. Kuma ba zai iya rayuwa yana kallonta cikin haɗari ba.
"If you don't want her… then give me her divorce paper," Tajuddeen ne ya yi breaking silence ɗin da wannan furucin nashi, yana kallon EHSAAS da hankalinsa gaba ɗaya is focused akan motar da ta riga ta fice daga compound ɗin gidan amma ya kasa dena kallon gurin.
Jin kalaman Taj ya sa ya juyo da kansa a hankali, yana kallonsa da wani irin kallo da ke cike da tsana, da raini, da jarabar da ba a iya fassarawa.
Irin how dare you ɗinnan ba tare da an faɗa ba, saboda she is his and she will forever belong to him.
Taj ba ya damu da mummunan kallon da EHSAAS ya jefesa da shi ba, ya ci gaba da faɗin:
"She deserves someone better. A woman who can love a man to the extent of leaving her family, her religion… she deserves to be worshipped. If you won't do it, I will."
Kallon da EHSAAS ya kafa masa wannan karon, kallo ne na if you don't shut up, I'll kill you.
Duk da ƙwarjinin da ya mugun yi wa Taj, ya cika masa ido, bai hana sa faɗin:
"Yes, I will do it. Just set her free. Zan bita duk inda take."
"Idan ka sake buɗe wannan kazamin bakin naka ka yi magana kan iyalina, I will cut off your throat!"
EHSAAS ya faɗa da muryar da tabbas Taj ya san ba wai barazana ba ce ba - zai iya aikatawa.
Ganin sun tsaya suna kallon juna kamar su kashe kansu ne, sai Paa ya ce: "Tajuddeen, je ka waje pls. Zan yi magana da shi."
Taj kallon EHSAAS ya yi, shima ransa a haɗe kamar yadda na EHSAAS ɗin yake, ya wuce kawai yana jin cewa duk girman kan da ke kan prince ɗin, sai ya sauke masa shi. Saboda a nan ɗin ba kingdom dinsa ba ne, kuma kome za a yi, wallahi ba zai taɓa bari ya auri Mehtav ba, tun da shi ji yake ya isa, zai yi abin da yake so a lokacin kuma da take so.
Fitar sa ke da wuya, Paa ya kalli EHSAAS cike da tausayawa, irin da yadda yake masa magana a can ɗin kafin hankalinsa ya dawo, ya dafa shi. Duk da shakkar da yake ji a zuciyarsa, dole ne ya faɗa masa abin da shima yake nasa ran.
"Why did you do it? Why, EHSAAS?"
EHSAAS ya daɗe bai ce komai ba. Daga ƙarshe, da muryarsa mai sanyi, ya ce: "Because I want her to live. To survive. I want her to be far away from the storm that's coming for me."
Paa ya girgiza kai, ya ce: "Amma you did it in the wrong way. Me yasa baka gaya mata hakan ba?"
EHSAAS, sighing ya yi deeply, kafin ya kalli Paa. Ya dan murmusa kaɗan, ya ce: "She's stubborn. Ba za ta tafi ba. Kuma yanzun ma ba wai ta tafi bane don ta yarda da duk abin da na faɗa. I just used her weak point. Na san Islam idan aka yi maganar kishi, she never thinks straight. That is why I used that - to protect her from everyone."
Paa ya daskare yana kallon shi, saboda babu abin da yake gani a ƙwayar idon EHSAAS da muryarsa sai tsantsar soyayyar da yake wa waccan yarinyar.
"Kana tunanin shi, mahaifinta, will give her enough protection?" Ya tambaya yana kallonsa. Jinjina kai EHSAAS ya yi yana faɗin: "He will hide her well. Saboda kar in sameta ko nan gaba. Kuma in dai ya boyeta a inda ni kaina ba zan sameta ba, babu wanda zai sameta - sai ni din."
Jinjina kai Paa ya yi, yana yaba hikima irin ta EHSAAS. Ya ce, "Kana sonta sosai da alama."
Dan kallo Paa ya yi kafin ya ce: "What I feel for her is beyond love. Ina fatan zaka taimaka mini kamar yadda kai a baya, ba tare da ka san ni wanene ba, ka bar ni na ci gaba da zama a tare da ku har se lokacin da ya dace in koma." Sannan kuma... ya ƙara da sosa keya.
Paa ya ce: "Kuma me?"
Ya ce: "Karka faɗa wa Mehtav wannan maganar. Pls, can we go on with the plan? Na ce wa aurenmu za a yi. Just let's keep organising everything. Zan ci gaba da shirina ni ma ta ƙarkashin ƙasa."
Girgiza kai Paa ya yi yana faɗin: "A'a fa EHSAAS, kar muyi haka da kai. Kaga yarinyata na sonka. Idan aka ce za a ci gaba da wannan wasan, she will fall deeply, kuma ka zo daga baya a fasa, ka karya mata zuciya. Gara ta sani kawai ba ka sonta, matarka kake so."
EHSAAS ya girgiza kai yana faɗin: "Pls, don't tell her. Bana son kowa ya sani. Kaga she's crying over what I did to her friend. Na san ba ma zara za ta ringa shiga sha'anina ba sosai. So let's just keep it that way. I'm pretty sure she hates me for what I did to Islam. Bana son na yi taking risk ɗin barinta ta sani - zata iya faɗa wa wancan." (yana referring to Taj).
Paa, ba don ya ji abin ya kwanta masa ba, kawai ya ce masa: "Toh, a'ishi kenan."
Dame zai iya taimaka masa? Farko dai, ya ce yana son wayar hannu da international SIM, sai kuma laptop sabuwa. Dalilin da Paa ya ce: "An gama."
Paa da kansa ya fita zuwa Apple store, ya siya masa, ya kawo masa. Kuma tabakin EHSAAS ɗinne gaba ɗaya; gani ya yi Mehtav ta fita a sabgarsa. Da sun haɗa ido, hararar sa take yi. Ma abin shi, dariya ma yake ba shi. Wai haushinsa take ji saboda abin da ya wa Islam.
Everything is fresh in his brain. Shi hakan ma yafi masa saboda yana jin kunyarta in ya tuna abubuwan da ya ringa mata lokacin da kwakwalwarsa ta kauce.
Kuma har yanzu suna mugun good time da Abeey. Yana nan, amma zuciyarsa tana ga tunanin in Islam ta wuce tare da mahaifinta, ko jirginsu ba kaiga tashiba.
Kamar Taj ya san tunanin da yake yi, ya yi sallama, ya shigo. Abeey ta tare shi da "Oyoyo", tana tambayarsa inda yake.
Anan yake sanar mata: "Ai airport na je, na tarar ma har jirginsu ya tashi. Ba na samu na yi magana da ita ba sosai."
EHSAAS ya ji daɗin wannan information ɗin da ya samu. Ya ɗau laptop ɗinsa, ya shige ɗaki kawai yana daddanawa.
Tun farkawarsa ta wayar Mehtav da Abeey ke wasa da ita, duk inda suke, ya san sun bazu a NURISTAN da kewaye nta.
Kuma yanzu yake shirin kiran Aman, duk da a wannan karon bai yi planning saka shi a cikin harkokinsa ko kaɗan ba, saboda yadda ya shirya yin rashin mutunci akan me uwa da wabi.
Saboda ya san abin da zai aikata din dole zai taɓa zuciyar Aman, one way or the other.
Bayanan sirri suke ta aiko masa da su akan abubuwan da suke faruwa. Ciki babu abin da ya fi raunata zuciyarsa da daga masa hankali irin kisan da aka yi wa kakarsa, har batan da suke tunanin matarsa tayi da ɗansa. Duk an sanar da shi.
A ransa ya gama shirya: gara su ci gaba da tunanin ta bace, na har zuwa lokacin da zan tarwatsa su ɗaya bayan ɗaya.
Kuma anan ya samu labarin kisan Jay, da aka mai da rashin lafiyar da Mai Martaba yake fama da ita.
Sati ɗaya cif yayi a cikin ɗaki yana shirya komai. Babu abin da yake fitowa da shi sai idan lokacin sallah yayi.
Kuma babu me zuwa inda yake sai Abeey - ita ce take kawo masa abinci wanda Mehtav ke hada mata.
Sai ta labe, ta sa ta kai masa. Saboda duk da fushin da take yi da shi, ta san ba za ta taɓa daina son shi ba deep down, har abada.
Musamman da Paa ya ce a ci gaba da shirye-shiryen bikin, kar a dakata.
Duk da she's feeling guilty, tana ji kamar ba ta yi wa Islam adalci ba - in ta aure mata miji.
Amma kuma tunawa da cewa EHSAAS ne ya zaɓe ta da kansa, sai hakan yake ƙara ba ta ƙarfin gwiwa akan cewa in su kai aure, za ta sa shi ya dawo da Islam, su rayu tare har abada.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to: Share Like Comment & Vote [21/06, 18:00] Fatima Rufa'i Nasidi: *** Follow me on all my social media handles @fatoumspassion
It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.