EHSAAS

Chapter 37

by @fatoumspassion

Paa, sanin cewa auren na gaibune, be wani yi taron gayya ba - kawai isu isu suke yin sha'aninsu a gida. Ita kanta Mehtav tana mamakin yadda Paa ya canza daga cewa za a yi grand wedding kawai, tafara d'aya yace mata simple wedding za a yi. Gaba ɗaya auren a baibai yazo musu.

Yaune Aka gayyato mai henna ta musamman ta musu lalle su su uku ita da Abeey da Inna. Tayi expecting EHSAAS daya shigo yatarar ana musu he will be irin excited to see it amman ganitai kmr ma abin bewani dadashi da kasaba,hakan kuma yatsaya mata arai sosai.

Tana tsaye ƙasan shower, ruwan ɗumin na dukan kanta, tasoma analyzing abubuwa da yawa da suka faru. Amma kuma ta kasa gane me hakan ke nufi musamman yadda EHSAAS bai taɓa tinkararta da batun maganar aure ba ko makamancin ta.

Tasan da fari dai, itace take avoiding dinsa, amma yanzu da kanta take zuwa inda yake, ta zauna ko zata samu ya yi mata maganar wani soyayya ko na aure, amma bai taɓa bata fuska ba. Impact: he is just treating her kamar yadda yake treating Abeey, abin na ci mata rai. Kullum yana kan system dinsa.

Kallon jan lallen hannayenta tayi, da yakiyin jaa sosai. Na kowa yayi jajir, yayi kyau, banda nata. Duk yadda aka zana mata shi, an zana, amma rashin yin jajir dinsa ya saka ba a ganin kyansa.

Tana tunawa yadda Abeey ke tsokanarta dazun, cewar angonta baya sonta, shiyasa henna dinta looks very weak.

Kuka ta saka tana rufe fuskarta da tafin hannunta. Wani abu na cake mata a tsakiyar kirjinta, tana jin kamar EHSAAS is just not into this marriage - kwata-kwata. Saboda ai Islam ta bata labarin aurensu, aiba haka yake ba. Yanuna zumudinsa akan abin sosai.

Amman me yasa ita akan nata yake nuna ko inkula sosai? Tasha kuka ita kadai a ƙasan shower kafin ta daure ta ƙarasa wankan, ta ɗauro alwala ta fito. Sallar Isha'ee ɗin da batai ba tayi, ta ɗaura da Shafa'i da Wutri. Tai kuka tana roƙon Allah ya zaɓa mata mafi alkhairi a cikin rayuwarta, ta mika lamarinta zuwa gare Shi baki ɗaya, kuma tana roƙonsa idan EHSAAS ba alkhairi bane gareta, Allah ya yaye mata zazzafar soyayyarsa da take ji a cikin zuciyarta.

Bayan ta gama addu'o'inta ta shafa, ta koma closet, ta zauna gaban mirror tana kallon yadda idanuwanta suka shige ciki sosai. Farar fatarta tai jajir - tsabar kukan da taci. Kuma sosai taga ta faɗa saboda rashin kwanciyar hankalin zuciya. A hankali ta cire hijabin jikinta, ya rage daga ita sai pajamas masu santsi, riga da wando da suka lafe a jikinta domin kasancewar barci zata kwanta. Ko bra bata saka ba.

A hankali ta shiga goge jikinta da humrah's ɗin da Inna ta mata na aure, masu shegen daɗi. Tana jin ita kanta kamshin da take yi yana burgeta. Ta madubi ta hango Abeey ta shigo, ta shiga tube kayan ta, zata yi wanka tana faɗin:

"Yah Mehtav, se yanzu wai kika fito? Tun dazu nake shigowa ina fita, ai na ɗauka kwana zakiyi cikin bathroom ɗin."

Banza tai mata, ta san neman magana take - ita kuma bata da ƙarfin zuciyar da zata yi entertaining ɗin silly dramas ɗin Abeey.

"Yah Mehtav, wai azumin magana kikeyi?"

Ta ƙarasa faɗa daidai tana ɗaura ɗan ƙaramin towel dinta a ƙirji. Ta ƙarasa gabanta tana riƙe kugu da niyyar tsokana, se kuma ta tsaya ganin kamar kuka Mehtav ɗin tayi.

Se tace: "Yah Mehtav, kuka kikayi?"

Mehtav ta juyar da kanta, ta bar gefen da Abeey zata ga fuskarta.

"Yah Mehtav, me ya sameki? Baki da lafiya ne?" Abeey ta tambaya cike da damuwa.

Girgiza kai Mehtav tai tana faɗin:

"Ki kyaleni please, karki dameni"

Abeey ta girgiza kai tana komawa ɓangaren da zata iya ganin fuskarta, tace:

"Yah Mehtav, auren ne baki so?"

Girgiza kai Mehtav tai.

Abeey tace:

"Tohm, menene? Prince ne ya bata miki rai?"

Girgiza mata kai tai.

Kamo hannayenta Abeey tai tana tambayarta:

"Tohm meye matsalar, Yah Mehtav? Ko abin da ya faru da Islam kike tunawa?"

Girgiza kai Mehtav ta shiga yi alamun a'a. Se kuma hawaye ya fara bin fuskarta. Abeey ma jinta gaba ɗaya tai duniyarta ta tsaya. Domin babban baƙin cikin ta a duniya taga Mehtav cikin kunci a rayuwa.

Mikewa tai itama tana hawayen, ta rungumeta tana faɗin:

"Tell me, menene Yah Mehtav? Is it Inna or Paa?"

"Baya sona fa." Mehtav ta faɗa tana kankame Abeey. "He is not excited about this whole wedding. Kullum yana daki yana aiki da laptop, ko kallona fa ba yayi. Har kwalliya nakeyi, in naga ya fito in je in zauna don yayimin magana, baya ko kallon inda nake. Gaisuwa ne kawai yake haɗa mu."

"Abeey, tayaya zanyi rayuwar aure dashi haka? Nasan karya yakeyi. Islam ce a zuciyarsa. Akwai dalilin da yasa ya zaɓeni akanta. Idan yasan haka zeyimin, why did he even choose me? Abeey, ni dai I want our old EHSAAS back. Wannan bedamu damu ba kwata-kwata!"

Shafa bayanta Abeey tafarayi tana faɗin:

"Kidena fadar haka. Who told you he didn't care about us?"

Tana ɗagowa daga jikin Mehtav a hankali, dake Mehtav azaune take saman kujerar dressing mirror, ita kuma tana tsaye. Sai tayi cupping face dinta a hannayenta, ta shiga share mata hawaye tana faɗin:

"Mehtav, he deeply cared about us. Duk aikin da yake yi, in na shiga dakin, yana bari yayi hira dani. He even told me about his parents da mamanshi, da babanshi, da kakarshi. Ya ce min idan yatashi tafiya NURISTAN, dani zeta tafi. Mamanshi zata soni sosai. Kuma ya ce min: I'll make a very beautiful princess."

Juyar da fuska Mehtav tai tana faɗin, "Ke kaɗai yadamu da ita. Ai banda ni, dan yaga inason shi ne, yana tuno komai da ya faru tsakaninmu. Nasani, ina ganin hakan, in yana avoiding ɗina."

Murmushi Abeey taitana gyaran murya alamun zatai karya tana faɗin: "Kinsan me yace min dazun kuwa, dan na je nuna masa henna ɗina?"

Girgiza mata kai Mehtav tai.

"Ya ce min be yi kyau ba, naki yafi kyau. I even told him his love is weak, naki be kyauba. Be ja ba, sai yace ai this silly art ba zai iya expressing kalar love ɗin dake tsakaninki da shi ba. Kuma ko be yi ja ba, yasan everything looks beautiful on you. Yanzu ba kin ji nace miki na shigo nemanki ba? Banine nake nemanki ba, shine yake turoni in dubo masa ke. Ya jiki Shiru yau. Gashi yana taso yaga lallenki."

Dan kallonta Mehtav tai, sanin Abeey na da wayo, zata iya shirya ƙarya ta faɗa mata don ta ji daɗi, hankalinta ya kwanta.

Tace: "You're trying to calm me down, Abeey. Nasan ƙarya kikeyi."

Abeey tace: "Ba ƙarya nake ba, kinji yah Mehtav. Kuma in baki yarda ba, yanzu kije dakin shi, na bar shi a garden yana tattaunawa da Paa. Ki nuna masa lallenki, zakiji me zece."

Dan kallonta Mehtav tai. Bata son ta biye da shawarar Abeey, taje mutuncinta ya gama barewa a gabansa. Amma kuma zuciyarta na ingizata gurin son tabbatar da abin da Abeey ɗin ta faɗa.

"Zakije?" Abeey ta tambaya tana kallonta, tana kifi-kifi da ido.

Mehtav dan shiru tai kafin tace: "Tohm."

Wani irin murmushi Abeey tai - irin na cin nasara nan. A zuciyarta take ayyana taya zasu fahimci juna bayan basa kasancewa a tare a guri ɗaya.

"I have to make them understand each other again. Idan EHSAAS ba zai yi making move ba, Mehtav ba zata yi ba, hmmmmm ni zan yi."

Jin Mehtav ta amince yasa tace: "oya, kiyi sauri ki gama shiryawa, ina zuwa."

Ficewa tai a haka nan, daure da towel a jikinta. Ba abin da ya dameta. Tanufi garden din gidan inda ta baro EHSAAS tare da Paa. Shi shi kaɗai ta hango, wannan karon yana waya.

Tana ƙarasowa, taga ya ajiye wayar. Murmushi ta shiga mai tana faɗin: "Our handsome prince!"

Shima murmushin ya mata yana faɗin: "Ke ko tsoro baki ji? Da daren nan kike fitowa waje haka ba ɗankwali, ba kaya? Babu kyau, ki dena. Kar in ƙara gani."

Sunkuyar da kai tai, najin kunya, kafin tace: "Tohm, na dena in shaa Allah."

"Prince, dama yah Mehtav ce ke son magana da kai."

Dan jim yayi yana kallon agogo a wayarsa yace: "At this hour?"

"Abeey is late," dan tabe fuska tai tana faɗin, "It's kinda urgent. Na ganta a cikin damuwa sosai. Can't you do this much for me, prince? Ni fa kawarka ce."

Ta faɗa tana riƙe hannunsa. Shafa kanta yayi yana faɗin: "As you wish, Princess. Tana ina?"

Tsallen jin daɗi tai tana riƙe towel dinta, gata 'yar ƙucila, ba girma sai shegen wayo. Tace: "Yanzu zata zo dakinka. Ka same ta a can. Ba ta son Inna tasani ne kasan zatai fada tace metakeyi agunka before wedding"

EHSAAS ya ɗan yi jim kafin yace: "Dakina kuma? Abeey, ki kirata nan. Inaga kamar dare yayi."

Tace: "Nan fa akwai sauro, prince. Kasan ita fa amarya ce, she's always indoors. Kuma fa sirri ne zakuyi, irin na masoya."

Ta faɗa tana jijjiga hannunsa irin ya yarda don Allah ɗinnan.

Yace: "Okay. But it won't take long, ok?"

Da sauri ta juya tana faɗin: "Thank you, prince!"

Ta juya, ta koma ciki da gudu. Dakin EHSAAS ta nufa. Taje ta ciro makullin dakin dake bayan ƙofar ta ciki, tana boyewa cikin wani flower vase a ƙofar dakin. Kafin ta saki murmushi tana wucewa dakinsu.

Akan gado ta tarar da Mehtav tana shirin kwanciya. Ta ƙarasa, ta yaye bargon da take shirin lulluba tana faɗin: "Yah Mehtav, ya haka? Ina alkawarin?"

Mehtav tace: "Ke, na fasa. In yana son ya ganni, shi me yasa ba zai zo nan ba?"

Tace: "Kinsan fa nan dakin matane, kuma yana da hankali, ba kamar da can ba. And Paa ba zai ji daɗi ba ya ganshi anan din. Ki yi haƙuri, kije dakin shi. Ya koma can yanzu. Ko minti biyu ba zaki ɗauka ba, se ki dawo. Yanzu na rigada na faɗa masa zaki zo."

Zunɓur Mehtav tai, tace: "Me da me kika je kika gaya masa? Ba dai abubuwan da na faɗa miki a closet ba?"

Girgiza kai Abeey tai tana faɗin: "Haba yah Mehtav, inafa da hankali. Wai ba ki yarda dani bane ba ne? Uhm, please trust me more. Kinsan ba zan zubar miki da aji hakanan nan ba."

Mehtav tace: "Abeey, are you sure yana son ganina?"

Jinjina mata kai cike da reassurance, tana faɗin: "Kinsan dai ba ƙarya zan miki ba."

Tana ƙarasa wa ƙofar toilet tace: "Ki yi sauri ki je fa, kar yayi barci."

A hankali Mehtav ta mike, ta nufi closet, segata da wani zunbulelen hijab dinta, jelbab har jan ƙasa yake yi. Ta nufi ƙofa. Abeey ta tabe baki a ranta tace, "How can she even attract him? Tana zuwa gabansa kamar wata matar liman,"

pretending tai, ta shige bandakin bata rufe ba. Tana jin rufewar ƙofar dakin su, tafito da sauri.

Saida ta tabbatar Mehtav ta kai dakin EHSAAS, sannan tafito daga dakin. Ba kowa a falon, shiru ko'ina, an kashe wuta.

Labewa tai bayan kujera tana ganin shigowar EHSAAS. After few minutes later, ya shige dakin ya turo ƙofar.

Wani irin tsallen murna tai, towel ɗin ya faɗi, ta tsugunna tana sake daurewa tace, "Let's see how they create a bond when they are alone - home alone ko room alone part 1."

Ta ƙarasa tana dakko key din inda taboye, ta shiga murɗa key din da yake soundless a jikin ƙofar kafin ta tsaya gaban ƙofar tana wani irin tunani mai zurfi.

Daki ta wuce, ta san kalar faɗin ran Mehtav tsaf zata cuci kanta fa ta ƙi faɗawa EHSAAS abin da ke ranta.

Hakan ne yasa ta ja wayar Mehtav da ke nan saman bedside drawer dinta. Text tai ta tura wa Taj tana faɗin:

"Bro, sorry I text you this late. Wutar dakinmu ce ta dauke. Last time data samu matsala, kaine ka taba mana fuse, ya dawo. Pls, wanne zan danna ya dawo?"

Saida yayi taking few minutes sannan taga respond ɗin shi:

"Mehtav is dangerous. Ki kira Danliti ya taba miki ko ki tayar da Paa."

Tsaki Abeey taja tana faɗin: "Wai Danliti? Mutumin da kila yakai Makkah abarci?"

Sa'annan seta saka emoji din marairaicewa.

"Duk sun kwanta. Kaga ba dede bane in tashesu. Just explain to me, zan gane."

Voice message taga ya turo mata. Ta buɗe, dalla-dalla ya mata explaining number fuse din kowane daki da kuma abin da zata danna yakawo ko yamutu.

And he asked her to be very careful. Duk da tsoron da Abeey ke ji, ba shi ya hanata mikewa ba.

Ta saka hijab din Mehtav, ta fito daga dakin, ta nufi store room cikin sanda.

Kunna wayar tai, ta sake jin voice ɗin tukunna, ta ɗakko stool, ta hau kai tana kallon fuse din wutar, na ko ina.

Saida ta ƙirga takaranta tsaf daidai na dakin EHSAAS, ta cire, tana ajiye wa a gefe, ta diro.

Duk da bigewar da kafarta yayi, bata damu ba. Ta dafa tana faɗin: "Ashhhh!"

Kafin tai saurin mikewa, ta nufi dakinsu.

Wanka tai, ta zira kayan barcinta, tai tafiyarta dakin Inna, ta kwanta a bayanta , dake ta daɗe da kwanciya, ta lumshe ido tana murmushi tana ji: "Inama tasaka camera, taga idon Mehtav lokacin da wutar dakin nan ta ɗauke. Tasan Mehtav da na tsoro sosai,amman tasan fuska zatai bazata nunaba agaban EHSAAS"

Daga ɓangaren Mehtav kuwa, ta shiga dakin EHSAAS. Wani irin bakon kamshi ne da bata san shi dashi ba ya cika dakin, ga wani irin kyau da taga dakin ya ƙara da tsafta. Kodan andaɗe bata shigo ba, har da beddings ɗinsa ba irin wanda tă bari bane last time.

Saman gadon shi laptop ɗinsa ne a kai, sai few takardu wanda bata san na menene ba, kuma ya akai ya samesu. Tă ƙarasa tana kallon screen din laptop ɗin dake ɗauke da taswirar wani guri da yafi mata kama da gari guda.

Jin buɗewar ƙofar sa yasa tă juya da sauri, daidai yana shigowa suka haɗa ido. Ya tura ƙofar ya rufe batareda ya sake kallonta ba, ya ƙaraso ciki da sallama, cike da masculine voice ɗinsa dake sending chills cikin jikinta.

Da ƙyar ta iya buɗe baki tana amsa sallamar. Gaban dresser ɗinsa ya ƙarasa yana ajiye wayarshi. Ya cire agogon hannunsa, kaɗan yayi unbuttoning saman shirt ɗinsa daya ɗan shaƙewa. Ta mirror yana kallon yadda tă yi ƙasa da kanta, ta kasa haɗa idanu da shi balle ta mai kwakkwaran kallo.

Shi kansa wani iri iri yake ji. He has been avoiding her, saboda har yanzu yana tunanin irin yadda ya ringa mata abubuwa, wanda suka dace da wanda basu dace ba - lokacin da memory ɗinsa ya kauce. She tolerated him a lot, kuma yayi troubling dinta. Wannan kunyar yasa yake avoiding dinta, ya kasa sakin jiki da ita. Ya ga kamar ta ga wani side nashi da babu wanda ya taɓa gani a rayuwarsa bayan matarsa, kuma sosai yake ganin girmanta darajatar ta a idanuwansa kuma ko kadan beriketa akan allurar data maiba domin dabadan allurar ba da kwakwalwarsa bata zama fresh yagama tina duka abubuwan dasuka faru dashi anitse ba,cikin kuwa har abinda yafaru ranar dayay hadari da kuma musabbabin hadarinsa da abin yagama gigita kwakwalwarsa,yasanya yaji he have to protect Islam from this danger at all cost.

Zama yayi saman gado. Ganin bată da shirin zama kuma ba tă da niyyar magana yasa yayi sighing a hankali yana faɗin:

"Sit."

Wani irin mugun ƙwarjini yake mata, namu musamman yana cikamata ido. Yanzu, hakan ne yasa a hankali ta ƙarasa gefensa zata zauna saman lallausan farin carpet ɗin dake shimfiɗe a ƙasan dakin. Da sauri yace:

"No Mehtav, pls sit here." Yana nuna mata gefensa, Cikin nutsuwa sosai.

Ta ji daɗin hakan da yayi mata, that shows how much he respects her. Ta zauna tana wasa da yatsunta da lallen ta da bai yi wani jaa sosai ba. Amma da yake farace, ya ɗan fito, ba lefi kuma yayi kyau.

Yana mugun son yaga mace da lalle. Ya ɗan murmusa, yana tuno wani lokacin da Islam ta saka a zo a mata lalle da cikin Jr. Bayan da aka gama lallen, yatsokaneta ta hanyar dameshi, gaba ɗaya hannun ya yi dungulmi da ƙafar, haka tawuni tana kumbura, tana cika, tana batsewa.

He can still remember yadda sai da yayi bribing ɗinta da littafai goma, ta hakura aka shirya.

Mehtav, ganin yana kallon hannayenta yana murmushi mai sanyi, irin murmushin nan da yake fitowa daga ƙasan zuciya wanda daɗe bata ga yayi ba, kyawawan dimples ɗinsa na motsawa yasa ta kafa masa ido.

Wani irin hope na tasowa a cikin zuciyarta.

Shi kuwa, matarsa kawai yake tunawa. A ransa yana jin wani irin hole daya kasa cikewa a ransa saboda rashinta a kusa da shi.

Sun ɗau mintina a haka kafin yace mata, "It's beautiful," yana nuna mata hannayen nata da tA buɗe masa su yanzu sosai dan ya gan su da kyau. Tana jin kamar ta je ta goya Abeey, ashe kenan gaskiyarta take faɗa.

Mehtav tă ɗan jujuya hannayen kafin tace mishi, "Thank you." Murmushi yayi mata mai sanyi, yana jin ɗan kunyarta da tausayinta a ransa - sanin cewa shirya-shiryen auren da ba zai wakana ba takeyi.

"Ykk?" taji tă tambaya tana ɗan kallonshi ƙasa ƙasa. Ɗan shiru yayi yana ƙare mata kallo tsaf, da ƙaramar oval-shaped face dinta, fara tass, irin ba wai farin nan mai haske sosai kamar nashi ba, amma farin Mehtav yellow yellow ne kamar madara. "Me ɗan banzan kyau, irin haskennan ne da inka kalleta sau daya seka kara kuma manyan kyau gareta kana kallonta zakasan tanada kyau" ya tabe baki a ranshi yana raya, "tanada kyau ba lefi, amma ba ta kai matana ba, saboda Islam the more kana kallonta the more zaka kara ganin kyanta duhun fatarta yakan boye kyanta wanda bazaka gani tafaraddaya inka kalleta ba" other heart dinsa ta faɗa mishi.

"I'm fine, ke fa?" ya tsinci kanshi da tambaya ba tare da ya shirya hakan ba.

Ɗan jim tayi kafin tace, "I'm good," sai kuma ta miƙe tana kallon kan gadonshi, ganin kamar aiki yake. Ya tashi, sai tace, "Bari na wuce, sai da safe. Daman gaidaka nazo yi."

Miƙewa shima yayi yana shirin mata sallama - duf! - wutar dakin ya ɗauke, baki ɗaya.

Dundum dakin yayi, babu haske ko kaɗan saboda window ɗin dakin a kulle yake. Tsoro ne ya kama Mehtav dake ta haddace dakin, ƙofa ta nufa tana faɗin, "Meya faru? Power disruption aka samu ne ko yaya?"

Murɗa ƙofar da zatayi taji ta tsaya gam-gam. Shikuma EHSAAS ya ƙarasa gaban switch, yana ta kunnawa da kashewa, ko zata dawo. Ganin ba zata dawo ba yasa ya ƙarasa gaban curtains din window, yayewa yayi ya buɗe tagar , ga wani irin mugun zafi da ake yi wanda bai taɓa jin zafin garin ba sai yau. Saboda kullum cikin air conditioner yake. Ba wani iska sosai, duk da ya buɗe tagar.

Ya juya yana kallon Mehtav dake ƙi-ƙi-ƙin buɗe ƙofa don fita, kwata-kwata taki buɗuwa.

Ƙarasa yayi yana faɗin, "Let m...."

Mamaki ne ya kamashi, sanin tabbas ya bar key jikin ƙofar, amma yanzu ya ga babu. Yasa ya tsaya yana kallon ƙofar speechless. Yace, "Where's the key?"

Ya shiga dakin, ya ɗau wayarshi, ya kunna torch, ya soma haskawa ko'ina ko zai gani, babu shi. Babu dalilin sa,kuma kofar bata taba kulle kantaba.

Mehtav kallon wutar da take hangowa ta can wajen gidan kawai take tana mamakin me ya samu ta cikin gidan ta ɗauke.

Bubbuga ƙofa ta soma yi, ko wani zai ji ya buɗe mata ƙofar. EHSAAS ganin abin da take yi yasa ya ƙaraso gurinta yana faɗin, "Kibari, kinsan sunkwanta. Babu wanda zai ji."

Cike da ruɗewa da tsoro take faɗin, "I need to go back to my room. Zan duba naga me ya samu wutar."

Zata ƙara bugawa, taji ya riƙe hannayenta yana faɗin, "Stop," a sanyaye ,da yasa gaba ɗaya tsigar jikinta ta soma tashi.

Riƙe ta da yayi tana jin wani irin abu tun daga tsakiyar kanta. Da sauri ta zare hannayenta a nashi tana kallon wayarshi tace, "Call my phone. Tana daki. Abeey zata ji, zata buɗe."

Miƙa mata wayar yayi yana faɗin, "I don't have your number." Ba bata lokaci ba ta shiga saka lambarta.

Switch off. Ta jima tana cewa, "Tanata trying, ya ƙi shiga." Tinani tasomayi anya wannan abin ba sa hannun wani kuwa saboda tasan kofofinsu bawacca tataba yin hakan amman dai tinawa datai gidan iya su isune yasa tai brushing abun daga kwakwalwarta don bata taba kawowa Abeey can go to this extent ba don ganin tashiryata da EHSAAS.

Ga zafin da ya soma damunta. Shikansa zafin yake ji, jurewa kawai yake yi, nasanma ya fi nata.

Ta kalleshi tana faɗin, "Bari na kira paa...."

Da sauri taga ya karɓe wayar yana mata kallon nan irin "ba ki da kai" dinnan.

Ya koma gurin tagar ya tsaya, wannan karon yana unbuttoning shirt ɗinsa duka, tă buɗe ana ganin farar white vest ɗin dake jikinsa, tă kama shi damdam.

Tsayawa ta yi a gefen door ɗin tă ci gaba da trying lock ɗin ta, amma ya ƙi ya buɗe. Tă ɗau kusan rabin awa tana abu ɗaya.

Ganin ba sarki sai Allah, ƙofar ba buɗewa zata yi ba, yasa tă koma saman carpet, tayi zaman sallah tana rafka uban tagumi. Ga wani irin gumi take ji tana yi ta ciki saboda uban hijabin da ta kimsa.

EHSAAS juyowa yayi, ya ajiye wayarshi a ɗaki akwai ɗan haske kaɗan yasa yake ganin ta, ta zauna kamar zata fashe da kuka, tsoro takeji sosai da alama hakan kuma yana tuno mai da Islam ɗin shi. Idan itace ma, da tuni tă cukuikuyeshi, ta soma mai kuka.

But Mehtav is very bold, ba ta cika bari yana ganin weaknesses ɗinta ba. He can see how she's trying hard ta ɓoye feelings ɗinta towards him koyaushe. Dayanzun, yadda take trying hard ta ɓoye tsoronta da kuma zafin da take ji.

Ƙarasa wa ɗakin yayi, ya jefar da shirt ɗinsa yana faɗin, "I don't know what happened, but I'm sure dazun da na fita key yana jikin ƙofa."

Kautar da kanta tayi daga ganinsa, taga ya nufi toilet. Jin ƙarar saukar shower da kamshin sabulun wankansa na tashi a ɗakin yasa kawai tă fara imagining ganin that hot hunk body ɗinsan under shower, shirtless, ruwa na bin jikinsa, that damned piercing grey eyes, wannan hair ɗin nasa mai tsayi yadda zasu kwanta yadda ruwan zekebin huge chest dinshi da abs dinsa... sosai take fantasizing abin a cikin brain ɗinta, how he would look like.

Bata san lokacin da ya fito ba ma, sai jin ɗan digar ruwa tayi a saman hannunta. Da sauri tă ɗago ido, suka haɗa ido da shi.

Wandon pajamas ɗinsa ne kawai a jikinsa, sai wata ƙaramar vest again da tă kama shi - take showing well-built chest ɗinsa da cikinsa da ke ɗauke da wasi abs da ta kasa ɗauke kai akai, da mini towel akansa yana dan tsane gashinsa daya dan jike tagefe da gefe

"Are you not feeling hot?" ya sake tambaya a karo na biyu, yana kallon yadda take kallon shi kamar ba ta taɓa ganinsa ba a rayuwarta.

"Mehtav," yă faɗa, yana tsugunnawa ya hura iska a idonta, da yasa ta yi saurin farkawa daga fantasy ɗinta.

Wata irin muguwar kunyarsa ce ta shiga kamata. Tanajin kamar zai iya karanta all her dirty fantasies a kansa idan yakalli cikin idonta. Sunkuyar da kai tayi tana faɗin, "Uhm… ahm, me kace?"

Yace, "Ba ki jin zafi ne? Ki cire hijab ɗin, kisha iska."

Ta manta ma meye ne a jikinta. Kawai tă tsinci kanta da bin umarninsa - tă cire hijab ɗin daya mugun kama kamshin dake tashi ajikinta tana miƙa mishi. Bata ma san dalilin da yasa ta bashi ba, kamar wani ɗan aikinta.

Da sauri zata cewa yabata yaninke, kawai taga ya miƙe da hijab ɗin a hannunsa. Gently, yă shiga folding mata shi, yana ninkewa. Wani irin melting zuciyarta ta sake yi, saboda tanajin he is a perfect gentleman. Ji yadda ya ninke mata hijab, ba girman kai, ba komai, kamar ba prince ba.

Ɗauke kayan aikinsa taga yayi daga kan gadon, ya nufi gurin tagar, ya shimfiɗa darduma, ya ɗaura su akai. Sai taga ya dawo ɗakin, ya kaɗe zanin gadon, ya sake gyarashi. Gently yace mata,

"You can use the bed in kinajin barci. I still have a lot of work to do. Nasani, no one will come sai zuwa asuba."

Dan jim tayi tana kallon gadon, tana kallonsa. Wai yana nufin a ɗaki ɗaya zasu kwana, shi da ita? Duk da ba yau ta fara kwana a ɗaki ɗaya da shi ba, but she felt something all of a sudden. Ba wai shi ne bata yarda da shi ba-uhm uhm-kantane ba ta yarda da shi ba in tana tare da shi.

"Ko ba zaki yi barcin ba?" ya faɗa yana avoiding kallon jikinta wannan karo sosai, saboda tun kallon farko da ya mata ya gane ma kanshi yake lowering gaze ɗin shi.

"Thank you," kawai ta ce mai tana hayewa saman gadon. Tă lumshe ido ta yi shiru, sai da ta tabbata ya bar kanta sannan ta buɗe ido, tana ganin yadda ya zauna ya jingina da bangon window ɗin, ya soma danne-danne a laptop ɗinsa.

Se juyi take, ta kasa barcin saboda zafi. Sannan kuma idonta yaki gajiya da kallonsa.ga kamshinsa daya kama zannuwan gadon nashi yana kara narkar da zuciyarta yana haifar mata dawata irin kasaka, Tanajin kamar tă hadiyeshi tă huta da jarabar sonsa dake mugun-mugun kashe mata zuciya.

NURISTAN

Gimbiya Mimah ce ta fito daga motarta da isa da izza dawani irin dan banzan ego datakejin yana hawa kanra yanzun ta nufi bangaren Mai Babban Daki. Duk bayin da ta haɗu da su a hanya suka gaisheta, seta ciro damin kuɗi ta danka musu sadaka. Kawai bakinta yaki rufuwa don farin ciki da wani irin mugun annashuwa da take ɗauke da ita.

yau ɗin ta musamman, straight ta nufi ɗakin uwarta dake can sama. Ta haura tana wani irin kwalamata kira kamar sa'ar ta tabanka ɗakin. A take, ranta ya haɗu yay mugun baci ganin uwar tata abinda take yi.

Duk da ba yau ne karo na farko da ta ganta tana aikata irin wannan alfashar ba, amma ta ɗauka zasu daina ko daga kafa da don darajar lalurar da mahaifinta ke ciki a yanzun.

Mai Babban Daki tana zare ido, take faɗin, "Ke me yasa ba kya neman excuse? Bakya girma san mimah! Ba kya sallama in zaki shigo ne?"

Tsaki ta ja tana kallonta daga ita har kwarton nata, tana faɗin, "Sallama ai mutane nagari ake wa, ba irinku ba. Wai Umma, yaushe zaki daina wannan dabi'ar kinfa girma,ko tumin takabar, ki kewa kanki baƙin cikin ci, ai se ki ci gaba."

Ta faɗa tana shigowa ɗakin dukan ta. Tana ganin yadda Erfan ke wani sunsunkuyar da kai yana faman neman kayansa ya mayar jikinsa.

Tsayawa tai akansu har suka gama shirin nasu. Ta dire musu paper a tsakiyarsu tana faɗin, "Ku fara kirana Mace Mafi Arziki a ƙaf fadin NURISTAN, dake wayenta baki ɗaya."

Mai Babban Daki da sauri ta shiga kallon takardun, ta ɗauka. Dake ba wani ilimi teke da shi ba, kasa karantawa ta yi. Da sauri ta miƙa ma Erfan, ya shiga duba takardun.

"Meye wannan haka nake gani?" Erfan ya faɗa yana murmushi, bakinsa yaki rufuwa.

Ta ce, "An bani grant. Na shigo da kayan nan da muka yi order na billions of dollars daga Columbia. Idan kayan nan suka ketare border ɗin NURISTAN, irin arzikin da zanyi-komai Martaba banajin ko mai Martaba ya isa yataka ni,kuma matan damuka shirya musu da yaran suma zamu fita dasu a containers din dazasu shigo da drugs din"

Mimah ta shiga faɗa musu tana murmushi.

Mai Babban Daki cikeda farin ciki ta tashi, ta rungumeta tana faɗin, "Ashe dai haihuwa ta min rana! Yar nan, ashe zanga ran da zaki gogemin gorin arziki da mulki da ake dade ana min a cikin gidannan!"

Mimah tadan ture uwar daga jikinta tana faɗin, "Pls ki daina tabani da wannan kazantar da kuka gama yi a jikin ki. Kinga dai abin da zan zama ke, kin tsufa, girma yazo miki. In zaki hakura, ki bar wannan rayuwar, ki barta.I can't take anymore risks Saboda ta sanadiyyar ki asirinmu ya kusa tonuwa a gurin Mai Martaba. Da ba dan na tura Ja'afar cikin su dogaran Mai Martaba ba, da tuni yanzun wata maganar ake ba wannan ba, Barganin jay yamutu ja'afar munyanke mai harshe baze iya magana ba mai Martaba mutuwar nan ce takwantar dashi binciken yatsaya So duksanda yafarka komai ze iya faruwa don haka abinda zan gaya miki shine, arziki baya zama da zinace-zinace.

Kin auri Mai Martaba farko, kin bi wansa, gashi nan a zaune." Ta nuna Erfan dake bin takardun ɗaya bayan ɗaya yana jin a ransa tabbas lokaci ya yi da Mimah zata san asalin wacece ita.

Domin arzikin nan a hannunsa ya dace ya zauna, ga mulki da already crowning dinsa ne kawai ba a yi ba. Amma ya rigada ya zama nashi saboda duk wani abu shi ke zartarwa ba NASHWAN ba tun mutuwar mahaifiyarsa da batan matar danshi da jikarsa da ya faɗi yake jinya.

Mimah tacigaba da fadin "ki ɗaura da hadiman gidan nan maza, ban san adadin mutum nawa kikasa na kawar ba saboda ke. Sai daga baya kika rasa wa zaki nema. Sai shegen yaron nan Jay dan cikin ki da tuni ya tona mana asiri. Don haka ki koyi yadda zaki ringa rage maitarki. In ba haka ba, wallahi wallahi wallahi, kin ji na rantse miki sau uku, sai na wanke hannuna daga cikin lamarinki! Idan asirinki yatono tattara arzikina zanyi inkoma gidan aurena in playing victim innuna ma bansan kinayi ba"

Da sauri Waziri yace, "Mimah ai ba za a yi haka ba, in sha Allah. Tă daina. Ko, my love?" Ya faɗa yana mikewa, ya karaso gaban Mai Babban Daki yana rikota, "Ni kadaina, Na ishe ta." Ya ƙarasa yana ɗage mata gira ɗaya da wani irin murmushi.

Tana rungume shi, Mimah ta tsaki, ta jefa musu wani mugun kallo, tace, "Kunci sa'a kawai. Ina cikin mood mai kyau da yau, kun ga tijara." Ta ƙarasa tana kwashe takardunta har zata fita.

Erfan yace, "Ba ki ji ba, Mimah?"

Juyowa tayi tana faɗin, "Meye kuma? In kuɗi ne, banda ko sisi, sai kayan sun zo."

Dan murmushi yay, yana faɗin, "Tambayarki kawai zan yi. Me ne yasa tun da can basu bar ki kin shigo da kayan ba har bayan da Prince ya mutu?"

Juyowa tai, tadan tabe baki tana faɗin, "Saboda shegen yaron can EHSAAS ne. Kasan yadda ya saka ido akan lamarin trafficking ɗin nan. Kasan trade by barter za mu yi, zan basu mata da yara, su kuma su shigo min da drugs ɗina.that bastard EHSAAS, idon shi na kan abinnan. South South is like his home, tana tafin hannunsa tun bayan da Mai Martaba ya bashi hakkin kula da ita.

Duk wasu harkallolina ya hana. Ya kame min yara. Don ma dai masu amanane dukkansu kuma bana bari su shura, nake aikawa a kashe su balle a tona min asiri.

Da gaske nake, ni kaina I tried bayan mutuwar EHSAAS, in ga na karɓi kayana na basu nasu. Amma tsarikan dokar da ya saka a gurin yasa dole na hakura. Saboda one mistake zan yi-za a yi game over. Tohm yanzun haka da basira nai aiki. Na yi amfani da saka hannunmu, na haɗin gwiwa da Princess Islam tayi akan takardun nan," ta faɗa tana ɗaga takardun tana wata shegiyar dariya.

"She didn't know what she is getting herself into. I used her for this, saboda ya kasance duk abinda zan yi a takarda zan nuna ni da ita muke yi, because I promise I won't go down alone.

Nayi hakan ne saboda duk ranar da Allah ya sa EHSAAS ya binciko wannan sirrin, ya kasance ba zai iya komai akai ba, saboda nasan ita ce weakness ɗin shi. Kuma haka aka yi. A taron dayaje Nigeria, ya gane ina daga cikin manyan drug dealers da yankin Africa baki ɗaya and I am using his wife's name,sannan yagane yaron jay dake cikin security dinsa yagane duk abubuwan damuke kullawa saboda mugun zurfin binciken. Amman besan inyasan wata besan wataba,the worst part ɗin dayazo yasani shine, shares ɗinta yafi nawa cikin business ɗin. There's no way he can protect her from this storm idan har yay nasara. Unfortunately, be yi nasarar ba. I overpowered him. He was on his way back to ruin me. He was angry. Ya kirani a waya, ya zazzageni, yayi tir da halina, ya min Allah wadai. Bai san wannan ne kuskurensa da yayi causing life ɗinsa ba."

ta ƙarasa tana kallon Erfan dake sauraron ta closely, saboda sai yanzun yake tono iri yadda ta zo mai da plan ɗin kisan EHSAAS a ɗan kankanin lokaci bayan original plan ɗinsu ba haka yake ba.

Murmushi kawai yake, saboda yasan yadda take amfani da kowa. Shi kansa amfani take yi da shi don yana da yan daban da zasu mata dirty work. Kuma idan amfaninsa ya kare, shi ma ƙarshe nasa zai iya zama kamar Jay and he will never allow that.

Yau ya tabbata da cewa dan na gada yafi dan na koya, barewa ba za ta taba gudu danta yay rarrafe ba. Duk muguntar ta Mimah, taci uwar tashi.

Murmushi kawai yay yana faɗin, "Weldone Mimah, I'm very proud of you."

Wani irin yatsine face tayi, tanajin kanta. "Kadan daga aikina kenan."

A hankali Mehtav take buɗe idonta, jin kamar sanyin asubah na busowa ta taga dakin dayake abude duk zafin dakin sai da yayi wani sanyi saboda asubah da ke gabatowa. A hankali ta mike tana kallon kyakkyawar fuskar EHSAAS da screen ɗin laptop ɗin ya haske, da alamu aikin yake barcin ya ɗauke shi.

A hankali ta mike tana zira slippers ɗinsa da yayi mata yawa a kafa sosai. Tayi miƙa tana karasowa gurinsa tana taku a hankali, gudun kada ta tasheshi.

A hankali ta tsugunna gefensa. Ko tsoro bai yi ma wuyansa yayi ciwo, yana barci a zaune haka.

Dauke laptop ɗin tayi daga kan cinyarsa, ta rufe a hankali ta ajiye a gefe. Ta soma haɗa takardun guri guda neatly, ta ajiye su suma. Ta zauna daf da shi tana kallonshi kawai tana murmushi. She's just remembering some of his silly attitudes na baya. Tana jin "inama wannan attitudes ɗin zasu dawo," lokacin da baya one second bai zo ya takura mata ba, ya zauna a gefenta, ya rike hannayenta ko ya ja ta jikinsa. She really missed his warm body sosai.

Ganin kamar wuyansa ya masa wani iri yasa ta tallafa fuskarshi tana sata a tafin hannunta. A hankali idonta na lumshewa, ta daura goshinta saman nashi tana jin yadda numfashinsa ke sauka a hankali kamar ba ma jin daɗin barcin yake ba.

Wani irin farin ciki da kuma tsoro take ji yana cike mata zuciya. Saboda son shi ba fa raguwa yake a ranta ba karuwa yake. Shine babban tashin hankalin da ta kasa ganewa.

"I love you," ta faɗa gently, tana kai hancinta saman kan dogon hancinsa ta haɗe su guri guda.

Gently, taji yace, "Babyyyyyyyyy..." da cute red lips ɗinsa da taji wani ƙamshi na fitowa daga cikin bakinsa kamar ba me barci ba. Wani irin tsalle zuciyarta ke yi, gashi ta kasa sakinsa tana tsoron kar ya tashi.

Janyota taji ya ƙara yi, ya haɗe bakinsa da nata. Ya shiga kissing batare da yasan me yake yi din ba, don a tunanininsa he's just kissing matarshi a cikin mafarkinsa ne.

A wani irin firgice Mehtav ta buɗe idanuwanta tana kallon yadda ya wani zaunar da ita saman cinyarsa, kissing her passionately kamar yaron da ya samu alewa ake shirin ƙwace masa.

Rawa jikinta ya fara yi. Ta soma ƙoƙarin tashi, amma ya ƙi bata wannan damar. Gashi she's feeling it too, itama ta fara kissing ɗinsa back. Hakan ne yasa ya buɗe idonsa a hankali, jin kamar abin ya fara zama mai too real.

Ya ɗaga ido,da fararen idanuwanta da ba su da girma sosai, dai-dai Tubarakallah.

Ganin bai yi tozali da gwaran idanuwan matarsa da yayi expecting gani ba yasa ya wani irin zabura, yana turata baya da sauri.

She's speechless, shima haka. Kasa motsi tayi, takasa kuma kallonsa.

Shi kansa wani irin haushin kansa da kunyarta ce ta mamaye shi.

Da sauri ya mike ba tare da ya kalleta ba, ya shiga bathroom, yana turo ƙofa. Zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri.

Ya karasa gaban sink yana kallon kansa a madubi.

He just cheated. Abinda zuciyarsa ke raya masa kenan.

He just made a great sin har guda biyu-ya taba macen da ba ta shi ba kuma ba shi da niyyar maidata tashi.

Sannan ya ci amanar Islam, da ta ɗauki dukkan yarda ta ba shi. Kuma yayi alkawari he will never even see any woman that way.

The worst part of it shine how that stupid kiss turned him-is something da bai taɓa tsammani ba a rayuwarsa. Kuma bai taɓa faruwa da shi ba batare da matarsa ba.

Matarshi has always been the one who triggers his manhood. Ko tsirara zai ga mace, ba ya jin za ta yi wani effect a kanshi.

A da toh, me ya canza yanzu?

Ya shiga tambayar kansa yana rike kansa.

Yana jin tabbas, lokacin barin gidan nan ya yi.

Saboda if he stays, ba zai sake iya haɗa ido da Mehtav ba. Kuma yasan shi ba zai iya haɗa matarsa da kowace mace ba.

He doesn't want to break her heart.

Kiran sallar da yaji ana yi ne ya sanya shi haɗa ruwan wanka. Jikinsa a sanyaye, yana jin kansa kamar ba shi ba. Ya shiga yin wanka yana tunanin ta inda zai iya sake kallon idon matan nan guda biyu da yake jin suna da matuƙar mahimmanci a rayuwarsa. Ba wacce zai iya cutarwa a cikinsu.

Islam is his everything-the love of his life, his wife kuma uwar ɗansa da yayi mata alkawari ba zai taɓa kallon wata mace ba bayanta.

Mehtav is his life saviour. She had been there for him. Bai kyautu ace ya karya mata zuciya haka da irin abubuwan alkhairin da ta mai a rayuwarsa ba. Da badan Mehtav ta taimake shi ba, da yanzun kila ba ya wannan duniyar.

Tabbas Mehtav zata kasance ɗaya daga cikin mata mafi daraja da mahimmanci a rayuwarsa, kuma he will forever be indebted to her for saving his life and taking good care of him har zuwa wannan lokacin da hankalinsa ya dawo.

Mehtav na sonshi, amma ba ta taɓa buɗe baki ta faɗa masa ba, sai yau din da yaji kamar a mafarki ta faɗa, wanda yaji shaiɗan yasa muryarta ta rikide ta zama irin ta matarsa.

Saboda matarsa ke mai irin wannan tashi inda zata tasheshi a barci, is always sweet and memorable.

Ta na sonshi. Ta yaya zai iya kallon idonta ya ce mata ba zai iya zama da wata ba bayan Islam? Cewar ba zai iya adalci tsakanin su biyun ba.

Son da yake ma Islam ba wai ƙaramin so bane da zai iya managing, ya kasa nunawa a gaban kowa.

Da ace wata ce ba Mehtav da yake jin she's precious a ransa ba, kila da ya aureta. Amma ba zai iya aurenta ya yi hurting dinta shi da matarsa ba, don yasan alakar su ba wacce third party za ta shiga ba ce.

Don haka zai faɗa mata gaskiyar abin da ke faruwa. Ko Allah zai sa ta fahimta kuma ya bata haƙuri da wasa da zuciyarta da yayi haka.

Da wannan tunani ya kammala wankansa, yayi brush, ya ɗauro alwala, ya fito.

Mamakine ya kamashi ganin wutar dakin ta dawo kuma Mehtav is nowhere to be found.

Ganin dakin a buɗe yasa ya fara tunanin ko dai Paa ne ya zo su tafi mosque ya barta ta fice.

Wata irin kunyace ta sake lullube shi saboda bai san me zai ce ma Paa ba, kuma bayan clearly ya faɗa masa ba zai auri 'yar shi ba. Kuma ya kamata a dakin sa, duk da dai it was accidentally, amma still ba zai ji daɗi ba.

Bai gama rufe baki ba yaji Paa ya zo bakin ƙofa yana faɗin,

"A'ah prince, ashe ka tashi? Ni ma yau naso makara, kaga na fito a gaggauce, kashirya, mu wuce mosque."

Wani irin sanyi yaji ya dira masa a rai ganin Paa ma yanzu ne ya zo.

Sai yace masa, "Bari na sa jallabiyata," yana zuwa ya koma a gaggauce, ya shirya ya fito, ya bi bayan Paa, suka wuce mosque.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to: ✨ Share 🗨️ Comment ❤️ Like 📥 & Vote [22/06, 20:16] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

Follow all my social media handles @fatoumspassion

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.