EHSAAS

Chapter 38

by @fatoumspassion

Aman na zaune cikin office din EHSAAS, wanda yawanci a ciki yanzun yake ayyukansa, saboda wani bincike da yake yi akan wasu boyayyun files din EHSAAS da ya samu nasarar kai hannu kansu lokacin da yaje chaje sashensa a cikin safe din Islam. Bayan tabata gaba daya, jiyake yi kamar ze zare, don gani yake kamar har da sakacinsa uncle dinsa ya daura dukkan yarda da amana ya bashi. Amman yanzun, gashi sun bata a kasar da ba tasu ba ma. He checked everyway Oxford, NURISTAN all her numbers bawanda take tafiya.

Amsa waya yake yi a daidai lokacin da yake jin wani information da ya mugun jin dadinsa. Kallon kofar yayi kafin ya bawa sakatariyarsa damar shigowa, saboda yasan da zuwan nata. Shigowa tayi a hankali, a bayanta wani middle-aged dake sanye cikin wata bakar suit. Kana ganin zubinsa, kasan jami'in tsaro ne.

Katse wayar Aman yayi yana maida hankalinsa kan mutumin. Ya mike yana bashi hannu, suka gaisa cikin girmama juna, kafin ya bashi damar zama. Sakatariyarsa ta fice, ta koma kan aikinta.

Kallon mutumin Aman yayi yana bude wani file dake gabansa, ya tura masa yana fadin: "Can you explain what this means? Akwai wani bincike da Prince ke yi ta karkashin kasa ne wanda ban sani ba?"

Daukar file din mutumin yayi, ya shiga dubawa a nitse. Ya kammala, ya rufe, ya ajiye yana kallon Aman, dake jiran jin karin bayani.

Aman yace: "Ina sauraronka."

Mutumin a nitse yace mishi: "Wannan bincike ne wanda Prince yake yi a South-South, kuma an riga an rufe file din tun bayan mutuwarsa. Border din ma ba a bude taba, sai wannan watan ake shirin budewa, wasu kayan matar Prince su shigo."

Kallonsa Aman yake cike da mamaki, yana fadin: "Kayan matarshi? Kuma dama Princess Islam na yin wani business ne wanda ni ban sani ba? Kuma me yasa Prince ya boye mini binciken da yake yi, alhali komenene nasa, nine akai, nine nake mishi duk wani bincike akan abubuwan da yake da bukata? Akwai wani abu da ake boye mini ne? Kuma taya za'ayi a shigo da kayan wadda ta bata ba mata kasar, ta ina zata samu nutsuwa da ba order a shigo da kaya?"

Mutumin da shi kansa be san me ke faruwa ba, girgiza kai yayi yana fadin: "Nima babu abinda na sani bayan hakan. Prince dai ba ya son kowa ya sani."

Jinjina kai kawai Aman yayi, sanin gaskiya yake fada. Ya sallameshi ya tafi. Fitar sa ke da wuya, ya daga waya yana mai umartar sakatariyarsa ta siya masa ticket na zuwa LA, domin yasan anan ne kadai zai samu amsoshin tambayoyinsa.

Amman kafin nan, dolene ya dakatar da shigowa da wadannan kayan, domin yasan tabbas wani ne ke amfani da sunan Islam don shigo da wannan kayan. Yana fita daga office, straight hukumar tasu ya nufa. Director General gaba daya aka bashi damar gani, sanin matsayinsa a kasar ba me iya dakatar da shi da shiga ko ina.

Da fara'arsa, dattijon ya tare sa yana mai sake mishi ta'aziyyar rasuwar great-grandmother dinsa. Aman ya amsa yana mai godiya kafin ya samu guri ya zauna.

Director General ya tambaye shi dalilin zuwansa, ko akwai wani abu da yake so yayi masa. Aman dan gyaran murya yayi kafin ya tambayi, "Wane kaya ne Princess Islam ta yi approving a shigo da su ƙasar?"

Dan kallonsa Director General yayi kafin yace masa, "It's confidential. Abu daya zan iya gaya maka - daga Columbia suka zo."

Yace, "Columbia kuma? Princess Islam bata taɓa zuwa Columbia ba. Ban ji ma tana da wani side business, kuma yanzun haka ta daɗe da bata. Ta yaya za a ce ta bada order kayan su shigo?"

Girgiza kai Director General yayi yana fadin, "Nima bansani ba. Kasan order kawai nake karɓa."

Aman yace, "Ina so a dakatar da shigowa da kayan nan. Ban yarda da su ba. Ina tsammanin wani ne ke amfani da sa hannunta ko sunanta."

Director General ya dan yi murmushi, jin smartness din Aman din. "No wonder Prince yake aiki da shi tun tsawon wannan lokacin, kuma ya daura shi akan dukkan dukiyarsa. Babu shakku."

Yace, "Ka yi haƙuri Prince Aman. Kayannan doka ce muka samu daga sama. Babu yadda za a yi su fasa zuwa, saboda kayan sun fi rabi a hanya. Ba yadda za a yi su koma yanzu."

Aman kallonsa yake da mamaki, domin betaba bada wata order akaf faɗin NURISTAN, an ce No ba, Sai dai idan akan dokar Mai Martaba ne ko na Prince EHSAAS.

Aman, cike da izzar nan ta mulki, yace: "DG, ina ji ka manta wanene ni a ƙasar NURISTAN, da kake tunanin zan bada wata order kace 'a'a'. Saboda a kowane lokaci, ina magana ne da yawun Yarima EHSAAS marigayi. Ina so in san a saman waye yabaka umarnin barin kayan su shigo - Mai Martaba ne ko Waziri?"

Dan shiru DG yayi, saboda yasan ba zai taɓa iya faɗawa Aman gaskiya ba. Yace: "Na maka alkawari, ba zan taɓa bari wani abin cutarwa ya shigo NURISTAN ba. Prince Aman, ka yi haƙuri. Ka zare hannunka a cikin wannan maganar. Saboda haka Yarima yake so - shine last wish dinsa."

Wannan kalamai na DG ya sake saka Aman a cikin duhu, domin in dai har Yarima zai iya ɓoye masa wani abu, yasan abin gagarumi ne kuma ba zai kasance alheri tare da sanin da zai yi ba. Murmushi kawai yayi, saboda ba darajarsa ba ne tsayawa ja-in-ja da DG. Ya mike kawai, ya mai sallama, ya fice, domin so yake ya samo amsoshin sa zuwa nan da satin gaba da kayan za su zo.

Palace ya wuce straight inda ta zama ko ina shiru, kamar ba lively fadar NURISTAN ba.daba a rasa dubban al'umma a ciki da wajen ta, dalilin rashin lafiyar Mai Martaban Waziri ya zama shine me riƙe ƙasar baki ɗaya. Hakan ne yasa bakin halinsa da mulkin zaluncinsa ta kori duk wani talaka dake rabe a jikin Mai Martaban.

Kayansa ya haɗa straight, ya wuce ɓangaren Fulani. Be same ta ba, kuma dama yasan ba zai same ta din ba, domin ita ce ke tare da Mai Martaba - ba dare ba rana - tana kula da shi tana jinyarsa.

Sakon tafiyarsa ya bar mata a cikin wata doguwar wasika dake sanar da ita ta kwantar da hankalinta. In sha Allah, zai dawo tare da Princess Islam da Prince EHSAAS Jr - ya gano inda suke.

Daga nan ya wuce filin jirgi zuwa LA, saboda nan ne private investigator ɗin da ya haya. Ya ringa bin mahaifin Islam ɗin, yace yayi kuma yayi tracing wayar Abraham Zion. Kamfanin wayar direct ya saka suka duba masa call history ɗin da kuma waye yayi waya daga inda aka yi wayar zuwa Nigeria. Tunda Islam ta bata, ya yi expecting zata nemi babanta, saboda yasan kalar connection ɗin da yake dashi, zata yi tunanin shi shi kaɗai ne zai iya protecting ɗinta.

Daga ɓangaren su Islam kuwa, a wani luxury apartment dake heart of Beverly Hills, suka sauka. Ɗaya ne daga cikin gidajen Abraham Zion dake ƙasar. Gidan ya tsaru matuƙa, amman duk tsaruwarsa, kwata-kwata ba ya burge Islam ba, saboda a yanzu ita ba ta ma da nutsuwar zuciyar gane abu mai kyau da mara kyau.

Gidan yana daga cikin ginin, akwai chapel corner, inda Abraham yake gudanar da service. Duk inda kika juya, akwai hoton Yesu, cross, da kalmomin Bible da ya manna a bango.

Ranar da suka sauka, ba su samu sun yi wata magana takirki ba, Islam sanyi guda ɗaya da ta ji shine ganin mahaifiyarta a gidan. Sanin cewa tare zasu zauna su duka ukun, ba da iya babanta zata zauna ba, ya dan kawo sassauci a zuciyarta. Saboda tun da suka baro Nigeria, bakin Abraham bai yi shiru ba, sai mita yake, yana tsine ma EHSAAS yana ce mata, "I told you so."

Mamanta ce ta kai ta ɗakin da aka tsara saboda ita. Ga mamakinta, duk wani abu da zata buƙata an zuba - ita da jaririnta - ciki kuwa har da kayan wasan yara da cradle. Wanka tayi, ta fito, ta zaɓi kayan da aka saka mata a wardrobe, irin dai ƙananan kayan da a da can ta saba amfani da su. Ta saka a jikinta, take jin kayan sun matse ta saboda tayi adding weight akan wanda take dashi kafin aure. Ta dada cika, ta zama cikakkiyar mace. Tasan mamanta tadaɗe bata ganta ba, kila shi yasa ta kasa predicting accurate size dinta. Hijabin da ta zo dashi ta zura, ta fito parlour. Cikin sa'a, Abraham already ya shige ciki. Ta ari wayar mamanta, ta koma ciki. Alƙibla ta duba, aikuwa tana gani, ta shimfiɗa wani ɗan kwali mai tsafta a ƙasa, ta tada sallah.

Sallar, duk da ta rasa a jirgi, ta shiga jerawa. Tana raka'ar ƙarshe, taji an buɗe ƙofa. Zuciyarta sosai take bugawa, amman cikin nutsuwa ta karasa sallar. Ta yi sallama, kanta a ƙasa, saboda taji kamshin turaren mahaifinta da ya shigo. Ta ɗauka zeyi mata wata magana, amman ga mamakinta, sai taji yace: "Fito ki ci abinci."

Ya ɗau Jr dake wasa saman gadonta, ya fice. A hankali ta mike, tana bin bayansa.

A saman dining ta tarar da shi tare da mamanta suna cin abinci. Bata ce musu kala ba, ta ja kujera ta zauna ba tare da ta zuba abinci ba. Mamakine ya kamata ganin Abraham ya shiga zuba mata abinci yana fadin, "You need to eat well. Kar ki ke ƙin cin abincin - wani ciwan kuma na daban ya zo ya kamaki."

Ita kanta Veronica kallonsa ta shiga yi cikin mamaki - it's so unlike him, da alama akwai abin da yake so tunda taga yana haka.

A hankali Islam ta fara cin abinci, ba dan tana jin daɗinsa ba - hasalima wani irin ɗaci yake mata a baki. Amma saboda ta san idan bata ci ba, danta ba zai samu shima wanda zaici daga jikinta ba. Take ci a hankali, tana danné nauyin da take ji a saman kirjinta.

"Ashe har yanzun kinayin sallah?" Abraham ya tambaya yana sha coffee, cike da izgili da rainin wayo, bayan ya ganta tana yi dazun. Bata ce masa komai ba - sanin ba zata ce ɗin ba yasa yace: "You think you're doing the right thing staying in this darkness?" Cikin tambaya, kafin yace: "Hmmm, ai ba zaki taɓa samun kwanciyar hankali ba in dai kika cigaba da bin addinin nan."

Sai a lokacin Islam ta dago ta kalleshi, amma bata ce masa komai ba, still.

Veronica, cike da tattali, ta dafa shi - dayake yana gefenta - take fadin: "Honey, please not now. Ka barta ta huta. Kun fa kwaso gajiya da yawa, itama. Ta yaya za a ce ta cigaba da addininsu? Ai ta san abin da ya dace."

Kallon Veronica yayi yana fadin: "Ai da alama bata sani ba, shi yasa nake tuna mata cewa a gidan na na ke - baki ji tayi shiru ba? Ai ta san bata da gaskiya." Ya juya kan Islam yana fadin: "Your silence will not help you here." "You are lucky I didn't take that boy away. He is my blood, not EHSAAS's." Ya ƙarasa yana shafa kan Junior da ke ta wasa a saman cinyarsa.

Sai a lokacin Islam ta buɗe baki tayi magana: "He is my son. And please, Dad, ba kai ne zaka fada mini ga addinin da zan yo ko ga wanda ba zan yi ba. I'm a grown-up now - I know what is best for me."

Wata shegiyar dariya yayi yana kallonta, sanin Peace nada mugun taurin kai. Ai dama yasan ba zai nitsar da ita cikin sauƙi ba. Wai yau har shi take iya kallata ce masa ta girma?

Veronica, cike da ladabtarwa, tace: "Peace, meye hakan? Kike ce ma babanki?"

Kwafa Abraham yayi, ya kalli matarsa yana fadin: "Ki barta kawai."

Kafin ya koma kan Islam yana fadin: "You are still lost in that delusion! I will fix you. I will fix you, Peace. You will return to Christ. You think a religion of oppression is what defines you?"

Jitai abinci ya gama, ficewa ranta baki ɗaya. Kawai ta miƙe ta ƙarasa gaban Abraham, tana ɗauke da danta daga saman cinyarta. Suka bita da ido. Ɗakinta ta wuce, ta rufe ƙofar a fusace tana saka key.

Abraham ya kalli Veronica yana fadin, "Kingani ko irin lalacewar da tarbiyyar ta ta sake yi kenan? Ai yanzu gani take kanta ne ya damu, tunda ta san namiji har tayi ciki ta haihu. Ya gama lalata min yarinya. Amma zata san da ni take magana." Ya ƙara sa yana ƙwafa, wanda yasa hankalin Veronica ya sake tashi. Ba ta son ace wani abu ya sake faruwa da zai saka family ɗinsu ya ƙara rabuwa.

Washegari bayan ta tashi, tayi sallar asubah. Kasa komawa barci tayi, saboda barcin gaba ɗaya ya kaurace mata daga ido. Ko da dare sai dai ta tashi ta yi sallah tana addu'a. Ba wai addu'a take Allah ya dawo mata da EHSAAS ba - saboda wani irin baƙin ciki ma take ji in ta tunasa - saboda yayi mata abin da nata tana tsammanin zai yi ɗin ba. Kuma tana da mugun zuciya. Addu'a take Allah ya bata ikon jurewa da cinye wannan jarrabawar, kuma Allah ya tsare mata imaninta daga faɗawa sharrin mahaifinta. Da roƙon Allah ya raya mata danta cikin tafarki na gaskiya.

Bubbuga ƙofar ɗakinta taji ana yi. Hakan ne yasa ta ƙarasa ta buɗe - Abraham Zion ta gani tsaye cikin ƙananan kayan white T-shirt da sweatpants black. Bai nemi ko izinin ta ba, ya shiga ɗakin. Ya kalli Jr da yake ta barci abinsa. Ya kalleta sama da ƙasa kafin yace, "Let's go," yana kamo hannunta. Ko damar zura hijabi bai bata ba. Ya fito da ita har zuwa falon gidan, inda ta tarar da wani farin bature yana zaune yana shan coffee, yana sanye cikin wata polished Tom Ford suit brown colour. Har da gashinsa blonde colour ne. Yana da doguwar fuska da idanuwa madaidaici da pink lips. Yana da ƙanana da murmushi mai kyau. Tun da suka haɗa ido yake mata murmushi.

Abraham ya ƙarasa yana zama, tare da nuna mata kusa da shi ta zauna. Gaba ɗaya she's feeling uncomfortable, tunda tayi aure bata taɓa tsayawa a gaban namiji wanda ba muharraminta ba a haka. Gashi sai kallonta yake cike da sha'awa, alamar ta burge shi.

Zama tayi. Abraham yayi murmushi ganin yadda Blaine ɗin ya kasa ɗauke idonsa daga kan 'yarsa. Ya kalli Islam yana fadin: "Peace, this is Mr. Blaine. And Blaine, this is my daughter Peace. I'll like the two of you to get to know each other before the wedding."

Wani irin zaro ido Islam tayi tana kallonsa kamar idanuwanta zasu faɗo. Blaine sai murmushi yake, cikin American accent ɗinsa mai ɗauke da wannan 'gonnas', yake faɗin: "Nice to meet you, Peace. You're very beautiful. You're more than what I even expected." Ya ƙarasa yana haɗe kafa.

Nan take Islam taji ta tsanesa kawai har cikin ranta.

Abraham yace ma Peace: "Na faɗa mishi you recently got divorced. Bai da matsala da hakan. Kuma he promised to give my grandson his name. Kinsan family ɗin Blaine are one of the most influential family here in LA. Peace, have you ever heard of people we call old money? Blaine's family has always been super rich. Kuma abu mafi burgewa shine yadda suke bada gudummawa sosai wajen addini - kullum cikin yi ma addini hidima suke yi. Kin tuna maigidana, one of the founders na ƙungiyarmu ta Jehovah's Witnesses? Tohm, kakansa ne Mr. Andrew Brian. Their family had always been very supportive and they knew everything that happened to you. Even Blaine here, ba shi da matsala da past ɗinki."

Yana mata bayani, Blaine na jinjina kai - irin hakane dinnan.

Islam ta buɗe baki, ta rufe - yakai sau uku tana kasa magana saboda bata taɓa expecting Abraham abinda yake shiryawa kenan ba. Tayi ma tana Musulma, zaka kawo mata arne yace ta aura? Kuma waye yace mishi mijinta yace ya saketa? Ko an taɓa aure akan aurene? Kuma ko da EHSAAS ya saketa, ita ba zata iya ƙara auren wani ba - kuma haramunne, ko da zatai aure, ta auri kāfiri?

"Dad!" ta faɗa, ta ma miƙewa tsaye. "I can't do this," ta ƙarasa tana barin gurin baki ɗaya.

Zuwa yanzu ran Abraham ya kai kololuwa gurin ɓaci. Da sauri ya kalli Blaine yana fadin: "I'm sorry, she's just overreacting. Kasan bata saniba, so the surprise cut her off guard. Ina zuwa."

Bin bayanta yayi. Aikuwa yana shiga ɗakinta, yaga ta ɗauko handbag ɗin da ta zo da shi, ta shiga zuba 'yan kayayyakin da zata buƙata - ciki kuwa har da international passport dinta. Tanata mita a cikin zuciyarta a fusace. Ya ƙarasa yana fizge jakar, yana fadin:

"Peace, ke ba ki da hankaline? Ba ki da buri a duniya? Sai na kunyata ki a idon duniya. What do you think you just did? And what are you trying to do?" Ya ƙarasa yana saurin ɗauke passport dinta da idonsa ya kai kai.

"Ba zan zauna anan ba, in dai abin da zaka ringa min kenan. I can cater for myself and my son. I have money. Just give me my passport - I'm leaving this country!"

Cikin ɗaga murya yake fadin: "Gurin mutumin da ya wulakanta ki zaki koma, eh? Ko gurin 'yan addinin da kika shiga marasa kirki zaki koma? Faɗa mini! Peace, enough is enough! I've forgiven you for your madness, but I will not watch you raise my grandson in the path of lies. You will go back to Blaine now and apologize or else I swear-"

Cike da taurin zuciya take fadin: "Apologize for what? Me nayi ma? Nifa ba zan yi aure ba. Ko an faɗa maka haka aure ke mutuwa? Mijina bai sakeni ba, kuma addinina ba ya bani damar auren kāfiri ba!"

Cike da bala'i ya ɗaga hannu zai kauda ta da mari. Ta zaro ido tana ja da baya, domin ta manta da kalar wannan rayuwar. Zuciyarta na bushewa, take fadin: "Duka? Duka? That's all you can do in your life? Beat me?" Ta dawo gabansa tana tsayawa: "Ka dake ni! Amma ka sani, ko ka kashe ni zaka yi, ba zan bi abin da kake so ba. Rayuwa ta ce kuma I'm leaving this place right now!"

Kasa dukan nata yayi, don yadda yaga idonta, ko yayi ba zai yi wani tasiri ba. Yace: "Haka kikace?"

Tace: "Eh, haka nace."

Yace: "We will see. Tsakanin ni da ke, waye kafiri? Kuma addinin ma sai kin bar shi. Kuma zan ga yadda zakibar garin ai!" Ganinta, ya juya, ya fice da international passport dinta.

Ihunsu ya tashe Jr, ya fara kuka. Da sauri ta ɗauki Jr, ta fara jijjigashi. Da mugun sauri kuma, ta tuna da passport dinta - ya fita fa a 360° ta bi bayansa. Maganganun ta fara jiyowa daga wani direction, bi tayi inda take kyautata zaton kitchen ne. Ta hango shi - ya saka wani abu a kwanon ƙarfe yana wuta.

Da sauri ta shiga ciki tana zare ido, take fadin: "Meye wannan? What did you just do? Me yasa zakai min haka?"

Veronica ma, cike da tausayin 'yar tata, take fadin: "You shouldn't have done that."

Kallon Islam yayi, cikin tsantsar mugunta, yace: "Ba dai ƙasar nan zaki bari ba, ai sai mu ga ta yadda zaki tafi ɗin. Just put this behind the back of your mind. Don't you ever think of going back to that filthy religion or country again. If I ever see you perform that blasphemous prayer again - I swear, I'll take that baby from you. I will take him far away and get him saved. I will raise him like a true son of Zion. Ba zaki sake ganinshi ba!"

Islam ta ruɗe, ta rushe da kuka tana jin ta mutu, ta lalace. Yanzu tayaya za a yi ta ceto danta daga tashin cikin kafirci? Ta cetoshi daga waɗanda suke so su halaka rayuwarsa ta hanyar kashe shi? Yanzu kuma ta kawo shi inda za a halaka imaninsa. Ta shiga uku. Sai yanzu take ƙara jin she's hating EHSAAS for what he did. Da bai ce ta bi shi ba, da bata biyoshi ba, then the iman of her child would be safe.

Wata irin fargaba ce take shigarta, fargaba irin waccan da uwa mai matuƙar kaunar danta take da shi, domin bata son danta ya tashi cikin irin rayuwar da tayi. Kuma she will do everything in her power to save him.

Ta rigada ta gama fahimta cewar Abraham Zion da ita halinsu ɗaya ne - taurin kansu da ƙafiyarsu iri ɗaya ne akan abin da suke so. Domin haka zata ja da baya, ta san ba zata taɓa nasara a kansa da zafi-zafi ba. Don haka dole ne tai ƙasa da kai, ta ja da baya domin nemar wa kanta mafita a gurinsa.

Shar hawayenta ta shiga yi, tana ƙara rungume Jr a jikinta, tana fadin: "I'm sorry, Dad. You're right. I was blind. I will never go back."

Ba tare da ya yarda da abin da tace ba, ya shiga kallonta. Veronica ma cikin mamaki take kallonta.

Islam ta haɗa hannu bibbiyu tana fadin: "Zanyi addinin naka, amma don Allah, karkace zaka min aure da Blaine. Bana son in yi aure. I just want you to focus on my child."

Cikin masifa yake fadin: "Ni dama yanzu nace zan miki aure ne? Ai ba aure nace zan miki yanzu ba. I will give you time to heal, to be yourself again. Kuma duk abin da kikaga inayi is for your well-being. Bana son inga an je lahira mun shiga heaven ni da mom ɗinki, ke in ga ana ƙona ki a hell fire, my dear. Amma ke kin kasa ganewa."

Ya ƙarasa yana kamo hannayenta: "I care for you, Peace. Tayaya kike tunanin I don't? Ke ɗin flesh ɗina ce, my only blood. Pls ki fahimce ni, ki ringa jin magana ta."

Jinjina kai tayi, kirjinta na ci gaba da nauyi, tana fitar da kalaman da ita kanta ta san ba har zuciya suke ba. Take fadin: "I hate EHSAAS too. Nasan nayi kuskure, Father. Forgive me. I won't go back to him ever again. I won't leave my religion ever again. But pls don't give me out to another man again. Banason Blaine."

Dago ta yayi, yana share mata hawaye. Ya rungumeta a jikinsa yana fadin: "I'll explain it to Blaine. Nasan zefahimta, kinji? I won't force you. Just promise me you will be with Jehovah na har abada. Zan roƙa miki yafiya. Waɗuka zunubanki, za a yafemiki. Ki zama tsarkakakkiya ta har abada."

Jinjina kai take cikin amincewa.

Veronica tayi shiru tana kallon Islam, domin tasan halin 'yarta, ta kuma san namijinta. Tasan dukkansu yaudarar juna sukeyi - babu wanda zebi ra'ayin wani daga cikinsu. Amma dai tayi shiru, for peace to reign.

Da ƙyar Islam ta ɗago, ta fice daga ɗakin tana jin zafin ƙona mata passport da yayi, kuma tana jin tsanar addininsa na ƙara samun guri a ranta.

Tana fita, ya kalli Veronica yana fadin: "Ki saka mata ido. Sam-sam ban yarda da abinda tace ba. Nasan Peace will go out of her way ta samu hanyar guduwa. Sannan duk sanda kikaga tayi sallar nan tasu, ki faɗa mini."

Jinjina kai Veronica ta shiga yi kamar uwa na bawa ɗanta umarni yana saurara. Haka ya cigaba da tsara mata yadda zata lura mai da Islam ɗin.

Tun daga wannan ranar, ya zama na Islam asace take, labewa tai sallah, in ta kulle ɗaki. Kuma sarai Veronica tasan tana yi ɗin, amma idan Abraham ya tambaya, seta ce masa ai ta daina. Ita kanta bata nuna mata tagane tana yin sallar ba.

Abraham Allah ya haɗa zuciyarsa da son Jr, don yana mugun son ɗa namiji a rayuwarsa. Jr ma na son Abraham saboda yadda yake masa wasa, yana bashi abubuwan wasa iri-iri. In ya shigo, in dai yana gida, yana jikinsa har yana fita. Lectures iri-iri dashi, duk wanda ya tambaya, waye? Cike da alfahari yake faɗa musu: "Ai jikansa ne shi yaron."

Yayi wa Blaine bayani kan abinda Islam tace. Shi kuma, dake yana ganin Islam, yaji duk duniya ba mace da yake so irin ta, yasa ya amince ze jira ta - ko shekara nawa ne har ta gama healing.

Islam ba wai ta manta da EHSAAS bane, don babu ranar da bata kulle kanta a ɗaki ta tuna da shi tai kuka ba. Amma kuma ta sawa kanta juriyar rashinsa, na ƙarfi da yaji. Da ta soma tuna abin kawai seta soma ce ma kanta: "Mijina ya mutu. Ya mutu. Baze dawo ba."

Abinda take ta nanata ma kanta kenan domin ta samu sauƙin abinda zuciyarta ke ciki.

Kuma kullum sai Abraham yana nanata mata abinda EHSAAS ɗin yayi mata cikin salon gwaba magana, musamman in yaga tayi shiru, takeɓe kanta cikin jama'a, ko kuma Blaine yazo ya yi asking ɗinta out ta ce, "A'a."

To fa, in ya fara masifa, ba mai taroshi. Bai san hakan tayar mata da wound ɗin yake yi yana zama sabo a cikin ranta ba.

Sai kaje su na zaune, ya fara fadin:

"He used you like tissue paper and threw you away, and still… you're grieving? You are not just foolish, you're blind. I told you! I told you over and over again but you chose him. And look where it got you. Broken. Alone. In my house."

Duk lokacin da ya gama faɗin hakan, sai ya shiga da'awarsa kamar wani injin Jehovah Witness. Yana nuna mata littattafansa, yana gaya mata labaran cikin Bible. Ko sau ɗaya bai taɓa tambayarta "How do you feel?" ba. Shidai abinda ya damu da shi guda ɗaya ne-shi ne ya tabbatar ta dawo cikin addininsa.

"This is your salvation. Don't throw it away for a man who's marrying another woman as we speak. EHSAAS is nothing. Islam is a lie. Wake up, my daughter!"

Za ka ji yana tisa mata lokaci zuwa lokaci. Ita kanta Veronica zuwa yanzu tausayin 'yarta ya fara cika zuciyarta. Ganin tana zama tana tunani-tunani yasa ta fara tafiya da ita shagunan ta, amma ko sun je haka, zata zauna tai shiru tana kallon wuri ɗaya-wanda hankalinta yawanci ba akan gurin yake ba, akan tunanin abinda EHSAAS yace mata ne.

A cikin kowanne dare, Abraham yana tilasta ta zama a gabansa, ya buɗe littafinsa yana karanta mata scriptures cikin harshen Turanci. Yana yi yana sata ta maimaita bayan shi, don gani yake a da can shiyayi sakaci bai koyar da ita addini ba, hakan ne yasa wani yazo yayi nasara akanta. Shi yasa ya dage gurin koyar da ita wannan karan.

A gabansa haka zata zauna tana murmushi. Ta karɓi Bible ɗin, ta karanta masa duk verses ɗin da ya karanta mata. Hakan yana muguun faranta masa. Sannan duk sanda ya kawo maganar EHSAAS, haka zata amsa da: "Yes, Daddy. You're right. I was wrong."

Gaba ɗaya ta gama sakewa da lamarin babanta, tayi losing hope akan cigaba da rayuwa. Murmushin Jr ne kawai yake keeping ɗinta alive, yana tafiyar da ita day by day.

Amma as days go on, wani irin mahaukacin depression ta shiga, seta wuni bata fito a ɗaki ba, tana zaune ita kaɗai.

Sanin tana son littattafai yasa Veronica ta siya mata shelf ɗin sabbin littattafan da tasan bata taɓa karantawa ba. Amma kwata-kwata ta daina karatu; sha'awar buɗe littafi bata yi. Sai dai in ta gaji da zaman kaɗaici, kaga ta tashi tana ta sallah.

Abin ya soma taba Veronica sosai. Wataran zakaga tazo tazauna, ta ɗauko babban gele, sun kulle ɗakin wai tana tayata sallah. A duk ƙoƙarinta na ganin ta fitar da 'yarta daga cikin damuwa, haka zata jata su je shopping, ta bata katinta don ta saya duk abinda takeso. Amma yadda ta bata, haka zata dawo mata da shi. Don komai ya daina burgeta.

Yauma fita sukayi ita da mom ɗinta siyayya, su biyu kacal. Sun bar Abraham da Jr a gida.

Mom ɗin ce ta shiga can cikin mall ɗin, tana ta siyayya. Ita dai ta tsaya ta jingina a wajen reception, tayi zurfi cikin tunani. Taji an ce...

"Aunt Islam... it's really you," Aman ya faɗa da wani yanayi na farin ciki daya daɗe bai tsinci kansa a ciki ba, saboda kwanansa uku kenan a LA yana gagararin nemanta. Saboda private investigator dinsa da Abraham ya gano, ya saka aka kama shi yana stalking dinsa. Saboda Abraham ba haka kawai yake yawo babu tsaro ba, shi yasa ya rasa address dinta.

Yanzu haka zuwa yayi nan don siyayyar kayayyakin wanka, wanda a da bai yi planning ɗin daɗewa ba-yake amfani da wanda hotel ɗin da ya sauka suka provide masa. Sai kuma yaga abin ba yadda ya tsammani ba, shi yasa ya fito don ya siya abubuwan da yake bukata.

Islam juyowa tayi tana kallonsa chak!, zuciyarta na wani irin bugawa tana jin kamar ta juya ta fita. Shi ne, saboda in ta kalli fuskar Aman tana tuna mata da EHSAAS sosai-saboda aminci da kaunar dake tsakaninsu.

"Where have you been?" Aman ya faɗa, yana kallonta cike da rauni. "I've been looking for you. Kinsan I made a promise to uncle cewa I'll always protect you if anything happens. I've searched the UK, I've called your old numbers, checked Oxford, even tried Nuristan but....."

Katse shi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu ɗaya-ba ta son taji ma duk abinda zai ce daya danganci EHSAAS. Saboda daga maganarsa ta fahimci kila har yanzu EHSAAS na can yana enjoying aurensa, har yau bai koma gida ba.

Tace: "Stop." Cikin murya mai sanyi amma cike da gajiya. "You don't have to feel guilty for losing us. You didn't lose us, Aman. I chose to leave."

Aman ya zaro ido, still confused, yace: "Aunt, what do you mean?"

"Because... the person who was supposed to be responsible for us is back. Sire is alive."

Ta ƙare maganar tana ɗauke idonta daga kan Aman, daya yi duf! Tsabar shock ɗin da ya shiga na ɗan lokaci, ya kafe ta da ido kamar yana so ya karanta ko dai ƙarya take a fuskarta.

Girgiza kai ya soma yi yana faɗin: "Uncle Prince is alive? Is alive fa kikace... ta ina?"

Jinjina masa kai tayi, tana jin farin ciki da bakin ciki na cakuduwa a ranta lokaci ɗaya. Farin cikin kasancewarsa a raye da bakin cikin abin da yayi mata. Kirjinta na wani irin sama da ƙasa, saboda bugawa da kuma zafin da yake yi mata. Muryarta na sarkewa tace:

"He's alive. He survived the accident. He was in Nigeria the whole time… and I saw him."

"Alhamdulillah…" Aman ya furta, cike da wani irin farin ciki mara misaltuwa. Ya daga hannunsa sama yana sake maimaita kalmar "Alhamdulillah." Wasu irin hawayene masu dumi suka shiga zirara a idon Islam ganin irin farin cikin da Aman yake yi-tamayi wanda ya fi na lokacin da ta gane EHSAAS yana raye.

Addu'ar da take yi daya ce: Allah yasa kada EHSAAS ya wofantar da family dinsa kamar yadda yayi mata akan mace.

Cike da kulawa Aman yace: "Aunt Islam, me yasa kike kuka? Na dauka zaki fi kowa farin cikin jin cewar Uncle EHSAAS is alive."

Tace: "I'm very happy, Aman, but it hurts. Kasan yadda nake son Sire fiye da rayuwata. You know how I suffered lokacin da aka ce min ya mutu. But Sire just chose to forget us, to move on."

Cike da rashin fahimta Aman ke tambaya: "What? What do you mean, aunty?"

Ita kanta bata san me yasa take opening up to Aman ba-kodan tasan cewa shine mutum mafi kusanci da EHSAAS bayan ita? Deep down, tana son Aman ya gaya mata kalmomi masu daɗi na cewa it's just her illusion, EHSAAS na sonta har yanzu. Koda zata samu wani ɗan hope da zai fitar da zuciyarta daga ƙuncin da take ciki a yanzu.

"He asked me to leave with my father," ta fada, idanuwanta na zubda ƙwalla. "He said he's moved on. That he's getting married. And that he wants nothing to do with me again."

Aman jinta yake in disbelief, ya soma baya yana girgiza kai. "No, no. That's not possible. EHSAAS? Marry another woman? Abandon you? Islam, this doesn't make sense... Anya ba wani mai kama da shi kika hadu da shi ba?"

Wani irin murmushin takaici tayi. "I know him more than how I know myself-that's what I thought too at first. And it didn't make sense to me either," ta fada tana dafe kirjinta. "But that's what he said. That's what he made everyone believe. He pushed me out like garbage. He told my father to take me."

Ta saki dariyar ɓacin rai. "He didn't even try to stop me. Not once."

Aman ya rik'e kansa da hannaye biyu. "Ya Allah... Babanki fa-Abraham Zion? EHSAAS ne ya bar ki tare da Abraham? Kai, impossible."

"Aina zama makaryaciya yanzu?" Islam ta fada, tana ƙoƙarin ɓoye ɓacin ranta. Ta soma zazzage fādanta kan Aman:

"You weren't there when I cried like I lost my soul. You weren't there when my own father burned my passport and said if I keep practicing Islam, he'll take my baby from me. And it's all because of what EHSAAS did, shine kake ce min impossible? I went through it all."

Zuciyar Aman kusan daina bugawa tayi saboda mamakin kalaman Islam ɗin. Domin a yadda yasan EHSAAS yana cherishing Islam, ba zai taɓa mata haka ba, kuma duk abinda tace Abraham yayi, yasan zai aikata ɗin.

"He... he did what?"

Islam ta numfasa, tana kallon wata sales woman da suke sakkowa tare da mahaifiyarta, da kaya niki-niki a hannun matar da alama kayan Mom ɗin nata ne. Ta riƙo.

A hankali ta juyo kan Aman tana faɗin, "Kasan he's a Jehovah Witness. He's trying to convert me back. He watches me. Follows me. Threatens me. I pretend to be what he wants... just to keep my son. But I never left Islam, Aman. I still pray. I hide in my room and cry to Allah."

Tausayinta ne ya cika masa zuciya. Ya ma rasa me zai ce mata don ya kwantar mata da hankali. Ya kai hannunsa saman bakinsa. He was speechless.

"EHSAAS pushed me into this," ta ƙara faɗa a hankali kamar tana wa kanta magana.

Shima Aman a hankali yake faɗin: "Maybe... maybe he has his own reasons, Aunt. Maybe he was saving you… I know how much Uncle Prince cares for you. Or maybe the man you're talking about just looks like Uncle Prince."

Daidai lokacin da Mom ɗinta take ƙaraso gurin, cikin mamaki take kallon Aman domin ta sanshi sarai-yaron EHSAAS ne. Wani irin tsoro ne ya kamata domin ta san idan Abraham ya san sun tsaya da yaron EHSAAS sun yi magana, ba ƙaramin bala'i da tashin hankali za su cokalowa kansu ba.

Riƙo hannun Islam ɗin tayi tana faɗin: "We need to go. I think I'm done for today," ba tare da ta sake kallon inda Aman yake ba.

Ta ja ta suka fice gurin da sauri. Aman ya bi bayan Islam yana tare su. Daidai zasu shiga mota yace mata: "I'll help you, I'll take you away from here. I'll find a way."

Veronica kallonsa take tana kallon Islam, domin ba ta san me yake nufi ba. Sai jin tayi Islam tace: "You can't," tana girgiza kanta. "He burned my passport. He controls everything."

Veronica tace: "Peace, kin san idan babanki yaji kina magana da shi zaki shiga matsala. So just get inside this car, mu tafi. Karki bata mana lokaci."

"Mom, one sec," tafada tana kallon Aman. Ta yi gefe ta masa alamar ya biyo ta. Shima gefen yayi. Kasa-kasa ta shiga faɗa masa wasu maganganu da sa'id da idon Aman suka ƙara firfitowa waje-da alama mamaki yake sha sosai.

Tana gamawa tace: "Help him get out of that place, pls." Ta juya tana dawowa gun Veronica da ke ta kalle-kalle tana addu'ar Allah kada a kawo wani da ya san Abraham gurin, balle kuma shi.

Cikin sauri Veronica ta shiga motar. Driver ya ja su. Hankalinta bai kwanta ba sai da taga sun haura saman babban titi.

Suna dawowa daga mosque, Paa yawuce ɗakin motsa jiki. EHSAAS ciki ya koma direct, ya nufi ɗakinsu Mehtav saboda yana ganin the more ya cigaba da ɗan lokaci ba sanar da Mehtav ainihin gaskiyar da sababin da ke ransa ba, the more zata fi getting hurt in tazo ta gane daga baya. Tabbas abinda ya faru dazun yasaka ya gane boye mata ne da yayi ba ƙaramin kuskure ya tafka ba.

A hankali ya fara ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin. In seconds, yaga anzo an buɗe-Abeey ce tsaye, ta riƙe kugu domin shigowarta ɗakin kenan. Tayi expecting Mehtav zata tsareta da tambayoyi don tasan dole zata zarginta, ko ba daɗe ko ba jima, amma sai taga Mehtav din akwance, ta lullube kanta da bargo kamar me barci, tana ta magana mata banza, ma tafi kulata. Shine ta ƙi bugun ƙofar, ta ma ɗauka Paa ne ta haɗa ta da shi. Sai kuma taga EHSAAS.

Wani irin murmushin jin daɗi tayi ganin EHSAAS yau yazo ɗakinsu da kanshi kenan. Shirinta na jiya ya tafi daidai, har ya zo nan-abinda tunda ya dawo hankalinsa, ko ƙofar ɗakin ba ya sake nufa ba.

"Good morning, handsome prince," Abeey ta faɗa da yar ƙaramar muryarta tana mai murmushi. Murmushin ya mayar mata yana faɗin, "How's your night, Abeey?" "Great," ta faɗa tana matsa mai hanya, alamar ya shigo ɗakin. Bai yi musu ba, ya shigo.

Jim kaɗan, shiru. Motsin Mehtav yayi kasa da murya yana tambayar ta: "Mehtav fa?" Gadonta ta nuna mai inda ta kwanta ta dukunkune. Ya kalla yana ɗaga gira ɗaya, because ya gane kunya take ji. Ya yi smirking, abin na ba shi dariya aransa yana raya: Just one kiss, she's silly.

Yace, "Kamar barci take ko? Gashi kuma ina son magana da ita." Yana kallon Abeey wanda yasan seta tadata. "Kora ki ko ta so-" bai gama magana ba, yaga Abeey tayi tsalle, ta faɗa saman gadon Mehtav wacce ta tashi afusace, don tana jinsu ƙasa ƙasa amma bata yi expecting Abeey zata hau ruwan ciki haka ba, kamar zata karyata.

Dariya abin ya ba EHSAAS. Ita da Abeey faɗa suka fara yi sosai kamar wasu sa'annu. Mehtav na demanding respect, ita alallai lallai Abeey ta raina ta, zata karyata meyasa zata faɗo kanta haka. Itakuma tace mata ai tasan tanaji tai musu banza, don haka ta tashi zasuyi magana da mijinta.

Da ƙyar EHSAAS ya samu yayi musu sulhu. Shima kuma don Mehtav na kunyar sa kawai ta bar Abeey ta ci bulus. Bayan an yi sulhu, aka kori Abeey waje, suka ce zasu yi magana. Ai tana fita, ta labe jikin ƙofa tana sane, ta ƙi rufewa duka don taji me zasuce.

Mehtav kallon ƙofar tayi, ta hango gefen hijab din Abeey kawai. Ta miƙe ta nufi ƙofar. Sai da ta leƙa, suka haɗa ido da Abeey wacce ta runtse ido irin ba ta so an kama ta dinnan ba. Mehtav tayi mata gwalo tana faɗin:

"Almuna funfun aisski! Ware ko ta rufo ƙofar garam!" kake ji.

Abeey ta dunkule hannu tana ji kamar ta kaima ƙofar naushi ko ta buɗe, taji me suke cewa, don tasan abu ne mai mahimmanci Prince zece-tunda ya zo da kafarsa-tana son taji abinda ya faru a ɗakinsa jiya, ko yaya ne.

---

It's Fatoumspassion! EHSAAS, don't forget to: Share Like Comment & Vote [26/06, 21:14] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

Not edited

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.