EHSAAS

Chapter 39

by @fatoumspassion

Tana rufe ƙofar ta juyo tana kallon EHSAAS da idanunsa ke kanta. A hankali ta soma takowa har ta ƙarasa daf da inda yake tsaye. Suka tsaya suna kallon juna ba tare da ɗaya daga cikinsu ya iya furta abin da ke ransa ba. Da ƙyar ta iya yin ƙasa da kanta tana jin idon shi akanta har lokacin, ta rintse ido tana tunanin abin da suka yi yau da asubah. Tana ji kamar ta nitse. So take ta buɗe baki tace masa "It was a mistake," ba nufinta ba kenan. Duk da ta san ba ita ce ta yi kissing ɗin shi ba, shine ya yi kissing ɗinta. Amma da laifinta a ciki, domin da ace ba ta je inda yake ba, da babu yadda za a yi ya yi mata abin da ya yi mata cikin barcin nasa. Tana jin haushin kanta akan hakan.

Tana cikin wannan tunanin, taji muryarsa cikin sanyi yana faɗin: "I know you deserve answers, and I owe you that much, Mehtav."

Dago ido tayi tana kallon shi, sai kuma a hankali ta koma ta zauna a gefen gadonta, tana ƙoƙarin kame kanta. Ya matso kusa da ita, amma bai zauna ba. Yana tsaye yana kallonta da idanuwansa da take jin kallon da yake mata sun mata nauyi sosai. A hankali, kamar wanda ke magana da jariri, ya yi ƙasa da murya yana tsugunnawa a gefenta ta yadda zeri inga iya kallon fuskarta da ta durƙusar, yace: "I lied to you, and that was wrong. I shouldn't have said I would marry you when deep down, I knew I couldn't."

Wani irin abu ne ya daki kirjinta a lokaci guda. Ta lumshe ido kamar za ta fashe da kuka, amma dai haka ta daure. Da ƙyar ta dago ta kallesa, alamar tana sauraron shi: "You are one of the most important people in my life. You saved me, Mehtav. I owe you my life. If it wasn't for you and Abeey, maybe I wouldn't even be here. You risked everything for me."

Ya ƙarasa yana kallonta, kamar yana ƙoƙarin karanta zuciyarta amma ya kasa gane me take tunani a wannan lokacin, domin idonta ya tsaya chak cikin nashi. Dogon numfashi ya ga ta ja tana ƙoƙarin ɓoye ƙwallar da ta zo idonta. Shima rintse ido yayi, domin da yana da wani option ɗin bayan wannan da ya zaɓe shi don skipping wannan conversation ɗin ba tare da ya yi hurting ɗinta ba. Yace: "And because of that, I can't lie to you again. I respect you too much. You deserve someone who will give you his whole heart, not half of it. Not what remains after loving someone else to death."

A hankali ya ƙarasa yana zama a kusa da ita. A hankali cikin muryarta da take ƙoƙarin sheƙewa tace: "Is it because of Islam?"

Ɗan jim yayi kafin yace: "Islam is not just someone I love… she's my life. And what I did, pretending I moved on… pushing her away… it was to protect her."

"Protect her?" Mehtav ta furta da wani irin murya mai rauni, mai cike da tausayin Islam da ita kanta. "By destroying her?" "Yes," ya ce da zuciya mai nauyi. "By keeping her away from Nuristan, from the mess I have to clean up. I need her safe, even if that means she hates me. Even if I lose her forever."

Dogon numfashi taja tana juyar da kanta gefe, sai hawaye - ga hawayen da take ta ƙoƙarin fighting kar su zuba - sun biyo kuncinta. Saboda wannan ne abin da ta daɗe tana zaton yayi. Zuciyarta ta daɗe tana saka mata cewa EHSAAS will never stop loving his wife. But hearing it from him broke her more.

Kasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta. Cikin kalamai masu sanyi take faɗin: "So all this while… all the moments I thought I mattered… I was just....." Kasa karasawa tayi, kawai ta kifa kai da gwiwa ta fara kuka kamar wata ƙaramar yarinya, tana jin haushin kanta - akan me ma zata na kuka a gabansa? Amma duk yadda ta so ta hana kukan fitowa, yaƙi yadena fitowa. Ba ta san hakan da take, sake karya zuciyarsa ne ba.

"You matter!" EHSAAS ya faɗa, yana ƙoƙarin dago da ita don ya goge mata hawayen da take, amma taƙi bashi damar haka. Cikin rada taji yana faɗa mata: "You do. You matter more than you know. But not in the way you deserve to be loved. I can't love you the way you want. I'll never be the man that completes you."

Shiru ne ya ratsasu sosai lokacin da yayi nasarar dagota ya soma share hawayenta da yatsansa, yana faɗin: "You're good. You're beautiful. You're kind. Kuma ki sani… someday, a man will come who will love every inch of you with all his heart. And you will laugh at how you almost settled for someone like me."

Ya ƙarasa yana ɗan dage mata gira ɗaya, alamar tsokana - duk dan ya lighten mood ɗinta da weight ɗin da take ji a zuciyarta na rasa shi. Wani irin bala'in kyau yayi, bala'in mata, da ya sa taji kamar ba zata taɓa iya son wani bayan shi ba.

A hankali tace: "It hurts, but I'm glad you told me."

Dafa kanta yayi a hankali, cikin sigar lallashi yake faɗin: "From today, I'll be like your big brother. One that protects you. That shows up whenever you need him. You deserve happiness, and I'll make sure you find it."

"Brother kuma? Ana zaune kalau, ni dai I'll always be your yah Mehtav. Ni ne babba?" ta ce tana dariya cikin hawaye.

Murmushi EHSAAS ya shiga yi yana goge mata hawayen, yake faɗin...

"Har aunty ma in kin so duk zan ce miki ko Your Royal Highness," heartily ya ga ta fara dariya tana girgiza kai. "A'i ni ba tsohuwa bace. Tsofaffi fa ake ce ma aunty, yayan dai nake so," ta ƙarasa tana turomai baki cikin shagwaba kamar wata Abeey.

"Silly," ya faɗa yana jan dogon ƙaramin hancinta, yace: "Yah Mehtav," cikin siga da salon da yake faɗa lokacin da ya yi losing memory ɗin shi.

Wani irin daɗi sunan yake mata in ya faɗa. Ta rufe fuska tana jin pain ɗin rasa shi na har abada. Cike da dauriya take faɗin: "Tunda love ɗin ya gagara, let's just do sibling goals. Yah Ehsaas."

Dariya suka yi tare, kafin ɗakin ya ɗau wani shiru saboda dukkansu sun rasa abin cewa. Da ƙyar Mehtav ta buɗe ido tana kallonsa. "When will you tell Islam all this?" ta tambaya. A hankali ya sauke numfashi, yace: "Soon. But not now. She's safer thinking I don't want her. I can't bring her into the fire I'm about to walk into."

Ɗan shiru tayi kafin tace: "Ya kamata ka faɗa mata dai, saboda she's heartbroken sosai." Kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace: "I'm leaving for Nuristan tomorrow."

Waro idanuwanta tayi cikin mamaki. Ya cigaba da faɗin: "I have things to fix. If I survive it… I'll come back for my family, for you guys and for Islam."

Cikin ƙaramin ƙarfin gwiwa take faɗin: "In case you need someone to cover you, you know where to find me."

Murmushi yayi yana faɗin: "You'll make a great decoy bride."

"And you'll always be my favorite heartbreaker," ta ce tana dariya itama, heartily.

Kallon agogo yayi yana miƙewa tsaye. A hankali yace: "Thank you… for everything, Mehtav. You're gold."

Cike da ƙarfin zuciya tace: "Just don't die. Don't you dare."

Murmushi yayi yana jinjina mata kai: "Not before I put everything in order," ya ce. "I promise."

---

Tsawon wunin ranar gaba ɗaya Mehtav a ɗaki tayi, ba kuka take yi ba amma dai ta kasa ƙara fitowa. Koda Inna ta zo mata da gyaran jikin da ake mata, kin yarda tayi. Sai tace mata ƙanta ne yake ciwo kawai, ta kyale ta.

Abeey tun dazun take sintiri akanta tana tambayarta me EHSAAS yace mata. Kin kulata tayi kawai saboda ba ta son magana kwata-kwata.

Abincin ranama da Abeey ta kawo mata, kasa ci tayi har sai da ta fita ta kira EHSAAS ya sakata a gaba, sannan taci. Hakadai tayi wunin ranar gaba ɗaya babu walwala.

Ba wai ba ya sonta ne ya fi damunta ba - a'a, tafiyar da yace zai yi gobe ce tafi damunta. Tasan haɗari zai shiga. What if wani abu ya same shi? What if ya zo kuma ya je Nuristan ya manta da su, bai sake waiwayensu ba? What if mission ɗinsa yayi failing?

Tuna-ninnika take yi kala-kala - da masu kyau, da marasa kyau - a lokaci guda.

Washegari kuwa da sassafe ta farka, domin bata koma sallar asubah ba. Karfe shida ta fito tana nufi kitchen, ta shiga aikin breakfast. Duk abin da ta san yana mugun so, shi ta fara dafawa. Ba ita ta kammala ba sai wurin karfe takwas, ta fito tana jera manya-manya food warmers, waɗanda Inna ke ji da su. Ba ta ma amfani da su a gidan, sai za a yi baki na musamman.

Buɗe front door ɗin da kaye ne ya sa ta juya hankalinta na komawa kan ƙofar. Paa ne ya shigo tare da Tajuddeen. Sak, tak ganin babu EHSAAS a bayansu. Gashi ta ga su ashirye, ba da kayan barci ko jallabiya da ta saba ganinsu da shi da safe ba.

Karasowa suka yi. Paa yana murmushi yake faɗin: "Kai, Allah ya yi miki albarka Mehtav, kamar kuwa kin san da yunwa na dawo cikin gidannan." Taj yace: "Our great chef, good morning." Murmushi tayi tana faɗin: "Good morning, bro."

Ta juya gurin Paa ɗaya zauna saman kujerar da ya saba zama a dining, tace: "Good morning, Papa." Yace: "Morning Mehtav. Yau da wuri aka tashi haka. Ina mutumiyar ta wuce makaranta ne?"

Girgiza ma Paa kai Mehtav tayi, don yau tana sane ta bar Abeey ta koma barci. Tana so suyi sallama da EHSAAS ne in zai tafi. Paa yace: "Fatan dai lafiya. Me yasa bata ji ba?"

Tea ta fara zuba ma Paa take faɗin: "Jiya mutumin nata ya ce min zai koma gida yau, shi yasa nace bari in barta suyi sallama. Ka san idan ya tafi bata sani ba, zata yi rigima." Taj yace: "Wai wa yana zama shi ma?" Mehtav tace: "Prince mn brother." Murmushi yayi yana faɗin: "Wannan mara mutunci ne. Za ki ce haka? Ya taso ni karfe ukun dare ina zaman zamana wai za ka kai shi airport!" Paa yace: "Tajuddeen, kai dai kawai, jininku ba a haɗe bane. Amma yaron nan yaron kirki ne. Kuma baby wanda bai bar wa sako a gidan nan ba. Abin da ka ga yasa ya tafi tsakiyar dare nan, saboda tsaronsa. It's not safe fa. Yanzun ma fatan isa lafiya muke mishi, duk da dai jirgin shi kaɗai ya ɗauka sai matuka."

Mehtav ɗaskarewa tayi tana sauraron su. Wai wane EHSAAS ɗin? EHSAAS ɗin su ne ya tafi ba tare da yayi musu sallama ba? Ko dai abin da yace mata jiya… sallamar ce?

All of a sudden, kawai sai ya tafi haka kawai. Ta ɗauka ma itace zata kai su airport. Ganin jikinta gaba ɗaya yayi sanyi yasa Paa ya kalleta yana riƙe hannunta. A hankali yake tambayarta: "Kun yi magana da shi ko?" Ɗan jinjina kai tayi tana ƙoƙarin hana kanta kuka.

Mikewa Paa yayi, ya rungumeta. A kunnenta yake rada mata: "Everything will be fine, kin ji? Za mu koma rayuwarmu kamar yadda muke yi a baya ba tare da shi ba. And zaki samu wanda zai kaunace ki fiye da yadda kika kaunace shi, bi iznillah." Ɗan jinjina kai kawai Mehtav tayi.

Taj kallonsu kawai yake yana tura breakfast ɗinsa a baki, kafin Paa yace ta zauna a gefensa. Da kansa yayi serving ɗinta breakfast. Amma ta kasa ci kwata-kwata. Daga ƙarshe ma, mikewa tayi, ta excuse kanta tace zata je tayi wanka kawai.

Ta nufi ɗakinsu tana jin ƙafafuwanta na harhardewa, tana jin muryar Taj na tambayar Paa: "Wai me ya canza ma EHSAAS ra'ayi ya tafi da sauri haka? Domin ashirin da ya ce min zai ɗauki sati biyu a ƙasar nan kafin ya tafi." Paa yace: "Allahu ta'ala a'ala. Ni ma nayi mamaki. Jiya da ina zaune ya zo ya sanar min da tafiyar tashi ba kaɗan kuma. Shine ya roƙe ni kar na sanar ma yaran, saboda ka san rigimar Abeey zata iya karya masa zuciya. Ya ji tafiyar ta fita a ransa."

Tajuddeen yace: "Allah sarki. Sun shaku sosai. Tun tana iya jiyo hirar tasu da yake da ƙarfi suke yi, har tazo ta daina."

Ta shiga ɗaki tana buga ƙofa kamar zata karya. Hakan ne ya tashe Abeey daga barcin da take yi. Ta diro daga gadon da sauri tana kallon Mehtav da ta durƙushe a ƙasa tana kuka kamar ranta zai fita.

Cike da damuwa take tambayarta: "Lafiya? Me ya faru?" "Ya tafi! Ya tafi kawai!" take faɗa mata. "Waye ya tafi?" Abeey ta shiga tambaya, looking very confused.

EHSAAS ya koma garin su. Wani irin faɗuwa kirjin Abeey yayi. Tace: "What? Yah Mehtav, me kike cewa? Ta yaya zai tafi bai mana sallama ba?" Da sauri ta buɗe ƙofar ɗakin, ta fice da niyyar ko bai yi nisa ba ta tare shi.

NURISTAN

Mimah ce ke kaiwa tana komowa ita kadai a cikin falon Mai Babban Daki. Ta kasa zaune, ta kasa tsaye. Hannayenta rike da waya, sai faman kiraye-kirayen waya take yi. Amma duk wanda ya daga, babu abin da suke ce mata banda ban hakuri, nacewar su ma fa ba su san wanda ya kwace kayan ba.

Mai Babban Daki kallonta take cike da zakuwa, domin haka kawai taga Mimah ta shigo mata a haukace kamar zautacciya tana waya wai an kwace kayanta a border.

Kiran da tayi na ƙarshe ya sa ta fara ɗura ashar tana zagin mutumin: "Kayan nawa kake cewa an kwace? Dan kutumar ubanka! Ka san ni wacece a cikin ƙasar nan? For God's sake, me kuka ɗauke matsayin Princess ne? Yau idan naga dama, Nuristan zata zama tawa. I am King Nashwan's only daughter! Ba da kowa se ni! Yanzu kake faɗa min haka? Uban waye ya ba da order wai a tare min da kaya, eh?"

Wanda ke wayar, cikin rawar murya saboda tashin hankalin da yake ciki, yana tsakiyar jami'an tsaron na farin kaya da suka kama shi kuma suka saka shi amsa wayar Mimah. Da dole yake faɗin: "Is someone powerful ne ke riƙe da ƙasar nan bayan mahaifinki."

Cike da mamaki da kadawa, ta kalli wayar tana faɗin: "Ka tabbata?" Zuciyarta na raya mata Erfan ne ke son cin amanarta, wato don ta faɗa masa plan dinta da kalar arzikin da zata yi in kayanta suka shiga, shine zai go behind her back ya ci amanarta? Ko yau ko, zega other side of her da bai taɓa gani ba tun da yake a rayuwarsa.

Katse wayar tayi, tana kallon mahaifiyarta. Cike da bada umarni take faɗin: "Umma, kikiramin saurayin ki nan yanzunnan." Mai Babban Daki cikin lallabi take faɗin: "Yar nan, ba za a yi haka ba. Na san Erfan ba zai taɓa iya cin amanarki ba."

Wani irin kallonta Mika tayi da idanuwanta daya kaɗa yayi jajir, take faɗin: "Kin san meye kuɗi kuwa? Kodayake na miki uzuri, you never belong cikin category ɗinmu na 'yayan manya. Shi yasa kike ganin kuɗi ba zai iya canza mutum ba."

Mai Babban Daki, cike da takaici take faɗin: "Ke Mimah! Ni fa mahaifiyarki ce kike kallo kina faɗa min irin waɗannan banzayen kalaman?"

Mimah karasowa tayi tana ɗaukar wayar uwar a saman cinyarta kamar wata sa'arta. Taka hannunta, ta saka fingerprint dinta, ta buɗe wayar. Direct ta lalubo lambar Erfan da uwar, saboda badda kama, ta saving da Sadauki. Tashiga kiransa. Bugun farko ya daga, wanda tasan in itace ta mai, ba zai daga ba.

"Kana ina?" ta ji Mimah ta tambaye shi a tsaitsaye kamar wani sa'anta, yadda dai ta saba mai magana. A hankali yake faɗin: "Menene ya faru, Gimbiya?" Cikin datse maganarsa take faɗin: "Ina tambayarka kana tambayata? Kana ina nace?" Ta ƙarasa tambaya cike da fushi, tana kasa holding anger dinta. A sanyaye taji yace: "Ina bangaren Mai Martaba. Jikinsa ne ya motsa… yanzun likita…"

Bai ƙarasa maganar ba, ta cilla wa Mai Babban Daki wayar. Ta ɗauki key ɗin motarta da purse ɗin da ta shigo da shi, ta fice kamar guguwa.

Irin biliyoyin da ta kashe kawai take tunawa. Tana jin idan kayan nan suka salwanta, zarewa zata yi baki ɗaya.

Bangaren Mai Martaba ta wuce direct, dake musamman da ba shi da lafiya. Nan ita da Fulani da sauran matansa ba su da restrictions da shiga bangen, ko damu ba ta yi ba da yadda masu gadin suka yi yawa a bangaren kuma suke ta gaishe ta, bata amsa ba.

A babban falon ta tarar da Erfan ya rako manya-manyan likitocin waje suna tattaunawa. Gaba dayansu durƙusawa suka yi suna miƙa gaisuwarsu gurinta. Da ƙyar ta daure ta amsa ba tare da ta tambayi ya jikin Mai Martaban ba, kawai tace: "Sufita, ku bamu guri. Za mu yi magana."

Basu musa mata ba suka fice. Suna fita, Erfan ya buɗe baki zai mata magana, ta tari numfashinsa tana faɗin: "Kafin ka ci amanata, kai tunanin consequences ɗin da zasu iya biyo baya, Kawun Erfan. Ko kuma ince Wazirin Nuristan. Ina kayana?"

Cike da mamaki yake faɗin: "Gimbiya, calm down. Mu fita mu yi magana…"

Cike da fusata, ta jefar da jakarta tana faɗin: "Babu inda zan je! Anan zaka faɗa min inda kayana suke. Saboda duk fadin ƙasar nan, babu wanda yake da power ɗin da kake da ita a yanzu. Kana tunanin zan yarda Mai Martaba wanda bai ma san inda kansa yake ba zai tashi lokaci ɗaya yace a fara kwace kaya a border?"

"Mimah!" Erfan ya faɗa yana ɗan ɗaga murya, domin ya san Yar Fulani can cikin turakar Mai Martaba, tare da Sarauniya Hassana, yana tsoron ɗaya daga cikinsu ya fito: "Kisan me kike faɗa a nan gurin? Kuma kisan da wa nake magana?" Kallonsa tayi sama da ƙasa tana nunashi da yatsa kafin tace, "Waye kai? Kaiba kowa bane se bawa, duk da kasancewar ka ɗan sarki na fari. You lack the competence to hold this country. Shiyasa gashi nan kullum kana gindin kaninka kana bauta masa saboda kai ɗin da babu."

A bazata taga ya ɗaga hannu ya gaurama ta mari, cike da takaicin jin 'yar cikinsa tana mai wannan zagin. Saboda har yanzu bai manta da cewa this throne actually belongs to him, aka tsallake shi aka ba Nashwan saboda shi ɗin ɗan baiwa ne.

Kuma har yanzu bai manta da mahaifiyarsa na kulle a cikin prison ɗin Nuristan, ana jiran ranar da za a yi executing ɗinta.

Har yanzu bai manta cewa 'yarsa mafi soyuwa a gare shi tana prison, kuma a prison zata ƙare rayuwarta - saboda Nashwan.

Taya zata cigaba da gaya masa how incompetent he is? Kuma ba zai taɓa mantawa da cewa ɗaya daga cikin yayansa yanzu tana rayuwa a matsayin 'yar Nashwan ba.

Kuma itace take tsaye a gabansa tana zaginsa, yana matsayin kawunta - wan ubanta - a cikin idanuwanta.

"Ni ka mara?" Mimah ta ƙara sa fāda tana dafe kuncinta, idanuwanta sun yi jajir kamar garwashi.

Ɗaga hannu tayi zata rama marinsa, daga baya taji an ɗaka mata tsawa ana faɗin, "Mimah!"

Koda bata ga mai maganar ba, ta tabbatar Fulani ce. Amma hakan bai hana ta ƙarasa kifawa mai mari ba, wanda yasa taji salati ya fara tashi daga bayanta.

Sarauniya Hassana ce wannan karon, tana tafo hannu. Mimah da ta kasa controlling kanta, ta rama.

Wani irin dana-sani ne ya shiga zuciyarta. Bata san yadda za a yi yanzu ta kare kanta daga idon Fulani ba, da take mata kallo saint-like.

A take taji innaa, dubunta ba zata taɓa cika yanzu ba.

A bazata suka ga ta kama kwalarsa, ta fashe da kuka tana faɗin, "Why would you do that to EHSAAS? Why? Na ɗauka mu duka ka ɗauke mu abu ɗaya ne kamar 'ya'yanka. Ashe daidai da rana ɗaya baka taɓa ɗaukar mu naka ba. Meyasa kawu? Meyasa?"

Ta ƙarasa faɗa tana dukan kirjinsa. Dayasa yaji ya daskare a gurin saboda duk iya sharrin da makircinsa, ba a taɓa ƙoƙarin ɗaure shi da jijiyoyin wuyansa kamar yau ɗin ba.

Fulani, that is looking very confused, kallonsu kawai take. Jin an ambaci sunan EHSAAS, taji zazzabi na ƙoƙarin kamata.

Sarauniya Hassana ce take faɗin, "Mimah, wai me ke faruwa ne? Kawun naki kika ɗaga hannu kika mara, kike duka haka?"

Kamar jira take a mata tambayar, ta juya tana kuka. In ka ganta zaka rantse da Allah wani ne daga cikin iyayenta suka mutu.

Ta shiga nunashi tana shassheƙa tana ja da baya tana faɗin, "Shine nan! Ya kashe EHSAAS. He planned everything! I have the evidence - the recording of them planning everything together, shi da Jay. I got this message from anonymous number!"

Da sauri ta tsugunna tana ɗaukar wayarta. Hannunta na rawa, ta fara scrolling recording ɗin. Da ta kunna musu, muryar su biyun ce - rangadadau suna kulla yadda za a kashe EHSAAS a hanyarsa ta dawowa daga Nigeria.

Fulani wani irin jiri-jiri taji ya zo mata zata faɗi. Da sauri Hajiya Hassana ta tareta tana faɗin, "Subhanallahi!"

Mimah ta taho da gudu tana rungume ta, tana ƙara faɗin, "Maama, sune! Sune suka kashe min kanina! Sune suka kashe min EHSAAS ɗina, Maama!"

Rungumeta Fulani tayi baya. Wani irin hawaye masu ɗumi suna sauka a iduwanta.

Tana jin mutuwar ɗanta na dawo mata sabuwa, saboda a da can tana zargi - ne saboda Islam.

Ta daɗe da faɗa mata hakan, amma saboda da zato zunubi ne, yasa ta kasa yarda, ta kasa gasgata.

Amma yanzu da take jin wannan maganar tare da hujja mai ƙarfi, ji take yi inama ita suka raba da duniya, ba ɗanta ba.

Me EHSAAS ya musu? Her only son?

Erfan kallon Mimah kawai yake, speechless. Don bai taɓa tunanin zata iya yimai haka ba - 'yar cikinsa itace zata kawo ƙarshensa.

Matsin lokacin da Gimbiya Hassana ta danna danger alert na sashen, ba a jima ba, ga dogarai a seconds sun zagaye su.

Hannun Hassana na rawa take faɗin, "Ku kamashi! Shine nan ya kashe Yarima! Allah dai yau ya tono asirinsa, ku kamashi nace!"

Gaba ɗayansu kasa tabashi sukayi, domin sun san kalar matsayinsa a gurin Mai Martaba. Kuma sun san, tabashi ba tare da order mai kyau ba, zai iya saka su cikin matsala babba a cikin ƙasar nan.

"Kai! Wai ba ku ji me nace ba? Ba za ku kamashi ba?" Kallonsa suke kamar yadda shi kuma idonsa ya kasa sauka akan Mimah.

Daidai shigowar Mai Babban Daki, akwazare. Tunda taga fitowar Mimah, hankalinta ya tashi ta kasa zama, sai da ta biyo ta.

Ganin dogarai sun cika falon da ba a shigowa sai da ƙwarin dalili, yasa jikinta ya soma rawa. Tana kallon tijarar da Gimbiya Hassana take yi, idonta ne ya faɗa cikin na Mimah, dake rungume da Fulani suna kuka kamar ransu zai fita.

Hassana, ganin ba za su ji maganarta ba, yasa ta kalli Fulani tana faɗin, "Ranki ya daɗe, in ba ke kika ce musu magana ba, ba za su kamashi ba."

A hankali Fulani ta dago, tana kallon Erfan.

Gabansa ta ƙarasa, tana kallonsa cike da wani irin raɗaɗi irin na uwa wadda ta rasa ɗanta, kuma take kallon makashin ɗanta a gabanta.

Tana faɗin: "Me yayi maka? Me EHSAAS ya taɓa maka a rayuwarka da ka zaɓi hukunta shi da mutuwa? Mutuwa ka rabashi da matarsa, ɗansa, mahaifinsa da mahaifiyarsa? Kai wa ne irin azzalumi ne?"

Rintse ido yayi, domin at this end ya san cewa tashi ta ƙare baki ɗaya.

Yana kallon Fulani tana kallonsa da wani irin azaba da bai taɓa gani a cikin idonta ba. Kuma ya san na Mai Martaba sai ya fi haka - saboda yadda yake ƙaunar EHSAAS.

Yasan rashin EHSAAS ne yasa yake kwance haka - da kuma abinda Jay ya yi masa.

Kallon Mimah yayi yana faɗin: "I'm a sinner. Na tabbatar ni ɗin sinner ne babba. Gashi babban sin ɗin cikin rayuwata ya kawo ni ƙarshe. Daman an ce kyau da ya gaji ubansa - kin yi mummunan gadon. Kisani, yadda kika tarwatsani yanzu, haka naki ɗan zai tarwatsa ki. Lokaci na nan zuwa. Duk abinda ka yi sai an maka, duk abinda kika yi min kisani sai an miki shi kema."

Mimah, cike da borin kunya take faɗin: "Saboda na faɗi gaskiya na tono asirin duk abinda kake yi? Ka sani, ni ba 'yar ka bace. Kuma ƙarshena ba zai taɓa zama irin naka ba. Kuma ba zan taɓa zama mace kamarka ba. Saboda iyayena duka mutanen kirki ne, tsatsona mai daraja ne. Mahaifana ba su taɓa kashe kowa ba."

Wani mugun murmushi yayi kafin ya kalli Mai Babban Daki dake kallonsu biyun, cike da fargaba, don ta san tata ta kare tun da Mimah ta taro mata wannan tashin hankalin. Shiyasa ake cewa yaro bai san wuta ba sai ya taka.

"Ke 'dib flesh ɗina ce kuma blood ɗina. In kina tantama, kuma, ungo wannan-" Ya ƙarasa yana tsigo gashi daga cikin sumar sa da ta soma furfura sosai.

Ya ƙarasa yana ɗanka mata: "Conduct a DNA test. Na tabbata cewa zaki gaskata abin da nace. Ke yatace NASHWAN ba zai taɓa haifar mugun iri kamar ki ba."

Zubarwa tayi kamar ta taɓa wuta. Tana wara ido tana kallon mahaifiyarta, saboda she never expected this at this point.

She is speechless.

"Karya kake!" Erfan yaji an furta daga baya, wanda yasa gaba dayansu suka juya.

Mai Martaba ne, tare da hadimansa, sun turo shi a wheelchair. Fuskar nan tasa tayi duhu saboda jinya.

He looks very pale, kamar wanda ya shafe shekaru da shekaru yana jinya.

"Ka manta abin da ya faru da mahaifiyarka kenan lokacin da tayi questioning identity ɗin ɗana? Yanzu kana son ka maimaita kuskuren da tayi? Kasani zan lamunci komai - amma banda taɓa mutuncin matana."

Ya ƙarasa yana kallon Mai Babban Daki, da ta shiga zubda hawaye kamar ruwa. Saboda yadda take jin tata ta kare, kamar ta rufe Mimah da duka da ta kwanto mata wannan masifar.

Tasan Erfan will never go down alone.

Erfan ne ya ƙaraso gabansa yana faɗin: "Na sani. And I know the consequences. Shiyasa nake sanar mata domin ta san cewa she is not who she thinks she is. Ita ɗin nobody ce. Kamata kuma ita ɗin 'yar mutumin da take kira 'incompetent' ce. Ita ɗin 'yar wanda ta marace."

Cike da kaɗuwa yake kallon Mimah, jin an ce ta mari wan ubanta.

Mimah daskarewa tayi, tana jiran taga reaction ɗin Mai Martaba. Tana son taga yadda zai sa a kama Erfan, a tsire shi saboda ya shegantata.

Sai taga yayi murmushi kawai yana faɗin: "Mimah, yatace-kuma har abada zata cigaba da kasancewa 'yata. Kuma kai ma ubanta ne har abada, saboda kai ɗan uwana ne."

Ya ƙarasa maganar in riddle, yana kallon dogarai, alama ɗaya yayi musu.

Erfan yaga an fara dragging ɗinsa zuwa waje. Kallon Mimah yake yana faɗin: "Sai kin yi dana-sani lokacin da ba zai taɓa miki amfani ba har abada."

Fulani ce ta ƙaraso kusa da Mai Martaba, ta tallafo kansa tana rungume shi. Saboda ta san pain ɗin da yake ciki.

Ace 'yan uwanka gaba ɗaya babu wanda yake kaunarka tsakani da Allah saboda mulki. Ace 'yan uwanka sune suka kashe maka ɗanka tilo a rayuwa.

Tasan she just can't imagine irin heartbreak ɗin da Mai Martaba yake going through.

Ita ɗan nata kawai ta rasa - shi kuma yarasa 'yan uwansa duka. Biyun waɗanda duk duniya ba shi da kamarsu-saboda mulki da son duniya.

Kowa kasa motsi yayi a falon bayan fitar dogarai suka yi tare da Erfan, wanda kowa ya san a dark cell za su jefa shi har sai lokacin da za a san yadda za a yi da shi.

Mai Babban Daki kasa kallon idon Mai Martaba tayi. Saboda daga yadda yayi magana da Erfan, ya nuna kamar yana da masaniya akan wani abu wanda shi bai sani ba.

Da kuma yadda yake claiming Mimah 'yar sa ce despite all odds, ba tare da wani zargin komai ba, ya ƙara saka zuciyarta cikin shakku mai tarin yawa.

Da ƙyar ta iya ƙarasowa gefensa da Fulani ke rungume da shi. Ita da Fulani suka tura shi don mayar da shi daki, Sarauniya Hassana na bin su a baya.

Mimah na tabbatar da cewa sun fita, ta tsugunna. Ta soma laluben gashin da Erfan ya ɗanka mata. Hannunta na rawa, saboda tana son tayi conducting DNA ta tabbatar - mai dacewa - ita ɗin ba 'yar sa bace.

Her mind will never be at ease in har bata yi ba.

Tana ƙarasa ɗibawa, ta fice daga falon. Cikin gari ta shiga, saboda ba zata iya ɗaukar risk ɗin yin DNA a palace ba - ko kaɗan.

Bayan sun kwantar da Mai Martaba a daki, gaba dayansu jigum-jigum suka yi suna kallon shi. Domin kai kana ganin yanayinsa kasan ciwan ya riga ya gama cin ƙarfin jikinsa lokaci ɗaya - abu ne mai mugun wuya ya yi surviving.

A hankali yake kallonsu ɗaya bayan ɗaya kafin ya ce, "Asiya."

Dagawa Mai Babban Daki tayi tana amsawa. Jiki a sanyaye ya kalli Fulani yana faɗin, "Hajar," itama ta ɗago tana kallonsa cike da tausayawa da kauna. Ya koma da idonsa kan Sarauniya Hassana yana faɗin: "Hassana," ta amsa tana matsowa kusa da shi don ta fahimci magana yake so yayi da duka su ukun.

"Kudin gaba ɗaya matana ne na sunnah. A cikinku idan akwai wacce na taɓa cutarwa a zamanmu na tare ko nai mata wani rashin adalci, ina roƙon ku yafe mini. Kusani kasancewata shugaban wannan daular baya nuna cewa nima ba ɗan Adam bane. Nima ɗan Adam ne kuma ina yin kura-kurai. Amma abu ɗaya na sani - cewa duk abin da ya shafi iyalina ina ɗaukarsa da matuƙar mahimmanci. Ina ƙoƙarin sauke duk wani haƙƙin da Allah ya ɗauramin a kanku. In kuma bana yi, ku faɗa mini don Allah."

Ya faɗa cike da murya wacce ba su taɓa jin yanayin irinta ba - saboda wani abu daya toƙare masa zuciya, yana jin kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu.

Gaba ɗayansu jikinsu sanyi yayi - musamman Mai Babban Daki da ta san da ita a je maganar indirectly.

"Kai ɗin adalin mijine, kamar yadda ka kasance adalin shugaba a cikin ƙasarmu mai girma. Ban taɓa ganin ka shiga haƙƙin wata ba cikinmu. Ni dai ba ka taɓa shiga nawa ba - sai dai in cikin rashin sani da kishi namu na mata da ba a rasa ba."

Gimbiya Hassana ta ƙare da faɗa a sanyaye tana kallonsa.

Kallon Fulani yayi. Da sauri ta ƙarasa tana kama hannunsa. Ta kai hannayenta, tana pecking knuckles ɗinsa cike da kauna. Tana fara girgiza kai - kana gani kasan sonsa da shakuwar da suke da shi daban yake da na sauran matan. Kuma duk ta fi su kuruciya. Duk da ta girme Hassana, amma yanayin kyan jikinta da yadda take kula da kanta yasa ta fi Hassana kyan gani.

"Fulani, na kibar kuka ki faɗa mini idan na taɓa zalintar ki a zaman aurenmu?"

Hararar wasa ta galla masa, tana girgiza kai: "Ba ka mini komai ba - bayan tarin alheranka gareni. You're the best husband ever," ta ƙare da faɗa tana ce musu ko alamar su amince da abin da tace.

Hassana tabe baki tayi tana faɗin: "Eh fah."

Mai Babban Daki se zare ido take kamar shege arabon gado. Hannunsa ya miƙa mata alamar ta ƙaraso gare shi. Ta ƙarasa tana hawaye. Ta kama hannunsa - wani irin squeezing hannun taji yayi.

It's not ordinary squeeze - don duk da kasancewarsa shugaba, in dai yana cikin turakar iyalinsa, sauke mulki yake yi, yana basu duk wani attention da kulawa da suke bukata.

Hakan ne yasa ta gane wannan squeeze ɗin is not natural - irin wanda yake yi if he is prostrated.

"Asiya na… zo Asiya. Ki faɗa mini, in na taɓa tauye miki haƙƙinki na aure da yake kaina. I'm I not enough?"

Ya faɗa yana ƙoƙarin haɗiye baƙin cikin da yake ransa.

Girgiza masa kai tayi saboda Mai Martaba has always been good to her. Ya san cewa duk cikin matansa, tafisu buƙatu na aure da na abubuwan al'ati na duniya. Hakan ne yasa idan lokacinsa zai bata, yana tabbatar da cewa ta samu satisfaction yadda ya kamata. Kuma duk sanda ya samu dama, ko ba lokacin da ya kamata ba, yana aika mata sako don tazo gare shi.

Tunawa da duk sauran mazan da take bi - it's just sex. Amma Mai Martaba is a lot more - shi na daban ne. He was very caring towards her. Duk da ta san cewa zuciyarsa na tare da Hajar, amma baya taɓa nuna mata hakan - musamman in yana tare da ita.

Jikinta gaba ɗaya rawa yake yi tana jin danasani mara iyaka ya baibayeta. Tana jin in da ma bata biye wa zuciya da zugar shaiɗan ta biye wa Erfan ya nuna mata wannan hanyar ba… It all started as a mistake - lokacin da ya fara taɓata tasamu cikin Mimah.

Tagane ashe tana haihuwa NASHWAN ne matsalar. Bayan tasamu ciki, she tried to cut ties tana tunanin ta rigada tasamu abin da take so.

Amma kash! Sai Allah ya bata ya mace - wacce ba ita take buƙatar haihuwa ba.

She tried again - not once, not twice, not thrice - har lokacin da tayi losing count, sai process ɗin ya ƙi.

Sai ta fara gwadawa da wasu mazan. A duk iya ƙoƙarinta na ganin cewa ta haifa wa Mai Martaba na gaji - har abin yazo, ya riga yazama jikinta.

It's like addiction. She's always looking for one man or the other.

"Asiya, Mimah 'yata ce?" "Yata ce, ko." Ya faɗa cikin sigar assuring kansa cewa 'yarsa ce kuma babu abin da ya isa ya canza hakan, cike da tsoron jin amsarta. Saboda yana tunawa sanda ya fara ɗaukar Mimah a hannunsa the first time da yaji yazama uba - that fatherly love.

Yadda yake goyata yana tafiya da ita gurin aikinsa tun yana prince, rintse idonsa yayi yana sauraron kukan Mai Babban Daki a cikin kunnensa, wanda ya sa ya fara wani irin tari kamar ransa zai fita.

Duka matan suka rirrikeshi. Hannunsa a saman bakinsa ya buɗe - sega jini.

Fulani loosing vision ta soma yi saboda ganin halin da mijinta - mafi soyuwa a gareta - ɗaya rage mata, yana ƙoƙarin shima ya tafi, ya barta.

Daidai ana buɗe ƙofar ɗakin, wanda ya sa Sarauniya Hassana juyawa tana ƙoƙarin ganin wanda ya ke da audacity ɗin shigowa wannan sashen.

Ya shigo ɗakin nan direct, ba tare da wani ya iya dakatar da shi ba.

Idonta ne ya sauka akan fararen piercing eyes ɗin shi - ɗaya tsaya chak yana kallon mahaifiyarsa, data rikice gaba ɗaya tana kallon mijinta tana ƙoƙarin hanashi yin tarin.

---

It's fatoumspassion EHSAAS Share Comment Like & Vote [27/06, 21:02] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's Fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.