Chapter 40
Ahankali Fulani ta shiga kokarin bude idanuwanta tana jin sun mata wani irin nauyi kamar an daura mata wani abu a saman su. Duk da har lokacin bata dawo daidai ba, amma tana jin lallausan hannayen da suka fi mata kama da na danta wanda ba zata taba mantawa da shi ba. Cikin nata ta runtse ido tana rokon Allah idan mafarki take yi, kada Allah ya bata ikon tashi daga shi, in dai zata kasance tare da EHSAAS dinta.
Danshin lips dinsa da ta ji saman knuckles dinsa ya sa ta ji abin kamar gaske. Ta bude idonta baki daya tana kallonsa. Murmushi taga ya sako mata, kyawawan dimples dinsa irin nata ya bayyana a kokarinsa na sa ta farin ciki, amma ta gano damuwa a can cikin idanuwansa - damuwarsa a kanta akan kuma halin da mahaifinsa ke ciki.
"Maama," ya fada gently, yana sake rike hannunta dake cikin nashi.
Fashewa tayi da kuka, hawaye na bin cheeks dinta. Ahankali ta shiga fadin, "Babana... babana, kaine! Kaine!"
Da sauri ya rukufa yana tallafota, ya rungumeta irin runguma mai cike da kauna - irin ta da da uwa da suka yi tunanin sun rabu har abada, ba za su sake haduwa ba. Kankameshi tayi tana jika masa gaban rigarsa da hawayenta, tana fadin:
"Where have you been? Na yi tunanin mun rasa ka. Me ya same ka? Me ya faru da kai?"
Ta karasa fada tana dagoshi daga jikinta, tana kallon cikin idonsa tana jiran answer.
"Calm down, maama," ya shiga fada mata gently, yana shafa bayanta kamar yadda ake ma kananan yara.
Da kyar ya samu ta dena kukan, amma bata rabu da shi ba. Tana ganin kamar tana kyale shi ne za ta farka a ce mata ba gaske bane, kamar yadda tayi tsammani.
"You're not dead?" ta fada ahankali kamar mai tambayar kanta.
Jinjina mata kai yayi yana zama kusa da ita, hannunsa cikin nata. Ya kwantar da kanta dake mata mugun nauyi a mafarki yana fadin, "I'm alive, mama. Ina nan tare da ke."
Sai a lokacin ta dago tana kallon inda take - nan din ba sashen ta bane. Kasancewar ta haddace duk wani daki da lungu da sako na bangaren Mai Martaba, ta gane cewa a cikin bangarensa suke.
Hakan ne yasa tayi saurin kallon EHSAAS tana tuna abinda ya faru har ta sume, ta tashi ta tsinci kanta tare da shi a gefensa.
"Baban ka EHSAAS, Mai Martaba... me ya same shi?" ta tambaya tana kokarin mikewa.
Da sauri ya rikota yana fadin, "He's in the next room. Attack ne ya samu, maama."
Dan kallonsa tayi, domin ta san sun dade suna boyewa EHSAAS ciwon mahaifinsa - babu wanda ya sani a kaf fadin duniyar nan cewa Mai Martaba yana da matsalar zuciya, sai ita kadai da mahaifiyarsa (Allah ya yi mata rahma).
"Is he okay?" ta tambaya tana kallon cikin idonsa.
Ya jinjina kai yana fadin, "He will be fine, maama, in sha Allah."
Ya yi muttering ahankali saboda shi kansa ya karaya da yadda ya ga mahaifin nashi - wanda shima ko samun damar ganawa basu yi ba. Ya yi passing out, duka wani medical facility yana dashi na musamman a dakin da ake duba shi duk sanda ba shi da lafiya. A sashensa ne, babu bukatar kaishi asibiti. Likitocinsa kawai aka kira.
EHSAAS idonshi kamar garwashi saboda bai san ga halin da mahaifinsa ke ciki ba. Da ya sani da tuntuni ya zo gareshi - koda ganinsa zai sanyaya masa, ya rage masa radadin rashin mahaifiyarsa da yayi da kuma 'yan uwansa da suke neman rayuwarsa da ta danshi ido rufe ba.
EHSAAS kana raye? Ya ji Fulani ta sake tambaya cikin sigar so, ya sake reassuring dinta shi ɗinne. Baice mata komai ba face kama yatsunta da yayi, yasa cikin bakinsa ya gatsa. Zafin da ta ji ya ratsata yasa tayi saurin janyewa da sauri tana kallonsa, ta dan ture masa goshi cike da shakuwa irin ta da da uwa, tana fadin:
"Me hali ai baya fasawa! Wato cin zalin nawa zaka ci gaba da yi? Ko wanda kai da yarinta ba ishe ka ba ko?"
Murmushi yayi mai sanyaya ranta yace, "Tun dazun kinganni, kin tabani amma kin kasa yarda ni ɗinne. Shiyasa na cijeki, in kika ji ai zaki yarda."
Jinjina kai tayi tana murmushi, hakoran mamakanta na fitowa. Ta sake rungume shi yanaji tana ta hamdala, tana sauke ajiyar zuciya, kafin wani irin tsoro ya dabaibayeta. Ta dago, kasa iya hada ido da shi tayi. Kawai sai ya ga hawaye na bin kuncinta.
Ahankali, cike da damuwa, yake fadin, "Maama, he will be fine, in sha Allah."
Girgiza kai ta shiga yi tana fadin, "Ba shi ba EHSAAS! Ka yi hakuri... I'm sorry. I'm so sorry, ban iya protecting amanar da ka bani ba."
Dan jim yayi sanin inda maganar ta tado, sai ya kalli dakin baki ɗaya. Sanin the walls have ears yasa ya shiga goge mata hawaye yana fadin, "I've heard about them. Duk inda suke a fadin duniyar nan zan nemo su in sha Allah. Nasan Islam is safe a duk inda take. Na yarda Ubangijina zai kareta."
Sosai Fulani ta shiga kuka tana fada masa yadda Islam ta taɓa convincing dinta cewar kannen mijinta da na hannu a kisan sa. Ta ki yarda. Cikin shashsheka ta dago tana fadin:
"Tasha wahala sosai saboda abinda ya same ka. Bata iya haihuwa da kanta ba. It was a miracle da yarinyar nan ta yi surviving. Tana matuƙar kaunar ka fiye da mu baki ɗaya. Tafi kowa wahalar rashinka a cikinmu. Ta zama marainiya - ba uwa, ba uba, babu kai. Gashi ni ɗin da take ma kallon uwa, na kasa yarda da ita. I thought kawai… kawai shirmenta ne na yarinta. Ashe ita da gaskiyarta.
(Sai ta kalli EHSAAS, ta kalli dakin kamar tana gudun wani ya jisu, ta shiga rada mai cike da jin kai): "Mimah... yanzun na ji, nima zuciyata bata yarda da ita ba. Duk da ina mata kallon yar da na haifa a cikina, amma ba hakan ne zaisa in barta idan har tana da hannu a cikin abinda ya same ka ba."
Cikin dan mamaki da jin abinda mahaifiyarsa ke fada akan Mimah - da take kira first daughter dinta - yasa ya dan girgiza kai yana tambayar, "Meyasa kike son in bincike ta maama?"
Cikin son gasgata zarginsa cewar Islam ta san wani abu game da Mimah shiyasa take bibiyar rayuwarta, itama tace: "Saboda ranar da ta farfado, ta hana ta ɗaukar mata yaro, ta mata rashin kunya sosai fiye da tunani. I even scolded the poor child. But after everything da ya faru yanzun, with all this, zuciyata bata yarda da ita ba. Gashi Erfan yace ba 'yar Mai Martaba bace ba 'yar shi ba ce bafa."
Fulani ta cigaba da ba ma EHSAAS labari cike da kaɗuwa. Kana ganinta kasan a rikice take. For the first time, the calm Fulani Hajar is not composed saboda abin ya gigita ta. Tace: "Sunason su kashe babanka, EHSAAS. Baƙin ciki kullum suke kunsa mai. Na tabbata wannan maganar ce ta sake tayar da ciwansa. Yana matuƙar kaunar Mimah. Banajin zai iya leaving da wannan gaskiyar."
Lallashinta ya shiga yi ganin ta ki daina kuka. Gashi gaba ɗaya jikinta rawa yake yi. Yasa ya jawo wayarsa. Typing taga yayi, bata san me ya rubuta ba.
Sai ga likitar ta nan - wata dattijuwar mata ta karaso wacce za ta girme mata a shekarun haihuwa. Fulani ko kallon matar bata yi ba, tana jikin EHSAAS kamar wani zai kwace mata shi. Tana ce masa: "Ya ce ci... babansa... bazata iya rayuwa babu shi ba."
Har Dr. ta tsira mata allurar barcin da ta rigada ta haɗa. Kawai ta shiga lumshe ido tana ambaton sunan Mai Martaba a bakinta har barci mai nauyi ya dauke ta.
Sai a lokacin ya samu ya gyara mata kwanciya. Saboda yasan tana bukatar hutawa. Gashi hawan jinin ta ya rigada ya tashi. Ta cigaba da firgita da daga hankalinta - haka za a iya samun matsala gagaruma.
Yanzun kam lokacin hutun iyayensa yayi domin shi dinnan ba zai bar duk wani wanda yasan yana kinsu ko yana neman rayuwarsu ya ci gaba da yawo a doron kasar NURISTAN ba. Fitowa yayi gaba ɗaya, dogaran gurin Mai Martaba ya kwashe, ya zuba sababbin amintattu da suka dade suna aiki da shi a South-South, da strict order kar a bar kowa ya kara shiga sashensa bayan likitocin da suke dubasu. Ciki kuwa har da matan babansa, saboda suma ya gama tsinkewa da lamarinsu.
Ganinsa da suka yi, mai babban daki, shidewa tayi a gurin tana sambatu, sai kwasarta akayi ranga ranga. Sarauniya Hassana kuwa har fitsari tayi a tsaye a gabansa. Don abin kunya wai tsoronsa take ji. A tunaninta fatalwa ne, but deep down, yasan it's more than that-musamman mai babban daki da ta birkice musu gaba ɗaya, aka fice da ita.
Shi ba su san ayanzun bata tasu yake ba; ta lafiyar iyayensa yake-gaba ɗaya su biyun. Tun saukarsa yake neman layin Aman, baya samu. An sanar masa yayi tafiya, bai ratsa bincike ba, saboda dama yana bukatar aikashi wani gurin kafin lokacin da zai yi fito-na-fito da uwarsa.
Mimah gaba ɗaya a rikice take har lokacin da lab scientist ɗin ya karɓi samples ɗin, aka ida. Sai Nanda 3 days zata dawo ta karɓa. Amma saboda yadda ta saka shi a gaba, ta dire mai kuɗade, ya sanya ba musu yace ta jira nanda awa uku.
Cikin motarta ta koma, cike da takaici. Ta duba wayarta, da taga missed calls din baiwarta ta musamman-kusan guda ashirin-sai na uwarta guda biyar. Tsaki taja, sanin cewa Hajiya Asiya ce zata saka Ashe ɗin kiranta, don ta samu ta janye kalamanta akan Erfan, wanda tasan ko sama da ƙasa zata hade, ba zata yi ba.
Kashe wayar ma tayi baki ɗaya ganin cewa zasu dameta. Awa ukun nan jinsu tayi kamar shekara uku. Aikuwa tana cika haka, ta fita, har tana hankadawa. Ta karasa kofar ofishin da ta bayar da sample ɗin. Budewa tayi, daidai shima yana kokarin fitowa da wani farin katon envelope a hannunsa.
Yana kallonta yace: "Ke nake shirin zuwa kira."
"Is it ready?" ta tambaya tana karɓewa daga hannunsa.
Bata jira me zai ce ba, kawai ta shiga tafiya tana farke takardar baki ɗaya. Kawai burinta taga report ɗin. Tana burin ace bai yi matching. Paternity test tayi, kuma duk tsananin kusancin dake tsakanin Erfan da wanda ta tashi da shi a matsayin mahaifinta-indai har shi ɗin ba shine ubanta ba-test din ba zai taɓa matching ba.
Idanunta ne ya fara ganin dishi-dishi. Ta gurde, ta faɗi saboda heel ɗin dake gabanta. "Subhanallah!" taji wasu mata dake zaune kan kujerun jira suka faɗa suna kokarin karasowa su daga ta.
Ta yi saurin daga musu hannu saboda tana tsoron kada su zo inda take ko kusa da takardar, su ga menene a ciki. Sai da ta ɗau mintuna a zaune, ba ta san me za tayi ba, menene takamammen abinda take tunani a kwakwalwarta.
Kanta ya mike, tana ganin yadda idonsu ke kanta har ta fice. Ta nufi harabar asibitin inda tayi parking motarta. Yau kam taga advantage din rufe fuskokinsu da ake ce wa suyi a matsayin suna royal women. Ta tabbata da yadda matan nan ke kallonta, sun san itace Princess Mimah of NURISTAN.
Da tunani, ta fara ganin kanta tana trending a social media. Tana shiga motar, ta jefar da takardar akan kujerar mai zaman banza. Ta fizge gyalen kanta da tayi rolling da shi, tana rike kanta da taji yana neman juyawa mata.
Dukan steering wheel din tayi tana fashewa da kuka, tana jin gaba ɗaya duniyarta ta yi crumbling. Tashiga uku yanzun-har da identity da uban da take takama da shi-ba nata bane. Duka na EHSAAS ne. Shi shi kadai yanzun ba ta da gadon King Nashwan kenan!
Kirjinta na zafi, ta shiga ihu. Gaba ɗaya mascara dinta ta bata-gefe da gefen idanuwanta, make-up din fuskarta ya cabe baki ɗaya. In ka ganta, zaka dauka mahaukaciya ce sabon kamu.
Taja motar tana maganganu ita kadai: "No, I can't let this be! I'm Princess Mimah! I can't lose my name and my identity. I'm the only daughter of King Nashwan!"
Ta shiga fada ma kanta da kanta. Memory ɗinta da mahaifinta lokacin da tana ƙarama ya shiga dawo mata.
Yadda yake ɗaurata akan kafadarsa yana mata waka, tana dariya-that innocent laugh-da shi shi kadai yake samun nasarar sakata.
Yadda in taki cin abinci yake satar hanya ya fita da ita yawon shakatawa. Ya kulle fuskarsa, daga shi sai ita, bayan dumbin uban hadarin da zai iya shiga ciki in makiya suka far masa. Amma duk bai damu da hakan ba, don faranta mata rai.
Yadda idan bata yi assignment ba, take boyewa, kada mai babban daki ta gani saboda zata daketa. Shi yake zagayawa, ya faɗa mata, ya rungume ta yace mata: "She can do better. They should try again. Try harder next time."
"He is my father!" ta fada da ƙarfi tana jin wani irin mummunan tsanar Erfan da mai babban daki a ranta-for going behind that man's back and cheating on him.
Wani irin kaunar mahaifinta taji tana yi. Tana jin duk abubuwan da tayi a bayan idonsa suna dawo mata-how she started hating EHSAAS slowly saboda auren da aka yi mata da wuri ya kawo distance mai girma tsakaninta da mahaifinta.
Amma banda EHSAAS-shi EHSAAS can always come back and see him. Tana ganin yadda yake zuwa ganin EHSAAS regularly a makaranta, shi da matarsa Fulani Hajar.
By Allah, wannan matar has always been good. Bata taba nuna mata bambanci tsakaninta da danta ba.
"What changed?" ta shiga fada tana dukan kirjinta kamar mai aljanu.
Kafin tayi saurin juyar da kan motarta, Hukumar Custom ta ƙasar ta nufa baki ɗaya.
Kanta na tafasa, ta tsaya a wani convenience store, ta sai ruwa, ta wanke fuskarta. Tass-farar fuskarta nan tayi jajir kamar nama.
Sannan ta samu damar karasawa shigiyar takardar da ta tabbatar mata Erfan ne ubanta. Ta fizgo ta, ta shiga yaga ta fici-fici tana zage-zage ita kadai.
Tana jin kamar taje ta kone mahaifiyarta kurmus saboda samar da ita ta wannan kazamar hanyar da tayi.
A ranta, tunani ta fara: Kodai shiyasa bata taba kyamar abinda taga tana yi ba? Duk da ita bata taba yi ba, amma ta ɗauka abin ba zai taba shafarta ba-har abada.
Bude mata ƙofar akayi. Ta ɗauko nikaf ɗinta mai ɗauke da tambarin wacece ita. Ta soma taku, daidai taba karasawa ciki, ko ina taratsa. Gaisheta ake har ta karasa babban office din mai fada aji a hukuma.
Bata wani sha wahalar samun iso agunsa ba, saboda matsayinta a ƙasar, akai mata iso.
Da fara'arsa ya tarbeta. Tun da take bata taba zuwa nan din da kanta ba, saboda tasan hakan zai iya komawa kunnen mahaifinta. But right now, she don't give a damn. Tasan ayanzun da ta gane ita ɗin ba 'yar Mai Martaba bace ba kuma Erfan ya fada a gaban jama'a, words will spread kuma ta tabbatar Mai Martaba ba wai doguwar rayuwa zai yi ba. Ayadda ta kiyasta yanayin ciwansa da baƙin cikin da yake ciki, ba zai jima ba zai rasu. Kuma ba za a raba gado ba har sai an tabbatar da kasancewarta 'yar shi-wanda hakan tasan zai ƙare da tona mata asiri ita da mahaifiyarta.
Don haka, za ta yi duk yadda za ta yi ta karɓi kayan nan, ta raba su-tunda yanzun Waziri na prison, Mai Martaba na kwance. Gaba ɗaya su Turaki da Wambai kallon yarinyar kirki suke mata, babu wanda zai yi questioning authority ɗinta har zuwa lokacin da Mai Martaba zai mutu. Ta tattara arzikinta da ɗanta, ta koma gidan mijinta. Domin bata da dawainiyar wanda zai hau kan mulkin-as far as ba EHSAAS bane ba, bata damu ba. Baƙin cikinta a kansa yake kawai.
Bayan Comptroller General ya gama sauraronta, jinjina kai kawai yayi kafin ya miƙe, yana ɗauko mata wani file daga cikin bookshelf ɗinsa, ya ajiye a gabanta. Cike da girmamawa yake fadin: "Ba zan iya barinki ki shigi da kayan nan ba sai da sa hannun sole owner din. Kuma a cikin wadannan takardun an nuna cewa kaso casa'in na kayan na Princess Islam ne, matar marigayi Prince EHSAAS."
Fici-fici tayi da ido tana kallonsa irin yama rainata dinnan. Ya jinjina kai yana samun guri ya zauna yace: "Indai har ba a sake takardun kayan ba, to tabbas ina fada miki indai ba wai order zamu samu daga Mai Martaba ko Princess din ba, ba za mu taɓa iya ba ki kayan ba."
Tashi tayi a fusace tana fadin: "Ni kake faɗawa haka? I'm the real Princess! Who the hell is Islam da har kake cewa sai tazo za a bani kayana? Kana da hankali?! Nice asalin 'yar King Nashwan! Ita ɗin surukarsa ce. Karka sake kace zaka shiga bakin littafi na-hakan ba zai maka kyau ba."
Mikewa yayi cike da girmamawa, ya shiga ba ta haƙuri yana fadin: "Princess Mimah, nima ba laifina bane. Wannan dokace wacce aka daɗe da sakata tun lokacin da tsaron border ɗin ya koma hannun EHSAAS."
"Tace mataccen?"
Sarcastically kafinta tace: "Ka sani yanzun-idan na so, sai ƙasar nan ta komo tafin hannuna. Waye kuma EHSAAS? Yaron da aka daɗe da gama babin rayuwarsa? Zaka sako min kaya ko ba zaka sako min ba?"
Cike da nutsuwa yake fadin: "I'm sorry. Sai dai idan wanda ya shigar da takardun ya koma ya canza su."
Tsaki taja, mai tsayi, tana shiga dogon tunani. Yanzun manyan ƙasar ƙaf ba su da nutsuwar saka ido a lamarinta. In tace za ta canza takardu, za a bi due long process-kafin lokacin kuma Mai Martaba zai iya mutuwa ko ma ya tashi.
Da sauri ta kalleshi tana fadin: "What if idan na yi rubutu kafin in karba? Is that fine?"
Jinjina mata kai yayi yana fadin: "As you wish, Your Royal Highness."
Yana ciro mata wata plain paper daga cikin drawers ɗinsa.
Purse ɗinta ta shiga dubawa, ko zata samu biro. Bata ganiba, gani tayi ya ajiye mata biron yana kin hada ido da ita cikin risinawa.
Tsaki tasake ja mai tana fadin: "Shi matsalar talaka kenan-bai iya samun guri ba. Kai ba kaiba, kowa ne. Don an ba ka matsayin kula da wannan shegiyar hukuma da ba fi in sa ai burning dinta down a rana ɗaya ba kake kafafa, kana jin kai wani ne!"
Ta kasa. Tana ɗaukar biron a fusace, ta shiga zana statement din da yake nuna itace ta karɓi kayan ta a matsayin sole owner.
Ta ƙare tanayin wata 'yar iskae signature-da kana gani kasan faking tayi. Ba tata bace ba.
Ta dire biron tana fadin: "Fine! Sai ka bani takardar izni."
Murmushi yayi. Ya koma, yana ɗauko wani sealed envelope ya mika mata. Ya buga wani stamp a ciki yana fadin: "Asauka lafiya, Hajiya."
Tsaki taja tana kallonsa sama da ƙasa-kallon nuna wulakanci da ƙasƙanci. Ta wani fizge, ta kama gabanta tana ficewa daga office ɗin.
Yayi murmushi, ya ɗau wata leda fara tas irin wacce ake saka evidence a crime scene. Ba tare da ya taɓa biron da tayi amfani da shi ba, ya sa hanky, ya zura a ledar, yana kullesa cikin wata drawer.
Wayarsa ya daga. Bata jima a kunnensa ba na ji yace: "Done, Sir."
Ya saki wani murmushi mai kayatarwa kafin ya koma ya zauna a mazauninsa, yana relaxing.
Mimah na fita, wayarta ta ɗauka ta kunna. Cikeda farin ciki, tayi clearing duk wani notification da tagani rututu a saman wayar, ba tare da ta duba ba. Ta shiga kiran manyan-manyan clients dinta da suka riga suka kama order, tana sanar da su kaya sun iso fa, ga inda za su sameta. Kasancewar ayanzun bata yarda da kowa ba kuma bata da wani shakka ko ɗari-ɗari akan cewa wani na binta ko zai san abinda take yi. Straight ticket ɗin jirgin ƙasa ta siya na zuwa can border, Daje South-South, saboda a can ne suke da katafaren ruwaye iri-iri. Duk wata harkalla anan take yi.
---
California
Abu kamar wasa, kwanaki-kwanaki sun shude, sati-tikka sun wuce, yanzun maganar wata ake yi. Islam, rayuwarta babu ci gaba, sai ma cibaya.
Kul-kum! Jiya, iyau... ayanzun bata iya tsayawa ta kalla kanta a cikin mirror, saboda gaba ɗaya ji take ta tsani kanta da rayuwarta. Kullum cikin buya take, da tsoro da fargaba, kan cewar Abraham Zion zai gane cewa ita Musulma ce. Da wannan take kwana, da wannan take tashi.
Yauma kamar kullum, sai da dare ya ɗan fara latsawa, ta miƙe ta kulle ƙofar ɗakinta. Ta shimfiɗa ɗaya daga cikin scarfs dinta a ƙasan tiles, tana shirin gabatar da sallar Isha'i. Da batai ba, ta jinkirta saboda tana shirin kowa ya yi barci kafin nan.
Tunda ta fahimci babanta ya cire duka keys din dakunan gidan, take kaffa-kaffa. Jr na kwance a gefe yana barci, numfashinsa mai sanyi yana fita a hankali. Duk da tun dazu taji kirjinta na bugawa cikeda fargaba da shakku, bata ji cewar yau ba zata iya yin sallar ba. Tasan farilla ce a kanta, kuma dole ne tayi ta kafin ta kwanta barci.
Sallarta bai kai raka'a ta biyu ba… taji wata irin ƙara akanta-
Bang! Ƙofar ɗakin ta buɗe da ƙarfi kamar ana yaki.
Abraham Zion ne a tsaye a bakin ƙofa, idonsa jajir, hannunsa riƙe da wayar da take haska bidiyon CCTV da yasa a kama installing a ɗakin jiya da yamma da suka fita siyayya ita da mamanta. He had been watching her closely, yana monitoring duk wasu motsinta, saboda yasan yadda take da taurin kai. Duniya ace ta hakura cikin sauki haka?
> "I knew it! I knew you were still doing this madness behind my back!" Ya ƙwala ihu, muryarsa kamar zata fasa bangon gidan tsabar faɗa.
Zabura tayi tana cikin salla. Ta runtse ido tana hawaye, amma ba tayi magana ba.
> "So this is the daughter I raised?! So you are choosing Islam over your own son?!" Ya tambaya, yana fizgota daga saman sallayar, wanda ya sa dole ta idar da sallar ba shiri. Kamar zai ball da ita sai kuma ya dakata.
Sai ya tsaya gaban Jr dake barci. Ya ɗaga shi da sauri daga kan gadon. Da sauri ta miƙa masa hannu, tana neman karɓarsa, tana kuka.
> "Please, Daddy… wallahi I didn't mean to! Please don't take him away. Don't touch my son!" Ta fara rokarsa, tana shashsheka kuka.
> "He's not your son anymore!" ya faɗa da ƙarfi. "You've made your choice. Now watch me make mine. I'm taking him away, and you won't see him until you drop this nonsense!"
Ya ƙare yana ficewa da Jr, wanda ya riga da ya farka, ya fara kuka jin ana masa ihu.
Aka ji Islam tana ihu, amma ba tare da ya saurare ta ba.
Kifewa tayi a gurin, daidai mamanta da ihun nasu ya taso ta a barcin da ta fara. Itama tashigo, taga Abraham na fita da Jr, amma bata san inda za shi ba. Kuma ganin Islam ɗin a haka tana kuka yasa ta gane me ya faru. Ita ta daɗe da sanin Islam bata ajiye addininta ba-kawai dai ta yi shirune, ta ƙi faɗa to avoid this-this conflict that is happening right before her eyes, wanda tasan babu abin da zata iya yi da zai canza hakan.
Rungumeta tayi, ta shiga lallashinta. Islam nata roƙonta, tace ya dawo mata da ɗanta, wanda da tana da iko da tayi-amma tana tsoro. Tsoron irin son da take ma Abraham. Yanzun da ta fara tsufa tasamu ya dawo da ita, bata son ace ga wani abu da zai sake rabasu.
Sai da dare ya raba taga mahaifiyarta ta yi barci, ta miƙe, taje ta sake ɗaura alwala, ta cigaba da sallah. Kuma har lokacin Abraham bai dawo cikin gidan ba tun da ya ja mota ya fice tare da Jr.
---
Washegari
Ba ta runtsa ba. Ba ta ci abinci ba. Ba ta iya ko magana, saboda ƙuncin da take ji ya mamaye ranta.
Ko minti ɗaya ta yi ba tare da Jr ba, ji take kamar shekara. Tana tsaye jikin taga tana jiran tsammani, tana addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki, Abraham ya dawo mata da ɗanta.
Har rana ta fara fitowa, sai can taga motar mahaifinta ta shigo compound ɗin. Wani irin sanyi taji sanda taga driver ɗinsa ya buɗe masa mota, ya fito-shi shi kaɗai, babu Jr.
Jita tayi tana neman zarewa ita ɗaya. Sanda suka haɗa ido, ganin ta yi ya zaro mata ido-irin yadda yake mata sanda tana yarinya. Ta firgice, ta fara ihu, amma yanzun maimakon ta yi ihu sai kawai kallonsa take.
Ta fara wondering: anya kuwa wannan mutumin shine ya haifeta? Anya shi ne yay sanadiyyar kawota duniya kuwa?
Tana kallonsa har ya ƙaraso front door, ya buɗe, ya shigo abinsa yana taku daidai, yana jin kansa kamar sarki. Ya zauna-ba ta ko kalli inda yake ba. Hawaye na zuba a idonta. Sai taji yace:
> "Peace."
Banza tayi masa, ta ƙi ko kula shi. Sai taji muryarsa a dake yana fadin:
> "If you want him back for good… You want your son, Peace? Then you will listen to me now and forever."
Ya faɗa with authoritative voice ɗin da yasa dole ta juya tana kallonsa. Da hannu yayi mata alamar ta ƙaraso inda yake. Babu yadda zata iya-dole ne ta je kusa da shi. Saboda indai har wani abu ya samu Jr, tasan kuskuren kiran babanta da tayi bazata taɓa yafewa kanta ba.
Ta share hawayenta tana zama ba tare da ta ce komai ba.
> "I have two choices for you. Listen well. One: zaki auri Blaine. He's a good Jehovah Witness boy. He knows about your past, and he's willing to take you and your son to Ohio to start a new life."
Islam ta runtse ido, zuciyarta na bugawa-sanin ba zata taɓa iya zaɓar wannan choice ɗin ba. Amma dai ta jinjina masa kai, alamar tana sauraronshi. Ya cigaba:
> "Or two: You can stay a Muslim… and I swear by the God I serve-"
Ya dakata, yana ɗaga murya:
> "I will take Jr to Jerusalem, and you'll never set eyes on him again. Not in this life. Not in the next."
Islam shiru tayi, tana jin zuciyarta kamar zata tarwatse. Ta kasa dena zubar da ƙwalla. Tana jin ta failed as a mother-da ta kawo Jr inda mahaifinta yake, bayan tasan wanene shi kuma me zai iya aikatawa.
Tasan idan Jr ya tashi a Jerusalem, tabbas ko sunan Allah ma ba lallai ya sani ba. Za tashi a ƙungurmin arne ne.
Ta ma rasa me za ta ce ma mahaifinta. Amma dai tasan-komai zai faru, sai dai ya faru. Ba zata taɓa iya barin ɗanta ya tashi a Jerusalem ba.
A cikin zuciyarta take fadin:
> Ya Rabb… What do I do? What do I choose? My faith or my child? How can I choose between You and him? Ya Allah, Kaine Allah. Kafi kowa, kafi komai. Banida kamar Ka. Kana ganin irin yadda rayuwata take tafiya… Ya Allah, Ka kawo min ɗauki da gaggawa.
"Zaki zaɓane ko kuma in wuce airport na kaisa, uhm?" Taji muryar Abraham a sama yana faɗa, yana ƙoƙarin miƙewa. Tanajin sa yana waya, yana shirya kayan yaron, zasu wuce.
Ta rintse ido, ba tare da ta san kalmar da ta fito daga bakinta ba, take faɗin: "I choose Blaine. I'll marry him."
Veronica dake fitowa daga kitchen da tray ɗin abincin da ta haɗoma Abraham kasa karasowa tayi, saboda she's sure Peace ba ta san me take cewa ba. Aure fa, aure fa, ba abin wasa bane.
Wani ɗan iskan murmushi Abraham ya saki, yana faɗin: "Ashe na fi ki rashin ji since I won."
Yana dafa kanta kamar wata baby, ya shiga girgizawa da yasa ta ƙarasa fashewa da kuka, tana jin duk duniya babu wanda ya kaishi tsanar ta.
Ganin ta yi, ya ɗagata, ya rungume ta a jikinsa yana rarrashi. For the first time yake ce mata she won't regret her choice-she will be the happiest girl ever with Blaine. He is a good boy.
"Tohm ka dawo min da baby na," tace.
Murmushi ya shiga yi yana kallon Veronica, ya ɗaga mata gira ɗaya yana faɗin: "V, you see your stubborn daughter ko? Yadda zata iya yin komai akan danta, nima haka zan yi komai akan tawa yar. I hope you understand-what I'm doing is good for you."
Jinjina kai kawai Islam tayi saboda tasan cewar she is not her father. She will never be her father. Idan Jr ya girma, ta saka a ranta she will never force him yayi wani abu-sai dai ta bashi shawara, sai dai tai guiding dinsa.
Veronica kallon Islam kawai take cikeda tausayi, tana murmushin yake kafin tace: "Congratulations, baby."
Ta ƙarasa tana joining hug ɗin nasu gaba ɗaya. Duk da ƙuncin da yake danne a ƙasan ranta, sai take jin wani iri-iri. Because this is the first time suke having family hug irin wannan. Duk tsawon shekarunta, bata tuna sanda daddyn ta is very polite kamar irin wannan kwanaki.
---
Abu kamar wasa Peace gani tayi an fara shirye-shiryen aure gadan-gadan. Cikin sato yake so ayi biki a gama, saboda haka kawai yana jin yana feeling restless. Kullum Abraham ya fita, yana jin kamar zai dawo ya tarar da EHSAAS ya nemosa, ya ƙara hurewa yarsa kunne data rigada ta hakura-zata bi umarninsa, zata auri saurayin da ya rigada ya zaɓa mata, wanda ya tabbata shine daidai.
Domin be taɓa ɗaukar auren da yake tsakaninta da EHSAAS wani abu ba, saboda a gurinsa, auren Christian da Muslim, ko anyi shi, is not valid, kamar haramun ne-is not permissible.
Shirun yarinyar kuma yana damunsa. Amma deep down, sanin cewa dama can miskila ce, sai ya bar wa abin wani mugun mahimmanci. Kuma sau tari yana leƙata a surveillance camera ɗin da ya saka, yaga tana yin sallah. Amma don ba ya son ya matsa mata ta canza ra'ayinta akan auren, yake nuna be san tana yi ba.
Sau tari zai ganta cikin dare ta tashi tayi shiru, ko kuma tayi kuka-tai kuka kafin barcin wahala ya ɗauke ta. A ransa, ji yake inta auri Blaine, ta samu partner mai kaunar shi kamar ta, kuma dan addininta, zai saka ta manta da duk wani ƙuncin rayuwa da EHSAAS ya saka mata. Hakan ne yasa ya ƙara kaimi gurin shirye-shiryen.
---
Yau suna zaune a falon. Kamar yadda ya saba, ya zauna gaban TV, amma ba kallo yake ba-karatun littafin Watchtower yake yi.
Veronica tana kai da kawo, shirye-shiryen biki wanda suke shirin gudanarwa a gobe. Tuni sun aika da Invitations ko ina-abokan arziki da 'yan uwa na nesa duk zasu halarta:
> "Blaine and Peace: United in Jehovah's Grace."
Grand wedding a Beverly Hills Church.
Amma gaba ɗaya, Islam is not in her righteous senses. Kullum idan Blaine yazo da niyyar ɗaukarta su fita don su saba da juna, sai ta samo excuse din da zai sa tace ba zata je ba.
Ba ya takura mata, saboda yadda ya mutu akanta. Kuma yana ganin ai matarshi zata zama-in no time, zasu dawo rayuwa a tare a guri guda.
Mikewa tayi tana kallon wayar mamanta dake charge a gefe. A hankali ta faki idonta for the second time, ta dauki wayar, ta shiga dakinta da sauri. Kallon camera ɗin tayi, tana boye wayar sosai a cikin rigarta kafin ta tura bandaki. Tashiga, ta kullo tana karewa saman bayan kallo, ta tabbatar babu camera a ciki, sannan ta kunna ruwa, ta shiga danna number ɗin Aman, wacce ta rigada ta haddace.
Tana fatan ta shiga duk da tayi tunanin ba zata ƙara neman taimako a gurin wani daga cikin ahalin EHSAAS ba. Amma ta san ba ta da option-ba don kanta take kiransa ba, saboda ita already ta san rayuwarta yazo ƙarshe. Da Jr take, so take tai alerting ɗinsa. Ba don yazo yay stopping wedding ɗin ba, sai don yazo ya tafi da ɗansu, ya kai wa babansa. Duk da ba ta san Mehtav ba, amma a yadda ta ɗauki Jr, ta goyashi, duk da tasan shi ɗin ɗan mutumin da take so ne kuma take kishi da matarsa, tana sonshi.
She saw light a idon Mehtav-na tausayin da jinkan ɗanta wanda ba ta taɓa gani a idon mahaifinta ba. Don haka gara ya tashi hannun EHSAAS, ko matarsa zeba wa, ko maama. Tasan duka a Musulmi ne, ɗanta zai samu ya tashi.
Wayar bata shiga kwata-kwata-ta rasa yadda zata yi. Ji tayi muryar mom dinta tana kiranta, da yan koke-koken Jr, da alama kawo mata shi tai. Feeding dinsa. Da sauri ta shiga wanke hawayen da ya rigada ya bata fuskarta, ta fito tana ƙakalo murmushin ƙarya. Already ta boye wayar cikin toilet ɗin. Karɓarsa tayi tana ɗan mai wasa. Kuwa yafara dariya, wai yasan mamansa.
Veronica tana kallonta. Tasan tayi kuka. A hankali ta haɗa ta da Jr cikin kunnenta, taji ta rada mata: "You can keep the phone."
That means tasani-tasan tana ɗaukar mata waya ba tare da saninta ba. Amma me yasa ba ta taɓa mata magana akan hakan ba?
Murmushi kawai Veronica tayi mata, sanin tambayoyi take yi a cikin ranta. Ta yi kissing a cheeks dinta tana faɗin: "I love you, darling."
Tsawan daren ranar, Islam bata yi barci ba. Sallar ma ƙasa da ita take yi. Haka ta kwana tana kallon fuskar ɗanta, tana jin wannan ne karo na ƙarshe da zata sake ganin sa. Suicidal thoughts ɗin da suke zuwa kanta suna neman fin ƙarfinta. Ta soma tunanin ko ta shiga toilet, kawai ta cika bathtub, tai drowning a ciki.
Sai ta fara girgiza kai tana faɗin: "That is a long process. What if I survive?"
Sannan kuma ta soma tunanin inda zata samu tsauni mai tsayi da zata faɗa, ta mutu, ko kuma bindiga. Tasan babanta na da bindiga, amma bata san inda yake ajiye ta ba. Da tasani da tasani-maybe zata ɗauko: it's either ta kashe kanta ko ta kashe shi.
Wannan lissafin take ta yi a ranta tana saje, trying number kowa da ta sani a cikin zuciyarta, ciki har da ta EHSAAS. Amma saboda nisan da yake tsakanin ƙasashen, babu wacce ta samu ta shiga.
Rubutu ta soma yi, tanayi tana kuka. Ba tayi expecting zata yi this long type ba. Kawai ta gama rubutawa, ta bawa Aman amanar ɗanta, ta cewa ya ɗanka shi a hannun EHSAAS ko Fulani.
Yadda taga rana haka taga dare a ranar. Ba ita ta tashi daga zaman da take ba, sai Asubah. Kuma tun a lokacin take jin masu decorations suna ƙara kammala wanda ba su gama ba jiya. Domin wani irin ado na kawa Abraham ya sa aka mai gida kamar wani auren soyayya za a yi.
Islam ta rayu a ranta sanda take ganin yadda ko'ina na gidan yayi kyau, yayi haske kamar kasace.
Sallar Asubah tayi a hanzarce, ta dawo ta ɗauki Jr da ya farka. Shima tai mai wanka, ta shiga shirya shi. Tanajin wani irin mugun son mutuwa kawai. Shedan ke ingiza ta cewa she should just end everything.
A hakanan tana gama shirya Jr, taga shigowar mom dinta. Lokacin rana ta fara fitowa. Ta ce mata tayi wankan? A'a.
Ta ce mata tana girgiza kai. Mom dinta tace taje tayi. Ta aje mata duk wasu turarruka da zata buƙata. Ta tabbatar tayi using da su, ta soma faɗa mata amfaninsu a jikinta.
Tabe baki tayi, ta shiga yi, tanajin wani irin abu-wai ita ce zata yi wankan turare ma wani? Ba wa kanta ba? Ba wa mijinta EHSAAS ba?
"Allah ya kiyaye," ta faɗa a ranta.
Amma a fili sai ta girgiza kai tana tuna aurenta da EHSAAS a NURISTAN. It was nothing like this at all. Though tasan babanta babu kalar wedding ɗin da ba zai iya affording ba, amma tasan deep down, yana tsoron yay throwing big wedding saboda kada wani daga cikin ahalin EHSAAS ya ganta.
Ko kallon kayayyakin da aka ajiye mata da sunan tayi amfani da su ta gyara saboda aurenta batayi ba, tawatsa ordinary ruwanta ta fito. Kallon matan da suka jere a saman gadonta tayi tana kallon empty cradle din Jr, tace: "Kudin suwaye kuma? Me kuka shigo nan yi? Ina yarona?"
Ta jefa musu tambayoyin a lokaci daya tana yatsine fuska, alamar duk sun nuna a mugun fusace take. Dayar tace: "Calm down, beautiful bride. Your parents sent us in. Babanki ne ya dau yaron, yace ingaya miki sai kun hade a church."
Dan jim tayi, sanin wannan ba wai sako bane-barazana ce. Tacewa ya dauje mata Jr, kuma in ta isa taki showing up for the wedding, ita da sake ganin danta sai Allah.
Yayi. Dogon numfashi taja tana kallon wayar mamanta dake saman gadon. Ta dauka. Babu call, babu message ɗin ko daya daga cikin lambobin da ta kwana tana kira jiya.
Zama tayi kawai suka fara shiryata. Suna yi suna kokarin janta da hira, musamman dayar da take zargin tana da alaka da Blaine-kila 'yar uwarsa ce ko cousin dinsa. Ta runtse ido tana tuna mutanenta su Hajiya Jannat. These two young ladies are nothing like them.
Su ba maganar da suke yi sai ta soyayya, soyayya; su kuma Hajiya Jannat are women of wisdom, wanda ko zaman minti biyu kai da su, dolene ka karu da abu ko kwara daya ne.
Tun kafin su gama suka fara santinta saboda ba karya-kwalliya namugun mata kyau.
"Wow! Blaine is so lucky!" cewar dayar tana karasa styling kan Islam. "Damn girl, are you even real?" "I bet the angels are jealous of this look!"
Dayar ta fada a kokarin son ganin Islam din tayi murmushi, don seta kara kyau. Amma sai kara hade ran tawa sukaga tayi.
Ta tsaya chak tana kallon kanta a cikin madubi. Ta kalli fuskarta. Yes, she looked like a queen. But inside, she was a graveyard of dreams.
Excusing kanta tayi tana mikewa da sauri. Ta dau wayar ta nufi bathroom. Ta kullo kofa, ta kunna famfo, ta cigaba da kiran layin Aman. Seda ta kira sau goma sha hudu.
Ta tura mai: Text. Voice note. Duk ba a amsa.
Silence. "Number you're trying to reach is not available. Please try again later."
Harta haddace kalaman da ake fada a waya. Hannunta na rawa kawai taji wayar ta fadi sai cikin ruwan da ta kunna. Tana rawa don kar su ji tana magana, ko da an daga kiran. Kallon wayar ta shiga yi tanajin kamar the universe just wants her to end all of this. Tsabar fushi, she didn't even bother ta ciro wayar a ruwan-ta fito.
Su suka taimaka mata ta saka hadaddiyar white wedding gown dinta, da ta mugun yi mata da jiki, kamar daman an rigada an gwadata, an gama komai cif da cif. Tana tsaye kamar mutum-mutumi tanajin yadda suke santin kyawunta.
A lokacin da komai ya kammala, music was playing from the living room. Camera crew sun ɗora domin za'a fara daukar amaryar ne tun daga lokacin da ta fito daga dakinta.
Blaine, daya kasa jira sai sun hade a altar ya ganta, ya biyo ta. Yayi hakan ne don yana ganin kamar in aka barta ta zo tare da mom dinta, ba zata zo ba. Kamar yadda duk wani date da ya saka bata taba zuwa ba.
Ya shigo dakin sanye da white three-piece suit, da tayi bala'in amsar jikinsa. Wani irin kamshi mai dadi na fitowa daga jikinsa.
Ya tsaya kawai yana kallonta. Yan matan ihun murna suka fara yi da reaction dinsa towards kwalliyar, irin antashi kansa dinnan. Kafin ya karasa daf da ita kamar zai shige jikinta, yace:
"Peace, you look breathtaking!"
Ya riƙe hannunta yana jin kamar yau ce rana mafi daraja kuma mafi tsada a rayuwarsa.
Runtse ido tayi jin tabon da yayi kamar wani garwashi ne ya taba jikinta. The touch is so unfamiliar-unlike that of EHSAAS. His touch, his scent…
Runtse ido tayi tanajin comparing su biyun ma kamar zunubi ne babba. Bata ankara ba, taji numfashinsa a daci da ita.
Ya kai bakinsa kusa da nata da niyyar kissing, "Wait for me in the car," ta ce da wani sauti mai ƙarfi da ya sa shi yadakata da abin da yake shirin yi.
Ya shiga kallon yadda ta kau da fuskarta a ƙasa, kamar ma ƙyankyaminshi take yi. Ya ɗan murmusa, though confused. Ya bar ɗakin. Sunsun sun yan matan ganin angon ma ta ɗaka mai tsawa ya fice, su ka bi bayanta.
Tanajin rufe ƙofar mutum na ƙarshe, taji kamar ya rufe da babin rayuwarta ne gaba ɗaya. Ƙofar ta fara nufa, cikin dabara ta saka jamlock ɗin ƙofar da ya fara lalacewa-wanda in ka rufe, da ƙyar kake buɗewa ta ciki. Ta kan sanya shi ne saboda Abraham in za ta yi ibadar dare.
A hankali ta juya da niyyar komawa bandaki ta wanke kwalliyar ta, sai kawai ta hango rope ɗin fashion levels da Veronica ke amfani da shi don manne-manne.
Kallon rope ɗin ta tsaya yi chak kafin ta ɗaga kai ta kalli fanka. She saw it happening several times in news, books, movies, amma bata taɓa tunanin abin zai reaching kanta ba.
A ranta take raya dukkan characters ɗin littafi, especially her favourite characters da suke losing hope a kan rayuwa su kashe kansu. Ashe-ashe haka suke ji? Ta taɓa cewa bata saniba-had it been ta sani, she would have never ever judged them no matter what.
Cikin hanzari, jin music ɗin da ake playing a compound ɗin gidan nasu na ƙara ƙarfi, yasa ta ƙarasa walk-in closet dinta, ta ɗauko stool doguwa. Ta fito ta ajiye a sa'itin fankar.
Rigar dake mata rito a baya taja, ta yage net ɗin tana watsarwa a gefe. Ta hau dake-tanada tsayi, abin bai mata wani wuya ba.
Daurawa? She wasn't thinking straight gaba ɗaya. Ta shiga faɗin: "Ya Allah, Ka gafarta min… Na yarda da ƙaddara, amma ba zan iya ba. I can't take this anymore. If I'm wrong, forgive me. I leave Jr to You."
Tana ƙarasa faɗar hakan, ta ɗaura igiyar a kanta. Cikeda dabara, ta tunkudar da stool ɗin da ta hau gefe.
At first, it's pain. Ashe, rai baya fita da wuri.
Ta shiga rayawa a ranta lokacin da taji yadda rope ɗin tayi strangling wuyanta. Wasu irin wahalallun hawaye ne suka shiga bin fuskarta. Tanajin numfashinta yana kokarin barin jikinta.
Me? Jikinta na bari. She felt so cold. A lokacin, tanajin kamar ranta ya riga da ya tafi.
Saboda kalar azaba ce wadda bata taɓa sha ba a rayuwarta. Ta tuna sanda Abraham yayi mata mugun duka da ya kai ga hospitalisation, amma bata ji kalar wannan pain ɗin da take ji a yanzu ba.
Tanajin, "Ashe haka fitar rai yake?" "Is this what she chose for herself?"
Ƙakari take yi ba tare da ta san tana yi ba.
Ga zuciyarta wadda ta danganta da mahaukaciya a daidai wannan gabar. Da take kokarin kiran sunan wanda bata yarda ta kira sunansa ba a bakinta:
"EHSAAS…"
BOOM! Kamar ƙofa ta faɗi, taji ƙarar ta shiga kunnenta.
Wani irin mahaukacin buga ƙofar ake ci gaba da yi. Tana jiyo muryoyin jama'a da ta kasa gane muryar waye da waye-kamar faɗa ake yi.
Sai kuma wani murya… daga can. Tanajinta kamar from a distant world take fita. Ta fara wondering ko dai ta riga ta mutu ne?
Muryar ce wadda ko ina ta ji ba za ta taɓa iya kin ganeta ba. Mai cikeda tsoro, tausayi, jinkai da ƙuna, kauna mara sirki, wadda ta kasa tantance me yinta-kuka yake yi ko kuma tsabar tsagwaran tashin hankali ne yasa ta rawa.
"ISLAAAAAAM!!!" "PEACE!!!" "Open the damn door, please, please, don't do this to me!"
Muryar nan… Muryar da ya taɓa ce mata: "I'll protect you with my life." Muryar EHSAAS.
It's fatoumspassion. EHSAAS. Don't forget to:
Share
Vote
Like
& Comment [28/06, 11:33] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
It's fatoumspassion EHSAAS another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.