Chapter 42
Ahankali ta kwanta a kirjinsa tana fadin, "Meyasa baka dawo da wuriba? Or did you get married for real?"
Girgiza kai yayi yana fadin, "I didn't, billah har in mutu. Kinsan bazan taba iya hadaki da kowace mace a cikin zuciyata ba, ko baby."
Shiru tayi, dai bata bashi amsa ba, kafin tace, "So you used her to make me leave?"
Tadago tana kallonsa, ya jinjina kai. Wani iri taji a ranta saboda tana tuna yadda Mehtav taringa binta, don ta saurareta, tatsaya. Allah sarki. She vent her anger akanta. Bata ji ba, bata gani ba. Gashi yanzu EHSAAS ya karya mata zuciya itama.
Ahankali ta daki kirjinsa tana fadin, "You're a bad boy. She doesn't deserve that."
Dage mata gira daya yayi yana turo mata lips. Tace, "She love you sosai."
Tana facing dinsa wannan karon, tana shafa lips dinsa da yake pouting ahankali. Hakan kuma na nuna mata ba ya son magana.
"And I love you," ya fada yana dora bakin nashi saman nata. Quick kiss ya bata kafin ya bar shi yana kallonta. Yaso ta yi shiru da maganar Mehtav because deep down he is feeling guilty. Yasan fa halin bakin kishin Islam. Kuma yasan he did something wrong in Nigeria-he kissed Mehtav, and she even turned him on. Abinda be taba ji akan kowace mace ba bayan ita, yaji akan Mehtav. Yana tsoron in ta ritsa shi da tambayoyin nan zata gane.
Kallon kurillar da take masa yasa ya dan dauke kai yana fadin, "Stop looking at me that way."
Itama dage masa gira daya tayi kamar yadda yake mata times without number. Tace, "Why? Ko kayi laifi? Something wrong ne? Uhm? Are you feeling guilty?"
Takarasa tana shafa kanshi. Lumshe ido yayi kafin yace, "I'm sorry, Islam. Kinsan duk abinda na yi is wrongly, so dole zanji feeling din guilt da kunya sosai."
Jinjina kai tayi, sai kuna. Ta koma ta kwanta a jikinsa, tayi luf kamar wata jaririya. Tace, "Baka fada min what take you long ba? And how did you find out ina nan?"
"Hmm," yace, kafin yace, "It's a long story."
Labarin kafin hadarin ya bata, da kuma yadda akai hadarin. Da yadda ya gane abubuwan da Mimah takeyi. Da sanda ya kirata yana mata barazana da tahowarsa. Shi shi kadai a hanya, yadda suka yi tunanin ya mutu suka barshi. Shi kuma ya tsira, ya hau kan titi. Su Mehtav suka tsinceshi. Da abinda ya faru bayan nan-na losing memory dinsa.
Har zuwa zuwanta, bai wani bata labarin yadda ya cigaba da rayuwa a gidan Paa ba in details, saboda yasan ko ya bata, duk abinda yace akan Mehtav na kirki zata dauka a matsayin wani abu ne. Yasan mata da kishi-musamman tashi, gwanar.
Sai kawai yace mata, "Bai wani jima a Nigeria ba. Ya saka mutanensa su mai plan din komawa Nigeria."
Ya dan nisa kafin ya cigaba da bata labarin yadda Mimah ke plotting shigo da kayan maye kasar da kuma safarar yara da sunanta. Abin ya mugun girgiza Islam. Ita tama manta kwata-kwata da dukiyar tata dake hannun Mimah, da tace zasuyi business. Tunda Fulani tace tayi hakuri ta fita sha'anin su, da ta gane ba ta sonta-shikenan. Kuma bata sake mata maganar kudin ba.
Ahankali ta dago tana kallonshi tace, "Mai, trust me sire, bansan komai akan kasuwancinnan ba. Sanda ta saka nai signing, I thought it's something legal. Ban ma karanta document din ba."
Jinjina mata kai yayi yana fadin, "Nasani, Islam. I know you're innocent. Shiyasa nai duk kokarin da zanyi don proving hakan. I worked with few people akan hakan. And now everything is over, kinji? Babu wanda ya isa ya shafa miki wani laifi da baki ji ba, baki gani ba. But be careful next time-even if it's me da na miki document, karki taba signing batareda kin duba ba, kinji?"
Jinjina masa kai kawai tayi. Ahankali tace, "Where is she now? Me ya faru da ita?"
Yace, "I let her have her way," yana murmushin gefen baki.
Tadago tana kallonshi da mamaki. Take tace, "Kayan mayen kabari suka shigo Nuristan?"
Jinjina kai yayi yana fadin, "Of course. Kuma na kwace su. And we caught her right-handed in the act. Taje South-South tahowa da su, and guess what? All her dealers are there with her. Zata raba musu kayan, muka chafke su a bakin ruwa."
Dan zaro ido Islam tayi tana fadin, "In public?"
Jinjina kai yayi yana fadin, "Bata yi tunanin cewa wani za kamata bane ba. Saboda Mai Martaba is very sick after losing Granny. Sannan ta daura laifin accident din da yasameni akan accomplices dinta gaba daya. Na farko, she ordered Jay's murder-itace ta kasheshi."
"Salati!" Islam tafara tana fadin, "Aunt din?"
Jinjina kai yayi. Yana jin wani irin abu a ransa saboda yadda ya dauketa a matsayin 'yar uwarsa, tajininsa, wacca ba shi da kamarta na har abada. Amma shi bata taba daukarsa dan uwa ba-sai ma makiyi. Kuma har take neman ransa saboda abin duniya.
I'm sorry, sire, nasan is not easy for you. Nodding yay mata kafin yace, "Is not. And the funniest thing shine, taki tai confessing cewar natane ko kuma tai regretting. Yanzun haka tana cikin one of the most dangerous and darkest cell na NURISTAN. We are patiently waiting for father's recovery saboda gaba dayanmu are under him. Nasan yadda yake kaunarta. If not, I would've cut up her throat, billah," yafada da muryar da tasan tabbass ba wasa yake ba, domin sarai tasanshi, tasan sanda yake wasa da kuma sanda ba yayi ba.
Islam ta shafa gefen fuskarsa cikin sigar comforting nashi. "I hope maama is fine. Nasan this whole thing must've shocked her."
Jinjina kai yay yana fadin, "She's fine, baby. Ta bude idonta finally, tayi realising cewa ba ita ce ta haifeta ba, kuma bata taba daukarta a uwa ba, saboda ta fada mata hakan. Because she went to visit her."
Dan waro ido Islam tayi cikin mamaki. Yace, "That's Fulani Hajar for us. Wai taje mata nasihane, tana son ta canza ways dinta."
Girgiza kai Islam ta fara yi, tana jinjina kyakkyawar zuciyar Fulanin. Tace, "Maama's selflessness is on another level."
Jinjina kai yay yana fadin, "Sure. Because she's too good to be real. Nima na fada mata hakan. And let me tell you something- I use them against each other. Yanzun haka, Erfan is ready ya bada shaida akan Mimah ce tai order a kashe ni, kuma tareda hujja masu karfi. Itama kuma ta bada shaida cewa Erfan ne, and she even have the edited audio recording of it. Saboda natabbatar is edited-ta cire kanta a ciki ta bar su."
Islam tace, "Exactly! Nima haka nace sanda na saurara."
Kallonta yay cikin mamaki yace, "Baby, kin saurara kema kenan?"
Tace, "Yes, na saurara. Kuma ita ta kunnamin da kanta. Bata san I know who she is ba already. Na taba jinsu suna plotting against you-ita da mamarta. Tun daga lokacin na dena yarda da ita. Na fadawa maama, itace tace karna fada maka saboda it would've ruined your relationship da ita back then."
Dan jim yayi kafin yace, "Baby-"
Tace, "Uhm?"
Yace, "You're not supposed to hide anything from me, ko?"
Ta jinjina kai. Yace, "Please, daga yau ki daina boye min irin abubuwan nan. Kinsan ita maama she's too soft, she don't take this royal family stuff as something. Bata san daga kananun abubuwan nan suke farawa ba. Imagine da kin gayamin a wancan lokacin, da duk businesses din da take saki ki bata kudinki- I would've tackled the issue early. Baby, da ba kai da haka."
Ahankali tace, "Sorry. I made a mistake. In sha Allah, bazan sake ba."
Dogon numfashi yaja yana fadin, "Promise?"
Tace, "I promise, sire." Tana saka dan karamin yatsanta jikin nashi, suka yi pinky promise.
"Yajikin Mai Martaba?" Islam ta tambaya cike da damuwa.
Yace, "He's getting better, baby. Amman dai mu cigaba da yimai addu'a saboda what happened hit him hard."
"Allah ya bashi lafiya," Islam ta fada.
Ahankali yace, "Ameen. Ya Hayyu Ya Qayyum."
"Kiyi hakuri, kinji? Rashin lafiyarsa ce tasaka ban zo da wuri ba. If not, kinsan I would've come earlier, baby. I couldn't leave the palace saboda Aman wasn't there. Koda yana nan, kinsan case ne daya shafi mahaifiyarsa. Banason ya getting involved."
Dan jinjina kai Islam tayi tana fadin, "Hakane. And I totally understand."
"Yanzun ya yake? Na ganshi fa kwanaki anan."
Yace, "Eh, nima dana koma, bayan nan. Amman ranar da aka kama Mims, washegari ya dira a kasar. And he was shocked to find out duk abinda ta yi. Ni da shi muka je inda take a prison, and she shamelessly begged him wai ya karasa abinda ta fara. Ko ta mutu, ya temaka yakaini lahira, data gagara kaini. Imagine, a gabana fa take wannan maganar."
Islam cike da tausayi take fadin, "I'm sorry to hear that, sire."
Yace, "Islam, stop apologizing. Is not your fault. Itace ta zabar ma kanta hakan. She looked very miserable. Take cewa in je in ce da Babanmu Mai Martaba yazo ya fitar da ita, indai ba so yake ya nunawa duniya. Can, daman ita ai ba a dauketa ba-saboda tazo amace. She insulted our parents. Nima kuwa, na saka suka mata muguwar azaba. I no longer care. Bansan ya akai ba, Aman called his father, ya fada masa. Ko zuwa bai yi ba. Daga can ya aiko da takardar saki uku, a bata. Kuma ya yi masa umarnin komawa gida."
"Yanzun haka da kika ganshi a tare dani, da kyar na lallabashi ya bani shi, tareda alkawarin kada Mima ta kusanci dan shi. Saboda Aman was depressed tun da ya koma Turkey. He's been battling da emotional health dinsa. Yana jin kamar he's not good enough, daya kasa protecting Dina daga gareta."
Sosai taji tausayin Aman ya cika zuciyarta.
Addu'a ta shiga yi mai a zuciyarta, Allah ya sassauta mishi.
Likita ne yashigo ya same su a haka, tana jikinsa. Ya dagota, ya dan duddubata, yana mata tambayoyi, tana amsawa ahankali kamar wata karamar yarinya. Haka ya shiga tambayarta yanzun me take ji a ranta.
Tace, "Okay."
Yace, "Tana tunanin kar ta kashe kanta?"
Girgiza masa kai tayi. Ya dan yi shiru yana kallonta kamar ba ya yarda ba, kafin ya kalli EHSAAS yace, "Mai jiki?"
Yace, "Da sauki, alhamdulillah." Yana gyara mata zama a jikinsa. Ta wani lafe kamar jinjiriya.
Doctor ya dan yi murmushi cikin tsokana, yake fadin, "Har ina shirin ce miki, your therapist is ready. Ko dai shine personal therapist dinki?"
Murmushi tayi tana boye fuskarta a jikin EHSAAS. EHSAAS yayi murmushi kawai.
Few hours later
Wani irin nutsuwa da kwanciyar hankali ta jita a ciki, wanda rabon da ta samu irin shi tun kafin haihuwar Junior. Tunda mom dinta ta shigo da Junior, Islam ta lura EHSAAS gaba daya hankalinsa ya koma kanshi. Ganin yana son daukarsa yasa Veronica ta mika masa shi tana karasawa gefen 'yarta. Sama-sama yake jin maganar su, ta rungume ta, ba dai san me tace mata ba, sai ya ga Islam ta dago ta kalleshi.
Addu'a yake, itama dai Allah yasa ba fushi tayi dashi ba, don ya lura koda ya gaidata bata wani amsa da kirki ba.
Amman kallon da ya ga Islam ta masa kafin ta maida kanta gun mom dinta ya tabbata. Amman bai nuna ya gane me suke ba, yana ta wasa da Junior, da yake mai wani irin kallo, alamar ba ya sanshi. Amma da yake ba ya qi, sai bai yi masa kuka ba. Sosai yake jin kamar ya yi ta kasancewa tare da su irin haka har abada.
Veronica ce ta kalleshi, fuskarta a hade, tace, "Mai ya kawo Junior? Yana jin yunwa, za a yi feeding dinsa."
Ahankali ya taso yana satar kallon Islam, da ya ga itama tana kallon nashi take yi. Daurawa Islam shi yayi a saman cinyarta. Maimakon ya fice, sai taga ya nemi guri ya zauna a gefen Islam. Gashinta daya danyo gaba ya rufe mata gefen fuska. Yaso gyarawa ahankali, dan kallonsa tayi, sai ta kalli mom dinta da ta koma baya ta ja kujera ta zauna, domin she's very well determined bazata bari su ci gaba da wasa da zuciyar 'yarta ba. Dole ne ta bita garinsu, ko tana so ko bata so.
EHSAAS cikin rada yake tambayarta, "Me mo din tace miki?"
Dan waro ido tayi tana mai nuni da ido, alamar tana jinsu fa. Shiru yayi kafin ya kalli Junior da ke ta tafa kirjin Islam alamar yana jin yunwa, zai sha. Yana yanguna-guni, da alamar mutumin aci-cine ki, ya tambaya yana murmushi. Jinjina masa kai tayi, tace, "Ai kai ya gada."
Dariya yayi kafin ya girgiza kai yace, "Pipi kiji tsoron Allah, ai kin san I'm not foodie. Ke dai ya gada 🤣. I can still remember our honeymoon in that island da kike hade abincina da naki ki cinye."
Hararar wasa ta watsa masa tana cewa, "Ai dai ba laifina bane, laifin yaronka ne, da yake cikinane toh. Shine aci-cin, not me."
Ta karasa tana kallon Junior da yake kokarin fara kuka. Laka ce kumatunsa tayi tana fadin, "Kagani ko? Haka yake sani a gaba, ya yi ta karar dani, shi yana ta gaba."
EHSAAS yace, "Gaskiya hakan ne," yana kallon Junior. "Ka ga matata ta ce min kana karar mana da ita, ya kamata ka rage ci ko muyi maka kishiya ba."
Ya fada yana dage mata gira daya. Ta yi kici-kicin da ido lokaci guda, tana fadin, "Ai ba ka san wuyar haihuwa bane, shiyasa kake fadar haka."
Chuckling yayi yana dan shafa kanta kafin yace, "It must be very hard. I'm sorry I wasn't there for you."
Zata bada amsa, Junior ganin sun ki bashi abinci, sai hira suke, yasa ya canyara kuka. Wanda yasa Veronica ta dago daga karanta magazine din da ta samu a dakin tana kallonsu. Button din rigar dake jikinta sabuwa da tasa bayan tayi wanka, taga EHSAAS na kokarin ballewa. Da sauri ta kauda kai, don ta lura sam-sam alamarinsu daga shi har peace din ba su san kunyaba.
But deep down, tadan ji dadin ganin yana kulada ita sosai, don shine ya tayata tayi wanka, ya fito ya shirya ta, ya gyara ta tsaf-tsaf.
Islam kallon yadda yake kokarin zaro mata boobs yake, ta wani saurin rungume Jr tana fadin, "Sire, ka bari mana, mom is here fa."
Shi shaf yama manta dasu hudun ne a dakin, saboda in yana tare da ita, mantawa yake da kowa da komai around him. Dan juyawa yayi suka hada ido da Veronica, tai saurin dauke kai, sai kuma yaga ta dire magazine din, tafice dakin kawai.
Turowa Islam baki yayi cike da shagwaba yace, "Sorry, kinsan I'm a father, nima sonake babyna yasamu abinda yakeso kawai." Ya karasa yana maida hannunshi saman kirjinta. The way he is touching her din tasan is more than that.
Girgiza mai kai tayi tana fadin, "Nidai ka bari, ka juya. Tohm, agabanka zan bashi."
Dariya taga yayi, irin dariyar da tasan ma'anarta - dariyar tsantsar shakiyanci da rainin wayo. Kawai taga ya cije lips dinshi da kasala yace, "Uhmmm, Pipi, sabo kikeyi fa..." Yakarasa yana janye hannunta daga jikin rigar. Tai wani raurau da ido kamar zatayi kuka, tana ganin yadda yayi kasa da rigar ya gyara Junior akan cinyarta, yana leka fuskarsa lokacin daya fara sha.
Ahankali har yana lumshe ido saboda yayi missing dinsa tun safe yau be shaba. Murmushi EHSAAS kawai yake. Daga ya kalli Junior yana sha, sai ya koma da kallonshi kan fuskarta, datake tamai kunburin rigima wai dan me zetaba ta. Ya kuma kalli mata kirji.
Dataga abinsa bana karewa bane, zumbura baki tayi tana fadin, "Nikam ka bar kallona Sire, I'm feeling uncomfortable, kamar baka taba ganina ba."
Yace, "Fanshe duk na months din daban kallaba nakeyi." Ya karasa yana dada gyara Junior a jikinta, dayake kokarin yin barci.
"Baby, kalleshi. Oh wow, nasan yanata shan dadinshi, ze kwace ma daddy sweet milk dinshi," yakarasa yana kissing saman kirjinta da Junior ke sha. Wani irin yar takeji a jikinta, daya sa tai saurin janye Junior daga jikinta.
Dayayi hakan, Junior ya fashe da kuka, ya farka.
"Oh-oh, Pipi, why are you punishing him for daddy's naughtiness? Come on, ba mu koshi ba, a temaka..." Ya karasa da kokarin maida rigarta. Ta fara fushi. Ya dau Junior yana dan lallashi. Ahankali ya koma barcin yana mata murmushi.
Tana harararsa. Durkusowa yayi yana fadin, "Dan kadan zekara... dan kadan fa."
Mikewa tayi, tanufi jakar da Veronica ta hada mata kaya. Cikin sa'a kuwa, ta samu bra a ciki. Tasan EHSAAS halinshi sarai - he will never keep his hands to himself in dai tana ci gaba da zama a hakan.
Junior na hannunsa, taga yabi bayanta. "Tohm, kiyi hakuri mana. Na bari fa, bazan sake ba," yashiga bata fuska yana tura mata jajayen lips dinshi, wanda tasan tuban muzuru ne - babu abinda hanasu sakewa anjima.
Agabansa ta zira bra dinta, ta maida rigarta. Ta dawo kan gadon, ta zauna tana gyara carnular din hannayenta. Tai shiru.
Ahankali ya biyo bayanta, yana kwantar da Jr a gefensa. Ya jawota, yana kwantar da ita saman faffadan kirjinta. Yasan wani abinne ke damunta kuma ta kasa fada mai - shiyasa take rigima haka.
Yana shafa hannunta ahankali yace, "Tell me?"
Dan shiru tayi kafin ta dago ta kalleshi tace, "Mom tace bazan koma NURISTAN ba."
Shiru taji yayi kafin yace, "Why?" Ahankali muryarta na fita asanyaye.
Dan shiru tayi kafin tace, "Because of everything that happened. Tana ganin kamar na ngaba ma zaka sake karyamin zuciyata. Ka dawo kace is for my safety again. She don't trust you anymore, Sire," tafada tana lumshe ido.
"I'll gain her trust again in sha Allah," yay reassuring dinta yana shafa bayanta.
"And you... do you trust me?"
Yafada yana leka face dinta, jinjina masa kai tai ahankali. Yace, "Why did you try to end your life then? Bayan nasan kinsan hukuncin da Allah yatanada rma duk wanda yay ƙoƙarin kashe kanshi. Uhm, kin kyauta ma kanki kenan? Inda kin mutu baby, wuta zaki shiga. Bazaki taba samun rahamar Ubangiji ba. And by killing yourself, nima binki zanyi because I can't do without you. Yaronmu zezama maraya fa. Kinason ya tashi as orphan? Bashida uwa, bashida uba. Kiduba consequences din action dinki. Bakisan duk abinda ke faruwa acikin rayuwarmu kaddara bace? Allah is testing our faith in Him. Meyasa kikai giving up that easily? Kinsan me hakan yake nufi kuwa?"
Girgiza kanta tafara, sobbing gently. Take fadamai, "Nikaina bansan meyasa nai hakan ba. I was just tired and want some peace, saboda zuciyata can't take it. Zafi yake, yana nauyi, yana tafasa." Takarasa tana daura hannayensa a saman kirjinta.
"First of all, your death came unannounced. Kuma inaganin wanda suka maki amma banida hujjar da zan iya gabatarwa a hukunta su. And Jr... kasan I've never ever been with babies. Ban iya kula da yara ba. You promised to teach me. When Jr came, I knew nothing. Thank God grandma and maama by my side. If not, I would've lost it, sire. I wasn't thinking straight at all. Gaba daya abubuwa dayawa sun faru marasa dadi dabakanan which forced maama to send us to Nigeria to protect us. But..."
Seta fashe mai da kuka tana kankameshi. "They attacked us. They killed our grandma. The gunshots, the bomb... har yanzun in narufe idona, ina hango yadda suka binmu. If not for Taj dani, da na mutu yanzun."
Dan shiru yay yana tuna Taj. Duk da he is kinda annoying, amma seyaji yana mugun darajashi saboda abinda yay wa Islam din. Lallashinta yasoma yi, duk da yasan wasu daga cikin labaran da take bashi daga gun Mehtav, be katse ta ba. Yacigaba da sauraronta, yana ji kamar yay replacing duk wani bad memory dake rayuwarta with good sweet ones.
Tacigaba da fadin, "I was happy dana gane kana raye, saboda rayuwata tasamu sabon ma'ana. I thought komai yazo karshe dana ganka. But what you did shattered my whole life. Kasan kaine rayuwata ko."
Rungumeta yay sosai yana feeling pain dinta. "I'm sorry baby. Nasan my words will never be enough, but I'm truly sorry for breaking your heart."
"Amman nayi regretting," tai blurting out tana kallonshi. "I did regret what I did. Saboda nasan bai na bawa kaina rai ba. Banida hujjar cewa zan raba kaina dashi. I was foolish and stupid. Ya Allah, Ka gafartamin. And it's hard... lokacinda naji nadena numfashi, naji muryarka. Alokacin ne nai realising I'm coward too. Saboda naji banason in mutu. Naji inason narayu again... for my Perfect Rabb, and for my son, and for you."
Lallashinta yafarayi sosai yana fada mata kalamai masu dadi, yana kuma sake tinatar da ita kan haramcin aikata suicide da irin azabar da mutum ze tarar idan har yay nasarar mutuwa yaje yasamu Ubangiji. Yakarasa da, "Ubangiji nasonmu, shiyasa yake jarabtarmu don yagwada imaninmu. So pls keep on having faith, Islam. Allah baze taba iya daura miki abinda bazaki iya ba, kinji?"
Jinjina mishi kai tai, tanajin kalaman nashi sun ratsa ta sosai. Tanajin bazata sake iya bari shedan yarudeta har taji zata kashe kanta ba.
---
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like And Comment
[04/07, 19:19] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's FatoumsPassion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.