EHSAAS

Chapter 43

by @fatoumspassion

Bayan Veronica ta fito daga office ɗin doctor da ya buƙaci ganinsu ɗaya bayan ɗaya, jima tak tana jingina a bango. Maganganun likitan sun shige ta sosai game da halin da Islam ke ciki. Ji tayi niyyarta na ɗauketa daga gurin EHSAAS ta rugujewa baki ɗaya domin likita ya gargaɗe ta da kar ta yi forcing dinta ko kaɗan; a guji duk wani abin da zai trigger dinta ta sake tunanin ending rayuwarta.

Abinda yafi tsorata shine yadda likitan yace ba wai yanzu ne take cikin damuwa ba - tsawon rayuwarta duka she's been depressed saboda rayuwar da suke yi da ita. It's all their fault - ita da Abraham - su ne suka jefa yarsu cikin halin da ta shiga har ta ji gara mutuwa akan rayuwa.

Jiki a sanyaye, ta ɗau waya ba don tayi niyya ba, sai don likita ne ya buƙata ta kira Abraham. Aiko tana fara ringing ya daga domin a kusa yake yana tambayar lafiyar Peace. Bata bashi amsa ba sai sanar da shi sakon likitan, ta yi, ta kashe wayar tana barin gurin.

Ta ƙarasa kofar ɗakin da aka mayar da Islam, bata shiga ba saboda tasan EHSAAS na ciki tare da ita, kuma daga dukkan yadda ta ga alamu, they need time alone - she is not supposed to be invading in their privacy. Amma tayi ma kanta alkawari bazata taɓa barin Islam ita kaɗai ba har abada - in tayi deciding bin EHSAAS Nuristan, ƙafarta ƙafarta.

Abraham a hankali ya tura ƙofa, ya shiga office ɗin doctor bayan ya mai izni, ya zauna, ya kalleshi yana gyara medicated glasses ɗin fuskarsa.

Yace, "Mr. Zion?" Ko ya jinjina kai.

Wasu rubuce-rubuce yayi a jikin takarda kafin ya dago yana faɗin: "Nayi magana da Islam, sannan nayi da mijinta, nayi da matarka ma. And it all came back to you, Abraham Zion. I'm not here to judge you, amma ka fada min gaskiya - kaine mahaifin Islam kuwa?"

Jikin Abraham a sanyaye yace, "Yes, I'm her father."

Doctor yace, "Biological father nake nufi."

Yace, "Tabbas, nine na haifeta. She's my flesh and blood."

Yace, "But you don't love her. Saboda the girl is going through a lot for a 20-year-old. Shekararta ashirin - ban ji ta ma gama cikawa ba - amma har take tunanin kashe kanta."

Abraham kasa magana yayi saboda wani irin nadama da ta cika ransa.

Doctor yace, "Bazan kai da nisa ba, saboda she's an adult. Daga kai har mijinta. Da ace she's still a minor da cewa ƙarfinmu ne gurin ƙwatar mata 'yancinta. Musamman kai - because it all starts with you - kai da mahaifiyarta."

Ɗan ɗagowa Abraham yayi yana kallonsa cikin mamaki, jin Veronica is involved too.

Jinjina kai doctor yayi yana faɗin: "Mr. Zion… abinda ya faru da Islam ba rana ɗaya bane kawai ta tashi taji bakin ciki tana son ta kashe kanta ba. Abu ne da ta daɗe tana so yi tun tana ƙaramar yarinya. Ta shafe lokaci mai tsayi cikin damuwa da ba a kula da ita ba, jin ba a fahimta ba, ba a saurare ta ba - har ta kai zuciyarta ta ɗinke da wani irin nauyi da ya zama abu ɗaya ne kawai zai sauke ta: mutuwa.

From the beginning, ba ku taɓa bawa 'yarku irin soyayyar da kowanne yaro yake buƙata ba. Bata iya rayuwa da kowa ba sai da kanta ita kaɗai da littattafanta. You guys thought she's just calm and peaceful, like the Peace you named her after, amma she's suppressing herself deep inside saboda ta burge ku.

Kamaida ita kamar wata asset da kake possessing, baka bata damar deciding akan duk abinda take so a rayuwa. Duk sanda tayi objecting, kuma zaka bugeta har hakan ya ƙangarar da zuciyarta. Saboda kasani, Mr. Zion - duka baya taɓa gyara tarbiyyar yara, sai dai ma yasa su daina shakkar ka kwata-kwata, har su fara iya mayar maka da magana."

Doctor ya ƙare maganar yana miƙa ma Abraham Zion wata takarda. Ya karɓa yana kallonta, anitse likitan ya soma masa bayani: "Wannan daga cikin rubuce-rubucen dana yi ne lokacin da take opening up to me. She never wanted to, but I used my specialty har ta haƙura ta fara bude zuciyarta.

She's been deeply depressed tun daga ƙuruciya, hakan yasa ta tashi kamar ba yarinya ba - bata da abin irin yara masu shekarunta. Abu na biyu kuma shine rabuwar ka da mahaifiyarta ya sake traumatizing dinta. Kuma ku ka zo kuka cigaba da living under the same roof - daya ƙara confusing dinta matuƙa. But you never gave her chance to ask questions.

But after meeting her husband, that's EHSAAS, abin ya fara raguwa. Saboda idan mutum yana cikin damuwa ya samu wanda zai riƙa zama tare da shi, ko da ba ya faɗa masa damuwar ba, as far as she's not lonely - zai rage.

Shiyasa ta kasa giving up on him. Saboda shine only source na farin ciki a rayuwarta. Kai da mahaifiyarta - ba ku taɓa bata farin ciki ba."

Ya dinga kallon takardar kamar zai dawo da hannun agogo baya ya zama uba nagari ma Peace.

"She's depressed... in a very deep and clinical state. Tana jin wani irin nauyi da yake zama a kirjin ta har ta kasa numfashi. Wasu lokutan a ƙarƙashin roof ɗinka, takan daina cin abinci. Har bacci ya zo ya daina ɗaukarta. She shut everyone up. She kept pretending... smiling... but internally she's been bleeding."

Abraham tunowa yake - tabbas an sha kiransa ace ta ƙi cin abinci. Maimakon ya lallabata ya ji damuwarta, ba taɓa yin haka ba, sai dai yayi mata barazana akan cewa zai ƙona mata littattafai ko ya daketa. Da yadda few weeks ago yake watching dinta through CCTV ɗin da ya sa a ɗakinta - bata taɓa barci da daddare. Why didn't he realize cewa discipline ba shine solution ba? Shifa duk tunaninsa idan ya lallaba Islam ya sakar mata fuska, raina shi zata yi kuma ta zo ta daina jin a maganarsa. Ashe ba haka ba ne ba.

Maganar doctor ce ta katse masa tunani:

"Gaskiyar magana Mr. Zion... ta kusa tafiya. We nearly lost her, and I'm sure ku ka ci gaba da treating dinta kamar asset, zata zo ta sake yin abin da tayi ne kuma babu tabbas mu iya saving dinta."

Jin likitan yace zata iya sakewa ya sa Abraham ɗagowa da sauri yana kallon likitan. Likitan ya jinjina masa kai - alamar da gaske yake. Girgiza kai ya soma yi yana faɗin:

"I'm so sorry. Ni ban taɓa niyyar cutar da Peace ba. Duk abin da nake mata na ɗauka is for her wellbeing. Ina son ta tashi matsayin perfect human being. I want her to follow my legacy, to be like me. I want her to be as strong as me. Ashe I've been pushing her hard, har take tunanin ta kashe kanta saboda ni.

I thought I was saving her from hellfire. When she chose EHSAAS over me, I was angry. I was mad, and I hated her for that. Sanda ta dawo gareni, na ɗauka Jehovah ne ya bani wata damar don in bata irin kyakkyawar rayuwar da nake mata mafarki akai - ashe hakan ba daidai ba ne.

She's the only daughter da nake da ita. Ban san yadda zan yi ba in ta mutu. Ina mata barazana, damuwa... amma ban taɓa ɗauka zata so ta mutu da gaske ba.

I want my child to live. Ni dai na daina takura mata - tai yadda take so da rayuwarta. What kind of man have I become?"

Doctor ya natsu yana kallonsa. Yaga sosai tsoro a idon Abraham. Duk da taurin kansa, yadda ya samu labarin yana da shi a gun 'yarsa hakan na nufin maganganun sun shiga kwakwalwarsa kenan.

Ya ɗan yi jim kafin yace:

"Akwai sauran lokaci... amma muna buƙatar mu fara kulawa da gaggawa kafin ya makara gaba ɗaya. Peace needs constant monitoring, medications, trauma therapy.

Kuma mafi muhimmanci, yanayin da zata dawo cikinsa ba zai sake tunzura damuwarta ba. You should care for her. Tana buƙatar kulawar dukkan ku - kai, mahaifiyarta, da mijinta, da duk wani ma wanda take kauna.

Ku daina nuna rashin jituwa ko gaba a gabanta. Show her soyayya irin wacce ba ta taɓa tunanin zata samu ba a rayuwarta. Hakan ne zai sa ta sake samun hope of living."

Jinjina kai Abraham ya shiga yi yana faɗin yarantse da Jehovah he will be a good father to her this time.

Doctor murmushi yayi, ya ƙara miƙa masa wata takarda yana faɗin:

"Wannan plan ne da muka tsara - weekly therapy sessions, da kuma family involvement.

She needs empathy now... ba ladabtarwa ba. Ba tambayoyi ba. Ba 'me yasa kika aikata abinda kika aikata?' ba. Yanzu kawai tana buƙatar kulawa mai tsanani."

Abraham ya girgiza kai, yana share gumin da ya tsattsafo a fuskarsa duk da AC ɗin da ke kunne a office ɗin. Yace:

"Zan yi komai, Doctor. Ba zan ƙara matsa mata ba. I won't force her to leave him. I won't curse her again."

Doctor yace: "That's very good. Ka zamo uba nagari kawai gareta. Just be her comfort. Ka barta ta riƙa yin duk abinda tayi deciding - besides, it's her life and she's a grown-up. Mu aikinmu mu iyaye: shawara. Matse yara da cewa sai sun yi abinda muke so ba shi da amfani."

Jinjina kai kawai Abraham ya shiga yi, har ya fito daga office ɗin likitan - hankalinsa ba a kwance yake ba.

Dakin Islam ɗin ya wuce. Anan ya tarar da Veronica tana zaune gefe, ta rike kanta. Itama a hankali ya tsugunna a gefenta. Takardun na hannunsa ya shafa kanta. Ta dago a hankali yana kallon idonta. Yasan itama kuka tayi. Ya dago ta sosai, ta ɗauke kai daga kallonsa.

A hankali yace mata, "I'm sorry, V."

Mikewa tayi kafin tace masa, "Me kake yi anan? Did you come to curse her again?"

Girgiza kai ya soma yi yana jawota jikinshi, yake faɗin, "I'll never do that again. Kinsan she's our only child - how can I curse her?"

Tace, "Nas nawa kuma? So nawa kana cursing rayuwarta? Shiyasa she's never happy."

"I never meant it," ya fara bayani. "I just thought abinda tayi ba daidai bane. Kinsan how I can become at times. I punished her not because I don't care, but because I care too much."

Fizge hannunta tayi daga nashi tana faɗin, "Don't touch me. I was so stupid to be blinded by love har na yi neglecting 'yata for you. Ba ka ji me doctor yace ba? Duk mune sanadin abinda tayi yunkurin yi yau. From the beginning tana tare da mu bata taɓa jin farin ciki ba."

Saita fashe da kuka. Abraham ya rungumeta ya shiga lallashinta. Sun jima a hakan kafin suyi deciding shiga dakin barci. Suka tarar da ita tana yi, EHSAAS na zaune saman sallaya yana lazumi.

For the first time, Abraham yaji tsanar da ya yi ma EHSAAS yana dan raguwa a cikin ransa, amma duk da haka kwata-kwata bai ji yana sonsa ba.

Basu jima suna jira ba, EHSAAS ya shafa addu'a ya mike. Can gefe ya samu ya zauna. Ganin su sun zo, sun tsaya gefen gadon Islam suna ta kallonta, ita da Jr da suke barci kamar yau suka fara ganinsu.

Closely yake watching Abraham saboda sam bai yarda da shi ba, kuma yana jin kamar zai iya sake wani abin da zai cutar da Islam anytime.

Sun jima a tsaye a gurin kafin su samu guri su zauna suma. EHSAAS ganin sun zauna, ya mike yace ma Veronica zai je ya dawo.

Tace, "Tohm, babu matsala."

Ya juya yana kallon Islam kafin ya fice a hankali, yana dannan kiran Aman a wayarsa, don so yake takardun da yace a haɗa mata su haɗu su wuce ko zuwa gobene su karasa treatment ɗin a NURISTAN, domin hankalinsa in yace zai barta anan - rabuwa zai yi sam.

Saboda halin da Mai Martaba ke ciki a NURISTAN, duk da yasan yana cikin tsaro mai girma kuma yana warwarewa, amma duk da haka in ya haɗe su guri guda, hankalinsa zai fi kwanciya.

Tun Mehtav na kirga satittika har ta koma kirga watanni - shiru. Babu EHSAAS, babu alamar sa. Deep down, tana jin zai dawo amma kuma it's been long.

Kamar ya zo ne matsayin wani almara a cikin rayuwarsu, sannan kuma ya tafi.

Abinda yafi bata mamaki, takan ji yana waya da Paa suna gaisawa, amma ko sau ɗaya bai taɓa tambayarta ba - sai dai Abeey. Kuma shima kiran wayar sai ya shafe sati bai yi ba.

Yanzu gashi Paa ya bar ƙasar ma baki ɗaya - bata da hanyar jin daga gareshi kwata-kwata.

Ta gama degree dinta na farko, gaba ɗaya shirye-shiryen tafiya NYSC take yi yanzu haka, amma tunaninta na makale da EHSAAS har wannan lokacin.

Duk iya yadda take ƙoƙarin taga ta cire sa a ranta by being busy, ta kasa kwata-kwata.

Abeey, tun tana na cin neman EHSAAS har ta hakura. Yanzu da wuya ma zaka ji tana hirarsa. Ta so na mantawa da shi - itace dai har yanzu yake makale a ranta.

Paa bai janye damar sauraron manema daya ba taɓa - don yanzu in aka zo gurinta, taki fita. Har Inna taji labari, seta lallaba ta kira shi, ta faɗa masa.

Shi kuma ya kira ta, ya fara yi mata wa'azi yana faɗa mata aure rahama ne, he is not trying to force her.

She is 22, going to 23 by December, don haka she's not getting any younger.

Ba yace lallai sai tayi aure yanzu ba, amma dai ta taimaka ta saurare su - ta tsayar da manemi guda ɗaya.

Sosai taji mamaki lokacin da ta fita - tag! Wanda yake na cin zuwa gurinta - Doctor Kamal.

Kamaluddeen ne farkon lecture ɗinsu, wanda bata taɓa tsammanin ganin shi ba.

Doctor Kamal saurayi ne duk da shekarunsa sun dan ɗata - saurayi ne bai taɓa aure ba. Kuma kana ganin shi kasan dan gaye ne. Na bugawa a jarida, domin tun kafin ya ƙaraso gurinka kamshin sa zai tarar da kai.

Babu macen da zata samu mutum kamar Doctor Kamal.

Tace ba ta son shi - idan da ace a da ne kafin ta bawa EHSAAS zuciyarta, yadda take kallon Doctor Kamal da yadda tasan history ɗin sa da 'yan matan school da yake dizgawa.

Bai son raini. Duk wacce tace tana son shi - baya ko sauraron ta.

Da ta bashi dama - amma har ya gama gabatar da kansa da faɗar intention ɗinsa na son aurenta - kwata-kwata bata ji wani abu a kansa ba.

Kawai dai tace masa "Toh" ne, zata yi tunani - saboda damar da Paa yace ta ringa bayarwa. Tasan waye mutum.

Washegari - sega Nura.

Nura, Nura - dai nata mutumin ta me waya.

Ko last month shine ya kawo mata sabuwar waya da Paa yace a bata. Bayan ya bata, har gida ya shiga ya gaishe da Inna, kuma suka sha hira.

Bai taɓa nuna mata abinda ke ransa kenan ba - sai yanzu da take ji daga gareshi - shima yazo neman aurenta.

Bata taɓa mai kallon ma wai namijin da zata iya aura ba - saboda tun-tuni ta jefa shi a zone ɗin aboki kuma dan uwa, kamar dai Tajuddeen - da yanzu ba shi da aiki, sai tsokanarta wai tana raina mazan Nigeria, taga Balarabe dan fari ta makale da shi a ranta.

Tasan tsokanar ta yake, amma kuma ita har ga Allah ba wai don kyan EHSAAS ko matsayinsa ko kasancewar sa hakan yasa take son shi ba.

A baya inda za a ce mata "Mehtav, zaki faɗa a soyayya da namiji kamar EHSAAS," ba zata taɓa yarda ba - saboda kyawawan maza ba sa burgeta.

Ta kan ce, "Me zata yi da kyau mai yi mata? Su ta kalli miji ashe bata san shi so ba haka yake ba."

Baya tambaya balle neman izni in zai shiga.

Bata iya ɓoyewa - Nura komaiba, ta faɗa masa gaskiyar abinda ke ranta.

Cewa yayi hakura - ba zata iya aurensa ba. Ita kallon yayanta take mishi.

Dayake Nura na da fahimta sosai, bai ce komai ba. Ya yi mata fatan alheri kawai - domin dama yasan gwada sa'ar sa kawai yake yi. Amma Mehtav ba kalarsa bace ba - tafi ƙarfinsa nesa ba kusa ba.

Dr. Kamal ne ke zuwa gurinta lokaci bayan lokaci. Yakan kira ta su gaisa, amma ba wata shakuwa bare hirar kirki tsakaninsu - sai respect.

Abeey sam ba ta yin Dr. Kamal - duk inda ta zauna, sai tayi comparing ɗinsa da EHSAAS ta kushe shi.

Saboda ita har yanzu tana tunanin ba ta cire rai da cewa wata rana Mehtav zata auri EHSAAS ba.

Sau da yawa suna faɗa da Inna in taji Abeey na ziga Mehtav kan kada ta saurari kowa, saboda kaf cikin masu cewa suna sonta - ba wanda ya kai EHSAAS: kyau, kuɗi, ilimi, da wayewa - ga kuma mulki.

Inna seta bi bayanta tana, "Zaki ci ubanki, yar jakar uba! Ke ce kike zigata ko?" Suyi ta zagaye a falon tana tira Inna, suna zuwa su dawo har se Inna ta gaji, ta zauna don kanta.

Inna yanzu har wani jan Mehtav a jiki take yi, wai duk don ta saki ranta, ta bawa Doctor Kamal fuska ai magana rauren aure.

Dawowar Paa NURISTAN ke da wuya, yayi hosting wani walima inda ya tara manyan abokansa da suka yi karatu tare, kamar wani get together.

Aka yi a gidan manyan mutane ne na gaske - wasu 'yan siyasa, wasu shahararrun 'yan boko, wasu kuma 'yan kasuwa.

A nan ne Ahmad ya ganta. Ahmad shine firstborn din Alhaji Mukhtar Gaya, kuma CEO na The Great Gaya Motors NG.

Yana daga cikin haɗaddun manyan big boys da ake jida su a Abuja. He is in his early 30s - kamar dai EHSAAS.

Melanin ne, gashi dogo, kakkarfa saboda gym ɗin da yake yi. Yana daga cikin eligible bachelors da mata ke rububi a kai a Abuja.

Yake zaune a gidan kansa, kuma business ɗin kansa yake - ba ya dogara da mahaifinsa.

Duk da tarin arzikin Alhaji Mukhtar da yake harkar canji, babban dansa Ahmad ba ya dogara da shi, kuma prestigious family ne.

Domin ba a iya Kano ba, a ko'ina a fadin Nigeria in ka ce waye Alhaji Mukhtar Gaya, za a faɗa maka.

Shi din dattijon arziki ne, kuma mai kudi - uban masu kudi.

Tunda Ahmad ya kyalla ido ya ga Mehtav, yaji duk duniya ba wadda ta kai ta - se ita.

Gashi he's an extrovert, very outgoing.

Domin da ya kawo mahaifinsa wanda ya sauka a gidansa don halartar taron, barin manyan, ya shigo ciki, suka gaida Inna.

Ya fara hira da ita da Abeey, da take ta tambayarsa kan abubuwa da dama saboda yana daya daga cikin Instagram influencers da take bi.

Domin shi irin mutanen nan ne - 'yan social media, na bugawa a jarida.

Mehtav bata ce komai cikin hirar tasu ba - sai an tambayeta kiji Abeey ta fada masa wani abu, tace ko yau, Mehtav se kawai ta jinjina kai.

Duk da ba ma ta fahimtar hirar da suke yi - duk na social media ce, ita kuma ba yi take ba.

Abeey ce take karbar wayarta, ta yi ta yi.

Ba su yi wata magana ta kirki da Ahmad ba har suka wuce, bayan abokan Paa ɗin sun haɗa mata kyaututtuka na gani na faɗa.

Bayan da suka tambayi waye yayi girkin, aka ce itace - haka ta na jin kunya ta rinka karɓa tana musu godiya.

Alhaji Mukhtar Gaya yana ta saka mata albarka, don ya lura da irin kallon admiration da Ahmad ke binta da shi, har suka tafi.

Washegari da safe, sega Alh. Mukhtar ya dawo gidan. Itace ta kai musu tea a falon Paa tare da Ahmad ɗin. Yazo da wani kaninsa wannan karon. Ta yadda kanin baban Ahmad ɗin yace, "Itace wannan", sanda tana gaidasu kaɗai yasa gabanta ya faɗi.

Alh. Mukhtar yace, "Itace fa." Ya fara cewa, "Masha Allah."

Itadai haka ta kammala serving nasu tana sunkuyar da kai, ta koma ciki.

Bayan da suka tafi ne, Paa ya tara su dukkansu, ya fara tambayarta maganar ta ita da Doctor Kamal - cewa yaji shiru, ko sun daidaita ne.

Girgiza kai tayi, yace, "Meye matsalar?"

Abeey ce tayi saurin daka tsalle tace ma Paa, "Ai Mehtav ba ta son shi ne."

Closely yake kallon Mehtav kafin yace, "Wai haka?"

Jinjina kai tayi. Inna ta dake Abeey da duka tana faɗin, "Itake zigata, makunshin gishiri ke! Kam Mehtav an yi shashasha! Ashe magana da nake gaya miki gaba ɗaya ta bayan kunnenki take shigewa. Yanzu menene aibin yaron nan Kamalu?"

Turo baki Mehtav tayi tana kasa cewa komai.

Paa ya nisa saboda yasan matsalar. Ba ya son ya tambaya ne yaji tace EHSAAS har yanzu take so - saboda yadda ma yake gani, EHSAAS has already settled - shi da matarshi, ba ma ya taɓa maganar Mehtav kwata-kwata.

Yace, "Tohm Mehtav, aikin san ba wanda za miki dole, amma dai ki nutsu kada mutanen kirki su yi ta wuce ki."

Ya kalli Inna yana faɗin, "Abokina Alh. Mukhtar..."

Ta ɗan yi jim kafin tace, "Wanne?"

Yace, "Gaya fa, na Kano."

Kabbara Inna tayi tana faɗin, "Tabbas, Alh. Mukhtar - na ganeshi."

Yace, "Jiya kinsan yana daga cikin waɗanda aka yi walimar da su."

Tace, "Ba shakka, ai yana da zumunci sosai. Ina tunawa lokacin da kuke degree, har zakka yana bamu wallahi. Mutumin arziki."

Jinjina kai Paa yayi yana faɗin, "Ashe kam ba ki manta ba Inna. Tohm, yaron shi Ahmad shine jiya ya ga ita Mehtav, kuma yace ma baban yana sonta da aure. Kuma da gaske yake, don shi so - samunsa ma ai aure nanda ƙarshen shekarar nan."

Zaro ido Abeey da Mehtav suka yi a lokaci ɗaya. Mehtav na tsoro, don tasan yadda babanta ke daraja Alh. Mukhtar.

Da ƙyar ne yace musu, "A'a..." Abeey kuma na amusement.

"Finally yayarta ta samu kalar mijin da ya dace da ita bayan EHSAAS. Oh wow!" cewar Abeey, har da rufe baki tsabar daɗi.

Paa da ya ga reaction ɗin Mehtav, se duk jikinsa yayi sanyi.

Cikin lallabi yake faɗin, "Come and sit close to me."

A hankali ta ƙarasa ta zauna a gefensa. Ya kama hannayenta yana faɗin, *"No one will force you kinji? But please, open your heart. Give someone a chance. You're still young, Mehtav.

Na san cewa it's not easy, it's not - sabods I've went through the same thing.

Shekaru da dama da suka wuce na taɓa baki labarin cewa ba mom ɗinki bace first love ɗina, a bazata."*

Ta ɗago tana kallonshi saboda he always tells her the great love story ɗinsa shi da mamanta. Amma ace ba itace ya fara so ba?

Jinjina mata kai yayi cikin alamun tabbatarwa. Yace,

*"Yes, my first love mace ce wacca I can't even dream of reaching - but I still chose to love her. My love story was never complete, saboda bata taɓa reciprocating abinda nake ji a kanta ba.

Kamar dai naki da EHSAAS. Kisani, you'll find someone better - someone that will love you wholeheartedly, Mehtav. Give them a chance, kinji?

Na san mantawa da Prince won't be easy, amma na san you're a fighter, Mehtav. You've always been strong."*

Jinjina mai kai ta shiga yi. Yace,

*"I won't force you sai kin auri Ahmad ko Dr. Kamal, amma zan baki shawara a matsayina na mahaifinki. Dukkansu su biyun - na ga tsananin soyayyarki a idanuwansu. Kuma dukkansu nasan suwaye.

Nayi bincike akan Kamal tun kafin ya fara zuwa gidan nan. Sai da nasan waye shi, suwaye iyayensa, sannan na bar shi ya ringa zuwa yana ganinki.

Ahmad kuma kamar a gabanmu ya girma, Mehtav. He is a good boy. Yana da ilimi daidai gwargwado - arabi da boko - though bai kai Dr. Kamal ba.

But he is good, ga asali mai kyau. Sannan hankalina zai kwanta, nasan duk inda na juya kina cikin Gaya family.

Alh. Mukhtar ba zai taɓa bari ki wulaƙanta ba. Zaki bashi dama?"*

Paa ya shiga tambayarta gently. Kasa cewa komai tayi. Abeey ta shiga rokonta, "Yah Mehtav, dan Allah se yes. He's very nice. Yah Mehtav, he has money, kinsan nawa ne networth ɗin shi kuwa? Kuma he is handsome."

Inna ce tayi kanta da gudu, ta miƙe tana yin guri wajen Paa tana kyalkyala dariya. Inna tace, "Kaga wannan 'yar taka Abeeda, ba ƙaramar ƙwalluwa bace ba, shiyasa ba ta girma. Gatan nan, kullum jiya iyau kamar ba ta cin abinci. Wallahi se ka tsaya a tsaye a yan matancinta. Ke, mutum mai kuɗi kaɗai shine mutum?"

Ko zumburawa Inna baki tayi. Paa yace, "Abeey," cikin sigar gargadi. Da sauri tace, "Tohm, I'm sorry. Amman dai kawai fa shawara nake bata, saboda ba zata haɗa Ahmad da wancan lecturer ɗin me fama da farin glass ba."

Inna tace, "Ke da uban me kike fama shi glass ɗin fuskar ki? Me neye?"

Tace, "Ai ni dai nawa lalura ne, ko kuma ba kyau. Yi wa mutum gorin dan yana sa glass ai Allah ne ya ɗaura masa."

Inna tace, "Daman an ce in kashi a jikinka yake, ba ka jin warinsa. Sai na wani tsabar rashin son gaskiya irin taki. Shi kuma se yace miki nashi ba lalura bane ba. Ai nashi na gayu ne, ki tambayi yaya Mehtav - iyayi ne kawai da famar da takarda."

Duk tana bayan Paa take maganar nan, don Inna ta zama kamar sa'ar ta. Duk abinda ta faɗa se ta mayar mata. Sai da Paa ya kama kunnenta sannan tayi tsit. Tace, "Ahhh Paa da zafi fa, I'm sorry tohm."

Yace, "Is that the way you're supposed to talk to your grandmother?"

Girgiza kai ta shiga yi, still ba ta ɗauke kunnen nata ba. Yace, "Tohm, apologize."

Kallon Inna tayi tana kwabe baki, take faɗin, "Kiyi hakuri tohm, ba zan ƙara ba."

Girgiza kai Inna tayi tana faɗin, "Habibu, rabu da ita. In dai Abeeda ce, an jima kaɗan zata sake, ta iya tuban muzuru ai. Sakinta yayi."

Inna ta cigaba da mita: "Yarinyar kamar ba ta taso cikin gidan arziki ba. Burinta taga mai kuɗi. Wannan da a gidan talaka kika tashi da zanga yadda zaki. Ba ki san wahalar da Habibu ya sha kafin yazo nan ya tara kuɗin da kike takama kuna da shi ba? Daga har kike raina arzikin wasu."

Abeey dai kicin-kicin tayi da fuska. Daga baya ma miƙewa tayi, ta tafi ɗakinta.

Mehtav na ganin haka, ta san fushi tayi saboda Paa ya mata faɗa akan Inna. Kuma yanzu zata fara share Inna, ita kuma Inna ba ta iya zuciya da mutuniyar tata. Da kanta zata je tai lallashi.

Back and forth ɗinsu har ya soma isar Mehtav.

Paa ya maida kallon shi ga Mehtav yana faɗin, "Kin ji ko?"

Jinjina kai kawai tayi tana faɗin, "In sha Allah Paa, zan saurare shi."

Yace, "Yauwa. Gobe zai zo zuwa yamma-yamma, se ku tattauna."

Ta kara jinjina kai, alamar tohm.

Da ta koma ɗaki, Abeey ce ta saka ta a gaba. Ta shiga Instagram tana ta scrolling account ɗin Ahmad, tana nuna ma Mehtav. Da hankalinta gaba ɗaya ma baya kanta. Tayi nisa gurin tunanin EHSAAS.

Har Abeey tayi clicking, tayi following ɗin shi - bata saniba. Da dai account ɗin da sunan Mehtav aka buɗe, nan da nan Abeey taga yayi follow back. Ihu ta saka, tayi tsalle tana direwa akan gadon Mehtav. A firgice ta tsaya tana kallonta irin "Lafiya dinnan?"

Miko mata wayar tayi tana nuna mata, "Wait, kalla Mehtav!"

Ba taga komai ba, sai notification. Tace, "Meye wannan din?"

Tace, "Ahmad Gaya ne fa yay following dina back. Wayyo Allah, na daɗi dagaske. Yah Mehtav yana sonki!"

Da sauri Mehtav ta fizge wayarta tana faɗin, "Wannan wane irin rashin mutunci ne Abeey? Zaki ringa bini karti da suna eh? Salan ma yace nima ina so ko ko da man abinda nake so? Lemme - bari kiga se nayi unfollow."

Da sauri Abeey ta fizge wayar itama tana ja da baya. Take faɗin, "Wallahi baki isa ba. Ai naga ba ma kece kike yin IG ɗin ba. Nice! What's the harm a ciki? It's just IG friendship haba mana, don Allah ya Mehtav, kiwaye."

"Abeey ki kiyayeni fa!" Mehtav ta shiga gargadinta - wanda ta san ba ma shakkarta zata ji. Tanayine kawai don taji daɗin bakinta.

Daga ƙarshe ma, Abeey guduwa can garden tayi, ta barta a ɗakin ita kaɗai cikin tunani. Kuma wayarta na hannunta. Babban tsoronta shine kar taje ta taita chatting da shi a matsayin ta. Tasan Abeey can write very well, ba lallai ya gane ba ita ba ce.

Kuma bata da energy ɗin zuwa tayi faɗa da ita, don taga yau din da neman bala'i.

Ta tashi, ta nufa ta tsokanar Inna, yanzu kuma ta dawo kanta.

Sai da aka yi azahar, Abeey ta dawo mata da wayarta. Bata tanka mata ba. A ranta tana raya, tasan me zata yi.

Yarinyar bata son abin yara. Ga iPad ɗinta da aka cika mata da kayan karatu da games a ciki, bata taɓa tabawa. Sai wayarta.

Tana shiga bandaki alwala kawai, ta canza mata password. Ta cire Face ID ɗin Abeey da tayi adding, ta ajiye wayar a gefe. Tasan zata sha rigima, amma it's better kar taje ta yarfata a gaban Ahmad.

Ai kuwa Abeey na fitowa, ta ɗauko hijab, tayi sallah. Ko addu'a bata gama ba, ta miƙe tana salati a fili. Ta nufi wayar, ta kalla Mehtav dako kallon inda take batai ba.

Ta ɗau wayar kamar tata, ta shiga latsawa. Ganin fuskarta taki buɗewa yasa ta shiga goge fuskar da idonta da kyau da hijab ɗin jikinta, amma still yaki buɗewa.

Sai ta saka password - ya saka wrong. Kallon Mehtav tayi, ta sake sawa, taga wrong.

Kyabe baki tayi cikin wata irin lalatacciyar shagwaba ta sangartattun yara, take faɗin, "Wallahi password kika canza. Meyasa kika canza password ɗin, uhm? Meyasa?"

Mehtav miƙewa tayi tana faɗin, "Ai da aka tashi siyo waya da sunana aka siyo. Ba haka aka ce ta Abeeda dani ba ce ba. Kin mayar da wayata kamar tawar sa'ar ki. Ban da privacy kwata-kwata. Tohm daga yau, naga yadda zaki ringa taba wa."

Abeey bubbuga kafa ta fara yi tana faɗin, "Ni dai ki buɗe min. Allah se kin buɗe min!"

Tsantsar rigimar Abeey har dariya yake bata. Wataran halinta yana kamanceceniya da na Inna. Mehtav tace, "Ai in ke kika haifeni, se ki sa in buɗe kinji uwata."

"Wallahi se na faɗa wa Paa!"

Mehtav ta kyalkyale da dariya tana faɗin, "Kifi ruwa gudu - ga hanya nan."

Don tasan ba zata iya zuwa ba, saboda Paa ya sha mata faɗa ma akan bata wayar da take yi tana ganin social media.

Sanin tasan Paa bayan Mehtav zebi, yasa ta kifar da wayar saman gado. Ta cillar da hijabin da tayi sallah a tsakiyar ɗakin, ta bar sallayar ma a gurin.

Duk dan ta bawa Mehtav haushi. Cikanka, bata ce mata tafice daga ɗakin ba. Tana kumburi, tasan ba zata je gurin Inna ba, don dazun sun yi faɗa. Sai dai tafi kallon cartoon - for sure.

Ranar dai ba su shirya da Abeey ba sai da daddare. Da ta shiga kicin abinci, ta ƙi yi wa kowa magana. Da suka matsa mata, sai ta fashe musu da kuka saman dining ɗin, wai dan an ga ita marainiya ce ake kowa yatsaneta a gidan. Da farko iya tana ta zaginta tana ce mata "me son kuɗi," yanzu kuma ga Yah Mehtav, ta daina sonta, ta hanata ɗaukar mata waya.

Ita kawai dama ba a haifeta ba, ta tafi tare da mamanta. Tasan mamanta ba zata ringa hantararta haka ba; ko tayi fitina zata so ta sosai.

Abeey ta ƙware da irin wannan emotional manipulation ɗin, shiyasa duk irin abinda za ta yi, take cin bulus a gurinsu saboda tsananin tausayinta da suke ji.

Ƙarshe dai har Paa ya yi mata alƙawarin zai siya mata waya itama, in ta shiga JSS2. Daɗi kamar zai kashe Abeey haka ta rungume su tana musu kisses a cheeks tana cewa tana sonsu.

Bayan sun gama lallashinta sun ba ta abinda take so, haka suka koma ɗaki. Ta shiga mata hirar Ahmad, tana nuna mata chats ɗin da suka yi dazun bayan ta faɗa mata sabon security ɗin da ta saka.

Tace, "Ai ba nace ke ba ce ba? Nace mai nice saboda banason yarainaki. Yanata tambayana abubuwan da kike so, kingani he want to win your heart."

Ko kalla Mehtav bata yi ba, ta ci gaba da sauraronta har barci ya ɗauke ta.

Washegari haka suka tashi. Allah ɗaya ɗaya ta taimaketa, Abeey ta tafi makaranta, aka bar ta daga ita sai Inna. Paa ma ya fice abinshi.

Inna ce ta taso ta, wai tazo su yi girki ma baƙon da zai zo anjima. Mehtav kallonta kawai take, sai tace mata cikinta taji yana ɗanciwo, ba ta jin daɗi, za ta kwanta kawai.

Saboda the idea of cooking for someone ba EHSAAS ba ma, kadai haushi yake bata.

Komawa ɗaki tayi, ta kalli littattafan da tayi order, aka kawo mata har gida daga Amazon. Ta shiga dubawa, duk sune - littafan EHSAAS da tayi searching online, ta gansu. So take ta karanta, duk da ita ba mai yawan karance-karance bace ba.

Amma saboda na EHSAAS ne yasa zata karanta. Gani take kamar in ta karanta littafin, zedan rage mata kewar shi da take mummunan damunta.

Tun da ta fara The Man, babu abinda ke tasheta daga saman gadonta sai sallah. She's just seeing wonders. Is he this amazing? Sai yanzu take tambayar kanta, saboda tsantsar ilimin da ya zuba cikin littafin.

Kuma da ta duba sanda aka yi publishing ɗinsa, yana undergraduate ya sake shi.

Abin sai ya ƙara kayatar da ita kenan. Bata ankara lokaci yayi ba har sai da Inna ta shigo. Ganinta tayi ta burying face ɗinta cikin book, tayi sakatoto tana faɗin:

"Menake gani Mehtav? Ciwan cikin kenan? Ke da na ɗauka barci kike tuntuni."

Kasa tayi da littafin, tana turo mata baki take faɗin, "Ai na warke is."

Inna tace, "Toh maza tashi ki shirya kinji, yaron nan yazo ya aiko Jabeeru, yanata kiran lambar wayarki, ba kya ɗagawa?"

Kallon wayarta da ke gefe a silent tayi. A ranta ta raya, ko a ina ya samu lambar ta? Sai kuma ta tuna Abeey. Kasa-kasa ta ja tsaki, tana miƙewa.

Babu abinda ta shafa a fuskarta. Ta ɗauko katon hijab dinta, ta zira, ta firo.

Inna tace, "Mehtav, me zan gani? Haka zuwanta na farko fa kenan. Fisabilillahi, ki dan yi ado mana."

Kicin-kicin tayi da fuska, tana faɗin: "Tohm Inna, daman se na yi kwalliya yake sona kenan?"

Cikin kulewa Inna tace, "Ni ba nace miki haka ba, amma ki je gaban saurayi, ko kwalli babu a fuskarki, kamar wacca ta tashi daga barci ko an korota. Dan goga yar hoda da kwalli mana."

Zama tayi saman gado tana faɗin, "Ni yaji yake min a ido. Ban so."

Inna, sanin duk salon cewa ba zata je take nema ba, sai tace, "Zo ki je kawai. Allah ya bada sa'a ya haɗa kanku."

Har cikin ranta taji, tace ba amiin ba.

Binta ta yi a baya, zata kai mata duka. Takauce a guje tana nufar waje tana kyalkyala dariya, don tasan ta tsokano Inna.

Seda ta fita sannan ta tsaya ta saita kanta, ta daina gudu, ta nufi falon Paa. Mamaki taji ganin baya nan, sai ta fito. Can ta hangosu tare da su Jabeeru, yana zaune akan bench dinsu, suna ta hira kamar ba Ahmad Gaya ba - girman kai ba komai - sai ta ga ya ɗan burge ta, amma ba cancanta ba.

Da alama ya hangota, ta ga ya miƙe yana miƙa wa su Jabeeru hannu, suka gaggaisa kafin ya ƙaraso gurinta, yana taku cikin nutsuwa da wani irin aura da ke tattare da shi na tashen samartaka da kuɗi.

Amma me? Sam, sai ta ga takunsa ba yayi kyau kamar na EHSAAS ba.

"Ina kwana ma," ya faɗa cikin sigar tsokanar da ta zama jinin jikinsa lokacin da ya ƙaraso gunta. Amma ko kaɗan bata ji ya burge ta ba.

Tace, "Lafiya lau, ina kwana."

Murmushi ya saki mata, shima yana da dimple a gefen kumatunsa da suke lobalowa in yayi dariya. Amma sam, sai take ga babu wanda dimple ya fi kyau sama da EHSAAS.

Kasan shade ɗin babbar bishiyar da ke compound ɗin ya mata nuni, yana faɗin: "Muje ko?"

Ba tace masa komai ba, ta bi bayansa. Ya ja mata ɗaya daga cikin fararen kujerun da aka ajiye na shan iska, ta zauna tana ce masa "Thank you." Shima ya zauna yana kallonta ƙasa-ƙasa saboda ba ya son ya cika kafa mata ido ta ji feeling uncomfortable.

Wani irin awkward silence ne ya shiga tsakaninsu bayan da suka gama gaisawa. Ya tambayeta "Ya mutan gida?" Ta amsa masa da "Lafiya lau."

Yace: "Ina mutuniyarshi Abeey?"

Tace masa: "Tana school," kafin ta ja bakinta ta yi shiru.

Dake Ahmad mutum ne mai magana, sai ya soma mata hira. Farko ya yi introducing kansa - shi waye, inda aka haife shi, matakin karatunsa da sana'arsa - none of which Abeey ba ta riga ta zayyana mata a daren jiya ba.

Amma, dayake daga bakinsa ke fitowa wannan, sai ta fi bada hankali tana sauraronsa, duk da yadda take jin kanta kamar akan kaya.

Yana gamawa yace: "Kinyi shiru abinki, I admire your calmness."

"Thanks," kawai tace masa.

Yace: "What about you Mehtav? I'll love to get to know you better."

Ɗan jim tayi kafin tace: "There's nothing much to know about me. And how can you like someone without knowing them that well?"

Ta ƙarasa tana ɗauke idonta saboda ba ta son ma ta cika kallonsa.

Ɗan gyaran murya yayi kafin yace: "You're right, and I admire your directness, Mehtav. Ni kaina I never believed da love at first sight, not until da na yi arba dake. This heart started beating for you."

Ya ɗaura hannuwansa saman kirjinsa yana kallonta. Ita kuma hankalinta yanzu ya koma kan ƙofar shigowa gidansu inda ta ga wasu irin arnayen Rolls Royce suna shigowa compound ɗin da wasu black SUVs.

Kirjinta taji yana bugawa da ƙarfi da ƙarfi haka kawai saboda plate numbers ɗin da tayi arba da su da yake nuni daga royal family na NURISTAN suke.

Har motocin suka gama parking a harabar gidan guda biyar, daidai da dogarai suna sakkowa da wasu black BGs suna buɗe ƙofar motar tsakiya.

Kafafuwansu ne suka fara fitowa masu yi, wanda kallo ɗaya ta yi masa, kirjinta ya ƙara sauti.

Ta ji kamar jinta da ganinta na neman ɗaukewa. Har ya gama fitowa gaba ɗaya daga baya ba ta iya ganin fuskarsa ba. Amma ba za ta manta da wannan ƙakkarfar figure ɗinsa ba.

White suit ce a jikinsa. Tana ganin yadda dogarai ke kasa da kansu suna gaishe shi, kasa riƙe kanta tayi. Da sauri ta miƙe, ba ta ji me Ahmad ke faɗa mata ba.

Ta soma nufar inda yake tana wani iri murmushi. Koda ba zai so ba, in ta ganshi kawai hakan yana sata farin ciki.

Daidai yana juyowa, ta ƙara sauri. Wani dark google ne idonsa wanda ya ƙara ma farar fuskarsa kyau.

Duk da idonsa na cikin glass, amma ta tabbatar kallonta yake.

Sai da ta ƙaraso daf da shi, tayi turus, taji jiri na neman ɗibar ta saboda gani tayi kamar kamanninsa sun kuma rikide, sun fara sauyawa.

Kamar za ta faɗi. Da sauri Aman yayi ƙoƙarin tareta. Ba ta barshi ya taɓata ba, ta ɗaga masa hannu ɗaya, tana sake warware idonta.

Ta ɗaura kanshi. Wannan karon ya cire 👓 din fuskarsa.

Ta shiga kallonsa kamar ta ga wani zombie. "Ba shi bane ba, ba shi bane ba," zuciyarta ta shiga raya mata, tana jin ƙuncin da take ciki yana dawowa.

Aman yace: "Sannu, are you okay?"

Kallonsa ta ci gaba da yi, wanda yasa ya yi murmushi yana faɗin:

"Kin ɗauka shine ko? Hhh. Ba ke ce mutum ta farko da tayi mistaking dina for uncle Prince ba. I'm Aman, his nephew," ya faɗa silently - wannan karon, not like his usual jovial introduction da yake yi a baya with full confidence.

Yace shi ɗin nephew ɗin EHSAAS ne, saboda he can't even place asalin mamarsa.

'Yar Erfan ce - kanin mai Martaba - har yanzu. Saboda kalar kamar mai Martaba da ya debo kamar dai EHSAAS.

Wanda ba abin mamaki bane, saboda zuriyarsu gaba ɗaya kamanninsu ɗaya ne.

Mehtav tace: "Excuse me," tana gyara tsayuwarta tana kallonsa.

Kafin ta daure ta sakar masa murmushi tana ƙara jinjinawa sarautar Allah da irin wannan kama.

Amma sai da ta matso kusa take ƙara ganin ba wani ma cancanta suke ba.

Hasken fatarsu ne iri ɗaya, da yanayin jikinsu. Duk da yanzu ta gane EHSAAS yafi wannan ƙauri.

Kuma idanuwan wannan bakake ne. Na EHSAAS grey eyes ne.

"Sannu Aman," ta faɗa tana murmushi, wanda yafi kala dana.

Yace: "You must be Mehtav right?"

Cikin mamaki take kallonsa ba tare da ta bashi amsa ba.

"Mehtav, right?" ya sake tambaya.

Ta jinjina kai tana faɗin: "Yes. Ya akayi ka san ni?"

Rufe baki yayi, sai kuma ya sake buɗewa yace:

"Wow, wow, you're more than abinda na yi imagining. So I'm in front of my uncle's saviour right now," ya faɗa yana dan mata salute, dayake he's a very friendly man.

Yace: "I've heard so much about you, the saint Mehtav."

Ba tare da tasani ba taji ta saki masa murmushi, don yadda yayi maganar da girmamawa kamar ya ga wani Shehun Malam, sai kai dariya.

Gashi yace he heard much about her - kenan EHSAAS ne ke bashi labarinta.

Yace: "Ki yi hakuri I came here unannounced, without notice. Amma saƙon ne aka aikoni dashi zuwa gurinki ke da Dad ɗinki. In babu damuwa zamu iya shiga ciki?"

Sai a lokacin ta tuna da Ahmad da ta barshi a zaune.

Sai taji duk babu daɗi.

Tace masa: "Ina zuwa, bani minti kaɗan."

Komawa tayi, har lokacin kuma yana zaune. Taga alamar kamar ma ba ya damu da tashin da tayi without notice ba.

Yana danna wayarsa.

Ta tsaya a gefensa, sai a lokacin ya dago a hankali.

Tace: "Uhm, sorry I was carried away, nayi baki ne."

Murmushi taga ya saki kafin yace: "Is okay. Kungama ne?"

Yana kallon direction din Aman da ya kafa masa ido ya ƙi ɗaukewa.

Girgiza kai tayi tana faɗin: "Shiga ciki zamu yi yanzu."

Ya miƙe yace: "Oops, nazo wrong time kenan Princess. Zan dawo some other time."

Jinjina masa kai kawai tayi.

Ya ce: "Take care of yourself."

Ba ta ce masa komai ba. Kafin ya mata bye, ya juya.

Tana kallon bayansa har ya ƙarasa kusa da motarsa.

Wayarsa taga ya ciro yana dannawa na tsawon lokaci kafin taga yayi wa dan Liti da Jabeeru alamu, suka ƙaraso da sauri bayan motarsa.

Ya buɗe musu suka shiga.

Fito da wasu manya-manyan shopping bags.

Ita kuma ganin abinda suke yi yasa tayi saurin wucewa gurin Aman.

Tana mai iso cikin falon, fa dogaransa suka tsaya a waje.

Fitowa tayi daga falon ta nufi cikin gida.

Ba ta kalla jakunkunan shopping da aka ajiye a falon ba.

Ta tafi ɗaki, ta kira Paa, ta sanar da shi zuwan Aman ɗin.

Ta wuce kitchen.

Inna na shirin haɗa tray, ta kira Mehtav ta ɗauka.

Taganta ta dawo, tace: "Menake gani? Ba dai har kun kammala ba?"

Jinjina kai tayi tana faɗin: "Eh, ya tafi. Yace zai dawo wani lokacin."

Tagumi Inna tayi tana faɗin: "Allah yasa dai ba bakin halin nunƙufarcin ki kika je kika gwada mai ba."

Dariya taga Mehtav tayi - abinda bata tsammani ba.

Taga ta sunkuci tray ɗin tana faɗin: "Thank you Inna," ta fice.

Kawai Inna ta bita da kallo tana tunanin inda za ta kai tray ɗin bayan tace baƙon kuma ya tafi.

Hanyar falon Paa ta nufa.

Kalmomin "I've heard so much about you," da Aman ya faɗa tana tunani.

Kenan EHSAAS bai manta da ita ba - har yana bawa nephew ɗinsa labarinta.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Vote & Like [05/07, 20:16] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's Fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.