Chapter 44
Ahankali ta ajiye tray ɗin hannayenta saman center table ɗin falon kafin ta ɗago ta kalli Aman da yake waya yana murmushi yana kallonta. Itama murmushin ta mayar masa tana samun guri ta zauna, domin ba za ta iya barin baƙon EHSAAS shi kaɗai ba. Gatanan ma ai, taji ya faɗa yana kallonta kafin ya miƙa mata waya. Kallonsa ta yi kafin ta kalli wayar hannunsa cikin ɗan mamakin me za ta yi da ita. Yace magana za a yi da ke yana murmushi. Wani irin skipping taji kirjinta yayi saboda sanin kila EHSAAS ne. Yau EHSAAS ke nemanta a wayarta. Yau zata ji muryarsa after many months.
Ahankali ta ƙaraso ta karɓa, ta zauna a kujerar gefen Aman wannan karan. Ta karɓi wayar ba tare da tayi magana ba ta kara a kunnenta.
Mehtav taji an furta daga dayan side ɗin cike da irin farin ciki ɗinnan. Tace "Na'am," da ɗan disappointment a tone ɗinta da fuskarta, jin muryar wacca bata yi tsammani ba, don bata taɓa tunanin bayan abinda ya faru anan ba, Islam zata taɓa nemanta a rayuwa.
"Mehtav, ykk? Ygd? Yasu babanki? Yasu Abeey?"
Islam ta shiga jera mata tambayoyin kamar tana gabanta, with full of concern. Mehtav tace, "Muna nan lafiya, alhamdulillah."
Islam tace daga daya ɓangaren, "Dan Allah kiyi hakuri kinji. Baki jimu ba ni da Sire har zuwa wannan lokacin. Jikin Mai Martaba ne se ahankali, amma wallahi kina ranmu kusan kullum. Saina ce ma Sire yaushe ne za mu je mu ganku, se yace 'da saura, ba yanzu ba.' Hope ba ki yi fushi ba?"
Ɗan murmushi Mehtav tayi saboda jinjina kalar kirkin Islam ɗin a ranta. Tana wondering, Kena har sun shirya sun jone? Shedan na ɗan samata jin wani iri-iri a ranta, amma se daya zuciyar ta shiga tausarta tana faɗin, Tsakanin mata da miji se Allah, kuma barema su da suke matuƙar kaunar junansu.
Ahankali ta buɗe baki tace mata, "Ba komai Maman Jr, Allah ya bawa Mai Martaba lafiya. Fatan kuma duk kuna lafiya."
Islam tace, "Alhamdulillah muna nan klau." Tace, "Ya Jr?"
Tace, "Mutumin naki yana can gurin mutuniyarshi Maama, shiyasa bakina zobe." Murmushi Mehtav tayi, sanin mahaifiyar EHSAAS take ce ma Maama.
Islam tace, "Mehtav, please do accept my request. EHSAAS ya yi magana da babanki, yace ba shi da matsala se hukuncin da kika yanke."
Ɗan jim Mehtav tayi kafin tace, "Wane request ne wannan?"
Islam tace, "Fulani ce take so ta ganki. Kinga tana jinyar Mai Martaba, ba zai yiwu tazo nan ba. Shi kansa Mai Martaba yaji labarin kalar alherin da kukama EHSAAS. Wallahi da ba dan jikinsa ba, da kansa zai zo. Shiyasa nake miko kokon bara ta agareki. Dan Allah ki amince da takardar gayyata ta zuwa NURISTAN."
Wani iri taji tsinkewa. Mehtav taji gabanta yayi saboda ta san abu ne da ba zai yiwu ba. Ta yama Paa, wai zai yarda? Taji kuma tace EHSAAS yayi magana da Paa.
Shiru tayi, ta kasa ce mata komai.
Islam ta dan marairaice, ahankali take faɗin, "Mehtav, please. Ba dan ni ba, nasan akwai differences me girma tsakaninmu. Nasan cewar maybe yadda muka rabu ne yasa kiji ba ki son zuwa inda nake. Amma ki duba dattijannan guda biyu da suke son ganinki. Ki daure ki yarda Mehtav."
Ɗan shiru tayi kafin tace, "Duk abinda Paa yace banida ja akansa."
Murmushi taji Islam ta saki tace mata, "Thank you so much Mehtav. Dan Allah ki bawa Aman number ɗinki ya turomin, saboda ina son mu cigaba da zumunci a tsakaninmu."
Jinjina kai kawai Mehtav tayi kamar tana gaban Islam. Surprisingly, yau itace tazama miskila, ta kyale Islam nata magana. Godiya Islam tayi mata jin ta amince, kafin su yi sallama. Ta katse wayar tana miƙawa Aman wayarshi, daidai Paa da Abeey na shigowa. Dayake ya bi ta hanyar makarantar ya ɗauko ta yau, bus ɗin da take kaisu ta dawo da su tasamu matsala. Itama daga baya ta hangoshi, aiko ta ɗako tsalle tana faɗin, "Handsome, handsome! Ga handsome prince ɗinmu ya dawo!" Wuyansa ta makale da yasa Aman ya yi kokarin juyawa ya kalleta, amma ta bi ta cukuikuyeshi, ta ƙi bashi damar hakan, har seda Paa yace ta sake shi, tukunna ta sake shi.
Ya juyo, ta fara kallonsa kafin tayi baya, itama tana wara ido. "Kai, kai! Wallahi bash bane!" Ta fara nunawa Mehtav kafin ta ƙarasa kusa da ita ta zauna tana faɗin, "Allah mai iko! Yah Mehtav, kinga kamar da nake gani kuwa? Kamarsu ɗaya da EHSAAS fa. Are you his twin brother?" Ta ƙarasa tana kallon Aman da yake mata murmushi. Ya girgiza kai.
"Tab, amma kai ƙaninsa ne. Kaima prince ne," ta ƙarasa tana kallonsa cike da admiration na abinda baka taɓa gani ɗinnan ba.
Girgiza kai yayi yana faɗin, "I'm his nephew."
"Wow," tace tana jinjina kai.
Paa ne ya zauna yana faɗin, "Ya hanya Aman? Kasha zaman jirgi?"
Murmushi Aman yayi yana faɗin, "Barka da yamma Alh," yana ƙarasawa ya miƙa mai hannu. Sukai musabaha, ya amsa gaisuwarsa.
Yace, "Da aida kun sanar min zuwanka da nasaka an je an ɗaukoka daga airport. Da kuma nasan Mehtav ta shirya maka wani abu."
Aman ahankali ya kalli Mehtav, da jikinta gaba ɗaya yayi sanyi. Domin ta gane cewar zuwan Aman ma ba EHSAAS ne ya turo shi ba, Islam ce. Kenan bema damu da ita ba. Ya ma manta da ita. Ina alkawarin da yayi mata na cewa zezama yaya kuma abokinta? Ya manta kenan.
Ihun da Abeey ta fasa ne ya dawo da hankalinta kan abinda suke.
"Yah Mehtav, za mu je NURISTAN! Wayyo Allah na! Daɗi! Zan je naga palace, zanga sarki fa! Sarki!" Yah Mehtav jitai kamar ta tashi ta kwada mata mari wallahi, saboda yadda take wani ihu kamar ba ta taɓa shiga wata palace ba a duniya.
Kallon Paa tayi da pleading eyes irin pls, yace, "No."
Dinnan Paa yayi jim yana kallon Aman, har ya gama mai bayani, ya faɗa mai duk ya siya musu tickets da komai. "In ba matsala ko zuwa gobe se su wuce."
Dogon numfashi ya ja kafin ya kalli Mehtav yace, "Mehtav, kin amince mu je?"
Kallon Aman take ta ƙasan ido, yadda ya zuba mata ido yana jiran amsarta. Gashi zuciyarta ba ta son zuwa saboda kar ta ga EHSAAS. Abinda take ta kokarin dannewa a ranta ya sake tasowa.
Abeey ce ta riƙe hannayenta tana faɗin, "Yah Mehtav, dan Allah ki ce eh, kinji? Pls, pls, ki ce eh."
"Abeey, school ɗinki fa? You're about to start your Terminal Examination in the next two weeks. You can't travel," cewar Mehtav tana kallon Paa. Tace, "Paa, kaga Abeey needs to study well for the exams ko?"
Kallon Abeey yayi wacce ta yi saurin miƙewa tana faɗin, "Wallahi nayi karatuna ni tuntuni. Kuma aida saura jarrabawar fa, saura sati biyu. And you know I study ahead of time. Kinsan kaina yanaja duk shekara Grade A nake ɗauka."
Tasan Abeey gaskiya take faɗa, amma kuma ta ƙi amincewa saboda ta san shi kaɗaine excuse ɗin da zata yi amfani da shi, Paa ya ƙi amincewa su je ɗin.
Aman yace, "Then fine. Gaskiya nima ban goyi bayan baby Abeey ta yi missing school ba. Se ta zauna a gida intagama exams se ta zo. Da kaina zan dawo in ɗauketa mu je."
Abeey fasa kukan da taje ta faɗa jikin Paa tana faɗin, "Itafa bata yarda ba! Tana son taje taga handsome prince! Dan Allah a je da ita!" Paa lallashinta ya shiga yi yana faɗin, "Abeey kiyi hakuri kinji? Ni da Mehtav mu fara yin gaba. Kinga in mun dawo, ke da Inna se ku je."
"Ni bazan zauna anan da Inna ba! Ka fata kafar Yah Mehtav, ni banason zama da Inna! Please, please ku je dani!"
Rungumeta Paa yayi, ta cigaba da kukanta.
Mehtav asanyaye tace, "Paa mu bari se ta gama exams ɗin toh." Cikin son zamewa zuwan.
Paa ya girgiza kai yana faɗin, "Mehtav, I already said yes to EHSAAS. Kinsan ba zaku maidani ƙaramin mutum ba."
Se ta shiru kafin ta kalli Aman tace, "Yaushe ne tafiyar?"
Yace, "Gobe in Allah ya kaimu."
Se tace, "Tohm, Allah ya kaimu. I'll take care of Abeey's studies da kaina, saboda bazan iya tafiya tare da ita ba."
Da sauri Abeey ta dago tana kallon Mehtav, ta washe baki ta bar gurin Paa ta zauna a gefenta tana faɗin, "Za a je dani da gaske?"
Jinjina kai Mehtav tayi tana goge mata hawayen fuskarta gently, jiki a sanyaye.
Yay! Ta faɗa cike da murna tana rungume ta. Aman cike da admiration yake kallonsu, domin yanayin yadda family ɗin yake ya burge shi, duk da yana iya ganin damuwa a kan fuskar Mehtav, daya shiga wondering kodai ba ta son ganin EHSAAS ne.
Mikewa yayi yana excusing kansa, yace akwai saƙon da Princess Islam ta bayar a bawa su Mehtav da Abeey. Kamar tabishi, tsabar zumudi.
Bai jima da fita ba, sai ga su Jabeeru da shigowa da wasu irin haɗaɗɗun boxes da Mehtav tun da take a rayuwarta bata taɓa ganin irinsu ba. Haka suka ringa shigowa da su guda sha biyu rairai, sannan suka musu sallama suka wuce.
Abeey ce take ƙoƙarin tashi ta je kan kayan, Mehtav ta riƙe hannayenta tana zare mata ido tana nuna mata ƙofa, alamar Aman na tahowa. Ta shiga ta tayinta.
Da ƙyar ta iya tattaro nutsuwa, but she's still giggling tana kallon shi kansa packaging ɗin da ya gama ta'asar kanta.
Da sallama Aman ya shiga falon, ya ƙarasa gefen Mehtav ya ajiye mata wani royal envelope da aka rufe da stamp ɗin masarautar NURISTAN, aka yi folding ɗinsa da wani golden ƙyalle mai mugun kyau.
Yace, "Ga saƙon Princess ɗin, tace a bawa yaran." Yana kallon Paa da mamaki, ya kashe shi a zaune, "Wannan hidima haka ai tayi yawa," ya faɗa yana kallon Aman.
Gaskiya, "We can't accept all this, sun yi yawa fa,"
Murmushi Aman yayi yace, "Ba kyau maida hannun kyauta baya Alh. Ayi hakuri a karɓa, saboda ba zai yiwu in mayarwa da Princess wannan kayan ba. Za ta ga laifina ne sosai. Dan alheri ne ta yi ma yaran. Ina fatan zaka hakura, ka daure ka karɓa."
Kallonsu Abeey yayi, da ta zuba mai ido tana marairaice, alamar "Yabari." Idon Mehtav a ƙasa, tun da ta ma boxes ɗin kallo ɗaya bata sake kalla ba.
Yace, "Tohm. Ka ce mata an gode, Allah ya saka da alheri."
Wani murmushi Abeey ta saki tana faɗin, "Me kama da handsome kace an gode."
Murmushi yayi mata yana faɗin, "Za ta ji kyakkyawa."
Daɗi tayi kamar ya kashe ta, yace mata kyakkyawa.
Daga nan ya mike yayi musu sallama. Duk da yadda Paa yace ya sauka anan, amma haka ya ƙi, yace mai ai already an tanadar mashi masauki a embassy ɗin NURISTAN dake nan, kuma akwai abinda zai yi a can ɗin.
A ƙofar mota, Abeey da Paa suka rakashi, ya wuce.
---
Abeey da sauri ta dawo tana fizge ƙaramin hijab ɗin school dinta, tana warware necktie dinta. Ta hau kan boxes ɗin, daidai Inna na shigowa, don ta ga fitar motocin daga gidan, tana tambayar ba'asi. Taga Abeey na ƙoƙarin warware boxes. Washe baki tayi tana faɗin,
"Menake gani haka Habibu? Ba dai lefe ne har an kawo ba saf saf?"
(Sharp sharp) ta ƙarasa tana taya Abeey buɗewa.
Abeey tace, "Inna, ba saf saf ake cewa ba, sharp sharp! Kuma wannan ba laifenta bane. Gift ne Islam ta turo, aka kawo mana."
"Islam kuma, wacce kenan?" Inna ta tambaya tana kallon Abeey da tayi busy tana buɗe box.
Tace, "Matar prince mana. Wannan maman baby ɗin nan dan lukuti mai kyau."
"Ayyo, na ganeta! Ita ce! Duk ta aiko muku irin wannan abin arziki haka?"
Ihu Abeey ta saka lokacin da ta ƙarasa buɗe boxes ɗin.
Ta farko, wasu Valentino Haute Couture Gown's ne - both size ɗinta da na Mehtav. Sai Dark Emerald Green Lace, hand-beaded with South African diamonds.
Box ta biyu kuwa: Christian Louboutin Gold-Soled Heels ne - lambar ƙafar Mehtav da tata kuma Exclusive Royal Edition.
"Innalillahi Yah Mehtav kinga!" Ta daga takalman tana nuna mata.
Mehtav ta tsaya tana kallon ƙyawun takalman, ta soma tunanin meyasa Islam za ta yi honouring ɗinta haka bayan ta san niyyarta a kan mijinta.
Sauran boxes ɗin kuwa suna ɗauke da:
Cartier Diamond Wristwatch, 18-karat rose gold with pink diamond bezel
Chanel Perfume Gift Set, Limited Royal Collection
Hermès Birkin Bag mai Crocodile Skin, Gold Buckle
Royal Jewelry Box cike da emeralds, rubies, da sapphires
Box ta uku kuma:
MacBook Pro M3 Max 1TB - Platinum customized casing, guda biyu
Sai ƙaramin box mai ɗauke da:
iPhone 16 Pro Max, Royal Edition, engraved with their names and palace crest
Abeey rungume wayoyin tayi tana faɗin, "Paa! I finally have a phone! Kaga ka huta, ba sai ka siyamin ba. Wayyo waya!"
Ta koma kan Mehtav tana nuna mata, "Wai takalmin harda sunanta a jiki!"
Mehtav murmushi tayi tana faɗin, "Yayi kyau."
Inna ta shiga daga kayan da yake cikin boxes ɗin ƙarshe tana faɗin, "Ikon Allah! Wannan kamar kayan barci nake gani."
Abeey ce ta ƙaraso tana kalla tace, "Inna, this is not ordinary sleepwear! Kalleshi fa - is handwoven! Wannan daga gani daga Istanbul ko Persia aka yosu."
Ta shiga duba royal silk sleeping wears ɗin kafin hankalinta ya koma kan:
Skincare and Spa Set da aka siya na musamman daga Japan da Morocco
Da wasu Luxurious oils and serums.
Tana gamawa kuwa, ta tafi ta ɗauki envelope ɗin da Aman ya ajiye ma Mehtav.
Karo taci da:
Flight Tickets to Nuristan, First Class Emirates
Royal Palace Access Card - Laminated with sapphire-stone edge wanda zai ba ka access da shiga fadar NURISTAN a duk sanda kaga dama ka je.
Sai wasika da taci karo da ita - that is handwritten...
Ta soma karantawa a fili kamar haka: To the Honorable Miss Mehtav and Beloved Abeeda (Abeey), Her Royal Highness Princess Islam of Nuristan humbly invites you to the Royal Palace of Nuristan for a special evening of appreciation, joy, and royal bonding. May these gifts remind you that you are treasured beyond measure. Looking forward to seeing you and Abeey at the Palace soon. Love, Princess Islam.
Abeey bakinta ya kasa rufuwa. Haka itama Inna tace, "Ikon Allah! Yarinyar nan kuwa, da nace karta manta damu, ashe bata mantaba. Amma dai ta cika 'yar halak. Duk da ban ji ta kira sunana a cikin wasikar taku ba, amma dai shatara ta arzikin nan da tayi muku. Allah ya shi mata albarka. Habibu, duba fa! Ashe haka take da kirki? Mehtav, ki ka so sallah mata iya shege wancan lokacin."
Ita kanta Mehtav, she's feeling guilty sosai. Bata ɗauka zuciyar Islam na da fadi kamar haka ba. Wallahi, ba za ta taɓa iya yi wa mace da ta ko da furta tana son mijinta sau ɗaya kallon arziki ba, balle ace har ita take gayyatar ta zuwa gidansu kuma ta bata waɗannan haɗaɗɗun kayan wanda zata iya sawa ta sace zuciyar mijin gaba ɗaya.
Sai wata zuciyar tace mata, Ta ina? Ta yarda da kanta ne. Tasan mijin nata ba zai taɓa kallon ki ba, shiyasa take duk abinda take yi.
Paa yace, "Gaskiya tana da kirki. In anjima, se ku kirata ku yi mata godiya."
Jinjina kai suka shiga yi. Yace su haɗe kayan, Jabeeru ya shigar musu da shi ɗakinsu.
Inna tana ta ɗagawa wai ko za ta ga abinda zata ɗauka. Aiko ta ci karo da jewelry box, ta kwashe rabonta har suna faɗa da Abeey, sannan ta fita ta bar su.
Abeey ta juya ga Mehtav tana faɗin, "Yah Mehtav, kinga abin arziki koh? Royal family ake faɗa musu basa kyauta ƙarama. Yanzun dai, meye matsayarki akan auren Ahmad? Yau kuka yi da yazo."
Kallonta tayi, lamarin Abeey na ƙular da ita. Yanzun nan fa she's head over heels for EHSAAS, amma tana mata maganar wani Ahmad.
Mikewa tayi tana faɗin, "Ki ka sake min maganar wani, sena saba miki."
Ta nufi ƙofa, Abeey ta tattara hijab ɗinta da jakarta tana biyo bayanta. Ta fara magana ƙasa ƙasa, tana faɗin: "Nifa sam ban ga laifinki ba. In ki ka ce ba za ki auri kowa ba sai EHSAAS, kalli yadda matarshi tayi mana wannan kyautar. Ina ga shi, in ke ma ki ka zama matarshi haka za ki ringa yin irin wannan kyaututtuka na girma-ko ma fiye da haka. Ki lallaba, in dai da dama, ki shiga. Ko a ta biyuce. Kinga sena dawo gidanki abina luf-luf."
Juyowar da Mehtav ta yi a fusace yasa ta yi saurin juyawa tana kyallawa, ta koma baya. "Wallahi da gaske nake miki, Yah Mehtav. Ni bana bin ƙarya. Duk inda yafi kuɗi, nan nake yi."
Cikin ɗaga murya take faɗin, "Abeey wai me yasa ba kya tsoron Allah ne, eh? Ki fa yi wa kanki fada. Kuɗi ba shine rayuwa ba! Ko haka muka koya miki? Where do I went wrong ne a tarbiyyar ki har ki ka san kuɗi?"
Riƙe kugu Abeey tayi tana zazzare ido. Duk da tayi maintaining distance dinta da Mehtav, amma kamar ka ce cricket ta gudu, saboda ta san Mehtav ta fusata da maganganunta.
Mehtav tayi ƙwafa tana nuna ta da yatsa. "Don't let me catch you! In na sake jin maganar 'masu masu kuɗi' ko wanda yafi kuɗi a bakinki, sena yi maganin ki!"
Ta ƙarasa tana shigewa ciki. Ko ba ta kalli kayan da Ahmad ya kawo ba, saboda wani abu da ya gama cake mata a rai-abu mai kama da tsoro da jin tausayin kai mai girma. Saboda yadda ta san EHSAAS ya mata tazara mai nisa wanda ba za ta iya cimmawa ba.
Bayan an yi sallar magrib ma, kasa fitowa falo tayi. Duk da tana jin hayaniyar su Inna da Abeey anata firar kayayyakin da ta samu, both daga Islam da Ahmad.
Kuma Abeey, se da aka yi isha ta lallaba ta shigo ɗakin. Already tayi wanka a ɗakin Inna, ta saka ɗaya daga cikin kayan da ta kan bari a can. Sadaf sadaf, ta nufi closet box dinta, ta ɗauko ahankali, ta shiga hada musu kaya kala bibbiyu-ita da Mehtav-don Paa yace mata kwana ɗaya zasuyi kawai, su dawo.
Cikin kayan sallar su na bana da bama a rigada an sa ba, ta shiga zaɓa, ta dirje, ta zira a box ɗin. Tana faɗin, "Tuwan girma ai miyarsa nama," don itama tana son a gansu da capacity ɗinsu.
Tana fitowa zata fice da box ɗin ta boye a ɗakin Inna, taji Mehtav tace, "Wane kayan kika ɗiba?"
Kawai daman idonta biyo ta. Ta shiga tambayar kanta sanda taga ta mike zaune tana kallonta, tak wiki-wiki da ido tana faɗin, "Eh eh..."
Mehtav taci magani tace, "Bude box ɗin in gani."
A hankali Abeey ta kwantar da box ɗin, ta zuge tana gintse idonta don tasan ba lallai Mehtav ta bar ta ta saka kayan sallar.
Mehtav ta kare ma kayan kallo kafin tace, "Tohm, rufe."
Da mamaki take kallon Mehtav da ta koma ta kwanciyar ta. Tace, "Yah Mehtav kin barni mu saka kayan sallar?"
Tace, "Ko ba shi kike so ki sa bane uhm?"
Girgiza kai Abeey tayi da sauri tana faɗin, "Shi nake so ai."
Tace, "Tohm, kama gabanki, kar ki damani."
Da sauri tace, "Tohm," don ba ta son Mehtav ta canza ra'ayinta.
Ta fice da box ɗin tana jin daɗi. Yau ranar sa'arta, tace, ta shiga rayawa a ranta.
Ranar, da daddare, ta dawo ɗakin, ta kwanta. Mehtav tana jin ta, ta gama iya-iyanta, har da gwada yadda zata gaida sarki. Duk sai da ta yi practicing kafin barci ya ɗauketa.
Mikewa tayi, ta ƙarasa gadonta, tayi mata addu'a, sannan ta shiga bathroom, tayi wanka, ta ɗauro alwala, ta zo ta yi sallar isha' da batai ba, tayi shafa'i da wutri, tayi addu'o'i, tukunna ta kwanta.
Barci juyi kawai take tana ji. Inama kada gobe tayi, saboda tasan in dai har tayi tozali da EHSAAS, soyayyarsa ce sabuwa zata dawo zuciyarta.
Gajiya tayi da tunanin EHSAAS. Hakan ne yasa ta ja wayarta da niyyar duba time kawai, sai taga missed calls ɗin Kamal da Ahmad - rututu, musamman Ahmad, don shi har da text, yana tambayarta: "Ya take? Hope she's fine? Ya baki?"
Bude wa tayi, tana kallon time - sha biyu saura. Kamar ta share, kar ta maida masa reply, sai kuma ta tsinci kanta da dannawa, ta rubuta masa: "I'm fine alhmdlh. Baki sun tafi."
Kawai sai taga yana typing, kamar daman wayar na hannunsa. Ta dan zaro ido tana kallon yadda kmr zata dakatar da shi, sai ganin message ɗin da ya sake shigowa:
"Guess real Princess na ɗauko, saboda naga bakin naki har da dogarai aciki. A gai she min da shi."
Ya faɗa yana dan saka emoji ɗin kanne ido alamar tsokana, don shi a ransa ya raya daya daga cikin suitors ɗin ta ne.
Har za ta mai banza sai kuma ta mai typing da zai ji kawai...
Emoji ɗin zare ido ya saka mata kafin ya saka: "Hmm... Har na ji kishi. Da alama ana ji da prince ɗinnan. Kice mai 'dan mutan gaya' ya rigashi."
Dariya ma ita ya bata da yace 'dan mutan gaya' nan... kmr wani ƙaramin yaro.
Tace, "Wa yace maka prince ne?"
Yace, "Everything about him screams that. Amma dai da alama prince ɗin Larabawa ne, ba na mu ba."
Banza ta mai, bata yi reply ba saboda bata san me za tace masa ba. Sai taga ya rubuta:
"If I can guess well, he's from Persia, Nuristan or Indonesia."
Shiru ta mai, tayi leaving ɗin shi unread. Ta ajiye wayar tana jin she don't owe him any explanation. Yaje yayi duk tunanin da zai yi.
Tayi kwanciyarta. Da ƙyar barci ya iya ɗaukarta, don har makara sallah sai da tayi - duk da bugun ɗakinsu da Paa ya rinka yi. Ashe Abeey ta tashi, amma saboda ta shiga bandaki tayi amfani da skincare products da ta hanata amfani da su saboda sun mata ƙarfi, taƙi tashi ta sallar.
Ai kuwa tana farkawa, ta wuce toilet, aciki ta same ta - ta saka mask, tana ta raye-raye ita kaɗai da wayarta da ipods ɗinta duka, don bata rigada ta haɗa wayar da aka kawo musu jiya ba.
Cike da takaici Mehtav ke kallonta ti tsuru-tsuru. "Get out," kawai tace mata.
Sum-sum ta fice kafin ta kwasa a guje ta je ɗakin Inna, saboda tasan kwana biyun nan Mehtav na mugun ɗaga mata kafa, bata biye mata samsam.
Tunda safen, Abeey ke bouncing around the house da excitement, tana shela a gidan kamar dai ba wanda yasan da tafiyar sai ita. Take faɗin: "Hello Nuristan, it's your girl Abeey!"
Inna ma na can tana ta haɗa komatsanta. Ta sa sabon lace dinta, ta saka mayafinta irin lace ɗin, ta fito da bakko dinta.
Tunda Abeey taga bakko, take roƙonta da Allah tayi hakuri ta ɗau akwati, kar ta badasu ace su kauyawa ne. Sai da ƙyar ta amince. Taje ta canzo jakar nan da tayi manipulating ɗinta da cewa ba za a bar ta ta shiga palace ba in dai da wannan jakar ne.
Paa ma ya fito cikin shaddarsa fara kal Getzner, sai ƙamshi take. Ya sa hularsa tangaran, kamar wani sabon matashi.
Abeey sai hyping ɗinsa take yi tana cewa wai: "Ai ko da na shekara talatin ba zai nuna mai iya wanka ba."
Don ta saba tsokanar sa irin haka kamar kakanta.
Ya rage Mehtav kawai suke jira. Da ƙyar ma Abeey ta yarda ta ci breakfast saboda zumudi.
Seda Aman yazo tare da tawagar motocin da zata ɗaukesu zuwa airport tukunna Mehtav ta fito, Cikin simple abaya me shape kamar na Fenty Capsule-baƙa da ta mugun haska farar fatarta-sai Maison Cartier necklace a wuyanta da bracelet ɗinsa. Ta nade mayafin abayan a fuskarta, da yayi mugun mata kyau. Bayan powder da gazal, sai ɗan Chapstick pink kaɗan a lips dinta, da ya bata wani irin elegant look na mace me asalin kyau da aji wacce ba tayi overdressing ba. Don tayi kyau ba da ƙoƙari ba, amma kyanne yake nuna kanshi da kanshi.
Abeey ce ta ƙarasa kusa da ita da sauri tana cewa: "Yah Mehtav kinganki kuwa? Kinhadu!"
Kallonta tayi tana kama hannunta. Kasa-kasa take cewa, "Bawai kinga za a je ƙasar mutane da gidan mutane kije kina sakin baki da uban surutu ki bamu kunya ba. Allah kinga dai bana dukanki koh? Tohm, ki ce zaki rinka irin wannan halin a gidan su EHSAAS, sena fasa miki baki wallahi."
Abeey turo baki tayi tana faɗin, "Allah bazanyi ba Yah Mehtav, nafasan me nake yi."
Mehtav ta jinjina kai tana faɗin, "Inma ba ki saniba, yanzun inason kisani. Because I won't tolerate this shit there."
Ta ƙarasa da hannunta cikin na Abeey, suka ƙaraso suka gaisa da Paa da Inna, da ke tambayarta bazata yi breakfast ba-sabin jirgin karfe goma zai tashi. Ba lokaci, ta jinjina mata kai kawai.
Aman ne ya ɗaukar musu trolley, suka fito. Suna fitowa, kuwa dogarai suka karɓa suka sassaka a bayan mota. Motar su Inna da Paa daban aka tukasu, tasu Mehtav da Abeey ma daban, wacce Aman ke ciki ma haka. Mehtav sai sake gargadin Abeey take, ko a cikin mota har suka fito.
Paa yayi musu ɗan little sallama tare da alheri mai tsoka, yana basu amanar gidan har suka wuce zuwa Nnamdi Azikiwe International Airport.
Tun daga airport din Nigeria suka fara ganin royal treatment, saboda yadda aka fara jidasu. An rufe Special Wing gaba ɗaya domin VIP & Royal Boarding. Emirates First Class Suite aka tanadar musu-each suite worth ₦8.4 million na seat ɗaya, ticket duka na su huɗu ya kai ₦33.6 million.
Kuma ba su kaɗai bane ba, har da Aman da dogaransa.
Abeey sai santi take yi duk da bawai taja taba hawa jirgi ba-suna zuwa Saudi Arabia kuma sukan je vacation ƙasashen Europe lokaci zuwa lokaci, amma ba a first class ba, economy suke hawa. Amma yau gata a first class, daɗi kamar ya kashe ta.
Suna hawa jirgin, aka kawo musu menu na Arabic gourmet dishes: Saffron-infused rice, lamb tagine, caviar da saffron tea. Abeey tace: "Yah Mehtav, kinga fa yadda flight attendants ɗinnan ke jidamu, 'Your Grace' fa suke ce mana. Yau jina nake yi ai kamar nice EHSAAS ma."
Murmushin Mehtav tayi mata saboda tana son taga Abeey cikin farinciki. Haka kasa-kasa take cewa, "Ke, maintain mana. Karki yarfamu."
Abeey tayi dariya tana ci gaba da karanta menu ɗin.
Haka har jirgin ya tashi. Tafiyar awa biyar ce da wani abu zuwa Nuristan, amma ji suka yi kamar awa ɗaya aka yi saboda yadda ake kulada su, ana tattalinsu. Sun ci, sun sha abinda suka so. Anan Mehtav ta samu tayi breakfast ɗin da bata yi ba.
Har da kyaututtuka aka kawo musu daf da zasu sauka a Nuristan. Aka raba musu Limited Edition Gift Hampers da aka yi specially for Royal Passengers, with gold-plated pens and pure oud perfume.
Suna sauka daga cikin Emirates, da Aman a gaba, yay musu jagora suka shiga cikin Royal Limousine zuwa Nuristan Palace.
A yayin da motocin suka ƙaraso gaban masarautar, busa Royal Trumpet aka fara yi cikin girmamawa da nutsuwa, don nuna farincikin zuwansu matsayin su na manyan bakin mai martaba-amma babu yawan hayaniya sosai saboda rashin lafiyarsa.
Duk wani biki an rage shi saboda wannan dalili, amma dai sun ga karamci mai tarin yawa.
Manyan dogarai ne suka buɗe musu ƙofa lokacin da aka karaso dasu cikin palace ɗin. Aka shimfiɗa musu farin Royal Carpet daga bakin ƙofa har zuwa cikin Royal Main Courtyard. Aka tsayar da Flower Girls guda shida, kowacce sanye da Royal Silk Gown, suna jefa musu flowers suna miƙa musu Silver Scented Scarves.
Abeey, tsabar mamaki da jin daɗi, bakinta yaƙi rufuwa. Amma dukkansu sauran sun kame kansu sosai.
Mehtav taji mamakin Inna da bata nuna wani kauyenci ba, duk da tasan daulace suka shiga wacce basu taɓa ganinta a rayuwarsu ba, kuma basu taɓa mafarkin samun damar shiga kalarta ba.
Islam ce ta fito a hankali daga babban zaure, sanye da Handwoven Damask Dress daga Morocco. An nannade kanta da Gold-Embroidered Headwrap. Tayi wani irin masifaffen kyau da Mehtav ba ta san har yakai haka ba-sai yanzu da take ganinta cikin kwanciyar hankali har murmurewa taga karayi.
Fatarta sai kyalli take kamar wata sabuwar amarya. Cike da fara'a ta ƙaraso, wasu kuyangu a bayanta. Ta shiga yi musu barka da zuwa, tana rungume su duka biyun. Suma rungumeta suka yi suna jin ta kamar wata 'yar uwarsu-tsabar yadda ta shiga musu da godiya da amsa gayyatar da suka yi.
---
It's FatoumsPassion EHSAAS Don't forget to: Share | Like | Comment | & Vote [06/07, 17:45] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
Follow all my social media handles @fatoumspassion.
atoum's Passion: EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.