EHSAAS

Chapter 46

by @fatoumspassion

Bayan sun gama wankan EHSAAS ya ɗauko Islam a hannunsa kamar wata jaririya, jikinta har yanzu ruwa-ruwa, towel din daya daura mata ya rufe daga kirjinta zuwa cinyarta. Shi ma towel kawai a jikinsa, yana bata wani intense look like he was still hungry, Har yadire ta cikin closets dinsu, tana dan wani jajjan towel din kasa kamar mai jin kunya,dariya yay yana kallonta tacikin madubi yake fadin "Yanzu kika gama kashe ni a bathroom, kina wani sunkuyar dakai" Ya karasa yana zaro handryer dinta, murmushi tai tana kashe mishi ido daya,kiss yamanna mata asaman idon yasoma drying hair dinta, tana kallon jikinsa da love-filled eyes,ta dafa saman towel dinshi gently take fadin "Are you sure you're ready to be seen by anyone tonight? The way you moaned my name, Sire, you should be in bed resting." Wani dan banzan naughty smile yasakin mata kafin yace

"Wallahi I should… ko in kwantane baby ni kaina banson zuwa" Dariya ta farayi tashiga girgiza kanta tana fadin "daman wasa nakema ainasan bason zuwa kakeyi ba aikam sekaje kuma"

Turo baki ya shigayi irin cikeda shagwabar nan yake fadin "Nidai a'ah kawai ki kwanta muyi barci" Make mai kafada itama tayi tana mikewa tsaye tace "Oyah lets quickly get ready ka gama kayi missing sallar aidaman nafada maka kaqi ji" Kissing lips dinta yay yana fadin "Your right baby,your always right......" Yana dariya datasan ta shakiyanci ce cikin kankanin lokaci suka shiryawa Already ta rigada tafito musu da kayan da zasu saka, Ita wata flowing custom emerald green abaya taciro, hand-stitched with real gold thread, da stones masu sheki ajikinsa,se shikuma ta dakko mai wani royal kaftan of white and silver, embroidered da Nuristani royal crest, sword belt dinsa polished and ready,dawani matching turban lined with white gold edges.

Dakanta tashiga shiryasa tai picking robe dinsa, tasaka mai ta tsaya abayansa,ta daura mai belt din gently kafin tadawo ta gabanshi tana kare mai kallo tana murmushi kafin tace "You look powerful," ahankali kamar mai yimai rada tana dage mai gira daya kafin tace "but I know the man who melts in my mouth." Dariya yay yakama hannunta yana matsawa ahankali kafin ya jawota jikinsa yay kissing forehead dinta yana fadin "And you look holy. But I know the woman who made me beg in the shower."

Atare suka kyalkyale da dariya cikeda soyayya,ahaka suna tsokanar juna har suka kammala, ya kamo gashin ta, ya dora mata royal bejeweled veil, sannan ya zura mata earrings dakanshi yace "Kinsan me baby?" Girgiza kai tai alamun a'ah seya fada, Ya danyi murmushi yana fadin "I love dressing you… because I also love undressing you." Yakarasa yana kai hannunsa saman kirjinta,buge hannun tai tana dariya tace "After dinner, I'll let you do both. But for now,let's go honour the people that gave you a second chance at life." ta karasa tana jan hannunsa suka fito.

Mehtav da Abeey na zaune cikin dakin su na royal guest wing bayan sun idar da sallar magrib lokacin da sukaji anfara buga musu kofa ahankali.

Abeey ce tadago daga game din datake bugawa awaya takalli Mehtav dako kallon kofar bataiba kafin tabada iznin shigowa.

Two palace maids suka shigo da royal golden boxes, suka aje su a gaban su cikeda ladabi, kansu akasa sukace

"ga sako daga Fulani Hajar tace abasu,shine kayan da zasu saka suzo cin abincin daren nayau" Abeey cikeda excitement tace musu "tohm sungode" Jinjina mata sukai kafin su juya sufice adakin dasauri Abeey tadiro daga saman gadon ta buɗe box din farko da sauri. "Wow" ta fada cikeda mamaki tana ciro stunning gown dinta baby blue satin with hand-beaded crystals, tajona da jikinta daidai ita har tsayin tashiga jujjuyawa tana fadin "yah Mehtav kalleni kamar wata Princess kidubeni dan Allah"

Murmushi Mehtav tai tace "kinyi kyau Abeey yanmata" Dariya Abeey tai tashiga bude dayar box din tana fadin muga naki, Tana kammala budewa tazaro rigar Mehtav tana fadin "OMG" saboda bala'in kyan data mata tata kalar gown din was deeper, wine red velvet da royal embroidery na gold ajiki. Everything screamed elegance. "Yah Mehtav kinzama Queen dubi kayannan dan Allah irin wanda queen's ke sakawa fa just look at it" Mehtav kallon kayan tai sun bala'in mata kyau amman kuma bataji sun dadata da qasa ba ko kadan hasalima ita zamanta anan jitake kamar akan kaya take Allah Allah takeyi kawai suyi sutafi.

kawai mikewa tai takalli Abeey tace "let's get ready karsu dawo suga bamu shirya ba," Abeey tafara kallonta cikin mamakin ganin tadau rigar ta fara shiryawa kamar wata robot,babu farinciki ko kadan akn fuskarta "Are you okay?" Abeey ta tambaya tana kallonta cikeda yar damuwa, "I just want this to be over,"ta ce a hankali. "Ni so nake kawai mukoma gida" Abeey jin abinda tafada nason komawa gida yasa tawani kyalkyale da dariya domin itafa taga gun zama kawai gani take yah Mehtav tanason tai musu bukulun royal treatment dinnan shiyasa take acting weird hakanne yasa tacigaba da sha'anin ta bata sake bi takanta ba har suka kammala shiryawa wata maid tazo ta kwankwasa musu tace musu "ai Paa da inna na jiransu akasa," riko Abeey Mehtav tai tana me jaddada mata ta nutsu gaban sarki zasuje banda magana mara amfani kada ta sake tabasu kunya Abeey jinjina kai tashiga yi kamar dai tanajin duk abinda tace harsuka samu su Paa a babban falon.

Inna tashiga rangada guda tana kallonsu saboda kyan dasukai mata,suma kallon inna suke saboda itama anbata hadaddun kaya sababbi daga ita har Paa din.

Inna ta saka royal purple wrapper and blouse, an saka pearls a jiki,Paa kuma ya saka noble kaftan wanda EHSAAS ya aiko mai yayi kyau matuka amman fuskarsa kwata kwata babu walwala akai, sosai Mehtav talura da hakan,tadan matso kusa da shi,tana fadin "Paa, lafiya kuwa?"

"Lafiya Lau" Yafada kafin ya danyi murmushin yake yana fadin "Kinyi kyau" Bata sake cemai komai ba amman, She knew there was more, but she let it go tasan in yanason tasani ze fada mata dakanshi,shikuma babbar damuwarsa bata wuce kada sarki NASHWAN yasheda fuskarsa ba saboda besan yaya ze tarbesu ba duba da misunderstanding din da king Abdul Aziz yay creating atsakaninsu shekaru da dama dasuka wuce yana cikin wannan tinanin

Handmaiden ɗin Islam ta iso, ta durƙusa cikin girmamawa, tana mai sanar musu cewar, "Islam din ta aikota ta rakasu zuwa dining hall din" Babu musu suka shiga bin bayanta.

Suka fara tafiya cikin shiru babu mai magana atsakaninsu se kalle kalle sukeyi musamman inna da Abeey dasuka sake sunata bawa idanuwansu abin kallo, Dukkan corridors din da suka wuce an saka furanni da scented candles masu kamshi na saffron da rose. Kafin su karaso cikin wani gigantic golden door wanda guards suka buɗe musu cikeda girmamawa saboda sunsan da zuwansu. Bude ƙofar ya bayyana private royal dining hall hadadden gaske ginin da aka ƙawata da pure gold chandeliers, dining table din mai tsawon mitoci da aka jera da real silver plates da exotic dishes daga kasashe daban daban.

Adaidai lokacin dasuka karaso, Islam da EHSAAS suka mike tsaye daga zaunen dasuke suma shigowarsu kenan.

Islam na murmushi kamar wacce taga family dinta takarasa tana rungume Mehtav tana mata barka da karasowa itama rungumeta tai tana dan mata murmushi mai kyau,idon EHSAAS nakan Mehtav da yaji Abeey ta rikoshi tafara tambayarsa wai tayi kyau murmushi yay yatsugunna yadda zeyi daidai tsawonta yaja cheeks dinta yana fadin "Ai bangane kiba da farko na dauka Cinderella ce tashigo dakanta" blushing ta somayi irin an yabetannan tana fadin "shiyasa nake sonka prince,yah Mehtav kinji abinda prince yacemin koh," ahankali idonshi yasauka akan Mehtav dake magana da Islam kasa kasa suna dan murmushi besan meye suke cewa ba amman sarai yasan taji maganar Abeey ko juyowa takalleshi bataiba kwata kwata,abin yasoma dan damunsa saboda dukkan alamu sun nuna kamar fushi take dashi wanda shikuma bayason hakan. bayan yasake gaisawa da inna da Paa yakarasa gefen su Mehtav yace "gist din ya isa haka ladies azauna koh," islam ce kawai takalleshi tana murmushi takalli Mehtav tace "kinji shi ko he is jealous yaga munata magana shikuma mun mai banza," takarasa tana lakace mai hanci yaturo mata baki yana dage mata gira daya, Mehtav jan jikinta tai bata nunama tasan wasan da sukeba dukda Islam taso ta tofa amman kanzil batace ba takarasa gefen Paa tazauna.

EHSAAS ma jan hannun Islam yay bayan yaja mata kujera tazauna shikuma yaja kujerar dake facing wacca Mehtav tazauna yazauna yana zaro wayarshi a aljihu, yasoma dannawa batareda yasan meyake dannawar ba saboda gaba daya hankalinsa nakan Mehtav wacca ta watsar dashi tanuna kamar ma he doesn't exist,Basu jima da zama ba Ƙofar grand royal dining room din yasake buɗewa a karo na biyu cikin natsuwa, guards suka tsaya suna sunkuyar da kai alamun girmamawa yayin da wani luxurious electric power chair ya shigo, Mai Martaba ne akai cikin simple shiga mai matukar kyau data amshi pale body dinsa dukda ciwan dayake ciki amman hakanan yadaure saboda yanason ya karrama mutanen dasuka ceci EHSAAS dinsa dakanshi,kuma yau haka kawai karfi yakeji ajikinsa na musamman,gefensa, Fulani Hajarce tana rikeda Jr dake kallonsu kuri kamar yagane su, matching outfit ne ajikinsu itada Mai Martaba da Jr kana kallonsa kasan jikansu ne saboda yadda yadauko features din fuskar kowanne daga cikinsu kamar eai EHSAAS.

Ganin shigowarsu yasa kowa ya miƙe tsaye,cikin girmamawa har suka karaso ciki EHSAAS zagayawa yay yakarasa tura Mai Martaba mazauninsa da aka tanadar mai already yasa ancire kujerar dake gurin saboda akan wheelchair dinsa ze zauna yadda tafiya take mai wiya akwanakinnan baya iya taka kafarsa kwata kwata.

Murmushi mai Martaba yayi ahankali tsufanshi yau yasake fitowa ganin sunyi carko carko atsaye suna jira iznin zama,ya daga hannunsa a hankali,yana mai musu nuni da su zauna,zama sukai gaba dayansu suna masa masa barka da shigowa cikin girmamawa, EHSAAS yakarasa gurin Fulani data zauna gefen Islam yana fadin "maama kawoshi yanata wahalar min dake ko?" yafada yana dan yiwa Jr wasa, hanashi shitai tana fadin "Anqi din ina ruwanka damu bafa nason shisshigi," dariya Islam tafarayi mai harda gwalo,ya dan tabe fuskar alamar anbata mai rai,itada Fulani suka fara mai dariya.

Har yakoma ya zauna agurinshi,idon Mehtav nakasa tanata wasa da fingers dinta, Har zuwa lokacin da Mai Martaba ya danyi gyaran murya kafin yasoma magana cikeda nutsuwa,his voice is deep irinna EHSAAS sak sedai nashi yay kasa kasa saboda ciwo dayake fama dashi yace "my beloved guests. Barkan ku da zuwa fadar Nuristan, nagode sosai dakuka amsa gayyatata" Cikeda girmamawa suka amsa suna mai fada masa sune da godiya tareda mai addu'a Allah yatashi kafadun sa yabashi lafiya ya amsa da "ameen" yana kallon yaran cikeda kauna saboda tina abinda EHSAAS yabashi labarin sun mai na alkhairi.

EHSAAS tunda Aka fara magana hankalinsa na kan Mehtav yana watching dinta closely yadda tabada attention dinta ga mai Martaba da mahaifinta baki daya. so daya tak suka hada ido yace mata "Hi" through his lips batareda yafurta ba sarai tasan meyace amman seta nuna kamar bata saniba tacigaba da sabgar ta har akazo aka fara jera masu dinner, Dishes irin su roasted duck with saffron, chicken paper, chicken biryani, paratha,meat balls,meat paper, lasagna, lamb biryani da raisins, date pudding da rose ice cream, cardamom milk da cucumber water duk an ajje, domin se angama cin abinci tukunna za'a dan tattauna daga baya, kowa yazabi abinda yakeso Islam ce tatashi da kanta tashiga serving EHSAAS kafin Mai Martaba da iya abinda tasan yanaci ayanzun tazuba, kafin ta zubawa Paa shima ta zubama Fulani tazo ta zubama Inna. takalli Mehtav datai saurin karbar saving spoon din daga hannunta tace mata ta gode zata karasa,xuba nata tai tana mikewa ta zubama Abeey itama ahankali tana satar kallon plate din EHSAAS saboda abincin da Islam tacika mishi sarai tasan baze iya cinyewa ba kuma naman dayake kai yamai kadan, amman dai batace komai ba tazauna.

addu'a akai kafin mai martaba yabada umarnin kowa yaci abincinsa gently aka soma cin abinci,kamar kuwa tasani EHSAAS naman kai ya kwashe yana gama cinyewa taga yana kallon Islam,asace take kallonsu don kosu basusan tana kallon sunba, setaga yatsoma spoon dinshi abincinta yana kwashe naman kai yana mayarwa nashi dayasa tazare ido irin tana nuna mai akwai jama'a fa yadan dage kafada alamun bai damuba, Mehtav kamar tai dariya ganin yadda Islam tai looking helpless tasan daba acikin jama'a sukeba ba yadda za'ai takyaleshi dagani sun saba iri wannan bickering din se abin yaburgeta ba kadanba.

talura beci abincin ba kwata kwata se naman kamar hankalinsa baya gurinne,inna da Abeey kuwa se ziri akeyi kamar ba'a tabacin abinci ba,don Abeey babu abinda bata dan dana ba wai ai yadda zatafi kararwa.

babu abinda kakeji a hall din se karar utensils da gwalanton junior daketa kokarin chafko plate din Fulani tana hanashi har Allah yasa kowa yakammala cin abincinsa mai martaba kwata kwata chokali biyu yay ya ajje saboda yadda bakinsa yake mai ba dadi.

Gaba daya Paa atsarge yake don beyi expecting irin wannan karramawar daga Mai Martaba ba musamman bayan dayaga fuskarsa ya dauka ze koreshi ne koyace wani abu mara dadi amman kuma babu abinda yace din sema godiya dayay musu dasu ka zo nandin, aransa ya raya kodai be ganeshi bane ba? Amman kuma wata zuciyar setace mai aiko be gane kaba hajar zata sanar mai waye kaidin.

Ganin kowa ya kammala cin abincinsa yasa maids sukazo suka tattara komai suka sake tsaftace table din aka zuba desserts iri iri akai suka tafi,Mai Martaba Ya ɗaga glass ɗinsa da hannun dama. Golden no alcoholic wine goblet aka tanada, an zuba apple cider a ciki, yana glowing dawani irin haske mai kyau. Yace "To The Golden Girls!" Suma duk suka daga nasu glass din yacigaba da fadin "A toast... to courage, to compassion, to the girls who stood in front of death and said 'not today'. To the ones who carried the future of Nuristan on their backs unknowingly,to Mehtav and Abeey, thank you for saving how prince"

Abeey jitai kamar tatashi tadaka tsalle lokacin da sukai raising toast din wai yau king ne guda yake making toast dasunan su, giggling kawai takeyi tana kallon Mehtav da kanta yake kasa amman itama murmushin take saboda ita kunyar king NASHWAN ma taji tanaji.

"And to Habib Bai. The man who didn't let fear stop him from answering our invitation, despite everything that happened between us few years ago, I really appreciate yadda ka kular min da yarona kaida iyalina though bansan ko kasan dana baneba kila da baka rikeshi hakanba but I appreciate your kind heart alot inason kamanta dacewa we are old rivals because I already won she's mine now and you have your own share of happiness too with this two beautiful golden girls," Yakarasa cikeda barkwanci yana dan tari ahankali dayasa EHSAAS saurin mikewa zeyi kansa yadaga mai hannu alamar ya dakata tsayawa yay chak har tarin yalafa amman kana ganin fuskarsa ya matukar damuwa da halin da mahaifin nasa ke ciki, murmushi Mai Martaba yay yakalli Paa yana fadin "My own share of happiness" yana nuna EHSAAS da yasa Paa yay murmushi yana jinjina kai,yana fadin "yes your highness,he is such a lovely boy" jinjina kai EHSAAS yay Yana zama yasoma wondering tohm daman mai Martaba yasan Paa ne wana kalar rivals ne sudin haka zalika Mehtav da Islam abinda suketa wondering Kenan.

Muryar mai Martaba ce ta katse musu tinani, "Daga yanzun family dinka habib Bai sunzama nawa kudin kunzama wani bangare na rayuwar NURISTAN wacca har abada bazata manta dakuba, Abeey Mehtav mungode sosai" yafada yana kallon yaran guda biyu Mehtav tashiga girgiza kai saboda kunya takeji yadda dattijon ke musu godiya tashiga cemai bakomai Allah yatemake ka ai yiwa kaine,cikeda kulawa take mai maganar tana mai fatan Allah yabashi lafiya sosai yarinyar tasake shiga ransa, Kallon Fulani hajar yay wacca tadan lumshe mai ido tana jinjina mai kai alamar tabashi izni,sannan ya dawo da kallonshi kan Mehtav. "Mehtav," ya ce da murya mai natsuwa, "do you want to be my daughter?"

Mehtav cikin dan mamaki take kallonshi,takalli Paa dake murmushi kafin idonta yasauka akan EHSAAS da hankalin sa gaba daya yadawo kansu itada mahaifinsa, kamar bazata ce komai ba se can tace masa " yes your majesty it'll be an honour," "Masha Allah I'm now a father of 5" Seda kowa ya murmusa adakin saboda tone ɗin king Nashwan yayi kamar mai tsokana.

Kallon Fulani Hajar yasake yi suka kalli juna for a brief second, suka yi exchange din wani silent magana ta ido, kafin Fulani ta kama hannun Islam a ƙarƙashin table.

Amamakance Islam tadawo da idonta kan Fulani wacca hannunta daya ke rikeda Jr dayan kuma tarike Islam dashi,da dan mamaki tasakar mata murmushi, Tana fadin "maama," Fulani tace " you'll always be child kinji my favourite daughter not daughter in law" Islam jinjina mata kai tashiga yi tana fadin "I know," gyaran muryar mai martaba ne yamaida attention dinsu duka kanshi, Yafara da "Habib Bai… I know I am asking a lot. But I must speak what is in my heart. This young girl, yar ka, ta ceci rayuwar yarima… not because she knew who he was, but because that is who she is. She cared for him like blood. Like soul. And I believe… Yarima will never find a woman like her again. Not in this duniya. Not even in the next. So I ask as a father ba sarki ba,zaka iya bamu aurenta Let her become part of this family... completely."

Wani irin shiru ne yaratsa dining hall din kamar antsayar da lokaci,kowa yashiga tinani musamman wadannan mutane guda ukun Mehtav, EHSAAS da Islam kowa da abinda zuciyarsa take ayyana masa, Kirjin Islam bugawa ya shigayi da karfi saboda irin yadda maganar ta dake ta abazata, aure tohm dawaye? badai mijinta ba ko? koda itace taji ba daidai ba,tashiga kallon kowa da yake dining hall din idonta yasauka akan Mehtav da kanta ke kasa tamaki yarda tahada ido da kowa kafin tamaida kallon ta kan EHSAAS, wanda idonsa ke akan mahaifinsa da yay mgnr.

Fulani taji tamatse hannayenta dake cikin nata cikin son bata karfin gwiwa take fadin "I'm here be strong" Batasan ya akaiba sejin hannayen EHSAAS tai acikin nata,tashiga kallonsa tana son karantar abinda ke kan fuskarsa babu komai se tsantsar tausayinta data hanga a idanuwansa so that means is true shine za'a aurama Mehtav shi mijinta, EHSAAS dinta sire dinta kuma the fact that he is sitting here yana kokarin lallabata batareda yacema Mai Martaba baya soba means only one thing daman tadade tana zargin hakan one way or the other he has feelings for Mehtav.

Janye hannayenta tai cikin nashi tana hadiye wani irin abu daya tsaya mata arai tanaji kamar tatashi tabar dining hall din gaba daya amman bazata iya ba saboda tsananin girman iyayensa datake gani.

Mehtav wani irin taurin zuciya taji yazo mata,kanta na wani irin juyawa kamar ze tarwatse,she knows she feels something deep for EHSAAS. She knows her heart wants him. Amma ba tahaka takeso ta sameshi ba,bata irin wannan hanyar ba. "I want to be his choice… not his father's decision, I don't want to be a prize. I want to be a choice. I want him to choose me... not because his father thinks I'm worthy."

Haka zuciyarta tashiga maimaita mata Yayinda kowa yay shiru ana jiran jin amsar da Paa ze bayar wanda yay nisa cikin tinani, kafin yaja dogon numfashi yakalli Mehtav da idonta ke akasa sannan yakalli king NASHWAN dake jiran jin amsar yafara bayani anitse "Mai Martaba… I don't know how to thank you enough for this honour. Gaskiya, wannan karamci da martaba da kuka nuna wa iyalina… ba abu bane dazan taba mantawa dashi."

Ya dan tsaya, yana jin yadda idon dukkansu yake kanshi, mutane ukunnan sunaji kamar zuciyarsu zata fasa kirjinsu don tsabar yadda take bugawa kawai so suke suji me Paa zece "Amma Mai Martaba… Ni ba zan iya yanke hukunci a madadin diyata ba. She's seeing someone already. Though... bawani abu me karfi tsakaninsu amma... I don't know how deep her heart is into that boy,"

Dakinne ya sake yin shiru, EHSAAS ya lumshe ido. Zuciyarsa na bugawa tamkar zata Faso daga kirjinsa He didn't expect that. The jealousy he never admitted to himself started to crawl through his chest, kalmomin da Paa yafada nakarshe na yawo akanshi Wai she's seeing someone already, I don't know how deep her heart is into that boye, Who? when? Where? dama Mehtav zata iya son wani bayan shi ashe soyayyar datake mai zata iya mantata cikin few months haka? tambayoyin da yashiga jerama kansa kenan yanajin kirjinsa kamar ze tarwatse, Yama kasa imagining wai Mehtav dawani kai wani fa? Mgnr Paa ce takatse mai tinaninsa

"So I leave the decision to her. Whether she chooses the prince... or the other boy." Yakarasa yana kallon Mehtav,kowa kuma ita yake kallo musamman EHSAAS saboda shikansa bai san me yake so yaji daga bakinta ba. Rabin zuciyarsa na son yaji tace "yes" nan take - amma rabin kuma na tsoron hakan saboda yadda yake ganin fuskar Islam na tafasa da kishi da tashin hankali,ko kadan bayason abinda ze daga mata hankali

Fulani Hajar ce tamike tana mikama Islam Jr da yasoma barci ajikinta,rungumeshi tai yayinda take kallon yadda Fulani ta zagaya gurin Mehtav tadan dafata gently kamar tana magana da kwai,cikeda lallabawa da taushin lafazi take fadin

"My dear… what do you want?" ta tambaya da wani irin faffadan murmushi. "Are you ready to marry the prince?" Girgiza kai Mehtav tai alamar a'ah,

Dasauri Abeey tataso takaraso kujerar Mehtav itama tadafata tana fadin "Yah Mehtav handsome prince dinkifa kiyi tinani mekyau abamu lokaci your highness" takarasa tana kallon Fulani cikin murmushin yaqe jin Mehtav zatai mata bakin cikin zama a palace Mehtav kam jitake kamar tatashi tarufe Abeey da duka domin bata taba bata haushi irin nayau arayuwarta ba waya sa bakinta ma manya na magana,kamar Paa yasan metake tinani yace "abeeda go back to your sit" authoritatively sum sum tajuya takoma ma zauninta tana aikama da Mehtav kallon magiya.

"I'm listening to you Mehtav" Fulani tafada tana sake kallonta, Girgiza kai tai saikuma kunya ta rufeta tashiga jinjina kai se kuma tagirgiza,kafin hawaye su fara gangarowa ta gefen fuskarta saboda tasan bata da ƙarfin zuciyar fadin "a'a" a gaban iyayensa musamman king NASHWAN da ya nuna mata girma da soyayya har yakeson yahada zuriya da ita abinda mata da dama ke nema. tasan cemishi A'a a nan, tamkar cin mutunci ne. Amma kuma bataso tazama matar cushe saboda tasan matar cushe bazata taba farinjini a idon mijiba.

King Nashwan fahimtar halin da Mehtav take ciki yasanya ya saki murmushi kamar wanda ya karanci zuciyarta yace "It's okay, Mehtav,base kinfada yanzun ba, Ki ɗauki lokacinki. I will wait. But ki sani… ba za ki bar wannan fadar ba sai kin fadi zabinki. Take your time, my daughter."

Yafada cikin sigar wasa yana dan mata murmushi, murmushin itama tashiga mayar mai tafara goge hawayen fuskarta Fulani ta rungumeta tana jinta tamkar yadda takejin Islam acikin zuciyarta, Ahaka dai dinner takare, Fulani tasaka akai escorting su Mehtav zuwa chamber din da aka saukesu.

takalli Islam dake zaune agurin takasa motsi EHSAAS yajuya zefara mata magana Fulani tace mai "yawuce da mai Martaba zuwa sashensa! kallon Mai Martaba yay dayay looking so pale and tired saboda doguwar maganar dayayi wacca ya dade beyi irinta ba. yamike don baze iya musu da itaba yadan kara kallon Islam data ki yarda suhada ido jr na jikinta yana barci yarike bayan wheelchair din mahaifinsa suka wuce ta private door dazata sadaka da sashen mai Martaba kai tsaye. har cikin dakinsa ya kaishi yana mai kiran personal nurse din da aka ajje mishi shida shi suka taimaka ma Mai Martaba suka kaishi bathroom yakama ruwa yadauro alwalar barci daya sabayi,azaune yayi shafa'i da wutri da baiyi ba se yanzun kafin yaa idar yashiga addu'a EHSAAS na zaune yanata kulawa dashi har ya kammala suka sake dakkoshi suka dawo dashi saman gadon da niyyar kwantar dashi zaunar dashi yace suyi basu masa musu ba suka zaunar dashi din yasallami nurse din zuwa waje.

yana kallon EHSAAS da tunda yaga bece yatafi ba yasan akwai magana domin da daddare kullum shike korashi daya wajensa yace yatafi gurin iyalinsa amman yau bece ba yasan yanason magana dashi ne.

gefensa yanuna mai alamar yazauna,zama yay yana kallon mahaifin nasa dabe taba sanin girma ya kamashi hakaba seda ciwan nan yazo masa, Mai Martaba yace "I know what I did is not right. Na bukaci a aura maka mace ba tare da na tambayeka ba. But I also know I did the right thing." EHSAAS yayi shiru yana sauraronsa mai Martaba yacigaba "amman I'm not regretting it… saboda nasan da na tambayeka, I know you would have said no. And I would've let you lose her,saboda banason bacin ranka,amma ka ga yanzu,bakada bakin cewa no nasan bazaka bari babanka yazama karamin mutum ba" yadanyi murmushi yana kallon EHSAAS daya dago kai,cikeda mamaki yana kallon wayo da hikima irin ta Mai Martaba,cikeda girmamawa yace "amman Allah yatemakeka… I don't even like her that way. I don't want to make Islam angry. I promised her… I am hers forever." King Nashwan besan sanda yafara murmushi mai karaba har yasoma tari dasauri EHSAAS yarikoshi yashiga shafa mai baya har ya lafa yace "Allah yatemakeka kahuta pls gobe semu cigaba da maganar," girgiza kai king Nashwan yay yana murmushi yajanye daga jikin EHSAAS yana fadin "Kaine me gobe ka sani ko zamu kai ko bazamu kaiba," dan bata rai EHSAAS yay yana fadin "zamu kai in sha Allah" murmushi yay kafin yace "Kaga kuruciya ko? EHSAAS kafa girma lokaci yayi da zaka shirya karbar labarin mutuwa na ako yaushe kuma dangane da matarka Islam,kasani you can never be hers alone. Because kai magajin sarauta ne. Kai makomar Nuristan ne."

Ya matsa jikin pillow, yana kallon dannasa wanda yasan dayana da way din dazebi yay skipping conversation dinnan dayayi domin tunba yauba yagane EHSAAS bayason zancen mutuwa ko karin aure,

"Koda bana raye - kafin coronation dinka, dole kayi aure,saboda kasan haka tsarin yake tayaya zakai ruling da mace guda daya tak" EHSAAS girgiza kai yashigayi kafin yace "Bani da niyyar cutar da Islam… she's everything to me." "Na sani. That's why I didn't bring in some foreign girl. Mehtav bata da wata matsala kai kasan da haka kuma da bakinka kafadamin hakan. She didn't even know who you were. She cleaned your blood. She cried for you. That's a woman fit for your palace, irin wadannan matan once in a life time ake samunsu aduniya EHSAAS banaso karasawa"

sunkuyar da kai EHSAAS yay saboda yasan duk abinda Mai Martaba yake fada gaskiya ne,dafa kafadarshi Mai Martaba yay kafin yace "Ka duba rayuwata. Apart from your mother… I never trusted any of my wives. Saboda ba zabina bane, They wore crowns, but not my heart.bari infada maka kai din mesa'a ne acikin yayan sarakuna saboda ka auri zabinka islam kuma she's here with you sannan ka kara samun wata gold din mehtav, ni lokacina banida wannan yancin harta mamarka ma zabamin ita akai amman senai sa'a ita tazo tadaban saboda ita din zabin mahaifina ce dakansa,don haka Bazan bari hakan ya sameka ba. That's why na mika maka zabin zuciyarka a gaban kowa EHSAAS bantaba adawa da aurenka, despite our differences Muda iyayen matarka da ita kanta,saboda ina kaunarka inason inga farinciki akan fuskarka I'm old, son. But I still know what love is."

EHSAAS ya dafe kansa. Ya kasa magana,saboda gaba daya ya gamsu da maganganun da mai Martaba yafada mai amman yana mugun tsoron halin da Islam zata shiga,da ace watace ba Mehtav ba yasan abin zezo dasauki but deep down yasan idan yasake ya auri Mehtav bazata taba zama second best arayuwarsa ba because she's a part of him dabaze taba mantawa da ita ba… his promises, his past… and now, his future.

Mai Martaba kallonsa yakeyi cikeda kauna ganin dogon tinanin daya tafi yi ahankali yarike hannayensa cikin nashi yana fadin "Rike mata biyu ga sarki? Farilla ne. Yana koya maka adalci. Kuma idan ka kasa yin adalci a gida - yaya za ka iya yi wa al'umma? Ka natsu, EHSAAS. Kar ka rasa macen da kakeso saboda ka damu da halin da daya wacca kakeso din zata shiga,ba haramun bane just accept that inner voice dakeson yanunama Mehtav wannan bangaren naka, halal ne EHSAAS Allah yasan zuciyarmu zata iyason mace fiyeda daya alokaci guda shiyasa ya halarta mana auren guda hudu just go for it, You'll figure it out. Ka tuna… duniya zata gane mulkin ka daga yadda kake tafiyar da iyalanka."

Ya shafa kansa, yana murmushi "And Mehtav? I know you love her. You just haven't admitted it to yourself, I can see well with this old eyes yadda kake kallon yar mutane tana cin abinci"

EHSAAS runtse idanu yay kunyar mai Martaba na baibayeshi saboda beyi tsammanin wani ze iya kamashi yana kallon Mehtav ba don yayi matukar jurewa gurin takatsantsan kar kowa yagani Sosa qeya yasoma yi ahankali yana mikewa daga gaban Mai Martaba Cikin jin kunya yace Mai "Uhmmm...... Yes. Maybe that's the truth."

Yana rufe fuska kamar wata mace Mai Martaba yay murmushi irin nasu na manya yana fadin "nasan za'a rina from maybe ma za'a koma sure that's the truth" shida EHSAAS atare sukai dariya yabude mai hannayensa alamar yazo ya rungumeshi ya rungume shi kuwa yana shafa kansa. EHSAAS najin bugun zuciyarsa kamar yakwana anan kusa dashi haka yakeji Mai Martaba yace "tohm maza atafi gurin diyata nasan tanacan tana jira sekayi aikin bayani da lallashi nasani," murmushi EHSAAS yay kafin yay masa sallama yawuce.

Kirjinshi na bugawa haka yakarasa sashensa saboda besan dawani kalar rigimar Islam zata tareshi ba domin yasan yanayin kishinta, ahankali yamurda kofa yashiga dakin ko fitila bata kashe ba hakanne ya tabbatar mishi da idonta biyu ko kuma bata dade da kwantawa ba, karasawa bakin gadon yay tana kwance luf, ta juya mai baya, tana sanye da light silky sleep dress da ba kasafai take sawa ba sai idan jikinta ba daɗi, Jr yana tsakiyar gadon yanata kwasar barcinsa daman basa sakashi agadonsa indai ba tabarar EHSAAS ce tatashi ba yace shi bazeyi sharing bed dinba "babyyyyyy…" dawata irin sanyayyar murya dayasan tana narkar da zuciyarta amman seyaji shiru babu amsa, "Babyyyyy" yasake Kira yana leka fuskarta nanma shiru sema kara gimtse ido dayaga tayi, yasan halayenta tamkar tafin hannunsa,kuma yasan me rashin amsawar nan tata take nufi da rufe idon datai alamune daya nuna batason jin komai kuma karya dameta,ba barci takeba, amma tana ignoring dinsa. Wani irin ba dadi yaji aransa saboda yasan she's suppressing everything inside kuma yasan bazatace komaiba din ayanzu amman sanda zata fashe aiseya shiga uku da rigima. Sai ya juya kawai ya shige toilet, yayi shower shi kadai, he's feeling lonely already saboda wannan shine karo nafarko da yakeyin wankan dare shishi kadai tun bayan dasuka dawo daga LA,yanajin aransa anya ze iya kuwa anya shidin ze iya jure fushin Islam har haka.dakyar yasamu ya kammala wankan ya fitowa da towel a kugunsa, yaganta har lokacin tana kwance, idonta a rufe, kamar mai son bacci ya dauketa da karfi da yaji.

Ya tsaya yana kallonta na wani lokaci. Bai ce komai ba. Ya san cewa a irin wannan yanayi, ba magana take bukata ba, space take so, kuma zebata in sha Allah,damuwa biyuce acikin ransa dake neman dagula mai lissafi ayanzun na farko Islam na biyu Mehtav,her recent attitudes na mugun damunshi, closet yawuce "Maybe I deserve this..." ya furta a hankali shishi kadai,yau for the first time yashiga shirya kansa da kansa, Ya zaro wata simple but breathtaking English wear daga cikin wardrobe, grey turtle neck da black tailored pants. Daya bashi wani Classic, Royal and Soft look, yafashe jikinsa da turarrukansa masu mugun kamshi,inkagansa bazakace yana cikin wata damuwa ba He looked very calm, but his soul was burning.

Ya zauna a kan dressing table ya rubuta mata short note, "I'm going to see Mehtav. Don't worry. I'll be back before midnight" SIRE."

Ya ajje note din a kan gado kusa da side pillow nata. Ya fice Ahankali don yasan bazata kulashi dinba yana fita tamike zaune,tana kallon takardar daya ajje mata dawani irin sauri tadau takardar takaranta kamar bata iya karatuba haka tasake dawowa takaranta takalli agogo wato daga cewa anbashi aurenta shine har yafara zuwa tadi koh,tafada tana fashewa dakuka ita kadai kamar wacca aka bata labarin daya daga cikin iyayenta sun mutu ta rungume takardar akirjinta kafin tai saurin ciro takardar tashiga yagata into pieces tawatsar adakin takoma takudundunne da bargo tacigaba da kuka.

EHSAAS nafita yanufi royal guest wing, dayake babu nisa daga sashensu in minutes yakarasa, gently yayi knocking a bakin side wing ɗin da Mehtav da Abeey ke ciki. Maids din da aka basu suka fito suna dan sunkuyar da kansu cikin girmama suka fara gaidashi amsawa yayi kafin yace "Tell Mehtav I'm outside. I need to speak with her." Ciki suka shige shikuma yasamu guri a babban falon yazauna yashiga danna wayarsa hankali kwance amman hankalinsa yana kan kofar gurin, Bayan dan lokaci saiga maids din sun dawo suka durkusa atare suke fadin

"ranka yadade tace gatanan fitowa" Gyara zaman sa yay kafin yabasu umarnin barin gurin tareda strict other kada wanda yasake dawowa falon harse yafito jinjina kai sukai sum-sum suka je suka sanar da sauran duk suka fito suka fice.

aransa yasan akwai munafukai cikin hadimannan kuma Mehtav iyalinsa zata zama don haka baya bukatar duk wata tattaunawa da zeyi takasance daya daga cikin su yaji,shiyasa ya koresu,zama yay yanata jiranta amman shiru babu Mehtav babu dalilinta ga lokaci yanata wucewa yadanja numfashi yana kallon wayarsa inda lokaci yake nunawa,besan har time yaja hakaba amman bata fitoba Tundaga 10pm… zuwa 11… Sannan 12:08am… Mehtav bata fito ba. Gashi ya kira number dinta. Switched off. Yanajin kamar yakarasa ciki yashiga har dakin nata yazaro ta, yatambayeta dalilin shanyashin datai anan gurin da sharesan datakeyi,kodan tayi sabon saurayine amman kuma nan din NURISTAN ne bayason yayi wani abu daze bawa makiya damar farmishi ta inda bezata ba,kuma bayason amman sarai yasan idonta biyu kuma tana sane tashanya shi anan kodai rama abinda kamata takeyi wata zuciyar taraya masa yana tina yadda sauda dama yake attempting yakirata amman he didn't for her sake saboda bayason tai falling harder for him "No no no… Mehtav…" ya furta a hankali. Ya lumshe ido. Yana dafe kansa,saboda shidin prince ne babu macen data taba shanyashi haka acikin palace dinsa tunda aka haifeshi se ita,kuma yadda yake tinanin rashin ganintan baze dameshi ba amman ba karamin zafi yaji zuciyarsa tanayi ba fiyema da yadda yaji lokacin da Islam taki kulashi dazun, mikewa yay ganin har daya na neman yi,kawai yafice abinsa yana nufar sashensu zuciyar sa na tafasa.

Dakin tsit ya tarar sanda yashigo, takashe fitila wannan karon hasken bedside lamp ne kawai yake haskata ta jingina da crown din bed din, tana rike da Junior, tana bashi mama. Idonta na kallon wani guri daban alamun tayi nisa cikin tinani,tsayawa yay yana kallonta kafin yacire takalman sa ahankali yazare rigarsa da pants dinshi yarage dagashi se vest da boxer, Ya haye gadon a hankali, ya zauna kusa da ita,yana kallon yadda junior keshan maman fuskarta ta.mayar daya gefen karma takalleshi hardai tasamu Junior ya kammala har yay barci don daman yunwar ce ta tasheshi saboda beshaba yay barcin dazun.

kwantar dashi tai agefenta taja duvet tana kokarin kwanciya tarufe kanta yarike duvet din yana fadin "babyyyyy" ashagwabe yana kwantawa saman kirjinta, "baki ganni bane uhm ko kin dena sonaneeeee da danki kawai kika damu,kofa tayin milk din baki minba" yakarasa yana dagowa suka hada ido,wani irin urge din ta daga hannu ta wanka mai mari ta rike saboda gani take yama gama raina mata hankali ita wacca ya dawo daga gurinta batada kirjinne aida tabude masa yalatsa wato itace marainiyar wayonshi amman seta mugun hadiyewa "Welcome back," tace da murmushi… Murmushi wanda ake kiransa yafi kuka ciwo,hankalinsa ne yasoma tashi ganin yadda idanuwan ta suka tashi alama ce datake nuna mai tunda yafita kuka takeyi yamike yana kunna wutar dakin se alokacin yalura da takardar data yayyaga tazuba akasa,yakamo kafadarta ahankali,yana fadin "Kuka kikayi,islam hawaye bakinmin alkawarin kindena kukaba, Islam I'm sorry dan Allah kidena kuka" Janye jikinta anashi tai tana fadin "don't touch me, nika kyaleniiiiii" tai shigewarta cikin bargo tana rufe duka jikinta har kanta.

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment & Vote. [11/07, 20:00] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

Follow all my social media handles@fatoumspassion Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.