Chapter 47
Gaba ɗaya su su ukun ba wanda yayi kwanan dadin rai a cikinsu, kowanne a cikinsu yana ƙoƙarin samun mafita daga halin da yake ciki. Musamman Mehtav da take ganin a wannan gabar zata iya accepting auren Ahmad ko Kamal duk da ta san ba ta sonsu. Saboda da ta amince ta auri EHSAAS a matsayin matar chushe, gara ta auri wanda ta san yake sonta, ko da ita ba ta son nashi. Ta san zuwan da EHSAAS yayi kila ba alkhairi ne ya kawo saba saboda... sarai taga yadda fuskarsa ta canza shi da matarsa lokacin da Mai Martaba yake nema mai aurenta. Ta san baya sonta kuma kila zuwa yayi ya roƙi alfarmarta akan tace bataso, Shiyasa ma ta ƙi sauraron sa, domin ko ya nema ko bai nema ba, ita tasaka aranta bazata taɓa auren mijin da baya sonta ba. Kusan raba dare yau tayi tana sallah tana roƙon Allah ya zaɓa mata mafi alheri a cikin rayuwarta. Ba ta san lokacin da barci ya ɗauketa a saman sallayar ba.
Daga ɓangaren masoyan guda biyu kuwa, duk yadda EHSAAS yaso Islam ta saurare shi, ƙi tayi. A wannan daren da ya isheta ma, sai ta ɗau ɗanta ta tattara zata bar mai ɗaki, abin da ba su taɓayi ba tun farkon aurensu: raba ɗaki. Duk da kowa nada nashi, amma ba su taɓa kwana a dakuna mabanbanta ba. Duk inda ɗaya yake, anan ɗayan zai kwana shima.
Sai da ƙyar ya lallabata ta koma ta kwanta ba tare da ta fita ba. Yana jin shasshekar kukanta dake ƙara raunata masa zuciya. Har barci ya ɗauketa, shima bai rintsa a daren ba. Ya tashi, ya ɗauro alwala, istikhara ya fara yi. Ya roƙi Allah ya zaba mai abin da yafi alheri cikin rayuwarsa. Idan auren Mehtav alheri ne a gare shi, Allah ya tabbatar da shi, ya kuma saka ma Islam haƙurin dangana ta karɓe shi. In kuma ba alheri ba ne ba, Allah ya warware lamarin cikin aminci, ya kuma cire masa duk abin da yake ji a cikin zuciyarsa dangane da Mehtav. Kuma ita ma yana roƙar mata, in Allah yasa akwai sauran sonshi a ranta, in dai shi din ba alheri ba ne ba, Allah ya cire mata.
Yana nan zaune har aka yi kiran sallar asubah na farko. ya shiga yayi wanka kamar yadda ya saba, ya fito ya shirya cikin jallabiya fara kal, ya ɗaura farar hular nan da ake kira da taba kaji hadisi.
Ya nufi bakin gadon, gently ya fara shafa fuskarta yana faɗin, "Baby ki tashi lokacin Sallah yayi." Sarai yaga yadda ta fara motsa idanuwanta amma ta ƙi buɗewa. Ya san ganinsa ne ba ta son yi. Hakan ne yasa ya sumbaci forehead dinta, ya ƙarasa gurin Jr, ɗaya ya buɗe idonsa yana ta wasa da hannayensa shi kaɗai yace, "My champion ka tashi kenan." Ya fara mai wasa, nan take ya soma dariya. Ya sumbaci kumatunsa da forehead dinshi shima. Ganin zai makara yace, "Daddy have to go now baby. Take care of mommy for him."
Ya ƙarasa yana kallon Islam da ko motsin kirki ta ƙi yi, kuma ya san tana jinsu. Har ya fice a ɗakin ba ta motsa ba. Direct ya tarar da Aman na jiransa kamar yadda suka saba. Tare suka wuce mosque.
Yau ji yayi kwata-kwata ba shi da ƙarfin zuciyar jan sallar. Haka ya ce ma malam liman ya jasu, suka yi sallar asubah. Saboda barcin daren da bai samu yayi ba, ko tsayawa karatunsu na asubah bai yi ba.
Yayi hanyar gida straight. Mamaki ne ya kama shi ganin ɗakin da ya barsu babu kowa. Ya shiga toilet, nan ma babu kowa. Closet ya nufa, nan ma babu kowa. Amma dai ya ga undies dinta inda take zube masa su in ta cire. Kuma he can still remember, jiya sune a jikinta.
"What the fuck?" Ya faɗa yana fitowa cikin tashin hankali, domin ya san Islam can try to step out of this palace. Ya san it is not safe for her and Jr. Cike da kidimewa, ya nufi dakinta don ya tabbatarwa konan tayi? Nan ma babu kowa a ciki.
"Guards! Guards! Security! Security!" Ya fara kira a fusace. Gaba ɗaya dogaran da ke bakin ƙofa suka ƙaraso, wanda suke can nesa ma gaba ɗaya sun ji hayaniyarsa.
"Ina Princess take?"
Ya shiga tambayarsu a gaggauce, dogaran da securities ɗin gaba ɗaya sun rude.
"If something happened to her a cikin gidan nan, zaku ga other side of me! Me na faɗa muku akan barinta ta fita ita kaɗai?"
Dogarai har da rantsuwarsu suka durƙusa suna bashi haƙuri tare da faɗa masa su ba su ga fitar ta ba wallahi, kuma ba a ɗau mota ba ko ɗaya a gidan ba.
"Kamar ya? Ba ku ganta ba, bacewa kuke nufin tayi haka kawai ko yaya?"
Ya shiga furtawa yana komawa ciki don ɗauko wayarsa. Har yayi stepping in, ya fito yana faɗin:
"Ku ce wa main security na waje su saka ido kada su sake su bar Princess fita daga gidan nan!"
A gaggauce ya koma ɗaki, ya ɗauko wayarsa, ya nufi ƙofa, har ya gifta sai kuma ya dawo sakamakon hangota da yayi gashinta na kadawa a bakin wajen swimming pool, tana zaune saman lallausan grass carpet ɗin dake gurin. Ta shimfiɗa ma Jr wani comfy mattress, yana ta rarrafawa. Ita kuma da novel a hannunta tana ta kallo kamar me karatu. Ko ɗankwali babu akanta daga ita sai wasu kananun English wears, guntaye.
Tsayawa yayi bakin tagar, yana jin hankalinsa na soma kwantawa a hankali. Saboda bai san yadda rayuwarsa zata kasance in ya rasa ɗaya daga cikinsu ba. He knows how she finds solace in reading, shi kuma solace ɗinsa a gurinta yake samu. He no longer reads books on his own ba tare da ita ba. He always enjoys listening to her tana karanta masa, in kuma ta gaji shi ya karanta mata. Haka suke wannan rayuwar tasu me cike da kauna, amana da soyayya.
Wai me yasa zuciyarsa taci amanar Islam ne? Meyasa ta iya ma jin wata a ranta ba ita? Soma jin tsanar kansa yayi saboda ya san Islam doesn't deserve baƙin cikin da yake ƙoƙarin kunsa mata ba.
A hankali ya ƙarasa. Shi tsoron yi mata magana yake yi. Ya zauna gently a gefenta. Ya soma yiwa Jr wasa, da ke ta kyalkyala dariya yana rarrafawa a guje don kar yace zai ɗauke shi.
Ɗan satar kallonta yayi, yaga gaba ɗaya hankalinta na kan novel ɗin. Gently ya sa hannunsa tare da shammatarta ya karɓe littafin, yana rufe shi ya riƙe a hannunsa.
Cike da mamaki ta dago tana kallonsa irin "kai ɗinnan…"
Basarwa yayi, shiko faɗa ne tamai yayarda amma wannan silent treatment ɗin da take bashi ya ishe shi haka.
"Ba nace miki ba a karanta novel bayan asubah ba? Ko kin yi bitar Al-Qur'ani'nki uhm?"
Ya tambaya yana wani cin magani. Hannunta ta buɗe tana miƙa masa alamar ya bata littafin. Ta ƙi kulawa da hakan yay sai ma tsugunnawa da yayi, yay peck ɗin hannun, da sauri ta janye tana yarfar da hannun kamar cinnaka ya cije ta. Ta soma aika masa da wani uban kallon da yasan na gargadi ne.
"Don Allah ki min magana Islam. Mun yi alkawari, mun daina irin wannan cikin alakar mu. We will always communicate. Silent treatment is not an option."
"Alkawari?" Ta faɗa tana kallonsa. "Ka ce alkawari koh? Ka san darajar alkawari ne kake zuwa kana jaddada min wai mun yi wani alkawari? Sire, please get out of my sight kafin na faɗa maka something you and I will regret later on. I'm not in the mood to talk to you. Plz ka tafi."
"ISLAM pls," ya faɗa yana riƙo hannayenta. "Kin san I don't want this too. Kin san cewar I never planned all this. Kaddara ne Islam. Kin san kuma ɗan Adam baya wuce kaddararsa."
Fincike hannayenta tayi daga hannayensa, tace:
"Na san meye kaddara kuma na san meye zaɓin mutane. Maybe you planned all this. Sire shiyasa ka ƙi yarda mu je mu yiwa su Mehtav godiya da kanmu. You insisted on bringing them here to the palace because you already know that Mai Martaba will like to arrange your marriage with her.
"I've tried hard, Sire. I accepted her wholeheartedly. I invited her here for our parents' happiness, saboda iyayenka da iyayena na ɗaukesu. EHSAAS, Mai Martaba bai yi making wannan decision ɗin kai tsaye ba. Na tabbata ka faɗa masa labarin abin da ya faru a Nigeria ne and he saw it in your eyes abin da na daɗe ina gani - that this heart," tasake mai maitawa tana dafa kirjinsa, "is beating for Mehtav. Ka sani ba zan taɓa hanaka aurenta ba. Kuma yau for the first time na yarda da statement ɗinnan da ake cewa men are polygamous in nature. Amma ka sani women aren't. Kuma polygamy choice ne, and I'm not even considering choosing it. Ba zan zauna da kai ba. Just ka sallame ni in wuce, ta yadda zaka yi rayuwar aurenka hankali kwance ba tare da Islam tana gefe tana baka ciwon kai, tana takurawa amarcinka ba. I know you want this."
"Babyyy..." Ya faɗa yana curving face ɗinta. "Just look at me, look at me. What are you trying to say?" Ya ƙarasa yana haɗa idonsa da nata. Sai hawaye sha-ta-kasa riƙewa ta fara kuka:
"Ni, ka sake ni. Ba na son ka. Ba zan zauna da kai ba. I can't share you with any woman not even Mehtav. I like her as my sister in Islam. And for whatever she has done for you, I am grateful amma ba zan iya ba. Kawai ka zaɓa: ko ni, ko ita."
"Baby pls ki daina faɗar haka. Ai kin san ke fa rayuwata ce. Ba zan iya rayuwa babu ke ba. Kin sani. Ta yaya kike tunanin zan iya rabuwa da ke uhm? Kuma ba ki san babu kyau mace tace mijinta ya sake ta ba. Ni a cikin tarihin rayuwata babu saki. In kika shigo, kin shigo kenan , mutu ƙaraba, takalmin kaza. Baby na ki daina irin wannan banzan wasan. Babu kyau. After all we went through, kike tunanin akwai abin da zai taɓa breaking wannan marriage ɗin? Uhm?"
Jinjina kai ta soma yi, ta fara magana tana shassheƙa:
"Yes. It's already broken. Saboda you cheated on me EHSAAS. Meyasa da yace ka aureta, ba ka ce ba ka so ba? Uhm? Sai kace ba ka so, ai na san ba zai yi maka dole ba. Just tell him the truth,"
"Islam," ya faɗa gently yana ɗaura kanta saman kirjinsa. "Kisani what is about to happen is inevitable. Ke ba kya tunanin akwai abin da Allah yake so ya kullar tsakanina da Mehtav, shiyasa ya kaini kasarsu, kuma ya sanya na faɗa hannunsu. I think wannan auren shine dalili. Baby, let's stop fighting Allah's will. In Mehtav matata ce, kada mu dagama kanmu hankali. Kada muce zamu jada hukuncin Ubangiji, kin ji? Kinaso in bijire ma Mai Martaba akan umarnin da yayi min wanda ba haramun ba ne? In haɗi da fushin Ubangiji? Baby, kin san his heart failed already. So kike in bijire masa zuciyarsa ta ƙarasa bugawa?"
Daga kanta tai daga jikinsa, ganin yana neman ya gama raina mata hankali, sai wani hanya-hanya yake mata. Ya kasa fitowa yace mata direct, shima yana son auren ne ba wai yayi amfani da sunan Allah da kaddara da Mai Martaba ba.
Turesa tayi daga jikinta tana miƙewa tsaye. Dogon gashinta na wani irin kadawa saboda iskar safiya. Tace:
"Mai bijire wa iyaye kake magana koh? Nisau nawa ina bijire ma nawa saboda kai Sire? Ni ne banida hankali koh? My father even cursed me, duk saboda I choose you over him. Amma kai ce masa ba zaka iya auren Mehtav kaɗai bane ya gagare ka koh? Tohm, na fahimta. Just come out ka ce min, Islam ke ce ba ki da hankali. Ba ki san ciwon kanki ba. Ba ki san darajar iyayenki ba, shiyasa kika yi haka. Kuma kana son Mehtav , ko ka ƙi ko ka so, kana sonta. Just accept it already. Kaje ka yi sabon aurenka. Ni ma ka sake ni, in je in nemi wani mijin da zan ishe shi ni ni kaɗai, ba zai ga gazawata ta ko ina ba, har yayi tunanin min kishiya!"
Ta ƙarasa tana ɗaukar Jr, miƙewa yay zuwa yanzu ransa ya fara ɓaci da ƙalar maganganun da take gasa masa, amma kuma ya san ita kanta batasan me take faɗa ba, shiyasa ba zai biye mata suyi batacciya ba.
Bayanta ya bi, ta juyo tana nuna shi da yatsa:
"Kada ka sake ka biyoni. If not, idan na bar gidan nan, ba zaka sake ganina ba. Na rantse."
Ta fara tafiya. Muryarsa ta ji:
"Pls don't hurt yourself, baby. Take care of yourself. I love you. Ina sonki kuma har abada zan ci gaba da sonki."
Ji take kalaman nasa kamar garwashi a cikin zuciyarta. Domin ita ba ta yarda mutum zai iya son mace fiye da ɗaya a lokaci guda ba. Kawai tana kallon abin as rainin wayo. Straight dakinta ta wuce, ta sake yin wanka, ta ci ado kamar yadda ta saba, kamar ba ta cikin wata damuwa. Ta shirya Jr shima, ta ɗauki trolley ɗinsu, ta haɗa musu kayansu kusan kala goma-goma a ciki.
Ta nufi dakinsa inda yake ajiye makullayan motocinsu. Ta buɗe, ta ɗauko makullin favourite car dinsa don tabashi haushi tasan sarai bayason atabamai motarnan tohm da ita zata tafi taga yadda zeyi. A bakin ƙofa suka ci karo, da sauri ta ɓoye makullin, domin ta san in ya gani ba zai bar ta ta fita ba.
"Menens abayanki kike ɓoyewa?" Ya tambaya yana kallonta suspiciously.
Daɗa lulluɓe makullin tayi hannayenta na bayanta, ta soma masifa:
"Au, yanzu tun kafin kai aurenma har an kwace min right ɗin shigowa dakinka in ɗau abinda nake so a lokacin da nake son fita?" Ta faɗa tana kifi-kifi da ido da yasan akwai abinda take ɓoyewa.
"Baby, in ga. In gani. Tohm, in dai kin san kina da gaskiya." Ya faɗa yana ƙara matsowa daf da ita.
"Ni dai ba zaka gani ba." Ta faɗa tana baya-baya. Da yayi taku ɗaya, ya cafkota, ta faɗa saman kirjinsa. Ya shiga lalube hannunta.
"Me neye haka? Ka bari!" Ta fara ƙoƙarin kwace kanta. "Na ce ka daina tabani! Ka bari mana!"
Bai saurareta ba har sai da yayi nasarar cafko makullin da yake hannunta. Ya karɓe su yana faɗin:
"Ina zakije uhm? Your stubborn baby, fita a palace ɗin nan is not safe for you and Jr kin sani ko?"
Bubbuga ƙafa ta fara yi cikin gardama. Ta ce:
"Ni gidanmu zan tafi gurin iyayena, nima in yi musu biyayya. Ai dama ba sa son aurenka. Saboda na tubure ne suka hakura. And I still remember what daddy told me da muka sauka a airport. Ya ce ya canza, ya daina takuramin. I should call him or visit him duk sanda nake so. I'm highly welcome. Don haka nima tafiya zanyi."
Bai saurareta ba, kawai ya wuce, ya maida makullin motar, ya kulle drawer ɗin, ya saka makullin a jikinsa, ya wuce bathroom.
Zaune tayi, ta fara ƙunkuni ita kaɗai, har yayi wankan, ya gama, ya fito.
Closet ta bishi. Ya fara shiryawa. Ba ta ce masa kala ba. Kuma yana kallonta, fakon key ɗin drawer ɗin dake gabansa take yi.
Kaya ya ɗauko kananu, ya shiga fara sawa. Ta tsaya tana kallonsa cikin mamaki, domin in ba yamma ba ce, ba ya cika saka kananun kaya a Nuristan ba, musamman in fita zai yi,yakansa kanun kayane da yamma ko kuma inyana gida tare da ita don ya burgeta, jiya taga yasa yafita d daddare tasan gurin Mehtav yaje yanzun ma can zai same komawa kenan tashiga rayawa aranta,batasan lokacin da tace masa
"Ina ne zaka je haka? Naga ka sa kananun kaya uhm?" Ta tambaya tana kare masa kallo, saboda wani irin masifaffen kyau da ya mata.
Smiling taga yayi kafin yace mata: "I have meeting da Mai Martaba da Paa, shiyasa."
Kicin-kicin tai da fuska tana faɗin: "Engineer Habib bai."
Jinjina mata kai yayi, tace: "Uhm, you're already calling him Papa tun kafin a ɗaura kenan?" Ta ƙarasa gabansa.
Kallonta yayi yana humming, yana faɗin: "Baby wai yaushe kika koyi fassara duk abinda nace ne da something negative uhm? Bafa nason rigima aikinsan tuntuni Paa nake cemai kamar yadda yaransa suke fada"
Dafoshi tayi tana faɗin: "Oh nicema yanzun nakoma mara gaskiyar koh toh bari kaji,Kai ma babu inda zaka je, tunda nima ka hana ni fita."
Dariya ya fara yi yace: "Ohhhh, ramawa zaki yi kenan?"
Ta jinjina kai, Bilhaqqi da gaskiya I kuma take magana.
"Ke yanzu kin taɓa jin inda mata ta hana miji fita a tarihin rayuwar ma'aurata?"
Jinjina kai tayi tana turo masa baki gaba. Yace: "A ina uhm?" Yana ɗaukarta, ya ɗaurata saman dressing mirror.
"Anan mana," ta ce tana gyara zaman gyalenta.
Chuckling yayi yana faɗin: "Mai Martaba ne fa baby."
Tace: "Shi fa yace a min kishiya."
Yace: "Ohh, shima harda shi ake fushin? Za a yi punishing kenan?"
Jinjina kai tayi kafin tace: "Harda ma Fulani - dukkansu. Da baban Mehtav ɗin duka. Na san yanzu ma kuma maganar auren za a aje ayi. Don haka babu inda zaka je."
Yace: "Baby, wai haka kike kin auren nan uhm?" Yana ɗaga mata gira ɗaya.
Ta jinjina kai alamar "eh." Yace: "Tohm, an fasa. Ranki ya daɗe. Aikin san girman ki ya wuce haka a gurina."
Hararar wasa ta watsa masa, saboda daga tone ɗinsa ta san raina mata hankali yake shirin yi, dan tabarshi ya fita din,shikuma had cikin zuciyarsa yakejin ze iya hakura da aurennan in har zuciyarta bataso,kuma bada wasa yake ba,domin duk abinda zeshiga tsakaninsa da Islam har yadauke peace od mind dinta gudunsa yakeyi,yanzun dai zecigaba da lallabata yasan tanada taurin kai sosai amman tanada mugun saukin kai idan yay mata bayanin situation din dasuke ciki as far s zata tsaya ta saurareshi kaso dadi nacikin kiyayyar ta da aurensa zata ragu, Yadda yake kallonta da yadda idonta yatashi yanuna mai cewar bakaramin saka abin aranta tai ba, Abazata taji yayi kissing cheeks dinta, Ahankali yace mata "inasonki baby inakaunar ki,wllh babu wata macen dazan kawo cikin gidannan amatsayin tawa batareda amincewar ki ba just listen to me kibarni inje meeting dinnan yanada matukar mahimmanci inje din" Dukda taji yadda kalaman shi nafarko suka so tasiri azuciyarta amman mgnr fitar dayay akarshece yasa taji kamar wayo yake kokarin yimata don yafice din tamakale mai kafada tana fadin "I will not allow you to go outside!" Ta ƙarasa faɗa tana dirowa ƙasa.
"Dan Allah baby ki yi haƙuri, kar mu yi haka dake…" Ya shiga lallashinta.
Girgiza kai ta fara yi tana faɗin: "Ba inda zaka je fa. Sai dai nima zaka barni in je inda nake so."
Riƙe kansa yayi yana faɗin: "Plsss ki yi haƙuri da batun zuwa gidan nan naku. Na miki alkawari idan na zauna da kaina zan kaiki, ki je ki wuni musu. Amma batun kwana, kin san I can't sleep in ba kya tare dani baby. I can't."
"Another lie," ta faɗa tana ficewa a closet ɗin, ta nufi ƙofa. "How many months ka yi spending a Nigeria? Da wa kake kwana? Uhm? My ghost ko Me? Stop sugarcoating everything, Sire. Dama ku marubuta shegen daɗin baki ne daku." Bude baki yayi har zeyi magana sekuma yafasa,bayau tasaba mai irin wannan gabuntar ba, Sam sam ita bata iya boye boyeba musamman intana tareda shi duk abinda yazo ranta shitake fada,jifa yanzun wai shitake cema yana karya,girgiza kai kawai yayi yana bin bayanta yayi, yaga ta soma ƙoƙarin lalata security ɗin ƙofar. Da sauri ya fara lallabata.
"Plz kibari babynah, Islam Mai Martaba najirana fa kiyi hakuri," ganin batada shirin sauraronsa yasa yace "Jr fa? Ina kika baro shi?"
Sai sannan ta tuna. Ta ce masa: "Ai yana barci a can cikin dakina."
Yace: "Tohm, a can za a bar shi shi kaɗai? Ai bari na je na ɗauko miki shi. Sai mu shiga lockdown ɗinmu duka ko baby it'll be fun just the three of us baby"
Jinjina masa kai tayi, alamar "toh." Ba ta taɓa kawo wayo yayi mata don ya gudu ba.
Ta tsaya tana jiransa.
Shikam, yana karasawa dakin ɗaukar Jr dake barci yayi, ya fice daga gidan baki ɗaya. Saboda ya san duk rintsi, ba za ta taɓa tafiya ko nan da can batare da Jr ba.
Tun tana jiransa, shiru-shiru, har ta gaji. Ta biyo bayansa. Taga babushi babu Jr. Sai a lokacin ta gane, wayo yayi mata.
Ita ma kamar ta fita ta bisun taji don ta san gurin Fulani zai kai Jr. Amma ita kanta Fulani, haushinta take ji, don tasan ba yadda za ayi Mai Martaba yayi hukunci irin wannan ba tare da neman shawarar ta ba.
Ita babban takaicinta daya, kasance ita ce da hannunta ta gayyato su Mehtav. Da ta sani, da bata yi ba ta ke ta maimaitawa a ranta.
EHSAAS kam yana ajiye Jr gurin Fulani, Ya sanar mata abinda ke ransa regarding the marriage be boye mata komai gameda rigimar da Islam takeyi ba yace mata shikuma duk abinda ze daga mata hankali bayaso the girl has seen enough shi he can sacrifice the throne abawa wani kawai indai har bata amince ba Murmushi kawai Fulani tai irin nasu na manya kafin tace yaje kawai zatai magana da Islam din zuwa anjima in sha Allah komai zetafi yadda ake bukata,saboda taga tsananin damuwar dayake ciki akan fuskarsa,abinda in EHSAAS yana cikin damuwa bame ganewa amman indai batune akan Islam baya iya controlling kanshi kwata kwata. Umarni tabashi yatashi yaje meeting din, Yay mata sallama straight ya wuce can sashen Mai Martaba, inda aka shirya musu breakfast, su su uku: shi da Mai Martaba baban Mehtav. Contract suka bashi ta renovating palace ɗin baki ɗaya. Hukunci ne wanda Mai Martaba ya yanke a daren jiya saboda yasan koda ya bawa Habib Bai dukiya mai tsoka ba lallai ya karɓa, amma ta hanyar aikinsa, in suka bashi babban aiki irin wannan da zai samu ɗumbin alheri, zai ji daɗi sosai.
Aiki ne da zai ɗauki wata ɗaya cif-cif Yana yinsa, kuma Mai Martaba ya bashi aikin ne tare da hikima mai tarin yawa domin yana son ya ci gaba da zama anan tare da iyalinsa har zuwa lokacin da za a kammala. Shikuma yana sa ran daga nan Mehtav da EHSAAS za su sasanta kansu.
Kwangilace irin wacce Habib Bai bai taɓa samu ba ,saboda palace ɗin NURISTAN gari ne guda wanda renovation ɗinsa za a barnatar da dukiya mai tarin yawa kuma gashi sun bada short notice. Already sun yi structuring duk yadda suke so tsarin ya tafi. Architects ɗinsu sun gama zana yadda abin zai tafi.
Aikin Paa shine ya jagoranci ginin da tsarin komai da komai ɗin. Yaga musamman bangaren prison ɗin cikin gidan sunason a ƙara mai tsaro da high-tech ɗin zamani.
Daga bangaren su Mehtav kuwa, washegari da safe har cikin dakunansu aka kai musu breakfast. Inna ma dakinsu ta dawo don ta gaji da zaman kaɗaici ita kaɗai.
Wani 3-tier golden tray aka ajiye musu mai cike da royal dishes: lamb chops in cranberry glaze, roasted breadfruit, croissants with rose petal jam, Nuristani butter tea, da sabbin fruits daga gardens of Khorasan.
Sunci, sun koshi, sun yi nak musamman Inna da Abeey. Mehtav ce dai taci kaɗan saboda rashin appetite da kuma cuisine wacce bata saba da ita ba, saboda sosai abincin ya bambanta da nasu.
Suna gamawa maids suka zo, suka kwashe kayan, suka gyara gurin tsaf. Mehtav ta nufi cikin balcony, ta zauna tana kallon garden din gurin, wata iska mai daɗi tana ratsata. Yayinda Abeey ta zauna gefen gado tana ta dannan wayarta, kamar wacce ke jiran kiran gaggawa.
Mehtav ganin kamar abu take jira a wayar yasa ta dawo dakin tana faɗin: "Ke Abeey... lafiya kiketa duba waya every minute? Are you waiting for someone's call?" Ta ƙarasa maganar da shakku a cikin ranta.
Abeey ta ɗan tabe baki, tana faɗin: "Nothing. Just expecting something special." Ta ƙarasa tana basarwa.
Mehtav ta ɗan kalleta da tsantsar shakku, amma bata samu damar cigaba da tambayar taba, suka ji ana sake kwankwasa ƙofa. Da sauri Abeey tace: "Shigo!" Don ta san maid ce.
Aikuwa, segata ta shigo da murmushi akan fuskarta. Ta tsugunna kamar yadda ta saba, ta gaidasu, Abeey tai caraf ta amsa kafin ta isar da saƙon da Fulani ta aikota da shi. Ta faɗa musu: "Please, Her Majesty, Queen Fulani Hajar is requesting your presence. She would like to take you around and host you in her personal chamber."
Inna ce ta watshe baki tana ɗaukar mayafinta tace: "Oh tohm, tohm, ki ce mata gamu nan. Ai muna nan tafe. Daman ko ba ta gayyacce mu ba, za mu zo mu mika gaisuwa."
Abeey ma cike da murna take faɗin: "Mehtav, let's go.Next Mother Queen ce fa take kiranmu da kanta!"
Mehtav kallonsu take yi cike da takaici, yadda suke rawar jiki a gaban maid. Ta girgiza kai kawai, ta kalli maid ɗin tana faɗin: "Tohm, gamu nan."
Fita tayi ta jira su a waje. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fito, already duk sunyi wanka, sun shirya cikin haɗaɗɗun natives ɗinsu , daya daga cikin kayan sallarsu wanda Abeey ta sako. Sunyi bala'in kyau. Sai suka fita daban a fadar dake su NURISTAN ba sa saka irin kayannan sosai, sai daidaikun mutane.
Gaba ta yi, suka soma binta a baya. Dayake Fulani tana so su ɗan gaggar palace ɗin, bata ce a kawo su da mota ba. Aikuwa sun sha kallo.
Suna tafe cikin wani long hallway da bangarorin ke ɗauke da zane-zanen tarihi na royal ancestors.
Abeey zata shiga tambayar maids suwaye da waye, Mehtav ta daka mata tsawa. Hakan ne yasa tayi shiru, ba don ta so ba har suka fito wajen chambers -chambers na mutanen gidan.
Chamber ɗin Mai Martaba suka fara wucewa kafin su wuce bangaren EHSAAS. Abeey keta santin wurin tana nuna ma Inna wai nan inane.
Maid ɗin ce ta sanar mata bangaren Yarima ne da matarsa.
Juyowa tayi tana kallon Mehtav, tana mata signal da ido irin "Tagani fa, itama irin wannan za a mata."
Mehtav basarwa tayi kamar bata gane me Abeey take cewa ba.
Opposite gidan EHSAAS, wani haɗaɗɗen royal horse stable ne. gurin nashi ne, ba na masarauta ba. Duk wasu dawakai da ke gurin mallakinsa ne.
Abeey kallon maid ɗin tayi. Ganin kyawawan fararen dawakai yasa ta fara tambaya: "Wai zan iya zuwa?"
Girgiza mata kai maid ɗin tayi tana ce mata: "A'a, ba wanda yake shiga gurin sai Prince Aman da EHSAAS da matarshi. Gurin sai da izininsa ake zuwa."
Turo baki tayi. Suna tafe tana ce mata: "Ita ba ta san shi abokinta bane ba? Ta shiga da ita. Ta tabbatar ba zai hanata ba."
Maid murmushi kawai takewa Abeey, bata daice komaiba har suka ƙarasa bangaren Fulani.
Tarbar girmamawa aka yi musu, aka shirya musu sabon kayan makulashe iri-iri a gabansu. Dake sunyi breakfast sun koshi, cikinsu babu wanda yaci da yawa.
Fulani tana ta nan-nan da su. Jr na saman cinyarta. Abeey ta matsa gefenta, don kar Mehtav taji ta hanata. Har ƙasa ƙasa da murya take ta fara zuba wa Fulani tambayoyi iri-iri kan abubuwan da ta gani a hanyar da ta zo sashen:
>"Who is that man in that painting da muka gani a hallway din farko?"
Fulani tayi ɗan jim kafin tace: "Duk kakannin EHSAAS ne. Ban san wanda kike nufi a ciki ba."
Tace: "Me wani gemu dayawa, baya murmushi."
Fulani tayi murmushi tana faɗin: "That must be EHSAAS' great-grandfather."
Abeey ta jinjina kai kafin tace: "Kuna jin daɗinku. Y'all really live in here?"
Murmushi Fulani tayi itama, tace mata: "You can live here too in kinaso. Zan ce ma babanki yabarmin ke, kinga dama ba mu da ƙananun yara."
Girgiza kai tayi tana faɗin: "I like it here, amma dai kin san ba zan iya zama anan babu Mehtav da Innata ba. Sai dai dukkanmu zaki bari mu zauna anan din."
Jinjina kai Fulani tayi, saboda maganar yarinyar na bata nishaɗi. Tace: "Why not?"
Mehtav wani irin bombastic side-eye take bata, irin "Tai shiru nan", amma Abeey ta ƙi ma yarda ta kalleta balle ta gane abinda take nufi.
Ta kalli Fulani tana tambayar: "Do horses get cold at night? Can I ride one pls? Naga wasu kyawawan fararen dokuna a wani guri, wai an ce na prince ne. Ba mai hawa. Naga ai abokina ne kuma ko shi na tambaya ba zai hanani ba koh?"
Mehtav daurewa tayi kawai ta kalli Abeey cike da murmushi. Cikin sigar lallabawa take faɗin: "Abeey, pls stop disturbing her with all this your silly questions..."
Murmushi Fulani tayi tana faɗin: "Uhmm uhm, karki hanata. She's my daughter too. This is her house. Let her talk, let her ask anything she wants."
Abeey ta sa dariya, tana faɗin: "Tohm kin ji, tun dazun take ta hanani magana wai in kama kaina, in kama kaina. Aikin ce duk mun zama ɗaya ko Maama." Tafada tana leaning towards her.
Shafa kanta Fulani tayi tana jinjina kai tana faɗin: "Exactly. We are all one."
ɗaya daga cikin maids ɗin ta kira tace mata: "Ga Abeey nan, a kai ta horse stable ɗin Yarima. Let her pick any of the horses she wants and climb it. I'll send the royal handler to guide her."
Tsalle Abeey ta daka tana rungume Fulani kamar ta dade da saninta. Tayi dariya, itama ta rungume ta back tace: "Nagode sosai Maman Handsome Yay. I'm finally going to ride a horse!" Tafada tana sakin ta.
Maid ɗin ce ta kama hannayen Abeey tace su je. Sanin Abeey ba kaine da ita ba, zata iya zuwa ta yi ta kiriniya, yasa Mehtav ta miƙe tana faɗin: "I'll like to join her too."
Ɗan kallonta Fulani tayi, ta yi ƙasa da kanta. Murmushi kawai Fulani tayi tace: "Tohm, ba komai,tabi su," suka zauna daga ita sai Inna wacce ta karɓi Jr daga hannun Fulani, suna ta wasan su.
Mehtav ce a gaba da wasu maids biyu da suka musu rakkiya. Abeey da third maid din a baya. Tana jin kus-kus dinsu amma bata san me suke cewa ba, saboda taga Abeey din nema take ta mayar da duka maids ɗin kawayenta.
Ganin Mehtav tayi gaba sosai yasa Abeey ta ja rigar maid ɗin tayo baya da ita. Juyowa tayi tana tambayarta: "Lafiya?"
"Aunty please. Ki taimaka ki kai wannan card. It's from Princess Islam. My friend is at the palace gate, Ahmad Gaya. Just tell the guards he's here and give him the card." Ta miƙa mata royal guest card ɗin shigowa palace da aka haɗa musu cikin kayan da Islam ta turo musu Nigeria.
Kallonta maid ɗin take cike da mamaki. Ina ta samo katin nan? Saboda sai manyan mutane da 'ya'yan sarauta ne ke samun shi, shine zai baka access ɗin shigowa Palace a kowane lokaci, ko da ƙarfe uku na dare ne.
Abeey ta daura da cewa: "Please, don't let anyone know. Just give it to him. He'll understand. And come back quickly."
Maid ɗin jinjina kai kawai tayi, ta karɓi card din, ta juya da sauri. Abeey tayi sauri ta falfala don tana son ta kamo su Mehtav kafin su karasa gurin.
Tana haki ta cim musu adaidai ƙofar gurin inda maid ɗin ta faɗa musu saƙon Fulani Hajar. Aikuwa nan da nan aka buɗe musu, suka shiga. Abeey sai daɗi take ji.
Zagaye kayataccen gurin suka soma yi. Abeey sai tsalle-tsallenta take yi tana jin daɗi, tana ta kallon dokuna wai zaɓa zata yi ta dirje wanda zata hau.
Mehtav kam ba wata walwala a fuskarta kawai biye ma Abeey take yi saboda ba ta son ta bar ta ita kaɗai tare da maids ɗin nan.
"Yah Mehtav, kinga wannan dokin fa? Kamar dokin fim ɗin Zorro ne! Kingane shi? Gaskiya ni shi zan hau." Abeey ta faɗa tana ƙoƙarin shafa ɗaya daga cikin dawakan masu launin chestnut.
"Ke ki yi a hankali dan Allah. Ko tsoro ba ki ji... Ta ina kika iya hawa doki?" Ta ƙarasa tana jawota baya.
Abeey tana murna take ƙoƙarin komawa kusa da dokin, amma Mehtav ta hanata. Daidai lokacin Aman ya iso gurin.
Yana sanye da royal riding jacket mai fitinannen kyau. Ya kalli Abeey yana cewa: "Princess Abeey, ke ce wacce Grandma ke magana kenan? Y'ar ƙaramar ki dake kike son hawa dokin?"
Tabe baki Abeey tayi tana faɗin: "Ni ba y'ar ƙaramar bane, I'm in JSS1."
Dariya ya fara yi, ya shiga janyo dokin da yaga tana so yana faɗin: "Tohm, Big Lady, are you ready for the ride? Amma fa sai kin matsar mana da waccan matsoraciyar 'yayar taki anan gurin." Ya ƙarasa yana kallon Mehtav da ta basar, ta ɗauke kai kamar ba da ita yake ba.
Abeey ta kyalkyale da dariya tana faɗin: "Kamar kuwa ka sani, tsoronsu take ji fa. Ni dai mu kyaleta kawai. Inason ka koya min." Ta ƙarasa gabansa.
Yace: "Of course, Your Highness." Yana mata murmushi. Itama ta mayar masa. Ya soma gyara sirdin dokin. Yana gamawa, ya ɗaga Abeey cancarakas kamar y'ar tsana.
Ta soma ciccilla ƙafa tana faɗin: "Wayyo, kar fa in faɗi! Ka rike ni da kyau."
A haka ya ɗaura ta saman dokin. Duk da uban tsoron da take ji, amma bai hanata washe baki ta fara bragging ba. Tana cewa: "Mehtav, waita gani! Ta iya hawa doki fa!"
Sosai Aman ya rike mata abin dokin, a hankali ya fara jansa yace: "Ta rike da kyau..."
Mehtav tana gefe, tun ba ta kallonsu har tazo ta fara kallonsu, tana wa drama ɗin tasu murmushi tana watching yadda ake tafiyar. Kafin ta juya da nufin tafiya daga wurin, idonta ne ya sauka akan maid ɗin da ke shigowa tare da wani mutum dawani aura of glow da masculine confidence ya lullubeshi, wanda ba ta taɓa tsammanin gani a lokacin ba. Kallo ɗaya tayi mishi, ba tantama ta gane wanene shi.
Innalillahi wa Inna illahirraji'un, ta shiga maimaitawa a cikin zuciyarta saboda ta san...
Ahmad Gaya ne.
Tsayawa tayi cak har ya karaso daf da ita, yana sanye da fitted wear, classic kaftan da western suit top, looking breathtaking. Chocolate complexion ɗinsa na haskawa da luxury perfume ɗinsa na Prada Intense ya cika mata kirji tun kafin ya karaso. Mamakin zuwansa da kuma shigowarsa har cikin palace take yi.
Murmushi ya sakar mata, ta rasa ma me za ta ce mishi.
"Ahmad…?" ta furta cike da mamaki.
Matsowa daf da ita yayi yana faɗin, "Na yi missing ɗinki sosai Mehtav. I had to come… ba zan iya jurewa ba. Na san ba daidai bane, but I came to see you. I'm sorry."
Kana kallonta kasan damuwa ce fal a idanuwanta, damuwar kada ace ba a barin baƙi su shigo haka kai tsaye, damuwar kada ace ta karya wata doka, damuwar kuma tausayin Ahmad da ke mata irin wannan son, wanda tasan ba za ta taɓa iya reciprocating masa irin son nan ba.
Tana kallonsa kamar ta rasa abin da za ta ce. Da ƙyar ta iya buɗe baki, muryarta asanyaye tace: "Ahmad, this… this is not right. Ka san palace ɗin nan na da rules, I don't want a scene here. Ka san nan ba gidanmu bane, ba ko?"
"Zan tafi, wallahi zan tafi. I just wanted to see you, Mehtav. I needed to confirm da idona cewa kina lafiya. Saboda duk sanda na kira, Abeey ce ke ɗagawa. In na yi chatting ɗinki ma, ita ce take amsawa. Allah yasa ba wani laifin na yi miki ba." Ya furta yana kallonta kamar wanda zuciyarsa ke shirin karyewa.
Mehtav ta kalli gefe, tana jin zuciyarta na ƙoƙarin relating da abin da yake faɗa. Ace mutum ya taso kafa da kafa, ya bar ƙasarsa, ya bar aikinsa kawai don yazo yaga kina lafiya ko akasin haka. Ahmad really cared about her. Yau ta tabbatar da hakan.
Amma kuma ba ta son ta cutar da zuciyarsa, ta ba shi fake hope. Har ta buɗe baki za ta yi magana kamar wadda ta tuna wani abu kawai, sai ta juya da nufin tafiya. Ta kan wani tudu kaɗan da ke wurin ta bi… sai kafarta ta subuce.
Ba dan Allah ya sa Ahmad yayi zafin naman tareta ba, da babu abin da zai hana ta ci da ƙasa. Ya riko hannayenta da kyau, cike da concern yake faɗin: "Be careful durlin, are you okay?" Ya rike ta sosai har sai da ta daidaita.
Sai dai kafin ta ce komai, muryar EHSAAS ta daki dodon kunnenta. Kana ji kasan asama yake cikin bala'in da ba ta taɓa sanin yana dashi ba. Taji yana faɗin:
"WHO THE HELL IS THAT?!"
Kowa ya tsaya cak. Guards ne suka zagaye sa duka, don ba iya su dake cikin gurin ba, duk wanda ke area ɗin gurin yaji tsawar da ya daka. Yana tsaye a bakin ƙofar gurin, da alama shigowarsa kenan, da idanunshi jajir suna bin Ahmad da Mehtav da wani mugun kallo.
Guards ɗin yake bi da wani banzan kallo, wanda ba su taɓa ganinsa yana irin shi ba. Yake faɗin: "Ku gaya min waye wannan mutumin? Who the hell even allow him in?! This is the Palace of Nuristan! Haka dama kuke barin kowa yana shigowa ciki kamar club?!" Ya fasa musu ihu, wanda ya rikirkita su. Yana kallon su daidai daga Ahmad din har Mehtav.
Zubewa guards ɗin suka yi, suka soma ba shi haƙuri suna roƙon afuwa akan ya yi musu rai,sun dauka tareda bakin yake.
Mehtav ta kalli EHSAAS da shock a fuskar ta. Kamar iska haka ya karaso gabanta, yana kallon cikin idonta. Ya fizgo hannayenta daga cikin na Ahmad da ƙarfi.
"EHSAAS stop..." Ta faɗa tana ƙoƙarin fizge hannunta a nasa saboda yadda ya matse hannayenta.
"Ke shiru!" EHSAAS ya katse ta, yana kallon Ahmad daga sama zuwa ƙasa. "Kai waye?! Waye ya baka damar shigowa nan?! Kuma why the hell are you holding my wife?!"
Ahmad ya ɗaga gira cikin confusion: "Excuse me?! Wani wife? Who is your wife?"
Wani irin kishi da wuta suka huda zuciyar EHSAAS. Ya juya da sauri yana kallon guards ɗin:
"GUARDS! THROW HIM OUT! NOW!"
Abeey da Aman ne suka taho da sauri suna ƙoƙarin fahimtar me ke faruwa, musamman Abeey da tasan itace ta kulla komai.
Guards ɗin kuwa da bala'in sauri suka yi kan Ahmad, zasu yayyeme shi su yi waje da shi, Mehtav ta fizge hannunta cikin na EHSAAS, tayi wuf ta tsaya a gaban Ahmad cikin gargadi. Ta ɗaga ɗan yatsanta tana faɗin:
"No one is touching him! Ahmad is my fiancé! The man I'm going to marry! So if you will touch him, start with me! Kuma duk wanda yace ze wulakanta shi, tamkar ni ya wulakanta!"
Ta ƙarasa faɗa zuciyarta a ɗake tana kallon cikin grey eyes ɗin EHSAAS da ya juye ya zama ja don azabar kishi.
Kamar an dasa shi, ya tsaya chak, yana daga wa guards ɗin hannu alamar su tsaya.
Idanunsa cike da shock, anger, da wani irin zazzafan kishi yace:
"Fiancé...? Mehtav...?"
Abeey ganin Mehtav da EHSAAS na shirin rigima akan Ahmad, haƙuri ta fara basu tana faɗin: "Pls pls, it's all my fault. Nice na saka a shigo da su. Handsome prince, kayi haƙuri. Kar kai masa komai. Ahmad is a nice guy, kayi haƙuri, kaji." Tana janyo hannayensa alamar ya saurareta, amma kamar da gunki take magana saboda idanunsa kawai Mehtav suke gani, data tsagalgalenshi take iya gaya masa wai wani namiji fiancé ɗinta ne.
Shifa? kenan Har ta bawa wani da namiji sunansa daga tafiyarsa a rayuwarta.
Ahmad kuma gaba ɗaya ya gama karance ruwan wutar kishin dake cikin idanun EHSAAS. Ya saki wani murmushi saboda sosai yaji daɗin yadda Mehtav tayi depending ɗinsa.
"Uncle Prince, pls... let's go," Aman ya faɗa yana damke kafadar EHSAAS. Saboda yasan EHSAAS is not himself right now, kada yaje ya saka a yi wa ɗan mutum wani lahani da zaizo yana dana sani daga baya.
Saboda tun akan Islam, yasan cewa uncle ɗinsa na da masifar kishi.
It's fatoumspassion EHSAAS Share Comment Like & Vote.
[12/07, 20:51] Fatima Rufa'i Nasidi: Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.