Chapter 48
Daga bangaren Fulani kuma shiru-shiru jin su Abeey basu dawo ba har zuwa lokacin. Ga Inna sun bari a gurinta da Jr, ya gama luguiguitata daga ita har shi, sun kwanta barci a falon. Seda taga barcin Inna na kokarin yin nisa ta saka aka tasheta, domin ba zata ji dadin kwanciyar anan din ba. A mota aka maidata dakinta, aiko nan da nan ta cigaba da kwasar barcinta.
Anan ne Maid ɗin da ta raka Inna take sanar mata ai su Mehtav ma sun jima da komawa masaukinsu. Jinjina kai kawai tai, ta shiga mamaki kenan har Abeey ta gama zumudin hawa dokin. ba ta tambayi ba'asi ba? Amman dai ta bada umarnin duk abinda ya kamata a kai musu sashen nasu na lunch, sannan itama ta shige ciki tare da Jr abinta. Seda Jr ya tashi daga barci yana rigima sannan ta lura yau din tun da Islam ta tashi ba ta zo tagaidata ba. Murmushi kawai tai saboda ta san kila fushin ne har da ita Islam takeyi. Ta daga waya ta kira ta. Seda ta kusa katsewa tukunna aka daga.
Shiru Islam tai daga dayan bangaren kamar ba zata ce komai ba, sai kuma dai tagaidata kamar yadda tasaba. Amman murya ciki-ciki. Fulani murmushi kawai tai tace: "daughter, har yanzun ba za a zo a gaidani ba?"
Shiru Islam tai, ba tace komai ba. Seta ce: "Tohm, ga mutumina fa ya tashi kuma kin san baya wasa da cikinsa. Ko in kawo shi da kaina?" Da sauri Islam tace: "A'a Maama, ganinan zuwa," Saboda ta san Fulanin ita takeson gani, ba wai saboda Jr ya tashi ta kirata ba. In ba haka ba, ai yana da baby formula. Da ya fara sha a sashenta zata iya sa wa a hada masa ta bashi. Murmushi Fulani tai tana fadin: "Tohm, se kin karaso Princess," tana kashe wayar.
Islam kamar kar taje, se kuma dai kawai ta mike taje ta sauya kayan jikinta zuwa wata haɗaddiyar lifaya da ta ci uban gwal-gwalai. Domin Fulani ta koyar da ita kwalliyarsu a duk inda zata shiga a cikin fadar nan, in dai ba tare da mijinta ba, saboda yana kawar da raini. Text ta rubuta ma EHSAAS, zata je sashen Fulani. Ba ta ga ya karanta ba kuma be mata reply ba. Hakan ne yasa tai ficewarta. Guards ɗin suka bita da kallo saboda ba a mota suka gan ta ba. Yasa ba su yi ƙoƙarin dakatar da ita ba, se zubewa suke suna gaidata sama-sama. Ta ansa, ta wuce sashen Fulani Hajar ɗin direct.
A ƙofar babban hallway ɗin ta dan tsaya tana ƙoƙarin gyara lifayarta, ta ji ƙus-ƙus ɗin wasu maids: "Wallahi ke, kinga tsawar da ya daka mata? Ita da mutumin?" "Ni ban taba ganin mai girma Yarima cikin irin wannan fushin ba," ɗaya daga cikin maids ɗin suka fada.
Kirjin Islam bugawa ya soma yi jin suna ambaton sunan EHSAAS. Kar dai wani abu ne ya same shi? Se kuma taji muryar ɗayar tana fadin: "Da alama dai maganar da muke ji a gari gaskiya ce - wai da gaske ita bakuwar ita ce matar da ze sake aura?"
Dayar ce tasheke da dariya tana fadin: "Au wai har soyayyar ta kare, ita ina uwar yan jinkannan da bata kallon kowa da gashi ta hana ma muke shiga gunsu. In yana nan don kar ya kallemu, ashe bata da wani tasiri har angama cin amarcin kenan."
Dayar tace: "Ke Bilkis Gimbiyah Islam aikuwa bata da wulakanci. Itadai kawai bata shiga harkar kowane."
Tace: "Toh, ai duk abu dayane. Nifa dama can gimbiyah Islam dinnan batamun ba, amman Mehtav dinnan dakuke gani koh gaidasu mukaje yi, bakiga yadda take amsa mana ba cikin mutunci da mutuntawa. Ga kanwarta basa kyamarmu sam, har dakinsu muke shiga, itakuwa bantaba ko leka dakinta ba, balle na yarima."
Ke kibar saurin murna. Dayar tafada kasa kasa: "Ke Mehtav dinnan kar take tsagera ce, batada mutunci. Itama wllh, inajin tamafi Gimbiyah Islam rashin mutunci, saboda ita har yariman bata bariba. namiji fa takawo har cikin private horse stable dinsa. Kinsan bame shiga, kuma yace afitar dashi. Tatsaya agabansa, tace be isaba, sedai yafara fitar da ita. Allah nadauka alokacin yarima kikkifar da ita zeyi, amman tsayawa yay yakasa Katabus ingaya miki, seda Prince Aman yajashi fa. Kinga idonsa kamar garwashi kuma itama bata raga mai ko kadanba. Shiyasa nake cemiki ba girin girinba, karmuje adakko wacca, shikansa tafi karfinshi, baremu. Kuma da alama yana masifar santa, inba hakaba meya kawo kishin."
Dayar ce tafara shewa tana fadin: "Zamuga drama acikin gidannan amman ke Bintu, a ina kikaji labarin nan eh?"
Tace: "Nida nice nashigo dashi aikuma kinsan dai turancinnan inajinsa degree garan. Karki rainamin wayo, nasan tambayar dakike shirinyi kenan." Shekewa da dariya sukai Dayar tace: "Amman lallai wannan Mehtav din, akwai tsaurin ido. Tunda nake ko cikin idon yarima bantaba ko kuskuren kalla ba. Ita har rashin kunya take iyamai Kenan."
Dayar tace: "Kedai bari ai Gimbiyah Islam, ankawo wacca zata takata da alama. Don ban taba ganin tawa yarima rashin kunya ba. Ke, ko kallon banza, kullum suna manne da juna kamar chingam. Ni haushi suke bani, waisu masoya."
Dayar tace: "Kedai Bilkis, kibari. Hassadace kawai take dawainiya dake, amman wace zata samu miji kamar yarima? Tai sanya gurin nuna masa soyayya."
Islam still tai tanajin kirjinta na kokarin fara tafasa, amman se wata zuciyar tace mata: "They are talking behind your back. Let them stay behind you." Dan sakin fuskarta tai tana sallama.
aida wani irin mahaukacin sauri suka tarwatse, kowacce takama aikin gabanta, suna zubewa suna gaidata kamar basune suke Yida ita yanzun ba, kana ganinsu kasan gaba daya arude suke, musamman wacce take cemata batada kirkin. Don daga yadda jikinta yake rawa, Islam tasan itace tafada din amman dan ta sake tabbatar wa, seta kalleta tace: "Ke tashi zonan."
A wani irin rikice tasoma yarfar da hannu tunkan Islam tai mata komai kota tambayeta komai tafara fadin: "Dan girman Allah, ranki yadade, kiyimin rai, kimin afuwa wllh. Subutar baki ne, narantse da Allah, nayi nadama."
Murmushi Islam kawai tai ta girgiza kanta. Tace: "The next time you talk around like that, I'll make sure I cut your throat dakaina" tafada cikin sigar barazanar da ta sake dugunzuma Maid din tashiga bada hakuri, harda majina wucewarta tai ciki kawai.
Anan ta tambaya inda Fulani take, akai mata iso zuwa dakin hutunta. Dayake dama Islam batada gate da sashen acan ta sameta tana kan saqa ma Jr wata hular sanyi da hannunta, domin in bata komai zakaga tadau saka, tanata yi.
Gaisawa suka sakeyi, fuskar Islam dai bayabo ba fallasa. Jr nata wasa da kayan wasanshi da aka baje mai adakin daya zama kamar nashi. Bata kallesa ba saboda yar alkunya ta zauna.
Fulani tace: "Barka da zuwa daughter."
Barkanki dai Maama, fatan munsame ku lafiya.
Alhmdlh, Fulani ta amsa da tana ajje sakar hannayenta, domin tanason attention dinta gaba daya yakoma kan Islam.
Tun safe na jiki shiru, baki shigo ba. Shine nace bari nai bikon 'diyar tawa, kodai nayi wani laifi ne?" Islam, Fulani ta tambaya tana kallonta. Kasa da kanta tai, bata ce komai ba, ta soma wasa da 'yan yatsunta.
Fulani tace: "Shirunki ya bani ansa, Islam. Ni me laifin ce agareki koh?" Ba kunya, Islam ta jinjina kai.
Fulani ta saki murmushi saboda honesty ɗin yarinyar yana burgeta. "Tohm, menai?" ta tambaya cikin salon janta, tai hira da ita kamar yadda suka saba.
Shiru Islam tai, bata ce komai ba. Seta ce: "Nifa na tambayeki, ki fadamin mana, yata." "Tohm, ba kune kuka ce Sire ya ƙara aure ba? Kuma Maama, aikinsa banason nai sharing ɗinsa da kowa. I want him to be mine alone." Takarasa idonta na cika da ƙwalla.
Fulani ta dafa ta tana faɗin: "Na fahimce ki sosai Islam, saboda nima mace ce. Babu ɗiya mace da zata so ta raba mijinta da wata, kinajina Islam? Amman a cikin kaddararmu ta auren yayan sarki, hakan tazo, kinji?" Fulani tafada cikin sigar rarrashi, da nuna mata tabbas ta fahimci halin da take ciki.
"Islam, do you want EHSAAS to lose his throne?" Girgiza kai Islam ta shiga yi.
Fulani tace: "They will never coronate him as far as basu aura mai mata biyu ba. Wannan wata bakar al'adar ƙasar NURISTAN ce. Duk Crown Prince se ya auri mata biyu. I'm not Mai Martaba's first - kinsan da haka koh?"
Islam ta jinjina kai.
Tace: "And I'm not his last - kinsani koh?" Ta ƙara jinjina kai.
Tace: "Duka aurenmu da Mai Martaba yayi babu zabinsa ko ɗaya a cikinmu - duk bashi mu akai. EHSAAS is lucky to have you, ke zabīnshi ce."
Da sauri Islam ta ɗago tana kallonta kafin tace: "But you and Mai Martaba, your..."
Tace: "Our love, ko?" tana ɗan murmushi.
Jinjina kai Islam tai, tace: "That is the reward of what we find da mukai haƙuri, muka rungumi kaddararmu hannu bibbiyu, musamman shi. Saboda ni daman nasan babu yadda zanyi, ko na ki, ko na so, sena zauna da shi. Islam, ni 'yar sarki ce banida zabi kamar ki."
Tausayin Fulani Islam taji tana ji. Tace: "Nasan kishi da zafi, Islam musamman akan abinda kake so. Bansan nima inada kishi ba sai lokacin da aka coronate Mai Martaba. Kuma ranar aka bashi kyautar Hassana. Ni da shi munyi alkawari cewa daga ni ba ƙari. Ban taɓa ɗaukar mai babban daki a matsayin kishiyata ba, saboda nasan zuciyar mijina a hannuna take saboda na yarda da kaina a matsayin mace.
"Amman Hassana alokacin, kowa yasan Hassana na ɗaya daga cikin matan da suka fi kowa kyawun sura da kyawun jiki. A zamanin da aka aura ma Mai Martaba ita, babu budurwar da take tashe kamar ta. Alokacin kamar dai ni a alokacina. Haka kuma inaji, ina gani, babu yadda nayi, aka kawota cikin gidannan. And she's cruel. She's super evil, fiye ma da mai babban daki, saboda ita muguwar fuskarta a waje yake, sabanin Hassana da tai kokarin shiga jikina awancan lokacin. Daga ni har mai babban daki babu wanda take so, saboda ta ga mu mun taɓa haihuwa da Mai Martaba, ita bata taɓa ba. Ta tsani EHSAAS da Mimah sama da komai a rayuwarta. And she tried everything to ruin them, musamman EHSAAS.
Saboda tsoron hakan, na barshi ya tafi Saudiyya gurin dan uwana Abdul Aziz bayan dawowata NURISTAN. Domin ba anan nai rainon cikinsa da haihuwar Saba."
Sauraronta Islam takeyi da alamar maganganunta suna shiga jikinta. Tace: "I am sorry, Islam. Wallahi, I am sorry. I didn't want this to happen like this. I never wanted your heart to be broken. I'm a mother, and I saw what was coming… and I panicked. I acted before you got hurt deeper, saboda nasan EHSAAS ya tsaye musu a wiya. Musamman da yayi rejecting ɗuka yayansu, ya zabeki, kuma mahaifinsa ya goya masa baya. Tabbas wannan lokacin suke jira a cikin majalisar dattawa su naɗashi, su bashi yayansu."
Dan zaro ido Islam tai tana kallon Fulani cike da tsoro.
Fulani ta cigaba: "Islam, I went through hell... wallahi I suffered. Banason ki sha wahala ko da makamanciyar wacca na sha, balle irin ta. Nayi asarar ciki a cikin gidannan sau ba adadi, duk da na fawwalawa Allah dukkan lamarina. Nasan cewa babu yadda za'ai susamu nasarar ciresa inba Allah ne ya ƙaddara hakan ba. Ba kalar binne-binnen tsafin da bana cirewa a ƙasan sashena ba. Suna ɗaukata a matsayin wata barazana agaresu saboda mijina na kaunata.
They used every wicked means to break me.
Tohm, kisani, kwatankwacin kaunar da EHSAAS ke miki, ban samu gurin Mai Martaba ba, saboda shi yana iya boye abinda yake ji akaina. Amman EHSAAS baya iyawa akanki.
Tohm, idan an min irin haka, Islam, inaga ke... nasan duk wacca za'a aurama EHSAAS ba outsider bace - 'yar gidan sarauta ce. Kuma sun fi komai hadari.
Islam, shiyasa na bi shawarar Mai Martaba. Munason musamar muku da farin ciki, ku duka, tun kafin ƙasa ta rufe mana ido."
Islam tagumi tai tana sauraron Fulani, tana jin wani irin tsanar kishiya na ƙaruwa a ranta. Fulani tayi shiru na ɗan lokaci kafin ta ja dogon numfashi ta cigaba...
"A dan zaman da kika yi da Mehtav a gidansu zakisan wacece ita. Nayi bincike mai zurfi, irin binciken da ke kanki ba zaki yi tunanin zan yi shiba. Har ta da lokacin da take kwanciya barci nasani ayanzun. She is not perfect, kuma ba zan ce ki zauna ki ta sakar mata fuska a matsayin ta na wacce EHSAAS zai aura ba. Saboda kina asama da ita har abada a cikin gidannan, kuma nasan idan kika ja girmanki, zata darajaki matuƙa har nan gaba. Islam ta girme miki a shekarun haihuwa, amma kin girme mata a zama a cikin gidannan.
Se abin da kika daurata akai zata yi. In dai kika nuna mata komai ba komai bane yarinyar ba muguwa bace. Nasan waye mahaifinta. Sudin ba mutanen banza bane. Nasan yadda Habib yake da rikon addini. Yarsa kila ko kalmar tsafi bata saniba balle tayi tunanin amfani da shi ta cutar da ke ko yayanki.
Even if she doesn't like you as a co-wife, she will love your children. Kuma that alone is more than I ever had. Daga kallon da naga tana wa Jr nasan cewa tana son yaron, ba don saboda ke ba a'a saboda shi din dan EHSAAS ne. Tana matuƙar son EHSAAS, Islam."
Dan Shiru Islam tai kafin tace: "Maama, shima yana sonta."
Dan murmushi Fulani tai kafin tace: "Nasani. Amma tsoro yake ji. He doesn't want to break your heart. He even told me earlier shi ya fasa zama sarki, in dai har se ya miki kishiya. Islam, he is crazy for you. Ba Mehtav ba - har sarautarsa ya hakura da ita saboda ke. Kuma ba ina faɗa miki hakan saboda ni mahaifiyarsa bace, a'a ina faɗa miki haka a matsayina na mace da ta yi experiencing rayuwa sama da ke, Islam."
Islam ta dago ido, idonta cike da ƙwalla, tana ji kamar zuciyarta na saukowa kadan-kadan.
Fulani ta matsa kusa da Islam, ta rungumo ta zuwa jikinta tana faɗin: "Ban so ki sha wahala irin tawa. Banason ki kasance cikin mata masu tsoron kishiya, kinji? Na yarda dake. Nasan zaki iya, Islam. You're strong. Ki zama cikakkiyar mace. Be the queen you are a zuciyarsa, ta hanyar zama zakaran gwajin dafi a rayuwarsa koda ace yana da wata bayan ke, kinji?
Kisani, na yarda EHSAAS ya auri Mehtav ba don banasonki ba, ina matuƙar kaunarki shiyasa na amince. Saboda bana so wata rana su aura mai wata muguwar macen da zata rabaki da shi sannan ta rabashi da yayanki. Mehtav will never do what my co-wives did. She's not perfect, but she's not wicked. Kiyafemin Islam idan decision ɗin da na ɗauka akan rayuwarki ya bata miki rai, kinji yata?"
Islam ta saki wani irin numfashi mai nauyi, hawaye na bin fuskarta a hankali, muryarta a sanyaye tace: "Maama, ki daina bani haƙuri. Nima ki yafemin. Na ɗauka kin daina sonane. Se EHSAAS da Mehtav kawai. Amma yanzun, na gane duk saboda gobenmu ta zama mai kyau kika yi hakan. And I forgive you. But you must promise me... promise me you won't push me aside. I'll always be your favourite."
Fulani murmushi ta saki, ta shiga goge mata hawayen da ya soma zuba a idanuwanta tana faɗin: "I will never push you aside. You are my daughter too, Islam. Dake da EHSAAS duk ɗaya ne a gurina, kinji? And Mehtav..." Saita ɗan kalli ƙofa kamar ba ta son kowa ya ji, saita ce: "Matso kunnenki kiji." Tana murmushi.
Islam ta bata kunnenta. A hankali ta rada mata: "I'll be a bossy mother-in-law to her. Ke kuma kizo, zan koya miki duk dabarunmu na tsofaffin hannu, wanda zai saka EHSAAS ya ƙara matowa akanki. Classes zamu fara sosai."
Islam jitai tana mugun kunyar Fulani kamar ta nitse, duk da ta san wasa take mata, amma ta mugun jin daɗin abin da tace din. Tana lullube fuska, take faɗin: "Maama, amma ni baruwana da aurensa. Kar ya sake saka ni aciki. Kuma baruwana da ita. Tai harkarta, inyi tawa."
Murmushi Fulani tai, tace: "Kintaba ganina a gefen kishiyata?" Da sauri Islam ta girgiza kai.
Tace: "Tohm, ai haka ake. Kowa yayi sabgarsa. Zaki iya sheƙara ma baki ganta ba."
Islam ta jinjina kai, tana sauke numfashi alamar taji daɗin abin da Fulani tace.
Fulani sosai taji daɗi, domin bata ɗauka convincing yarinyar zai zo cikin sauƙi haka ba. Amma ta lura da rashin wayau da ke tattare da ita, da kuruciya, da kuma rashin guidance na wani babba a tare da ita. Se yanzun take dada jin mutuwar Uwar Soro. Allah ya jikanta rai. Tasan da tana nan, da ita ce zata jata a jikinta ta zame mata uwa a wannan yanayi. Abubuwan da Uwar Soro zata gaya ma Islam da dama, ita bazata iyaba. Saboda takan tuna cewa ita matar EHSAAS ce, saita ji kunya ta lullubeta.
Ga Mimah ,Mimah da suka yi matuƙar yadda da ita, ta zamar wa yarinyar tamkar garkuwa, ashe itama ba rikon tsakani take mata ba. Yanzun tasan ita kaɗai ta rage ma Islam. Su iyayenta ba su san wani abu wai shi kishi ba, saboda ba sa auren mace sama da ɗaya. Don haka tasan ba yadda za'ai mahaifiyar Islam ta zauna tana bata shawarwari akan zama da kishiya.
Don haka dole ita zata daure, tayi ɗin.
Agajiye, Mehtav ta shigo dakinsu da aka sauke su bayan ta dawo daga raka Ahmad har bakin ƙofar motarsa. Ta rakashi tareda roƙonshi da Allah kar ya sake dawowa nan ɗin. Itama ta kusa dawowa Nigeria gani tayi. Yayi murmushi yace mata, "Ko saboda kada saurayinki ya sake yin fushi?" Uhm, daure fuska tayi ta tambayeshi, "Waye saurayina?" Yace, "That fair guy mn. Yana sonki, amma kice mai nafishi sonki kuma in sha Allah sena kasashi, duk da naga kamar faɗa kukai yaritsa dani. Ta shafeni." Murmushi kawai Mehtav tayi, tace mishi, "Seda safe." Yace mata, "Ki kula da kanki."
Harta juya zata tafi sai yace mata, "And pls" Ta juya. Gaban motarsa ya buɗe, ya ciro wani ɗan box, yana miƙa mata. Kin karɓa tayi, sai da ya haɗata da Allah tukunna ta karɓa. Yace mata, "Pls, pls, try and avoid that your saurayi, saboda nima ina kishi. No impact, ba ƙin ciki nake ma. He get to see you here everyday, ni kuma bazan iya ba." Murmushi kawai ta masa kafin tace mai, "Tohm, na gode." sosai yaji daɗin yadda ta masa murmushi wannan karon, saboda sanda ya je gidansu ko haƙoranta be gani ba. Kuma alamu sun nuna cewa tafi tsanar wancan guy ɗin a kanshi, so ya ɗan fara ganin alamun nasara a alakar su.
Sighing tayi deeply tana tuna yadda suka rabu, sai kuma zuciyarta ta soma karkata ga abin da ya faru cikin horse stable ɗin. Kirjinta bugawa ya shigayi tana tuna idon EHSAAS a lokacin. Bata taɓa tunanin she's strong enough to stand before him, ta kare Ahmad ba. Kuma bata yi da na sanin kareshin ba, saboda yadda taganshi ya fusata, zai iya sawa a ci mutuncinsa a palace ɗinnan. Itakuma bata kyauta ba inta bari haka ta faru, ko ba komai ai dan ita ya tako ƙafa ikafa gari igari har ƙasar NURISTAN, in an barshi a ci mutuncinsa, da me zata kira kanta?
EHSAAS ya matuƙar ba ta mamaki, domin bata taɓa sanin he can be this rude ba. Wata zuciya tace mata, "Kila dama haka yake. Don a gidanku yake, shiyasa baya muku rashin mutunci. Nan ai garinsa ne kuma masarautarsa ce, dole ya nuna ma mutane jin kai da isa." Ɗaya zuciyarta ce take ƙoƙarin tono mata abin da take ƙoƙarin birnewa. Ta kasa yarda cewa EHSAAS kishin Ahmad yake, saboda tana ganin reaction ɗinsa da yadda ya maimaita kalmar "fiancé" ɗin da ta faɗa. Tana godewa Allah, tana kuma godewa Aman daya fitar da shi a gurin nan. Da ba haka ba kila rufesu da duka zai yi daga ita har Ahmad ɗin, ga dakaru na zagaye da su, ba me iya kwatar su.
Wata zuciya ke faɗa mata: "Toh dan me yasa EHSAAS zai yi kishinki?" Gaskiya ba kishi bane ba. "Kila he is just overprotective ne." Wata zuciya tace mata: "Why would he be overprotective towards you a matsayin sa na wa?"
Jitai kanta na neman fashewa saboda tunani, daidai lokacin da ta ji an murɗa ƙofa, an shigo. Abeey ce. Sumsum-sum ta shigo ta tsaya a tsakiyar makeken ɗakin, kanta a ƙasa, tana wuri-wuri da ido alamar rashin gaskiya Karara, Mehtav ita rasama abin da za ta ce ma Abeey tayi, don zuwa yanzu rashin jin Abeey ya fara bata tsoro. Yarinya kamar aljana in ta sa kanta a abu, se tayi. Komene za ai mata daga baya, ta yarda ta yi ɗin. Banza tayi mata, sai da ta gaji da tsayuwar ta sannan ta karaso kusa da ita a gefen gadon tana faɗin, "I'm sorry Mehtav. Wallahi bansan handsome prince zai ji haushi haka ba. Bansan abin zai zama faɗa ba. Da ban faɗa mishi inda muke ba, da bansaka a shigo da shi. Yah Mehtav kiyi haƙuri."
Girgiza kai Mehtav tayi. Ta miƙe kawai, ta nufi bakin taga ta tsaya. Abeey tace, "Kiyimin magana yah Mehtav. At least scold me kamar yadda kika saba. Give me proper lecture akan in daina rashin ji mana yah Mehtav."
Mehtav ɗagowa tayi tana faɗin, "Kinsan abin da nake yi koda yaushe ma kenan. Shiyasa kike yadda kike so, saboda ban isa in faɗa miki ki ji ba. Abeey, ba komai. Na gode. Ai kin nuna min ni ban isa dake bane kawai saboda ban haife ki ba. Kuma nima ban ce na haife ki ba"
Abeey kalar tausayi ta soma yi. Ta ƙarasa tana rungume Mehtav da ta ɗauke mata kai. Tace, "Yah Mehtav, pls I'm sorry. Wallahi daga yanzu zan ringa jin maganarki. Na daina rashin ji. And you're like my mommy. Bansan mommy na ba. Ke kaɗai nasani. How can I not listen to you, yah Mehtav pls forgive me."
Shiru tayi bata ce mata kalaba. Kuka Abeey ta fasa kamar ana yankar naman jikinta "Kefa kika ce min mommy ta bar miki wasiyyar ki kula dani, karki ringa min wulakanci, kina shareni. Ai nace na daina. Kuma in ƙarami yay laifi yace a yi haƙuri,ba aikin babba ne yace ya yafe mai."
Dariya tabawa Mehtav. Ta shiga kyalkyalawa, kai ta dungure mata, tace: "You'll never change Abeey. Allah dai ya shiryeki kawai. Amma yau kin bata min rai fa."
Tana goge hawayenta, tana turo baki, take faɗin: "Ai shiyasa nace kiyi haƙuri. Bazan sake ba."
Tace, "Tohm Allah yasa." Tare suka tsaya bakin taga na tsawon lokaci kafin Mehtav ta juyo ta kalli Abeey tana faɗin: "Tell me, Abeey. Wai kinsan dalilin da yasa EHSAAS yayi acting weirdly dazun? Daman shi dan wulakanci ne haka wai bamu sani ba? Ni kam zaman gidan ma ya isheni. Bari Paa ya dawo Allah gida zamu koma."
Abeey murmushi ta shiga yi tana kallon Mehtav irin "you have no clue" ɗinnan kafin tace: "Yah Mehtav, seriously? It's obvious! He's jealous, like, wallahi."
Mehtav tayi shiru. Zuciyarta na son ta gasgata abin da Abeey ta faɗa wanda shi tata zuciyar ke faɗa mata. "Jealous? For real?" Ta tambaya tana son ƙara tabbatarwa. "Why would he be jealous? He's with Islam. He's happily married."
Abeey ta ɗanyi tsaki, ta kalli Mehtav irin "ina ruwanki?" Tace: "Listen, Mehtav. Whether you admit it or not, EHSAAS has feelings for you. He can deny it, he can act all cool, but it's there. He's protective of you, and that's a sign of something more than just friendship or big brother thing. Wai baki ga kallon da ya watsa wa Ahmad bane?"
Mehtav ta ɗan yi shiru, tana jin maganar tana shiga zuciyarta. "But... but why wouldn't he just say something? Why won't he just speak up? Meyasa ba zai ce yana sona ba in haka yake ji, uhm?"
Abeey girgiza kai tayi tana faɗin: "He won't speak up until you make him, saboda yana son matarsa itama. Ba ya son ya bata mata rai. Shiyasa you have to make the first move. And trust me, yana sonki. Ingaya miki gaskiya kenan. So ma sosai kuwa."
"I can't just give in like that, Abeey. If EHSAAS really has feelings for me, he needs to tell me himself. Nawa ne maza masu aure da ke son matansu kuma sunason wasu a waje, amma hakan baya hana su nuna musu soyayya. I'm not gonna make it easy for him. He has to ask for my hand... I won't settle for less. Wallahi kuwa, Abeey, ai banmanta yadda yafito karara yacemin baya sonaba wancan karon"
Abeey kyalkyalewa tayi da dariya tana faɗin: "That's the Mehtav I know. Always strong, always holding her ground.anaso ana kaiwa kasuwa Maza ki ci gaba da holding ground ɗinnan. Za ki ji kida a magwan kuwa!"
Girgiza kai Mehtav ta shiga yi tana faɗin: "I'm not going to give in, Abeey. I need him to be the one to confess. Not anyone else."
It's Fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment & Vote [17/07, 21:03] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.