EHSAAS

Chapter 49

by @fatoumspassion

Cikin ƙasan ƙasa na fadar Nuristan - wato the darkest dungeon of the palace - wani irin huci take yi tana gurnani kamar zakanya, zuciyarta na tafasa jin wani kwaro ya ci kafarta. Yasa tayi sauri kokarin mikewa don ta fara bugeshi, amman me? Tana mikewa, wani irin muguwar kumewa tayi don ta manta cewar ba za ta taba iya tashi tsaye a cikin inda take ba, sai dai zama da tsugunnawa.

Wani irin raɗaɗi ne da ƙunci ya mamaye kirjinta, tana kirga wa da yatsunta tsawon watanni kenan tana cikin wannan wuri mai bala'in sanyi. Ga datti, ga wani irin wari - kamar ba ita ce the great Princess of NURISTAN, Mimah, ba. Jita ke kamar ta shake kanta ta mutu ta huta da wannan zaman bala'in da EHSAAS ya saka ta a ciki.

Amman me? Tasan in ta mutu haka, EHSAAS yake so - saboda kar ya fito ya yi mata hukunci a zageshi ko asirin masarautarsu ya tonu. Shi yasa ya zaɓi ya yi mata irin wannan tozarcin mafi muni - wato ko darajar trial ba ta da shi. Rabo da ta ga rana har ta manta a rayuwarta.

Jinjina kai kawai take yi tana lissafi a cikin zuciyarta, domin a yadda ta kiyasta lokacin kawo mara abinci yayi. Kuma prison warden ɗin da ke kawo mata abinci sau ɗaya tak kullum a rana - ta san dole zai zo mata da wani labari dangane da abin da ke faruwa a cikin fadar.

Ba ta gama kiyasta a cikin ranta ba, ta ji heavy footsteps dinsa yana tahowa ta wajen dungeon ɗin da aka ajiye ta ita kaɗai kamar mayya. Cikeda zakuwa ta karasa bakin ƙaramar tagar da yake miko mata abinci ta gurin - kuma idan an buɗe tagar ne kaɗai take iya dan ganin haske kaɗan.

Masu mahaukatan makullaye ya shiga cirewa, har sai da yayi nasarar buɗe tagar. Ya ziro mata abinci yana gaidata, yana kalle-kalle don ya tabbata ba me ganin shi. Da sauri ta karɓi abincin tana direwa a gefe, ta soma tambayarsa ko akwai wani update.

Sai da ya kalli hagu da dama, ya tabbata ba me zuwa wajen sannan ya fara magana a ɗarare:

"Gimbiyah... akwai wani sabon labari, and you need to know."

Ta ɗago kai, with that cold deadly stare, tace, "Talk, Usman. And make it worth my time."

Usman ya shafa ƙeya, domin duk da tana cikin kasurgumin gurin nan, har lokacin jin ƙanta da isarta ba ta rabu da ita ba.

A hankali ya fara faɗin, "An fara babban renovation a palace... biliyoyin dollars kuma Mai Martaba ya fitar don gudanar da wannan gyaran. Sannan... Prince zai yi aure."

Ɗan waro idanuwanta da suka koma loko, suka yi bakikkirin, suka koma ciki-ciki. Tai jin abinda Usman ɗin yake cewa kamar almara. EHSAAS ɗin ne zai yi aure? Again?

"With who?" Ta tambaya tana kafeshi da ido.

Yace, "Allah ya temakeki. Wata 'yar Najeriya ce. Na ji an ce ita ce ta ceci ransa lokacin da ya ɓace dinnan."

Zuciyarta ta buga, ta shiga harbawa da ƙarfi da ƙarfi. Tana jin koma wacece, 'yar iskar yarinyar da ta ceci rayuwar EHSAAS dinnan - itama ta shiga cikin lissafinta. Domin da ba dan tace ce shi ba, da tuni yanzu tana nan tana cin karenta babu babbaka. Domin tasan EHSAAS ba zai taba surviving ba.

Amma a fili, sai ta tambayi Usman:

"Wai kana nufin da amincewar Mai Martaba duk za a yi waɗannan abubuwan? Shi da ba shi da lafiya, har yana da ƙarfin zartar da wannan hukuncin?"

Usman a ɗarare yake faɗa mata, "Mai Martaba fa jikinsa yana ta kyau alhamdulillah. Kuma yanzu yana fitowa kaɗan, ba kamar da ba."

Wani irin bacin rai ta tsinci kanta a ciki kenan. Mai Martaba sarai ya fara samun sauƙi, amma ko bi takanta ba ya taba yi ba. Ko irin yace a kawo masa ita ya gani, dinnan ma bai yi ba - tana matsayin 'yarsa, jininsa. Ko dai ya riga ya yarda da maganar Kawu Erfan ne, cewar ita ɗin ba 'yarsa ba ce?

Wani irin zafafan hawaye ne masu ɗumi da zafi suka shiga zirya a cikin zuciyarta. Tana tuno rayuwarta da mahaifinta kafin a haifi EHSAAS - ita ce komai nashi, ita ce duniyarsa. Amma EHSAAS ya zo ya kwace komai, har da identity ɗinta ya kwace.

Tasan sarai Mai Martaba mutum ne mai adalci - he would've called for a fair trial. Tasan EHSAAS ne ke zugashi, yana juyashi. Shi yasa dukkansu suka yi moving on, shirye-shiryen biki ma suke, sun manta da ita kamar ba ta taɓa zama part of them ba.

It seems like he's fully supporting EHSAAS.

Wanda ba ya san hakan babban kuskure ne ba. Saboda rayuwata ba zan taɓa bari ta kare anan a banza ba," ta ƙarasa a fili, wannan karon tana kallon Usman.

Tace, "Se kuma menene ya kamata in sani?"

Usman ƙasa-ƙasa ya soma mata bayani.

"Kuɗin da za a kashe wajen wannan renovation da bikin ba ƙananun kuɗi ba ne. Kuɗi ne - mazaajen kuɗi ne. But it's all going into the bride's family's pocket, saboda mahaifin amaryar shi ne aka bawa kwangilar aikin."

Bushewa da dariya tayi cikeda tsana. Tace, "Ainasani, in kaga tsohon nan ya fito da kuɗi tohm magana ce ta abinda ya shafi EHSAAS. Anan komai nashi zai kare. Da alama matsiyata ne dangin yarinyar da zai aura. Shi yasa ya yi musu haka don ya farfaɗo da su. Hmmm… I don't even know yarinyar nan da zai aura, but I despise her already. She's the reason EHSAAS came back powerful. If only she had let him die..."

Ta ƙarasa cikeda takaici, tana wata muguwar ƙwafa.

Usman a hankali yace, "Ranki ya daɗe, wannan shine iyakacin abinda ke faruwa a fadar yanzu haka."

Ɗan motsawa tayi, ta ƙarasa daf da tagar tana kallon Usman. Sarkokin da aka daureta da su na ƙara karan ƙulli.

Tace, "This is our chance. The palace will be busy. Amma kafin komai - stalk Princess Islam. By fire by force, I want her watched."

"Princess Islam?" Ya faɗa atsorace, yana ran kalle-kalle.

Tace, "Yes, ita! She's his weakness. I'll make her suffer. I want to see her cry. In fact, I want her child. If I can't get out through justice - I will burn the palace emotionally. I'll take everything that makes EHSAAS happy."

Usman ya tsaya cak, yana kallonta. Tace da muguwar dariya, "Don't worry, I'm not asking you to touch her... I just want information, inda take, me take yi. I need full details." Sai Usman yace da girmamawa, "Zan kokarta... amma wannan aikin yana da wuya ta gaske." Aika masa da wani irin kallo mai cike da barazana tai tana fadin, "Ka manta da cewa har yanzu yayanka suna karkashin ikon yaran a Persia ko? Ka ƙi taimakona, kuma zan sa a lalata rayuwar ka da tasu gaba ɗaya." Cikeda rauni yake fadin, "To Gimbiyah, ki gaya min yadda kike son ayi."

Mimah ta gyara zama, ta sauke ajiyar zuciya. "Nasan al'adar masarautar nan sosai don haka ka saurareni kaji dakyau. Lokacin bikin, za a shigo da kaya da yawa daga warehouse na waje - katifu, riguna, flowers da sauran su. Daga storage shed din bayan gidan yari, mu kuma za mu jefa ƙananan tayoyi guda biyu da za a kunna a lokacin da palace ta cika tai makil. Idan suka fara ci, hayaki zai fara tashi, wanda zai sa guards su raba kansu zuwa wurare daban-daban."

"Ke kuma fa?" Usman ya tambaya. "Zaka shigo da kayan tsafta da aka saba kawowa wanda kake gote wajen can da su. Cikin su zaka boye ƙananan tools. I'll break the first two locks da kaina. Daga nan, zaka shigo da fake ID naka kamar ka dawo daga cleaning assignment daga sashen bak'i. You'll unlock the final exit gate."

"Wani gate ne?" ya tambaya. "Gate na underground path da ke kusa da royal garden. Babu wanda ke amfani da shi tunda aka kulle shi shekaru aru-aru da suka wuce. I already paid someone years ago to leave a second route open through the drainage panel bayan wacca Mai Martaba yasa aka rufe kwanaki. Akwai wata."

Usman yayi shiru yana kallonta cikeda shakku. Ta cigaba: "Zan fita, and I want to see Erfan first." "Erfan? Me zaki masa?" Usman ya tambaya.

Straight tace masa: "Kasheshi zanyi."

Usman ya bude baki da mamaki. "Kawunki ne fa!" Cikeda bala'i tace, "Ko ubanane, sena kasheshi xanji dadi. He betrayed me. He handed my secrets to EHSAAS. Because of him, I lost everything."

"Prepare," tace. "Ina bukatar kayan sanyi, ID badge, da map na sabon layout din gidan. I have two weeks. After that, EHSAAS will regret ever putting me here."

Usman ya sunkuya. "Na gane, Gimbiyah. Komai yadda kika ce, haka za'ayi."

Se a lokacin ta samu damar ɗaukar abincin ta shiga turawa a bakinta tana tsinema EHSAAS da duka iyayen da suka haifeshi - ita kadai.

Tana zaune saman doguwar kujerar bedroom ɗinsu tana karatun Qur'ani cikin zazzakar ƙira'ar da ta koya daga gare shi take karantawa a bayyane. Sarai taji buɗewar ƙofar ɗakin da shigowarsa tare da yadda kamshin turarensa yake dada tunkarota, amma ta cigaba da karatunta kamar ma ba ta san da mutum a gurin ba.

A gefenta taji ya zauna, ya daura kansa a kafadarta. Ba ta ce masa komai ba. A hankali ya lumshe ido ya soma bin bakinta suka fara karantawa a tare. In ka gansu, gwanin ban sha'awa, cikin zazzaƙar ƙira'a irin ta Larabawa.

Har sai da Islam ta karaso kan izifin da za ta tsaya, tukunna ta tsaya, ta karanta addu'o'inta a cikin zuciyarta, kafin ta rufe Al-Qur'anin ta daura shi gefen inda take ajiye shi.

Idonsa a lumshe yake, duk da motsin da ta yi ba ya hana sa mikewa daga jikinta ba. Ta yi tsit kawai, itama ta lumshe ido ba tare da ta ce mai kala ba. Sun kai minti goma a haka, sannan ya dago a hankali, ya mike, ya karasa wurin gadon Jr ya leƙa shi. Ganin barci yake sosai yasa ya dawo gefenta yana tambayarta, "Baby, ba ta tashi ba kenan?"

Kala ba ta ce masa ba har ya dawo ya kwanta a jikinta. Wannan karon saman cinyarta ya daura kansa yana kallonta. Sai a lokacin ta sauke gwara gwaran idanuwanta a kansa. Shi kansa ya san kalar kallon tuhumar da take masa. Gently yayi burying face ɗinsa a saman flat tummy ɗinta, ciki ciki taji yace, "I'm sorry baby please kiyi hakuri. I didn't come back saboda raina a bace yake kuma nasan kema ranki babu daɗi after what I did in the morning. Shiyasa ban shigo nan ba. Kiyi hakuri kinji baby please."

Ya dago yana kallonta. Numfashi yaga ta ja kafin tace masa, "Ina ka kwana?" Babu wasa a cikin muryarta tana tsareshi da ido. Kalar tausayi yayi da fuskarsa kafin yace, "At my old side, baby." Jinjina kai tayi kafin tace, "An bata maka rai a waje, sai kace deciding I'll get punished for that. Is that fair, Sire?"

Da sauri ya mike yana ɗan jawota jikinsa cikin rarrashi yake fadin, "Wllh nima ban tsammanin bacin ran zai daɗe haka a cikin zuciyata da har zan kasa tunkarar ki, baby. Kinsan inada zuciya, in raina ya baci kuma kema kinada shi sosai. So shiyasa ban shigo ba, don kada a zo a samu matsala. Na bari sai da na sako tukunna baby sannan nazo."

Shanye ƙwallar da ke ƙoƙarin zubo mata ido tayi, tana kau da kanta daga kallonsa. Ciki ciki take fadin, "Jiya jiya ka gama cemin ba zaka iya barci in ba a gefe na ba, amma ka tafi ka barni ni ni kaɗai. I was sick and worried har sai da na kira Aman ya tabbata min da kana cikin palace ɗinnan, sannan hankalina ya ɗan kwanta."

"Billah baby ba barci na yi ba. Kinsan cewa gaskiya ne I can't sleep without you by my side. Jiya ba mani da nutsuwar yin barcin kwata-kwata, raina a bace yake."

Tace, "Sire, don Mehtav ta bata maka rai baya nufin zaka ringa venting ɗinsa a kaina. This should be the first and the last time zaka samu issue da ita ka kwana a waje."

"I promise hakan ba zata sake faruwa ba in sha Allah. Kinji baby? Kuma wani munafuki ne ma ya fada miki ita ta bata min rai? Uhm baby kidena jin maganganun jama'a fa."

Daga mai gira ɗaya tayi irin "ya ma gama raina mata hankali" nan a fusace ta mike tana fadin, "Ni ban san sanda ka koyi boye min abu ba. A haka zaka yi aure kana hiding things from me kamar wasu strangers? Sire, ni ce fa peace ɗinka. Look at me. What changed between us? Ko dan zuciyarka ta fara bugawa for someone else shiyasa kake yin haka eh?" ta faɗa tana riƙe kugu.

At this point ya san ta gama fusata kuma tayi mugun jin haushin kin dawowarsa gida. Kuma tabbas ya san ta san komai da ya faru a stable. Don haka gwarama ya fito fili ya faɗa mata don in ta fashe ba zai iya tarota ba.

"I'm sorry," ya faɗa yana rafka uban tagumi kamar yaro mai laifi a gaban babarsa. Kasa kallon idonta yayi. Ciki ciki yace mata, "I was just got carried away by jealousy, Pipi. Kinsan I can manage my temper sosai, amma that girl triggered me. Wai imagine kina ganin ta kawo wani kato har cikin gidan nan, wao, take kallon idona tana cemin wai fiancé ɗinta ne."

"Pipi I felt disrespected. Bayan ta san jiya jiya Mai Martaba ya mata proposing aurena. In ba ta sona ba sai ta faɗa straight, ba don me yasa zata kawo mana cin fuska ta wannan hanyar?"

Dogon numfashi Islam ta ja tana hadiye wani irin abu da ya caka mata a wuya. Ta zauna a gefensa tana kallon yadda yake mata bayani cikeda tsagwaran kishin Mehtav da take gani a idanuwansa. Irin abin da ta ke gani a idonsa ne duk sanda wani namiji ya zo kusa da ita.

"Pipi, kin yi shiru ba ki ce komai ba," ya ƙara da cewa yana kallonta.

Rintse ido ta yi kafin tace, "Toh kai meye naka don ta kawo namiji as her fiancé? Ba da zunnan kake fadamin ba kasonta ba? Biyayya zaka ma Mai Martaba? I think Mehtav has every right ta kawo wanda take so. That'll make it easier for you and her."

Ba ta bude baki ta fadi ba, her actions shows that. Ta karasa tana kallon shi kasa-kasa in "I don't care" manner. Gyara zama taga yayi kafin yace mata, "Wai da gaske kike zata iya dena sona? Am I someone irin da mace zata yi saurin mantawa haka?"

Bude baki tai tana kallonsa kafin tace, "Aiba ita ta fara mantawa da kai ba, kaine kai pushing dinta away. So why not? Ko nice Mehtav, abinda zanyi kenan." Ta karasa tana fidgeting fingers dinta, trying hard to act strong kamar yadda Fulani tace wai ita ce suke magana da sire akan wata, haka tana ganin yadda ya bada attention dinshi gaba daya. Yake on edge kawai ya samu mafita, yaji opinion dinta akan maganar.

"Pipi, ni fa banyi pushing dinta away saboda wani abu ba. Kinsan bana son bacin ranki, kuma tunda kika nuna min baki so, na bari. Shiyasa ita kuma gani tayi kamar kawai mantawa da ita nai ko wulakanta ta nai. Ni kaina nasan ban kyauta ba, ko ba komai ita din life saviour dinta ce, koh?" Ya karasa fada yana komawa saman jikinta. Don haka yake da shegen son jiki kamar mage.

Rintse ido Islam tayi kafin tace, "Ni ina ruwana tsakaninku? Na fahimce ku duka sosai, kuma in Allah ya kaddara da aure tsakaninku ban isa in hana ba, saboda ba haramun bane. But it still hurts. Amman zan daure. I'll try." Ta karasa tana wani irin murmushi wanda ake kira "yake"-yafi kuka ciwo.

Kallon ta yayi yana fadin, "Baby, kin ji me kike fada kuwa? Ko dai kunnena ne suke ji min ba daidai ba?"

Da dan murmushin yake, ta cigaba da yi tana rintse ido, ta jinjina mishi kai tana cizon lebenta, alamun maganar da zata fada karya take ba har cikin zuciyarta ba.

"Na amince, babu komai. Allah ya baku zaman lafiya, Sire."

Duk yadda yaso ya boye farin cikinsa, kasawa yayi. Wata irin wawura yayi mata, ta fada saman jikinshi. Ya shiga kissing dinta tako ina, yana fada mata "I love you," tun tana murmushin yake har sai da ta saki masa kuka. Haka ya ringa lallashinta, yana fada mata kalamai masu dadi tare da alkawurruka iri-iri, nacewar zeyo adalci a tsakaninsu kuma she will forever be the most special woman a rayuwarsa. Tsakanin mata da miji se Allah-musamman maza irin su EHSAAS da suka san duk wani lungu da sako na sarrafa mace.

Haka Islam ta sakar masa jiki, kalamansa na ratsata har ya dau wani layin karatu, tun tana basarwa har sai da ta zagé, ta shiga maida masa da martani. Suka kaure da zazzafar romance a tsakaninsu. EHSAAS ya kusa kaiwa cloud 7, daidai lokacin da suka jiyo kukan Jr alamar ya tashi. Ture kanshi ta shiga yi daga jikinta tana fadin, "My baby is awake," tana mai dariya.

Shima dariyar ya shiga yi yana turo mata lips dinsu da suka yi jajir saboda tsabar be barsu sun huta ba. Ya shanye mata ido seductively, yake cewa, "Your big baby will be waiting, Mommy."

Mikewa tayi tana zira t-shirt dinsa daya cire, data kawo mata, har gwiwa a naked body dinta. Ta jefa masa pants dinsa tana daga masa two middle fingers. Ya mike da gudu, ya bita. Ta dauko Jr tana murmushi. Ya cafkota daga ita har shi, ya hada a kirjinsa, ya rungume yana feeling like he is the most happiest man ever with this woman by his side.

Tare suka shiga, suka yima Jr wanka. Kafin nan su fito, ya rike mata shi, itama ta shiga tayi, ta fito lokacin ya gama shiryasa tsaf. Sannan ta karbe shi, ta fara lallabashi, domin ta san yana sha kua se barci. Amman me? Har EHSAAS ya fito, bai yi barci ba. Yanata wasan sa.

Tana kan shiryawa, EHSAAS karasowa yayi, ya zo gefen kunnanta yana fadin, "Wai ba zeyi barcin ba ne?" Yana nuna mata Jr cikin rada kamar wanda yake tsoron ya jisu.

"He can hear you," ta fada tana dariya, ganin yadda Jr ya tsaya da wasan nashi yana kallon su duka biyun kamar yana jinsu. Dariya EHSAAS yayi yana daukarsa da bathrobe a jikinsa. Yake fadin, "Little EHSAAS wai ba zaka bar Mommy tayi time din Daddy bane? Kaifa tun jiya kana manne a jikinta. Haba abokina, kayi hakuri, kai barci mana in dan samu nima a kwantar min da hankali na."

Jr kamar yasan me yake cewa, ya shiga jan kunnansa yana wasa da su. Tsabar sharri, EHSAAS ya fasa kara, "Wai washhh ahhhh! Yanzu don na ma nemi alfarmar ka bar min Mommy kake cin zalina?"

Dariya Islam take yi. Ta karasa, ta nada veil dinta tana fadin, "Ka dai karage sharri, Sire. Ba dole ya ja ma kunne ba. Ka dauke shi, kasan fa tun da ya fara rarrafe, ya tsani ya ga an dauke shi. Yafi son a bar shi ya yita zagayawa shi shi kadai, baya gajiya." Ta karasa tana jan 'yan kafafuwansa, ya kyalkyale da dariya yana shafa fuskarta.

EHSAAS yace, "Jr fa, nunamin kabilanci yake yi tun kafin ya girma. Yafi miki dariya akaina fa. Na gano shi." Ya karasa yana wa Jr hararar wasa, da yasa shima ya masa dariyar. Islam ta nuna shi tana fadin, "You see? He can hear. Kana ma sharri."

Ya tura mata aniyarta, ta karasa tana gyara gaban madubi. Sauke shi EHSAAS yayi, ya cigaba da rarrafansa. Ya karasa yana rungumota ta baya. Cikin rada yake tambayarta, "Ina zamuje ne? Naga kina ta shiri, my Pipi."

Murmushi tayi tana fadin, "Gurin Maama nake son zuwa. In gaisheta."

"Baby, wai ba kya gajiya da zuwa gurin Maama dinnan? Kullum fa se kin je. Inace fushi kike da ita har... kun shirya ne?"

Turarenta ta shiga feshewa a jikinta da nasa tana dariya take fadin, "Tsakanin ya da uwa, ina ruwan bare aciki? Tohm mun shirya."

Murmushi yay, kanshi a habarta yake fadin, "Da inason ki rakani wani gurine, kinga amma bansani ba ko zakije…" yakarasa yana dan kasa da kai alamar baida gaskiya.

Dagowa tao tana kallonshi tace, "Ina?" "Baby manta kawai, I'll handle it myself." "Tell me," ta fada tana riko kafadunshi, sounding very curious.

Yace, "Daman gurin Mehtav nake son ki rakani muje."

Juyawa yaga tayi, ta cigaba da gyara gaban mirror. Ciki ciki yaji tace, "Danine nake rakaka, katafi abinka. Ni I have somewhere to be."

"Nasani, daman nasan ba lallai ki amince ba baby. The thing is she's just angry, tayi fushi sosai tun da tazo palace dinnan. Maganar kirki ba ta taba hadamu ba, and shekaran jiya da naje haka fa ta ajjeni. I waited for 4 hours, she refused to come out."

Dagowa tai tana kallon yadda yake maganar cikeda jin haushi. Girgiza kai kawai tai domin ta gama gane yamutu akan Mehtav. If not, Sire will never give a damn about this kind of things.

Tace, "The whole prince ta shanye? No no no, Mehtav bata kyauta ba gaskiya." Ta karasa tana jan cheeks dinshi tace, "Sorry on her behalf," cikeda tsokana.

"Baby bayanta zaki goyama kenan?" yakarasa yana dan bata rai.

Tace, "Ai kasan bazan goyi bayanta ba. Ina bayanka. Ni da kai mun fi kusa yanzun. Me kakeso ayi, your majesty?"

Girgiza kai yay yana fadin, "Kibarshi kawai baby, nasan ba lallai ki yarda ba."

Tace, "I'm listening."

Dan kamota yay jikinsa yana fadin, "Idan mukaje tare, se ki aika a kirawo maki ita. In taji kece, ai zata fito. Kinsan it's not cool ince maids da kaina tazo in jiki bayan sunsan nine nazo ba ke ba. Zasu fara yada abubuwa marasa dadi. Kinsan halin gidan nan dai, base na fada miki ba."

Jinjina kai Islam tai tana kokarin hadiye duk wani irin tafasasshen kishin da yake tasowa a kirjinta. Saboda tasan baida abokai. She has always been his best friend. Tasan ba zai taba iya irin hirar nan da kowa ba, koda Aman kuwa. Se dai ita. Kuma shakuwarsu da yarda da ita dayane ya jawo haka. Amma it's truly hurting her yadda taga ya damj da Mehtav har haka.

"Zaki rakani?" ya tambaya yana lekarta.

Jinjina mishi kai tai kafin tace, "Amma kasan bazan taba maka campaign tasoka ba ko? Because you're still my husband."

Jinjina kai yay yana fadin, "Na yarda. Na yarda kawai, bring her out. Nasan abinda zance mata baby."

Jinjina kai tai tana fadin, "Oyah oga get ready."

Ta durkusa tana daukar Jr da taga ya fara kokarin shige wa wani section na walk-in closet dinsu. Tana kallonsa ta gefe da ido, yana ta ruwan ido kayan da ze saka, kuma tasan don yaburge Mehtav yay.

Ganin bazata iya jurewa ba tace, "Baby ina dan zuwa. Get ready. Zanyi feeding dinsa kafin ka gama."

Jinjina mata kai yay yana cigaba da abinda yakeyi. Ta fice zuwa dakin.

Jr na kafadarta saboda tasan ba yajin yunwa. Bata jima da gama bashi ba. Addu'a kawai ta shiga yi a zuciyarta, tana rokon Allah ya bata karfin gwiwar jurewa. Allah karya daura mata abinda bazata iya jurewa ba har abada.

Bata wani jima ba taji nauyin Jr ya karu alamar yayi barci. EHSAAS ya fito cikin wasu kalar grey colour royal kaftan da suka yi matukar amsar gina nan jikinsa. Yana tambayarta, "Yadai? Yayi kyau?"

Jinjina mishi kai tai tana fadin, "💯 Sire."

Murmushi taga yayi yana gyara brooch din gefen aljihunshi. Ya kama hannayenta yana karbar Jr a hannayenta. Suka fito. A bangaren Fulani zasuyi breakfast, shiyasa basu wani tsaya kula wanda aka shirya musu anan ba.

Can suka fara zuwa, suka ajiye mata Jr, suka gaisheta kafin suyi breakfast din sama-sama. Islam tace mata zata raka EHSAAS wani guri, amma yanzun zata dawo.

Sosai Fulani tai farin cikin ganinsu a hakan. Kamar da, ta musu "Allah ya kiyaye hanya," har suma bace daga ganinta.

Sashen su Mehtav suka wuce. Akai musu iso zuwa babban falon kamar yadda EHSAAS ya tsara. Suna zama, Islam ce ta bawa maid umarnin a ce Mehtav tazo.

Amsawa tao tana nufar hanyar wajen dakunan su Mehtav.

Islam kallon EHSAAS tai tana mikewa, ta dan yi murmushi tace, "Mission accomplished, Sire. Bari na wuce, Maama na jiran na," Kamo hannayenta yay, cikin marairaicewa yake fadin, "Kinsan tanada taurin kai. What if she doesn't forgive me?" Dan waro ido Islam tai tana fadin, "Itaku wannan? Nika kyaleni. Zan wuce. Don't expect me inzama middle woman tsakanin kai da budurwarka." "Baby pls, ki tsaya mana," ya karasa yana jawota, ta fado jikinsa. A kunne yake rada mata, "I'm sorry kinji. Banson kiyi feeling bad ne, shiyasa nakeso ai komai a gabanki. Pls baby, kinsan inasonki koh? Sosai." Yadda yake mata magana kunnensa na taba ainahin fatar ta, ya fara sending chills a jikinta. Kokarin mikewa takeyi, ya riketa gam-gam yana tattareta saman kirjinsa. "Pls," ya karasa yana kai lips dinshi kan nata. Bottom lip dinta ya fara chafkewa saboda wani irin kamshi da yaji yana fita daga bakin nata sanda take huci. It's very tempting. Ya kasa controlling, ya shiga kissing dinta gently. Tana kokarin toreshi amma ta kasa saboda karfinsu ba daya.

"Aby!" suka ji ya fadi kasa. Da sauri Islam ta tureshi ajikinta tana kokarin gyara gyalenta. Idonta ya sauka akan Mehtav dake tsaye bata karaso gunsu ba. Wani irin murmushi taga Mehtav ta saki, ta dan bude bakinta kamar zatai magana, se kuma ta kara murmushi tana fadin, "I'm sorry I walk in on you. I must've interrupted you guys at the wrong time," ta karasa tana tsugunnawa ta dauki box din da ta jefar batareda tasani ba saboda shock din da ta shiga sanda taga su a haka. Ba karamar jarumta ta aro ba take wannan maganar da murmushi.

Da sauri Islam ta tashi tana kallon EHSAAS cikeda takaici irin "kaga abinda ka jawo." Ko Mehtav tajuya da sauri zata koma, Islam ta tareta tana fadin, "Pls Mehtav, I'm sorry you meet us like this. I mean… ahm… this way..." Se kuma ta kasa karasawa. "Sire is here for you," ta karasa tana kallonshi, "Come Sire, kana son magana da ita ko?" Jinjina kai yay yana bin Mehtav da wani dan iskan kallo wanda ita kadai tasan me yake nufi. Mehtav ta kallesh, se ta maida kanta ga Islam tanajin kunyarta. Tasan how hard it is kina mace, kikawo mijinki yay magana da wata, shiyasa ta kasa watsa mata kasa a ido.

Tace, "EHSAAS, inajinka," tana tsaye a gurin da take. Islam dan kallonta tai kafin tace, "Pls sit." Kallon Islam tai kamar ba zata zauna ba, se kuma ta samu guri can gefe ta zauna.

Islam ta kau da dakanta daga irin zautaccen kallon da taga yana aika ma Mehtav, saboda ita kanta taga shigar da Mehtav dinta tayi yau ya matukar burgeta. Normal native bubune ne da yaji wani irin beadworks me walwali.

Da sauri tace, "See you later Sire," tana daga mishi hannu. Da sauri ya mike, daidai tana kaiwa bakin kofa zata fice, ya kamo hannunta, yay kissing forehead dinta yana fadin, "See you baby, I love you."

Bata bashi amsa ba, tai saurin ficewa, kirjinta na wani irin nauyi kamar zefashe. Ganin maids a gurin ya sanya tai composing nutsuwarta har ta karasa gaban mota. Dayake da driver suka fito, shine ya jata har zuwa sashen Fulani. Tana karasawa a can daki gurin Fulani taci kukanta, tagode Allah. Fulani nata rarrashin ta tana yaba mata fa namijin kokarin da take da kuma bata shawarwari akan ta cigaba da bashi listening ears. Namiji ne shi, ze gama rawar kai akan auren zata gani. Itadai ta zuba mai ido kawai ta cigaba da addu'a.

Daga bangaren su Mehtav kuwa, duk yadda taso ta nunawa EHSAAS abinda taga yana yi da matarsa be dameta ba, kasawa tai. Don sarai ta gane zuwa yay takanas, ya rama abinda tamai tare da Ahmad. Islam na fita, taga ya kulle kofar falon. Instead of ya koma gurin kujerar da yake, yazauna se taga ya dawo saman kujerar da take zaune. Ta hade rai tana matsawa daga kusa dashi kamar taga dodo yazo inda take.

Shiru taga yayi mata, ya jawo waya yashiga dannawa kamar ba san da mutum a gurin ba. Yanzu ne take fahimtar ainahin halayyar EHSAAS. Yana mugun ji da kansa. Ta dauka dacan lalura ce take sashi yin haka, ashe halinsa ne haka. Musamman ma da ya gane cewa tana mugun sonshi. Haka ta dauka a ranta shine yasa yake dada jin kanshi, haka yake tunanin ze yi mata duk abinda yaga dama a sanda yakeso. But she will show him cewa darajarta yawuce haka. Ba prince ba ko sarki ne shi. Se ta gyara masa zama.

Ganin sun fi minti biyar a haka yasa ta mike a fusace zata koma ciki. Taku daya tak taji kakkausar muryarsa tana fadin, "Don't you dare walk out on me." Juyowa tai tana kallonsa, har lokacin yana danna wayarsa kamar ba shine yay maganar ba. Tace, "Excuse me?"

Cikeda mamakin abinda yace mata, karasa danna wayarsa yay, ya kashe. Taga ya ajiye gefen kujera yana kallonta da shegun grey eyes din nan nasa masu dagula mata lissafi. Ya nuna mata gefen sa yana fadin, "Sit."

Kallonshi tai irin kallon sama da kasa sannan tace, "Okay paa," tana juyawa zatai tafiyarta. Ya fizgota, taji yayi taku daya, ya janyota, ta zauna a gefen nasa kamar yadda ya bukata.

"Leave me alone EHSAAS, meye haka ne kakeyi? Are you insane? Kai din muharrami ne da zakake tabani haka? Ko bakasan bakyauba eh?" Tafara masifa, idonta a rufe kamar za a kunnata.

Fizgotan yasake yo. Ganin tabatan ne bata son ayi yasa ya kara matso da ita daf da shi, jikinsa na gogar nata. Tashiga tureshi tana fadin, "Kasakeni! Ko ance maka ni banida kunya? Ni ba yar iska bace ba da zaka maidani kwandon shararka. How dare you touch me?"

Kallon full lips dinta yake with full admiration. Yasa babban dan yatsansa yana gogar pure pink wet lipstick din da ta shafa akai. A tsorace ta bude idonta tana kallonsa, jin yadda jikinta ke vibrating. She hate herself for reacting this way to his touch. Just one touch ya gama dagula mata lissafi.

Fashewa da kuka tai tana fadin, "Nika sakeni wllh, kasan bakyau."

Jin baice mata komaiba, ta sake dagowa, suka hada ido. Murmushi taga yana yi. Yace, "Ni inaso kuma ni dan iskane. And you just walk on me doing iskanci right? Nagane fa, duk borennan da kike yi, kishine. Just accept it, kiyi hakuri kinji? I'll give you the same in andaura. Wait a little bit lil sis," ya karasa yana goge sauran lipstick din nata. Yace, "Mafadaciya kawai. Kingama fushi?"

Girgiza kai tashiga yi. Gaba daya haushin kanta da shi take ji. Tace, "Kasakeni! Kasakeni nace! Ni waye ce maka ma nadamu dakai da har zanyi kishinka? Namanta dakai kamar yadda kace. Kuma nasamu wanda yake sona."

Hannayenta yasaki, yana daga hannayensa duk biyun in surrender. Yake fadin, "Nadena tunda bakiso. You know how much I respect you ko? But you trigger me Mehtav. Banason in ringa jin kina maganar kinsamu wani ennan. Raina baci yake. Kibari."

Da mamaki take kallonsa, "Trigger you? Like how?"

"Bakaine kace insamu waniba, ko kana tunanin I'll spend my whole life waiting for you?"

Ta tsinci kanta da tambayarsa tana kallonshi. "How could you even look at my eyes, ki bude baki ki kalli wani ki kira shi da fiancé dinki? Is that fair? And about what I said, that was before."

Tace, "Fair?" tana mai kallon mamaki kafin ta girgiza kai. "You don't even know what you're saying, EHSAAS." Tamike zata tafi.

Gabanta ya sha, yana fadin, "Please listen to me, my sweet yah Mehtav. I know ni din mai laifi ne agareki, amma kiyi hakuri. Laifin zuciyata ne da ta kasa gane abinda take so akan lokaci, se da takusa rasawa."

"You know how much you mean to me ko?" Girgiza masa kai tashiga yi tana fadin, "No, I don't."

Idanuwansa ya zuba akanta, yaga yadda hawaye ya kwanta saman kyawawan bakaken eyelashes dinta ya jikasu, da yadda farar fuskarta ta soma yin ja saboda bacin rai da hawaye. She looks super cute and adorable kamar wata yar karamar baby.

Cizon lips ɗin shi yayi na ƙasa, sannan yace, "Kinsan dai ni me aurene koh? Inada iyali, dole alakata dake bazata zama normal alaka kamar yadda muke a da can ba. Mehtav, I admit I pushed you away lokacin bansan menake ji akanki ba - but not anymore, Mehtav."

Shiru tayi, zuciyarta na yin wani irin sanyi kamar an sauke mata wani mahaukacin nauyi daga kai. Jin tayi tsit yasanya yace:

"Mehtav..."

A hankali ta dago idanuwanta da suka yi jajir tana kallon cikin nasa idon. A hankali kamar mai rada yake cemata: "I'm sorry... I'm so sorry."

Hawayene suka cika idonta. Taf! Zuciyarta na ƙoƙarin karɓar duk wani sakon da yake tura mata ta cikin idanunsa. A hankali, wannan karon tana kallon ƙasa tace:

"Why now, EHSAAS? Ka daina playing da heart dina. I'm not a toy."

Matsowa yayi kusa da ita sosai yana cemata, "I know. Kuma that's why I want to do it right this time. Marry me, Mehtav."

Kasa dagowa tayi, ta kalleshi. Yaci gaba: "Na jima da gane cewa I love you, Mehtav. But love alone isn't enough. That's why I'm asking you… not just to love me back, but to help me become the kind of man that deserves you."

Dogon numfashi ta ja, wasu irin hawaye masu sanyi na fitowa daga idonta saboda kalmomi ne da ta dade tana mafarkin jinsu daga gurinsa bata samu jin su ba se ya yi din.

Ganin tayi shiru, yace, "Say something, Mehtav."

"What about Islam?" ta tambaye shi, muryarta a raunane saboda tasan kalar tsananin son da suke ma juna, kuma tana ganin hakan a cikin idanuwan su duka biyun.

"Mehtav, I'm not here to lie to you. I love Islam too. Too much sef, saboda kinsan she's my first and my wife. She's kind, she's patient, she's been my rock in many hidden storms. I'm not perfect… kuma ba zan taba ce miki zan iya raba kaina daidai ba, because I'm human. But I want you to know cewa Islam is very special. She loves me and I love her too... just like I love you."

"But you love her more," cewar Mehtav tana kauda kanta gefe guda kamar wacce ta tafi dogon tunani.

Yace, "I promise I will love both of you differently but completely. Please… ki taimaka min. Don't make this war. Ki bani daman zama miji nagari gareku duka. I want to be the man you're proud of... the man da both you and Islam zaku yi alfahari da."

"I can get very possessive at times. I'm not as good as your wife Islam. Bazan taba iya rakaka zance gurin wata ba."

Dan murmushi yayi, yana dage mata gira ɗaya, irin "Ko dinnan?"

Sannan yace, "Itama dan kece in wata ce bazata yarda ta rakani ba. Tana sonki ne."

Dan ɗagowa Mehtav tayi tana kallonshi akaikaice, irin bata yarda nannan ba. Komawa yayi ya zauna a gefenta, yayi relaxing kari, sannan yace:

"I'm not asking you to be best friends. Amma ki girmama ta. Because she's part of me too. And if I ever deserve your love… it should be the kind that doesn't destroy what's already built."

Jitai kalamansa na sukar ta - kamar ma kawai zuwa yayi ya yi ta fada mata how great Islam is. Tasan a shekarun girma, Islam ce ke sama. Shine yake zama ya ke ta cemata ta wani bata girma. Ita dama ya taba gani tayi disrespecting dinta? Sai kawai ta mike, tayi serious tana fadin:

"I will never fight for love. I either have it fully or not at all."

Ya daga kai ya kalleta da full seriousness, yace: "You have it, Mehtav. I swear by Allah. Just help me protect it... help me protect you… da ita. Kuma zan bawa kowanninku haqqinta da ya kamata."

Matsowa ya kuma yi daf da ita, ganin kamar tana son ta canza ra'ayi don yana mata maganar Islam, so he wanted to clarify abinda yake nufi. Kasa-kasa yake cemata, "I'm not asking you to fight for me. I'm asking you to stand with me. I truly love both of you, kuma ba ƙadan ba."

At this point, kasa rike kukanta tai, sai hawaye shaaa kamar ruwa suka shiga sintiri a fuskarta. Handkerchief ɗinsa ya ciro, clean yana kamshi, ya mika mata. Cike da damuwa ya shiga bata hakuri, "Ka ce you love her... kuma nima kana sona. You're confusing me. It hurts to know you're not the only one in a man's heart. You think that's easy?"

"I know it's not. Amma this isn't about being easy, Mehtav. It's about being real. Kuma I swear to you, your place in my heart is not a shadow kamar yadda kike tunani. It's a kingdom. And if I ever failed to show you that, you can always walk away. I promise I won't stop you."

Hanky ɗin tasa ta shiga goge hawayenta a hankali kafin tace, "If I agree, EHSAAS… there's no going back."

"Na yarda," ya amsa da sauri.

"Islam..." ta fada muryarta na ɗan rawa kafin ta dorada, "She deserves peace. And so do I. If you bring chaos to my life again, I'll walk away, forever."

Jiyake yi kamar ya jawota jikinsa ya rarrasheta, amma sanin hakan ba mai yiwuwa bane yasa yace, "You won't need to. Na yi kuskure sau abaya, ba zan ƙara bari na yi wani ba barinki ba. Just say yes, my sweet yah Mehtav."

Ya fada da wata murtukacciyar murya yana kallonta kasa-kasa.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace, "Okay... but this time - I'm not falling alone."

Murmushin taga ya saki, kyawawan dimples ɗinsa na fitowa. Cikin deep voice ya rada mata kunne, "You never were alone. You just didn't know I was already falling too."

It's Fatoumspassion EHSAAS Don't forget to: Share Comment Like & Vote [18/07, 21:10] Fatima Rufa'i Nasidi: Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.