Chapter 50
EHSAAS se da ya yi kusan awa biyu tare da Mehtav. Daga shi sai ita. Ba wai wata doguwar magana suke ba, amma kasancewarsu tare da juna ba ƙaramin nutsuwa ya haifar musu ba, musamman shi da baya iya minti ɗaya idonsa ba akanta yake ba. Kallon agogo ya yi, ganin time ya ja sai ya ce mata shi fa breakfast sama-sama ya yi saboda yana zumuɗin zuwa ya ganta. Yanzu haka yunwa yake ji, yanzu zai koma ya ci abinci da kyau don baya wasa da cikinsa.
Murmushi tayi tana kallon sashen da royal kitchen yake ba tare da ta san ta furta hakan ba, ta tsinci kanta da tambayarsa ko ta yi masa breakfast. Dan kallonta ya yi, ya san yadda ta iya girki kuma ba ƙarya ya yi missing abincinta amma baya son ya wahalar da ita. Shi a tsarinsa, ba ya da ra'ayin ya maida matarsa cook dinsa. She's a Queen.
"Karki wahalar min da kanki kin ji, I'll just go there and grab something to eat. Na san sun ajiye min. Ko baki gaji da ganina bane, uhm?" Ya faɗa softly yana mata murmushin nan nashi da yake dada narkar da ita.
Girgiza masa kai tayi alamar a'a.
"Uhmmmm," ya faɗa yana folding hannayensa a ƙirjinsa. "Soma kike in tafi ko?"
Da sauri nan ma ta girgiza kai, alamar a'a. Sai ya ce:
"In na zauna, me zaki dafa min?"
Dan dagowa tayi kafin tace:
"something special." Kasa-kasa, because all this is awkward for her saboda bata taɓa soyayya da wani ba tun da take. Kamar shi, shi kaɗai ne take iya zama tare dashi tayi feeling comfortable har haka. Kuma bata iya ɓoye masa son da take yi masa a cikin ranta. Ko da bakinta ba ta furta ba, actions dinta ya rigada ya gama fallasa kanta a gurinsa.
"Ko zaki rakani sashen Maama se mu ci abincin tare mu dawo nan?"
Da sauri ta shiga girgiza masa kai irin "Ta yaya din nan ma?" Ya yi dariya yana faɗin:
"Words. I want words. Yaushe kika zama miskila ne ban sani ba, uhm?"
Murmushi tayi tana kasa da kanta kamar wata amaryar ƙauye don ji take kamar ta nitse a gurin. Agogo ya kalla kafin yace:
"Yunwa nake ji fa sosai, amma kuma ni kaina bana son na tafi saboda na san ba zan sake samun lokacin ganinki sosai kamar haka ba, musamman idan parents ɗinmu suka ji kince yes, za a sa min ido, ba za a riƙa barina ina zuwa nan ƙara zube ba. Let's go. I'll help you inside the kitchen."
Murmushi tayi tana miƙewa. Ita ce a gaba, yana binta a baya, watching how she's walking slowly kamar tana tausayin ƙasa. Har suka ƙarasa kitchen ɗin da ke nan tsaf-tsaf, fes-fes, don yau anan aka yi musu breakfast. Wasu maids biyu ne a ciki suke ƙoƙarin fara haɗa lunch. Ganin Prince a bayan Mehtav yasa duk suka yi ƙasa da kansu suna gaishe shi. Dan fuskewa ya yi kafin yace su basu guri. Ficewa suka yi sumsum kamar wasu munafukai.
Mehtav ta juya tana kallon yadda ya ci mur kamar ba shine ke giggling ear to ear a gefenta ba dazun. Ya koma kamar wani boss. Dariya ta kyalkyale masa, ba dai ta tsokane shi ba kamar yadda ta so yi, sai ta nufi wata ƙofa da take kyautata zaton nan ne store din. Ta shiga,cike yake, makil da kayan abinci iri-iri, ciki da waje. Bata tsaya anan ba, ta wuce walk-in freezer, ta shiga haɗo duk wasu abubuwan da take buƙata.
Yana binta a baya. Ta ba shi wasu, ya riƙo mata wasu. Suka fito a tare kamar sun yi shekara suna hakan. Ta ajiye saman kitchen island din tana kallonsa. Shi ma kallonta yake yi yana murmushi kafin yace:
"Your Highness, da wanne za a fara?"
Murmushi tayi kafin tace:
"Ka tafi kajira ni waje. You're not supposed to be here. You're a Prince, kada a zo a fara maka dariya nasaka a kitchen." Ta ƙarasa faɗa tana kunna tap.
Murmushi ya yi, ya tsaya a bayanta yana watching yadda take komai cikin nutsuwa, babu garaje. Amma kana gani ka san takwarance a iyawa. Yace:
"I don't care, as far as zan kasance tare da ke, you're cooking for me. I wouldn't miss this for the world."
Ya tsaya very close behind her, yana kallon yadda ta fara yanka albasa da tomatoes. "You still remember yadda kike sakani wanke-wanke? Imagine wai Prince ake sawa wanke-wanke fa, dan kawai ya ci kai." Ya ƙarasa faɗa cike da tsokana.
Mehtav ta juyo tana dariya, "Your memory is not remembering things quite well. Kaine kace zakai, ni ba ni na saka ka ba. Haka kake zuwa kana ta troubling dina."
Murmushi ya yi saboda sarai ya tuna shine yake takura mata,yana sane don son jan magana yace ita take sa shi. Girgiza kai yashiga yi kafin yace, "Really? You must've hated me back then. Duk abincin da kika girka fa, yana min daɗi sosai. In ciye kuma bana ce miki komai."
Dariya ta shiga yi tana faɗin, "Ai rigimarka back then yafi na tsohon mota. Har Allah-Allah nake yi in na yi abinci karka ce ba zaka ci ba. You're too picky when it comes to food." Ta ƙarasa tana ci gaba da yanke yankenta.
Freezer ya buɗe, ya ciro ruwa. Har zai buɗe ya kai bakinsa, sai kuma ya fasa. Ta kallesa, badai ta ce komai ba, amma tayi mamaki. Kamar wani abu ya tuna masa ne yasa ya fasa.
Yace, "Yah Mehtav ɗita ta kaina." Yana ɗaga mata gira. Sanin cewa ta san abinda ya tuna yasa ta fara ƙoƙarin ɓoye blushing ɗin da ke kan fuskarta.
"Awwwn, wai kunya na kike ji?" Ya faɗa yana leƙa fuskarta. Girgiza kai tayi amma ta kasa magana ganin ya saka ta a kwana.
Yace, "You're shy, especially when you know I walked in on you one day watching explicit romance movie or should I say s**."
"No, you didn't!" Ta shiga girgiza kai trying hard to deny it.
Gyara mata gyale ya shiga yi kamar mai rada, yace mata: "Stop being shy. We will explore all your fantasies after the nikkah, I promise. I can…"
Da sauri tace, "Pls stop..." Saboda yadda ta fara shivering, numfashinta na sama da ƙasa, hannunta ya fara rawa. Ba ta san sanda ta ajiye wukar ba. Ta fahimci EHSAAS is her weakness, kuma fitinanne ne na bugawa a jarida. A haka tana kallonshi simi simi, kamar ba zai yi ba, gashi with small naughty talks yana neman ya dagula mata lissafi.
Idonshi akanta, taga ya ɗau wani date da ta gama wankewa ya saka a baki.
"Are you cold?" Ya faɗa irin he is clueless dinnan akan abinda yake mata. Ya ɗau wukar gently yace, "Let me help you?"
Gefe ta ja ta tsaya. Sai da ta tabbatar numfashinta ya dawo daidai tukunna ta dawo gefensa.
"Kabarshi, zanyi. Kar ka yanke." Ta faɗa cike da kulawa tana leƙa yadda yake yanka veggies ɗin, manya-manya kana gani kasan ba ya iya ba.
Dariya ta shiga yi masa, ta ƙwace wukar tana faɗin, "Me zan gani haka?"
Dariya ya shiga yi yana faɗin, "Yayi kyau ko na burgeki?"
Dariya itama take yi tana girgiza kai, tace, "Na gode. Kabarshi kawai."
Turo lips ya shiga yi yana narke mata wai shi ala dole sai ya tayata. Tasha dariya sosai.
Ganin ba zai kyale ta ba yasa ta kunna wuta, tace: "Fine." Tana ɗauko sausage, ta saka a wuta. Tace: "Kaga sausage ɗinnan, ka dinga juyawa a pan ahankali-ahankali. Low heat fa. Kar ka ƙara komai, ka barshi yadda na sa."
Jinjina kai yayi yana faɗin, "Done ma'am."
Ya shiga juyawa a cikin flat non-stick pan ɗin, yana kallon yadda sausages ke yin "tsssssss" da sound. Yana dariya yana faɗin, "Kinganni nan, I'm a good husband material. Kinyi sa'ar samin miji kamata. Ko da baki faɗa min ba, ni na faɗawa kaina."
Dariya Mehtav ta shiga yi tana girgiza kanta. Tace: "Na fahimci some of those naughty stubborn behaviours da kake yi during that amnesia, ba wata amnesia, halinka ne. You're obsessed with yourself."
Murmushi ya shiga yi cike da tsokana, yake faɗin: "Ai an ƙi a ce min ana sona, shi yasa nake faɗa ma kaina don in ji daɗi."
Girgiza kai ta shiga yi tana focusing akan girkin da take yi. Ganin babu abinda yake sai kona sausage ɗin yasa tace ya zauna kawai, ya yi watching ɗinta.
Don dawo da ita baya yake yi haka yana yimata hira yana tsokanar ta har suka kammala. Da suka kammala, be barta ta ƙwaso komai daga kitchen ba. Anan suka jere shida ita simple breakfast ta yi masa na:
Grilled halal lamb sausages da herbs
Creamy scrambled eggs
Toasted brioche da honey a gefe
Sannan kuma ta ajiye bowl of black olives, feta cubes, and cherry tomatoes
Da pomegranate juice a cikin royal glass.
Tunkan ya fara ci, ya fara mata santi, wai kamshin girkin kadai ya kosar da shi. Sai murmushi take masa tana zama saman stool a gefenshi.
Yana kallonta, ta ajiye final tray ɗin. Yace: "Do I eat first? Or stare at you for a while longer?"
Blushing ta fara yi. Ya ɗauki fork, yana kai egg ɗin bakinsa. Ya lumshe ido yana taunawa gently, tana watching yadda small red lips ɗinshi ke motsawa. Kafin ya buɗe idonsa, suka sauka akan nata da ta kafe shi da ido. Amma ganin yana kallonta, da sauri ta ɗauke kai.
Cikin tsokana yake faɗin: "Yah Mehtav… this is unfair. You feed my soul and my stomach all in one morning."
Ta girgiza kai tana murmushi, tace, "You're being dramatic. Ka dai kawai ce santi kake yi."
Jinjina kai ya shiga yi yana faɗin, "Yes, abincin nan ba iya cikina ya shiga ba. Har cikin soul ɗina ya tafi, can-can ciki," ya ƙarasa yana kai wani bakinsa.
Murmushi take yi tana kallonsa, saboda tana jin daɗi sosai idan ta yi girki aka yaba mata. Ya ɗago bayan ya gama cinye na bakinsa, ya debo itama, yana kai wa bakinta. A hankali ta buɗe, ya bata yana tsareta da ido, yace:
"You're being dangerously perfect, Mehtav."
Murmushi ta shiga yi masa. A haka ya na ci yana bata, though ita kaɗan ta ci. Sai tace masa ta koshi, saboda already ta rigada ta yi breakfast dinta. Shine ya ci sosai. Don kaɗan ya rage, shima yace saboda cikinsa ya cika ne. Da akwai sauran space, da sai ya cinye. Ita dai dariya kawai take masa.
Ya kalleta softly, yace: "Let's do this forever. You. Me. Quiet mornings. Laughter and sausage."
Cike da tsokana Mehtav tace, "Sai ka koyi yanka veggies tukunna."
Murmushi ya yi yana ɗaga mata gira ɗaya. Suka fito a kitchen ɗin yana faɗa mata, ba veggies ba. In za ta riƙa yi mai abincin nan mai daɗi, ai har wanke-wanke zan riƙa yi mata.
Kiran da aka yi masa daga royal council ne yasa ya yi mata sallama, ya wuce can royal court, da yanzu shine yake zama, yana sauraron korafe-korafe, kuma duk wani hukunci na Mai Martaba, daga bakinsa ake ji.
Busy ya yi sosai yau ɗin saboda abubuwan da suka sha mishi kai. Sai bayan sallar la'asar sannan ya nufo ainahin cikin gidan. Yasan Islam na sashen Fulani, hakan ne yasa ya wuce directly, saboda kewarta da yake ji. Yau tun da safe ko waya da suka saba yi ba su yi ba.
A can cikin royal garden na sashen, ya samu Fulani tana shan special mint tea. Ya ƙarasa ciki. Murmushi ta sakar masa sanda ta hangoshi yana tahowa.
"Babana," ta ce softly, ta ajiye cup ɗin tea. "Ka zo."
Daf da ita ya ƙarasa cikin nutsuwa. Ya kama hannayenta duka biyun yana kissing, ya gaishe ta. Ta amsa cikin farin ciki a kan fuskarta. Dan kallon gefe-da-gefe ya yi taga da alama akwai wanda yake nema.
Murmushi ta shiga yi tana faɗin, "Lalle ake yi mata suna can sama. Mutumin naka kuma ya yi barci."
Jinjina mata kai kawai ya yi yana faɗin, "Is she okay, Maama?"
"Sure," Fulani tace tana tambayarsa "Ya su kai da Mehtav?"
Murmushi ya yi, yana dan sosa keya da alamar yana ɗan jin kunyarta. Tace, "Ina jin ka, babana. Ka yi shiru." Yace, "Ta amince, Maama…"
Cikin farin ciki Fulani ta ɗaga hannayenta duka biyun sama, tana faɗin: "Alhamdulillah! Alhamdulillah." Kunyar ta ya ji ta lullube shi, yana wani sunkuyar da kai. Ta miƙe tsaye tana buɗe masa hannayenta alamar ya zo ya rungume ta. Miƙewa ya yi, ya ƙarasa yana rungume mahaifiyarsa. Tana dan shafa bayansa tace:
"Allah ya sa albarka, habibie na. Ka yi min alkawari zaka kasance mai adalci a tsakanin matanka. Na san it's very hard, amma ina son ka ƙoƙarta, kaji? Kar ka bari ɗaya daga cikinsu ta shiga kunci sanadin wannan hukuncin namu."
Jinjina mata kai ya yi yana dan sakinta, yace: "In shaa Allah, Maama. Zan yi iya ƙoƙarina wurin ganin na kwatanta adalci a tsakaninsu."
Fulani tace: "Allah ya ba ka iko. Ai zama bai kama ni ba. Dazunnan babanka ke tambayana. Har yanzu maganar Mehtav shiru. Ka san yafi kowa son ya ga lamarin nan. Yanzu zan wuce in faɗa masa ne, kaji?"
Dan jinjina kai ya yi kafin yace: "Ko na haura sama na duba Islam ne?"
Dan jim tayi kafin tace: "Lalle ake mata. Ba na son ka je ka takura mata, ka sa a cire mata begama yin kyau ba. Kai wucewar ka kawai. Na san cida zucinka. In ta gama zata zo. Ka ci abinci kuwa?"
Dan gyada kai ya yi, saboda har yanzu he is full da girkin da Mehtav ta yi masa. Tace: "Tohm. Masha Allah, ni na wuce."
Gyada mata kai kawai ya yi, amma hankalinsa na wurin Islam. So yake kawai ya ji yaya take.
Fulani na wucewa, ya ciro wayarsa, ya yi dialing kiranta. Har ta gama ringing bata ɗaga ba. Dama ya raya hakan, saboda ba lallai ne ta fito da wayar ba.
A haka dai ya wuce sashensu, shi shi kaɗai, ba don ya so ba.
Akwance Fulani ta samu Mai Martaba a royal reclining couch, likitansa yana dan daddan masa kafafuwansa. Amma ganin Fulani ta zo da annurin da yake kan fuskarta, yasa ya sallami likitan. Don baya haɗa ta da komai a cikin rayuwarsa, hankalinsa gaba ɗaya ya bata lokacin da take sanar da shi labarin Mehtav ta amince da ta auri EHSAAS.
Murmushi kawai yake yi, ya shiga hamdala, shima cikin dan mamakin saurin amincewar. Yace:
"Fulani na… Mehtav ta amince da ɗanmu fa kike cewa?"
Jinjina kai Fulani tayi tana gyara masa farar sumar kansa.
Yace: "Masha Allah. Haka ake so. Ya kamata ki shirya mana ƙaramin taro na cikin gida - iya mu, sai EHSAAS da iyalinsa, da ita Mehtav da mahaifinta da grandmother ɗinta. I want to ask her da bakina."
Jinjina kai Fulani tayi tana ce masa, "An gama, Your Royal Highness. Yaushe kake so a yi?"
Dan jim yayi kafin yace: "Ko zuwa anjima bayan sallar Maghrib, kafin dai Isha'i. Tunda ba wani jinkiri zamuyi ba. Inada meeting da Wambai akan maganar mahaifiyar Mimah ne, da take asibiti."
Dan jim Fulani tayi, sanin baya son a maimaita maganar me babban daki, saboda itama abaya ta sha yi masa magana akanta amman zejita baze bata ansaba. Tunda ba wai warkewa ne ba zata yi ba, professional doctors ɗinsa ya ki ba su permission ɗin dubata. Domin da sun duba ta, da tuni an rigada an wuce gurin. Ta san kuma kunyar Wambai yake ji, shiyasa ya amince zema sauraresu.
Jinjina masa kai tayi tace masa: "Zan sanar da kowa yanzu In shaa Allah."
Within an hour ta sanar da kowa maganar taron, har sashen su Mehtav ta aika. Bayan Paa ya dawo daga sallar Maghrib, ya kira ta, yana faɗa mata maganar, "Ko an sanar da ke?" Jinjina kai tayi alamar eh, an faɗa mata.
Abeey da ke ta shiri zata je, yace ta zauna. "Babu inda zaki je, balle ki tsoma mana baki a maganar manya."
Shi da Mehtav kaɗai suka je. Suka bar ta tare da Inna. Se kunci take yi.
Royal garden din ado aka masa, an canza shi zuwa exclusive evening paradise. An saka wasu candlelight ga wani cool breeze dake kadawa cikin gurin yana kada hadaddun flowers dasuka zagaye gurin masu kamshi. Classic oriental instrumentalists suna ta busa light music na tashi a gurin. Maids ne suke serving finest dates, sparkling apple juice, da grilled lamb skewers.
Yayinda families din ke having good time, kai zakace an rigada an zama daya ma tuntuni. EHSAAS yana zaune a gefen Islam, dake itace karshen zuwa saboda lallenta da bata wanke da wuri ba. Sai satar kallon lallen yakeyi yana yaba mata a cikin kunnuwanta. Ba ta dai kulashi ba, saboda hasken fitilun da suka dallaresu duka ana ganin kowa da kowa a gurin.
Mehtav, as usual, tana kusa da babanta. Sai Mai Martaba da Fulani a gefe guda. Mai Martaba be ce komai ba sai da suka danci kayan ciye-ciyen da aka ajiye a gabansu.
Kafin nan, Mai Martaba ya kalli Mehtav yana fadin: "Daughter, I know I'm old and weak, but my eyes can still see pure love. My son loves you. But I want to hear it from you. Are you willing to marry him?"
Duk idanuwa kowa akanta yake musamman Islam, da take jin kamar her whole life depends on Mehtav's answer. Kan Mehtav a kasa, tana jin idanuwansu gaba daya a kanta. Kirjinta na bugawa gently, tace: "Hakane. Allah ya temake ka... Na amince."
Kabbara Mai Martaba yayi, ya kasa boye farin cikinsa. Yana mikawa Habib Bai hannuwansa, yake fadin: "Congratulations to us."
Paa shima murmushi yayi yana kallon Mehtav. Domin be san menene ya canza mata ra'ayi a lokaci guda haka ba, amma dai he trusts all her decisions. Yasan Mehtav nada hankali, ba zata dau irin wannan hukunci ba tare da zurfin tunani ba.
Shima congratulating Mai Martaba yayi, ya kalli EHSAAS yana mai "congratulations." Amsawa yake, kansa a kasa, irin na jin kunyar nan. Fulani ta dafa kafadar Mehtav tana fadin: "Thank you, my dear."
Murmushi kawai Mehtav tayi, idonta akan Islam, wanting to read her facial expressions. Gani tayi EHSAAS yayi leaning, ya rada mata wani abu a kunnenta. Sai taga tayi murmushi. Sai asannan ta dago suka hada ido.
Murmushi itama tasakar mata, tana mika mata hannayenta da sukaji jan lalle daya fito yayi wa dogwayen hannayen nata mugun kyau, tace: "Congratulations, Mehtav."
Itama murmushi tayi mata, tana mika mata hannun nata suka gaisa. Kowa yayi congratulating dinsu. Kafin nan, Mai Martaba ya soma bayani. Yayi wa Paa godiya da karamcin da suka nuna musu once again. Kafin nan ya koma kan Islam. Sosai ya yaba mata da namijin ƙoƙarin da tayi wajen amincewa da mijinta da supporting dinsa a wannan lokacin da yafi bukatarta sama da kowa. Yana alfahari da ita, kuma yana kaunar ta. Kuma ta sani har abada zata kasance diyarsa.
Jinjina kai tayi, tana mishi godiya da duk abinda yayi mata a rayuwa, tana nuna masa babu komai,ai duk abinda tayi ma EHSAAS responsibility dinta ne. Babu wanda bata burge a gurin ba, ciki kuwa har da Mehtav, saboda Islam ta cika jarumar mace.
Mai Martaba murmushi yayi yana kallon EHSAAS, yace: "Hold her tight. Itadin lu'ulu'u ce mai tsada."
Jinjina kai EHSAAS yayi yana aika mata da wani kallon tsumammen sonta, dake dada ratsa kirjinsa a kowace rana, a kowace dakika.
Mai Martaba ya hadasu duka su ukun, yayi musu nasiha akan zaman takewar aure mai ratsa jiki. Yana ta jaddada musu hakuri da juna da kuma girmama juna a cikin kowane hali da hadin kai. Kada su bari wani ya shiga tsakaninsu.
Duk suka amsa masa, suka mai godiya. Kafin ya koma da hankalinsa kan Paa, yace masa: "Ina so auren nan ya kasance cikin sati biyu, idan babu damuwa. Don kasan ba a jinkirta alheri."
Shiru Paa yayi yana nazari. Duk da shi ashirye yake ya aurar da Mehtav a koda yaushe, amma ba zai so auren Mehtav ya kasance a wata kasa daban ba. Yana son ya kasance a tsakiyar 'yan uwansa da abokan arziki, maza da mata, su zo su shaida-ko ba dan komai ba, domin kankarowa da yarsa Mehtav mutunci a wannan gidan. Yana son ya gwada tashi bajintar a auren diyarsa. Kuma yasan in dai har anan za'a daura, tohm da wuya su bar shi ya siyi ko da tsinke.
Dan murmushi yayi, ya kalli Mai Martaba dake jiran amsarsa, yace: "Allah ya temake ka. Tabbas hakane. Amma inaga kamar sati biyu yayi kadan. Ina ma laifin wata guda, saboda ina son ni da 'yan uwana mu je mu shirya ma. Tunda dai yara sun amince da junansu."
Mai Martaba respectfully yace ma Paa: "Ina son a daura auren ne as soon as possible. Kana ganin yanayin jikina, ka san rayuwartamu ba a hannun mu take ba. Ina fatan Allah yasa za'a yi dani."
Fulani ce ta rike masa hannaye ta kasan table, saboda yadda tayi sensing his emotion gaba daya Yayi giving up akan rayuwa. Normally tasan inda garau yake, zai bawa Habib Bai duk lokacin da yake so. Amma yanzun gani yake kamar idan aka ja abin, ba zai ganiba.
Habib Bai yayi shiru yana tunanin ta yaya zai bullowa da Mai Martaba cewa ba matsala satin biyun zeyi, amma zai fi so a daura auren a Nigeria, kuma Mehtav tayi bikinta a Nigeria.
Fulani Hajar kamar tasan me yake tunani, a nitse tayi murmushi tace: "Engineer Habib, a dan duba mana satin biyun nan dai. Amma kafin nan, let me ask you directly. How would you prefer your daughter's wedding to take place?"
Dan gyara zama yayi kafin yace: "It'll be an honour if it takes place in my country… Nigeria. Inda danginta da kawayenta zasu iya halarta. Ina rokon wannan alfarmar. Allah ya temake ka."
Mai Martaba ya kalli Fulani kafin ya kalli EHSAAS. Suka yi murmushi tare, yace: "Permission granted. Amma dai sati biyu."
Jinjina kai Habib Bai yayi yana fadin: "Na amince. Allah ya temake."
Mai Martaba yace: "But before then, there's a royal tradition. A royal engagement must happen here in Nuristan. It's where my son will officially request her hand in marriage before she returns with you. We'll make it grand."
Habib Bai jinjina kai yayi, ya amsa alamar ya gane. Nan yace masa Fulani zata musu sauran karin bayani, in sha Allah.
Jin ana kiran sallar Isha'i ya sanya mazan suka wuce zuwa masallaci baki daya. Islam ce ta fara tashi, tayi excusing kanta, duk da Mehtav ta so su dan tattauna su su biyu, amma ganin bata bata fuska ba ya sa itama ta wuce sashensu kawai.
Bangaren Fulani Islam ta koma ta tarar an gama dinner. Cikinta babu yunwa kwata-kwata saboda se kusan magrib ta yi lunch, sannan ga ciye-ciyen da suka yi a gurin small gathering ɗin, hada na EHSAAS kawai ta yi ta tura mai bangarensu. Domin har cikin kirjinta take jin ba ta son ganinsa kawai daga shi har Mehtav ɗin, daurewa kawai take yi.
Dakinta na sashen ta wuce, ta yi alwala, ta yi sallah, ta yi wa Jr sabon wanka, ta sauya masa kaya zuwa marasa nauyi na barci. Yana zaune saman gadon suna wasansu. Ta ji wayarta ya fara ringing. Ita tun safe ma ba ta bi takan wayar tata ba, sai yanzun. Tana ɗaukowa, taga Abraham Zion.
Da murmushi a kan fuskarta ta ɗaga wayar, suka gaisa. Yana tambayarta yaya take, ya Jr. Tace mai duk suna lafiya. Don har yanzun ba wata shakuwa mai ƙarfi a tsakaninsu, amma dai yakan kirata sau biyu a sati yaji ya take. Itama in ta yi fisha, takan kirashi.
Yanzun ma kiranta yayi yana ba ta labarin ya yi closing wani big deal a Atlanta, ya samu riba mai tarin yawa. Don haka ya yi musu arranging family trip if she's free, zuwa sati mai zuwa - just su, sai ita da ɗanta. Murmushi tayi tana tunanin wannan babban opportunity ne da za ta yi using, ta bar gidan ko zuciyarta za ta sanyi, saboda ba za ta iya watching wannan bikin ba.
Da sauri ta amsa, tace masa za ta tambayi EHSAAS, itama za ta so taje in sun yi deciding, she will get back to him. Bece komai ba kuma, ta san ba zai ce "din" ba. Don har yau ba wai kaunar EHSAAS yake yi can-can a cikin ransa ba, kawai dai ya yi accepting ɗinsa a matsayin namijin da take so, kuma ya yi alkawari ba zai taɓa forcing ɗinta akan wani abu ba har abada.
Da mom ɗinta ya haɗata, ta fara ƙwaɗaitama tafiyar. Tana dada gaya mata cewar they will enjoy a lot. Itama irin ansar da ta ba Abraham ɗin ta bata. Suka ce tohm, se sun jita. Ba ta jima da gama wayar ba, Fulani ta shigo cikin ɗakin wurin ƙarfe goma.
Cikin mamaki take faɗin, "Har zan wuce, sai naga wutar ɗakin nan a kunne? Islam, me kike yi har yanzun baki wuce sashenku ba?" murmushi kawai ta yi tana ƙasa da kai, alamar ta san ta yi ba daidai ba. Fulani ta riƙo hannunta tana faɗin:
"Nasan is not easy. But please, don't let this create distance tsakaninki da mijinki, kinji? Lokaci ne daya kamata ki jashi a jiki kinji? Ba wai ki ringa distancing kanki da shi ba. Maza mu je kiwuce. Ina keys ɗin?"
Hijab dinta dogo ta zira, ta ɗau makullin motarta. Fulani ta ɗaukar mata Jr. Ba tace komai ba har suka sauko ƙasa har bakin sashen Fulani ta raka ta. Ta yi ƙasa da kanta tana wasa da yatsunta, tace:
"Take care of yourself kinji? I know you can do it, my girl. Allah ya yi miki albarka."
Jinjina kai kawai ta yi, tace, "Ameen maama, thank you." Tana rungume ta, itama rungume ta tayi. Ta ba ta Jr, ta wuce parking space. A bayan motar ta ajiye shi, ta shiga gaban, wayarta ta duba taga missed call din EHSAAS tun dazun da ya yi mata da yamma. Amma daga nan bai sake kira ba.
She's wondering ko dai shima bai koma sashensu ya ga ba ta nan bane, shi yasa bai kirata ba, saboda ta san how clingy he can get. In dai har ya koma bai ganta ba, ze ta kiranta ne har sai ta gaji ta dawo. In ta ki kuma, ya bita koda faɗa suke yi, in ta mai haka ko da kwana tace za ta yi sashen Fulani. Haka shima zai karkade pillow ya kwanta a gefenta, yace "sai da safe." But he didn't even call today... me yasa? Ta tambayi kanta tana yi wa motar key.
Bangaren EHSAAS Ku wa yana fitowa daga mosque, sashensu ya wuce. Ganin Islam bata dawo ba har lokacin, ga dinner ɗinsa an shirya masa, ya sanya ya shiga cikin ɗakinsa kawai. Wanka yayi, ya fito da niyyar binta sashen Fulani, don yasan ba zai taɓa iya rintsawa ba tare da ita a gefensa ba. Musamman yau da yake cikin matsanancin farin ciki, he wants to share every joy with her.
Yana ciki shiryawa, ya ji wayarsa ta yi ringing. Yana dubawa yaga number Mehtav. Cike da farin ciki ya ɗauka. Abeey ce ta kira shi saboda Mehtav ta bata labarin duk abinda ya faru. Cike da farin ciki ta fara mai congratulations, tana faɗa mai kalar ɗakin da take so ya tsara mata a gidansu shida Mehtav.
Murmushi yake yi yana sauraron ta. Sun yi kusan 30 mins suna magana kafin Mehtav ta gaji ta kwace wayarta. Yana jin Abeey tana ƙunkuni, suka fara magana sama-sama. Be san lokacin ya ja ba. Ya sa wayar a speaker, ya cigaba da saka kayan barcinsa. Bayan ya gama, ya fito daga walk-in closet din. A gefen gadon ya zauna, ya ja laptop dinsa, yana duba wani file da ya manta bai yi saving ba.
Yana sauraron muryarta da ta yi wani irin laushi mai saka kwanciyar hankali. Ba shi labarin yadda taji dazun take yi. Jin tayi shiru yasa yace:
"I'm listening, my sweet. Yah Mehtav, kin yi shiru?"
Murmushi tayi tace:
"EHSAAS…"
"Na'am, Mehtav… still with me?"
"Still here, naji kayi shiru ne?"
Murmushi yayi kamar tana gabansa yace, "Kinsan I'm more of a listener than a talker, kuma tsabar dadin muryarki ne yasa nafison in ji shi akan inyi interrupting dinki."
Wani blush Mehtav ta saki daga dayan bangaren tana rufe fuska tana fadin, "Wai ni din?"
"Eh mn, ko baki san muryarki yana da dadi sosai ba?"
"Uhmmm uhm, ni bansani ba," ta bashi amsa tana girgiza kai kamar yana gabanta.
Yace, "It's super melodious. Yanzun dai fada min me kike so ki ce?"
Giggling tayi yanajin sound ɗin ta through the speaker. Ya yi murmushi, he loves making his women happy, irin sosai ɗinnan musamman ita da yasan ya bata wuya sosai a wancan lokacin.
Tace, "Kawai fa cewa nai I can't believe I said yes a gaban Paa, ga Mai Martaba, ga Mom ɗinka, duka suna jina. Like, I was shaking." Ta karasa tana dariya a hankali.
Yace, "And I'm super proud of you for that. I feel like the luckiest man alive."
Yanajin sautin murmushinta ta dayan bangaren. Bata ce komai ba. Suka yi shiru na seconds, suna jin saukar numfashin juna ta speaker ɗin, soft, calm, sweet.
Gently yace, "Mehtav, kinsan me?"
"Tell me," ta amsa mishi tana sauraronshi.
"Have you ever dreamt of me…?"
Dan shiru tayi saboda ba zata iya fada mai kalar yadda ba dare babu rana take cikin mafarkai da tunaninsa ba saboda kunya.
Jin tayi shiru ya saki murmushi yana sake tambaya, "Have you… uhm?"
"Uhmmm uhmm," ta fada muryarta a dan harde tana rufe jikinta da bargo gaba daya.
"Fada min mana sannan I want it to be in detail, ta yadda zan san each and every part me kika fi so and we will practice it in real life."
"EHSAAS!" ta fada irin kabari ɗinnan mana.
Dariya yayi yana fadin, "Mehtav…"
Ta sake cewa, "EHSAAS," da wata irin kasalalliyar murya, da tasa EHSAAS yace:
"Don't tempt me. Kinsan we are few meters away from each other, I'll just come..."
Kasa karasa statement ɗin nashi yayi sakamakon jin an bude ƙofar ɗakin. Sanin wacece zata shigo yasa da sauri ya daga wayar ya cire daga speaker, ya mayar da ita kunne. Tunkan Islam ta kammala shigowa, a gaggauce, with sudden shift a muryarsa yace mata: "Uhm... Mehtav, goodnight please. Talk to you tomorrow, okay? Ki yi bacci lafiya, take care of yourself for me…"
"Okay… but-" Bata karasa maganar ba taji click - ya kashe kafin ta kammala.
Daidai Islam ce ta shigo ɗakin rike da Jr a hannayenta. Fuskarta babu yabo babu fallasa, take kallonshi da laptop ɗin dake gabansa. Sosai hankalinta ya kwanta ganin kamar ma aiki yake and he's wearing pajamas, hakan na nufin ba wurin Mehtav ya tafi ba.
Karasowa tayi don a gajiye take. Tayi zaman lallen nan tana fadin, "Sire, ashe kana nan. Ko ma ka nemeni ban dawo ba, ko?" Ta kwantar da Jr cikin gadonshi. Ta gefe ido ta ga kamar yana tura wayarsa kasan pillow, yana mata murmushi kamar wani abu yake yi da bayason ta gani.
Ta saki murmushi tana fadin, "Mene ne kake boye Wayar? Me yake ciki?" Ta karasa tana cire hijab ɗin jikinta ta jefar kasa.
"Baby, you're late. Me kika tsaya yi?" ya tambaya yana ƙoƙarin dauke attention ɗinta daga kan wayar da ya danne da pillow.
Saman cinyarsa ta haye tana barbaza masa gashinsa tana fadin, "Ai ba kai missing ɗinaba. Tunda ban ga kiranka ko daya ba, me ka yi da wayar?"
Ta saka hannayenta kasan pillow tana kokarin cirewa. Rikota yayi yana fadin, "Baby, pls don't…" Saboda ba ya son duk abinda zai hurting dinta. Ba ya son taga kamar saboda Mehtav ne bai kirata ba.
"Na gani," ta tsare shi da ido tana miƙa mai hannayenta. Ba ya iya mata musu, musamman in ta haɗe mishi girar sama da ƙasa, sannan da wadannan shegun idanuwan nata masu rikita masa lissafi. Ya sa mata wayar a hannunta. Har zata bude, sai wata zuciyar ta ce mata, "Yanzun fa ba ke ke kadai bace a tare da shi. Bai kamata kike masa titsiye irin haka ba. Kar ki je ki buɗe wayar ki ga abinda zai bata miki rai."
Da ƙyar ta iya danne zuciyarta. Ta ajiye wayar gefe tana laka ce mishi dogon hancinsa. Tace da wasa, "Na dauka ba zaka bani ba…" Tana ganin yadda bugun zuciyarsa ya dawo daidai ganin ta ajiye wayar. Ta yi murmushi kawai kafin tace, "Baby, ana shigowa section ɗinnan a rinka ƙoƙarin ajiye wayar nan pls."
Sosai ya fahimci maganar tata. Kuma ya gane cewa ta gane da wa yake waya. Ya jinjina kai yana fadin, "In sha Allah, ba za a ƙara ba, my pipi."
"Ke ta musamman ce," ya karasa yana mata cakulkuli.
Ta shiga dariya tana fadin, "Ahh, ka bari fa… hhhh Sire, cakulkuli fa kanwar mutuwa ne, kar in mutu." Sai da ya ga tana dariya heartily, sannan ya kyale ta. Yana dariya shima ya ja ta jikinshi yana rungumewa. Ta yi lamo a kirjinsa kamar me barci amma ba barci take ba kawai tunani take yi. Ranar da za a ce wata zata kasance tare da shi haka a cikin irin wannan yanayin, kuma ya yi farin ciki haka wata ba ita ba. The thought of it kadai breaking heart ɗinta yake into pieces jitai ranta yayi dubu ya baci.
Wayarsa ta ga ya ja da sauri. Ta ga ya yi minimising, ya fita, ya shiga gallery. Hotunan wasu haɗaddun zobuna ya shiga nuna mata yace, "Baby, zabi."
Kallo daya ta yi musu ta san diamonds ne, saboda ba yau ta saba mu'amala da su ba. Kallon na auren su na hannunta tayi tana fadin, "Wannan fa? This looks like engagement or wedding rings."
Yace, "Eh, shine." Murmushi tayi tana dauke idonta daga kallonsu. Ta mike daga jikinsa tana fadin, "You're supposed to select it with your bride, not me."
Dawo da ita baya yayi. Ta fado jikin sa, a hankali yake fadin, "You'll forever be my bride too, baby. It's for you. Kingansu, limited edition ne - just for the two of you. You know my Queens deserve the best."
Kifara zaba ai kece babba, dariya tai tana kallonsa kafin tace, "Uhmmm, tohm mungode. Ka zabar min kawai, Sire, kasan Our taste is the same." "Sure," ya fada yana dubawa. Can seya nuna mata wani me pink ɗin ajiki yace, "Wannan seya fi miki kyau." Yana daukar dogwayen yantsunta, yay kissing yace, "Wannan kuma me black ɗin, it'll suit her well. Kinga tanada haske sosai." Jinjina mishi kai tai kawai tace, "Yes Sire."
Se kuma tamike a jikinsa ta kalleshi tace, "Dazun parents dina sun kirani. They plan vacation and they invite Jr and I, and I said yes to them." Dan kallonta yay kafin yace, "Baby, ba mun gama maganar nan ba. Kinsan it's not safe at all for you guys." "I already said yes, Sire," tafada tana hade ranta saboda tasan ba zai taba barinta ba inbatai dagaske ba. "Pipi, before saying yes, we are supposed to discuss it tsakaninmu. After what happened in Nigeria and LA, gaskiya bazan iya barinku kuyi nisa da ni ba. Anything can happen."
"Ai an kama gimbiyah, nothing will happen. Kuma duk suna prison. Just allow me to go, pls," tafada tana cukule fuska cikeda rigima.
"Gaskiya babu inda zakije, kina jina Islam, saboda duk da an kamasu, ba wai an kama duk masu temaka musu bane. A cikin palace ɗinnan, what if wani abu yaje yafaru daku like how we lost our grandmother in Nigeria. Our enemies are everywhere. Peace, no, baza kujeba gaskiya."
"Ni zan je," tafada tana harde hannayenta a kirji. "In Jr kake ji, zan bar maka yaronka a gurin Maama. But I just can't stay in this palace. I'm suffocating, Sire. Pls, understand me. It hurts," takarasa tana mikewa. Bata bari yaga kwallar da ta saukar nata a idanuwanta ba, tai saurin sharewa tana nufar saman couch ta zauna.
Biyo bayanta yay ya zauna a gefenta yana rike kansa. Yasan tafishi gaskiya a wannan karan and he truly understands her, irin sosai dinnan. Kuma shi kansa yana son taje wani gurin da zata sha iska, amma bai san me yasa yake having weird feelings akan kada ya bar ta ta fita ba. Na farko, yana tsoron kada taje tafita makiyansa su fara bin ta. Na biyu kuma, yana tsoron kada idan ta tafi, babanta ya zigata, ta rabu dashi. Saboda yasan yadda take da masifar kishi, kuma tana da zuciya. She can leave him, and she will indai har ta samu support daga gurin iyayenta, abinda yake tsoro matuka kenan.
"Baby," yafada yana ƙoƙarin riko hannunta.
Ta fauce tana fadin, "Just say yes. Saboda ni se na je."
Murmushi kawai yay, saboda yasan ba zata taba iya fita a palace ɗinnan ba Izininsa saba Kuma ita ma tasan ba zata iya din ba. Shiyasa take masa bore nan.
"Se kin jefa kikace Islam? Nifa mijinki ne. Ya dace in ce bazaki abu ba, kice se kin yi. Eh Islam, why are you stubborn? Uhm? This is not the Islam I know Ba ta musu dani. Ince tayi abu, tace setayi."
Fashewa tai da kuka tana hada kai da gwiwa saboda abinda ta dade tana kunshewa a cikin ranta from safiya har dare.
"Kabarni in tafi, dan Allah. Indai ba so kake zuciyata ta fashe ba, pls, pls let me go. Idan Jr ne bashi suke farmaka ba, ka rikeshi. Ba zan je dashi ba. Ni in mutu ai, dama ka dena sona, bazaka damu ba," takarasa fadar maganar har zuciyarta.
Yasan she's in pain sosai, yarasa Kalaman da zeyi amfani dasu gurin rarrashinta…
A hankali yace, "Islam, waye yace miki da Jr kadai na damu? Kina tinanin nafison shi kanki ne, Islam? Both of you are part of me, ku din rayuwata ne. Bazan iya rayuwa batareda ɗaya daga cikin ku ba. Kuma har abada, bazan taba dena sonki ba, Islam. Kedin rayuwata ce," ya karasa, muryarsa a raunace. Shima kamar yay mata kuka. Saboda da yana da iko da zuciyarsa, wallahi da me bata izni ta kalli wata macen sama da ita ba a rayuwarsa. Sosai yake jin haushi da tsanar kanshida kanshifor hurting her like this. Da ace wani ze fada masa, shi da kansa ze saka Islam cikin irin wannan pain din da ze karyata har cikin zuciyarsa...
Kin dago wa tai, bare tai masa magana. Tanajin yadda ya saka hannu ya daukota kamar jaririya, ya dawo da ita saman gadon. Ya tsugunna gefenta yana gyara mata gashinta da ya rufe mata fuska. Idonta a rufe, hawaye na fitowa. Goge mata hawayen dake zirya a fuskarta yay
"Islam pls ki kalleni,"
Kin kallan nashi tai. Numfashi yaja har cikin ransa yace mata:
"Should I just take you away from all this? Mu tafi daga ni se ke, baby. I'll apologize to Mehtav and our parents later."
Da sauri ta bude ido tana kallonsa. Cikin idonshi take kallo, saboda sarai tana ganewa in yana karya ko yana fadar gaskiya. Amma this time around it's a mixed signal-ta kasa gane maganar da yake fada. Har cikin ranshine ko kuwa dai wasa yake mata?
"Really?" takarasa tana goge hawayen.
"Yes baby. Kinsan cewar nafisonki sama da rayuwata. And I can go to war with anyone for you-ciki harda wannan inconsiderate heart din tawa."
Murmushi yaga tayi. Se alokacin shima yasaki murmushi. Domin saukin kanta sometimes yana bashi mamaki. Ta shiga girgiza kai tana nuna masa gefenta, ya dawo ya zauna.
"Ai ni nace, 'nayarda.' Nobody force me. If I take you away from her after saying yes da kaina, na zama me son kanta kenan."
Shiru yayi, be ce mata komaiba. Don at this point, kaffa-kaffa yake da kalaman da ze ringa fada akan Mehtav agabanta karya zake taga kamar yana cin fuskarta ne.
"She's good," tafada tana kallonsa. "Kawai dai kasan dole nai kishi. Saboda I've always wanted you for me alone, Sire. But muna tamu, Allah natashi. Just promise me you won't ever stop loving me the way you always do."
Yace, "I promise baby. You'll always have your special place. Billah, ba wanda ze kwace miki wannan matsayin."
Murmushi tayi before tace, "Tohm, ka barni in je vacation ɗin pls." Tana marairaicewa.
"I just can't bring myself in je bikinka. It's too much."
Dan jim yay kafin yace, "Okay. Since the wedding is happening in Nigeria week ɗin, I'll take you to your parents myself. Zan damkaki amana a hannun Mr. Zion, you and Jr."
"Ni inason da inje gobe, before the engagement,"
Girgiza kai yay. "Ban yarda ba baby. You can stay in this mansion. Base kin je gun engagement ɗin ba, amma you're not going anywhere kafin week ɗin auren."
Jim tai kafin tace, "Okay," tana zumbura mishi baki, irin ba haka taso ba. Tace, "Ba komai. Allah yakaimu."
Murmushi yay yana fadin, "Baby"
Tace, "Na'am?"
"Allah yay miki albarka," yafada yana jawota saman kirjinshi.
It's fatoumspassion Share Comment Like & Vote [19/07, 20:56] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
It's Fatoum's Passion - EHSAAS, another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.