Chapter 52
Hall ɗin taron dake cikin palace ɗin ya cika da wani mahaukacin ƙyalli. Ga wani ƙamshi dake tashi ta ko'ina, da royal flute da ake busawa cikin wani salo na asalin gargajiyar ƙasar NURISTAN.
Wasu crystal chandeliers ne suke sheƙi a saman hall ɗin, sai golden silk curtains - hadaddu - masu ɗauke da tambarin masarautar da aka lulluɓe bango da su, da wasu fitilu na diamond da suka cika ɗakin taron da hasken da ba zan iya fasalta muku ba, masu karatu - sai dai ku gani da idonku.
An yi decorating ƙasan hall ɗin da fresh white roses, lavender petals, sai royal blue and gold drapes tied in massive royal knots. A gaban hall ɗin akwai wani makeken stage inda ango da amarya za su zauna a saka zoben, zagaye da traditional drummers da mawaka.
Manyan influential people sun cika gurin daga ƙasashen duniya daban-daban. Duk sun hallara domin taya EHSAAS murna a wannan ranar. Ana ta hira sama-sama, masu hotuna na yi, reporters na ta aikinsu, suma ana musayar gaisuwa.
Har da masu ɗan rausayawa kafin isowar prince. Sai da aka sanar da isowar Prince EHSAAS da mahaifiyarsa Fulani Hajar, giwar King NASHWAN, da Prince EHSAAS Jr, sannan gurin ya ɗau wani shiri. Suka shigo, ana ta yi musu kirari. EHSAAS na ɗan daga wa jama'a hannu cikin salon amsa gaisuwarsu da jinjina gareshi da mahaifiyarsa. Kowa burinsa ya karasa inda za ya zauna, ya je ya gaida shi.
Manyan matan da suka samu halartar gurin Fulani na karasawa bangaren mata suka yayyameta. Ana ta "masha Allah wannan EHSAAS" ƙarami ne. Kowa yana mamakin yadda ya yi saurin girma haka, har da masu cewa za su ɗauke shi. Politely, Fulani take murmushi tana declining request ɗin duk wanda yace za ɗauke shi. Suka ci gaba da gaisawa da jama'a, tun suna na cín ɗaukar nashi har suka hakura suka bar mata shi. Shi kam sai kalle-kalle yake yi, abinka da ba ya saba ganin irin wannan taron ba - ya makalkale ta.
Masu yi mata jimami akan condition ɗin Mai Martaba suna taimaka mata. Da masu neman jin gulma a bakinta, saboda kusan kowa ya ji abin da ya faru da Mimah da mahaifiyarta - gashi gurin duka ba a ga ɗaya daga cikinsu ba. Amma uffan Fulani ba ta ce musu komai akan maganar ba. In sun mata jaje, godiya kawai take, ko ta yi musu murmushi. EHSAAS karasowa yayi ya zauna kusa da tawagar Royal Council na NURISTAN, yana karɓar gaisuwa da fatan alheri daga mutanen da suka gayyata iri-iri. Ba jima da zuwansa ba, aka fara shelar isowar amarya. Maroka na zuba mata kirari, kowa idonsa ya koma bakin kofa, ana son a ga matar da Prince ɗin zai sake aura.
Sai da ta ɗau mintuna kusan biyar sannan Abeey ta fara shigowa cikin wata haɗaɗɗiyar designer babygown, da gyalenta da aka saka mata a saman kanta har jan ƙasa yake yi, da wata haɗaɗɗiyar rose fara tas a hannayenta. Tana murmushi tana gyara eyeglasses dinta. Tun daga can ta hango EHSAAS, tana mai murmushi. Duk wanda ta juya ta haɗa ido da shi, sai ta mai murmushi.
Kowa ya miƙe tsaye yay ganin EHSAAS da kansa ya miƙe tsaye don ba ta girma, aka kunna turning light ɗin gurin zuwa dim daidai lokacin da Mehtav ta yi stepping in, hannunta cikin na Paa, cikin wata royal turquoise silk ensemble da aka saƙa da handcrafted zare na zinariya. Da veil mai tsayin gaske be walwali da ya ji diamond stones a jikinsa ya lullube mata jikinta gaba ɗaya. Rabin fuskarta a rufe yake kamar yadda al'adar NURISTAN take - ba sa exposing faces ɗin matayensu to the mass media.
Gaba ɗaya kayan jikinta Bvlgari bridal set ne da worth ɗinsa ya kai $1.2 million US dollars. Hannayenta da wuyanta kuwa wasu haɗaɗɗun gold sets ne da Fulani Hajar da kanta ta zaɓar mata su.
Wani irin glowing take - farar fatarta na kyalli tana ɗaukar ido - saboda fatar idonta da saman girarta duk a waje yake. Kowa zuba mata ido yay. Camera crews, bloggers, da royal documentation team suna ɗaukarta hoto tun daga shigowarta har zuwa lokacin da ta karasa daf da wurin zaman da aka tanada mata ita da EHSAAS.
Har gaban EHSAAS, Paa ya kawo ta. EHSAAS ya kasa ɗauke idonsa daga kanta saboda wani mahaukacin kyau da ta mai - ji yake yi kamar ya karɓe hannayenta daga cikin na Paa, musamman da yake ganin wannan jan lallen da aka yi mata ya fito yayi dodar a saman fatar hannayenta yana haskawa, abinka da farar mata. Da ƙyar ya iya riƙe kansa. Bai taba-taɓa ba har sai da Paa ya zaunar da ita, tukunna EHSAAS ya ƙara da ya rungume Paa yana masa godiya. Shima rungume shi yay kafin nan ya koma gefenta ya zauna yana ɗan bada tazara a tsakani su saboda yasan all eyes are on him kuma ba a rigada an ɗaura aure ba - yana kai hannayensa jikinta ze zama latest news a NURISTAN gobe.
"You look amazing, my bride," ya faɗa yana ɗan juyar da kansa gefe kamar ba da ita yake magana ba. Idonta a ƙasa, sarai yasan ta ji shi, amma ƙala ba ta ce masa ba. Gashi ba damar ya ƙara matsawa daf da ita, haka suka yi zaman shiru har aka fara gabatar da al'adun da suka dace da tsarin Musulunci da na masarautarsu.
Labule aka saka tsakaninsu da masses, kafin nan aka bawa Mehtav damar zamar da fuskarta saboda EHSAAS ya ganta da kyau. Kallonta yayi na tsawon minti daya don ya gane ta mai ko ba ta mai ba - al'ada ce da ake yi tun tale-tale, tun zamanin da ake yin arranged marriages a ƙasar.
Tana zame niqab ɗin, ya zuba mata ido. Idanta a ƙasa, ya bi kyakkyawar fuskarta da ta sha makeup - ya mata bala'in kyau. Kallo yana godewa Allah daya ba shi wannan kyakkyawar halitta a matsayin mata. He just can't get enough of her. Ba san har mintina sun cika ba sai gashi an ba ta umarnin ta maida niqab dinta.
Aka tambaye shi. Tayi ɗan murmushi. Yayi - yana cigaba da kallonta ƙasa-ƙasa, don ta ƙi yarda ta ɗago ta kalle shi ma balle su haɗa ido. Yace, "Not bad." Juya wa tayi a ɗan mamakance tana kallonsa. Da sauri ya saki shegen murmushi ganin ta kallesa - su haɗa ido - dama abinda yake so kenan.
Ya kalli Mother Fariha da ta tambaya, yace, "She's more beautiful than the moon itself." Da sauri ya ga ta sauke kanta, ya shiga murmushi shi shi kaɗai. Mother Fariha ta shiga girgiza kai a ranta tana wondering, shidai Prince baya iya boye soyayyarsa - a bayyane take. Tana tuna lokacin Princess Islam, ita ma haka ya ringa yi. Sosai take taya yaran murna da samun miji mai kyakkyawar zuciya kamar shi.
Jin ya amince ta masa, ya sa aka ce ita ma Mehtav ta kalle shi - ta gani. Ta ma ta ba ta kallesa ba, kawai ta ɗan jinjina kai. Yay smirking, yana binta da kallo har aka zarge labulen aka sanarwa da public cewa sun yi ma juna. Kowa ya ɗau kabbara kafin nan Fulani da kanta tana daf da su ta sa wa Abeey da ta zauna kusa da ita wasu small boxes da rings, tace ta kai musu. Paa already ya siya nashi saboda shima yasan iyalan amarya ke bawa ango zobe. Amma ganin already Fulani ta bawa Abeey, ta fara takawa zuwa inda suke a nitse babu garaje - saboda yadda ta sha warning gun Mehtav, ya sa kawai ya bar nashi cikin aljihun tuxedo ɗinsa.
Abeey na dire tray ɗin tana murmushi, ta shiga kallon EHSAAS da yayi ma Aman signal, shima ya kawo nashi guda biyu. Dariya aka fara yi ganin double engagement rings. Abeey tace, "Tohm, zata gani wanne za'a saka."
Murmushi EHSAAS yayi yana buɗe wanda Fulani ta bayar. Yace wa Mehtav, "Your fingers."
Stretching masa tayi yatsunta, yana kallo ba tare da ya saka zoben ba saboda yadda lallen ya tafi da shi. Sai da Aman yayi gyaran murya ganin ana ta ɗaukar hotuna, ya sa gently ya shiga saka mata a yatsanta na biyu ba tare da ya riƙe hannayenta ba. Cif-cif, ita kuma gold ne.
Yana gamawa, ta ɗunkule hannun guri daya, tana dawo da shi jikinta wanda Aman ya buɗe. Ya sake buɗewa yace, "The left hand."
"Wow wow!" aka fara cewa - because like abun ne - saboda a ga bride tayi getting two engagement rings at the same time. Ta ɗan kalle shi, ya ɗage mata gira ɗaya kafin yace, "This is mine," a hankali - gudun kada wani ya yi detecting maganar - "and ɗayan is Maama's."
Murmushi ya ga tayi duk da baya ganin fuskarta kafin ta miƙa masa yatsunta. Ya zira mata a finger dinta na tsakiya. Aka shiga kabbara.
"Your turn, Your Highness," Abeey ta faɗa tana tsayawa a gefe nata bayan ta buɗe mata zoben da Fulani ta bayar. A hankali Mehtav ta ciro - tun ma kafin ta yi magana, ya miƙa mata hannunsa na hagu. Ɗan kallon hannun tayi saboda ta san ana dama ake sakawa. Jama'a ma ɗan kus-kus suka fara yi ganin ta tsaya - ba ta saba ba - ya sa ya dan yi murmushi yana ɗaga mata hannun damansa mai ɗauke da ring ɗinsa shi da Islam, yana faɗin, "Already taken." Sai a lokacin ta yi murmushi - ta zira masa kawai - saboda she's not in place to be jealous of woman like Islam.
Tana zira masa zoben, da ɗan jima sai suka ji fashewar wani abu da ya sa Mehtav tayi saurin toshe kunnanta kafin wata irin jiniya ta fara kara ta ko'ina:
WOOOOOONNNGGG!!! WOOOOOONNNGGG!!
Mai nuni da cewa wuta ta tashi a gurin ko wani gurin a cikin palace ɗin, jin fire alarm na tashi ya sa jama'a kowa ya miƙe, hall ɗin ya fara girgiza. Kowa ya cakude guri ɗaya, ana ihu:
"Fire!!! Fire!!!"
Kamar daga sama, hayaki mai duhu ya fara tashi daga bangon hagu na hall ɗin. Mutane suka fara gudu cikin ruɗani. Ana tura juna, ana kururuwa, ana ƙoƙarin ficewa daga hall ɗin.
Miƙewa EHSAAS yayi da wani irin mahaukacin sauri, yana kiran Aman da already ya fara tattara security, yana tambayarsu me ke faruwa. Ya kalli Mehtav da Abeey da suka rude gaba ɗaya, musamman Abeey da ta kankame jikin Mehtav. Kwantar musu da hankali ya fara yi yana cewa:
"Ku tsaya anan, kar ku je ko ina."
Aman ya ƙaraso yana mai rada a kunnen EHSAAS wanda ya sa ya yi saurin zaro ido yana faɗin:
"This is bullshit. What the hell? How comes? Who dare?!"
Duk a lokaci ɗaya kafin ya ajiye rawanin kansa yana faɗin:
"Lock all the palace gates right now. Protect the women. Take the children inside. Kada wanda ya bar palace ɗinnan!"
Yana balbala masifa ya kamo hannayen Mehtav da Abeey, inda Fulani take ya ajiye su. Fulani na tambayarsa me ke faruwa, yace mata ta kwantar da hankalinta - zai tackle komai. Yace su tsaya anan, kar su je ko ina.
---
Few minutes ago
1:15 PM…
Usman ya latsa capsule ɗin da ke gefen storage room, capsule ne mai fitar da ƙura da hayaki. Cikin mintuna biyu, ko ina ya ɗauka. Daga wajen katafaren kitchen da ake dafaffen taron aka fara ihun:
"Wuta! Wuta!" Amma ba wutar bace - kawai triggering smoke alert suka yi.
---
1:20 PM…
Wani secondary guard ya bar post ɗinsa jin ihun da yake tasowa daga kitchen ɗin bai ƙarewa - domin ya taimaka wajen evacuation.
Da wannan damar Usman yayi amfani, ya shigo cikin dungeon ɗin da key card da ake ajiye wa domin emergency release. Ya wuce cikin gaggawa yana juye-juye don kar kowa ya buɗe - already Mimah ta cimma rabin aikin buɗe dungeon ɗin, ta gama jigata.
A hanzarce ya ƙarasa buɗe gurin. Ƙoƙarin miƙewa tayi, jikinta gaba ɗaya ciwo yake yi. Da ƙyar ya iya zaro ta tana dafa bango ta fito. A gaggauce ta shiga tambayarsa:
"Did you bring the clothes?"
Ba tsayawa bata amsa ba, kawai ya zaro wata blue gown mai sauƙi da yake uniform na palace maid, da hijabi mai launin ruwan kasa. Mimah ta cire kayan ta da suka yi futu-futu, suka yi baƙi-kirin suka fita a hayyacinsu tsabar dauda. Ta sa sabon kayan cikin sauri.
Tana kammala saka hijabi ɗin ta miƙe tsaye tana kallon kanta kafin ta fashe da dariya tana faɗin:
"Now, I'm no longer a prisoner. I'm a maid. The Game begins."
Usman ne ya ja ta da sauri suka ɓace ta ƙaramin path da ke gefen warehouse na baya inda ake ajiye royal gifts. Suna fita a gurin, ya bi da ita ta cikin ƙaramin drain way wanda ke kaiwa zuwa old servant quarters na bayan prison. A can akwai wata ƙofar baya da babu mai kula da ita saboda ana lissafa ta cikin guraren da ba a amfani da su sai lokutan overflow.
Mimah ta saka maid hijab ɗin jikinta tana ƙara kare fuskarta har suka fito. A lokacin, dukkan palace ɗin ta rude da hayaki da ifa-ifacen jama'a, ana "wuta!" security na can da nesa suna gudanar da bincike da calm-down operation, don suna so su gane musabbabin hayakin da inda wutar ta fara.
Hakan ne ya basu damar wucewa zuwa cell ɗin Erfan. Suna tafe Mimah na kallon Usman tana tambayarsa:
"Are you sure he's still in that cell?"
Usman ya gyada kai. "Har zuwa last week, da kaina na kai masa magani. Duk ciwo ya cinye - ya rame - bai da ƙarfi ko kaɗan."
Mimah tayi wani irin murmushi - irin "ga damar da ta zo" - murmushin da yake bayyana ƙiyayya da zafi da take ji a lokaci guda.
Ba ta sake cewa komai ba har suka ƙarasa zagayawa sashen tsaro na royal prison, inda ake ajiye prisoners masu special circumstances, ciki har da tsofaffin officials da manyan masu laifi daga cikin royal lineage. Anan aka ajiye Erfan - tsohon Waziri na NURISTAN, kani ga Mai Martaba King NASHWAN, kuma biological uba ga Mimah.
Kamar yadda Usman ya tsara, bayan ƙarfe ɗaya da ashirin na rana, sabis na ruwa da wutan lantarki za su kashe kansu na ɗan lokaci saboda lalata wasu wayoyi da ya sa yaran sa daga sashen palace kitchen. Wannan yasa guraren detention da ke kusa da basement suka fita daga surveillance na tsawon mintuna goma zuwa sha biyar.
Suna shiga, Usman ya nufi sashen wardens don ya kalle mata har ta gama abinda zata yi - ba me shigowa. Ita kuma, cikin sanda kamar kadangaruwa ta shiga bin bango ta nufi cell ɗin Erfan.
Ƙofar ta shiga kici-kicin buɗewa da wani mabudi da ta karɓa a gurin Usman. Sai da ƙyar ta iya buɗewa. Ta tsaya cak a bakin ƙofa tana kallon wani tsoho mai kunnuwa nata - fuskar sa da rigarsa duk sun jike da gumi. Yana kwance a gefen gadon ƙarfe, yana ta haki kamar mai ciwon zuciya.
Sai da ta kafe shi da ido sannan ta iya gane ashe Erfan ne - ya dawo haka. Ta kalli kanta, tana kallonsa. Ashe ita da sauran kyanta ganinta ma kenan? So this is EHSAAS' plan? Ya kamasu ya garkamesu a prison, ya yi ta azabtar da su har su mutu, ya sa abin nasu ba tare da kowa ya san me ya yi musu ba, ba tare da an saka shi a jerin sarakunan da ke kashe 'yan uwansu ba.
Tabbas, she won't rot here. Never. Ba za ta taɓa bari rayuwarta ta kare kamar ta Erfan ba. Kuma daga yau, ta bar prison ɗin har abada. Kuma she's ready to kill - ko ita aka kashe ta - za ta yi fito-na-fito da duk wani mahaluki da zai shiga tsakaninta da burinta.
Ganin Erfan ya ɗago yana kallonta - yana haki - kamar ma bai gane ta ba yasa ta shiga zagaye ɗakin tana kare wa ko'ina kallo kafin tace:
"Na daɗe ina jiran wannan lokaci, ranar da zan yi gaba da gaba da kai - bayan ka zama silar tarwatsa rayuwata. Don kaima in rama wulakantar da taka."
Bude idanu yayi da ƙyar, yana kallonta kamar bai yarda da abinda yake gani a gabansa ba. Yana haki ya fara kiran sunanta.
Tace, "Eh, nice. Ni Mimah dai. Daka tozarta."
Cikin in-ina ya soma faɗin:
"Mimah… na gaya miki gaskiya ne… ban yi hakan da niyyar cutar da ke ba... se don-"
"Gaskiya?" ta katse shi da karfi, tana aika masa wani irin mugun... "Gaskiyar da ta lalata rayuwata? Gaskiyar da ta sa aka daina kirana da only Princess of this kingdom? Gaskiyar da ta sa aka fara kirana 'yar zina? Gaskiyar da ta sa EHSAAS ya samu dama da lasisin wulakanta ni son ransa ba tare da ubanmu ya ce mai komai akan hakan ba? Ko kuma in ce ubansa, don shi kadai ya haifa ban dani ko?"
Ta fada hawaye na fitowa a idonta at the same time tana dariya. Wukar da ta boye a goben kugunta ta daga doguwar rigarta ta ciro tana kallonsa. Zaro ido yana kallon sharp blade ɗin da yake kyalli. Kana ganinta kasan sabuwa ce fil. Ya rare baki zai yi ihu, ta shiga girgiza masa kai tana dariya tace: "Don't shout, Uncle... ko should I say Father? This..." ta ce tana tsugunnawa kusa da shi, "is for being foolish enough to give birth to me. A zinace zinacenka ban dauka kana da ƙarfin zarrar haihuwar mutum kamata ba. Amma ina jin nazo ta tsatson kane don na kawo ƙarshenka, Erfan."
Ta yi slicing wukar a gefen wuyansa kaɗan, ba sosai ba. Jin zafin yankan ya sa Erfan ya buɗe baki yana cije leɓe cikin azaba. Mimah ta ci gaba. "This... is for daring to expose my identity in front of the King who raised me like his own."
Rokonta ya shiga yi yana ƙoƙarin miƙewa don guduwa. Ta bára da shi a ɗakin, ya faɗi jikin ba ƙwari, duk ya saki. Ta tsugunna a gefensa tana fadin: "Daga yau idan aka ce ka ƙara kusantar wata mace, ka yi zina da ita, ba za ka sake ba. Don zan dandana maka azaba wadda tun da uwar ka ta haifeka, ba ka taɓa jin irinta ba a rayuwarka. Sai yau, ni 'yar cikinka, 'yar da ka haifa ta hanyar zina da matar kaninka, zan dandana maka." Ta ƙara da cewa tana jan yaron kusa da ita.
Ya shiga ihu, amma tsabar ya yi weak, muryarsa ba ta fita. Wukar ta zira, ta yi slicing a ƙarƙashin ƙugunsa, cutting deep around his private part. Cikin hargowa, jini ya kwaranyo. Erfan ya saki wani irin ƙara mai tsanani, da ya sa ta sa ƙafarta tana take bakinsa. Yana fidda numfashi da ƙyar, ya shiga ƙoƙarin ƙwacewa. Mimah ta rufe bakinsa ruf da ƙafarta.
Tana wata dariyar mugunta take fadin: "Ka daina ƙoƙarin tara min jama'a. Ba kashe ka zan ba. No," ta ce cikin ƙeta, "that's too easy."
Ta tsaya, tana kallon yadda jini ke kwaranya ta ƙasansa. Ta sa ƙafarta ta hagu ta sake taka gurin, tana huci kamar wata zakanya. "Zan bar ka da rai. Amma ka sani, sai ka gwammace kashe ka nai a kowace rana."
Wata riga ta hango an yi hanging dinta. Da sauri ta fizgota, tana tsugunnawa ta kama bakinsa ta ɗaure. Jijjiga kawai jikinsa yake. Ta soma lalube a ɗakin, wani medical note ɗinsa ta gani a gefen gadonsa. Daidai Usman na dawowa yake gaya mata they need to go yanzu, saboda Prince ya nufi dungeon ɗinta. Da sauri tace masa ya ba ta ashana, jikinsa na rawa ya ciro lighter a aljihunsa, ya jefa mata.
Medical notes ɗin ta sa wa wuta, ta jefa a cikin katifar gadon da ke gefen rufin tabarma. Nan take, hayaki ya soma tashi. Sai da ta jefa chemical rag da Usman ya ba ta, ganin wutar ta soma ci balbal, yasa ta yi murmushi tana fadin: "You should have died before you brought me into this world. But now, you will suffer every second for who you are and what you've done."
Ta ja ƙofar ta garkame tana dariya. Usman ya tsaya kawai yana kallonta, yana girmama kalar mugunta irin tata. Fitowa suka fara yi, ita kaɗai take fadin: "Daga EHSAAS ɗin... har Mai Martaba ɗin... da arniyar yarinyar nan Peace... Since they all chose to betray me, I'll make sure the pain they gave me... spreads like fire."
Usman yace, "Princess, we need to leave. EHSAAS ya kulle ko'ina na wannan fadar."
Dariya ta shiga yi tana fadin: "Waye yace maka na fitone don na fita? Uhmmm uhmmm... na fitone ayi tafanjama fanjan, ko in mutu ko nai rai, sai na ɓakanta wa duk wanda ya ɓakanta min rai. Ina men din?"
Yace, "They are ready a gaban hall ɗin, amma an samu akasi, Princess bata zo taron nan ba kuma sashenta is highly secured." Kallonsa ta yi tana ɗan waro ido kafin ta sheƙe da dariya tana fadin: "Oh oh dear Peace, she most be mourning saboda ta rasa mijinta. Ga wata shiyasa kullum nake fada mata, namiji ba dan goyo bane ba. Namiji kanin ajaline. Gashi nan, yayi mata halin nasu."
Ta ci gaba da dariyarta kamar ta Babbiya kafin tace: "What about the Queen Mother? She most be very, very happy. Danta ze sake aure. Na san tazo. Mu kamata kawai. Kaga in muka kamata, both Mai Martaba da EHSAAS will be in pain kamar yadda suma su sani."
Tsananin tsoro yasa Usman yace: "Gimbiya, ki gafarceni, amma mun ga an shiga da yaron nan gurin taron nan fa. Mai makon mu kama Fulani, gwara mu kamashi kawai tunda shi jariri ne."
Zaro ido ta yi kafin tace: "Interesting. I want the baby and the Queen Mother at the same time, right away."
Daga cikin hall ɗin kuma da ƙyar aka samu kowa ya tsaya a inda yake bayan EHSAAS yayi making sure everyone is fine, ya fita, ya sa aka kulle ƙofar don yana son yaga menene musabbabin hayakin tare da Aman. Fitarsa keda wuya, wutar gurin ta ɗauke duf, hakan ne yasa hayaniya ta sake kaurewa. Duk yadda security suka so controlling dubban jama'ar da ke gurin, ƙasa suka yi. Wasu garin gudu suka fice, har suma da su akai.
Ta glasses ɗin wajen suka hango wuta na ci ta wani sashe daban na palace ɗin. Gudun kada ta ci da su ne yasa jama'a suka jijjige ƙofar, aka fara ficewa. Hayaki ya ƙara tirnike gurin. Tuni Inna ta yi waje, Paa se laluben yayansa yake, bai gansu ba. Gaba ɗaya hankalin kowa a tashe yake a gurin. Su kuma suna gefen Fulani da take wani irin mugun tari kamar kirjinta zai fito. Cough after cough. Severe wheezing ya kama ta. Babbar damuwarta ita ce tasan there's something wrong. Something deeper. Ganin EHSAAS yasa aka kulle su, tasan dole matsala ce babba. Gashi an buɗe - anything can happen, ta raya a zuciyarta tana tarin Jr na jikinta.
"Someone set this palace on fire… and it's not ordinary," ta faɗa a hankali tana kallon baby EHSAAS Jr da ke kuka, shima ganin tashin hankalin da ke faruwa. Gashi ba ta da ƙarfin gudu balle ta fice a gurin. Yasa ta dubi Mehtav da ke tai mata sannu, ita da Abeey da ke kuka.
"Mehtav!" Fulani Hajar ta kirata da sauri tana ƙoƙarin tsaida tarin da take yi. Ta shiga miƙa mata Jr.
Mehtav ta juyo da sauri, zuciyarta cike da rudani, tana kallon Jr da ke canyara kuka.
"Take him," Fulani ta faɗa tana ƙara miƙa mata shi. "Take him and run. Save him... Ko me zai faru, kada ki bar wani ya karɓe shi daga hannunki. Protect him, pls!"
Mehtav rufewa tai tana karɓar Jr, ta shiga faɗin: "Amma..."
Ba ta barta ta ƙarasa faɗar abinda zata faɗa ba, tace: "GO! Ku tafi, kun ji?! Save yourselves! Abeey, kema ki bita!"
Abeey ta cukuikuye Mehtav, ta ba kallon Fulani da ke tari kamar za ta mutu. Mehtav kamar ba za ta tafi ba, Fulani ta sake daka mata tsawa tana ce mata: "GOOOOO!" tana nuna mata hanya.
Da sauri ta juya cikin gaggawa ta nufi ƙofar da taga jama'a na ta wucewa. Suna fita, Abeey na makale a bayanta. Ba ta san ko ina a cikin palace ɗin ba, hakan ne yasa kawai take cilla kafarta duk inda ta daura. Tsintar kanta tai cikin wani lambu tana kalle-kalle tana ƙoƙarin nema musu hanyar fita. Ga Jr ya ƙi yin shiru, yana ta kuka. Abeey ta nuna mata wata hanya tana faɗin: "Kamar ƙofa ce waccan. Yah Mehtav, let's go." Da sauri suka nufi gurin. Sai dai kafin su kai ga wucewa, faɗa suka ga ya barke tsakanin wasu dagarai da wasu mutane masu bakaken kaya. Da sauri suka ɓuya a gefen wata pillar, tana tattaro rigar ta, ta lullube Jr tana ƙoƙarin rufe bakinsa don ya ƙi yin shiru.
"Shhh... please, Jr... just stay quiet," Abeey ta faɗa, muryarta na rawa, tana rukunƙume shi da Mehtav. Sun jima a gurin. Jr kuma kamar yaji maganarta, sai yayi shiru. Jin shiru yasa suka fito da sauri suka nufi Garden Exit ɗin. Abeey ce a gaba, da sauri ta fizgo ƙofar ta buɗe, ta fito tana wa Mehtav alamar ta hauro itama. Kawai taji an toshe mata baki da hanci. Struggling kwacewa take amma ta kasa. Mehtav jikinta ne ya hau rawa ganin wasu garadan maza guda biyar a ƙofar gurin, ɗayanne kuma ya riƙe Abeey da take mutsu-mutsun kwacewa. Ihu Mehtav ta fasa tana roƙonshi ya sakar mata 'yar'uwarta. Amma ba ya sakar Abeey har sai da ya tabbatar ta sume, ba ta numfashi, tukunna. Ya watsar da ita a gefe daya yana kallon Mehtav. Dayan ya nuna masa ita, ya ce:
"There she is! Ita ce naga ta fito da yaron!"
Zuciyarta na bugawa, ta ƙara lullube Jr a mayafinta.
"What do you want?!" ta faɗa da ƙarfin hali.
"Ba ke muke so ba. EHSAAS Jr muka zo karɓa. Give him to us and you can go."
"Over my dead body!" Mehtav ta faɗa, tana ja da baya, tana ƙara rungume yaron a kirjinta.
Dayan ne ya soma dariya yana faɗin: "Amarya, ki ba mu shi kawai ki wuce abinki. Za ki haifi wani Yarima naki nan gaba, amma dai wannan, ki ba mu shi kawai."
Girgiza kai ta shiga yi, tana baya-baya, tana neman faɗawa da gudu. Taku biyu ɗaya daga cikinsu yayi, ya cafkota. Yana ƙoƙarin kwace yaron da ƙarfi da yaji amma ta hanashi.
Wuka ɗayan ya ciro a jikinsa yana nuna mata alamar in ba ta ba shi ba, zai lume mata. Amma fafur, Mehtav ta hana shi yaron nan. Jr ya saki kuka jin ana wujijjiga da shi. Faɗawa Mehtav mari ɗaya yayi, cikin kukan azaba take faɗin: "Kada ku kuskura ku taɓa shi. Zan kashe duk wanda yace zai taɓa shi!"
Ganin za ta kawo musu cikas a cikin aikin nasu yasa ɗayan ya buga mata bakin bindiga a keyarta. Ta durƙusa ƙasa. Amma duk da haka ba ta saki Jr ba. Numfashinta na sama-sama, suka ɗaura wani black cloth a bakinta, suka ɗaure hannayenta da igiya.
"Idan ba za ki ba mu shi ba, sai mu tafi da ke!" ɗaya daga cikinsu ya faɗa cike da jin haushin bata musu lokaci da Mehtav tayi.
Daga ita har da yaron suka tattara suka wuce da su ta cikin corridor ɗin baya. Suna shiga ta hanyar da ba a cika bi ba - wani soro mai haɗe da Old Storage Wing. Mehtav na jijjiga a hannunsu, jini na zuba daga gefen wuyanta. Ba ta san me suka yi ma Jr ba. Duf, taji ya daina kuka.
Kamar a mafarki, taji muryar EHSAAS yana ƙwala mata kira, amma yayi mugun nisa da su. Nisan da tasan kila har su isa inda za su je, ba zai kamo su ba. Cike da rauni, take ƙoƙarin buɗe baki itama ta kira, amma ta kasa saboda daure mata bakin da suka yi cikin dabara. Duk da daure hannayenta sukai, ta cire engagement ring ɗinsa, ta zubar a ƙasa, cike da hope na cewa koda Allah ya sa ya biyo ta, hanyar zoben zai yi leading dinsa zuwa inda suke.
It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Comment Like & Vote. [25/07, 19:46] Fatima Rufa'i Nasidi: It's Fatoum's Passion - EHSAAS, another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.