Chapter 53
Sanarwar da EHSAAS yayi arufe ko ina na cikin masarautar - ba me fita, ba me shigowa - ya dada daga hankalin al'ummar da suka zo bikin, tare da gargadi mai nauyi wa 'yan jarida akan duk wanda ya fitar da labarin abinda ke faruwa a palace ɗin ba tare da izni ba, sai an yi beheading dinsa. Hakan ne yasa kowa ya zauna yayi jigum-jigum.
Inda suka fara gano kan hayakin da kuma gobarar da ta tashi a cikin prison ɗin, EHSAAS na zuwa dungeon ɗin ya ganshi a buɗe, al'amari babu kowa. Ya gane tabbas aikinta ne. Hakan ne yasa ya kalli Aman tare da ce masa ya je kawai ya sallame shi domin baya son ya saka shi a cikin aikin tozarta mahaifiyarsa, domin yasan haɗuwarsa da Mimah ba zata taɓa yin kyau ba.
Girgiza kai Aman yayi yace wa EHSAAS ba inda ze je, enough is enough, it's time for them su yi bringing abubuwan da take aikatawa. Ba don ya so ba haka ya bar Aman ya biyo shi. Suna komawa hall ɗin suka samu har maids sun wuce da Fulani Hajar babban asibitin masarautar, sakamakon hayakin da ya shige mata kirji yasa ta yi passing out.
Hankalinsa bai dada tashi ba sai da ya nemi Mehtav, Abeey da Jr ya rasa - gashi duk wanda aka tambaya inda suke sai ace ba a gansu. Inna sai rabza kuka take yi tana dada daga masa hankali. Da ƙyar ya kwantar mata da hankali ita da Paa, duk da dai shi namiji ya dan iya controlling damuwarsa ba kamar ta taba.
EHSAAS yayi masa alkawarin zai dawo masa da su safely in sha Allah. Yasan Mimah is after the prince, so kar ya damu - in sha Allah babu abinda zata iya ma yaran. Suke kawai su jirashi, yana nan dawowa. Paa duk yadda yaso yabi tawagar EHSAAS, kin barin shi yayi. Yace baya son ya sa rayuwarsa a haɗari. Haka yasa aka wuce da su sashensu.
Straight daga nan sashen Islam ya nufa. Security ɗin da ya saka suka tabbatar masa da cewa har lokacin tana ciki bata fita ba. Ya jinjina kai yana wucewa surveillance room na sashen - wanda bayan dawowarsa ya kirkiri dakin, ko Islam da suke kwana tare, suke tashi tare, bata san da wannan dakin a sashen nasu ba. Daga shi sai Aman suka san da dakin, bayan sun zagaye masarautar ƙafa da wasu irin mahaukatan CCTVs asirrince bayan official wacca ake da ita.
Ta camera ya ga inda su Mehtav suka fito tare da Abeey da yadda suka je garden, har da ɓoyewar da suka yi, da inda suka fito aka sumar da Abeey - duk sai da ya gani.
EHSAAS zuwa yanzu zuciyarsa ta gama tafasa. Aman ya dan dafashi ganin yadda katon ya shaqo Mehtav, yasa ya daga system ɗin dake gefe, ya buga ƙasa yana ɗauke kansa daga kan desktop ɗin.
"I will kill him, I must kill that man," ya faɗa yana nuna camera da hannunsa, kirjinsa na tafasa kamar zai faso ya fito. Aman ne yake gaya masa ya kwantar da hankalinsa.
Daidai nan aka kira su a waya aka sanar da su Erfan da aka wuce da shi asibiti, fa jikinsa yayi tsamari. Ai kiraye sunan EHSAAS yake yi wai ko zai samu yazo.
Wani irin mahaukacin tsawa EHSAAS ya dakawa likita ɗin da yake mai wannan maganar banza - a halin da yake ciki yace, "Ya mutum mana, sai meye?! Let him die! I don't fucking care!"
They all deserve what they get, ya ƙare maganar yana nufar ƙofar, yana cewa ma Aman ya tabbatar labarin abinda ke faruwa bai isa kunnuwan Mai Martaba ko Islam ba.
Kaci-bus suka yi da ita saboda ƙarar fasa computer da ta ji tana library tana karatu, ta fito ta duba waye ya shigo. Sanin ba me shigowa sashen nasu in ba dai su ne suka buƙata ba, ganininsa a birkice gaba ɗaya - ya ma cire rigar samansa da rawaninsa - yasa ta dan wara ido tana kallon dakin dake desktop ɗin, gaba ɗayane a dakin da wata katuwar TV da ta cika bango ɗaya. Kawai idonta ya sauka a daidai inda suka yi force, katon nan ya shaqo Mehtav da ɗanta a hannunsa.
In disbelief ta shiga kallo da sauri. Aman da EHSAAS suka tare view ɗinta don kar ta ci gaba da kalla. Da sauri ta yi kan EHSAAS tana ƙoƙarin matsar da shi tana nuna screen ɗin.
"What... what happened? Is that Mehtav and J... Jr, Jr Sire?" ta faɗa tana kallon fuskar sa domin ta gaza fahimtar video ɗin - na magani ne ko menene?
"Calm down Islam, look at me." Numfashinta ne ya shiga sama-sama. Lokaci ɗaya yaga idonta yayi jajir tana matsar da shi gefe. Da sauri ta yi playing, ya ci gaba. Wani baya-baya ta fara, numfashinta na ƙasa da sama. Da sauri ya ja ta jikinsa yana faɗin:
"Look at me Islam, nothing will happen to them, I promise you. Zan dawo miki da shi lafiya."
Hawayene ke fita ta gefen idonta sanda ta gama zubewa a jikinshi. Numfashinta na seizing, take faɗin:
"My baby, my child, Sire... pro..." Bata ƙarasa ba, ta sume baki ɗaya.
Wani irin tashin hankali ne ya sake lullube shi. Ya shiga jijjigata yana kiran sunanta amma bata responding. A mugun sauri ya ɗauketa, ya fice da ita, ya bar Aman a gurin. Sai asibiti, da kanshi ya ajiye ta har cikin emergency room, likitoci suka shiga dubata.
Daidai lokacin da aka shigo da Abeey, itama da Aman ya sa aka ɗauko - in no time aka shiga dubata. Dake suna da wadatattun likitoci, cikin ƙankanin lokaci gaba ɗayansu suka samu kulawa mai kyau, aka sa musu oxygen.
Lokacin da likita ya tabbatar masa ba wata damuwa babba, har Fulanin na, ya sa hankalinsa ya dan kwanta. Kamar mai rada ya ce ma likitan:
"Yaushe ta fara samun panic attacks?"
Dake likitan tane tun asali, ya ce masa ta jima tana fama da matsalar tun bayan haihuwar Jr da fake news ɗin mutuwarsa. Ya ce masa yaushe zata farka. Yace:
"Anytime soon."
Kallon dakin da Islam take yayi, ya kalli agogonsa, yace yana so ya yi mata allurar barci da zata kai ta zuwa dare bata farka ba. Da jin hakan, likitan yayi kafin yace babu damuwa. Da sauri EHSAAS ya mike ya fito yana amsa wayar Aman dake sanar masa cewar babu camera ɗin da ta nuna an fitar da su daga cikin gidan nan - that means har yanzu suna nan, babu inda suka je.
Jinjina kai yayi bayan ya ƙara wasu irin mahaukatan securities a asibitin. Ya ƙarasa garden ɗin inda aka tsinci engagement ring ɗin Mehtav, ta cikin lungun da akabi da ita aka boye.
Karɓar ring ɗin yayi yana jujjuya shi, Aman na nuna masa ƙarshen footage ɗin fitowar Mimah bayan ta tada gobarar sashen prison ɗin. Da aka ajiye Erfan, sun buɗe wata rijiya, sun shiga da inda 'ya'yanta suka yi da Mehtav.
Idonsa jajir, ya shiga daga murya cikin ƙarsashi, yake faɗin:
"Gather the team. We move in now," yace yana duban Aman.
Aman ya amsa masa cikin ƙankanin lokaci. Yayi gathering na special team ɗinsu. Palace ɗin ko ina tsit kake ji kamar an yi mutuwa.
Bayan ya zira zoben cikin aljihunsa, cikin gargadi jami'an tsaro yana faɗin:
"Wannan aikin family rescue ne. No gunshots unless necessary. Jr is only a baby. Mehtav is possibly restrained. We go in, we get them, we return alive. Kowa ya gane?"
Suka kada kai da ƙarfi, zuciyoyinsu cike da fushi da ƙarsashi.
A yadda suka shirya komai tare-tare, za su yi wa Mimah ta yadda idan suka tarfa ta, there's no way out zata iya tsira daga tuƙkun da suka ƙulla mata.
Daga bangaren Mimah kuwa, bayan sun isa maboyarsu, zama tayi tana watching live feed daga na'urar surveillance da ta sa Usman ya saka a dakin da aka ajiye Mehtav da Jr. Tana zaune, an jere mata makamai iri-iri a gabanta. Daidai lokacin babban yaron babarta yana shigowa yace:
"Mun kai su. Komai ya tsaya kamar yadda kika tsara. Prince ya rikice, yanzu haka ma yana asibiti kamar yadda kika tsara. Hankalinsa ya rabu biyu saboda mamarsa da gimbiya Islam da suka sume mar."
Murmushin mugunta ta saki, tana tafa hannu jin wai Fulani na asibiti kenan dai - itama ta san daɗin nata har ta suma saboda an kama mata jika an daure. Ita tata uwa tace me? Da aka kamata aka ajiye tsawon wata da watanni. Ta shiga jinjina kai tana faɗin:
"Good. Yanzu ina so a fitar da message. A bayyana wa duniya cewa EHSAAS bai isa ya kare Palace ɗin NURISTAN ba, balle Kingdom ɗin gaba ɗaya. A gaya musu gaba ɗayansa ya dawo tafin hannuna, and he has to beg for mercy kafin in wulakanta shi sannan in yi musu kisan gilla a gaban idanuwansa. Ita ce fansar abinda ya yi min a rayuwa."
Ganin yaron ya ƙi motsawa yasa ta dago tana kallon shi tace:
"Me kake jira? Ba zaka hau social media yanzu ba? Ka turawa duk gidan jaridu da mujallu."
Yaron wiki wiki yayi da ido yana faɗin:
"An kashe network ɗin palace ɗin gaba ɗaya. In dai ba ni da 'ya'yana ba, yau dai babu wanda zai iya fitar da wani abu daga palace ɗinnan ta hanyar yanar gizo-gizo har ta bakin ma."
A fusace ta mike tana faɗin:
"Ina Usman?! Nace ina Usman?!"
Yaron yace:
"Shi ne tsaye akan amaryar. Yarinyar na da ƙwarin rai - tun da ta farfaɗo take ba mu ciwon kai."
Hannu ta ɗaga, ta kwaɗa masa mari tana faɗin:
"Ai shiyasa ni ban saka ku ku ɗauko ta ba. Ni Fulani Hajar nace a da ita kuka ɗauko, da tuni EHSAAS yazo har ƙasan kafata ya fara rokona. Na tabbata wannan amaryar bata kai mahimmancin uwarsa ko matarsa ba. To me yasa zaku kamo min mara amfani?"
"Amma in yasan wata, bai san wata ba. Yadai hana labari fita ko? Idan aka kashe amaryar da zai aura, ai dole ko ya ƙi, labarin zai fita."
Ta ƙarasa tana ɗaukar pistol, ta boye a kugunta tana hambare shi da ƙafarta, ta fice a gurin duk da gargadin da Usman yake mata, yana cewa ta zauna anan, karta fita har sai an ba ta izini.
Amma sam, ba zata iya jira ba. Za ta je ta fara azabtar da su ne - ta yadda zata turama EHSAAS bangare-bangare na jikinsu, kila zai shiga hankalinsa ya zo ya roketa.
Ta underground tunnel ɗin ta bi, ta ƙarasa dakin da Mehtav ke ciki. A kwance, sun ɗaure mata hannaye da ƙafafu. Sai murkususun ƙoƙarin kwancewa take yi - ta kasa. Idonta a lumshe, tana kallon cikin ƙajin da suka ajiye Jr. Taji dai yayi shiru, ba ta san me suka masa ba.
Takun da ta ji yasa ta buɗe idanuwanta - suka sauka akan Mimah da ta shiga, zagaye ta, tana ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa, kafin ta tsugunna gefenta tana ɗan bugun gefen fuskarta da hannayenta. Irin ta tashin nan tarwai, idonta suka buɗe tana kallonta.
"Menai miki? Me jaririn nan yay miki? Don Allah kiyi hakuri, komenene ni, kirikeni ki maida jaririn nan gurin iyayensa. Nasan mahaifiyarsa tana cikin matuƙar damuwa. Don Allah ki kyaleshi."
Kyalkyalewa da dariya Mimah tayi tana tafa hannu tace, "What? Are you for real? Mehtav kike? Kowa your asking me in mayar wa da matar da take shirin zama kishiyarki, danta wanda ze zo ya zama heir a wannan masarautar? Kodai makircine irin na mata?" ta fada tana zama a ƙasan gaban Mehtav tana kallon yadda ta galabaita.
"You can be free with me. Kibarni in kashe shi kawai, ke kuma in sake ki. Kinga se ki haifa wa EHSAAS sabon magaji."
Mehtav girgiza kai ta soma yin kuka tana fadin, "Ni ba don haka nake sonshi ba. Tsakani da Allah nake sonshi, ba don mulkinsa ba. Ba ruwa da Jr da kishina da mahaifiyarsa. Don me yasa zaki drag din su ciki? Ke wacece? Me kike nema a tare da EHSAAS da zaki ɗauke mai yaro, eh? Ke wace irin azzaluma ce?"
Buge bakinta Mimah tayi tana fadin, "Meyasa EHSAAS yake samo mata marasa kunyane, eh? Daga farko dana ganki sumu-sumi ai na zata zakifi waccan hankali, ashe jirgi daya ne ya kawo ku. Ni kam bana son mutanen kirki. Idan naga mutum mai kirki, raina baci yake. Amma naga ke kirkin nakin is on another level tunda har zaki iya saka rayuwarki a haɗari saboda dan kishiya. Wannan dabbanci ne," ta ƙarasa tana saita bindiga kan Mehtav.
Se kuma ta girgiza kai. "Noo. I won't kill you. Na fahimci you mean nothing to EHSAAS, domin da waccan nakama da yanzu yazo har inda nake. Na ji labarin an ce ma tasume, yanzu haka yana tare da ita a asibiti. Imagine - you're kidnapped, ya bita asibiti, ke kuma ya bar lafiyar ki a hannun makiyarsa. Mehtav, ki haɗa kai dani kawai mu kawo ƙarshenta. Kinga se ki mallakeshi ke kaɗai. Let's kill both the boy and his mother," ta ƙarasa tana dariya tana kallon Mehtav.
Mehtav a fusace ta tofa wa Mimah yawun da ta tattaro a bakinta tana fadin, "God forbid! You're a bitch. Do you think maganganunki zasu shiga kaina? Duk da bansan ke wacece ba, amma nasan ke din da kinada power din da zaki iya kawo ƙarshen Islam, da baki biyo ta bayan fage, kin kama mata danta ba. Do you think I hate her? No, I don't. Dan inason mijinta ba hakan yana nufin zan iya cutar da ita bane. Ba me ta taba min da zan haɗa kai da mace irinki a cutar da ita."
Girgiza kai Mimah ta shiga yi. "Irin baki sanni bane dinnan," ta sa hannu tana goge yawun da Mehtav ta zuba mata. "Tace ya fisonta a kanki? Ba ki jin haushin hakan?"
"I don't care," Mehtav tace, idanuwanta a buɗe kamar ba ta tsoron halin da take ciki. "Sona da nata ba zai taɓa zama daya a ransa ba. Because we are two different people - she's Islam and I'm Mehtav. He both love us in a different way. Amma bazan mamaki idan mace azzaluma irinki ta kasa gane hakan ba."
Wani irin mikewa Mimah tayi a fusace, ta take kafar Mehtav. Ta kwalla ƙara saboda azabar da take ji, amma duk da haka bakinta bai mutu ba. "Ai ke matsoraciya ce. In kin isa ki kwance ni. Nace ki kwanceni ki ga idan zan bari ki min wani abu."
Mimah kallonta take - a gaban wata yar ficiciyar yarinya da ta san Aman dinta ya girmeta ma. Gata ba wani girman jiki ba, se shegen baki kamar reza. Kwanceta ta shiga yi tana fadin, "Okay. Bari mu ga mezaki iya yi parrot. Let's see what you're capable of."
Mehtav ta shiga zare ido, domin ita kanta ta san kurine. Tana kallon bindigar da ke hannun Mimah har ta gama kwance mata hannayenta. Daidai Usman yana shigowa a firgice. Ganin Mehtav na kallonsu yasa yayi wa Mimah alama, ta mike, ya shiga rada mata abu a kunnenta.
Murmushi tayi tana kallon Mehtav. Da kafarta tasa ta take cikinta. Mehtav ta koma ta kwanta tana fasa kukan azaba har ba ta san lokacin da suka fice a gurin ba. Dafe cikinta take tana murƙususu domin ta soma tunanin ko wani abu ya fashe a kayan cikinta saboda azabace wacca ba ta taba jin irinta ba a rayuwarta.
Daga bangaren EHSAAS kuwa, a lokacin da suka kutsa cikin tsohuwar fortress ɗin da Mimah ta boye Mehtav da EHSAAS Jr, duk da tsare-tsarensu na sirri, bai san cewa sun riga sun ganosu ta surveillance camera da suka saka a ciki da wajen gurin ba. Suna shigowa…
Kamar daga sama, alarms suka fara ƙara da wata murya wacca ba a tantama cewa ta Mimah ce ta cika gurin: "EHSAAS… Welcome to hell!" Ta ƙarasa tana kyalkyala wata muguwar dariya.
Kafin ma su kai ga Mehtav da Jr, flash grenades guda biyu suka fado daga sama, suka tashi. Wani irin bakin hayaki ne ya turnike gurin.
"Aman! Shields up!" EHSAAS ya faɗa da ƙarfi yana yin kan Mehtav da ya gani a kwance a ƙasan guri, yana kareta da jikinsa.
Ganin farmakin da suka kawo musu a bazata yasa Aman ya fara mayar da martani, yana jifansu shima da smoke discharger. Amma before they could stabilize, Mimah ta karasa fitowa da kanta daga wata ƙofa gefe, hannunta na rike da silenced pistol.
Akan EHSAAS ta tsaya, wanda ya ɗago Mehtav a jikinsa yana tattabata, tako ina yana dubata yana tambayar if she's okay. Tana kasa magana saboda galabaita, hannunta dafe da nasa, daidai kan cikinta da take rikewa. Ganin irin rikicewar da EHSAAS yayi yana tambayar Mehtav lafiyarta yasa Mimah ta saita kanta tana fadin:
"Step away from her, EHSAAS, or I'll shoot her first."
EHSAAS ya kafe ta yayi da kaifafan idanuwansa cikin gargadi yace: "Mimah, let her go. Faɗanki dani kikeyi, ba da wani ba. Let's not drag innocent souls into this."
Fashewa tayi da dariya tana matsowa daf dasu. Yayinda sauran jami'an tsaron da suka shigo bayan Aman suka shiga fafatawa da men dinta, take fadin: "Innocent? Kai har ka na da bakin cewa wani innocent? Kaga wancan ke ji?" ta nuna mai inda aka ajiye Jr. "Time bomb ne aciki. You should choose between her and him," ta faɗa tana nuna Mehtav.
Wata yar iskar dariya taga EHSAAS yayi yana fadin: "I don't have to. Because you're a nobody. Ba ki isa ki musu komai ba, daga shi har ita."
Wani irin fusata Mimah ta sake yi. Ta shiga saita kunamar bindigar, wanda yasa Mehtav ta fara rokon EHSAAS akan ya yi shiru, ya daina mayar mata da magana, karta cutar da shi.
Kara rungumo ta yayi a jikinsa yana kallonta, yana fadin: "You're safe with me. Nothing will happen. Ba zata iya yi miki komai ba. You're safe, darling."
Muryar Usman ce ta ankarar da Mimah, inda yake cemata: "Tao, ƙasa!" saboda ɗaya daga cikin jami'an EHSAAS ya juya da bindiga zai garnets kafin ya harbeta - t harba mai bullet straight to his shoulder! Ya faɗi yana rike kafadunsa. Tsoron Mehtav ya ƙaru sosai.
Juyowar da Mimah zata yi, seganin EHSAAS ta yi a gabanta. Ba ta san lokacin da ya tashi ba. "Hello," kawai taji yace mata. Da ƙafarsa ya daki hannunta - bindigar ta zame a hannunta. Ya haɗa hannayenta biyu yana matsewa abaya. Cikin kunnenta ya shiga faɗa mata: "You have to stop all of this, Mims. It's enough. You've caused enough trouble already."
"Don't ever call me that, you bastard!" Ta shiga kokarin kwacewa, amma dayake ƙarfin namiji ba da mace ba, ta kasa. Jami'an tsaronsa ma gaba daya sun cafke yaran nata cikin kankanin lokaci. Ta fara ihu tana zage-zage tana mai cewa zata tarwatsa shi kuma bazata sake komawa prison ba. "Datayi zaman prison, gwara ta kashe kanta!"
"Aman the prince!" EHSAAS ya faɗa yana nuna mai cage ɗin da suka saka Jr. Da sauri ya wuce ya ɗauko yaron. Da tsabar wahala da sakashi, yayi barci. Amma numfashinsa is very low, jikinsa yayi zafi radau.
Mimah ta saki kara kamar zautacciya tana fadin, "AMAN??? YOU TOO?? You betray your own mother??"
Girgiza kai kawai Aman ya shiga yi. Yana kallonta cike da takaici yace: "Ummi pls ki tuba. Just give up already. Enough is enough. Stop choosing this path, it'll only destroy you more. Kuma banyi betraying dinki ba. Hasalima, ina yin wannan abinne don in dakatar dake da cigaba da aikata laifuka da kikeyi."
Haukacewa ta shiga fizge-fizge, hawaye na kwarara a idonta tana fadin, "Idan duk duniya sun juya min baya… Aman, you are my son... my everything! Why didn't you save me? Meyasa se makiyana kake goyan baya kana temakawa? Kai wane irin dan ne? Soka ke intsine maka, kabi duniya koh?"
Hawaye ya shiga gogewa, cike da kunar rai ganin abinda uwar tashi ta zama. Yake fadin, "Ummi, I've tried. Kinyi nisa, kinyi nisa, Ummi. You never wanted to be saved. You wanted power… gashi baki samu ba. Daga karshe kin rasa darajar da ake baki, kuma power din da kikeso ba zata taba zuwa gareki ba."
Daidai nan EHSAAS ya watsata gurin jami'an, suka riketa tigijimjim. Ta soma tsinema Aman ta inda take shiga bata nan take fita ba. Jin ba zai iya jurar abinda take cewa ba, yay kofa ya fice da Jr a hannunsa.
Ta juya ta koma kan EHSAAS, ta cigaba da zagin tun daga kan uwar da ta haifi ubansa, da baban babansa, da Mai Martaba, da Fulanin. Kuma tace duk zasu gani, wallahi "she will not let irin cin mutuncin da yay mata yau yay sliding ba."
"Shut up!" ya karasa yana daka mata tsawa. "Ke ko kunyar kanki baki ji? Look at you," ya shiga nunata daga sama har kasa. "As old as you are, baki san me ke miki ciwo ba. The Mims I know is not you. Wannan dake tsaye a gabana monster ce in human disguise. Kin bar greediness yayi tasiri a zuciyarki kamar wacca bata taba shiga aji ba. Koda yaka, I should not be surprised," sai ya fada yana tabe baki. "Kila jini ne. Kinsan an ce duk inda yake sai ya nuna kanshi." Ya karasa yana durkusawa gefen Mehtav.
Zaginsa ta cigaba da yi tana fadin "Tanan zebi yo kenan? Ai kuwa zata gwada mai kalar jinin da yake running a jikinta very soon." "Take them away!" EHSAAS ya fada, hankalinsa gaba daya ya koma kan Mehtav yana kwance mata kafa. Suka juya da niyyar tafiya. Har lokacin bakin Mimah be mutu ba, security biyin sun sa ta a tsakiya, sai tirje musu take.
"Zaki iya tashi kuwa? Uhmmm ko in dauke ki?" ya fada yana curving face dinta a hannunsa. Mehtav ganin yadda yake mata magana kamar wata kwai yasa ta dada narke mishi tana girgiza kai alamar ba zata iya ba. Yace "Oyah zo nan," yana rungumo ta a jikinshi dukkanta kamar jaririya. "Zan fa, iya wasa nake yi," ta rada mishi a kunnensa. Ya yi murmushi yana fadin, "I love you. Thank you so much for being there for Jr.... I... I should-" "Shshhshh," ta fada ta shiga kokarin mikewa. Ya bi jikinta da kallon daya. Ganin sun yayyaga gefe da gefe na kayanta yasa ya juya baya yana fadin, "One sec," ya shiga cire mata rigarsa. "Don there's no way zeba bar ta tafita a haka. I'm changing, don't look this way," ya fada da dan mischief a voice dinsa. Abi ta fahimci he always finds a way to tease her duk da halin da suke ciki. Ta lumhe ido, ta shiga murmushi bata dago ba balle ma ta juya ta gansa. Kawai sai jin wata iriyar kara tayi da ta gigita mata lissafi. Tasa ta bude idanuwanta "Baby-" shiri jin mutum akanta. Ya rungumeta kam-kam. Ihun Mimah taji alamar an rirrike ta.
Tana fadin, "You deserve to die, both of you, both of you!" Sai alokacin Mehtav ta fahimci abinda ya faru. Mimah ta fizgi bindigar daya daga cikin security one way or the other, ta juyo zata harbeta. Saboda there's no way za'a ce EHSAAS ne target dinta, saboda EHSAAS abayanta yake. Mimah ce ta shiga tabbatar mata da zarginta tana fadin, "Die, lover boy." Bata rufe bakinta ba, itama taji saukar nata rabon bullet din. Ta juya tana kallon wanda yay harbin, idanuwanta ya sauka akansa. Mai Martaba na tsaye akan kafafuwansa yana kallonta da jajayen idanuwansa kamar garwashi, da tawagarsa a bayansa.
"Dad......." bata karasa ba, ta zube akan kafafuwanta saboda bullet din da ya shige har cikin kashin kafarta. Mai Martaba yayiwa dogaransa alamar shigowa. "Ku drag her out akan kafafuwanta, nake son ta karasa har zuwa rijiyar nan." Ihu ta fara yi jin abinda Mai Martaba yace, domin ta gane me yake nufi da rijiyar. Rijiyace wacce ake jefa masu laifi mai tsanani a cikinta. Ba mutuwar ta farat daya ake yi a cikinta ba. Rijiyace da aka hako shekaru dari uku da suka wuce a cikin fadar NURISTAN, kuma duk wanda ya shiga cikin rijiyar nan, ba a taba samun tarihin wanda ya fita ba. A jiki suke mutuwa, gawarwakinsu su rube. Ba me zuwa ko gefen rijiyar. Kuma haka in aka jefaka, zaka cigaba da rayuwa da skeletons din gawarwakin masu laifin nan har zuwa lokacin da rayuwarka zata zo karshe. Ba ruwa, ba abinci. Ba kakkarfin take. Don ko tafin hannunka baka iya gani a cikinta.
Dogaran Mai Martaba janta suka fara yi da kafafuwanta, tana ihu tana kururuba, aka fice da ita.
Da sauri kowa ya yi kan EHSAAS wanda ta samu nasarar harbi a gadon baya, saboda yadda yayi wa Mehtav shield, domin ita ta saita, ta so harbi bashi ba. Mehtav kuka ta shiga yi tana ambaton sunanta kamar ranta zai fita. Tana jijjigashi, "Pls, pls, pls, kar ka rufe idonka. You'll be alright, kaji? Don't leave me. EHSAAS, I can't live without you. I love you so much." Idonsa yana lumshewa yana bude wa. Ya shiga shafa fuskarta, hannayensa ya tsaya daidai kan lips dinta yace, "You... fi... nally said it..." Muryarsa very low, daidai sanda dogara ke kokarin daga shi a wuce da shi, ya daga musu hannayensa alamar su dakata. Ya kalli Mehtav. Wani irin painful smile taga yayi kafin yace, "I'm not gonna die har se ki haifamin cute, beautiful babies masu kama dake." "Ka bar magana, ku dauke shi, let's take him to the hospital!" ta shiga fadawa dogaran. Bai yi gardama ba wannan karon. Suka dauke shi dukkansa, hannunsa a cikin nata, tana dingishi har suka fice. Daga shi har ita aka saka cikin ambulance aka wuce.
Mai Martaba ya shiga taka kafarsa a hankali da wata sandarshi ta alfarma, ya nufi mota. Jama'a duk sun firfito. Saboda ko ina a masarautar zuwa yanzu an fahimci me ke faruwa. Ga Mimah da ake ja a bainar jama'a, tana ihu, kafafuwanta na jini. Tana rokon dogarai su taimaka su sa ta a mota. Ba me sauraron ta har suka karasa kofar rijiyar sosai. Mutane suka taru. Mai Martaba already ya isa gurin.
---
It's fatoumspassion Share Comment Like & Vote [02/08, 18:09] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
It's Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.