EHSAAS

Chapter 54

by @fatoumspassion

Awani irin sauri aka shigar da EHSAAS ciki, ba bata lokaci aka fara mai theatre. Mehtav ba ta kanta take yi ba kafarma, duk da zugin da take mata haka ta taka wani irin mahaukacin tsaro aka zuba a sashen da aka ajiye EHSAAS.

Tana tsaye tana kai kawo, kawai taji kukan jaririya ya canyara. Jr! Zuciyarta ta bata, tana wani bugawa, kirjinta yana tsalle saboda wani mahaukacin tsoro daya shigeta-kadai shima wani abu ake masa ne yake kuka haka.

Da wani irin mahaukacin sauri tabi inda take jin kukan. Duk da yadda dogarai suka so dakatar da ita daga shiga daki, haka ta kafe, ta jajjaga musu barazana iri-iri sannan suka barta. Daga Aman sai likitan yaran dayake duba yaron, wanda yariga ya galabaita ya sume tun dazun ake fama da shi. Ana so ya dawo, ya ki dawowa-se yanzun da likitan yayi masa wata allura shine ya farkar da wannan mahaukacin kukan.

Yana hannun likitan yana karasa masa dube-dube. A wani irin zabire Mehtav ta karasa tana karbe dan a hannunsa, ta wani rungume shi tana jin in wani abu ya faru da shi, ba zata yafewa kanta ba.

"What are you doing to him? Meyasa yake kuka? Are you trying to kill him?" ta fada tana kuka.

Tana dudduba jikin Jr taga ko ya mai wani abu. Daga Aman har likitan tsayawa sukai suna kallonta, musamman likitan da ba ya san Islam ba-cewa zai yi itace ta haifi yaron. Saboda tsantsar soyayya da kulawa da suka gani a idonta, rarrashin sa ta shiga yi tana zagaye dakin tana fadin:

"Shhhh... no one's gonna hurt you. I'm here with you, my baby. Daddy will be fine too, kadena kuka..."

Miraculously, yaron yayi fari luf a jikinta kamar yana jin me take cewa. Aman ya tsaya watching them-abin gwanin birgewa. Ganin duk se kallonta suke yasa ta tsaya da zagayen tana kallonsu.

"Meye kuke kallona? Mekuke mai eh?"

Likitan yayi murmushi yana fadin:

"Allah ya baki hakuri. Duk da dai ba san yaya kuke da yaron naki ba, amma dubashi kawai muke. Kinsan ya firgita dayawa, ya jigata, so he needs serious check-up. Ki bani shi in cigaba da aikina Madam."

Make kafada daya ta yi, yadda kasan Abeey kana kallonta, kasa arude take.

"Bazan baku shi ba. I won't let you hurt him and make him cry again."

"Please, Madam," likitan ya kara fada yana matsowa da niyyar karbar Jr.

Baya tayi tana sake kankameshi. A hankali, Aman daya fahimci yarinyar is traumatized da abinda ya faru, ya nuna mata gefen gadon yana fadin:

"Come here, no one's gonna take him away, kin ji? I promise you. Kirikeshi, seya duba shi a hannunki."

Dan shiru tayi na wasu lokutan, kafin nan ta rabe tabi taga gefensa, ta zauna saman gadon tana kallon likitan. Ta dan dago Jr a jikinta, amma she's still holding onto him. Ahaka a hannunta likitan ya karasa bincikensa. Ya kara yimai wata allurar da tasa ya kara fasa kuka.

Da sauri Mehtav ta mike tana kallon likitan cikin ido:

"Why are you so wicked?"

Kaita sa wa yaron karfe a jiki. "Come, my baby, come," ta karasa tana jijjigashi, tana zagaye da shi. Daidai yana yin shiru, taji ana gudu kamar ta hallway din section ɗin. Tana jin muryar wata mace tana kiran, "Please stop, Princess! Please stop!"

Murɗa ƙofar ɗakin, taga an yi da sauri. Idonta ya koma kan ƙofar tana kwakume Jr tana boye shi a jikinta, irin duk abun cutarwa da zai shigo yafara ta kanta kafin yaje gareshi. Wani irin zubewa a ƙasa Islam tayi, tana fashewa da wasu irin hawaye masu sanyi tana kallon yaronta a hannun Mehtav.

Mehtav data rintse ido expecting the worst, a hankali ta shiga budewa tana kallon yadda Islam ke kuma kamar ranta zai fita tana kallonsu. Jikin Mehtav ne yayi sanyi. Ta tsaya, ita ba ta motsa ba, itama kuma ba ta motsa din ba. Kawai suka tsaya suna kallon-kallo.

Tun daga kan Mehtav ta shiga kalla, kawai tana tuna kalar azabar da tasha a Nigeria, tayi lokacin da suke after Jr. She's just imagining how Mehtav made it-she managed to protect her son and he's back alive. Tashi nata kenan, ko tace ma kukansa ne ya tasheta. Saboda har layi take yi sanda ta mike, ƙarfin haline da na zuciya kawai yasa ta faki idon Jalila dake tsareta, tafito ta biyo inda ta ji yaron na kuka. Har kirjinta da kwakwalwarta take jin muryar kukan. Tashi da yake, asibitin ya ɗau wani mugun shiru kuma sashen da suke su su kaɗai ne a ciki.

Jalila ganin Islam ta ki shiga ɗakin kuma ta ki bata hanya, ta shiga yasa ta turar ƙofar, ta buɗe baki ɗaya. Ta tsaya tana kallon Jr dake hannun wata yarinya. Farace duk da butu-buɗun da tayi, ta gane hakan. A jigace take, amma hakan ba hanata hango dogon siririn hancin ta da idanuwanta madaidaici waɗanda suka yi zuru-zuru.

A ranta ta raya: "So this is the girl EHSAAS chose over me… again."

Ta tabe baki, ta karasowa ciki tana fadin, "Thank God he's fine." Ta juya tana kallon Islam, ta nufi Mehtav tana miƙa mata hannu. "Kawo shi nan, ta ganshi. Kada zuciyarta ta buga. He's alive, Islam, he's alright, look at him!"

Ta karasa tana ƙoƙarin banbare shi daga jikin Mehtav. Ja da baya tayi, tana ƙara kankame shi, ta hana ta, saboda ba ta santa ba. Harga Allah ba ta taɓa ganinta ba. Duk da taga kalar hasken fatarsu ɗaya da EHSAAS, amma kuma ai tasan EHSAAS ba shi da sister.

Kallon Mehtav tayi, irin kallon nan na "Are you okay?" dinnan tana riƙe kugu.

Aman yace: "She's my uncle's cousin sister. Mehtav is okay, you can give her the baby. Let's get you treated too. Kafarki is not fine."

Kallon kafarta da gefen rigarta duk yabi ya yage, Islam tayi. Tana miƙewa ta karasa gabanta, ba tare da tace ta bata ba, Mehtav ta mika mata shi tana fadin, "Please, take care of him. He hasn't eaten since morning."

Rungume shi Islam tayi, hawayenta na ci gaba da zuba. Mehtav na jin yadda take ta maimaita: "Alhamdulillah, alhamdulillah…" a cikin wata low voice mai rauni.

Mehtav ta juya a hankali zata bar ɗakin. Islam ta riko hannayenta tana miƙa wa Jalila yaron. Tace: "Let's get you treated, Mehtav. You're seriously wounded."

Girgiza kai ta shiga yi tana fadin: "I need to find Abeey. Ban san ko kun sameta ba, amma she fainted earlier somewhere near the garden."

Islam tace: "Ki zauna anan, I'll go. Ni zan nemo miki ita. I promise zan dawo miki da ita safely."

"No, you don't have to. I'm okay fah. Ba ki gan ni ba? I'm not that hurt, it's just EHSAAS…" Ta yi shiru tana kallon Islam da fuskarta na nuna alamar ba ta san abin da ya faru da shi ba. Gudun ba ta so ya kasance ita ta fara breaking bad news da zai sa ta ƙara firgicewa yasa tace: "Okay."

Aman ne yayi gyaran murya yana fadin: "Abeey is okay, tana the same ward dinnan."

Kallonsa Mehtav tayi, irin "Is he sure?" dinnan. Ya jinjina kai yana fadin: "Yes, she's fine. Uncle Prince da kansa ya sameta."

Sai a lokacin Mehtav ta yarda ta zauna a ɗakin. Sabon likita ne aka kira, ya shiga treating dinta itama. Ana farawa Aman ya wuce don ya ci gaba da monitoring abin da ake ciki daga bangaren EHSAAS.

Seda aka gama sannan taje tayi wanka. Islam tace Jalila ta dauko mata ɗaya daga cikin kayanta. In an kawo na Jr ma, ba don ranta ya so ba, sanin matsayin Islam yanzu ya fi nata a masarautar yasa ta juya don ba a mata musu. Taje ta ɗaukowa Mehtav, tana dire mata. A ranta ta soma Allah-Allah karshen shekara yazo, ai bikinta itama ta huta da kayan takaicin matan EHSAAS. Ganin wawtar Islam kawai take yi, ganin yadda take nan-nan da Mehtav sekace ba ita ce mijinta za a aurar ba.

Tana kawo rigar, ta fice, ta bar musu ɗakin. Seda Mehtav ta gama gyarawa tsaf sannan ta kwanta a kashingida saman gadon. Sai asannan Islam ta samu damar wanke jikin Jr, shima ta zira masa kayansa marasa nauyi. Already yayi barci saboda jigatar da yayi. Ta kwantar da shi gefen Mehtav da ta dan dago ta kalleta cikin mamaki, ta gyara kwanciyarta. Hankalinta na kan EHSAAS, amma tana jin shakkar tace zata je saboda ba ta son Islam ta shiga wani hali sanadin hakan. Ita kanta break-in take yi ta ciki, amma tsabar ƙarfin hali ta kasa nunawa.

Islam stool ta ja, ta zauna gefen gadon tana kallon Mehtav. Anitse, ta fara cikin sassanyar murya mai cike da nutsuwa wacce ta rigada ta bi jikinta tana fadin:

"Mehtav… I don't even know where to begin…"

Shiru Mehtav tayi tana sauraronta, don a iya saninta Islam din ba tayi mata komai ba bayan avoiding dinta da take yi these days. Kuma ba ta ganin laifinta akan hakan ba, saboda ta san in itace a situation dinta, zata yi abin da yafi haka. Islam ta ja dogon numfashi tana fadin:

"Na tsani kaina for how I treated you... for thinking you were trying to take what was mine…"

Ta matse hannun Mehtav da hannayenta duka biyu, tana jijjiga kanta regretting what she did, tana fadin:

"But you saved my baby… you fought for him. You almost died for him... for me. Mehtav… ba ki dauke shi as dan co-wife dinki ba. Mehtav, you stood up for him till the end. I should've listened to Maama lokacin da take fadamin ke mutumiyar kirki ce Mehtav, kuma zakiso yaron kamar naki. I owe you my life!"

Mehtav sosai taji Islam tana dada burgeta kullum saboda kalar maturity din da take da shi. Ko ita me shekarun da suka fi nata ba ta da shi. So all this while, itama ashe tana jin kishinta-kawai fita iya boyewa tayi. Ganin Islam din is just guilty for just ignoring her da tayi yasa ta ɗaura hannayenta saman nata tana fadin:

"Islam… you don't owe me anything. He's our child. Da na kowa ne. I'm sure inda inada yaro ya shiga irin situation din da Jr ya shiga, you'll do the same for me."

Jinjina kai Islam ta shiga yi, ta rungume ta tana murmushi. Da zuciya ɗaya take fadin:

"I'm sorry. For all the cruel silent treatments. For the jealousy. For trying to erase your place in his life. I was wrong. So wrong, Mehtav. I'm sorry. I wanna be your friend now. Let's make Jr happy by doing what he always wants - irin mu haɗe kai haka."

Mehtav ta lumshe ido tana murmushi, tana jin daɗin maganar Islam ɗin. Tace:

"Yes, friends. I'm sorry too, kin ji. Sometimes… love makes us all a little wrong. Ni kin manta duk abinda na miki a Nigeria, you did nothing compared to what I did. So let's just leave the past behind us."

Jinjina kai Islam tayi, tana sauke idonta kan Jr dake barci peacefully gefen Mehtav. Itama kallonsa tayi tana murmushi. Islam ta dawo da idonta kan Mehtav tana fadin:

"You're the reason he's breathing right now."

"Allah save the both of us, Islam. Da taimakon EHSAAS."

Murmushi Islam ta shigayi, ta kama hannun Mehtav kamar wasu teenagers, irin sabbin kawance nan, saboda both of them it's very awkward for them. Ba su da wasu kawayen kirki a rayuwarsu. Mehtav, Abeey has always been her only friend. Ko wata ta fara kulata ko a school, tana dawowa gida Abeey zata fara kushe kawar har se ta sa ta ji ba ta son kawancen anymore. Ita kuma Islam, uban miskilancinta yasa duk nacin da kawayen ke mata, haka suke kyaleta, saboda ko sun zo inda take, ba wani samun shiga suke ba.

"By the way, where is Sire?" Islam ta fada tana kalle-kalle, because tun dazun take expecting shigowarsa amma taji shiru.

Mehtav, jikinta ne yayi sanyi tana kallon Islam da take jiran amsa daga gurinta. Ganin ta kafeta da kaifafan idanuwannan nata yasa tayi saurin ɗauke kai, tana ja da baya, tana janye hannunta. Anata ta shiga stammering, tana so tayi magana, ya ki fitowa, saboda karya take shirin yi.

"Did something happen to him?" Ta tambaya a tsorace, tana kallon Mehtav da ko yarda su haɗa ido.

Kirjinta ta riƙe, tana jin yana mata wani irin nauyi kamar zai fashe. Ba ta san me yasa ba, wannan zafin da take ji a kirji intana cikin damuwa kullum, sai ƙaruwa yake. Tun lokacin da ta haifi Jr take jin hakan, but she never gave irin mahimmanci akan hakan ba. And the more tana jin pain, the more yake ƙaruwa.

Ganin abin da Islam ke yi yasa Mehtav saurin miƙewa tana ɗan dingishi, ta tareta tana tambayarta:

"Are you okay?"

Numfashi take ja sama-sama, idanuwanta sun fara ƙadawa, sun yi jajir. Take fadin: "Just tell me... me ya faru da shi. Don't worry... I can han...dle it. I can…"

"Islam!" Wannan karon Mehtav ta fada da ƙarfi, cike da damuwa tana tarota, ta zaunar da ita saman gadon tana fadin: "Breath in, breath out. You'll be fine in sha Allah."

"Just tell me… where…" Kasa karasa tayi, sai wani irin mahaukacin jan yewa numfashinta yake.

"Fine, he was shot. But I'm sure he'll be fine. He's alive. Ana cire bullet ɗin ne. Na san sun gama by now."

Ba ta ankara ba, kawai ganin Islam tayi, ta janye hannunta a kafadarta, ta fice da wani irin gudu da zafin nama. Tana haki, Allah ne kaɗai ya san me take ji a ƙasan kirjinta. Mehtav, na dingishi, ta shiga ƙoƙarin binta, tana jinjina wannan wace kalar soyayyace Islam take yi wa EHSAAS. Sosai ta fara jin tsoro, saboda shima taga kalar soyayyar da yake mata.

Kasa binta tayi saboda kafarta da tayi mugun riƙewa. Sai dogaran bakin ƙofar ɗakin tasa su bita da sauri. Tace a kira Aman, a sanar da shi me ke faruwa. Ta tsaya bakin ƙofa tana jin: "Inama ba ta fada mata ba…" Duk da yadda ta matsa.

It's Fatoum's Passion, EHSAAS Don't forget to: Like Share Comment & Vote [07/08, 20:17] Fatima Rufa'i Nasidi: *** It's Fatoum's Passion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.