EHSAAS

Chapter 55

by @fatoumspassion

Wani irin gurnanin azaba Mimah keyi saboda wani irin azababben ciwo da dukkanin jikinta da kafarta da aka harba ba a yi treating sukeyi ba. Sau uku tana suma, suna tayarda da ita da wani azababben ruwan kankara. Ta shide yafi a kirga, yayinda concourindon al'umma suka zagaye guri, ana ta Allah-wadai da halin mace irinta. Gashi an barta a saman rijiyar sarai.

Mai Martaba yana cikin limousine ɗinsa, yaki cewa a jefata kuma yaki cewa a barta. Ga jama'a sun taru ta ko'ina, ana mata ihu, ana Allah-tsine. Tunda take a rayuwarta bata taba jin wani abu kwatankwacin nadama akan duk abinda take yi ba sai yau, saboda tun da uwarta ta haifeta, bata taba tsammanin mace kamarta zata fuskanci tozarci irin wannan ba.

Wai yau itace a fadar NURISTAN, fadar da take matsayin gimbiyarta na tsawon shekaru arba'in da 'yan kai, tazama kamar wata mabaraciya. Bayinda ko kallon fuskarta basu isa suyi ba balle taka inda kafafuwanta suka taka, yau sune suke iya kallonta suna nunawa, suna zaga.

Rintse idanuwanta tayi. Kyakkyawar rayuwarta ta baya ta shiga dawo mata, da yadda ake daukakarta a fadar nan, da yadda duk wani abu na cikin gida da za a yi, itace ke jagorantarsa. Ko matan gidan basa baza mulkin da take bazawa.

Bata taba jin ta tsani mahaifiyarta ba kamar yau dinnan, saboda ta cuceta, ta cuceta matuka. Saboda bata taba nuna mata cewa tana bin tafarki ba daidai ba, kuma bata taba kwabarta akan hassadarta da muguwar boyayyiyar kishinta da take yi akan EHSAAS ba.

Gashi last last, takamarta da cewa itadin 'yar sarki ce, duk abinda ze je ya faru, title ɗin ma an zo an kwace. Zatai kaskantaccen ƙarshe wanda babu wata macen da ta taba yinsa a fadar NURISTAN.

Tana ji, itama inama hukuncin kisa Mai Martaba ya yanke mata ba shiga wannan muguwar rijiyar ba, da tama kasa hasaso kalar bala'in da zata tsinci kanta a ciki in aka jefata.

Ihu ta shiga yi tana kokarin mikewa, a kokarinta na zuwa gun inda motar Mai Martaba take, takeyi tace masa ta tuba, ya maida ta prison wallahi bazata sake ba.

Amman haka wani dogari ya daga bulala, ya shauda mata. Ta bankare, ta koma baya tana birgima a kasa, kafarta na jini tayi fututu. Mutane na mata dariya.

Daga cikin mota kuwa, Mai Martaba kasa fitowa yayi saboda shishi kaɗai yasan irin abinda yake ji a ransa game da halayen Mimah da abinda ta aikata. Kawai gani yake yi he is lacking somewhere, saboda ya raineta kuma ya rayu da ita sama da yadda ya rayu da EHSAAS. Koda ba 'yarsa bace, yana ganin ba laifinta bane kasancewarta hakan. Kuma shi idan da wannan mugun halin nata bai fito ba, ashirye yake a birne maganar asalin Mimah har abada, saboda shi a gare shi babban tozarcine ace ɗan uwansa yana neman matarsa, kuma har sun haihu.

Koda ba matarsa ce ta haifi Mimah ba, shi ma iya riƙe ɗan Erfan ne duniya da lahira. Amma Mimah ta bashi mamaki. Ya ma rasa me yake ji a cikin zuciyarsa dangane da ita ayanzun.

Kwankwasa masa glass yaji ana yi. Yasan Wambai ne, kuma wannan ne karo na uku yana kwankwasa masa saboda yamma tayi, lokacin sallah yana karatowa, ga al'umma sun taru ana jiran hukuncinsa.

Memo ɗin company EHSAAS dake hannunsa ya soma jujjuyawa kafin ya shiga rubutu cikin manyan baki na Larabci. Ya nannade takardar, ya zuge glass, ya bawa Wambai akan ya kai ma matarsa ta farko, Mai Babban ɗaki dake a asibiti.

Karɓa yayi yana jinjina masa, kafin nan yayi masa alamar ya buɗe mai kofa. Kofa ya buɗe mai da kansa. Duk majalisar dattawan ƙasar sun taru a gurin, ana jiran hukuncin da zai yanke. Kowa yasan King NASHWAN baida kyau a ɓangaren hukunci - kowaye kai, abinda ka shuka shi zaka girba. Musamman idan abinda ya danganci yarima ne, tohm baya wasa da shi.

Wata irin sandarsa ta alfarma tafito da ya miƙa masa lokacin da ya tsaya kan kafafuwansa. Duk suka bi suka jera a bayansa har lokacin da ya karasa gurin. Yana ɗan dingisa sandarsa saboda kafarsa ba ta gama dawowa daidai ba.

Ganin sa a gabanta a tsaye akan kafafuwansa - mutumin da take ma kallon gawa shine yake kan kafafuwansa. Haka ita kuma me lafiya gashi ta faraddaya. Allah ya nuna mata shine me rayuwa da kashewa. Tana kan gargadar rasa rayuwarta.

A buɗe rijiyar taji wani dogari yayi shela wanda tasan umarnin Mai Martaba ne. Da gudu mutane suka fara ja da baya saboda har rade-radin fatalwu da suke yawo da aljanu a gefen rijiyar da dare duk sun ji na mutanen da suka mutu a ciki.

A tsomare wata katuwar baiwa ta tattaro Mimah da kanta bajimin murfin rijiyar ta watsota gefe. Su kansu makullan da ƙyar ake murɗasu, ana daga su kuma majiya ƙarfi keyi. A haka suka ɗau lokaci kafin rijiyar ta buɗe.

Masu kallo daga sama suna iya ganin bakin duhun rijiyar mai shegen zurfi - ba kwa ganin ƙarshenta.

Ihu Mimah ta soma yi. Ta shiga ƙoƙarin rarrafawa gaban Mai Martaba amma sun riƙeta, sun hanata isa.

"Ku sake ni! Babana ne! Ka yimin rai Daddy! Bazan sake ba Daddy! Na daina! Ka kashe ni ta kowace hanya, amma banason in shiga rijiyar nan! Ina tsoro!"

Ko kallon inda take Mai Martaba bai yi ba, saboda shi din jagora ne, dole ne yayi adalci ga duk wanda aka zalunta.

Laifuffukan Mimah ba irin wanda za a iya yafewa bane. Bayan rayuwar matasa iri-iri da ta bata - wasu sun mutu, wasu kuma suna nan suna rayuwa da su kansu basu san amfaninta ba.

Bai san mata dubu nawa ta yi safara ta fitar da su ba - suna raye ko sun mutu, Allah ne kaɗai yasan da haka.

Baya ga haka, she openly revolted against the crown, tayi attacking Crown Prince har sau biyu. Ta so ƙona fada ta hanyar saka wuta da gangan. Ta illata ubanta mahaifi, illa wadda har abada ba zai iya farfadowa daga ita ba.

Menene batama aikata ba?

Tuna waɗannan abubuwan ya ƙara ba shi ƙarfin gwiwar yanke hukunci cewa ba 'yarsa zai jefa rijiyar ba - annoba zai jefa: wadda ta gagari gari. Wannan jahadi ne zai yi mai girma ta hanyar kawar da ita daga doron ƙasa.

"Execute the judgement!" ya faɗa da wata irin kakkausar murya da tun da Mimah take bata taba jin sa da irin wannan muryar me ban tsoro ba.

Ihu ta ƙurma, ta shiga fizge-fizge tana ƙoƙarin ƙarasawa gare shi. Ta na ji, tana gani wasu samudawan bayi mata ba maza ba suka yi mata ɗaukar amarya.

Ana "Allahu Akbar! Allahu Akbar!" aka jefata cikin wannan bakin zaɓaɓɓen ramin rijiyar.

Ko ihunta ba a iya ji, saboda kabbarar da ƙurin ya dauka.

Juyawa Mai Martaba yayi, yana wucewa bayan ya bada umarnin a rufe rijiyar.

A tafi da duk waɗanda suka taimaka mata gurin guduwa daga prison - su Usman gaba ɗayansu.

Ido ya raina fata saboda sun san idan har za a yi wa gimbiya Mimah irin wannan hukuncin, nasu azabar za fi haka.

Su ba 'ya'yan kowaba - ba kowa n kowaba.

Kuma nan take aka yi kiran sallah. Kowa ya baje a gurin kamar ba a saka ɗan Adam mai rai a gun ba. Tsit kake ji.

Islam na isa ƙofar ɗakin theatre ana buɗe ƙofa, wasu likitoci da nurses taga sun turo gadon EHSAAS kamar ba rai a jikinsa. Fuskarsa kawai take iya hangowa, ta taho a bala'in sauri zatai kanshi, wata nurse ta riketa tana faɗin, "He's fine, pardon me Princess, ki kwantar da hankalinki, he's fine."

Numfashinta sama-sama yake, ta shiga nunashi tana faɗin, "Meyasa ya kulle idonshi? Meyasa baya motsi? Kike cemin he's fine?"

Likitansu ne wanda ya rigada yasan condition ɗin Islam. Ya yiwa sauran nuni alamar su tafi da EHSAAS. Tana ƙoƙarin fincikewa ta bisu, yace, "Calm down Princess, as she already told you, he is fine. Bullet ɗin bai shiga ciki ba kuma an kawo shi akan lokaci. Anesthesia ɗin da aka masa bai sakar da shi ba, amma yadda mijinnan naki yake da ƙarfin hali, he will wake up soon in sha Allah."

Kallonsa ta shiga yi kamar wata wawiya tana sauke ajiyar zuciya tana kallon ɗakin da aka buɗe aka saka shi, kafin ta dawo da kallonta kan likitan, "Ka tabbata?"

Likitan ya jinjina mata kai yana faɗin, "Na tabbata, kar ki damu kanki, kinji? And kar ki bari hankalinki ya tashi. You passed situation da yafi wannan. Just continue having faith in God, Islam. He won't leave you, not now. He survived more than this."

Hawayenta da ɗaya ke bin ɗaya ta shiga gogewa tana jinjina ma likitan kai. "Jr is back too, we will live happily ever after, right?"

"In sha Allah, Princess. And your mother is also good."

Murmushi ta shiga yi kafin tace, "Can I go and see all of them now?"

Dan girgiza kai yayi, sai kuma ya jinjina yace, "Zaki iya zuwa gurin Mai Girma Fulani, shi kuma megidan a dan barshi ya huta ko?"

Dan turo baki tayi gaba. Daman yasan za a rina. Cikin wayo yake faɗin, "Can na nufa. In kika wuce yanzun baki je gunta ba, zan rufe visiting se gobe."

"Ni na yi gaba!" da sauri tabi bayansa tana faɗin, "I'll come with you, Doctor. Wait for me!"

A ƙofar ɗakin ta tarar da Babban Mehtav, da yake gefen ɗakin. Abeey take kuma tun farkawarta Fulani ta sa a dakko mata ita. Ta dawo kusa da ita duk da ba wani ƙwari a jikinta.

Bakin Abeey yaki mutuwa, sai bawa Fulani labarin arangamarsu da 'yan daba take yi. Bayan data gama koke-koke, sai da aka ce mata aisu Mehtav an karbo su, suna cikin koshin lafiya. Ta shiga bada labari kamar ba ita ta farfaɗo daga suma ba yanzun.

Gaisawa suka yi da Islam cikin girmama juna. Yay mata jaje, itama haka. A kaɗan suka jajanta ma juna kafin nan ta shiga.

Already likita ya shiga ya fara duba Fulani. Tana shiga suka haɗa ido da Fulani, tayi mata ɗan murmushi wanda tasan bai kai canciki ba, don tasata farin ciki ne - saboda har yanzun hankalinta ba a kwance yake ba.

Zama tayi a gefenta tana kamo hannayenta, tayi kissing tana faɗin, "Alhamdulillah Maama, are you okay?"

Jinjina mata kai tayi. Ta fara kalle-kallen bayanta kamar tana neman wani abu. Sanin me take nema ɗin yasa tace mata, "Yana tare da Mehtav. Likita ya duba shi, yayi barci a ɗakin."

Dan jim Fulani tayi tana kallon Islam a yadda tasan Islam. Musamman yadda abinnan ya faru, ba zata sake yarda ta bar ɗanta a hannun kowa ba. Amma sai taga tashin farko ya bata mamaki.

Lallai ta ƙara hankali, ta raya a ranta kafin ta filla tace, "I'm sorry... I'm so sorry... I shouldn't have..."

Shiiiiiii! Islam ta faɗa tana ɗaura finger ɗinta akan bakinta alamar tai shiru. "Maama, nasan da kinsan abinda zefaru kenan bazaki taɓa tafiya da shi ba, kuma nasan Jr jinin kine, bazaki taɓa cutar da shi ba. Ki daina blaming kanki akan abinda ya faru. You always tell me komai ƙaddarane daga Ubangiji. Abinda ya faru ƙaddara ce, rubutacciya daga Ubangiji. Don haka Maama, ki daina bani haƙuri, babu abinda kika min, it's not your fault."

Kwallace ta cicciko a idon Fulani tace, "You're so considerate, Islam. Ina alfahari da kasancewarki 'yata, ke ta musamman ce." Rungume ta tayi tana faɗin, "Get well soon, Mom."

Abeey ce ta shiga gyaran murya tana cewa, "Queen Mother, wai naga baki faɗa mata ba?"

Dariya ta shiga yi tace, "In faɗa mata me?" "Uhum Queen Mother, gwara dai tasani," ta ƙara faɗa tana gyara zama, tayi kicin-kicin da fuska.

"Menene zansani?" Islam ta tambaya tana kallon Fulani da Abeey a lokaci guda.

"Wai cewa tai in faɗa miki ki fara yimata mutunci. Ita ce ta cece rayuwar ɗanki. Ita da Mehtav. Tsautsayi ne yasa aka sumar da ita a hanya, ba'a wuce da ita gurin kidnapping ɗin ba. Da tuni ita ce zata fafata da manyan 'yan ta'adda."

Dan waro ido Islam tayi. Duk yadda ta so kar tayi dariya, dole maganar Abeey ta bata dariya. Tace, "Ashe haka kai?"

Jinjina kai Abeey tayi ta gyara zama tana faɗin, "Haka ma fa. Da aka ceci handsome, se wai a ce Yaya Mehtav ce. Aita gode mata ita kaɗai. Nifa duk fa abinda kukaga tayi, nice nake sakata. Da ba dani ba da bata ceci kowa ba da wancan da wannan din. Amma no one is seeing how good I am. Sai aita bama Mehtav credit ɗin."

Islam ta miƙe ta ƙarasa kan gadon da Abeey take, ta zauna a gefenta tana kamo hannunta kafin ta shafa kanta cike da kauna. Saboda tasan abinda yaran nan biyu suka mata a rayuwarta ba zata taɓa iya biyansu ba. Kuma duk kalar godiyar da zata yi musu isn't enough. Sun cece mutane biyu mafi soyuwa a rayuwarta a lokacin da suke tsananin buƙatar ceton.

"Abeey, I'll forever be indebted to you. Kalmomin godiya sun yi kaɗan gurin nuna miki irin girmanki da nake gani, da appreciating abinda kika yi."

A wani irin blushing Abeey ta shiga tana girgiza kai cikin jin kunya. Bata ɗauka Islam zata ɗau zancen nata har zuciya ba, don ita shirmenta take yi.

"Nifa… nifa…", sai ta kasa ƙarasa maganar, ta ɓoye fuska. "Amma zan nuna miki how thankful I am. Kinsan me? Sire always tells me how much you like him. Kuma kina son ki yi living tare da shi ko under the same roof."

Jinjina kai tayi. Islam tace, "From today, Sire ba shi kaɗai ne zaku riƙa abota da shi ba. I'll be your friend and big sister. Like Sire and Mehtav. You'll be living with me, not them. Kinga su aure za su yi, sai mu barsu su yi ta honeymoon ɗinsu. Mu kuma sai mu tafi namun yawon zagaye gari, ko?"

Wani irin zabura Abeey tayi tana kankame hannun Islam tace, "Really? Da gaske kike, Maman Jr?" Ta jinjina kai tana faɗin, "I'm serious."

Tace, "Zaki bar ni ina ɗaukar Baby Jr koda yaushe?"

Jinjina mata kai Islam tayi tana faɗin, "Of course. Kuma ba zaki riƙa kishi da Yaya Mehtav ba. Zaki barta itama ta samu soyayya irin wadda Handsome yake baki."

Jinjina mata kai tayi. Ai ko ta faɗa jikinta ta rungume tana faɗin, "Na yarda! Na yarda! I'll be your friend!"

Ta ɗago tana faɗin, "Yanzu wace ƙasa da wace ƙasa zamuje, uhm Maman Jr?"

Dan murmushi Islam tayi kafin tace, "Let Sire get better first."

A tare Abeey da Fulani suka ce, "Meya same shi?"

Islam dan waro ido tayi sanin tayi blunder, domin taga alamar basu san meya faru ba. Da sauri ta miƙe tana kallon Fulani tace, "He's just tired. Kuma kinsan akwai biki a gabansa, shiyasa nace haka. Jr must be awake by now. Bari na je gurinsa."

Da sauri ta nufi ƙofa without turning back, ko da na one second, saboda tana tsoron idanuwan Fulani masu kaifi, zai iya sa ta faɗi abinda bata yi shiri ba.

Aunty, taji an faɗa daga baya. Sanin ba me kiranta da hakan sai Aman, yasa ta juya tana kallonshi cike da concern. Yake faɗin, "Ina kikaje? They told me you're not fine, you're running around. Meyasa? Mekike uhm, kina lafiya? Is Uncle better now?"

Tambayar ta yake, amma kallon idanuwansa da yayi wani irin bala'in jajir takeyi. Kana ganinsa kasan yaci kuka. Yamore ayadda tasan da kiyayar zuciyar Aman, tasan ba ƙaramin abu bane zesa ka shi kuka.

Cike da tuhuma ta tsareshi da ido tana faɗin, "Meyafaru? Meya sameka? Kai kuka?"

Saboda tasan idan Ehsaas ne ya farka abinda zeyi kenan. "Are you okay?"

Ya sake tambayarta. Ta jinjina masa kai tana faɗin, "I'm okay. Sire ma is okay. He is out of danger now. Kai nake tambaya yanzun, me ke damunka?"

"I'm alright. I'm okay," ya fara tambaya yana ja da baya da baya. Saboda there's no way zai bari ta gane agony ɗinshi. Domin idan yayi hakan kamar yayi butulci ne agaresu. Yake ga dan me yasa ze ji ƙunci akan hukuncin da aka mata bayan she brought all of this upon herself.

Amma he can't help it. The pain is just not going anywhere.

Da sauri taga ya juya ya bar wurin. Tana kiransa amma ko waiwayowa bai sake yi ba.

Mamakine ya kamata a ranta. Tana raya kila dai halin Mimah ne ke damunshi. Tashiga jajanta abin a zuciyarta tana nufar ɗakin Ehsaas.

Ta glass ɗin ƙofa ta hangoshi yana ta barci hankali kwance.

Tafi minti ishirin a tsaye a gurin tana ta kallonshi kafin ta koma ɗakin Mehtav.

Ganinta tayi ta zuba uban tagumi tana kallon ƙofa kamar dama tana expecting wani ne.

Islam ta ƙarasa tana tambayarta jikinta tana ɗan taba Jr dake barci har yanzu ko juyi bai ba. Tace, "Da sauki Alhamdulillah. Ita fa? Is she okay? Saboda ta mugun tsoratata."

Jinjina kai tayi tana zama gefenta tace, "He is fine, barci ma yake yanzu. He will wake up any time soon. Kina son kije kiganshi ne?"

Da sauri Mehtav ta jinjina kai, sai kuma ta girgiza tana nuna mata ƙafarta.

Dan murmushi Islam tayi kafin tace, "I got you."

Wani abu ta danna gefen gadon Mehtav, segani wata nurse ta shigo ta duƙa tana kai gaisuwarta kafin ta tambaye su me suke so.

Islam ce ta ba ta umarnin kawo electronic wheelchair. Ta jinjina kai ta fita.

Mehtav ta ɗan zaro ido tana cewa mata, "It's not necessary. I can wait."

Girgiza kai tayi tana faɗin, "I know you're worried so there's no need to wait. Nasan he'll be very happy in ya farka ya ganmu a gefenshi, ko? Let's surprise him."

Bata jima da fita ba segata da wheelchair ɗin. Islam ta taimaka ma Mehtav ta hau ita, kuma ta rungume Jr a hannayenta suka fito.

Duk inda suka sa ƙafa, dogarai na binsu. Mehtav ta ɗan juya tana kallon Islam, tana mata alamar lafiya suke binsu irin she's feeling awkward. Ita Islam har ta saba da binnan, shiyasa ma ko sun bi ta, abin baya damunta.

"Don't worry, they are just doing dai jobs," Islam ta bata amsa tana ɗan dafa kafadarta.

A ƙofar ɗakin suka tarar da Mai Martaba, daga shi sai Turaki da Habib Bai.

Cikin girmamawa suka gaidashi. Ya amsa yana tambayar Mehtav ya ƙafarta.

Tace masa, "Da sauki." Ya shafa kan Jr dake hannun Islam, yana saka musu albarka.

Kafin ya fara musu korafi: "Meyasa suka fito? Ai jikin Ehsaas ɗin da sauki. Su zauna suma su huta kafin ya farka."

Dan ƙasa da kai sukayi dukkanninsu kamar munafukai, kafin Habib Bai ya ɗan roƙar musu alfarma, Mai Martaba ya basu su ganshi sai su koma.

Girgiza kai kawai Mai Martaba yayi yana kallon Islam yace, "Kece babba yanzun. Ita idan ba ta san ƙa'idar gidan nan ba, yakamata ki riƙa sanar mata. Musamman a irin wannan yanayin na rashin tsaro, koda a asibitin kuke, fitar barkatai ba ta da amfani."

Jinjina kai Islam tayi tana cewa, "In sha Allah za'a gyara. Ba laifin Mehtav bane. Ni ce nace mata ma su zo su duba shi."

Mehtav ta waro ido tana faɗin, "Duk mu biyu mukai ai, nine nace zan biyota."

Murmushi Turaki yayi kafin yayi wa Mai Martaba rada a kunne dayasa yayi murmushi, kafin yace, "Ai to, ni ba ruwana. Next time in kukai laifi kukace zaku haɗa kai gaba ɗayanku, zan haɗa in yi ma faɗa ko in hukunta. Ba ruwana ai."

Murmushi dukansu sukayi. Musamman Habib Bai da wata irin nutsuwa yaji ta shigeshi ganin yadda Islam da Mehtav suke magana da ido kamar wasu kawayen da suka daɗe da sabawa.

Mai Martaba da kanshi ya buɗe musu ɗakin, kafin ya karɓe Jr a hannun Islam, yana cewa, "Kada ku tasar da mai d. Yau kabilanci yake ji da shi dan shi kaɗai yasani."

Dariya duk sukayi suka shiga, manyan kuma suka wuce duba Fulani, Hajar, da Abeey.

Islam ce ta ƙarasa gefensa na dama, Mehtav ta gurgura kujerarta zuwa gefen hagu. Sukai shiru kawai suna kallonshi. Kowacce da abinda take rayawa a ranta. Suna jin soyayyarsa kamar zata fasa kirjinsu ta fito.

It's fatoumspassion Don't forget to: Share Comment & Vote. [09/08, 21:26] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.