EHSAAS

Chapter 56

by @fatoumspassion

A nitse Ehsaas ya fara motsa hannunsa a hankali, wani irin nauyi ya ji yana ratsa jikinsa, kafin idanunsa su fara buɗewa da ƙadan-ƙadan, kamar wanda yake tsoron haske. A haka har sai da ganinshi ya dawo daidai, tarwai idonsa ya sauka a kansu, jiyay kirjinsa ya buga, musamman ganin fuskar Islam a gefensa, tana riƙe da hannunsa gently, looking super sad kamar ta cire ciwon da yake jikinta ya dawo kanta, haka take ji.

A gefe guda kuma, ya ga Mehtav na zaune a kujerar wheelchair ɗinta, idonta sun cika da wani irin relief na ganin ya farka. She looks super tired and exhausted.

A cikin seconds ya kare musu kallo da yanayin nasu baki ɗaya, kafin ya shiga kallonsu duka biyun. Ya kalli wannan, ya kalli wancan, ba tare da ya ce komai ba. Mamakin su ya cikashi, a ransa ya shiga raya:

"So this is what real blessing feels like - having these two women beside him, after almost losing everything."

Cike da tsokana ya dan lumshe ido. "Wataƙila zan farka na ga wannan dream ne…" ya furta da rauni, wani ƙanƙanin smile na bayyana a lips ɗinsa.

Islam ta matsa kusa sosai, ta yi masa magana a hankali. "Not a dream, Ehsaas. We're both here… for you. How are you feeling now, ko na kira doctor?"

Da ido ya yi mata alamar uhm uhm, kada ta kira, yana assuring dinta he is fine. Ahankali Mehtav ta danna kujerarta ta matso itama, gently, da sanyayyiyar murya tace: "Alhamdulillah, you're back… We prayed so hard ka dawo gare mu, you have no idea how worried we all are."

Ta karasa tana kallon Islam, data jinjina masa kai alamar yes. Wani irin sanyi ya ji a zuciyarsa. Duk pain ɗin bayan da yake ji, ji yayi kamar ya ragu. Ya kama hannunsu duka biyu, yana lumshe ido.

"Kun fi duk wani gift a duniya… Na gode. Wallahi ba zan manta wannan moment ɗin ba har abada."

Islam ta yi masa murmushi mai sanyi, tana shafa gefen face ɗinshi, tace: "Rest now… we're not going anywhere this time."

Mehtav ta yi dariya softly, ta dubi Islam, sannan ta kalle shi. "Mu biyu? That means ka shiga hannun best nurses in the world."

Murmushi ya yi, cike da tsokana, yake faɗin: "Lallai kuwa, da na fada hannun 'yan sari."

Dariya dukkansu suka yi, don sun san halin tsokanarshi. Hannunsu biyu a cikin nasa, yana jin kamar duk duniya ta tsaya a wannan lokacin.

Sun dauki mintuna a haka, cikinsu babu mai magana sai dai sound ɗin monitor da yake buga daidaito, daya cika dakin. Islam tana shafa hannunsa, Mehtav kuma tana kallon yadda ya lumshe idonsa kawai.

Sai da aka jima tukunna ya bude idonsa kaɗan, yana kallonsu yace: "Tell me… me ya faru bayan an harbe ni?" Muryarsa cike da curiosity da kuma tsoro.

Mehtav ce ta girgiza kai tana faɗin: "Mun ga tashin hankali, Ehsaas. Har na dauka maybe… we will lose you. I don't want to remember that moment, I was so scared."

Cike da kulawa yace: "I'm sorry… for making you both go through that. Na san… ba zan iya biyan irin wannan soyayyar da kukemin. Thank you for staying by my side."

Murmushi Islam ta yi, tana cewa: "You already paid us back, da kasancewarka a raye. That's all that matters."

Mehtav tace: "Kuma daga yau, no more reckless moves. We need you… Jr needs you."

Ehsaas ya lumshe ido, yana jin kalmomin su suna shigar masa har kasan zuciyarsa. Pain ɗin bayansa bai gushe gaba ɗaya ba, amma warmth ɗinsu ya fara danne duk wani raɗaɗi da yake ji a jikinsa yanzun.

Daidai lokacin doctor ya dawo, ya fara duba reading ɗin monitor. Yana murmushi yace: "He's stable now, amma zai buƙaci hours da dama na rest. Please, no heavy talk ko stress, princesses."

Murmushi Islam ta yi tana jinjina kai kafin ta yi masa godiya, sannan ta kalli Mehtav da alamar let's stay. Dukansu suka yi shiru, kawai suna zaune kusa da shi, suna jin numfashinsa a hankali.

Doctor ya kalli Mehtav yana faɗin: "You too, you need some rest."

Dan kwaba fuska ta yi alamar ba zata tafi ba. Girgiza kai doctor ya yi, yana haɗa ta da Ehsaas alamar ya yi mata magana kafin ya juya ya fice, yana mamakin stubbornness ɗin both wife and would-be wife ɗin prince.

With seriousness, Ehsaas ya kalleta yana faɗin: "Mehtav… you're hurt."

She tried to wave it off. "It's nothing, just my leg."

"Nothing? You think zan zauna nan ina kallon ki while I know the trauma you went through earlier and your legs are not okay, you can't even walk properly. You need some rest, you have to go now."

Ya ɗaga murya kaɗan, yana ƙoƙarin tashi daga gadon, sai wani irin sharp pain ya ratsa gefen kafadar baya da aka harba. Ya rintse ido da sauri, Islam ta matsa kusa tana riƙe shi ta maida shi baya tana cewa: "Easy, sire. Ka tuna surgery aka maka, stop shouting, you need some rest."

Idonsa yana kan Mehtav yace: "You need to rest more than I do. Please… go back to your room, I'm okay now."

Girgiza kai Mehtav ta shiga yi, idonta cike da hawaye. "I don't want to leave you. What if..."

"No 'what if'. I'm alive, and I'm not going anywhere."

Ya janyo hannunta, yana riƙe shi sosai. "You stayed long enough to let me know you're here. Now let me take care of you… even if it's just by sending you back to rest. Baby, pls talk some sense into her."

Ya ƙarasa yana kallon Islam, wadda ta dafa shi ta hana shi yunkurawar da yake ƙoƙari yi don ta san ba zai iya ba. Cike da nitsuwa ya ce ma Mehtav: "Look, we will stay by him in turns. Ke ki tafi ki huta, sai ki dawo da safe. Remember, leg injury needs proper rest."

Mehtav ta kalli Ehsaas, ta ga seriousness ɗinsa har cikin idonshi, ta san babu yadda za ta yi masa gardama. Ta yi murmushi mai rauni. "Fine… but promise, if you need anything, you will call me."

"I promise."

Da kanta ta danna abin kiran nurse, sai ga ta nan tazo cikin gaggawa. Duk yadda Islam ta so ta rakata, hanata ta yi, tace kawai ta zauna anan tare da shi, ita she will be fine in sha Allah. Suka wuce da nurse ɗin.

Nurse ɗin tana tura ta dakinta, ta ji muryar Paa da doctor: "Eh, ka tabbatar dai ba wani major injury a ƙafar tata? Na ga tana yawo da kujera." Muryarsa cike da kulawa.

Ta ji doctor yana assuring dinsa: "She will be fine, hutu kawai take buƙata. Idan ta samu, zata warware cikin kwana biyu, zata ci gaba da tafiyarta."

Inna tana zaune gefen gadon asibitin, tana daddanna chasbaha, idonta na kan Mehtav da ta shigo a cikin wheelchair. Hannu ta daga, tana faɗin: "Alhamdulillah… kin dawo lafiya."

Daidai suna ƙaraso gabanta, ta shiga shafa kanta kamar wadda ta shekara bata ganta ba tana mata sannu. Mehtav kawai ta jinjina kai tana ce mata she's fine, don sosai ta ji daɗin ganinta - musamman Abeey da ta ganta se ciye-ciyenta take yi kamar ba ita ce ta sume dazun ba, though she's still looking a bit pale but with her usual mischief hidden in the corner of her smile.

Ta soma sana'ar maganarta: "Big sis, how are you feeling? Dama jira nake ki dawo in baki labarin yadda ake ji in an suma, dama ban taɓa suma ba." Ta faɗa cike da excitement irin sumar wata abin arziki ce.

Mehtav girgiza kanta kawai ta yi, irin me hali baya canzawa ɗinnan, kafin nurse ta taimaka mata ta miƙe tana dingishi ta zauna saman gadon.

Abeey ta taho tana rungume ta, kafin ta yi kasa da murya wannan karon tana faɗi: "I was so scared."

Mehtav tace: "You should be, sbd if you aren't, I would've run away from you."

Turo baki Abeey ta shigo, ta yi tana faɗin: "Shegen gardin nan da ya matseni wani irin wari yake yi, ina ji ma shi ya bugar da ni yasa na sume ban ankara ba. Kin dai san ni jinina mai ƙarfi ne, ba ci ace dan wannan drug ɗin yasa na sume ba."

Jin zata fara mata kuri yasa Mehtav tace: "Kofa minti daya bakina yana kamako, kik tafi luuuuu, a haka jinin yake da ƙarfi. Ahh, lallai."

Cike da tsari irin na Abeey da son musu, take faɗin: "That's because I saw lots of gun… you're about to be shot fa, and Jr, that innocent baby… and-" ta yi shiru, idonta ya fara yin ruwa, tana tuna abin kamar yanzun ya faru.

Paa dake sauraron su, sallamar likitan da ya gama mai bayanin lafiyar Mehtav yayi, yana matsawa kusa da su. Ya dora hannu a kan kafadar Abeey. "Shhh, ba son ki rinka tuna bad memory ɗinnan, my princess. Abinda ya gabata, ya gabata. Duka kun fito lafiya, that's what matters."

Mehtav ta kalli mahaifinta: "Yes Paa, you should tell her it's not something to brag about. She's too young to be talking about this kinda things."

Ya jinjina kai, alamar he agreed with abinda ta faɗa. Abeey ta shiga zumbura baki don bata gama faɗar abinda take so ta faɗa ba.

Dariya Mehtav ta shiga yi, tana faɗin: "Yawwa Paa."

Habib Bai ya yi murmushi, cike da hikima, yake faɗin: "Mehtav…"

Yadda ya kira sunanta yasa ta tattara hankalinta, ta bashi baki ɗaya. Ya dan nisa, yana magana cikin magana yace: "I want you to always remember… your health comes first. Ko da kuwa akan Ehsaas ne, you can't fight his battles while injuring yourself."

Inna ta shiga jinjina kai tana faɗin: "Eh fa, Habibu, gwara ka faɗa mata dai. Domin idan tace zata cigaba da haka a gidan sarautar nan, lallai wata rana za a kira mu ta kashe kanta garin kare wasu. Ai babu abinda Abeeda bata faɗa min ba."

Dariya Abeey ta shiga yi, ganin itama Mehtav ta karɓi rabonta, don dazun nan Inna itama ta gama mata. Mehtav ta jinjina kai kawai, ba tare da ta gane inda maganar tasu ta dosa ba.

Inna cikin mita take faɗin: "Nikam, in dai irin wannan tashin hankalin ake gani a gidan sarautar, wallahi gara a hakura da maganar auren nan. Na ji ta fara fita a kaina."

Da sauri Mehtav da Abeey suka ɗago, suka kalleta a lokaci guda. Abeey ta yi saurin jawo kujerarta kusa da Mehtav. "Don't worry, Inna… I'll be your nurse. Zan tabbatar tana cin abinci da wuri, tana shan magani… don ta warke da wuri, ayi-ayi bikin nan, tun kafin mummunan fatan da kika fara mana ya tabbata."

"Kaji yar jakar uba!"

Tana kai mata duka, da sauri ta kauce, tana wa Inna dariya, dama ta saba tuburata haka. "Ni kike gayawa ina muku mummunan fata? Ki yi ci gidanku ai!"

"Tohm, Inna, in ba mummunan fata ba, wa ye dan uwanshi ze samu miji kamar Prince? Wao! Yay fata a fasa aure? Haba, Inna, ke baki ga kayan da yake jikinki ba a Nigeria? Kin taba sasune ba? Darajar Mehtav ɗin aka baki ba. Dubi gwalagwalan da ke jikinki yanzun."

"Habibu, kana jinta ko?" Inna ta soma riƙe baki tana ƙoƙarin matse ƙwalla irin na tsofaffi. "Goru takemin saboda nazo cin arziki gidan surukan 'yar uwarta? An ce miki ni ƙwadayi yay yi, yace me son abin duniya irin ki? Ungo tsiyarku ungo."

Na ce ta soma cire warwaro da zoven, tana watsawa Abeey. Paa ya riƙe kanshi yayi: "Wato Abeey will always be Abeey. After everything they went through, yau ɗin ma ba zata bar kunnansu shiru ba."

Abeey kwashewa ta shiga yi tana dariya. Sai da Paa ya ɗaka mata tsawa sannan ta dakata, tana tsayawa ta shiga ture turen baki irin na shagwababbun sangartattun yaran nan.

"This is my mother," ya faɗa cikin jan kunne. "The next time na ji kin faɗi magana kin faɗa, zaki ga other side of me, Abeeda Habib. Oya, come here."

Da sauri ta ƙarasa gabanshi tana dukar da kanta. "Apologize to her right now, me kan ƙwakwa kawai. Baki jin magana? Kullum kina troubling mini mama."

Abeey ciki-ciki ta shiga faɗin: "Kiyi hakuri tohm."

"Hakurin ma ai seda ka tilasta ta. Tabani, Habibu, daka barta yau-yau ka siya min tikiti na koma Nigeria. Ba zata sake buɗe baki ta min gorin kayan gidan da Mehtav zata yi aure ba."

Mehtav me take bayan dariya ƙasa-ƙasa? Tana mamaki hali irin na Inna da Abeey - sun fi kowa amince amma basa shiri kwata-kwata.

"Dan Allah, Inna, ki yi hakuri. In sha Allah ba zata sake ba. Mu dan jira, kin ga gidan ba lafiya ba. In muka ce zamu tafi yanzun, kin ga kamar kar su ga gudunsu muke don sun faɗa cikin tashin hankali, ko Inna?"

Dan jin Inna tai kafin tace: "Toh, in banda abin, Habibu, wa ke son tashin hankali dama? Amma dai ba ma ki ta taka ba, kar ace mana butulu."

Ta ƙare tana hararar Abeey, tana mata kashedi da hannu alamar zasu haɗu ne. Abeey ma ta faki idon Paa, ta farfara mata ido.

It's FatoumsPassion EHSAAS Don't forget to Share, Like, Comment & Vote.

[27/09, 12:25] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

EHSAAS - The Lost Prince

My people, this is just a small glimpse of what's coming next in EHSAAS - The Lost Prince. The journey is getting deeper, the secrets are unfolding, and wallahi you don't want to miss what's about to happen. Stay tuned, follow my updates, and let's enjoy this ride together.

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.

Islam ta jingina da mota tana dariya ƙasa ƙasa, hannunta riƙe da laptop ɗinsa, ƙasa ƙasa take faɗin: "aikuma ka shiga hannuna yanzu. Catch me if you can, Sire," ta ƙara sa tana cije lips ɗinta nakasa tana rolling mai eyes.

EHSAAS murmushi ya shiga yi kamar wani fool yana tunanin irin abinda ze mata yau idan suka koma gida su su biyu, don ta ganshi anan da kowa da kowa, shine ta ke ta tsokano shi kamar wani kakanta. Ji yake kamar ya fizgota right now amma kuma ba ze iya ba saboda kunyar jama'ar dake gurin, ga Fulani, gasu Mehtav. Yasan ko ya sha giyar wake ba ze iya tabata gaban su ba dadai da ne amma yanzu duk wani abu da ze darsa mata jin kishi ko makamantansu ya kan yi iya yinsa don gudun kada ta gani.

Kwafa yay yana shafa hannayenta ya dage mata gira ɗaya yana faɗin: "zaki sanine tonight, kar ki bari mu haɗa…"

Jin motsin Fulani a bayansa ya dakatar da shi da maganar da yake ƙoƙarin ƙara faɗa.

Harta matso ta dawo gefensa ta shiga shafa fuskarsa, ya dan lumshe ido yana murmushi saboda gani yake in ya buɗe duk za su san halin da Islam tashigar dashi yanzunnan. Ita kuwa me take yi banda murmushi ƙasa ƙasa.

Fulani tace: "Alhamdulillah babana, ka ji sauƙi. Jiki yayi kyau sosai. Allah ya ci gaba da kare min kai daga dukkanin sharri."

Ya dan sunkuya da ladabi, ya kai lips ɗinshi kan forehead ɗinta yay kissing yana faɗin: "Ameen, rayuwata."

Islam murmushi take musu. Mehtav ganin haka yasa itama ta matso daga gefen Abeey data isheta da surutu tana tambayarta me ta shirya ma EHSAAS na tarbarsa. A hankali cike da jin kunya tai ƙasa da kanta tana faɗin: "We are happy to have you back, EHSAAS, Allah ya kara tsarewa."

"Ameen ya rabb," ya furta yana sakar mata murmushi mai sanyi. Itama ta mayar mai kafin idanuwansa su koma kan Islam da take wasa da yatsunta a hankali tana murmushi ƙasa ƙasa.

Dagowa tai suka haɗa ido, ya dage mata gira ɗaya alamar yadda. Turo masa baki tai tana faɗin: "Yanzun dai ka ji Fulani ta yi maka addu'a, Mehtav ta yi maka, uhummmmmmmmmmmmmmmmmm nikuma…" Ta faɗa kamar me tunani cike da wasa sai ta ce: "Zan shirya maka food mai dadi wanda ba ka taba cinshi a duniya ba, the most sweetest food ever." Ta faɗa idonta cikin nashi tana rangwada mai kai kamar wata ƙaramar yarinya.

Kowa ya saka dariya don duk sun san ba wani abinci da ta iya sai dai ta saka ayi. Mehtav bata taba sanin Islam nada wannan playful side ɗin ba sai da ta zauna zaman jinyar asibitin nan sosai, ta ke da tsokana da wasa da dariya in ta saba da mutum. Duk da bata fiya mata ba amma tana ganin yadda take wa EHSAAS, in ta sashi a gaba ko in ta samu Fulani da Aman, ta na da shiga rai sosai. Sai yanzu take dada gane dalilin da yasa EHSAAS yake mugun kaunarta, tana da sanyin hali sai dai uban miskilanci har yanzu yana nan sai dai in ba ta ga dama ba. Zuwa yanzu Mehtav ta saba da halayenta.

Fulani ta girgiza kai tana murmushi tace: "Tohm kai ka ji EHSAAS, ka ce ni da Mehtav da muka tashi tun sassafe girki mu adana kayanmu, ga 'yata tace ta shirya maka na musamman."

Murmushi yay sanin ba kalmar wannan abincin Islam ke nufiba yace: "Maama, kar ki biye mata, ki ciyar da ɗanki mara lafiya in ba haka ba…"

Islam ta katseshi tai tana dariya tace: "In ba haka bane uhummmmmmmmmmmmmmmmmm…" Tana farfara mai ido.

Da sauri ya girgiza kai kamar me tsoronta yace: "A'a ba abinda nace baby, ai duk yadda ki ka ce haka za a yi."

Abeey dake gefe ta sheƙe da dariya tana faɗin: "Se dake maman Jr, shiyasa nake yinki."

Mehtav wani kallo ta aikamata da yasa ta ja bakinta tai shiru tana ƙasa da kai. Islam tai murmushi tana cewa: "Ni ma ina yinki Abeey, ni da ke one love ai gidana za mu tafi tare ko?" Ta jinjina mata kai alamar eh.

Kana ganin su duka ka san suna cikin annashuwa like one big happy family.

Bude motar tai ta zira laptop ɗin ta ajiye tana faɗin: "Bari na je na karbo maganin Jr dazun nashi yakare."

Da sauri ta juya, EHSAAS yana ta tsaye a aika. Da gudu ta soma haurawa stairs ɗin da ze sada ka da ainahin asibitin tana faɗin: "One minute, I won't take long."

Taku daya biyu ta tsaya cak. Hannunta ta ɗaura gefen kirjinta, tana jin wani zafi a kirjinta, kusan irin abinda take yawan ji kwana-kwanan nan har yafi na dacan da take ji. Ta riƙe kirjinta, luuuuu tai zata faɗi cikin zafin nama babu wanda ya san sanda Mehtav tai wuff ta rikota ta faɗo jikinta. tsabar rudewa EHSAAS sandarewa yay a tsaye.

Cikin firgici ya furta: "Islam?"

Wani irin tari takeyi mai tsanani, tana riƙe ƙirjinta. Numfashinta ya fara yin sauri kamar mai nutsewa. Idanunta suka soma lumshewa, jikinta ya fara karkarwa. "Ya Allah!" Fulani ta furta a rikice. "Ku kira likita!"

Nan da nan security suka shiga asibitin da yan tsirarun hadiman da sukazo dasu, duk wani likita dake asibitin sai da suka fiddoshi. Kowa ya rude.

Ehsaas kwata-kwata hankalinsa baya jikinsa. Yana zuwa ya karɓeta daga hannun Mehtav yana dawo da ita jikinshi yake faɗin: "Islam! Baby, look at me, me ya same ki? Ki buɗe idonki ki kalle ni. Don't you dare faint on me now."

Da sauri Mehtav take faɗin: "EHSAAS I think she's having panic attack again. This is not the first time naga tana having breath seizures ba. I first thought she's asthmatic but I think is not that. Rannan ma naga tayi kuma…"

"And why didn't you fucking tell me?!" taji EHSAAS ya daka mata tsawa da yasa ta yi saurin yin baya tana kallon idanuwansa da yay jajir kafin ya maida hankalinsa kan Islam cikin wata irin raunatacciyar murya yake faɗin: "Baby pls pls don't close your eyes."

Ta yi ƙoƙari ta ce da muryar rauni: "si…Sire… my chest… I can't…"

Daidai lokacin da tayi collapsing gaba daya a jikinsa duk likitocin suka karaso.

Monitors daga cikin ambulance da aka kawo kusa suka fara hayaniya lokacin da aka ɗaura mata oxygen.

Babban likitan asibitin ne ya shiga duddubata a hannun EHSAAS, in minutes ya gano issue ɗin ya kalli EHSAAS yana faɗin: "She's going into cardiac distress! We need to move her now!" Ya ƙarasa a hanzarce.

EHSAAS ya kalli likitan, idanunsa cike da rudewa yake faɗin: "What's happening to her? Why?!"

Likitan ya girgiza kai: "I can't say anything now but we suspect Dilated Cardiomyopathy, heart failure caused by long stress and trauma. This could be life-threatening."

Jikin EHSAAS wani irin sanyi yay ya saki, yana kallon fuskar Islam da tai wani irin mugun kyau. Ya riƙe hannunta bai san ya akaiba sai jin dumin hawaye yay akan fuskarsa ya shiga faɗin: "No, no, Islam, ba abinda yake damunki ba kenan ko? You promise me zaki rayu dani. Na tsawon rayuwa."

Nurses ne suka zo suka ɗauketa duk da yaki sakinta. Da ƙyar Fulani ta banbareta a jikinsa aka shigar da ita asibitin. Kasa mikewa yay saboda yana tsoron maganar likitan nan ta tabbata. Ba ze taba yafewa kanshi ba. Rungume shi take tana faɗa mai: "In sha Allah Islam will be fine. Ba abinda ake zargi bane. Yarinyar da yanzun kuka gama wasa da dariya da ita ba abinda ze sameta bi iznillah."

Mehtav tsayawa tai daga gefe, tana kallon yadda EHSAAS yake kuka kamar ƙaramin yaro. Zuciyarta ta karye, ta shiga yi gaba daya tana tunanin wace irin jarababbiyar soyayya ce wannan suke yiwa junansu. Tun a asibiti ta gane cewa soyayyar da take tunanin EHSAAS yana wa Islam ta ninka tunaninta sau dubu. Bayan kasancewarta first love ɗinshi itadin babbar kawar sace, saboda wataran idan suna wa juna tsiya se ka rantse su din ba wai masoya bane ko mata da miji. Sannan sometimes in yana mata abu kamar kanwarshi. Haka zalika itama Islam rokon Allah ta shiga yi ya tashi kafadun Islam, don ta san idan wani abu ya sami Islam ba zata sake ganin walwalar EHSAAS ba har abada.

Don't forget to Like Share Comment Vote

To catch every new chapter as soon as I drop it, follow me on all my platforms: 📱 TikTok: @fatoumspassion 📸 Instagram: @fatima-rufai-nasidi 📖 Wattpad: @fatoumspassion 📚 Arewabook: @fatoumspassion 💬 WhatsApp: ***

If you don't have my number, save it and send me a message saying "saved", so I can save yours back and you'll always get my story alerts whenever I upload a new chapter.

This is just the beginning… EHSAAS - The Lost Prince still has a lot to show you. Stick around, the best parts are still ahead. [01/10, 11:07] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.