EHSAAS

Chapter 57

by @fatoumspassion

Ahankali take taka kafar tana dan zazzaga dakin kamar yadda doctor din yayi instructing dinta kafin yafita kuma sosai taji dadin kafartata don Allah Allah takeyi tagama tatafi dakin EHSAAS rabonta da zuwa tun safe da taje yakorota yace itama jinyar take tatafi takula da kanta kwana biyunnan se takega kamar beson taringa yawan zuwa inda yake amman dazarar tadawo yata damunta da texts kenan iri iri yana tambayarta ya kafarta take? yatake ji? ko kuma yana missing dinta! amman da zaran taje shidai baze hade mata raiba amman kuma baya shishshige mata yadda yakeyi insuka kebe su biyu aranta taraya kodan agaban matarshi ne? dukda zuciyarta tadanji ba dadi, amman kuma tamai uzuri saboda kamar bayason yafiya zaqewa ne kartaji kishi akanta.

Daidai nan taji anmurda kofar dakinta anshigo wata matace tafara shigowa, tana kallon uniform din jikinta tasan hadimar cikin palace ce, se ganan wata dattijuwar mata tabiyota cikin shigar alfarma wacca kallo daya tai mata dukda bata gane wacece itaba tasan tana da matsayi mai girma acikin gidan.

ganinsu yasa tadan cigaba da takawa harta karasa gefen gadonta donta soma gajiya daman da takawar tazauna tana sakar musu murmushi tana musu sannu da zuwa don bata san alakarsu ds EHSAAS ba.

dattijuwar ce da baza tafi sa'ar fulani ba harma tafi Fulani kuruciya tasaki murmushi tana zaunawa gefenta saman gadon tashiga kare mata kallo tundaga sama har kasa tana murmushi mai kayatarwa dayasa hakorin makanta guda biyu suka bayyana tace "sannu amarya ashe haka yafaru aimu duk bamu saniba se daga baya mukejin labari hardake ta ritsa ashe! Allah yatsare Allah yakiyaye gaba," "Ameen" mehtav tace tai kasa da kanta tana dan wasa da yatsunta feeling nervous saboda yawanci yan uwan EHSAAS dasuke zuwa basa wani sakar mata fuska kamar haka don yawanci tsofaffinnan da keji da mulki basu cika washe hakora gaban yara irin hakaba,amman wannan ta sakar mata fuska sosai, Tace "baki ganeni ba ko? ainasan bazaki sanni ba saboda agidannan ba'a cika daukata da mahimmancin da ya kamata ba, yarima aidashi wani mutumin kirkine tunda ancemin anan kike da ya kawoki har sashena mungaisa don asan juna, ni din surukar kice don uwace nake gun yarima,ni matar mai Martaba ce ta uku,ana kirana da sarauniya hassana,"

Se alokacin Mehtav tadago tana kallonta ta sake gaidata, Itama tasake mata ya jiki ta amsa mata cikin girmamawa.

Kallon hadimarta tai tamata signal da ido jinjina kai taga hadimar tayi tafice tabasu guri. susu biyu adakin kureta da ido taga matar tayi gaba daya jitai ta tsargu musamman tana fahimci kishiyar Fulani ce tasan ba lallai alheri ne yake tafe da itaba, tanajin inama batace atafi da Abeey cikin palace ba da inna ta koma atleast intana nan atareda ita tana kara mata karfin gwiwa don harga Allah tsoro suke bata musamman bayan tasan details din alakar meemah da EHSAAS da kuma abinda yazo yajuye daga baya shiyasa batajin zata yarda dakowa itadai. "Masha Allah tubarkallah dake, babu abinda kika rasa wanda ake bukatar ya mace ta kasance dasu da baki dashi," sosai Mehtav tadago tana kallonta a mamakance irin tanason tagane me take nufi sarauniya hassana tasaki wani shu'umin murmushi tana fadin "kamar dai mu lokacin da aka auremu,amman tambayar anan itace shin kin shirya zama bora nahar abada na tsawan rayuwar ki?" Mehtav batace komaiba bin ta kawai take da idanuwanta masu kaifi dayasa dole hassana tadauke nata idon akanta tana wani murmushin yake don kallon datake mata takasa iya daurashi a ma'aunin kallon banza ko akasin haka. dafata tai tana fadin "sanda aka aureni fatata tafi taki jajir wllh,amman kalleni yau saboda rashin kulawar miji" tana nuna mata hannayenta da kana kalla kasan bawani abinda yakodar dasu face bleaching me tsanani da shafe shafe sunsha awarwarayen gwal tace "be damu damu ba kwata kwata se Fulani iname tabbatar miki kema haka zaki kare acikin gidannan idan baki tashi kinyi yaki da waccan arniyar yarinyar ba da aka qaqabama sunan musulunci kinsan yadda matan kabila suka iya murza kan namiji kuwa kinsan su fitsararru ne ba abinda ba zasuyi wa namiji ba shiyasa suke haukacewa akansu, don haka tun kafin kishiga daga ciki nafara karbo miki wani lakani daga gurin Malam yacemin indai har kikai amfani dashi idan EHSAAS ya kasance tare dake baze taba kara jin sha'awar wata ya mace aduniya ba bayan ke, saboda ita kanta yarinyar ba'a zaune takeba kina ganin yadda Fulani hajar ke nan nan da ita bazata taba barinta hakaba abinda sukai amfani dashi akan Mai Martaba ya haukace akanta nafi kyautata zaton shine suka sakama EHSAAS shima bayaji baya gani akan waccan peace din, donhaka sekin tashi tsaye nayi bincike Mai kyau akanki tunda nasamu labarin ke marainiya ce da irin alheran da kikai ma EHSAAS hardama ita kishiyar taki nagane ke mutuniyar kirki ce kuma naji inason in temaka miki tunda bakida uwar da zatai miki wasu abubuwan inason daga yau kiringa daukata amatsayin mahaifiyar ki,"

Mehtav wata irin bazawarar dariya tasaki aranta tana fadin "Allah yakiyaye mushrika tazama mahaifiya ta" amman afili da yake batason tarama kanta makiya tunkan tashiga daga ciki da yake tanada wayo sosai seta cemata tagode sosai kawai. bude jakar ta tai taciro mata wasu kullikan magunguna ta ajje agefenta tana fadin "kada kibar kowa yasani kinji dagani seke wannan sirrin shina rike shiyasa ni har yanzun Mai Martaba yakasa rabuwa dani kamar yadda ya rabu da Mai babban daki gatacan ta haukace rai ahannun Allah don haka kema kifara da wannan muga kamun ludayin ki in yaso in kikaji dadinshi se indauke ki inkaiki takanas ta kano" jinjina kai Mehtav kawai tai tana kallon abinda ta ajje mata ta jingina da bed din ta lumshe ido alamar tagaji da saurarenta ganin haka yasa hassana washe baki tana fadin "aibase nace karki fadawa kowaba naga kinada mugun hankali da sanin yakamata amman zansake jaddada miki wannan yazamana dagani seke kada wani yasake yasan mena baki" jinjina mata kai Mehtav kawai tai tamike tanai mata sallama tafice daga cikin dakin tana sakin wani shu'umin murmushi aranta tace "ni jakace ai yadda nai sake akan waccan matar tafi karfina wannan dole takasance tadamana yadda nima za'a ringa damawa dani kuma bazan taba bari itama tazo tamike kafa har tai ciki ta haihu ba, dolene nai amfani da wannan dabarar na lalata mata mahaifa tunkan ayi auren inba hakaba yarima natara iyali agidannan nikuma tawa takare kenan itama dayar senasan yadda nai na tsayar da haihuwar tata."

Daga gun Mehtav kuwa tana ganin ficewar matar tatashi tana jan wani dogon tsaki ta wuce bandaki da zazzage magungunan cikin toilet tai flushing ta wurgar da ledojin a waste bin tana komawa saman gado da ace gari banza ne tsaf seta gargasa mata bakar magana amman kuma ba zataiba saboda ayadda taga matar inhar tanuna mata bata amince da manufarta ba she'll go against her batason tatarama kanta makiya tunkan arigada adaura auren amman bari ai auren ta ayyana aranta seta gyarama kowana shege zama itaba Islam bace bazata taba daukar rainin hankalin da akai mata ita anata farkon aurenba duk kar take kallonsu.

Kayan jikinta ta sauya zuwa doguwar rigar atamfa mai kyau tayafa gelenta ba tareda tasaka dan kwali ba tadau wayarta tawuce dakin EHSAAS. Ahankali takarasa tadan kwankwasa kofa cikeda nutsuwa seda yabata izni sannan tashigo.

hango Islam tai saman gadon nashi tana barcinta hankali kwance shikuma yana gefenta da hannu daya yake amfani yana rubuce rubuce a laptop dukda dayan hannun ma ya warke Alhamdulillah amman anhanashi yawan amfani da bangaren hannu gudun stressing gun ciwan.

tunda yaga itace yatsayar da rubutun nashi yana kallonta cikeda so kamar ya hadiyeta harseda taji kafafuwanta sun soma hardewa kafin takaraso gurinsa tabude baki zatai magana ya daura yatsansa a lebensa yana cemata "shhshhhhhh" Alamar tai shiru yay mata nuni da Islam da ido wacca ke barcinta hankali kwance mikewa yay daga saman gadon yay mata alama da su nufi couch din dakin laptop din tadaukar mai suka wuce saman couch Mehtav tadan samu guri nesa dashi tazauna, murmshi yay ganin se wani sunkuyar dakai take kamar budurwar kauye tasa laptop dinshi atsakiyar kujerar daukewa yay ya mayar saman table yana karasowa daf da ita, akunnenta ya rada mata yana fadin "Budurwana yadai irin wannan haske haka," murmushi tai tana wasa da fararen ya tsunta madaidaita dasuka ji manicure kana gani kasan tana kula dasu sosai, dama Mehtav ba daganan ba indai gurin tsafta ce.

tanajin saukar numfashinsa agefen wiyanta ya rada mata "ni bantaba ganin wanda zaman asibiti yasa kyau ba se wannan yanmatar meye sirri abani ma, anata glowing, look at your cheeks my cuticle" sosai wannan dabi'ar tashi take karasa tana sonshi kullum suka hadu one way or the other seya samu abinda ze fada yay complimenting dinta yace tanada kyau duk kuwa da tasan yafita kyau kuma matarshi ma tafita kyau amman kullum suka hadu seya nanata mata yadda takeda kyau sau ba adadi wai ko zasuyi canzan farar fatar yaga tata tafi kyalli dakyau," "shsshshsshhh" itama tace mai tana nunamai Islam dake barci alamar karya tasheta cikin rada yace mata "tagaji sosai jiya batai barci ba Jr ne ya kwana da zazzabi se yau yasauka maama tatafi dashi shiyasa data kwanta ma ban tashe taba banson stressing dinta," murmushi Mehtav tai cikin tsokana tace mai "loverboy," murmushin shima yayi yana kallon kafarta yace "how's your leg?" yana kokarin dubawa da sauri ta janye tana dan zaro ido saboda shock din dataji daya taba mata kafar. turo baki taga yayi yana dan kwanciya saman couch din yace "just innocent checking" yana mata naughty murmushin dayasa tashiga girgiza kai,alamar bataso. "yaushe sukace zasu sallamemu ne uhm? nagaji da zaman asibitinnan" ta tambayeshi tana marairaicewa,dan jim yay kafin yace "ni datini natafi gida kinga baby ce tace wai karya sallameni sena gama warkewa nikuma nace mai karya sallameki se ranar da za'a sallameni kinsan intasa rigima se abinda tace akeyi," Yakarasa yana kallon Islam dake barci yana murmushi, dan waro ido tai saboda tabbas taji ajikinta lokacin sallamar ta yayi saboda ta warke kuma kafafun tana takasu sosai yanzun meyasa likita be sallameta ba ashe ashe shine yace kar a sallameta, tace "tohm meyasa nikuma meye nawa aciki dazaka sani zaman asibitin dole, nifa I hate hospitals, is between you and islam why will you involve me in your lovers buffering" yace "inkika tafi bazan ringa ganinki kullum safe rana dare kamar yadda nakeso ba, you'll only becoming once kuma da mutane and I don't like that, sarki kishi kawai"

Murmushi kawai tai donta fahimci this is his way of telling her beson yay nesa da ita zeyi kewarta, "Nifa ba kishi nakeba" Tafada cikeda bore Yace "yes your jealous and is kinda cute" yakarasa yana tsokanarta, sunfi minti biyar ahaka yanaja tanaja kafin tasakarmai kawai ganin kawai fitina yakeji yaudin.

Tace "EHSAAS"

Lumshe ido yay yana amfasawa da "Mehtav," I had a visitor today tafada mai bluntly saboda batason ko yazo yasani daga baya ya tuhumeta dan meyasa bata fada mai ba duk yadda sukai da hassana seda takwashe da fada masa da yadda tai flushing magungunan.

kafeta yay da ido yana sauraronta harta gama bece komai ba duk kasa kasa suke mgnr koda akusa dasu kake ba lallai ka tabajin mesuke cewa ba don karsu tashi Islam dake barci.

Jin bece komai ba yasa tadago kai tana kallonshi tace "kayi shiru?" murmushi kawai yay yana riko hannunta yay kissing knuckles dinta yace "I'm very proud of you Mehtav, kinada wayo da hankali sosai fiyema da yadda nai tinani, don Allah don't listen to anyone dazezo adauraki ahanya mara kyau acikin gidannan dagaske itadin matar mahaifina ce yanzun idan nace zandau mataki akanta za'a ce am after them all inason in kori kowa daga kusa dashi inbar iya mahaifiyata zezama abin magana, kinga waccan innocent baby din dake sleeping yafada yana nuna mata islam dake barci babu abinda tasani Mehtav she's too good to be true, ayadda nasanta wllh bazata taba cutar dake ba duk wanda yazo don yay turning dinki against her pls don't ever listen to them kinji, that girl deserve to be loved and cherish Mehtav she went through alot, I want to give her peace saboda babu abinda takeso arayuwarta seni se peace dinta, she's ready to accept you for me, Mehtav nasan kishi halak ne amman banason ya kasance shine ze zama ladder din da za'a yi amfani dashi acutarmin daku biyun pls don't listen to them kinji duk abinda suka baki don't use it,impact duk sanda tadawo find a way to record your conversation inason in kamata da hujja," jinjina kai tai tace mai "I will in sha Allah bazaka taba samun issue daniba bi iznillah, we will leave peacefully," "Thank you" yafada yana dagowa yamatso kusa da ita yana wani shagwabe mata yace "Mehtav" tace uhm tana dan basarwa don ba karamin tasiri abinda yake mata ya keyi ajikinta ba, "inasonki " yafada yana murmushin daya bayyanar da dimple din dake both side na face dinshi dayasa itama tai murmushi tana kautar dakanta gefe guda. ya cigaba da rada mata wasu kalmomi dasuke dada narkar mata da zuciya tana murmushi. sun dan jima ahaka nan kafin suji anfara knocking kofar da dan karfi wanda hakanne yatashi Islam daga barcin da take tadan mirgino ahankali tana laluben EHSAAS dake gefen ta yana ganin haka yay saurin mikewa daga gefen Mehtav yawuce kusa da ita tunkanma tajuyo tai ido biyu dashi gefen Mehtav din su baby ansha barci yakarasa yana zama gefenta hankalinta kuma ya koma kan kofa tana turo baki cikin shagwaba take furta "waye kuma yazo ya tasheni ina dan barci na" daidai nan jalila ta turo kofar bayanta watta hadima rike da basket din abincin EHSAAS na musamman wanda aka shiryo musu daga bangaren Fulani Queen layla ce datafa da kanta. karasawa tai suka gaisa da EHSAAS Islam tamike tana fadin "shine daga cewa zakije kidawo dazun kikai zamanki koh," murmushi jalila tai tana fadin "tuba nake Princess kinga mommy ce tace gwara intsaya intaho muku da lunch dinku shiyasa ma kikaga najima amman aikinsan ingari banzane bazan tafi inbarki ke kadaiba" murmushi tai cikin wasa take fadin "sire kaji dadin baki koh," hadimar na ajje basket din bayan tagaida EHSAAS tamai Allah yakara sauki tafice a dakin.

Islam tasauko daga kan gadon se asannan ta lura da Mehtav da yake da baya tajuya mata dake zaune shiru ita kadai murmushi tai tana fadin "a'ah Mehtav kece anan yaushe kikazo bansani ba aiseki tasheni" murmushi kawai Mehtav tai tana tambayarta "yame jiki" tace mata " alhmdlh dasauki yanaki karfin jikin?" tace mata "itama da sauki alhmdlh," tace "kinci abinci ga abinci ankawo bari in zuba miki" takarasa gun basket din dasauri jalila tace "uhm Princess an ajje mata nata a dakinta ai kafin mu iso nan," Islam tai murmushi tasoma ciro hadaddun food warmers din daga cikin basket din me girma tace "aiduk dayane danan din dacan setafi jin dadi intaci damu koh," jalila hararar gefen ido take aikama Mehtav wacca tamike tana cewa Islam "tabarshi kawai ita batajin yunwa sef" Islam zata fara mita bata tsaya bata dama ba tai mata sallama tawuce. tana fita Islam takalli jalila tana tambayarta "wai meye haka mai tai miki na lura gaba daya duk sanda Mehtav kenan sekin nuna mata cewar ita barece acikinmu meye a abinci kuma jalila nima ba baren bace aka auroni aka kawoni cikinku kidena bakyau pls kefa macece," jalila hade rai tai tana fadin "waike islam wace irin zuciya ce dake ne eh kishiyarki fa zata zama, shine harda wani cewa azuba mata abincin mijinki, mommy fa ta girki na musamman saboda shi inaga ai batakai matsayin cin abincin da prince zeci ba, kuma kicigaba da bude mata hakora haka wllh zakizo kina dana sani nan gaba tunda ke ba zuciyar mata akirjinki" saroro Islam tai tana kallon yadda take hakilo kamar itace ma akace za'ai ma kishiyar itafa tunda taga abinda Mehtav tai akan danta tariga tasaka aranta bazata taba kishi da itaba kuma ba dare ba rana addua take Allah ya yayemata duk wani kishinta acikin zuciyarta. "Keeee..." EHSAAS yafurta yana kallon jalila data manta shaf yana cikin dakin tai tsuru tsuru da ido don tana mugun shakkarta, "get out," wuri wuri tai da ido tana fadin "uhmm ahmmm yaya....." "get out" yafada yana daka mata tsawar datasa tai saurin juyawa tafice adakin gaba daya Islam duk jikinta yay sanyi tatsaya rikeda plate ahannu tashi yay yakarasa da hannunshi guda daya ya kamota ya zaunar da ita gefen inda ze zauna kafin shima yazauna yace "don't mind her kinji, karki bari duk abubuwan datake fada yashiga kanki Islam pls promise me," girgiza mai kai tai kafin tace "can I ask you something?" jinjina kai yayi yana kallonta, "kodai jalila tana sonka ne bansani ba?" dan wara ido yay kirjinsa na bugawa yay saurin girgiza kai yana fadin "how when uhm?" tace "nima dai kawai tambaya nai I've being wondering kwata kwata she's not thesame girl I meet sanda nafara zuwa gidannan after I married you kullum batason taxo inda nake she's avoiding duk abinda ze hadamu,se bayan accident dinka muka koma yadda muke and now Mehtav she hate Mehtav sire, kuma Mehtav bata taba mata wani abin rashin kirkin ba why is that? idan ba sanka takeba tayaya zata ringa kishi da Mehtav kamar ita ce za'ai ma kishiyar," girgiza kai yay cikeda wayo don baze tabaso sirrin dasuka riga suka birne shida jalila wani yasani ba yasan idan har Islam tasan jalila na sonshi za'a iya samun matsala duba da alakarsa da jalila tunda bawai kishi Islam tadena ba kawai dai tadanne zuciyarta ne akan Mehtav kadai, ita kadai tayarda taraba mijinta dashi banda wani kuma yace "stop overthinking baby kawai ke take ta yawa kishi kinsan mata akwai taya bera bari, yarinyar da akwai saranar tama akanta,kibar wannan mgnr yanzun abinda nakeso kiyi shine yunwa nakeji come and feed me karna fara miki kuka" yakarasa yana jan dogon hancinta murmushi kawai tai tamike tazubo musu abinci a plate daya sukaci dukda deep down bata yarda da abinda EHSAAS yace mata 100% ba amman dai tashare maganar don tunda yabasar abinda take xargi ze iya zama gaskiya kenan.

Har dare Mehtav bata sake dawowa ba se abakin nurse suke jin tanemi sallama gurin likita ya hanata tace zatai tafiyarta bashiri ya rubuta mata sunmabar asibitin tareda babanta. EHSAAS yayi mamakin jin anyi discharging dinta batazo sunyi sallama ba bashiri likita yana zuwa shima yasaka rigimar asallameshi dakyar Islam da likitan sukai convincing dinsa yakara kwana gobe da safe se yatafi kawai.

Adaren ranar mom din Islam tazo taduba Jr dake gurin Fulani tabiyo taduba EHSAAS a asibiti ma, sosai Islam taji dadin ganin mahaifiyar tata ta tambayeta ina babanta tace mata yace yana musu Allah yasawwake amman baze sake shigowa palace dinnan ba hakanma Islam tace tagode, taraka mom dinta har gaban mota,nan taciro ATM cards dinta sababbi fil wanda bankin datake amfani dashine tun agida da babanta yasa akai freezing tun bayan aurenta da EHSAAS wanda suke loda mata kudade aciki nasa daban na babarta daban tabata yace gashinan in wata bukatar tatashi base tana yawan tambayar mijinta, hakan dayay kuma tasake tabbatarda Abraham Zion yayi accepting dinta fully amatsayin yarsa da auren kuma EHSAAS akanta taji dadi sosai dukda bawai matsalar kudi ce da itaba domin ita kanta batasan adadin kudaden da EHSAAS ke zuba mata a account ba ga monthly allowance da Mai Martaba ke saka mata shima, EHSAAS kuwa koda draft takaranta tamai reviewing seya biyata, Haka kawai inya samu alheri akasuwancinsa se taji alert aside from monthly salary dinshi na prince publishing da yake rabawa biyu yasamata rabi wai tai siyayyar gida bayan duk wani abun bukata kanma tace yakawo ya ajje, ga gifts iri iri da baya gajiya da bata,tana komawa dakin tanunama EHSAAS tana murmushi take fadamai yadda sukai da mamanta ya tayata murna sosai har yana tsokanarta wai rich kid,tace itakuma tace mai royal kid.

Washegari tun da suka tashi ta kira Mehtav data amshi lambarta tasanar da ita yau za'a sallami prince, tafadawa Fulani da yake yanzun suna sashenta tun bayan abinda yafaru, Mehtav ce tacema Fulani suyi masa girki cikeda farinciki suka shiga kitchen Fulani yarinyar ta matukar burgeta yadda taga batada gandar aiki ko kadan cikin awanni kadan suka shirya hadaddun girkuna na alfarma harma da wasu abinciccikan na Nigeria da Fulani batasan dasuba duk saida Mehtav tayi Fulani se sannu take mata tana tina tar da itafa jiya aka sallameta a asibiti tayi ahankali murmushi kawai take mata seda suka gama sannan Mehtav tatafi tafesa wanka duk suka shirya don Fulani tace sune zasuje sutaho dashi daga asibiti Abeey se zumudi takeyi. Acikin limo aka daukesu zuwa asibitin Abeey se jin dadi takeyi prince yasamu sauki, lumshe ido Mehtav tai harsuka isa harabar duk suka sassauka don karasawa ciki Mehtav kasa fitowa tai Abeey tadan girgiza ta tana fadin "anzo fa yah Mehtav lets go" girgiza kaitai takurawa kofar ido kafin tace "kuje ni zantaho daga baya" dan tabe baki Abeey tai kafin tasauka daga cikin motar tanufi entrance din asibitin intama. Mehtav rufe idonta tai kawai bata san me yasaba kawai she's feeling restless gaba dayanta yau.

Hadimai taga sun soma fitowa da kayansu EHSAAS anzuba acikin boot din motocin bayansu kafin ta hango inna da Fulani sunfito suna murmushi duk subiyun,

inna tanata magana batasan metake cema Fulani ba amman dai tasan duk abinda take cewa yana bawa Fulani nishadi shine yasanya take dariya har haka,kafin tahango EHSAAS da Abeey da Islam sun taho dasauri Abeey tawuce gurinsu Fulani, kallon EHSAAS da Islam takeyi yadda takemai magana kasa kasa shikuma ya kafeta da ido kamar ya hadiyeta wani abu taji ta hadiye akasan makoshinta dasauri tashiga addu'a tabude motar itama tawuce gurinsu fulanin amman tana satar kallon couples din ta gefen idonta. Itakam Islam tsokanar shi takeyi kasa kasa sanda suka fito take cemasa "Finally,Sire" Dage mata gira daya yay yana kallonta yasan she's up to something intana wannan dariyar da magana kasa kasan "Kasan me na tanadar maka surprise a gida? Amamakance sanin suna tare tun safe wana surprise zata shirya masa yake tambayar ta "which surprise?" Lumshe ido tai tashiga rada mai akunne "Do you know what I've been keeping for you in our bed? I made it soft and warm just the way you like… and I'm not wearing anything underneath my abaya. The moment you step in, I'll let you have me however you want" Wani dogon numfashi taji yaja idanuwansa nasake kankancewa,yashiga kare mata kallo to be sure she's just joking don abayan ne dagaske ajikinta yadan maze ganin da innerwears aciki yagirgiza kai yana lumshe ido trying hard yasaita kanshi saboda mutanen dake zagaye dasu "Islam…" ya furta da ƙasa kasa "don't start what you can't finish here." Dariya tasaki mai taushi ta jingina da kafadarsa kamar tana taimaka masa wurin tafiya. amman a zahiri tasa hannuntane tana wasa da yatsunsa, tana sosa masa shi tayadda bakowa ze lurada abinda sukeyi ba. Ya lumshe ido, yana matse haƙora saboda yana mugun kunyar Fulani da sauran mutanen dake gurin amman fitinar Islam nanema ta zautar dashi atsaye "Ya Allah, baby plss…Ki daina kafin kowa ya gane halin da nake ciki." Maimakon tabari segani yay tadanyi dage cikin kunnenshi tashiga rada mai "Tonight, I'll make you forget every pain, every bullet, every scar,just get ready royal kid." Besan sanda yay kokarin fizgota jikinsa ba amman in no time ta kauce tana kyalkyala masa wata naughty laugh tana nuna mai saitin su Fulani da idanu alamar ana kallonsu, karbar laptop ɗinsa tai daga hannun wani guard, ta nufi mota da sauri, tana tafiya da wani irin playful walk, tana waiwayowa tana mai gwalo besan lokacin daya soma binta abaya ba Har yakarasa inda take, Islam ta jingina da mota tana dariya ƙasa ƙasa, hannunta riƙe da laptop ɗinsa, ƙasa ƙasa take faɗin "aikuma ka shiga hannuna yanzu. Catch me if you can, Sire," ta ƙara sa tana cije lips ɗinta nakasa tana rolling mai eyes.

EHSAAS murmushi ya shiga yi kamar wani fool yana tunanin irin abinda ze mata yau idan suka koma gida su su biyu, don ta ganshi anan da kowa da kowa, shine ta ke ta tsokano shi kamar wani kakanta. Ji yake kamar ya fizgota right now amma kuma ba ze iya ba saboda kunyar jama'ar dake gurin, ga Fulani, gasu Mehtav. Yasan ko ya sha giyar wake ba ze iya tabata gaban su ba dadai da ne amma yanzu duk wani abu da ze darsa mata jin kishi ko makamantansu ya kan yi iya yinsa don gudun kada ta gani.

Kwafa yay yana shafa hannayenta ya dage mata gira ɗaya yana faɗin: "zaki sanine tonight, kar ki bari mu haɗa…"

Jin motsin Fulani a bayansa ya dakatar da shi da maganar da yake ƙoƙarin ƙara faɗa.

Harta matso ta dawo gefensa ta shiga shafa fuskarsa, ya dan lumshe ido yana murmushi saboda gani yake in ya buɗe duk za su san halin da Islam tashigar dashi yanzunnan. Ita kuwa me take yi banda murmushi ƙasa ƙasa.

Fulani tace: "Alhamdulillah babana, ka ji sauƙi. Jiki yayi kyau sosai. Allah ya ci gaba da kare min kai daga dukkanin sharri."

Ya dan sunkuya da ladabi, ya kai lips ɗinshi kan forehead ɗinta yay kissing yana faɗin: "Ameen, rayuwata."

Islam murmushi take musu. Mehtav ganin haka yasa itama ta matso daga gefen Abeey data isheta da surutu tana tambayarta me ta shirya ma EHSAAS na tarbarsa. A hankali cike da jin kunya tai ƙasa da kanta tana faɗin: "We are happy to have you back, EHSAAS, Allah ya kara tsarewa."

"Ameen ya rabb," ya furta yana sakar mata murmushi mai sanyi. Itama ta mayar mai kafin idanuwansa su koma kan Islam da take wasa da yatsunta a hankali tana murmushi ƙasa ƙasa.

Dagowa tai suka haɗa ido, ya dage mata gira ɗaya alamar yadda. Turo masa baki tai tana faɗin: "Yanzun dai ka ji Fulani ta yi maka addu'a, Mehtav ta yi maka, uhummmmmmmmmmmmmmmmmm nikuma…" Ta faɗa kamar me tunani cike da wasa sai ta ce: "Zan shirya maka food mai dadi wanda ba ka taba cinshi a duniya ba, the most sweetest food ever." Ta faɗa idonta cikin nashi tana rangwada mai kai kamar wata ƙaramar yarinya.

Kowa ya saka dariya don duk sun san ba wani abinci da ta iya sai dai ta saka ayi. Mehtav bata taba sanin Islam nada wannan playful side ɗin ba sai da ta zauna zaman jinyar asibitin nan sosai, ta ke da tsokana da wasa da dariya in ta saba da mutum. Duk da bata fiya mata ba amma tana ganin yadda take wa EHSAAS, in ta sashi a gaba ko in ta samu Fulani da Aman, ta na da shiga rai sosai. Sai yanzu take dada gane dalilin da yasa EHSAAS yake mugun kaunarta, tana da sanyin hali sai dai uban miskilanci har yanzu yana nan sai dai in ba ta ga dama ba. Zuwa yanzu Mehtav ta saba da halayenta.

Fulani ta girgiza kai tana murmushi tace: "Tohm kai ka ji EHSAAS, ka ce ni da Mehtav da muka tashi tun sassafe girki mu adana kayanmu, ga 'yata tace ta shirya maka na musamman."

Murmushi yay sanin ba kalmar wannan abincin Islam ke nufiba yace: "Maama, kar ki biye mata, ki ciyar da ɗanki mara lafiya in ba haka ba…"

Islam ta katseshi tai tana dariya tace: "In ba haka bane uhummmmmmmmmmmmmmmmmm…" Tana farfara mai ido.

Da sauri ya girgiza kai kamar me tsoronta yace: "A'a ba abinda nace baby, ai duk yadda ki ka ce haka za a yi."

Abeey dake gefe ta sheƙe da dariya tana faɗin: "Se dake maman Jr, shiyasa nake yinki."

Mehtav wani kallo ta aikamata da yasa ta ja bakinta tai shiru tana ƙasa da kai. Islam tai murmushi tana cewa: "Ni ma ina yinki Abeey, ni da ke one love ai gidana za mu tafi tare ko?" Ta jinjina mata kai alamar eh.

Kana ganin su duka ka san suna cikin annashuwa like one big happy family.

Bude motar tai ta zira laptop ɗin ta ajiye tana faɗin: "Bari na je na karbo maganin Jr dazun nashi yakare."

Da sauri ta juya, EHSAAS yana ta tsaye a aika. Da gudu ta soma haurawa stairs ɗin da ze sada ka da ainahin asibitin tana faɗin: "One minute, I won't take long."

Taku daya biyu ta tsaya cak. Hannunta ta ɗaura gefen kirjinta, tana jin wani zafi a kirjinta, kusan irin abinda take yawan ji kwana-kwanan nan har yafi na dacan da take ji. Ta riƙe kirjinta, luuuuu tai zata faɗi cikin zafin nama babu wanda ya san sanda Mehtav tai wuff ta rikota ta faɗo jikinta. tsabar rudewa EHSAAS sandarewa yay a tsaye.

Cikin firgici ya furta: "Islam?"

Wani irin tari takeyi mai tsanani, tana riƙe ƙirjinta. Numfashinta ya fara yin sauri kamar mai nutsewa. Idanunta suka soma lumshewa, jikinta ya fara karkarwa. "Ya Allah!" Fulani ta furta a rikice. "Ku kira likita!"

Nan da nan security suka shiga asibitin da yan tsirarun hadiman da sukazo dasu, duk wani likita dake asibitin sai da suka fiddoshi. Kowa ya rude.

Ehsaas kwata-kwata hankalinsa baya jikinsa. Yana zuwa ya karɓeta daga hannun Mehtav yana dawo da ita jikinshi yake faɗin: "Islam! Baby, look at me, me ya same ki? Ki buɗe idonki ki kalle ni. Don't you dare faint on me now."

Da sauri Mehtav take faɗin: "EHSAAS I think she's having panic attack again. This is not the first time naga tana having breath seizures ba. I first thought she's asthmatic but I think is not that. Rannan ma naga tayi kuma…"

"And why didn't you fucking tell me?!" taji EHSAAS ya daka mata tsawa da yasa ta yi saurin yin baya tana kallon idanuwansa da yay jajir kafin ya maida hankalinsa kan Islam cikin wata irin raunatacciyar murya yake faɗin: "Baby pls pls don't close your eyes."

Ta yi ƙoƙari ta ce da muryar rauni: "si…Sire… my chest… I can't…"

Daidai lokacin da tayi collapsing gaba daya a jikinsa duk likitocin suka karaso.

Monitors daga cikin ambulance da aka kawo kusa suka fara hayaniya lokacin da aka ɗaura mata oxygen.

Babban likitan asibitin ne ya shiga duddubata a hannun EHSAAS, in minutes ya gano issue ɗin ya kalli EHSAAS yana faɗin: "She's going into cardiac distress! We need to move her now!" Ya ƙarasa a hanzarce.

EHSAAS ya kalli likitan, idanunsa cike da rudewa yake faɗin: "What's happening to her? Why?!"

Likitan ya girgiza kai: "I can't say anything now but we suspect Dilated Cardiomyopathy, heart failure caused by long stress and trauma. This could be life-threatening."

Jikin EHSAAS wani irin sanyi yay ya saki, yana kallon fuskar Islam da tai wani irin mugun kyau. Ya riƙe hannunta bai san ya akaiba sai jin dumin hawaye yay akan fuskarsa ya shiga faɗin: "No, no, Islam, ba abinda yake damunki ba kenan ko? You promise me zaki rayu dani. Na tsawon rayuwa."

Nurses ne suka zo suka ɗauketa duk da yaki sakinta. Da ƙyar Fulani ta banbareta a jikinsa aka shigar da ita asibitin. Kasa mikewa yay saboda yana tsoron maganar likitan nan ta tabbata. Ba ze taba yafewa kanshi ba. Rungume shi take tana faɗa mai: "In sha Allah Islam will be fine. Ba abinda ake zargi bane. Yarinyar da yanzun kuka gama wasa da dariya da ita ba abinda ze sameta bi iznillah."

Mehtav tsayawa tai daga gefe, tana kallon yadda EHSAAS yake kuka kamar ƙaramin yaro. Zuciyarta ta karye, ta shiga yi gaba daya tana tunanin wace irin jarababbiyar soyayya ce wannan suke yiwa junansu. Tun a asibiti ta gane cewa soyayyar da take tunanin EHSAAS yana wa Islam ta ninka tunaninta sau dubu. Bayan kasancewarta first love ɗinshi itadin babbar kawar sace, saboda wataran idan suna wa juna tsiya se ka rantse su din ba wai masoya bane ko mata da miji. Sannan sometimes in yana mata abu kamar kanwarshi. Haka zalika itama Islam rokon Allah ta shiga yi ya tashi kafadun Islam, don ta san idan wani abu ya sami Islam ba zata sake ganin walwalar EHSAAS ba har abada.

Don't forget to Like Share Comment Vote

To catch every new chapter as soon as I drop it, follow me on all my platforms: 📱 TikTok: @fatoumspassion 📸 Instagram: @fatima-rufai-nasidi 📖 Wattpad: @fatoumspassion 📚 Arewabook: @fatoumspassion 💬 WhatsApp: ***

If you don't have my number, save it and send me a message saying "saved", so I can save yours back and you'll always get my story alerts whenever I upload a new chapter. [01/10, 11:10] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

Join our comments section domin tattaunawa kan EHSAAS

Guys yakuke ganin za'a kare shin tsakanin Islam fa Mehtav waye zefi kishi?

Kuna ganin auren Mehtav da EHSAAS ze yiwu kuwa?

Does EHSAAS deserve Mehtav in the first place?

Wana ciwo Islam take fama dashi?

Shin kuna ganin EHSAAS ze zauna dasu duka biyun kuma yay adalci?

Duk kubiyoni comments section don ku tofa albarkacin bakinku kafin next chapter yay dropping yawan comments dinku shize karamin karfin gwiwar cigaba da baku update on daily basis. [02/10, 10:08] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM And INTENSE LOVE.