Chapter 58
Tsit kakeji ko ina acikin asibitin shiru sakamakon abinda yafaru da Islam ko motsi bakaji saboda yadda akaga prince din yayi reacting yasa kowa yasha jinin jikinsa. Tunda mai Martaba yaji shima yakaraso asibitin tare dasu turaki da Paa amman har zuwa lokacin babban likitan bai fito daga dakin da aka shigar da itaba.
EHSAAS kasa zama yay dukda yadda Fulani taita lallashinsa tana kwantar mai da hankali amman zagaye ya ringayi akofar emergency room din yana kallon agogonsa gani yakeyi kamar lokaci baya tafiya.
Mehtav na gefe tayi jigum itama duk jikinta asanyaye tana rokon Allah yasa ba abinda ake zato din bane yake damun Islam.
Seda akai minti talatin cif da shigar da ita kafin babban likitan yafito daga emergency room din, Ya kallesu gaba ɗaya yadda sukai cirko cirko akofar dakin suna jiran jin bayanin sa, Mai Martaba yakalla yafara gaishe shi be tsaya amsa gaisuwar ba ya shiga tambayarsa "menene ya samu Islam din?" cikin nutsuwa likitan yasoma mai bayani yana fadin "Alhamdulillah. After cross-checking, mun gano ba heart failure bane kamar yadda muka zarga farko. Islam ba ta da dilated cardiomyopathy. Abin da ya faru dai acute stress reaction ne, wato tashin hankali da take yawan shiga akwanakin nan ya haɗu da panic attack ya haddasa sarqewar numfashi da chest pain, dadin dadawa kuma ga pregnancy tohm dole seta ringa taka tsantsan"
Wani irin baya EHSAAS yay yana lumshe idonsa yanajin wani irin mugun relief na shigarsa, because he can't just imagine his life babu Islam.
Jinjina kai Mai Martaba yay yana dan bubbuga kafadar EHSAAS yace "take care of her congratulations" se alokacin yaji wani irin kunyar Mai Martaba ta lullubeshi jin ance tanada juna biyu ya danyi kasa dakanshi yana fadin "in sha Allah I will Allah ya temake ka," duk sauran manyan suka mai Allah ya sauwake da Allah yaraba lfy kafin subi Mai Martaba subar harabar asibitin.
Fulani takalli EHSAAS tana fadin "kuka ya kare kaji dai me likitan yace ai" sunkuyar dakai yay yana bata baya danshi be masan kuka yayba se da yanzun take maimaitawa. doctor yay murmushi yana dafashi yace "gatanan fitowa she's okay don't show her this weakness mana prince be a man kai zaka bata karfin gwiwa,you guys can do this together kaji," jinjina masa kai kawai yay ya mai godiya daidai ana fitowa da Islam daga dakin akan gadon gaggawa, oxygen mask ɗinta aka cire saboda numfashinta ya dawo normal.
Duk da ta yi weak, murmushi tashigayi ganinsu duk atsaye suna kallonta dasauri EHSAAS ya matsa kusa da ita ya riƙe hannunta yana faɗin, "Baby…..ya kikeji yanzun, kinajin wani ciwo ajikinki how are you feeling uhm, I was so scared I thought I thought...." kasa karasawa yay ya kankame hannayenta cikin nashi.
dariya tayi kaɗan, ta ɗan murza hannunsa a nata cikin rauni tace "Sire… don't overreact. Ni fa na gaya maka zan rayu tare da kai har abada. Small panic attack kawai ne. Stop crying jare."
Kowa murmushi yashiga yi awurin saboda yadda take rarrashin shi kamar ita ce mai lafiyar shikuma mara lafiyar sudai nurses suka tsaya ganin ikon Allah.
Cire hannunta tai anasa sanda ta hango Mehtav agefe guda tana kallonsu kawai tana murmushi ta mika mata hannunta alamar tazo ahankali Mehtav ta karaso Islam takama hannayenta tana fadin "Thank you so much you saved my life to day," Mehtav girgiza kai tashigayi tana fadin "Is nothing Islam, I know you'll do thesame for me,don Allah kidena stressing kanki kinji,take good care of yourself," Murmushi tai tana fadin "I will in sha Allah yah Mehtav," because Mehtav is acting like the big sis she never had, murmushi sukai sanin duk tsokanar ta sukai se alokacin, Mehtav tai murmushi tana dafa cikinta tace "congratulations" dan kallonta tai kafin tace "for what?" Kallon EHSAAS tai da ido yamata alamar karta fada mata da sauri Mehtav ta wayance tana fadin "for getting better," tana karasa fadar haka tai saurin baya tana fadin "get well soon let me get going" dasauri tafara tafiya. Islam takalli EHSAAS tana tambayar sa "is Mehtav alright," sosai yasha jinin jikinsa saboda tinawa da irin tsawan dayay mata alokacin da Islam tafadi yake yasan kuma kallon shinnan datai tinawa tai kuma tabbas taji haushi yasan Mehtav da zuciya, Yanzun ya zeyi yafara aikin rarrashi.
nurses ne sukace zasu wuce da ita dakin hutu se asannan Fulani ta matso ta shafa kanta tana faɗin: "Alhamdulillah, Allah ya ƙara kareki 'yata Allah yakuma albarkaci zuriarmu baki daya." Da Ameen suka amsa mata baki daya, nurses ne suka turata har zuwa dakin hutun da aka tanadar mata fulani da EHSAAS na biye dasu.
Doctor ya danyi gyaran murya cikin nutsuwa yace, "Amma duk da ba heart failure bane, dole ne ta kwana a nan ana monitoring dinta na 24hrs. We just want to be sure babu wani hidden issue. Stress tana affecting zuciya sosai. Ku bar ta ta huta completely."
EHSAAS ya yi shiru, yana kallon Islam kamar zaiyi kuka kana kallonsa kasan yana cikin damuwa sosai jin abinda likitan yace gani yake kamar akwai wani abu daban likitan yake boye mai. kafin ya ce komai, Islam tafara dariya ƙasa ƙasa tana gyara kwanciyarta tace:
"Abeg Sire ka daina yi kamar zan mutu yanzu. Doctor just said ba wani abu bane. Hutu kawai yace nake bukata, Don't worry, when we get home, I'll still finish what I promised you earlier."
Takarasa tana kashe mai ido daya,
EHSAAS ya ɗan runtse ido ya kama hannunta ganin she's not even serious ana takai wayake ta Kaya, gently yace "Baby, you nearly killed me out there. Ni ban san yadda zan yi idan wani abu ya sameki ba. Forget your promise, your health first. abinda nake so yanzu shine ki tashi lafiya kawai."
Dariya Islam tafara tana fadin "are you sure?" Da wannan fitinan amuryarta, EHSAAS yace "very sure your highness,kifara warkewa duka tukunna" ganin haka yasa fulani tace zata wuce ta da dama Islam sannu sannan tasake jaddada mata takula da kanta.
likitan dakanshi yahada mata IV drip kafinnan shima yaymata allurai yace "tahuta har yana tsokanarsu tagama jinyar EHSAAS zeyi tata anramawa kura aniyarta," Islam tace "aikuwa hakane shiyasa sire yaketa bata rai don zaman asibitin da besone gashi kuma seyayi donba wanda zeyi jiyyarta seshi kamar yadda tamai."
Seda likitan yafita sannan EHSAAS ya zauna gefen gadon da take ta daura kanta asaman cinyarshi tana kallonsa cikeda damuwa wannan karon take fadin "ka kwantar da hankalinka dan Allah bafa abinda yasameni," jinjina kai yayi kafin yace "meyasa baki gayamin min ba uhm you've being battling with your health all this while uhm meyasa," dan jim tai kafin tace "banason insaka adamuwane nasan you'll react this way and I never thought is serious," Yace "yaushe yafara miki uhm?" yana shafa kirjin nata gently, "Not long ago after your accident" tabashi ansa tana kallon cikin idonshi, shiru taji yayi yana kallonta kafin yace "nine nasaki adamuwar nan ko Islam kuma gashi nazo nakara sakaki awata damuwar Islam kifadamin gaskiya idan aurena yanada alaka da ciwannan naki" ahankali tai yunkurin mikewa ya hanata yana maida kanta saman cinyarsa tace mai "no I promise you tunkan aurenka yafara kuma ba kaine sanadiba kaine kake gayamin koda yaushe mu ringa yarda da kaddarorin da Allah yake daura mana mai kyau ko akasinta jarrabawace sire Allah ne yadauramin kuma shine ze yayemin aurenka da Mehtav bashida alaka da abinda yasameni kwata kwata" dogon numfashi yaja kafin yashiga shafa cikinta ta saman rigar asibitin da aka samata, "Banason duk abinda ze tabamin lafiyarki kinji musamman awannan halin dakike ciki Islam,the baby need peace too idan aurennan ze kawo miki matsala baby zamu iya dagawa nida Mehtav harzuwa bayan Allah ya saukeki lpy" wani irin zaro ido tai tana mikewa zumbur daga saman cinyarsa da sauri ya rike hannayen da akasa mata drip din don kartai disconnecting tace "what?" Murmushi ya shigayi don daman yasan seta dana mai wannan rigimar inta sani, yace "yes baby our baby is inside you," wani irin fashe masa da mahaukacin kuka tai tana girgiza masa kai itawai batada komai.
yatsaya kawai yana kallonta kamar TV, "yaushe na haihun uhm kofa shekara daya fa beyiba kasan wahalar da akesha a haihuwa kuwa tohm ni me mutane zama suce gani kamar wata akuya naita haihuwa akai akai" dariya yaso yayi amman ya maze yahade rai don yasan yana sakar mata fuska iya shegen shagwabar nan zata cigaba damai. "Baby relax pls calm down kina jin doctor yace kiyi avoiding damuwa da stress kukan menene wannan uhm? kibari mana children are blessing impact Jr ai yagirma look at him his ten months old yaronnan kama abu ya kema yatashi bama wanda bazece yayi shekara ba and who fucking care about what people will say uhmmm?"
Islam bakison mu tarawa iyayenmu zuria'ar da su basu tara dakansu ba Allah ya albarkacemu da kyautar da sukutum da guda kice bakiso Islam, your parents ke kadai suka haifa likewise mine kuma duk seda sukai shekaru suna nema ido rufe kafin Allah yabasu mugashi Allah yasa rabon namu akurkusa yake dan meyasa zebamu muyi mai butulci eh Islam," jikinta ne gaba daya yay sanyi tai shiru tana sauraronshi kafin tace "tohm whatabout Jr how can I take care of two babies I'm too young for that I'm just twenty years old, sanda zan haifi Jr I thought I'm going to die and your not by my side I'm just scared I don't wannan die,"
tafada tana rufe fuskarta da tafikan hannayenta tana shashshekar kuka jawota yay yashiga lallashinsa yana mata nasiha da banbaki yana mata alkawarirrika iri iri kan cewar they will do the journey together kamar yadda sukai wancan kuma in sha Allah this time around he will stick together with her har cikin labour room din haka harta samu hankalinta yadan kwanta tai luf ajikinsa.
Sunjima ahaka kafin yaji nauyinta ya karu ajikinsa alamar tayi barci, ahaka ya ringa kula da ita na tsawan ranar kamar bashine aka sallama daga asibiti yau yauba.
Fulani da Mai Martaba da Paa sun sake dawowa sun duba Islam amman lokacin tana barci don allurar barcin da sukai mata mai shegen karfice sallah ce take tadata intai takoma ta kwanta dakyar ma ta tashi tadan samu taci abinci tasake komawa hankalinsa yakwanta saboda yasan Islam tayi accepting pregnancy dinnan hold heartedly don inda bataiba zata cigaba damai rigima koda tatashi.
hankalinsa gabada ya koma kan Mehtav don yasan tayi fushi se kiranta yakeyi bata shiga yatura mata sako nanma ba reply, ahaka dai ya kwana zuciyarsa gaba daya acunkushe saboda rashin ji daga gareta washegari bayan sunyi sallar asubah jikin Islam yay karfi sosai don dakanta ta tashi tai wanka tashirya tana jiran likitan yazo yasallameta, EHSAAS se dariya yake mata wai ashe ba dadi shida take cewa kar asallameshin tashiga turamai baki tana shagwaba wai zaman asibitin ya isheta itadai gida zata tafi.
Aikuwa likitan yana zuwa aka shiga dubata seda aka tabbatar da lafiyarta da abinda yake cikinta aka daurata akan wasu magunguna sannan yace inzata fara awo nan gurinsa zata cigaba tare da rubuta mata sanda zata fara sannan yagargadi EHSAAS sosai akan sata cikin damuwa da stress kafinnan yasallame ta babuma wanda yasan ansallame su se Fulani ita ta aiko musu da mota aka daukesu.
EHSAAS gaba daya jikinsa yayi sanyi saboda tunda yake asibiti yake expecting zuwan Aman amman gashi har yau bezoba koda abinda yasamu Islam jiya yasan ya karade palace amman kuma be ganshi ba kwata kwata yanata trying kiransa amman bata shiga kawai ya jingina kai cikin motar don ayadda yasan Aman dakyar ne idan ba blaming kansa yatafi yanayi ba. gaba daya jinshi yake incomplete inbabu Aman a side dinshi, Islam dake zaune a gefensa tana leken fuskarshi daga gefe, ganin yadda yake lumshe ido ya sauke glass din window yana shakar iskar safiyar datake hurowa yanajin dadin yadda take dukan fuskarsa.
Suna isa cikin ainahin palace din, Driver yanufi bangaren sa amman me EHSAAS dakatar dashi yay ta hanyar bashi umarnin yabi hanyar unguwar Fulani nan zasuce Islam dai batace masa komai ba har suka karasa.
aka bude musu motar shine yafara fitowa kan yajuya yariko hannunta ya temaka mata tafito ahankali wani sabon tattalinta yakeyi kamar kwai tunda yasamu labarin cikin dake jikinta, Kallonta yay gently yace mata "ta karasa ciki shi zeje yadawo" dan bata fuska tai jin wani gurin zeyi,aranta tace ina kuma zeje daga dawowarsa befa gama jin sauki ba, kin tafiya tai tana jinsa yana tambayar wani guard
"Where's Aman?"
Guard din ya danyi shiru kafin yace, "He's been in his quarters all this while Your Highness. Babu wanda ya ganshi yafito."
Islam ta kalle shi da mamaki, don itama tayi noticing rashin Aman din amman tayi tinanin EHSAAS ze tsaya yafara warkewa tsaf tukunna kafin ace yafara saka kansa adamuwar nemansa ai Aman is adult baze bata a palace dinnan ba. Ahankali tace "you just came back from surgery, and you want to...."
"Islam," ya katseta, muryarsa asanyaye yake fadin "This boy has been avoiding me for too long. And I know why. But enough is enough, zanje ni inganshi"
Babu yadda ta iya don tasan tunda yace haka toh fa se yaje din,don haka kin shiga ciki tai ta bi bayansa suka nufi wing din Aman tare.
Ko iso basu bari anmusu ba EHSAAS ya wuce zuwa master bedroom dinshi directly, yana murdawa kuwa yajishi abude yashiga kansa tsaye yana kallon yadda dakin yay duhu babu komai se hasken dim blue light kamar ba rana ba.
Aman ya hanga zaune agefen gado pajamas ne ajikinsa yayi shiru shishi kadai ga tulin files agabansa da laptop amman kamar hankalinsa baya wurin yayi wani gurin na daban hakan yasa EHSAAS yakarasa gun light din dakin yakunna duk wani haske dake dakin wanda yaja hankalin Aman har yay noticing dinshi ido suka hada dasauri Aman yamike yana kallonshi.
EHSAAS ya hade rai yakarasa inda yake da sauri Aman ya dauke kai daga kallonshi saboda wani irin kwarjini dayake masa a ido, sannan idan ya kalleshi kawai abinda mahaifiyar sa tai masa yake tinawa shiyasama yakasa komawa asibiti ya dubashi don gani yake kamar yana zuwa kowama gani zeyi shima ze cutar da EHSAAS kamar ita, jin EHSAAS bece komaiba ba yasa yazauna yana sauke numfashi ahankali yace "uncle prince… please, you shouldn't be here. You should be resting."
Zama EHSAAS yayi agefenshi yana fadin "I can't rest… not when you've locked yourself away from all of us."
Aman ya lumshe ido, hawaye na taruwa acikin idonsa yafara kokarin boyewa kada EHSAAS yagani muryarsa na rawa yafara fadin "How can I face you? After what my own mother has done? After everything she put you… and all of us… through? Wallahi I feel like it's my fault. If I had stopped her… if I had said something...."
"Kai kuma ka ce mata me?" Ehsaas ya katseshi dasauri kafin yadora da "Aman… you are not responsible for your mother's choices. Her sins are hers alone. You? You've been nothing but loyal to me."
Aman ya girgiza kai cikin tsananin nadamar kasancewarsa Dan mace kamar mimah yake fadin "But I carry her name, uncle prince. I carry her blood. Every time I see your wounds, every time I hear them talk about what happened… I feel like I'm the one who pulled that trigger."
Ehsaas ya dafa kafadarsa, cikin salon da zeyi reassuring Aman yake fadin "Blood doesn't make us who we are… choices do. And you, you have chosen to stand with me, to protect this family, even when it tore you apart inside. That means more to me than you'll ever understand, babu prince EHSAAS inba prince Aman hakanan babu prince Aman inba prince EHSAAS"
Yakarasa yana shafa kan Aman don har lokacin yana tina sanda yake koyama Aman keke sanda yana yaro a Istanbul da yadda Aman yake faduwa yana kuka yana complaining shi baze iyaba, yana cewa common Aman you can do it,da yadda suke kwana adaki daya idan Aman yazo madinah da yadda yakesa EHSAAS ya ringa fada da kowama akanshi don duk wanda yataba Aman EHSAAS baya hakura seya rama mai,shima Aman thesame tinanin yake hakanne yasa yafashe da kuka wani irin nauyin dayake akasan kirjinsa kamar ana mai lifting dinsa yarungume EHSAAS yana fadin "Uncle prince… I'm sorry. I'm so, so sorry." EHSAAS shafa kansa yashigayi yana fadin
"Then stop hiding from me. You're my nephew… my right hand Man. If I lose you to shame, then she wins. And I won't let that happen."
Islam dake tsaye bakin kofa tana watching dinsu itama hawayen tashigayi saboda sosai suka bata tausayi tana tina irin bound din yake tsakaninsu aranta tana dada tsinewa mimah dataso shiga tsakanin wannan zumuncin, itakanta bata taba rike Aman acikin zuciyarta ba daidai da rana daya wai kodan saboda abinda mimah tai, sudai Aman na sune they don't care about anything shi din nasune har abada.
Se asannan Aman yashiga share hawayansa yadago daga jikin EHSAAS yanajin wani sabon karfin gwiwa daya samu yace "I won't run again."
"Good," Ehsaas yafada yana mikewa tsaye, yana murmushi kadan. "Because I'm going to need you for what's coming next."
"What's coming next uncle prince?" Aman ya tambaya cikeda curiosity daidai nan idon EHSAAS nasauka kan Islam dake makale bakin kofa tana kallonsu , dan murmushi yayi yana sosa keya don mgnr aurensa yaso yayma Aman din amman ganin Islam yasa ya basar yana fadin "we'll talk laters Aman" yanamai alamar waya da hannu kafin nan yanufi bakin kofa yana riko hannun Islam yace "lets go my stubborn baby," pouting lips dinta tashigayi kafin taraba hannunta da nashi tashiga ciki tana kallon Aman dashima ya lura da yadda tadan fada,yace "our one and only princess yame jiki," bata rai tai tana fadin "aibazan ansaba saboda nasan dadin baki kake yimin yadda banganka a asibiti ba yanzun dai inason inganka a gidana don akwai magana," kallon EHSAAS dake kallonsu yay yace "kice inzo takanas tasamu" jinjina mai kai tai tana fadin "amman karka bari yaji" tana nuna mai EHSAAS da yashiga yimusu murmushi jinjina kai Aman yayi yana fadin "angama Princess" harda dan bowing na showing respect dariya tai ganin walwalar fuskarsa tadawo sannan tajuya tayi gaba tafara fita EHSAAS yabi bayanta Haka harsuka karasa sashen Fulani, Jr se jin dadi yakeyi ganin iyayen nashi yamakale Islam yaki yarda yasauka ajikinta, Queen layla tace "ja'iri wato kasan babarka shine tana zuwa ka dafeta kake nunamin banbanci" Dariya duk akai kamar Jr yasan metake cewa yashiga yimata dariya.
Anan sukai brunch yaga kowa Abeey,inna,jalila duk sun fito angaggaisa amman bega Mehtav ba koda ya tambayi Abeey asirrince sece masa tai aiwai Mehtav din barci takeyi kmr batada lpy take tinani nandanan yaji hankalinsa yakara tashi bayan sungama ne Queen layla da Fulani sukaja Islam dakin domin guiding dinta ta yadda zatai rainon cikinta da danta cikin sauki, sosai suka fara couching dinta dukda yadda takejin kunyarsu daga farko harta saki jikinta tana kwasar ilimi.
Suna shigewa dakin Fulani dake kasa EHSAAS yasamu ya lallaba yahada inna da Jr wanda aka barmai, ya haye saman yasan da jama'a sosai a bangaren ya rasa wana dakin ze bude wanda Mehtav ke ciki jalila yaga tafito daga dakinta tana danna waya tana murmushi gently,
Batasan yana tsaye ba kawai taji yace "hey you" dasauri tadago ido tana kallonsa don tun rashin kunyan data yi a asibiti take avoiding haduwarsu, "where's Mehtav?" ya tambayeta straight ba kwana kwana, batace mai uffanba kawai tanuna mai dakin dake bayansa alamar nanne inda Mehtav take, be sake ko kallonta ba yanufi kofar yana murdawa cikin sa'a yajita abude kawai yashiga.
Abeey ce zaune saman carpet tana game da ipad dinta tadago suna hada ido tasakar mai murmushi tana fadin "handsome prince" shima murmushin yayi mata yana fadin "how far Abeey?" Yana kallon gadon daya hango Mehtav akwance ta lullube jikinta tana barci hular kanta tazame gashinta ya baje yarufe mata kyakkyawan farar fuskarta, ahankali ya karasa gefen gadon yana kallonta Abeey ganin ba gurinta yazo ba yasa tacigaba da Game dinta dan gyaran murya yayi yana kallon Abeey yace "could you please get me some water" tashi tai tadau ipad dinta tana fadin "right away your highness"
tafita tana dariya aranta tana raya wai irin ita za aima wayonnan tasan bawani ruwa dazesha so yake kawai tafita tabashi guri.
Aiko tana fita ya tsugunna gefen gadon dayake Mehtav na bakin gadon sosai yashiga gyara mata kanta yana mata baya dashi sosai gashin nata yadade yana burgeshi ba baki bane kmr na Islam nata brown colour ne kuma baida cika sosai da tsayi kamar na Islam amman yawuce keyarta haryama kwanta abayanta sosai,kuma akwance yake luf kullum cikin gyara, tunda yasoma tashako kamshin turarensa cikin barcinta hakanne yafarkar da ita, daf dasukai yasa takejins saukar numfashinsa nafita ahankali ahankali tadan sake rintse ido don batason yasan tafarka fushi takeyi dashi, dariya yay ganin eyelids dinta na motsi yasan tatashi, hakan ne yasa yasaki murmushin gefen baki yamike yanufi gaban mirror dinsu inda ya tarar da kayan shafe shafe iri iri,dana kwalliya wani black jambaki ya dauko yana murmushi.
ya karaso gabanta tanajin kamshin jikinsa har tsakiyar kirjinta, taji kamshin jambakin da yadakko da jagira ahancinta sanda yabude yasoma goga mata ajikin lips dinta kasa kasa yake fadin "yau ni zan yimata make-up, is a surprise sedai kawai tatashi taganta da kwalliya,"
batasan meyake mata afuska ba tabasar duk cikin fushin taji yana mata zane agira da fuska aiba shiri tamike tai kicin kicin da fuska tana kallonsa hade ran datai yakara saka kwalliyar kauyawan daya zana mata fitowa dakyau takara yi kamar wata yar aljana sbd hasken fatarta kawai ganin sa tai yayi zaman dirshen akasa yana dariya yana nunata da yatsa "You look so cute kinga kyan dakikai kuwa wannan sekin cinye gasar sarauniyar kyau ta duniya"
dasauri tamike tanufi katon mirror din dake dakin tundaga sama harkasa tashiga kallon fuskarta yadda yaymata zanen yan kauye sak harda dige dige asaman goshinta anyima a kumatu daya, ba ayima dayanba anshafa mata bakin jambaki abaki harda saman bakinma duka harda yimata irin hawayen masoyinnan da kwalliya a ido guda.
jitai kamar zatafasa kuka tajuyo afusace tana kallonsa yanata dariyarsa kamar ma besan fushi take dashi ba, kuka kawai tasaka mai tana Mai zaman dirshen akasan carpet din se asannan ya tsagaita da dariyar da yakeyi yakarasa kusa da ita yana kokarin dagota tashiga tirjewa "haba ya Mehtav kiyi hakuri dan Allah kinsan I didn't do it on purpose nashiga tashin hankaline shiyasa I wasn't suppose to shout at you like that pls forgive me, I know is nto your fault"
yafada harda rike kunnuwanshi make mai kafada tashigayi tana kunkuni tashiga fadin "ita bazata auri mijin daze ringa mata fada ba akan gaskiya ba anyhow kuma agaban mutane yanzun zataje tacewa Paa itafa tafasa auren" dukda yasan wasa takeyi bazata iyaba amman hakan behana zuciyarsa bugawa dakarfi ba yatsugunna ahankali yana fadin "I'm so sorry Mehtav kiyafemin kinji and stop saying this bakisan yadda zuciyata take zafi innaji kina fadar hakaba kinsan I'm human being we are not perfect kinji, couples do face this kinda issues amman insukai sticking together suna over coming dinsa bawai suce zasu rabu da juna ba Mehtav," girgiza kai tashigayi cikeda takaici take cemasa "aibata taba ganin yayiwa Islam fada agaban mutane ba kullum se ita saboda ita bayasonta bashi ita akai kawai daga sama kodan yaga tana sonshine shiyasa, she won't tolerate this itadai," besan Mehtav ta iya bori nagaske ba seyau haka yasamu yaringa lallashinta dakyar yasamu tahakura tace "kuma inyasake bazata aureshi," ya jinjina kai alamar ya yarda, yajingina da gadon yana kallonta yadda tai kuka hawayen yahadu da bakin fentin fuskarta ya cabe, kasa danne wa yay yasheke da dariya da sauri tasake komawa gaban madubi tana kallon fuskarta this time around she look like zombie tajuyo tana kallonsa ashagwabe dakyar ya sassauta dariyarsa yana kama kunnensa, alamar ban hakuri.
daukar wipes tai zata fara gogewa dasauri ya karasa yana dauke wipes din yakarbe na hannunta ma yana fadin "one sec," wayarshi yaciro bata ankaraba kamar yana dannawa hoto kawai yashiga yimata tana kallonshi tana jiran taga me zeyi tana ankarewa hoto yake mata tashiga kakkara fuska tana buga kafa videos yashiga yimata iri iri yana tsokanar ta wai tayi kama da wata ladingo da kema kakarshi aiki a Maiduguri few years back. se asannan itama tafara mai dariya tace "tunda yashafa mata baki yabata mata fuska itama seta rama inba hakaba bazata hakura ba" ba yadda ya iya yama manta shaf a ina yake kuma tareda wa sukazo yazauna saman dressing stool tadakko jagirar itama tashiga shafemai a fuska tanayi tana dariya gashinsa da yakenan very neat tadafa tana goga mai harda jambakin duk seda tashafa mai kafinnan tadago tadakko wayarta tashiga mai hoto ganin he still looks cute yasa ta hargitsa hadadden gashin sa da hannayenta yana murmushi yana ganin how happy she is daman kuma hakane burinshi ya faranta mata saboda yasan yamata ba daidai ba.
Yace "tohm kin rama harda riba kinji dadi zan iya gogewa?" girgiza kai tashiga yi tatsaya gefenshi suka fara selfie awayar ta, tana kyalkyala dariya shikuma yazuba mata ido kamar ya hadiyeta yanata kallonta.
Dressing stool din tahau duk yadda yake gargadinta karta fadi wai taga yafita tsayi sosai so take suyi kai daya aiko seda tahau sukai kai dayan daidai nan aka bude kofar dakin da sauri tajuya zata diro ya rikota ganin inta fadi zata iya jin ciwo karaf a idon Islam data shigo duba Mehtav din har sungama tattaunawa dasu Fulani kallonsu tashigayi EHSAAS yay wuri wuri da ido yama manta menene afuskarshi yashiga sakko da Mehtav kasa wacca taji kunyar duniya tarufeta ganin yadda Islam takamasu suna tsaka da shirme kamar wasu kananun yara.
Islam hadiye wani irin abu tai dataji yana neman taso mata tashiga kallon fuskokinsu tana dariya take fadin "I'm I missing something here,kodai village zamu koma ne," se asannan EHSAAS yay feeling at ease dasauri Mehtav tadakko wipes din daya ajje gefe tana mikamai itama tazaro wacca zatai using tana dan murmushi kasa kasa take fadin "mom Jr ya jikin naki harkun fito kenan" jinjina kai Islam tai tana fadin "dasauki sosai Mehtav yanaki jikin, kafa tai lafiya kenan naga har kujera kike hawa kidai kula sosai" jinjina kai tai tana fadin "in sha Allah," tana goge fuskarta, Islam takalli EHSAAS tana fadin "I thought kama tafi se jalila tacemin kana nan ni bari nawuce inka gama seka sameni acan" dasauri tajuya bema samu damar cemata tatsaya sutafi tareba aransa yasan his doing nothing wrong tunda both of them are his women kamar yadda Islam takeda right din ganin this playful side nashi Mehtav ma tana dashi amman kuma meyasa yake feeling guilty why is it like that duk lokacin dayake kokarin sa daya farin ciki da zarar daya tagani se yaringa jin ba dadi shin haka ze kare rayuwarsa yana lallashi da kaffa kaffa da nuna soyayya akan daya agaban daya tabbas duk yadda mutane ke kallon polygamy yazarce haka not everyman is strong enough for that is not easy.
Don't forget to Like Share Comment Vote
To catch every new chapter as soon as I drop it, follow me on all my platforms: 📱 TikTok: @fatoumspassion 📸 Instagram: @fatima-rufai-nasidi 📖 Wattpad: @fatoumspassion 📚 Arewabook: @fatoumspassion 💬 WhatsApp: ***
If you don't have my number, save it and send me a message saying "saved", so I can save yours back and you'll always get my story alerts whenever I upload a new chapter. [03/10, 12:28] Fatima Rufa'i Nasidi: ***
It's fatoumspassion EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM.