Chapter 59
Ahankali ya bude kofar dakin nasu yana jin tsoron abinda ze shiga ya tarar don yasan fitar da Islam tai tabarshi tareda Mehtav sarai kishinne ya motsa shiyasa amman me? video call ya tarar tanayi itada iyayenta se dariya takeyi besan me suke ce mata ba sautin dariyarta kawai yakeji ahankali ya dan jingina da bango yana hangota da yake da tazara atsakaninsu sosai amman wannan gyaruwar alakar tsakanin Islam da iyayenta ba karamin farinciki take saka masa ba.
Harta kammala yana tsaye ba tareda tasan yashigo dakin ba, tajuyo suna hada ido tadan zaro ido tana sakin murmushi ta mike tana fadin "ashe kadawo" Murmushi yay yace "me daddy da mommy suke fada miki me dadi haka kiketa murna" girgiza kai ta somayi tana fadin "wai daddy ne yashiga kitchen ze yiwa mommy girki ya zuba detergent powder acikin miya shine mommy take bata labari suna making fun of him," EHSAAS ya dan zaro ido yana fadin "shi daddyn ne zeyi girki?" aransa ya raya "lallai kura tayi lafiya" tajinjina kai tana fadin "nima abinda yaban mamaki kenan and shine fa mommy tace dani dashi aiduk jirgi daya ya kwaso mu indai mgnr kitchen akeyi zero behind decimal point zamuci," smiling kawai yay yana fadin "danima and we love food alot shine abin mamakin" dariya suka shigayi shida ita tana tina mai lokacin amarcinsu daya taba cewa ze dafa mata pounded yam hardasu manja a ingredient din daya zuba waifa adafa doyar dan danyan aiki, bayan sun gama dariyar yayi expecting zata mai maganar Mehtav amman kala bata cemai akan hakanba sema sauya musu hira tai ta hanyar sanar dashi "tanason Aman ya temaka mata zata bude foundation na temakawa mata da kananun yara zalla wanda ze zamar masu shelter na marasa karfi da gajiyayyu, kamar matayen da aka saka aka barsu da yara ba temakon kowa da wanda aka mutu aka barsu da marayu wanda ba yadda zasuyi su ciyar dasu," jinjina kai ya soma yi feeling very proud of her jin manufofinta da niyoyinta akan yadda zata temakawa al'umma itama dukda yanada kafaffiyar nashi foundation dinza amman batace zatai joining kota dogara behind him ba she wants to build something of her own.
Yace "that's a very good idea nine zan zama first funder nakama tunkan abude" girgiza kai ta farayi tace mai "itadai she wants to build it ita kadai and if he permit Aman will assist her don taga yasan kan harkar batason ta daura mai wani nauyi na daban bayan wanda yake kanshi," yace mata "meye wani wahala aiduk aikin samun ladane" girgiza kai tai kawai taciro wayarta tana fadin "I have enough money, kasan nawane a account dina kuwa plus all the assets I have, da wanda babanta yabata kuma" balance dinta tashiga nuna masa tana dariya irin yakalla karba yayi yana zaro ido yace "what Islam kice ke muke ta nemawa kudi kawai daman bakya kashe kudi?" dariya ta soma yi tana mai gwalo tace "niko nake kashe kudi kashiga closet zaka gani, kasan sets din gold dina nawa dana siya dakaina kuwa," Dariya yafaryi yace seme kuma "Tace all my dresses are limited editions kasani" yajinjina kai yana murmushi tace sannan "nasiya mota biyu, farar benz din dakake hawa ainagama tawace bance nabar maka ba," Dariya yafarayi yace "ahh lallai kina kashe kudi yanzun gorin motar za'ai min kenan," Dariya tashigayi tace " Ba maganar gori kace bana kashe kudi, shiyasa natina maka" Yace " aina dauka anbarmin farar benz dinnan your highness inajin dadin hawanta kibarmin mana kinga aina siya miki sabuwa kwanannan" Make kafada tai alamar a'ah, Yace "tohm nima aban tawa tunda abin yar hakace" Tace "aitazo kenan bakyau kyauta da zobe, yariga yazama nawa" Dariya yayi yace "karfin hali barawo da sallama," Cikin dariya tace "harda kwankwasa kofa Ni so nakema kabarmin wannan RR dinka boat tail dinnan" Takarasa tana dariya kasa kasa Yabude baki yarufe irin your not serious dinnan, "Tace ainaga fa ba hawanshi kakeba benz dinnan dai nawa katakurawa kaga shikenan se muyu mucanje" Yace "Wannan wayone kawai akeso aimin kuma ban yarda ba bazan bayarba ba niyya" Dariya tashigayi tana "lallabashi wai yabata" Shi kuma seja mata rai yake,tasan sarai kuma inta matsa seya bata din, Harda cemai " wai zatai zuciya tasiya da kudinta fa," Tana sake nuna mai account balance dinta yace "yes I know but how comes Islam nifa banason kice zakita tara kudi saboda gaba ko wani abu I want you to be spending it like the spender you are,banson kice zaki ringa daga min kafa, inbabu kinsan ai zan fada miki" pouting din lips dinta tai tana kallonshi daman tasan seya mata fada danme take tara kudi haka shiyasama tace zata fara mgnr da Aman kafin shi amman kaikayin bakinta seda yakaita tafada mai.
tashiga turo lips tana cemai itafa ba tarawa taiba dukfa kudadenta da ake bata tundaga gifts din aurenta da allowances dinta da half salary dinsa dukfa sune yay sighing yane fadin "tohm nayarda if you need anything just tell me kinji inma bazaki iya fadamin ba you have my phone you got the pin, you can transfer a reasonable amount anytime you want" dariya tafarayi tana girgiza kai tana fadin "any amount ko?" irin karfa kajama kanka,dariya yayi yana kamata yace "reasonable nace bance kiyi bankrupting dinaba," dariya tashigayi tana fadin "aiko kasan abinda nake shirin yi kenan sedai katashi kaga wayam tunda dai kai kace ayi," kasa kasa yace "amman dai se bayan babynah ya sauka za'a fara wannan aikin koh" girgiza kai tai tana fadin "I'll start immediately after this wedding already inada plan din arubuce a laptop dinkama fa nake rubutawa baka taba budewa kagani ba?" tafada cikin mamaki yace "kinsan ai bancika bin wannan folder naki dakike cikawa da romantic novels ba wai da sunan ajiya kome naki system din yakeyi kawai dai se an takurawa nawa so probably bazan gani ba" tace "eh kumafa hakane ga rubutun diary da kakeso karasa, guess what?" Yace "what?" Dariya tafarayi tana hada goshinsu guri daya tace "na karanta ashe haka ake mutuwar sona bansani ba" waro ido yay tatashi da gudu ajikinsa tai bakin toilet wai karma yace ze kamota dasauri yafara dariya yana fadin "careful baby, your not alone" se asannan ta tina tadan tsaya tana mai dariya tana haki kadan tashiga shafa cikin ta kafin tace "laaaaa namanta sorry little one," EHSAAS ya girgiza kai kawai yana fadin "your going to be mother of two yakamata ace kindena guje gujennan fa," tace "tohm ai zandena bakaine zaka kamani ba bayan nasan the last thing you want aduniya shine inkaranta kuma na karanta baka sani ba," cikin dan mamaki yake fadin "wai dagaske kin karanta?" jinjina mai kai tai tace "Allah kuwan na karanta kuma alokacin daya kamata in karanta din," Yace "when baby?" Tace "after your accident Aman yadawo dashi gida nan gurina and he ask me to read it so that zeyi publishing," EHSAAS yace "publish what?" Yace "diary din mana he want the world to know about your story our love story you and I," EHSAAS ya shiga girgiza kai yana fadin "aiko dana balla hannayen dasukai publishing, that book isn't for the world Islam is for me and you just us, tayaya zan bari yazama published ai idan nai haka kamar nabar kowa ne yashiga rayuwarmu yay commenting yadda yakeso aciki, I won't want that sannan Mai Martaba ma will not like that" jinjina kai tai tana fadin "but why did you take it to your office?" EHSAAS yace "saboda kene, nasan kinata fakon shi zaki dauka ki karanta banson ki karanta saboda shinai planning baki ranar dakika haihu, I'll publish only one copy for you to revisit how we start amman muna namu Allah natashi" jinjina kai tai tana fadin "hakane sire and his the best planner, duk abinda kaga yafaru akwai dalili da badan accident dinba aida har yanzun muna zaune tare da poisonous people around us and da badan shiba I wouldn't understand the pain that shape me to be who I am today and da badan shiba you wouldn't have met mehtav and her family Allah sarki mutanen kirki is destiny that brought all of us together, so I always thank Allah for everything idan na koma baya ina duba abubuwan da suka ta wakana is all for the best jarrabawane."
Karasawa yay gabanta yana jan lips dinta cikeda tsokana yake fadin "wise wizard chai chai chai bakin ya iya zaro maganganu masu ma'ana haka,enyeee kodai kema rubutun zaki fara mana ne" dariya ta shigayi tana fadin "ka rufamin asiri ni rubutu aise dai kai din I lack the patience ga critics kosu aka barni dasu se sun ragargazani" takarasa tana bude toilet tawuce tana cemasa "kar ya biyota yana jidai likita yace tahuta karya takura mata" dariya yay yasan da biyu tafada kawai ya girgiza kai yakoma cikin daki yadau laptop dinsa ya cigaba da rubuce rubucensa.
One week later
Ranar asabar bayan sallar asubah Mai Martaba ya kira paa cikin private chamber dinsa yana sake jaddada mai ranar aurennan fa da akasa in sha Allah babu sauyi tsakiyar watan gobe za'a daura auren EHSAAS da Mehtav a Nigeria in Allah yakaimu, kamar yadda Paa ya bukata sosai Paa yay farinciki da jin abinda Mai Martaba yace yay na'am da batun hannu bibbiyu sannan ya fadama Mai Martaba batun tafiyarsu dawurwuri don suyi shirye shiryensu suma.
Izini Mai Martaba yabasu kuma atake ya kira akai musu booking tickets din komawa Nigeria gobe gobennan kamar yadda Habib Bai din ya bukata sannan suka karasa maganar renovation already yagama kusan rabin aikin karashe ne yabar babban yaronshi akan abin inyaso duk abinda ya taso ze iya tahowa daga Nigeria yazo yaduba.
Paa yana komawa chamber da aka saukesu ya sanar da inna batun, itakuma ta kira Mehtav ta sanar da ita wani irin farinciki taji ya lullubeta gani takeyi kamar mafarki takeyi wai itace zata zama matar EHSAAS,tun randa tarara ganinshi take mafarkin wannan ranar segashi tana daf da zuwa.
tana komawa daki kuwa tashiga kiransa karfe takwas na safe tama manta shaf cewa shidin mijin aurene, seda takusa katsewa taji ya daga yana wani mgn kasa kasa, "goodmorning Amor kintashi lpy?" tace "lpy lau alhmdlh my prince kaifa" yace "alhmdlh, amman sedai inata kewanki" murmushi tai kamar tana gabanshi, "ta samune yah Mehtav ko kewana kema kikai uhm," tace "wai yanaji kana magana baya fitowa dakyau mura kakeyi ne ko bakada lpy," tanajin dan karar smiling dinshi ta wayar yace "uhmmm uhm me kikaji," tace " Your voice Is too low banaji dakyau ma," yace "ina bandaki" tace "what bandaki kuma kadaga wayar ko shiyasa naji karar zubar ruwa," se kuma tafara dariya dan ta gano wayon nashi,tace "don't be a coward mana," shima dariyar yashigayi yana fadin "naji duk abinda zakice sedai kice amman zaman lafiya yafi zama dan sarki aikinga bedace inmata waya a bedroom ba ko beside I'm even warned," dariya Mehtav tai tana jinjina yadda EHSAAS ke respecting Islam da ace duk maza haka sukema mata inzasu kara aure babu macen da wata mace zata shigo gidanta ta rainata sannan babu macen da zata ringa hauka inza'a mata kishiya. tace "aikam bari na kashe nima mantawa nai kuma banga lefin Islam ba konima haka zanyi," kamar yana gabanta yace "auwai kema haka zaki ringa bugani kamar ball uhm haba Amor aike me hakurice nasani ba ruwanki da kishi," dariya tafarayi kafin tace "da Islam ba amman ka tabbatar dagani ba kari karufe kofa har abada,itama donta riganine" girgiza kai kawai yay yace "yadda kikace haka ai za'ayi ranki shi dade, but fadamin me kika kira kifadamin uhm," Tace "is a surprise in kazo zanfada ma amman kana fitowa kazo nan sonake nice zanmaka breaking news din da kaina" yace "pls kifadamin mana I'm curious," tace " uhm uhm I won't se kazo" yace " tohm I'm coming right away tunda kinqi fadamin" da sauri tace "a'ah stop banson haka yanzun time din mom din Jr ne kabari se anjima" yace "inkinaso inbari se anjima sekin fadamin" tace "wayo ko?" yace "uhmmm uhmmm I'm just stating a fact ko kiganni yanzun agabanki," tace "they set the date and is not changed" wani irin farinciki ne ya lullabeshi domin yagane wana date din take nufi yace "wow I'm so happy Amor finally," tace "and we're going back home tomorrow," atake fara'arsa ta disashe don bayason tai nisa dashi ko kadan yace "what? but why so soon?" Tace "I dunno but I'm so happy Paa ne kawai yace mushirya gobe tafiyar," Yace "and your happy zaki tafi kibarni koh Amor," Girgiza kai tai don tasan shagwabe fuska yayi ayadda yayi mgnr tace "nifa ba haka nake nufiba EHSAAS karka canzamin fassara yace ba gashinan ba your excited zaki dena ganina kullum and I'm sad zandena ganinki daman nasan baki sona kamar yadda nake sonki" yafada cikeda rigima, mehtav ta gimtse baki don sosai take jin dadi intaji yana nuna damuwarsa akanta haka,tace "aikasan ba haka bane meyasa zandamu bayan nasan in the next 20 days andawo maka dani uhm?" We'll stick together forever right,kaga dole mukoma don muyi shirye shirye akan lokaci," Seda ya danyi jim kafin yace "gaskiya se dai inbiku aidaman room dina yana nan nima aishirin dani,"
Dariya tafarayi tace "shirin ango daban na amarya daban impact tayaya zaka taho kawai kabimu bayan kaima akwai naka shirye shiryen se kace agarin gaba gaba," Dariya ya farayi yace "nagane wayon naki irin wannan traditional spa din zakije amiki dakike komawa very fair,skin dinki yake zama kamar tissue shine ba'a so inzo ingani se angama jamin rai ainasan komai da komai gyaran amarya akeyi shine zakimin wayo, wai nima inyi nawa shirin and that makes me super excited yah mehtav, can't wait mekika shiryamin after all the gyaran hope harda daya sabgar duk an koya miki" dasauri tacire wayar akunnenta ta katse dan ta fahimci EHSAAS baida ta ido gaba daya daman fa taji wasu coursemates dinta a cafeteria suna tattaunawa cewa duk macen da zatai soyayya da namiji me aure dole ta ringa tsare gira saboda suna da sakin layi lokuta da dama mantawa suke cewar bada matansu suke magana ba musamman idan hira tai dadi.
Dariya EHSAAS ya shigayi ganin ta kashe wayar and he expects that much,kunyar Mehtav na daya daga cikin abubuwan da yake mugun admiring about her yasan duk wata hanya ta turning dinta on tun ba yauba kuma ayadda yake ganin tana diriricewa tabbas internal body dinta na reacting idan tashigo daga ciki ba karamar yar hannu za'ai ba jikawai yakeyi he can't wait bayajin ko lokacin aurensu da Islam yayi zumudin zuwan first night hakaba saboda lokacin shi kansa saurayine besan dadin abun ba amman yanzun kam ji yake kamar yajawo ranar don ya kasance tareda Mehtav kawai so yake yagani nitsewa zatai da kunya aranar ko yaya. aransa yace "she's too innocent yet very dirty minded" ya rintse ido yana tina chapters din dasuka dan bubbude lokacin partial amnesia dinshi a Abuja sosai image din yaki gogewa akwakwalwarshi da zuciyarsa, cije kasan lips dinshi yay yana mannawa wayar kiss kamar itace Mehtav ya ajje gefe yashiga Shirin wanka.
ko bayan daya fito Islam is still sleeping yana tinanin amagungunan da aka hada mata akwai na barci shiyasa yanzun take dadewa tana barci kuma da cikin ma da yake kara mata kasala dan ko yanzun tatashi bataki takoma takwanta ba. Jr agurinsu ya kwana yau yana zuwa ya leka gadonshi yaga ya farka se kokarin mikewa yakeyi yafito. ya dakko shi yana mai wasa ya wuce dashi toilet daure da towel ajikinsa dakanshi yay mishi wanka yafito suka wuce closet ya shiryashi yanayi yana mai barna yana gyarawa har suka kammala kafin shima yashirya kansa suka fito suka nufi gadon Islam sunfesa wanka sunata zuba kamshi.
ganin kusan karfe goma yayi yasa yadaura Jr saman gadon aiko cikin xafin nama yay kan Islam ya soma shashafa fuskarta yana gwarancinsa da EHSAAS yake cewa ai maama yake cewa din in yanayi tayashi yakeyi kamar wani Sa'ansa in Islam tai magana se yashiga fassarawa yana cewa ai ga abinda yaron yace shikuma ga abinda yace masa. taita musu dariya tace "wannan dai sharri ya kema danta" jin dan karamin hannayen Jr yasa ta shiga turo baki tana fadin "Sire take your son away let me sleep pls" dariya ya shiga yimata yana fadin "we are hungry we need food" mikewa tai tana lumshe ido alamar barcin be isheta ba tace "okay then bari inzama food se ku cinyeni duka" dariya suka shiga yi daga shi har Jr din kamar sunsan me take ewa kafin ahankali tamike tana kunkuni tanufi toilet, "where are you going mama, we said we are hungry" EHSAAS yafada yana wani tsuke murya shi lallai muryar yara yake kwaikwaya tsabar haushi Islam dagowa tai tana daga mai middle finger dinta shima ya shiga daga mata yana mata gwalo yana making funny faces data kara kunna yaron yaringa kyalkyala dariya.
bandaki tashiga she just pee ta wanke bakinta ta daurayo fuska tafito tana yatsina musu hanci tana musu kunkuni yaga cikinnan harda sabon fitina da mood swings yake sata shiyasa ma yanzun koya tsokanota tahau seyaki biye mata.
daukar Jr yayi yabita abaya tafito kitchen tanufa yashiga dariya yana tambayar ta "me zatai?" inda take ajje baby formula din Jr tashiga hada mishi kasa kasa EHSAAS ke fadin "baby abinma kabilanci ne kenan yaronki zaki fara feeding kafinni koh,"
yana shagwabe mata tajuyo tana fadin "waye yagajiyar dani kuma yazo yatasheni da wurwuri uhm?" tana kicin kicin da fuska dariya yashiga yimata yana tambayar ta "wai yaga tafara zama orobo tafada mishi meye sirrin ne uhm," nan tafara dudduba kanta wai dagaske ita batason tai muni fa wai har cikin yafara sata kibane? kin cewa komai yay ya cigaba da dariya ya dau abincin Jr data gama hadawa suka fito dining yashiga bashi. button ta danna cook dinsu dake kasa tacan kitchen din kasan zeji kara alamar suntashi cikin kankanin lokaci akazo akajere musu English breakfast din da aka hada musu suna gamawa suka wuce.
itace tai serving dinshi tai serving din kanta seda ya tabbatar Jr yakoshi sannan shima yafara cin abincin shi ahankali yana kallon Islam da ingari banza ne yanzun ko kwatan abincin bata kaiba amman takusa share plate yanzun, dariya yakeyi kasa kasa don da cikin Jr ma haka tai wannan cin abincin kuma badama kafada seta hau fushi.
tana gama ci tajawo warmer tasake zuba wa tadago suka hada ido dasauri yadauke kai yana nuna shibe maga me take ba but she could see the mischief in his eyes dimples dinshi se lotsawa suke yana kokarin kakkarewa da hannunsa na hagu. tace "your laughing..... uhum uhuhmm" tashiga kukan tabara yace "tohm kiyi hakuri mana I'm not laughing baby kawai dai naga kmr ku uku kuke cin abincin anya ba double ajiya nai acikinnan naki ba," Tace "ai bakasan menake jiba shiyasa kake fadar haka suma maza ya kamata su ringa daukar pregnancy koda once in their lives suringa jin abinda mukeji," yana dariyar sa kasa kasa yake fadin "baby babu abinda kikeji wanda banaji bakiga har wata rama naiba" yafada yasoma pretending nuna mata wiyanshi wai har kashin wiya yayi, Sunfi minti talatin suna bickering saman dining table din tana mai rigima yana lallashi ahaka har suka gama cin abincin kafinnan aka kuma shirya.
Tace mai wai kasala takeji ita bazata iya wankanba bayadda ya iya haka yashiga yawanketa tas suka fito shiya gyara mata gashinnan duk yawanshi da cikarsa bayan yabusar mata a handdryer yashafa mata duk wasu mayukan da take using yaraba biyu yay mata braiding both side kamar wata mace akan Islam babu abinda be koyaba na yadda ake kula da mata ya shiryata tsaf sannan yadau jakar goyon Jr yashiryashi takoma saman gado tai musu bye bye yace mata "suntafi gurin second mommy tunda ita ta dena sonsu kodamuwa bataiba itadai burinta sufita tai barci tace musu "su gaisheta" suna ficewa kwa takoma barci abinta.
Barcin nata beyi wani nisaba taji wayarta nata ringing, ta mirgina ahankali tana reaching hands dinta donta dauki wayar dake saman bedside drawer dinta,tanajin dukma me kiranta be kyauta mata ba ya tasheta daga dan komawarta.
batareda ta duba me kiran ba tadaga idonta arufe takara wayar akunnenta tana fadin "hello," cikin muryar barci, "Islam barci kike I'm sorry don Allah na tasheki kina but is kinda urgent ina kofar sashenki wadannan securities din sun hanani karasowa wai yau bakice zaki ga kowaba dan Allah talk to them I really need to see you" jin urgency din dake muryar jalila yasa barcin Islam yasoma warwarewa don sarai tagane itace tamike ahankali tana fadin "basu wayar" jalila dake tsaye da securities charko charko ta mika wa daya wayar tana galla mai wata uwar harara yakarba, batasan me Islam tace maiba taga yace mata "done your highness" yamika mata wayarta da sauri ya kauce ya bata guri. tawatsa mai kallon banza tana fadin "zakasan ni kaiwa haka tai shigewarta ciki,"
kimono Islam tadaura saman t-shirt din EHSAAS dake jikinta data mata oversize ta dauro vintage scarf da wani slippers mai laushi akafafuwanta mai yar teddy ajiki tafito a falon kasan ta tarar da jalila aiko tana karasowa ko zama bataiba jalila tamike da wani file ahannunta. Islam anitse tazauna jalila ta dire file din agefenta tana fadin "I told you my instincts is always right check this out background check up nasaka akaimin akan waccan yarinyar da yaya ze aura, tunda naga mahaifinta dan borno ne naji ajikina sune wllh," Islam looking confused tarike file din ahannunta tana fadin "su suwa?" Jalila tace "BAGGARA shegun kenan ina mai tabbatar miki wllh kika bari ta auri EHSAAS keda shi sedai kallo, sunyi kaurin suna gurin raba mataye da mazajensu iyaye da yayansu yan uwa da dan uwansu,wllh insuka rike namiji duk mi taurin kansa da kauda kansa seya zama nasu su kadai har abada,su din taurarine masu wutsiya, Islam looking confused take tambayar ta "meye kuma baggara?" Gefen Islam jalila tadawo afusace take fadin wata kabila ce wadanda aka fi sani da "Shuwa-Arabs", asalin su makiyaya ne masu yawo da dabbobin su a kasashen Africa, sun fitone daga kasar Chadi wadda take daga yammacin Africa, yawanci zakiga ana samun yan kabilar Baggara akasashe daban daban kmr su Sudan, Cameroon, Niger, Chad, Nigeria, dadai sauransu, Jalila taja dogon numfashi tace "akasarmu anfi samunsu agaruruwan borno da yobe, abinda yasa nace miki sunada hadari na gaske Allah ya zuba musu kyawun sura ta kirar jiki data fuska, da wata irin kalar fata mai sheki da kyau, tunda naga yanayin fatar yarinyar nan itada kanwarta harma da kakartasu nasan cewa sudin ba Fulani baneba, dukda dai naji ance uwar tasu bama yarnan baceba amman dai uban an tabbatar min baggarane shi gaba da baya kinga that make her one, Islam jitai ba'a taba kona mata rai irin haka ba yanzun saboda tazo ta gaya mata wannan nonsense din kawai ta tasota tana dan barcinta ita bataga abu mai ma'ana data fada aduk wannan bayanin nataba. ita kuma ina ruwanta da kabilar Mehtav koda mutanen kabilar zata zauna ne. Ganin Islam batai reacting ba yasa jalila tashiga sake zuzuta abin tace "dandai keba yar Nigeria bace shiyasa kike gani kamar she's not a treat a rayuwar ki but she is Islam bar ganin azahiri kinfita face card bar namiji da farar mace kuma shuwa kintaba karewa dirin jikin yarinyar nan kallo kuwa yana fara tabata seta bude wllh, duk kankantar macen baggara ta iya sarrafa namiji ta yadda bakitaba zata ba sufa abinnasu ance natural ne wasu kuma sunce bin malamai suke shedanu ne nagaske, aborno anai musu take da matan manya wllh sudin basa auren talaka,they was a time lokacin da abbana muka dawo Nigeria aka aura masa daya daga cikinsu wllh zaucewa ya kusa yi kinga rawar kafa babban mutum dashi akan karamar yarinya kusan sa'a tace Islam, da mommy tai magana se yace wai aishi betaba sanin haka akeji in akai aureba seda ya auri yarinyar wai yadade yana cutar kansa ashe, wllh kina ganin mommy haka haka from outside she's okay but deep down she's not domin idan da badan atsaye take itamaba tuni yarinyar nan tafitar da ita daga gidan, Matan baggara duk leke leken namiji dason mata inya mallakesu dawiya kiga yakara bin wata macen duk wani kwadayi da kishi na yamace seta kashe mai, Islam banason kiyi going through irin wannan so nazo na baki shawara you should stop this wedding immediately tun kan EHSAAS ya taba yarinyar nan don yana aurarta yana tabata kinshiga uku wllh bar ganin sonnan dayake miki kilama seya manta kinyi existing,"
duk yadda Islam zuciyar Islam ke bugawa da sauri da sauri bata yarda tabari jalila tagane bayanin datai mata ya firgitar da itaba, afili se tace "ai ba akaina zata zaunaba kuma kowacce daga cikinmu da halinta zata zauna,inta kaicemiki ko sarauniyar kyau EHSAAS ze aura I won't feel threatened by her beauty saboda nasan kaina kuma I trust EHSAAS baze taba wulakanta niba ko mata dubu ze aura bayanni," Jalila rike baki tai tana fadin "Shi namijin ne kike cika kuri akanshi,lallai tohm bari kiji su wadannan jinsin ba'a shedarsu their brain is in between their legs," Islam waro ido tai kawai tana tinanin a ina jalila tasao wannan gurguntaccen tinanin nata. Jin tai shiru batace komaiba yasa jalila tacigaba "hmmmmm! Islam bakida wayo duk bayanin da zanmiki bazaki ganeba, kishi da BAGGARA ba abu ne mai sauki ba, sai dai kiyita jin jiki kina kunsar bakin ciki har karshen rayuwar ki wllh, nidai nagaya miki, And look abin bawai a iya surah dakyansu yakeba, sun iya hannunsu ne,kefa ko dafa indomie baki iyaba nasani, mema kika iyawa miji bayan yarinta da shagwaba da soyayyar turawa ina kallon kufa,zece kiyi Abu kifara mai gaddama kuma baya iyace miki no saboda yanason ki, amman su matan baggara da ace ana farfesun mutum adafa abawa miji yasha zasuyi su bashi yasha, sufa indai akwai kudi in kwanciya akace musu suyi yabi takansu zasuyi tsabagen biyayya agidan talaka ne kadai basa zama suke tata rashin mutunci, Islam sun iya kwalliya, ado kowana nau'i sun iya ga sanin sirrin turare, idan sukai miki tirare ze iya watanni jikinki be fitaba, yarinyar nan Mehtav kiduba ran engagement dinnan nasu da aka saceta ta wahala tai wujiga wujiga wllh koda tadawo bani dake muka je dakin ba koda yake lokacin bakya cikin hayyacinki amman wllh ina dosarta wani dan bura uban kamshi takeyi kamar ma alokacin tasake bulbula turare ajikinta, Islam the worst mistake of your life will be barin Mehtav ta aurar miki miji."
Mikewa Islam tayi tana hamma kamar batajin duk abinda jalila tafada tace "kingama" saroro jalila tai tana kallonta cikin mamaki ganin batama dauki duk abubuwannan da take gaya mataba,tace "Islam" hanya taga ta nuna mata "get out I need to rest" tana karasa fadar haka ta juya tanufi dakin hutawarta na kasa jalila bude baki tai tana binta da kallo tana kallon kofar data nuna mata.
kwafa kawai tai ta wurgar da file din anan falon ta kama hanyar fita tana kunkuni for the first time tayima Islam mummunar addu'a yau tana fadin "wanda beji bariba zeji hoho in sha Allah se tama shigo takwace mijin,yarinya bakida hankali ana kaiki kina dawowa soyayyar turawannan da kikeyi dashi ba itace zatasa inya samu baggara ya waiwayeki ba, hmmmmm baggara fa" tashiga nanatawa aranta. sosai jalila ke jiyewa Islam sbd har yau mahaifiyar ta fama take da Mai Martaba Abdul Aziz akan amaryar tashi dukda kuwa ta haifi yara har biyu agidan amman kullum yana jikinta kamar sabuwa ake maida ma sa ita kullum.
EHSAAS kuwa yana fita bangaren su Mehtav suka wuce Abeey se jin dadi takeyi ganin yazo da Jr da gudu taje tai kiran Mehtav tana fada mata daman she's expecting him tunda taga rana yafito sosai har ankusa azahar.
karbar Jr tai ahannunsa bayan sun gaisa yafara tambayarta tsare tsaren da take dashi akasa na bikin dame dame zatayi tunda a Nigeria zatai bikin besan suya kalar nasu al'adun yakeba kuma in anyi bikin a Nigeria hakan baya nufin in ankawota NURISTAN baza asake wani sabon bikin ba, daman tunkan yazo Abeey ta gama tsara mata abubuwan daza ai kasancewar batada kawaye se yadda Abeey tace haka za ayi,tace masa "Abeey dai tace tanason ai dinner, sannan zasuyi cocktail and bachelorette,sannan se bikin al'adarsu da za'ayi a Maiduguri dangin babanta ne zasuyi handling wannan, se kuma kamu da wuni shikenan EHSAAS yaja dogon numfashi yana kallonta, shifa duk lissafi yake bawai bikinne agaban shiba shidai kawai adaura aure a kawomai ita gani yake bukukuwannan duk cin raine amman he don't want to deprive her the right of doing what she wants da bikinta, Yace "is that all you wanna do" jinjina mai kai tai tana dan murmushi yace "badamuwa aimin total how much will you need for all of this," girgiza kai ta somayi tana fadin "don't worry Paa will handle all of it," hararar wasa ya shiga aika mata yadauko wayarta dake gefenta yana fadin "aishi za'a bawa kyautar mata sukutum da guda koh" batasan meya duba awayar ya kwafa anashi wayar ba yay wasu yan danne danne sejin karar shigowar notification tai koda bata dubaba tasan definitely alert ne kudi yasaka mata ganin be miko mata wayar ba yasa itama batace yabata ba yaciro black card dinsa acikin wallet yana daurawa saman wayar " incase if the money I transferred isn't enough you can withdraw the amount you want from here," godiya tashiga yimai yashiga girgiza mata kai yana fadin "tarike godiyarta he'll collect it some other time" tashiga yi masa dariya daidai nan kiran Mai Martaba yashigo wayarsa ya daga yana excusing kanshi, kiransa yay yace "yazo da sauri cikin gaggawa," yace "gashinan," ganin sauri yake yasa Mehtav tace " yaje kawai yabarmata Jr inyayi kuka zata maidashi gun mom din nashi" sosai yaji dadin hakan datai yawuce ya barmata Jr sunata wasa abinsu, text yaywa Islam koda tatashi daga barci in taje bangaren fulani bata ganshi ba kar hankalinta yatashi ya barshi gurin Mehtav kafinnan yakarasa private chamber din Mai Martaba.
Dawani irin mamaki yake kallon mutumin daya tarar suna zaune suna shan tea tareda Mai Martaba kuma bega alamar wani tashin hankali ba ciki. asanyaye ya karasa yana kai gaisuwa gurin Mai Martaba ya amsashi da fara'a yana kallon yadda Abraham ya dauke kai daga kallon EHSAAS. Mai Martaba yace "bakaga sirikin naka baneba yarima" se asannan EHSAAS yasake tabbatar wa Mr Abraham Zion ne dagaske afadar tasu yau, gaidashi yayi cikin mutuntawa.
Abraham ya amsa fuskarnan babu yabo ba fallasa,Mai Martaba yace " yazo ganin Islam ne shine yafara biyonan mugaisa surprise zemata don ko ita batasan zaizo nan dinba" murmushi EHSAAS yay yana fadin "aikuwa zataji dadi sosai inta ganshi" Mai Martaba yace "shiyasa na kirawoka saboda dakanka nakeso kai mai jagora zuwa sashen naku," EHSAAS dan sosa keya yay saboda yasan har lokacin Abraham bawai wani sonshi yake ba kawai dai ba yadda zeyi dashi ne kuma ya gane cewar duk taurin kansa islam taci ubanshi yakasa fizgeta ajikinsa shiyasa kawai ya hakura yabada kai bore ya hau.
Abraham sallama yashiga yima Mai Martaba kan cewar inze tafi ze leko suyi sallama kafinnan yabi bayan EHSAAS, EHSAAS harda bude mai mota da kanshi with due respect shiga mai siriki Abraham yadauke kai yawuce gurin motar da yazo da ita mai numfashi shishi kadai abinsa yauko driver be dakko ba.
EHSAAS yay murmushi yashiga tasa motar yanufi bangarensu da bashida wata tazara da sashen Mai Martaba, suna zuwa aka bude musu babban gate din sashen EHSAAS yakarasa yay parking a gurin da yake ajje motocinsa Abraham ma haka kafinnan yafito seda yajira abraham yagama gyara nasa parking din tukunna yafito, Abraham ko kunyar EHSAAS be jiba se karema gidan nashi daya mugun haduwa ya burgeshi deep down yay amman afili seya tabe baki kawai.
ba tareda yace mai komai ba bayan yafito yafara tafiya abraham yabiyo bayansa har suka karasa gaban babbar kofar shiga gidan fadawan wurin suka zube, ba dai sufara kirari ko gaishe gaishe ba saboda EHSAAS ya dade da taka musu burki akan yimai wannan dabi'ar acikin gida bayason wannan kirarin da hayaniyar agidanshi, afalonsa wanda yake saukar manya baki yasauki Abraham in no time ya bada order ai attaining to him nandanan aka cika gabanshi da kayan ciye ciye da taune taune wanda kallo daya Abraham yayi musu ya dauke kai yana kalle kalle alamar yarshi kawai yazo gani ba wannan ba yana jiran yaga inda zata fito. kiran wayarta EHSAAS ya shigayi yaji bata picking hakanne yasa kawai yajuya yawuce master bedroom dinsu kwata kwata bata ciki,dakinta nanma bata ciki seya fara tinanin kota tafi bangaren Fulani ne wata zuciyar tace mai yaduba library. kofar library yabude bata ciki amman yana kallon desk din datake zama yaga fitilar gurin akunne yasan tashigo, straight yawuce dakin hutunta.
asaman couch ya hangota ta kashingida da alawa mai tsinke abakinta da wani novel it end with us, ahannayenta tana karantawa tayi nisa acikin karatun shi don ko dagowa bataso tayi dukda taji motsin shigowar tashi. karasawa yay gabanta yana fadin "audaman abinda zakiyi kenan shiyasa kika koramu kikace barci zakiyi koh," murmushi tamai tana rufe fuska da littafin domin barcin harga Allah takeji alokacin kawai dai zuwan jalila ne ya rigada ya wargatsa mata dukkan nutsuwarta tayin barcin shiyasa tadakko novel tana karantawa.
karbe littafin yay yana mikar da ita tsaye akan kujerar, tace "ina Jr ko kakaishi gurin maama?" girgiza kai yayi yace "uhmmm uhmmm yana gun Mehtav" dan jinjina kai kawai tai alamar taji. ahankali yake fadin "nima zansha" yana kallon sweet din tata girgiza masa kai ta shigayi tacire alawar abakinta yanajin yadda kamshin alawar ke dukan hancinsa yawani lumshe ido yana fadin "yummy baby," dariya ta kyalkyala mai tana fadin "bakyau kwadayi" shima yace mata "bakyau rowa tohm sammin yar kadan baby," maidawa bakinta tai tana sha tana bin bakinsa da wani naughty look dake kwance kansa baki. seda ta tsotsa dakyau sannan tacire tana sakala hannayenta agefe da gefen wiyanshi tana zaro harshen ta tana fadin "Here," shikansa harshen yakoma red kalar alawar, tongue dinshi ya dora asaman nata yashiga sha yana wani lumshe ido, suka fara wani passionate french kiss, ahankali ya dago yana kallonta kafin yakasa controlling kanshi yake fadin "you have a visitor" dan waro ido tai alamar ita yajinjina tace "waye?" yace "is a surprise se kinje can zaki gani," "pls tell me who is it?" Girgiza kai yashiga yi tace "bari naje nagani" sakkowa tai ahankali daga kan kujerar ta dau scarf dinta daya zame ta daura shikuma ya koma saman couch din yakwanta yana kallonta kasa kasa yake fadin ,"kije kidawo you must finish what you start," dariya tamai tana fadin "ko zaka daukomin gyalena asama ni gandar hawa nakeyi," murmushi yay yana fadin "Lazy lazy don't worry the scarf is okay,aiba stranger bane, ni halin danake yanzun takawa ma bazan iyaba" tace exaggeration tana samai alawar abakinsa enjoy this one kafin indawo,girgiza kai yafara yana fadin "it taste better on your tongue," dage mai gira daya tai tanufi kofa irin really dinnan,. "Yana Main sitting room" yasanar da ita kafinnan tafice adakin, ji yay kawai baze iya barinta tareda Abraham ita kadaiba don harga Allah har yana shakkar abinda mutumin ze iyayi, mikewa yayi kawai yabi bayanta, saboda bata sauri hakanne yasa yacimmata daidai tana karasawa corridor daze sadata da falon da Abraham yake atare suka shiga da sallama abakinta sanin Abraham ne agurin yasa EHSAAS beyi sallama ba.
ganin Abraham Islam tawara ido cikin mamaki da farinciki takarasa kusa dashi tun zuwansa se alokacin EHSAAS yaga yayi murmushi kuma murmushin yamai bala'in kyau don Abraham islam ne asiffar namiji kamarsu daya kwabo da kwabo. " come here my durlin" yafada yana bude mata hannayensa adan kunyace because she's still feeling awkward itama da wannan shirin nasu gwarama tawaya tadan saba sosai akan physically karasawa tai gareshi ya rungumota ajikinsa yana fadin "congratulations I heard from your mom," rufe fuskarta tai wai ita tana jin kunya, murmushi Abraham ya cigaba yana cemata "his so proud of her," harda tambayarta "cikin wata nawane?" da hannu tai mai alama da uku yashiga jinjina kai ko damuwa da EHSAAS daya zauna agefe can daban ya shiga danna waya be yiba yashiga fada mata "so yake ta haihu agurinsu wannan lokacin he wants to pamper her like a baby,so yake duk abinda bemata ba da cikin Jr yaymata shi yanzun," harda tambayarta gender yafito girgiza mai kai tai alamar a'ah yace "immediately gender na fitowa ta kirashi tafadamai saboda siyayyar kayan haihuwa daya fara," EHSAAS abin dariya ya ringa bashi aranshi yace ga wanda yafishi zumudin haihuwar, Tace ,"daddy am so happy you came, I thought your too busy lokacin da mom tazo haka tacemin kana US kaje evangelism," yace "yah kuma suka batamin raiba,I couldn't do what I want ina gafa nakusa barin Jehovah," dan waro ido tai tana fadin "dadday da bakinka," yace "yah I think I'll go back to Catholicism kintina one gospel book dana taba...."
Ganin EHSAAS yadago yana kallonshi ne yasa kawai ya basar yana fadin "I couldn't let my daughter's life be too busy without her old man checking in." Cikeda curiousity take fadin "Daddy tell me what make you want to leave Jehovah witness," Yace "we'll talk about it some other time Yanzun dai… where's my grandson?" Murmushi tai jin ya kauce tasan beson yin magana ne agaban EHSAAS kada yafado matsalolinsu yasamu abin fada yaymasa dariya, Tace "yana gurin Mehtav?" Abraham yace "Mehtav whose Mehtav?" Banace kidena bawa maids dinnan shiba," Tace "calm down dad,ita ba maid bace" Yace "toh wacece" Ahankali tace "she's Ehsaas' bride."
Abraham ya tsaya, ya dan runtse ido yabude kamar yana son ya tabbatar da abin da ya ji, yace "Bride? As in… amarya?" Ta jinjina masa kai Yace "and who are you then? If someone is his bride?"
Dan shiru Islam tai takalli EHSAAS wanda hankalinsa ya koma kan wayarsa amman yana sauraron duk abinda sukeyi kuma ya zaunane bawai don yasa musu ido ko yaji me suke cikiba kawai he is here to protect her shi har yanzun be gama sakin jiki da Abraham ba. Anitse Islam ta shiga bayyana masa cewa Ehsaas zai kara aure, kuma ta yi masa bayanin yadda wannan ke cikin al'adu da dokokin gidan sarautar.
Data gama bece komaiba kawai ya kalleta yace "tatashi taje ta karbo mai jikansa yanzunnan aduk indama taje ta kaishi" jiki asanyaye ganin ya hade rai tamike,tanufi kofa dazata koma ciki tadakko hijab dinta.
EHSAAS mikewa yayi zebi bayanta Abraham yace "wait inason magana dakai" chak EHSAAS ya tsaya yajuyo irin yana son ya tabbatar dashi yake ya nuna kansa ya jinjina kai alamar eh shi, komawa yay yazauna Islam tafice tanayi tana waiwayansu tana fatan Allah yasan wannan abin baze zama sanadin kara tuburewar babanta ba tasan halinshi sarai Seda ya tabbatar Islam ta tafi duka sannan ya kalli EHSAAS kai tsaye cikeda gadara yake fadin "I want Islam to come have a vacation with us. I've booked and paid for everything already. I hope you won't make me waste my money… because I will not go anywhere without my daughter."
Ehsaas ya yi murmushi kawai saboda tsaf yagane Abraham yarsa yake tayawa kishi kuma so yake yasamu yayi slight mistake yay holding dinshi akansa yamai wannan tambayar gadarar ne saboda yana sa ran cewa zai ce "a'a" domin ya samu dalilin tuhumarsa da kulle 'yarsa a palace ya hanata zuwa ko ina da kuma cutar da ita tahanyar karo aure, gane wannan da EHSAAS yayi yasa cikin kwanciyar hankali yace masa
"Alright. She can go."
Shiru Abraham yayi jin EHSAAS be musa mai ba sam sam shi beso haka yace mai ba gyara zamanshi yay cikin dan basarwa yaace "Good," kawai.
Daganan har Islam tadawo tareda Jr ba wanda yasake wa wani magana acikinsu ganin Jr yasa Abraham yadan saki ransa amman har lokacin dacin mgnr karin aurennan yakeji aransa yana fadin "ji abinda peace tajefa kanta ciki" jin ana kiran sallar azahar yasa EHSAAS yafice yabarshi tareda Islam da Jr yana fita yashiga jera mata tambayoyi "badai ayi mata komai agidan ko? "is she okay with being a co wife? Is she happy?" irin yanason yatabbatar tana lpy tace mai "she's okay babu abinda tanema tarasa agidan she's fine," daga haka itama ta barshi da Jr taje tai sallarta batareda tagaya mai me zatai ba amman yasan sallar taje tai deep down koda tadawo tasa aka kawo mai abincin rana kinci yay ko ruwa besha ba se karfe uku yafito daidai lokacin da EHSAAS yadawo shima.
sallama sukai sama sama dashi, yasa security suka kwaso uban gifts shopping din dayay ma Islam da Jr harda unborn suka ringa kaiwa ciki Islam se murna take tana mai godiya sukai sallama yashiga motarsa yawuce kamar yadda yaywa Mai Martaba alkawari haka ya koma gurinsa, Akai mai iso yamai sallama kyauta aka bashi anannade awata box dukda yaso kin karba haka Mai Martaba ya tilasta mai ya karba tareda jaddada mai komai yariga yawuce duk sanda yakeson zuwa ze ringa iya zuwa yaga yarshi kafinnan Abraham yakama hanyar ficewa a palace din yatafi cikeda kewar yarsa da jikansa don jiyake yama fison Jr akan peace don Allah ne ya daura mai soyayyar yaron acikin ransa.
Afalon tashiga unwrapping boxes din gifts da abraham ya basu tanata murna tana nuna ma EHSAAS yace " yayi kyau angode," anan ne kuma yagaya mata maganar tafiyarsu da Abraham yayi masa kuma ya amince, kallon yadda yake gaya mata ya amince takeyi kamar ba EHSAAS ba wanda baya iya barinta taje konan dacan batareda shi ba. amamakance take fadin "Wait… so you actually told my dad yes?" ta tambaya, voice dinta low amma cikeda curiosity da little suspicion a ciki.
Ehsaas ya yi dariyar nan tashi tawasa yana fadin "Of course. What else did you expect? You think I will say no just to make him feel he's right?"
Islam ta dan tabe baki. "I just… I know my dad, Ehsaas. He's looking for something to use against you,he still despise you ga maganar aurennan takara hassala shi You agreeing so easily....." Takarasa tana daddaga kayan Yace "thats exactly why he won't have anything to use," ya karasa yana mikewa daga kujerar. "Besides, if you want to see him, you should. You've been through a lot lately. Maybe a little change of environment will do you good, nasan kema kinason zuwa shiyasama nayarda kawai base anta ja inja ba."
Shiru tai na dan lokaci, tana kallon sa kamar tana kokarin karanta wani abu a cikin idonsa ganin yaki yarda su hada idon yasa tace "Haka kawai? No drama, no conditions? Ka yarda ka amince intafi inbarka?"
"ohh I'm I a drama king," yafada Dariya tai kawai tana fadin "Kawai dai nayi mamakine yadda ka canza ra'ayin ka lokaci guda," Murmushi yay kafin yace "Sai dai ki yi sauri ki dawo kafin na fara missing dinki sosai." Yakarasa yana jan kumatunta, "kuma promise me you'll take care of yourself and our babies" Murmushi tai ta jinjina masa kai tana fadin "I will in sha Allah thank you, Yaushene tafiyar?" Yace "yafadamin in the next five days,"
Jinjina kai tai tana fadin "that's actually soon but nidama ashirye nake yanzun se muje daki ka tayani mu hada kayana dana Jr Allah sarki sire harna fara tausayin ka kai kadai za'a bari agida, amman kaji dadima ga Mehtav kaga se kuyita shan kwalliyar kauyawan ku,"
murmushi yay jin kamar cikin kunkuni tafada yasan she's overthinking it batasonn tatafi ta barshi tareda ita hakanne yasa to ease her mind yace mata "suma gobe zasu tafi ai," dan wara ido tai dukda deep down taji dadi amman azahiri se tace "dagaske" yajinjina mata kai yace "ni kadai zaku bari dagani se halina beside this days I'm distracted alot inada aiki sosai agabana inkuka tafi kunga sena samu time din yi sosai, nasan ana shiga wedding bazan samu naiba so gara nayi dawuri without being distracted" dariya ta shigayi tana fadin "aizamu gani, wato munema distraction din kardai inje kanna karasa afara kirana ana cemin ana missing dina" murmushi yay yana fadin "bazanyi ba, ko za'ai betting ne? mezaki saka?" ya mika mata pinky finger dinshi nata tamiko suka kulla tace "indai natafi ka kirani a day one that shows kayi missing dina zaka barmin comfort pillow dinka na study room, sannan zaka barmin right side of the bed kullum," girgiza kai ya shigayi yana fadin "wannan ojoro ne you know I can't sacrifice does things ke me zakiyi sacrificing tohm," Dariya tashigayi tana fadin "choose" tinani yay se kuma yace "indai ban kiraba ke kika kira you'll leave the whole dressing mirror for me duk sanda mukai wanka nine zanfara shiryawa and you'll take away all your girly stuffs from my mirror," dariya tafara tace "nayarda" yace "and the right side of bed will be mine forever" Tace "na yarda" se sannan suka saki karamin yatsan juna Islam tana dariya take fadin "harna fara ganin yadda zanji dadin pillow dinnan da ake kullewa adaki aboye ahanani tabawa kamar da gold aka yishi" yace "keda pillow dina kwalele bake babu shi ehen kicire raima" yakarasa yana daukar wayoyinshi yanufi daki.
Sada tagama kallon gifts din tasa akai mata nan dakinta nakasa aka shiryamata su tukunna tahau saman. se alokacin tai lunch EHSAAS dama be fiya cin abincin ranaba yaci nasafe shikenan ganin Jr yarigada yay barci tashiga dakin ta kwantar dashi tatarar da EHSAAS yayi shiru kamar wanda yake dogon tinani, "are you okay sire, kodai missing din nawa kafara" takarasa tana daura hannun ta saman goshinsa taji ko baida lafiyane girgiza mata kai yay kafin gently yace "I just have a request to make," nutsuwa tai tana sauraronshi,yay shiru yakasa cewa komai,hakanne yasa tace "akwai damuwane sire pls tell me hankali na yafara tashi," ahankali ya dago yakasa hada ido da ita yace "I want to go on a date tonight" se yay shiru tanajin yayi tasan bada ita zeje ba jikinta ne yay danyi sanyi yadago yace "with Mehtav I wanna spend sometime with her andnd thank her for all what she has done for me before she leave for Nigeria, so I will be very late tonight baby don't wait for me if that's okay with you" yafada yana rungumota jikinsa, "BAGGARA" kawai taji mgnr jalila na yawo ya kanta da sauri ta rintse ido tana hadiyewa tace "shine seka tambayeni nima ya kamata ingode mata ai she save our son's life she deserves more than a date sef you can go sire Allah yatsare hanya,"
Murmushi yay yana kissing forehead dinta ahankali yace "we'll go out too kafin kema kiyi naki tafiyan" murmushi taimasa kawai tamike tana fadin "is hot in here lemme quickly shower," tawuce toilet dasauri don batasan yaga raunin dake cikin idanuwanta, Bata karasa rufe kofar ba tajishi haryafara waya da Aman yana cemai yamai reservation awani hadadden restaurant wanda basu taba xuwaba tanaji yana tsara mai how sweet and romantic he wants it to be harta da abincin da za'a kawo he already planned everything tanajin zumudin dake cikine voice dinshi kawai tarufo kofar donta dena jin mgnr tasa tunkan zuciyarta tafara kitsa mata abubuwa marasa kyau.
Abeey kasa dena kallon alert din tai tana sake wara ido takalli alert din takalli Mehtav, Mehtav tace "dalla ban wayata sekace yar kauye baki taba ganin kudiba," tace "yah Mehtav ina ganin kudi amman bantaba ganin kudi masu yawan wannan a account dinkiba se yau 100M fa yasa miki, ga black card which is limitless is money water agurin handsome prince ne?" Tace "nikaina dana gani naji tsoro Abeey amman dana nunawa Paa ba abinda yace da alama dai yasan he's capable of doing that he even told me to use them inyi duk abubuwan da suke gabana amman yace I should not use the card yasan duk tsiya bazamu kashe 100m ashirin biki kawai ba kinsan su, su EHSAAS yadda suke biki ba kalar namu bane so he thought yadda suke zubarda kudi abukukuwa haka muma mukeyi," Abeey tajinjina kai tana fadin "shiyasa nace miki baki dace da kowaba se EHSAAS ya Mehtav akwai money ai dolema indawo gidanki bayan aurannan," girgiza kai Mehtav tai tana fadin "Allah yashiryeki Abeey wsi yaushe zaki dena son kudinnan ne wai," Abeey tace "kai gaskiya ba rana balle wata yah Mehtav ai inajin inban auri Mai kudi ba bazan taba aureba," rike baki Mehtav tai tace "ke tunkan ki tafasa zaki kone kike mgnr aure har nawa kike" dariya Abeey tafarayi tafara fara mata ido wai "itamafa macece kuma duk tsiya zata girma itama aimata aure," seda takai bakin kofa tafadi haka Mehtav tai yunkuri kamar zata cafkota dasauri ta fice tana dariya,text ne taga yashigo wayarta, ganin EHSAAS yasa tai saurin budewa.
Hey Amor, tonight at nine be ready, I've carved out alittle piece of time just for us, baby I want it to be a chapter of our own, is unwritten and waiting for us to write it the way we want, dress your heart in softness and your smile in magic my cuticle, I'll be waiting to turn this new page with you.
Love EHSAAS
Wani irin kwanciya tai saman bed din tashiga birgima after reading the message wato soyayya da writer tayi arayi look at how he managed to make her smile with just few words, jitake inama zata iya jawo daren yayi kawai taganshi agabanta.
Don't forget to Like Share Comment Vote
To catch every new chapter as soon as I drop it, follow me on all my platforms: 📱 TikTok: @fatoumspassion 📸 Instagram: @fatima-rufai-nasidi 📖 Wattpad: @fatoumspassion 📚 Arewabook: @fatoumspassion 💬 WhatsApp: ***
If you don't have my number, save it and send me a message saying "saved", so I can save yours back and you'll always get my story alerts whenever I upload a new chapter.
[04/10, 20:29] Fatima Rufa'i Nasidi: *** Its Fatoumspassion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM