EHSAAS

Chapter 60

by @fatoumspassion

Paa takirawo, bayan tagama birgime-birgemen nata na murna, ta saisaita nutsuwarta, ta sanar da shi EHSAAS yanaso su fita yau bayan sallar Isha. "In Allah yakaimu," saida yay dan jim tukunna, yabata izni tareda yimata nasiha tarike mutuncinta a duk inda zata samu kanta. Yadan dai jamata kunne sannan yace, "Allah ya kiyaye hanya."

Dama tasan baze hanata ba, hakanne yasa tafito tasanar da Abeey. Abeey kamar itace zata je date din; saboda murna suka shiga ciro duk kayan Mehtav don su zabi wanda zatasa yau din. Kwatsam bayan sallar Azahar, sega wata maid tazo EHSAAS ya aiko mata da wata box. Abeey ce takarbo, takawo mata, suka shiga budewa kayan dayake so ta sakane aciki.

Suna budewa, suka ci karo da wata hadaddiyar limited-edition handcrafted piece daga Elie Saab, Royal Modesty Line Abaya. An yi ta da silken chiffon black mai shimmering gold embroidery, an saka ɗan sparkle of stones masu shape din moon. Hatta veil ɗin is embroidered da zare na platinum mai laushin gaske, ga takalmi da karamar jakar purse din, duk kalar abayar da alama set ne, tare aka siyosu kuma cif daidai ita kamar ya aunata.

Abeey ce tashiga zuzuta wa Mehtav abayan, tana fada mata irin kyan da zatai idan tasaka ta.

Mehtav se jin dadi takeyi, kafin kuma tace, "Kedalla kiyi shiru, se terere kikema mutane, sekace yar kauye."

Dariya Abeey tashiga yi, tana fadin, "Kibarni nai murna ta, finally yau zanga yah Mehtav going on a date da mijin dana zaba mata." Waro ido Mehtav tai, jin me Abeey take fada, tace, "Wato mijin ma kece kika zaba?"

Abeey tana hura hanci tace, "Tohm, inba daban niba aiba inda ma soyayyar taki da EHSAAS zataje. Amman dai base kin godemin ba, I know you're already grateful for everything I did" Rankwashin wasa Mehtav takai mata saman kanta, tafara exaggerating zafin, tana wai, "Washhhh, dazafi fa ya Mehtav, karki fasamin kaina."

Tace, "Kigama sharrin naki."

Ranar dai wuni sukai suna farinciki, itada yar uwarta Abeey na mata describing what she should be expecting adaren yau din, kamar itace EHSAAS.

Fitowa EHSAAS yay daga bathroom, bayan yay wanka, yadauro alwalar Magrib. Islam bata dakin, tasauka shan iskar yamma cikin a garden. Shiryawa yay cikin normal kananun kayansa; yadau tuxedo din da ze saka da car keys dinshi, yasakko kasa. Anan yatarar da ita a cikin garden tareda maid; kafafuwanta na cikin katafaren swimming pool din dake gurin. Jr kuma yana kan baby walker dinshi, yanata wasansa tareda maid, da alama tayi nisa cikin tinani don har ya karaso bata sani ba. Murmushi yay, yana dafota yace, "Babe."

Juyowa tai, tasakar mai murmushi tana kallonsa. Yakalli agogo yana fadin, "I'll get going yanzun, za'ai sallar Magrib, yakamata ku koma ciki naji wajen kamar da sanyi." Dan jinjina kai tai tana fadin, "Jira nakeyi ayi kiran dama se mushiga." Yace, "Ahm, bari na wuce. Baby, don't forget to ensure eat your dinner early, kinji, take your drugs and sleep tight. Don't wait for me kinji tawan" yakarasa yana kai bakinshi saman nata; light kiss yay mata. Tai kasa da kanta, bata ce mai komaiba. Yadan dago da habarta, yana kallon yadda ta lumshe ido "Are you okay?" Jinjina mai kai tai; sarai yasan she's not okay, amman shiyaya zeyi.

Mehtav ma na bukatar attention dinsa; dole yakasance meyin adalci atsakaninsu. Inba haka ba, inyace ze biye ma zuciyarsa akan Islam. Koda anyi auren haka zasuzo yaringa shiga hakkin yarinyar mutane. Gara tasaba da rashinsa tun yanzun.

"I love you my peace," yafada yana kara kissing din bakinta. Kakalo murmushi tai, wanda kana ganinshi kasan iya fuskane baikai zuci ba; tace masa, "Oya, kai sauri, karka makara Nasan kai zaka ja sallar."

Jinjina mata kai yay ya karasa gun Jr, dayaketa dago mai hannu alamar yadaukeshi. Daukarsa yay, ya sumbaci cheeks dinsa da forehead dinshi before ya mikama maid shi yadawo gun Islam. Yace, "Baby, zantafi, bakice kina sonaba?" Dan dauke kai tai tana fadin, "You know I always do, right? Just go, my regards to Mehtav."

Yace, "Thank you. Pls take care of yourself for me." Jinjina masa kai kawai tai. Haka yamike yafice; jikinsa asanyaye. Already Aman ya tarar yazo yana jiranshi. Yashiga gaban motar bayan ya ajje kayansa a baya. Aman ya gaidashi suka wuce. Jin shirun yayi yawa; Aman ya tambaya, "Uncle Prince, lafiya kuwa? Kodai auntyn bata yarda bane?" Girgiza kai kawai yay yana fadin, "She's not someone da take going back on her word; baxata taba cemin batasoba. Amman actions dinta ya nunamin bataso, Aman." Dariya Aman yafara yi yana fadin, "Tohm, ka gode Allah bata daga ma hankali taita rigima ba, Kasan kishi fa kumallon matane zata sabane ahankali uncle, aitunda kai choosing polygamy you have to be strong. Irin abubuwannan nasu karya dameka, Inba haka ba zasu maida kai ball tsakaninsu su saka damuwa, you'll never satisfy both of them, Abu kadan zakai suce ai baka musu adalci indai matane. Amman gaskiya nikaina haushi nakeji, inaga aunty Islam aitama yi kokari. Wallahi ni inda macene ai babu yadda za'ai inyarda aimin kishiya."

Kallonsa EHSAAS yay, yana fadin, "Oh, yanzun dai bayanta zakabi kenan, zakaje kazigata karta yarda?" Girgiza kai Aman yay, yana dariya yace, "Just stating a fact. Kasan ni itace tawa, so don't expect me to support your so-called bride. I'll never like her the way I like Islam, Kaima kasani, Uncle Prince Date dinnan ma donba yadda zanyine dakai."

Daidai nan suka karasa kofar mosque. Yakalli Aman yana fadin, "Aman, am I really doing the right thing? Ko kaima kana ganin kamar ina cutar da Islam ne?" Dan jim yay kafin yace, "Religiously and culturally you're doing nothing wrong, but romantically you're doing something very wrong, Idan akaji labarin soyayyar ka da Islam daga farko, akasan kuma ayadda ze kare, tabbas masoya zasu dade suna caa akanka, Sunama Allah wadai da abinda kakeyi, Amman a addinan ce ai Allah yaga zuciyarka, ba don kacutar da ita zakai aurannan ba, Kuma aurennan halak ne, Allah yasan zuciyarmu maza shiyasa ya halatta mana auren daya biyu uku har zuwa hudu uncke we are polygamous in nature" Dan jinjina kai EHSAAS yay kafin yace, "Buy her a new RR Boat Tail 2025 irin nawannan sak." Dariya Aman yafara yana fadin, "Bribery zakai kenan?" Yace, "Bawani bribery ainayi niyya ne damacan tacemin tanaso."

Daidainan aka fara kiran sallah. Fitowa sukai daga cikin motar suka nufi ainahin cikin mosque din, inda aka ringa gaida EHSAAS wanda yaci serious kamar bashi ba yanata amsa gaisuwa. Har yazo yasamu Mai Martaba zuwansu befi da minti sha biyar ba aka tada sallah. EHSAAS ne yajasu, ana idarwa yawuce sashensa nadacan wanda yake matsayin na Aman ayanzun acan. Yay shirin nashi don kwata-kwata bayason yay abinda ze sosawa Islam ranta.

Mehtav ma daga nata bangaren seda tai sallar Magrib. Abeey ta tayata shiryawa. Sunajin anfara kiran sallar Isha, tatashi nanma tayi. Immediately, ana idarwa, aka aiko maid ɗin palace ta shigo da girmamawa. Ta sunkuya tace: "Yarima ne yace in sanar da ku, lokaci yayi. In Hjy Mehtav tagama shiryawa, akwai driver da mota suna jiranta a courtyard."

Abeey ce tai saurin amsa mata da, "Toh, tana zuwa." Mehtav tamike tana fadin, "Tohm, bari in wuce." Tare kofa Abeey tai tana dan waro ido tace, "Ke, baki iya dan jan ajinnan ba, yah Mehtav, koma kizauna. Haba, aise yazata ma, akan kaya muke harkin wani shirya jiki na rawa, zaki je akan lokaci. Senan da minti talatin zaki fita."

Dan jim Mehtav tai kafin tace, "Kumafa, Abeey, hakane, bari nazauna."

Zama tai. Abeey tacigaba da kallon reels a wayar Mehtav, tanayi tana nuna mata abubuwan da suka bata dariya. Mehtav mikewa tai tana fadin, "Abeey, karfa muyi rashin hankali, kinga munyi dashi fa, karfe tara gashinan har ya kusa."

Abeey tace, "Let him wait, your going to be his queen. Gwara yasan kema kinada steeze" "Nidai tafiya zanyi Allah." Abeey dagudu taje tasa key adakin, tana zarewa, take fadin, "Kibari taran yacika Pls mn, kinsan komai alissafe nakeyi, just listen to me."

Badan Mehtav tayarda da tsarin Abeey din ba, tazauna aiko tara nacika. Tamike Abeey tabude mata kofar. Dakin inna tafara zuwa dayake Paa ya gaya mata maganar fitar Mehtav din, albarka tasa mata, itama tanata yabon kyan datai mata kafinnan taciro wasu humrahs masu dadi data taho dasu tundaga gida, tashiga shafawa Mehtav awiyanta da hannayenta, harda daga kafafuwanta duk tashafeta dashi se wani tashin kanshi takeyi.

Harfa kabbasa seda tayi yau, amman inna tana sake bulbula mata wani tiraren, se kunya ta kamata duka. Abeey se murmushi take agefe itadai, seda ta tabbatar ta gamsu da kamshin da Mehtav takeyi tukunna tabarta suka fito chamber ɗinsu. Abeey sai ta tsaya abakin gurin tana kallon Mehtav, se taga takara mata wani mahaukacin kyau tace, "Dan tsaya incire miki daya don Allah."

Murmushi Mehtav tai. Abeey tadauki hoton nata tana fadin, "Antashi kaina ka gafa yah Mehtav dina, indai wankane, yau anya handsome prince ze iya dauke ido daga kanki kuwa."

Tace, "Nidai muje Abeey, kada kisa yayta jirana. Kinsan ba dadi." Tace, "Naji naji, tattabara sarkin soyayya, muje."

Suna karasa fitowa, suka ci karo da wata arniyar Rolls-Royce Cullinan Bespoke limited edition mai royal crest ta tsaya akofar gurin, cikin midnight blue lacquer finish tare da platinum details. Driver ɗin yatsaya agefe da alamar jiran zuwanta yake, cikin uniform na royal guard, cikeda girmamawa. Ganinsun fito yashiga gaishesu, suka amsa cikin mutuntawa. Ya buɗe mata ƙofar yana dan bowing.

Abeey ce tagyara mata gyalenta kafinnan tai mata alamar tashiga. She's feeling nervous gaba daya kamar tace Abeey din tazo tarakata, amman tasan hakan baze yiwu ba. "This is for just the two of them," kamar yadda yayi requesting, haka tashiga. Abeey tai gefe tana daga mata hannu alamar bye-bye.

Shikansa, interior din cikin motar abin kallone hand-stitched Italian leather ne in ivory, crystal decanter set, ambient lighting kamar ta sama, da fresh roses a cikin crystal vase.

Harseda Abeey tadena hangosu tukunna takoma ciki.

Yayin da motar ta fita daga Palace din, Mehtav ta jingina kanta a jikin glass din tagar motar, idonta cike da mamaki, ganin hadadden birnin NURISTAN da daddare. Wannan shine karo na farko da take ganin birnin, don tunda sukazo daga airport aka kawosu palace, basu taba fitaba.

Wasu irin manyan hadaddun fitilun manyan tituna suna haskawa kamar stars, gine-ginen classical da royal fountains suna ambaliya da launuka iri iri.

Jitake kamar ta shiga wata irin duniya ta dabam, kamar ba'a Africa take ba. Sam sam, NURISTAN batai kala da kasashenmu na Africa ba saboda haduwarta da tsaruwar birnin; ba'a cewa komai se wanda yagani.

Tafiya me nisa sukai sosai, wacca tasa Mehtav takashe kwarkwatar idanuwanta dakyau, tana karema birnin kallo cikeda jin sha'awar sa da shaukin kasancewarsa, inda xata dawo tazauna na har abada.

Tunkan su karaso gurin, Mehtav ta hango wata alama da bata taba gani ba. A gaban babbar kofar shiga gurin aka rubuta: "La Couronne d'Éternité - The Eternal Crown."

Restaurant ɗin kamar wata aljanna ce acikin duniya. Gine-ginensa an yi shi da crystal walls masu ɗaukar haske. Fountain ɗin da yake tsakiyar entrance ya mugun daukar hankalinta. Tashiga kallon ruwan tana murmushi. Se wasu mahaukatan chandeliers datake hanga, tundaga harabar gurin tunkafin ma akaiga shiga ainahin restaurant. Kuma gurin shiru kamar babu halitta ko daya aciki.

Motar ce ta tsaya cak. Driver yafito, yazo dasauri, yabude mata ahankali. Tasakko acikin motar tana saisaita nutsuwarta da hana kanta yin kalle kallen datake tayi tun shigowarsu.

Red carpet din dataga an shimfide tun daga kan gurin inda tafito daga motar har ciki, da wasu roses masu kamshi. Tashiga takawa ahankali tana matse purse dinta dake hannunta, alamar she's nervous. Tana karasawa dab taga wasu manyan glass doors ɗin da suka fi kama da golden arches sun shiga bude kansu. Ahankali tataka, tashiga cikin restaurant ɗin. Tsayawa tai cak, tana kallon gurin. This is the original definition of guraren da wutane takeji suna kirada heaven on earth.

Entire hall ɗin an lullube shi da warm golden lighting da candlelight a kowace kusurwa, yana bada wani irin haske wanda ke sa zuciya taji natsuwa. Ceiling ɗin crystal dome ne, wanda aka tsara da diamonds mosaic kamar sararin samaniya mai taurari.

A tsakiyar hall ɗin kuwa, table ɗaya ne tak aka bari. Round table, covered da silk white tablecloth embroidered da 24-karat threads. A saman an jera candelabra mai walƙiya, da fresh roses daga Netherlands, da plates masu platinum lining, specially designed for Nuristan Royals.

Background music kuwa live orchestra ce daga Italy da France, suna busa violin da harp kamar wadanda aka daidaitasu da bugun zuciyarta,haka takeji. Hangoshi tai atsaya a ƙarshen walkway, yana kallonta kamar ya hadiyeta. Yamata wani irin mahaukacin kyau, sanye yake cikin wata Tom Ford tuxedo black da satin shawl lapel, cufflinks ɗinsa diamond-studded, wristwatch ɗinsa limited edition na Patek Philippe Grand Complication.

Kasa cigaba da karemai kallo tai saboda wani irin kwarjini dayay mata yasa tai saurin yin kasa dakanta. hakanne yabashi damar cigaba da kare mata kallo. Yasoma takowa ahankali, ahankali, Hannunshi daya na cikin aljihun wandan suit dinshi, yana tafiya majestically har ya karasa daf da ita. Sunkuyo da kansa yay kadan, daidai gefen kunnanta, yashiga yimata magana cikin wata irin murya mai taushi yace: "Amor… you look like the crown jewel of Nuristan tonight. Honestly, I don't even know if this restaurant deserves you."

Wata irin kunhace ta lullubeta. Tashiga kokarin boye kunyar, amman kasa wa tai.

Murmushinta ya bayyana azahiri. Ahankali tace, "All this is too much prince Sekace wata princess."

Murmushi yayi ahankali yace, "No, it's not too much. You deserve every sparkle and every rose in this room,plus your going to be a real Princess my lady"

Yana karasa fadar haka, yakama hannunta gently, suka nufi table din. Kujera yaja mata tazauna because he wants her to eat first, kada ya cikata da surutu, takasa cin komai.

A lokacinne, wasu royal waiters cikin immaculate white uniforms suka fito. Suka sunkuya cikeda girmamawa. Soundlessly, suka fara serving starter: caviar da truffle soup ne a cikin glass bowls masu zafi, tare da fresh pomegranate juice.

Daga baya aka kawo main course: roasted lamb da saffron rice, da kuma grilled salmon da aka yi garnish da edible gold leaf. Tsabar kyan da abincin yay, it looks like a work of art.

Ganin bata taba komai ba yasa EHSAAS yace ta ci mana. Ahankali ta kai hannunta ta ɗau spoon ta fara ci. EHSAAS kam, ko kallon abincin bai yi ba, idon shi yana kanta. Kasa cin wani abin kirki ta yi duk yadda kuwa abincin ya yi mata mugun daɗi. Saboda duk sanda ta ɗaga idonta suka haɗa ido dashi kallonta yake. Ita kuma sai ta yi saurin sunkuyar da kanta ƙasa cikin jin kunya tana murmushi.

Sai da ta ce yaci tukunna ya ɗan taba abincin shi ma. Sai da suka gama dinner silently sannan aka kunna wani soft classical music.

Mikewa tsaye yayi yana miƙa mata hannunsa yace: "May I have this dance, Amor?"

Tsayawa ta yi kamar ba zata iya motsi ba, zuciyarta na racing. Cikin ɗan jin kunya kafin ta miƙa hannunta cikin nashi.

A ƙarƙashin crystal dome ɗin suka tsaya a tsakiya, suka fara slow dance. Hasken chandeliers na walƙiya a jikinsu, music ɗin violin na tashi ahankali.

Cikin kunnenta ya shiga yi mata magana ahankali kamar basu kadai bane a gurin, cikin whispering yake faɗin: "Na gode da dukkan abinda kika tabayi min Mehtav, I really appreciate it. Before you leave, I want this night to remain in your heart. Remember that no matter the distance, you'll always be part of me."

Mehtav ta rufe idonta, tana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri da sauri saboda kusancin da suka samu.

Feeling each and every word da yake rada mata a kunnuwanta, telling her how much he loves her. This is the kind of love she's been dying to have, amma yanzu da ta samu sai take ji kamar ya mata yawa, she can't handle it, it is overwhelming. Wata zuciyarta na rada mata idan ke ya miki wannan, Islam yanata ze kasance, Sai take jin kawai tana son ta san ƙalar soyayyar da yake gwada mata Itama insuka kebe, wani bakin kishin ne ya caka mata a kirji ta lumshe ido tana ƙoƙarin danne abinda ke taso mata.

Slowly ya ɗan ja baya yana kamo hannunta. Ganin jikinta duk yayi sanyi ta kasa ce masa komai. Ya ja numfashi mai nauyi yana bin ta da wani irin kallo yana aikamata da wasu irin sakonni da harshe ba zai taba iya furtawa ba. He's just communicating with her da idanuwansa telling her how much he loves her. Ganin gaba ɗaya she's uncomfortable yasa ahankali ya koma da ita ya zaunar da ita a saman kujerar da suka tashi sannan ya ɗauko wani small velvet box daga cikin aljihunsa. Black ne mai ƙyalli, an saka golden crest na Nuristan Crown ya daura saman cinyarta.

Mehtav kallon box ɗin ta shiga yi, sanin sun yi engagement already yasa ba tare da ta shirya ba ta shiga tambayarsa: "Prince, what is this?"

Murmushi yayi mata yana ɗan dage mata gira ɗaya yace: "Something that only belongs to one person in a man's life. Amor, this is not just a jewel, it's a promise."

Ahankali ta ɗauka ta buɗe box ɗin sai ga wani extraordinary necklace daga "Diary Ring Collection by De Beers, L'Éternité Series" ya bayyana.

Waro ido ta yi don ta san brand ɗin. Irin wannan collection ɗin ne wanda mutum sau ɗaya kaɗai yake iya siya a rayuwarsa saboda rarity ɗinsa. Ka'idarsa kenan mutum baya iya siya fiye da sau ɗaya ko da nawa zaka basu kuwa.

An yi necklace ɗin da wani flawless blue diamonds da aka samo daga Botswana, sai center stone guda ɗaya mai heart-shaped pink diamond, wanda farashinsa ya fi darajar gidaje da yawa a duniya.

Mehtav ta rufe bakinta da hannunta cikin rawar jiki. "Ya Allah…" kawai ta iya furtawa. Idanuwanta suka cika da hawayen farinciki ganin EHSAAS chose to give her this. Itafa kenan bai siya ma Islam na, sai ita. Jin kanta ta yi kamar ze fashe, finally ta fara jin gamsuwa akan irin matsayin da ya daurata a yau dinnan.

Ahankali ya miƙa hannu ya ɗauki necklace ɗin sannan ya zagaya ta bayanta, ƙadan ya ɗan dage gyalen abayan da bata yi rolling dinsa na dama, yana saka mata a wuyan ya furta: "I'll forever be indebted to you. Ke ɗin irin mutanen da ake samunsu ne once in a lifetime. Kinsaka rayuwarki a haɗari sau da dama saboda ni. You saved my son's life, you saved me. This jewel is rare, but you are rarer, Amor. Ke mutumiyar kirki ce. Inason ki kasance a haka har abada. Ina alfahari da ke Mehtav kuma inason ki."

Daidai nan ya gama saka mata sarkar ya dawo ta gabanta yana kallon yadda necklace ɗin ya yi mugun haske a kan farar fatar wuyanta.

Mehtav tai murmushi at the same time tana hawaye masu sanyi, ta shiga shafa sarkar a wuyanta, muryarta na rawa take faɗin: "I did all that because of humanity's sake, ba dan kayi rewarding dina bane EHSAAS. Koda wanine bakaiba, I'll do the same thing… but all this," ta shiga nuna gurin baki ɗaya, "You don't really have to. It feels like a dream… do I even deserve this?" ta faɗa tana nuna masa sarkar wuyanta, alamar ya sake tunani, anya ba Islam tafi cancanta yabawa ba.

Murmushi kawai taga yayi, ya kamo hannayenta ya sumbaci yatsunta softly yana cewa: "Don't ever say you don't deserve happiness, Amor. Idan akwai wani da ya cancanta a cikashi da soyayya da girmamawa, to ke ce. Ke din gift ce da Allah ya bani alokacin da na cire rai, na fidda tsammani da rayuwa."

Ganin tana kuka, ahankali ya miƙar da ita cikin sigar rarrashi, ya jinginar da kanta a kafadarsa. Slowly yake rarrashinta har ta yi shiru. Ji take inama duniya zata tsaya, yazama saura ita da EHSAAS kaɗai a cikin hall ɗin nan, just them da tarin soyayyar da yake cikin zukatansu.

EHSAAS jin tayi shiru a jikinsa yasa ya rintse ido, deep down feeling guilty. Yana tuna yadda sukai da Aman dazun alokacin da yake shiryawa.

"Uncle Prince, ka fa saki ranka. You can never please them hundred percent. Dole sai daya taji ka fi son daya akanta, haka mata suke ana gayama."

Sai yace, "Amman Aman, kasan me? Ban cika jin Islam ba because nasan she trusts what we have. And Islam will never ever think bana sonta. Sedai kawai zata ji ba dadi, amman Mehtav, nasan gani take kawai option na ɗauketa. Kuma ba abinda ban yi trying ba, koda na mata wani anin gwanintan She always talks about Islam."

Dan jim Aman yayi yana ajiye wayarsa kafin yace, "Simple. Buy her Diary Ring or necklace. Anything from Diary will do. Ina ganin a social media mata sun dau abin as trend, suna mugun jin kansu special yayinda aka basu something from Diary as gift."

Dan kallonshi yayi yace, "Kayi tunanin banyi tunanin hakan bane? I did. Amman kasan I already used mine. Na siyama Islam zobe."

Yace, "Kash! Wai kai, wace kalar kyauta ce tohm wacca baka taba bawa Islam ba? Wacce dai ake bawa mace a duniya?"

Dan shiru yayi, ya nisa, ya girgiza kai yana fadin, "Wallahi nidai duk basirar dake kwakwalwata na duba, naga babu. Duk abinda zanyi mata maimaicine. Kasan kuma mata they want something special of their own."

Aman yace, "Simple. Let's use my name and get the Diary necklace, shikenan,tunda ni kaga bama tsayayya gare ni ba."

Dan jim EHSAAS yayi kafin yace, "Amman kai fa, in kai aure matarka tace ka siya mata?"

Yace, "Duk ma aikatan gidannan zan yi amfani da sunan wani da information dinsa kawai."

Dariya EHSAAS yayi yana fadin, "Wannan idea me kyau ce. Amman… amman kana tunanin bazata gane na taba siyama Islam abin Diary ba?"

Yace, "Tayaya tunaninta ze kawo ko zata je ta soma tambayar Islam ne? A miskilancin Islam ma kasan ko ta tambaya, ba fada zatai ba."

Sannan yace, "In ita ta gani fa tace mata irin nata ne?"

Girgiza kai Aman yayi yace, "Ai ita zobe ka bata, sai ka sauya, ita ka bata sarka. Shikenan. Kaga itama zata fara feeling kanta daya da Islam din, tunda su dai mata burinsu a yi ta competition da juna."

Murmushi yayi yana fadin, "Bazaka ganeba, ne kawai."

Muryar Mehtav dake cemai bazasu tafi yanzu ba ce ta dawo da shi daga ɗan tunanin da ya tafi. Yadan kalleta kafin ya mata murmushi yace mata, "Sure."

Tare suka fito daga cikin La Couronne d'Éternité, iska mai sanyi tana dukansu.

Har yanzu ƙamshin roses da candles na cikin hall ɗin Mehtav na jin su a hancinta, kamar karsu bar wurin haka take ji. Amman tunawa da cewa Paa fa yasan bata palace, tasan duk dare bazeyi barci ba, seta dawo. Don haka gwara su koma da wuri yadda ze ji daɗin barinta konan gaba.

Driver ne ya buɗe musu ƙofar motar, ita yasa ta fara shiga kafin shima ya shiga. Ahankali driver ya zaga, ya shiga cikin limo ɗin. Wani irin shiru ne ya ratsa tsakaninsu.

Mehtav ta jingina kanta jikin glass, tana kallo yadda hasken fitilun titunan Nuristan ke ƙyalli kamar wasu taurari. Necklace ɗin da ya saka mata yana haskawa a wuyanta kamar ya ƙara mata wani haske na daban.

Bata ankara ba taji ya jawo hannunta zuwa kirjinsa, softly yace: "Amor… tomorrow by this time, you'll be in Nigeria. Na san zaki kasance da all your family members, ga preparations da dukkan excitement din wedding… but what about me? How do I survive 20 days without you?"

Murmushi tadan saki mai taushi tana kallonshi tace: "You're stronger than you think, EHSAAS. Kai fa prince ne…"

Ya girgiza kai yana riƙe hannunta tighter. "No Amor. I'm just a man. A man who is falling harder every second. And I can't let 20 days pass without seeing you."

Wani irin daɗi taji, tana jin kamar iya gaskiyarsa yake faɗa. Kewar tata zeyi sosai, tana jin this is the kind of position datai ta mafarkin samu a zuciyarsa, sai yanzu Allah yayi ta samu.

Daidai nan suka iso palace ɗin. "Kin yi shiru, kice wani abu," ya faɗa.

A hankali ta janye hannunta daga nashi tana faɗin, "Ni me zance? Kasan dolene natafi aiko."

Jinjina kai yayi kafin yace, "Amma ai baki min tayi in biki ba."

Da zaro ido tai, jin rigimar da zeyi kenan. "Toh, ai itama idan son samunta ne, yabita," amma sanin hakan ba zai yiwu ba yasa bata ce komai ba.

Yace, "Gashinan, kin yi shiru, kin daina sona, kin daina ji da ni duka."

Tace, "Ba haka bane, Prince. You have a lot of responsibilities here, and besides, kwana ashirin ne fa kacal. In sha Allah, we'll be together forever."

Daidai nan motar ta tsaya a gaban chamber ɗin da suke. Tana kallon yadda dogaran dake gadin gurin suka yiwa motar kallo daya sanin tawaye suka dauke kai. Dayake bata ganin driver ɗin, amma taji motsin fitarsa daga cikin motar.

Ta kalli EHSAAS, ganin bashi da shirin fita, tafara ƙoƙarin buɗe ƙofa. Da sauri ya ɗan matsa kusa da ita sosai, idonsa cikin nata. Hannunsa biyu yasa ya kama hannayenta dake ƙoƙarin buɗe ƙofar yace: "20 days are too long, Amor. But your smile will keep me alive till then, amin murmushinnan in gani mana."

Bata san sanda ta saki masa murmushi tana rufe fuska ba.

Yatsaya kawai yana kallonta, yana jin kamar ya hadiyeta. Ganin in ya cigaba da kallonta zai iya yimata kalar abubuwan da yake rayawa a ranshi yasa yayi saurin fita daga cikin motar. Ya zagayo yana buɗe mata ƙofar kamar ba prince ba. Cikin dogaran babu wanda yayi kuskuren dago ido balle har yakalli Mehtav data fito daga cikin motar gently.

Driver ya kira da sauri, yakaraso yace, "Ina sakon shi?" Da sauri yabude gaban motar, yadakko wani gift box, yamika mata.

Ta tsaya tana kallonsa da alamar tambaya, kuma yace, "It's for Abeey."

Murmushi tai, ta karɓa tana faɗin, "Thank you."

Yace, "Kice mata zanzo Nigeria in the next ten days. I can't wait for 20 days kafin inganki. I'll take the two of you out acan in Allah ya kaimu."

Murmushi tai tana jinjina masa kai kafin ta juya. Tafara tafiya cikin sassanyar murya tace, "Goodnight, Prince." Dayake ta dan yi nisa dashi, waiwayowa tai taga yayi wani smiling , dimple ɗinsa yamotsa. Babu kunya yay mata blowing kiss, ta lips ɗinsa tai reading yace mata, "I love you." Da sauri tajuya ta shiga ciki tana blushing ear to ear.

Karo suka kusan yi da Paa wanda ya hango tsayuwar motar tasu. Ganin sun jima basu fito ba yasa yasakko yaga ko lafiya. Se kuma suka ci karo. Kallon agogonsa yayi, yakalleta. Da sauri ta sunkuyar da kai, tashiga gaidashi.

Yace, "Seyanzun koh?"

Kasa cewa komai tai. Yace, "Ai kin kyauta." Yajuya yakoma. Duk seta ji ba daɗi don bata san ƙarfe nawa bane. Ganin yawuce tai sauri ta wuce dakinsu tana kunna wuta sosai. Tayi mamakin ganin Abeey azaune tana jiranta, batai barci ba.

Waro ido tai tana tambaya, "Baki yi barci ba har yanzu?"

Dariya Abeey ta shiga kyalkyawa. "Kinsan bazan iya barci ba in baki dawo kin ban labarin date ɗinnan in details ba."

Dariya Mehtav tai tace, "Bari infara wanka. Ungo wannan yace in kawo miki."

Da sauri ta karɓa Mehtav kuma tashiga rage kayan jikinta. Gaba ɗayanta kamshin EHSAAS takeyi.

Abeey tai unwrapping box ɗin tana faɗin, "Wow!"

iPhone 17 Pro Max tagani aciki. Tadakko tana wani kallon wayar tana jujjuyata cikin kwalinta, tama manta darene, Tawani sa ihu Allag yatemaka kofar sound proof ce,

Da sauri Mehtav ta rufe bakinta tana faɗin, "Ke, meye haka wai?"

Da sauri ta cire hannun Mehtav daga bakinta tana faɗin, "Mehtav, smartphone yabani! Look iPhone 17 Pro Max!"

Itakanta Mehtav tayi mamakin dalilin da yasa EHSAAS ya siyawa Abeey waya. Ta ciromata sabuwa dal akwalinta, wani complementary card tagani ciki.

Da sauri ta ɗauka, taga an rubuta: Thank you, Abeey, for colliding me with her.

Tashiga nunawa Mehtav tana hura hanci. "Menace miki dazun banace miki nice sanadin soyayyar kuba? Ke ko godi bare nagode. Look at what he bought me as a thank you gift!"

Tashiga jujjuya wayar tana murmushi, ta rungume ta a kirjinta.

Mehtav tace, "Toh, naji. Congratulations. Ina dai zuwa."

Tana karasa fadar haka tashige bathroom.

EHSAAS kuwa, sashensa yawuce straight, yanufi dakinsa. Mamaki ya kamashi ganin bai ga Islam ba balle Jr. Wanka yayi, yasauya kayansa zuwa na barci. Yafito, yadau laptop ɗinsa da wayarsa, yanufi dakinta, don yasan tasan basu taba raba daki ba tun da sukayi aure, kuma bazasu fara rabawa yau ba.

Islam dake saman sallaya ta gama addu'o'inta bayan tayi shafa'i da wutri. Tana jin motsin shigowarsa, tai saurin shafawa ta nade sallayar. Ta mayar ta koma kan gado tana rungume da Jr dake barci cikin kwanciyar hankali.

A hankali taji ya buɗe ƙofar ɗaki. Ganin wutar a kunne yasa ya kashe, yasaka dim light, yawuce saman bed ɗinta bayan ya ajiye laptop ɗinsa. Tana jinsa yana lekenta, she tried hard kar tai motsi da idonta balle yagane idonta biyu, don komai ze iya faruwa yadda zuciyarta nan ke tafasa da kishinsa yau ɗinnan idan yace ze mata magana.

Gently taga yayi kissing forehead dinta da na Jr. Yakwanta abayanta yana rungumeta, tai luf. Sun jima a haka, bata san lokacin da barawan barci yadauketa ba.

Da asuba, tanajinsa yafita lokacin da akai kiran sallar farko. Seda ta tabbatar yafice tukunna, tamike tashiga toilet ta dauro alwala, tai raka'atanil fajr. Seda taji sunyi kira na biyu, an tada sallah kafinnan, itama tai sallar asuba.

Ta tajima saman sallayar tana addu'a, kafinnan yauma tanajin motsinsa tamike, tahau saman gadon, tai luf kamar me barci. Ko sallayar bata iya tsayawa ta nade ba.

Yana shigowa, yakalli daddumar kawai ya nufi kan gadon. "Babe, babe," yafada yana shafa fuskarta, saboda ko jiya da dare yasan idanunta biyu sarai, banza tamai kawai. A hankali tashiga bude idonta tana mitsitsikawa irin me barcinnan. Yay murmushi kawai, yajawota jikinsa ya rungume yana fadin, "I miss you. Jiya nadawo, kinyi barci" Shiru taimasa kawai, yadago face dinta yana fadin, "Barka da safiya." a hankali itama tace mai, "Morning sire." "Barci zaki koma ne?" Jinjina mai kai tai tana lafewa ajikinsa. Hannunta yakamo, taga yasa mata key a hannunta. Tadago tana kallonshi a ɗan mamakance. Yace, "Uhmmm, it's yours." Dan waro ido tai saboda tasan makullin menene. Tace, "Kabar min." Girgiza kai yayi yace, "It's a brand new one. Ai nace bazan baki nawa ba." Sosai taji ranta yayi fari tafara murmushi tana fadin "Thank you sire, Allah ya kara budi, nim nabar maka faran benz din" Tana fadar haka yasan tayi cheering up Yace, "Ameen, other half, amman kirike kayanki kardaga baya azo anamin gori baruwana" Dariya tashigayi tana fadin "Allah bazanyi na ainadena" Shima dariyar yashigayi yana fadin "Sedai suna aka canza miki" Yahada hancinsu guri guda yana kai bakinsa saman nata saboda tsananin kewar rashin kasancewa da ita jiya dabaiba, asafiyarnan duk seda ya fanshe.

Kallon ƙasar da mutumin yake nuna mata takeyi cike da kaduwa, kafin ta kalli mutumin tana fadin,

"Lallai ma yarinyar nan, abinda tayi kenan."

Yace, "Tabbas, da ace tayi amfani da maganin da, tini wata maganar ake ba wannan ba."

Sarauniya Hassana ta numfasa kafin tace, "Kenan tasan ba don in temake ta na bataba ina da wata manufa in ta sanar da shi, Yariman fa banason ƙarshe na ya zama irin na mai babban daki da 'yarta a cikin Nuristan, Malam, ka taimaka mini da duk abinda zesa ta rufe bakinta, kar ta fada ko ma a fasa auren baki ɗaya, tunda ita makira ce. Ta nuna mini zatai azahiri, amma ashe shegen wayo ne da ita."

Malamin dariya yay yana jan dogon chazbaharsa, cikin shigar kamala kamar na Allah yake fadin, "Azahiri da baki ma wahalar da kanki ba, domin a cikin taurarinsu duka da na duba, zeyi wuya a ce auren ya tabbata, kuma ze iya yiwuwa yatabbata din badai tabbas duka Kingani," ya shiga bubbuga mata ƙasa yana nuna mata wasu irin zane data kasa gane ma'anarsu. Tace, "Toh Malam, nidai kasan ba gane rubutunnan nake ba. Me hakan yake nufi?"

Yace, "Na duba taurarin sa, da mace daya tak ze zauna har ƙarshen rayuwarsa,akansa za'a fara sarauniya daya a NURISTAN,ze kafa tarihi wanda babu wanda yataba kafashi a NURISTAN Ba zai taba zama da mace biyu ba."

Wani irin zaro ido Sarauniya Hassana tai tana fadin, "Kamar yaya? Yanzu fa saura kwana ashirin daurin aurensa, kuma ban ga alamar akwai wanda ze dakatar da auren ba tunda suna son junansu."

Malam din yace, "Kingadai shekara da shekaru kina zuwa muyi miki duba, ban taba fada miki karya ba, ko? Kintaba jina nayi?"

Girgiza kai tai tace, "A'a Malam, amma dai kenan auren ba zai faru ba?"

Yace, "Ze iya faruwa ya aureta, amma ze rabu da waccan. Ko kuma ya aureta, ya rabu da ita."

Tace, "Ita taurarin yarinyar fa? Ka duba da kyau kuwa?"

Yace, "Naduba ananne, kuma nasamu amsar. Abinda nasamu anan, zata zama sarauniya. Sarauniya kuma me ƙarfi, wacce sai a shekara ɗari ake samun sarauniya mai ƙarfin ikonta a daular Musulunci. Kuma zata auri yarima, Amma rashin gano mana ainihin asalin sunan mahaifiyar yarinyar, yasanya bincikenmu yakasa gane yarimar wace ƙasa zata aura. Kinga, idan ya kasan ce Nuristan ne, tabbas yarima EHSAAS se ya rabu da matarsa ta fari. Saboda tauraron Mehtav yafi na matarsa ta fari haske, kuma zata fita da ɗaukaka da samun girmamawa a duniya baki ɗaya. Wannan kenan."

Waro ido Sarauniya Hassana tai, for the first time tana jin yau dai bata yarda da zancen tsohon malamin nata ba, saboda babu yadda za'ai duk wanda yaga azababbiyar soyayyar da EHSAAS da Islam sukeyi, yay tinanin zasu iya rabuwa.

"Toh kodai asiri Mehtav take mai ne?" taraya aranta da sauri tace, "Malam, yanzu zata auri EHSAAS kenan?"

Girgiza kai yay yace, "Ban ce miki sha zata aura ba, amma dai tabbas a cikin ƙaddarorin rayuwarta akwai ta zama sarauniya a daular Musulunci mafi shahara a duniya, wacce Nuristan na daya daga ciki. Kuma a cikin taurarin yarima, ba zai taba iya zama da mace biyu lokaci guda ba. Don haka mujira lokaci, muga abinda Allah zeyi."

Daga haka Malam yamike, da sauri tamike itama tana fadin,

"kuma bawani temako da zaka bani akan hakan don ni yanzun hankali na ma yatashi naji ita amaryar nafi tsanarta akan uwar gidan don haka kawai ahanata aurensa kota halin kaka," Malam yace "ba abinda zan iya yi akan yarima saboda tarin tsaron da yake kan yaronnan da aka kafeshi dashi duk wanda yace ze taba tohm ze kona rayuwar sane baki daya, dagashi har iyalinsa bazasu tabu ba lakanine suke dashi wanda Mai Martaba sarki EHSAAS nafarko shine kadai yasan makarinsa asiri becika cinsu ba,koyaci baya tasiri"

Dasauri yace "Ita yarinyar fa yace itama atsaye take da ibada amman zamu iya tasiri akanta idan har tayi amfani da abinda zanbayar kuma tanada wayo bazata taba yi ba sedai kuma wani ikon Allah,"

gaba daya hassana jitai kamar zata zare jin daukakar da Mehtav zata samu amman me komeye zatai se tayi tasa Mehtav tayi amfani da abinda malaminnan zebayar, tace "zuwa yaushe zaka bani abin malam zan kokarta zanyimata wata dabarar sannan naji ana kishin kishin din cewa matar sa tafari nada ciki kwanaki amman nidai nakwan biyu banganta ba shiyasa ban tabbatar ba kadubamin mezata haifa innamiji ne insan abinyi tun kan yazo duniya, don bazan cigaba da zama yar kallo ba" Dan kallon sama Malam yay kamar wani zararre kafin ya zauna akasan yashiga rubuce rubuce akasa ya dago straight yace mata "zubewa zeyi" kawai ya mike yawuce tunda taga yay haka kuma yana nufin yagama magana.

Don't forget to Like Share Comment Vote

To catch every new chapter as soon as I drop it, follow me on all my platforms: 📱 TikTok: @fatoumspassion 📸 Instagram: @fatima-rufai-nasidi 📖 Wattpad: @fatoumspassion 📚 Arewabook: @fatoumspassion 💬 WhatsApp: ***

If you don't have my number, save it and send me a message saying "saved", so I can save yours back and you'll always get my story alerts whenever I upload a new chapter [05/10, 18:07] Fatima Rufa'i Nasidi: ***

It's Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM and INTENSE LOVE.