EHSAAS

Chapter 63

by @fatoumspassion

Ahankali ta buɗe idanuwanta suka sauka akan EHSAAS da ke fitowa daga bathroom, da alamar wanka yayi, duk ga lemar ruwa a jikinsa. Daga shi sai farin towel ɗaya da ya daura saman kugunsa, yay sakwasako kamar zai faɗi. Huge cikakken faffadan kirjinsa a waje tare da murdaddun muscles dinsa. Tun da ya fito, idonta biyu suka tsaya kansa, sai dai ta yi pretending kamar barci take yi.

Ta shiga kare masa kallo yadda ruwan jikinsa yake bin six packs ɗin shafaffen cikinsa da ido, karasowa yay ya zauna gefen gadon yana murmushi. murmushin da ya bayyana kyawawan dimples dinsa. Ita fa, tun da take a duniya, bata taɓa ganin namiji da dimple ba sai akan shi. Kai, koda ta taɓa gani ma, tabbas bata taɓa ganin wanda ya yima kyau irin haka ba kamar EHSAAS.

Dan ruwan dake kansa ya shiga sauka a saman face ɗinta. Gently, ya shiga shafa face ɗinta yana faɗin, "Wake up, Amor, safiya yayi."

Rintse ido tayi tana murmushi ƙasa-ƙasa. Murmushin da taga shima yayi, yana faɗin, "Ki tashi ko na ɗaga ki yanzunnan."

Kafada ta makale masa, ido a rufe take faɗin, "Ni dai a'ah, let me sleep more."

Rikota yayi yana mannata a jikinsa, yana goga mata jikakken beard ɗinsa a fuskarta. Ta shiga kyalkyala dariya tana ƙoƙarin kwacewa tana faɗin, "Stop, Mi Amor! Zaka jikani fa! Sto…."

Sai dai dariyar da taji kamar ta su Abeey a kunnuwanta yasa ta buɗe idanuwanta cikin ɗan mamaki. Idonta sauka yayi akan Abeey, Falmatta da Sarah da ke ƙasan carpet suna breakfast suna kallonta suna dariya.

Ta tsaya tai turus tana karema dakin kallo gidansu ne! And all this while, she's just been sleeping and dreaming about him!

Abeey tace, "Wai me ze bari ne? Kin wani kankame pillow kina ta kiran sunan Mi Amor."

Suka ƙara kyalkyala dariya.

Sarah tace, "Kinga Abeey dinnan, za a yi kwalluwa. In kika girma ke me naki da abin da take a mafarki, eh?"

Da sauri Mehtav ta miƙe, duk kunya ta lullube ta. Falmatta ta kalla tana faɗin, "Jeki ce ma Aunty Ameerah ta tashi, don tun dazun take mana sintiri a kai tana duba ki wai zaku yi turare, kuma an ce ta tashe ki. Tace, 'abar ki ki huta sosai.' Duba time fa ƙarfe goma."

Abeey miƙewa tayi, ta cika Irish a bakinta, ta fice daga ɗakin don isar da sakon yayarta Falmatta.

Bathroom Mehtav ta nufa da sauri. Falmatta take faɗin, "Kin ma isa." Ta karasa tana shan gabanta tana fadin "makira se kin gaya mana jiya uban me ya saki a mota yanayi har na awa biyu? Ku ba ku zauna a event ba, kuma ku ba ku dawo gida ba. Na tabbata da ba dan kaninshi nan ya ganku ba, ai da zaku iya kwana a gefen titi nan, Kuka kori driver!"

Harara Mehtav ta watsa mata cikin wasa tana faɗin, "Sa ido sana'ar banza. Kuma ba zaki ji me muke ba, duk abinki…"

Sarah tace, "Falmatta, Mehtav fa bazata taɓa faɗa miki abin da fitinannen mijinta yake ba. Daga ita har shi, duk munafukai ne. Ahaka sumi-sumi kamar ba zasu aikata ba. Aini tun daga rawar nan natsinke da lamarin guy ɗinnan… hope dai baki sakar masa jiki tun kafin first night ya kwashi angwanci ba, don naga kanki yana rawa akan guy ɗinnan ki daibi a hankali."

Wata muguwar harara Mehtav ta watsa mata, ta buɗe toilet ta shiga tana kullewa. "Wai ta bi a hankali," tsaki kawai ta ja, ta shiga cire kayanta.

Ta tsaya ƙarƙashin shower ta saki ruwan dumi. Maganar Sarah ta so bata mata rai, amma tunawa da daren jiya sai ta saki wani murmushi na jin daɗi tana kankame hannayenta a kirjinta. She still feels his lips on top of hers. In ta rufe idonta, da kamshin da bakin nasa ke yi. His lips are the sweetest thing she ever tasted, tunda take a duniya, bata taɓa sanin kiss can be this long and sweet ba sai jiya.

Yayi kusan 20 minutes yana yi, she could still feel how he was breathing heavily a saman face ɗinta. How he removed her head and started feeling her hair texture don kitson da aka mata da alama ya shiga ransa sosai.

A kirjinsa ta kwanta na tsawon lokaci, yana shafa bayanta, kafin ya kare hade bakinsu guri guda. Babu inda bai yi kissing ba a face ɗinta kafin ya gangaro zuwa wuyanta.

Kallon madubin mirror ɗin tai ahankali, ta shiga shafa gurin da ya yi shedar hickey ɗin da ya mata last night har guda biyu. Ɗaya a saman boobs ɗinta bayan ya zuge mata riga, looking at her fresh virgin white boobs kamar ya cinye su ya huta. Ya daura lips ɗinsa a saman ɗaya dake cikin bra. He almost unhooked her bra. Ta raya a ranta tana lumshe ido, tana tuna yadda suka ji ana musu knocking, da yasa EHSAAS dole ya mayar mata da zip ɗinta yana gyara kwanciyarta a saman kirjinsa.

Tai luf kafin ya buɗe glass ɗin. Aman, shine mutum na ƙarshe da ya dawo daga gurin party. Ya shiga kallon EHSAAS kallo ɗaya ya yi ma Mehtav dake saman kirjinsa akwance, ya ɗauke kai yana faɗa ma EHSAAS, "It's late fa, you should get moving. An fara cigiyar yarinyar agida."

Jinjina kai kawai EHSAAS yayi, ya ɗau wayarsa ya yi texting driver ɗinsa ya dawo.

Har suka karasa gidansu Mehtav, bata wani iya motsin kirki a jikinsa. Sai da motar ta tsaya tukunna ta ɗago, tana ɗaukar head ɗinta. Lips dinsa ta kalla yayi wani mugun ja. Idonta a kansu, still feeling how they softly crashed into hers few minutes ago.

Tace, "Goodnight, Mi Amor."

Ta karasa bakin ƙofa zata buɗe, hannunsa ɗaya yasa ya dawo da ita baya. Ta faɗo saman kafafuwansa gently. Ya shiga rada mata yadda yake son ta, da wasu irin kalamai masu nauyi da kunnuwanta basu taɓa jin irinsu ba.

Kafin dai ya ɗan saketa a hankali, yana ƙara kissing lips ɗinta, ya buɗe mata ƙofa. Da kansa ta sauka, yana miƙa mata purse ɗinta. Da sauri ta karɓa tana gyara veil ɗinta saman kanta, ta shiga gidan a kunyace, kasa iya haɗa ido da Aunty Ameerah da ke tambayar ta, "Me suka tsaya yi? An ce tun dazun suka taho."

Ta kuma kasa bata amsa, examining ɗinta taga Aunty Ameerah ta fara yi cikin tuhuma tana ce mata, "Meya samu dan kwalinki?"

Da sauri ta shiga ce mata, "Fitsari nake ji."

Tana zurawa da gudu ta shiga ɗaki tana jin kirjinta na bugawa. Da sauri-da-sauri ta shiga toilet.

Ba irin tambayoyin da su Falmatta basu mata ba suma, amma haka ta yi musu banza bata basu amsa ba. Taji daɗi da Aunty Ameerah bata sake zuwa ɗakin da ta shiga ba don ta titsiyeta.

Shine yanzu daga tashinta zasu fara mata wata magana daban. Turo baki gaba tayi ta shiga amfani da sabulun da Aunty Ameerah ta haɗo mata na wanka. Kamshi sai tashi yake. Ta wanke jikinta tas, sannan tayi wankan tsarki ta fito sanye da katuwar bathrobe ɗin EHSAAS da ta mata yawa, don ta san idan ta saka towel zasu ga hickey ɗin da ya mata and she doesn't want that at any cost.

Abeey ce zaune a tsakiyarsu, tana karanta musu yadda cocktail ɗin jiya ya trending a social media. Duk social media platforms Instagram, X, TikTok sun cika da videos da hotunan cocktail ɗin jiya. Hashtags ne suke yawo iri-iri na EHSAAS da Mehtav, da captions kamar haka: "EHSAAS's gaze on Mehtav should be studied at Harvard." "The chemistry! The class! The chaos!"

Bloggers sun samu abin yi, duk wani blog me tashe da suna sun yi posting wedding ɗin nan saboda haduwar da EHSAAS da Mehtav suka yi, da romantic lines kamar haka: "He looked at her like he built her with his hands." "Abuja's eligible bachelors should officially resign."

Yan mata kuwa sun rikice; se comments suke, sun faɗi: "Who styles Mehtav? I need her designer!" "EHSAAS is officially the most handsome man in West Africa!"

Influencers kansu ba a barsu a baya ba, da wanda suka je bikin da wanda ba su je ba, duk sun ɗora clips na dance scene ɗinsu, da caption kamar: "When your man looks at you the way Prince EHSAAS looked at Mehtav."

Abuja girls dai suna cikin collective heartbreak. Some of them are happy for her; some of them kuma taciki na ciki. Don da yawa yawan yan makarantar su Mehtav da suke gaisawa ma basu san da maganar bikin ba kawai se gani suka yi yana yawo a social media. Hakan yasa duk wani group din Nile maganan aurenta ake, har da yan matan da suke cewa: "they've deleted all their boyfriend's pictures. After seeing EHSAAS, they can't unsee perfection." "I don't even want to get married again. What's the point? Tunda nasan I won't get a husband like this."

Abeey kasa karasa karanta comments section din tai saboda uban yawan sa, tashiga scrolling tana dariya. Sarah ma ta dakko wayarta tana faɗin, "Ke, kinga mutanen da sukai following ɗina kuwa? Sanadin bikin nan, lallai Mehtav kin kankaro mana capacity mutane ba tsoron Allah a ransu, sudai harka In dai ta masu hannu da shuni ne gulma ba ze barsu su zauna kalau ba; se sun ji kwakkwafi."

Abeey ganin Mehtav a tsaye tana kallonsa yasa ta karasa, tashiga nuna mata ita kanta kyan da sukai ya ba ta mamaki. Ta dan basar kamar irin bata ji daɗin nan ba kafin ta saki murmushi tana faɗin, "Kudai ringa haɗawa da addu'a In kuka kasa, saboda baki kada ya cinyemin mijina, haba, kwalelensu!" Duk aka sheke da dariya. Ta zira hijab dinta, tawuce dakin Paa, don anan ta ajiye duk wani kayayyaki nata masu mahimmanci tunda aka fara bikin.

Cikin mamaki take kallon Taj dake kashingide a daya daga cikin dogwayen kujerun dakin Paa. Tayi sallama amma da alama be ji ba, yayi nisa cikin tunani. Da ɗan mamaki take kallonshi, don kwata-kwata se yau take ganinsa a gidan. Karasawa tai tana leka fuskar sa; taga ba barci yake ba, idonshi biyu ceiling kawai yake kalla. Tai murmushi tana faɗin, "Tinanin me kake yi?" Tanufi closet din Paa, da ɗan mamaki yadaga ido yana kallonta kafin ya tashi zaune yana faɗin, "Amarya, amarya, amarya bakya laifi."

Dariya tashiga yi; yana jiyo muryarta a cikin closet din tana faɗin, "Ai nayi fushi wallahi shine se yau zakazo koh?" "Aikinsa yanayin aikin namune kanwata, musamman yanzun da na samu karin girma, ba ko yaushe nake samun damar hutu ba saboda ayyuka da sukai yawa a table dina." Ya bata amsa yana miƙewa; tana dudduba kayan nata, taji yashigo ya tsaya a bayanta yana faɗin, "Wai wankan inji kikayi ne? Yana ga kin wani ƙara kyau kamar yar tsana." Dariya tashiga yi tana faɗin, "Santi dai kawai kake yi, Taj." Ya girgiza kai yana faɗin, "I'm serious. Ko dai duk glowing din amarcin ne...Ainaga hotunan bikin jiya, nace Amman daga ke har EHSAAS ba ku da kirki Allah dakuka bari aka watsa wannan abin." da ɗan mamaki take faɗin, "Au, mu nema zamu bari a watsa? Kasan we can't control people on social media. Ni wallahi ban ma san wanda ya fara daura wa ba; don ni dai ba yawuna akai Kuma shima banjin ya sani." Girgiza kai Taj yayi yana faɗin, "Amman you can control yourselves. Ko musamman shi ji wani yadda ya kafe ki da ido kamar tsohon maye, waishi dan soyayya."

Mehtav kicin-kicin tai da fuska tana faɗin, "Haba, yah Taj, me kuma ya yi maka? In ce kunyi sorting out differences ɗin dake tsakaninku." Yace, "Eh, mun yi. Amman dan yasa baki an karamin girma yamin alheri hakan ba yana nufin zai yi abu ba daidai ba. In kauda kai bawan Allah nan yasan cewa bake kadai ce matarsa ba. Ai, at least he should have self control. Shi yasa nace mai yarinyar nan Islam doesn't deserve someone like him. Allah, yarinya ga kyau, ga nutsuwa, uwa uba ga halacci. Ni wallahi in ze saketa zan aureta, saboda jinta nake a raina kamar wata yar uwata, wallahi."

Mehtav tace, "Wallahi karka bari ya jika! he can kill you for that furuci, ka san yadda yake sonta kuwa. Kuma kaima ai abin da ka faɗa yanzun be dace ba tunda ka san matar wani ce." Yace, "After abin da ya yi matannan Allah danice ita ko shine autan maza a duniya, na gama zama da shi; ke kuma se wani rawar kai kike yi. Za'a aure ki ana jidake ke gaki amarya tohm, kisani Hausawa nace wa bulalar da aka doki uwar gida da ita, aje zuwan wataran da ita za'a sake dukan amarya."

Turo mai baki tashiga yi tana faɗin, "You won't understand alakarmu, baka je NURISTAN bane, Shi yasa ya Taj amma ni bama zan iya karawa da Islam a zuciyarsa ba, Bafa ka ga yadda yake ji da ita ba, nima ya sha min wulakanci iri-iri akanta. Kawai dai baka gani bane, kuma ni da ita we are like sisters. Yanzu na tabbata wadannan videos ɗin ko ta gani ba za su wani ɗameta ba saboda ta san kowa da lokacinsa. Yanzu nawane ai itama tayi nata."

Taj yacije baki yana faɗin, "Allah, Mehtav. Ko da wasa naji kin shiga gidan nan, kintayar ma yarinyar nan fitina, se nazo har NURISTAN din na ciro ki domin alamu duk sun nuna ke ce fitinanniyar daga maganganunki." Dariya tafarayi tana fitowa daga closet din bayan ta dakko kayanta. Take faɗin, "Wai nice yar uwarka ko Islam ni na ji ƙoƙari, Allah ka fitar da su nan ta a bakin ki. In mijinta yaji baruwana, kuma ni ba wata fitina da zanyi, Abu ɗaya nasani shine I will make sure na mallaki mijina a tafin hannuna ta hanyar kyautata masa da yi masa biyayya. Baruwana da matarsa tsakaninina da ita mutunci da girmama juna. Duk wanda ya iya allonsa ya wanke ya sha." Ta karasa bakin ƙofar tana kallonsa.

"Ka yi ma breakfast tukunna?" Girgiza mata kai yayi yana faɗin, "Banjima fa da sauka ba, kuma mota na biyo, shi yasa a gajiye nake." Ta ce, "Yah Taj, mota ana zaune kalau, Aikam dole ka gaji, bari na saka Sarah takawo ma abinci." Da sauri yace, "No, ba Sarah zaki saba, Falmatta tafita, nutsuwa ita za ki turo min" dariya tafarayi tana faɗin, "Yah Taj, ko dai, ko dai." Yace, "Kefa, kin fi ya fassara,tafi ki ban guri." Dariya tashiga yi, ta wuce dakinsu.

Tasanar musu, aiga Taj yazo Sarah da rawar kai ta mike wai zata je tagaida shi, Mehtav tashiga dariya tana faɗin, "Abin da yake hada ki da shi kenan, beson rawar kai yanzun ya gama ce min wai in sa Falmatta ta kawo mai abinci, beson Sarah saboda Falmatta tafita nutsuwa." Dariya duk suka fara wa Sarah tace, "Aiko, seta rama tunda ita yayi ma haka."

Aunty Ameerah ce ta leko, tana ce ma Mehtav, "Maza tashirya anyi waya surukanta sun kusa isowa."

safiyar ranar da jirgin Nuristan Royal Jet ya sauka a Nnamdi Azikiwe International Airport, komai a Abuja ya tsaya cak har ta da kai komo na ababen hawa dakatar da shi akai na ɗan lokaci, umarnine daga federal government sabili da karrama zuwan sarkin NURISTAN. Security vehicles da motorcade mai royal emblem suka cika tarmac ɗin.

Mai Martaba da Queen Fulani ne suka fara fitowa cikin nutsuwa. Se Sarauniya Hassana da su Mother Fariha, harda su maman Maisoon tawagar su guda. Abuja sun riga sun shirya musu red-carpet reception a Royal Diplomatic Villa, Asokoro villa da aka tsara musamman don zuwan su.

Wajen ya cika da fresh white roses, gold drapes, da flag na Nigeria and Nuristan suna reto tare a sararin samaniya. Duk yadda Paa ya so a bari ya sauke su, amma gwamnati ta riga da ta karbi bakuncin Mai Martaba; don haka dole ya hakura. Shi da EHSAAS da wasu daga cikin kawunnan Mehtav suka je har airport ɗin suka dakko su suka kai su masaukin da gwamnatin ta tanadar musu.

Tun sassafe, dama yasa Inna da su Aunty Ameerah su yi girkuna na alfarma saboda asauki bakin nashi da shi. Mai Martaba be wani jima a villa ɗin ba - wanka kawai sukayi suka sake shiri. Shi da iyalansa na kusa-kusa suka wuce gidan Paa, akabar sauran anan villa, ciki kuwa harda maman Maisoon. Abin be mata daɗi ba sam ganin antafi da Hassana an bar ta, amma aje zuwa, ai gobe dai daurin auren; duk tsiya ba za a hana ta zuwa ba.

Aman ne ya jasu amota, EHSAAS na gaba. Fulani da Mai Martaba a baya.

Mai Martaba ya ɗanyi gyara murya yana kallon EHSAAS kafin yace, "Yarima, inmun fito daga gidan surukanka tare da kai zamu karbi bakuncin shugaban kasa in sha Allah, ka ji ko?"

Jinjina kai EHSAAS yayi yana faɗin, "Tohm, Allah ya temakeka, Allah yakaimu"

"I hope I'm not disturbing your Abuja honeymoon with the internet." Mai Martaba ya faɗa yana kallon titi kamar ba shine yau ba. Da sauri EHSAAS ya juya ya ɗan kalle mgnr ba dariya yay kaɗan, yana lumshe ido. "Ranka ya dade, you've seen it too?"

"Who hasn't?" Ya faɗa. Yayin da suka haɗa ido, da sauri EHSAAS ya ɗauke nashi saboda kunyarsa da ta lullube shi.

Aman dariya ce take cinsa ganin yadda aka kama EHSAAS right-handed, gashi sun sashi amota babu hanyar tserewa. Fulani ta ja numfashi ta ce, "Babana, ba iya mu kaɗai muka gani ba. The whole world did."

EHSAAS ya kasa cewa komai. Shi kansa be ɗauka haka yan Nigeria suke da saurin yada abubuwa ba. Yamanta shaf ba'a NURISTAN yake ba; kowa yasan dokar gidansu ba a ɗaukar su a dora a social media. Giyar soyayya ya ɗabe shi; gashinan shi da matarsa suna yawo a internet tako ina, kuma yanzun ko saukewa akace za'a yi, ya riga ya ga yaduwa wasu sun ɗauka.

Mai Martaba ya ɗanyi gyaran murya yana faɗin, "Even the elders in council sent me screenshots. What exactly are you trying to prove, my son?"

EHSAAS ya dafe goshi da hannu ɗaya. Beyi tsammanin koda yagani da safe wannan video zai tsallaka har NURISTAN ba, Gently yake faɗin, "Ayi hakuri, ranka ya dade. Ban ɗauka abin zai kai haka ba. It was just a cocktail, no intention to make noise."

Mai Martaba ya ce, "Cocktail? Ka san matsayinka kuwa, you are the crown prince. You think royal blood drinks without ripples?"

Jin Mai Martaba kamar ya ɗan ɗau zafi ya sa Fulani ta ƙarɓe zancen, cike da nutsuwa. Ta shiga faɗin, "Babana, katuna duniya tana kallon ku,kaida Mehtav ba kamar sauran mutane ba. Even your smile carries the palace seal."

Jinjina kai EHSAAS yayi yana faɗin, "Na sani, Maama. Amma it was an innocent night. I wanted her to feel celebrated, to see how proud I am of her. Nothing happened beyond that."

Ajiyar zuciya Mai Martaba ya yi, cikin sigar nasiha yake faɗin "Love is not the problem, son. Public display is. There is a thin line between affection and spectacle."

EHSAAS shiru ya yi; ya kasa magana don ya san ba shi da kalaman da za su kare kansa a gaban Mai Martaba.

"When your people see you in love, they should feel inspired, not entertained. Do you understand?" Mai Martaba ya ƙara nanata masa. Jinjina kai EHSAAS ya yi, idonsa a ƙasa. Aman kam murmushi yake yi kasa-kasa, don shima rawar kan EHSAAS din akan Mehtav har mamaki take ba shi.

"Ba kace ka gane ba?" Mai Martaba ya faɗa yana murmushi wannan karon: "I understand. Allah ya temakeka," ya faɗa cikin ladabi.

Ta madubi suka ga Mai Martaba ya yi leaning close to Fulani yana mata rada a ƙunne, waida sunan rada amma duk sun ji. "Fulani ta kìnga danki koh? Ni ya gada agurin iya soyayya, amma ki fahimtar da shi soyayyar sirri tafi daɗi, kamar dai irin tamu."

Ba Fulani ba shi kansa EHSAAS da Aman wata irin ƙunyarce ta kama su; duk sun ji meyace din. Aman har da ɗan tarin ƙarya wai don yasan suna fa motar basu fita ba.

Fulani blushing tai, ta matsa gefe daga jikinsa, ta kalli EHSAAS dake kallon titi ta ce, "Babana, I saw the videos. You looked happy. That's what matters. But next time, keep your happiness sacred. It's more powerful when the world can only guess."

EHSAAS murmushi yayi yana faɗin, "In sha Allah, Mama. I'll be more careful."

Fulani ta ce, "Good. Islam was quiet through it all. Learn from her grace. Dazun munyi waya amma kwata-kwata ko maganar ba ta mini."

Shiru EHSAAS yayi; se yanzun hankalinsa ya kai kan consequences ɗin yada hotunan nasu. Tabbas, indai su Mai Martaba dasuke NURISTAN sun gani, babu abin da ze hana Islam dake Greece gani. Yashiga uku ya faɗa kirjinsa na dukan tara-tara. Yau tace mai zasu je can wani Ireland abayan gari tun safe hakanne yasa ma ya samu text kawai ya mata sanda ya tashi da safe sanin tana tare da family dinta be wani takura mata. Amma kuma bata mai reply ɗin message ɗin ba sosai ya sha jin jikinsa, ko dai ta ganine yasa yashiga tambayar kansa.

Sosai yaji kirjinsa yayi nauyi saboda bai son hurting dinta. Fulani tace sun yi waya bata ce masa komaiba; ya san kuma koda tagani ba zata ce mata kome ba, saboda ita ba mace ce mai yawan kai ƙarar mijinta. She don't complain much. Idan kaji ta bude baki tayi magana tohm abu ya ci turane. Yasan indai har ta gani, kulle kanta zata yi a daki tayi kuka. Bai son kukannan musamman a halin da take ciki yanzun. Wayarsa ya ciro yana kallon number ɗinta; yashiga kira gently amma bata shiga, is switched off sosai yaji damuwa ta dabaibayeshi.

Muryar Mai Martaba da yake tambayar Aman, shi yaushe zai fito da matar ya yi aure ta katse shi daga kara sake kiranta; a ransa yace, "I'll call her later in sun dawo daga Ireland ɗin."

Aman yace, "Aini, Allah ya temake ka, kai ne zaka yimin komai, harda matar ma kai zaka bani." Murmushi Mai Martaba yayi, yace, "Kaddai kayi irin ta o'o in daddage in za ba maka ka dawo daga baya kace bakasan zancen ba." Duk dariya suka yi suna kallon EHSAAS da hankalinsa baya kan hirar tasu gaba ɗaya yay kan Islam.

Daidai sanda suka karya kwanar street ɗin su Mehtav.

Tun daga ƙofar layin su Mehtav, convoy ɗin motoci suka cika har ƙarshe, ga jiniyar motar jami'an tsaro tako ina. Hakan ne ya tabbatar ma da su Mehtav su Mai Martaba sun karaso. Gate ɗin gidan aka buɗe, motar Mai Martaba da ta su Sarauniya Hassana ce kaɗai ta shigo, sauran duk suka tsaya a waje tare da security.

Karɓar girmamawa na gaske su Paa suka yi musu a babban falon Paa ɗin, duk suka zauna aka sake gaisawa, ana yi musu "ya hanya", amsawa aka yi kafin a buɗe guri da addu'a. Suna kammalawa, Fulani ta ba da umarnin a shigo da kayan auren Mehtav da suka taho da su.

Kayan lefene dozen uku aka riƙa shigowa da su cikin falon, ba masaka tsinke, har sai da aka shiga kwashe wasu ana kaiwa ciki sannan. Bayan da aka gama shigar da su, kowa se sambarka yake, ana mata addu'ar Allah ya sanya alheri.

Aunty Ameerah ce ta fito musu da Mehtav, dake cikin wata tsadaddiyar customized lifaya haɗaddiya, an nade mata jikinta da shi, fuskarta a rufe. Aka karasa da ita har gaban Mai Martaba, ta durƙusa tana gaishe shi. Amsawa yayi, ya dafa kanta yana mata addu'a. Sai ga Abeey nan ta shigo, ta karasa bata kula kowa ba, sai gun Mai Martaba ta tafi ta zauna tana gaidashi.

Amsawa yayi yana faɗin, "Abeeda, ai na ɗauka dake za'a je a taro ni daga airport?"

Murmushi tayi tana ce masa, "Ai Paa ne ya gudu ya barni, amma ta mai masauki a ɗakinsu, ai shima ya basu masauki mai kyau sanda suka je gidansa. Itama yanzun zata bar masa ɗakinsu shi shi kaɗai duka."

Kowa a falon se da yayi dariya jin shirmen Abeey ɗin. Ta kalli Mehtav da tayi ƙasa da kanta, idonta a lullube, tace a buɗe mata fuska. Girgiza kai Fulani tayi tana faɗin, "Ai ba'a buɗe ma amarya fuska sai Mai Martaba ya biya ko."

Jinjina kai Abeey tayi tana faɗin, "Mai Martaba, nawa zaka biya?" tana kallonshi. Ita ko irin jin tsoron nan babu a tare da ita wai taga babban mutum. Hakan yayi nuni da kalar sakar mata fuskar da yake da sabon da suka yi a NURISTAN.

Yace, "Amman dai za a min ɗan sauƙi ko?" Dariya duk akayi. Tace, "Ba laifi, ai kaine da dai Prince ne, ba zan masa sauƙi ba." Ta faɗa tana karema falon kallo, ganin bata ganshi ba tace, "Ina yake wai?"

Mai Martaba yace mata, "Tare suka zo, sai dai in a waje ya tsaya."

Nan danan Mai Martaba yasa aka gabatar mata da kyautar wata dankareriyar sarkar gwal ta asalin gidan sarautar NURISTAN, mai ɗauke da tambarin ƙasar. Sarkar wuyace da ta hannu, harda na ƙafa, da ɗan kunnaye da abin kai. Kowa se kallon sarkar yake, don kana gani kasan zata yi mugun nauyi.

'Yan uwa da abokan arziki ma suka shiga loda kyaututtuka iri-iri a gaban Mehtav ɗin, harka ake yi kawai ta girmamawa a wajen Aunty Ameerah tashiga tunanin wane kalar tukuici zasu bawa waɗannan mutanen, saboda duk abinda suka kawo sun riga sun fi ƙarfin sa. Shiga gida tayi suka soma shawara da Inna kan abinda zasu ba su.

Sun jima ana bawa Mehtav kyaututtuka. Sarauniya Hassana se zare ido take ganin Fulani bata ajiye tata kyautar ba, sai can da aka gama taga Fulani ta mike tsaye ta kamo Mehtav ta zaunar da ita tsakankanin ita da Abeey dake kusa da Mai Martaba.

Ta ciro awarwaran, ita ba wai don komai take so ta bawa Mehtav awarwaran ba, sai don tunawa da surukarta uwar soro. Tasan da ace tana raye dole zata so Mehtav ma ta mallaki wannan awarwaran. Tana zira mata, Sarauniya Hassana ta wani lumshe ido tana murmushi, tana jin mission dinta is accomplished.

Jin da Paa yayi Mai Martaba yace daga nan villa zasu tafi, ya sanya aka yi musu packaging abinciccikan dana gargajiya da na zamani, ga drinks kala-kala da aka haɗa musu da na kanti ma, duk da aka siya masu shegen tsada. Mota guda aka yi musu ta abincin da zasu tafi da shi. Sannan Aunty Ameerah ta bawa Fulani kyautar turarrukan wuta da na jiki, kaya guda aka kai musu mota.

Tukuicin miliyan goma Paa yaje ya bawa Aman duk yadda Mai Martaba ya hana shi. Amma kin hanuwa yayi yace, "Indai basu karɓa ba, ya fahimci tohm rainawa sukai." Badon Aman ya so ba haka ya amsa. Ya sa kuɗin raw cash a bayan motarsu.

Sai da suka fito aka fara cigiyar EHSAAS, wanda tun da yazo ya shige can garden ɗin gidan, yana ta sake trying number ɗin Islam baya shiga. Kiran da Aman yayi masa ne ya sa ya fito harabar gidan, yaga duk an fito shi ake jira. Sallama yayiwa Paa, ko ciki bai shiga ba suka wuce suka tafi zuwa villa direct.

Gidan su Mehtav kuwa, kacamewa yayi, Duk rashin kin son gulma irin ta 'yan street ɗinsu Mehtav, haka aka riƙa shigowa saboda ba wanda bai ji zuwan manyan mutanen gidan Habib Bai ba. Lefen aka buɗe a tsakiyar falon aka shiga kallo.

'Yan mata zasu fara ɗauka a waya, Aunty Ameerah ta hana su. Tace taga alamar basu da hankali. Su ko gudun bakin jama'a basayi. Duk wacce taga ta ɗauka se ta fasa wayarta. Sunsan zata aikata hakan yasa kowacce ta ajiye wayarta.

Aka shiga kallo, ana santi. Kwata-kwata babu ordinary kaya a ciki, duk designers ne da limited editions da customized ones da aka yi just for her.

Akwatin jewelry kuwa kwata-kwata babu ordinary sarka, gwala-gwalai ne da diamonds ake ta ɗagawa ana kirgawa. Ganin haka yasa inna ta ɗauke akwatin ta kai can ɗakin Paa, ta datso ta saka masa key. Sauran kayan ma huɗu tana yi tace, "Kallon ya isa haka."

Ta saka su Falmata suka haɗe komai inda yake suka mayar ɗakin Paa, duk aka kullesu.

Masu tafi kwalliya duk suka wuce saboda grand dinner ɗin da za ayi yau ɗin, don yau kowa yana son ya bazama a capacity.

Mehtav tun dasu EHSAAS suka tafi, ta ɗau waya ta shiga kiransa. Dagawa yayi lokacin suna mota tare da Mai Martaba. Yace mata zasu je wani unguwa ne, he will call her later.

Haka kawai setaji ta hassala. Dan me yasa ko tsayawa yaji, me zatace beyiba? Yafara wani cemata zeje unguwa, ina ruwanta da unguwarsa? Ba dai ta sake kiransa ba; kawai tashiga tube lafayar jikinta tana kunkuni. Tanajin su Falmata sun shigo ana labarin kayan nata, amma setaji duk batta zumudin abin kamar da can. Kwanciya tai, zata fara barci, Aunty Ameerah tazo tatasheta suka shiga dakin Inna tana mata final gyaran jiki don daga yau, shikenan.

Gaba ɗaya fuskarta annurinta ya ɗauke. Ita kanta Aunty Ameerah seda tai mamaki Mehtav da duk abinda kashafa mata, seta tambayeka meye shi, me kuma yake? Rayawa tai aranta tace, kodai jikinta ne yay sanyi ganin dagaske zata bar gidansu.

Suna gamawa aka fara kiran sallar La'asar. Tashiga toilet tai wanka kamar yadda Hajiya Ameerah ta umarceta; ba ordinary wanka taiba, wankatai da wasu irin ruwan turare da sabulai masu kamshi, kafin nan tadauraye jikinta da ruwa, tadauro alwala tafito. Aunty Ameerah tafita tace tai sallah taci abinci, tara na tafe kada tazo basu gama ba.

Kinyin sallar tai; taji batason tai sallar gaba ɗaya. tai kwanciyar ta saman gadon har sanda Aunty Ameerah tadawo dakin da wasu farfesun zabi da akai mata na musamman, akasa magunguna aciki da uban romo. Tadire tana kallon yadda tai daidai a saman gado.

"Meye haka nake gani, Mehtav?"

Takalleta, takalli inda ta ajiye mata sallaya da hijabi, ko tabawa batai ba. Tace da girmanki, "Kalli fa lokaci, biyar saura yanzun. Sena maimaita miki kiyi sallah."

Mikewa Mehtav tai tana hade rai. "Yanzun fa zanyi." Tadau hijab din tana hawa saman sallayar. Aunty Ameerah tarike baki tana fadin, "Toh halin da banaki ba, karki fara aure zakiyi fa, wataranuwa zaki zama, Kina wasa da sallah akan lokaci, tohm da wane bakin zaki tarbiyyar yara kice suyi?"

Tanaji Aunty Ameerah nata mita haka ta tada sallah, don jitai kawai yau batason yin sallar. Bata tabajin haka ba tunda take a rayuwarta, se yau. Itakanta mamakin kanta takeyi. Haka tai sallar rabi tinani.

Aunty Ameerah bata bar dakin ba seda ta tabbatar ta idar da sallar. Ta tura mata ferfesun tace, "Kuma indawo in tarar da kwano kinji ko?"

Jinjina mata kai kawai tai. Tana fita taja ferfesun, don daman yunwa takeji, tun breakfast bata iyacin komaiba. Tashiga ci abinta har Aunty Ameerah tadawo, bata gama ba, tafara mita saboda tara mai kwalliyar ta iso tana dakinsu tana jiranta.

Ahaka Mehtav tagama, tadau plate, tawuce takai kitchen, tadawo. Seda tai fitsari tasake alwala kamar yadda Aunty Ameerah ta umarceta, tadawo tazauna aka fara mata kwalliya.

Babyu abinda take tinani aranta se, tohm inane unguwar da EHSAAS yatafi? Bini-bini tana kallon wayarta, koya kirata taga be kiraba, kawai tashiga yin kwafa tana hade rai. Harta da tara seda ta lura yau mood din Mehtav din is somehow not good, shiyasa tai kaffa-kaffa kar tai offending dinta.

Se kusan Isha suka gama kwalliyar. Zuwa lokacin, yanmatan duk sun fara dawowa daga nasu gidan kwalliyar; kowa yashirya cikin ashobe dinsu na shimmering lilic lace, hadadde gaske, don tare za'a daukesu duka da bridesmaid dinta zuwa gurin dinner din da za'ayi a Hilton.

Fadar irin kyan da Mehtav tai bata baki ne saboda wata iriyar hadaddiyar modest gown akai mata daga Aragon Haute Couture a Boston. Nicky Aragon ce da kanta tazana rigar akayi mata. Duk da sau daya tak tataba ganin Nicky din tareda mijinta a Saudiyya, da sukaje Umrah, amma ana kwatanta mata Nicky din ita ta ganeta tai mata fitting din daidai jikinta.

Ta tabbata da ba don Paa yasan mijinta ba, don kusan suna bashi kwangilolin gine-ginen kamfanoninsu, da bama zata samu Nicky tamata dinkin cikin kurarren lokacin da aka shirya na bikinsu ba saboda long waitlist din da take dashi suna jira.

She's one of the iconic fashion designers da ake damawa dasu a duniya baki ɗaya yanzun indai modest dress ne.

Margenta pink colour ne dress ɗin, hakanne yasa ya haska kyakkyawar farar fatar ta. tunkan tafito Ita kanta mai kwalliyar se santin kyawun da Mehtav tai tana takeyi.

Karfe takwas daidai EHSAAS ya aiko da convoy ɗin motocin da zasu ɗibe 'yan uwan Mehtav baki ɗaya, ga motocin da Paa ma yasa aka kawo iri-iri na 'yan'yan abokansa, duk suka ringa ɗibar jama'a har da su Nura. Taj ne ya tsaya a gidan seda ya tabbata da kowa ya samu yashiga mota sun tafi, sannan yashigo yana kallon Aunty Ameerah da amarya yana tambayarta lokaci yana ja, "In EHSAAS ɗin bezo ba, ita tafarayin gaba mana."

Dan jim Aunty Ameerah tayi kafin tace "ta kirashi Yanzu beyi picking ba, amma yana hanya." Basu jima ba sega motarsa ta karaso. Kiran Mehtav yayi, batai picking ba; kawai ta nuna ma Aunty Ameerah, itace ta taimaka mata da dogon takalminta. Suka fito harabar gidan, Taj yana rike mata net din kayan da yake jan kasa.

Aman ne yau yake tuka mai motar, don EHSAAS daga gaba yafito wani irin fitinannen kyau yay don yau kayan Hausawa sak yasaka; farin dakakken yadi ne tsadadde, yakafa hula yakawo ta 90%. Zaka rantse daman can yasaba sakawa. Yajingina da mota yana kallonta, yana dan murmushi, trying hard yaboye damuwar rashin samun wayar Islam da beyi ba, kasan ranshi.

Har gabansa aka tsayar da ita, idonta a ƙasa, tama ki yarda su haɗa ido da shi. Hannayenta yakama, yabude bayan motar, ya zirata yana dan murza hannun cikin nashi. Da sauri yaga tazare hannun tana kallon can gefe, alamar bata so. Aunty Ameerah ce tai musu bye bye. Tashiga motar Taj, don tare zasu tafi. Dan su Abeey Tuni duk suka yi gaba da su Inna.

Seda motar Taj tafara fita kafin Aman yay ma tasu key, yasoma fita a gate din gidan. Matsawa kusa da ita yayi yana kallonta, ya lumshe ido.

Yace, "Yan mata na is epitome of beauty," yana leka fuskarta, data kauda kai kamar bataji meyace ba. Ranta kamar abace yake abinda yay noticing kenan. Dan murmushi yay yana tunanin, tohm ko abinda yay jiya ne yabata mata rai? Amman kuma ai jiyan bata nuna mai haka ba.

Hannunta yakama yana haɗewa da nashi. Cikin dan mamaki yake kallon awarwaran hannayenta irin na Islam Sak awarwaron nan yasha tsokanarta dashi yana cemai "awarwaron gado," saboda bata bari a cire mata wai Fulani tace mata ba a cirewa heritage ne na kakannin kakanninsu.

Yace, "Is just awarwaro, nothing more. Islam, kicire mana, ga sabo nasiyo maki." Duk sanda yafadi haka seta make mai kafada, wai itadai yabar mata wannan, tafison shi. Yay ta tsokanar ta yana cemata "awarwaron gado," don har wanka dashi takeyi wani lokacin.

Ganin an bawa Mehtav ma, yashiga dariya yana kokarin cirewa a hannun, yake fadin, "Kema wannan tsohon awarwaron gadon suka baki koh?" Da sauri ta amshe hannayenta tana fadin, "Don't take it off, Maama ce tabani."

Yace, "Ainasani, but this bangle is outdated. Kicire mana, inkawo maki wani nagaji da ganin sa."

Turo mai baki tai tana kallon titi tace mai, "A'a."

Aman duk yana kallonsu ta mirror. Juyowa da fuskarta EHSAAS yay, yana karema make-up ɗin nata kallo kafin idonshi yasauka a bakinta.

Yace, "Amor, menayi ne haka? Ake fushi dani?"

Girgiza masa kai tai alamar ba komai, don ita kanta bata san menene yay mata takamame ba.

Yace, "Is it the kiss that offended you?"

Da sauri takalleshi, se kuma takalli Aman dake gaban motar, ta girgiza kai.

Yace, "This lip painting da aka miki is dangerously cute, adan rage mana. Kar kisa na maimaita abinda yafaru jiya kinga I lose control, I don't wanna do that again."

Make mai kafada tai tana dan tureshi a jikinta. "Karka batamin kwalliya," tafada tana kallon gefen titi.

"Okay," yafada yana jan wayarsa shima gefe daya, tasan kuma zuciya yayi. Yacigaba da kiran wayar Islam, wannan karon tana shiga amman bata picking.

Mehtav ganin yamata banza yasa tashiga kallonshi ta gefen ido irin danme ze barta tafison yayta lallabata, tana leka screen din wayarsa. Sunan da yay saving dashi tagane Islam ce. Jitai ranta yasoso gaba daya. Yau big day ɗinta ma he's calling his wife, kuma ma yasan ranta abace yake maimakon ya bada hankali ya rarrasheta se yashiga kiran matarsa amman dai Ba dai tace komai ba.

Tana gani, yazira wayar tashi a aljihu, shima yana kallon titi har suka karaso Transcorp Hilton.

jama'a sun cika harabar wajen taf ana jiran zuwan ango da amarya,ga convoy din Rolls-Royce na royal family atsaye alayi, security sun zagaye gurin akwai kuma nasirri wanda suka fara maganin paparazzi masu daukar hotuna suna yadawa a social media, Wajen a cike yake makil da manyan mutane, ministers, royal delegates, business moguls, fashion icons, duk sun hallara suna jiran fitowar amarya da ango.

Motarsu na tsayawa awurin, Red carpet aka shimfida tun daga entrance har zuwa babban ballroom ɗin da aka yi decoration da royal gold and white theme chandeliers masu kyalli suna haskawa kamar wasu taurari asararin samaniya, Gaba ɗaya wajen ya sha kyau, flowers da crystal vases se walwali suke, live band na tashi ahankali yana busa soft northern instrumentals.

Aman ne ya fara fitowa da farko, kafin bodyguard ya budewa su EHSAAS bayan motar yana kamewa,

Shine yafara fitowa daga cikin black Maybach ɗin, Traditional northern outfit ɗin da ya saka yawani mugun hawa jikinsa kai se ka rantse daman can yana sawa white babbar riga da richly embroidered silver cap sun zauna a jikinsa kamar an dinka jikinsa. expression dinsa nayau din is very serious amma full of class.

Juyawa yay yamika mata hannu ahankali takama hannayen nasa tafito da long fishtail gown ɗinta mai margenta pink da silver stones yana ƙara bayyana kyawunta. Official royal photographer din da suka daukane kadai ya tsaya yana musu hoto hannun shi cikin nata se ganan su Abeey da sauran bridesmaids duk cikin shimmering lilac lace sun fito sun zagayesu anata yaban yadda sukai kyau.

EHSAAS nema yadaure yake dan musu murmushi amman Mehtav ko alamar fara'a babu a fuskarta ganin haka yasa aunty Ameerah ta karɓi hannun Mehtav daga cikin na EHSAAS, tana murmushi take fadin "Ango adan bani aronta minti guda"

Murmushi kawai yay ya jinjina mata kai alamar ba matsala gefe tajata tashiga rada mata magana kunne "meye haka takeyi se wani daddaure fuska take, me aka mata ko EHSAAS dinne yabata mata rai?" girgiza kai ta shigayi hawaye na taruwa a idonta aunty Ameerah cikin lallabi take fadin "imma fada kukai bazaki iya fadamin ba don Allah kiyi hakuri kisaki ranki kinga dai taronnan muntara manyan mutane babanki yana nan duk yan uwansa suma suna nan, gidan sarautane Abu daya zakiyi ashiga fassara ki Mehtav ki nutsu kisaki fuskar ki yau rana daya ce dabazaki taba iya sake maimaitata arayuwarki ba"

dan jinjina kai tai aunty Ameerah tasa wani brush tana dan gyara mata gefen fuskarta, Tana murmushi cikin sigar cheering dinta off tace "you look like a princess truly, EHSAAS is a lucky man."

Tafada tana kallon direction din EHSAAS wanda ke tsaye tareda Aman suna magana kasa kasa shima, Abeey ce takaraso tana tambayar auntyn "me akama yah Mehtav dinta be?" aunty tace "bakomai suje sujeru kamar yadda aka tsara yanzun zasu shiga da amarya" jinjina kai Abeey tai tatafi tana sanarwa dasu sarah dagudu.

EHSAAS dake tsaye yana cema Aman "ya samu baban Islam din awaya?" ya girgiza mai kai alamar a'ah wayar dake jikinsa ce yaji tana vibrating daidai yana hango Mehtav da auntyn ta sun tsaya a red carpet din alamar shi suke jira, nufar gurin yay yana ciro wayar daga aljihunsa ganin Islam ce yasa yay saurin kallon Mehtav yaga itama direction dinshi take kalla alamar shi suke jira ya kuma kallan caller ID din kawai seya juya ya dan ja gefe yana picking call din,

"Hello Islam ina kika shigane? inata neman wayarki bana samu, baby are you okay? ya tambaya cikeda zallar kauna da kulawa Voice ɗinta da ya fito a phone is raw, cracking "Sire… I'm bleeding… I don't know… I feel the baby....." Kasa karasawa tai hakanne yasa hankalin EHSAAS yatashi, Jiyay kamar duk hayaniyar gurin an dauketa babu abinda yake saurare se maraitaccen kukanta dake tashi tacikin wayar tana kiran sunan shi, Take idanuwansa suka kada sukai jajir kamar garwashi kamar anzare mai dukkanin wani farinciki arayuwarsa muryarsa tana rawa yashiga tambayar ta "Islam Where are you?Meyasameki ki? Where are your parents" Jiyay numfashi ta na rawa kamar ma bata cikin hayyacinta take fadin

"they are.....not..here, I'm all alone here… I woke up and it started… it's coming out… I can't breathe… I'm scared…" takarasa fada cikin kuka mai tsanani, "I think I'm losing the baby."

Daidai nan wayar ta katse arikice EHSAAS yashiga kokarin sake kira tanata ringing ba'a dagawa, Mehtav kirjinta taji yana bugawa ganin his just focus akan wayarsa yanata dannawa yana karawa akunnansa, ta lura da sudden change a yanayinshi kamar ma hannunsa rawa yake yi, Aman ma ganin haka yakarasa yana tambayar sa "lpy? Is he okay?" Dasauri yadago Cikin bada order yake fadin "call Abraham Zion right now," "Islam is not okay she's losing the baby am heading to Santorini right now," dasauri yay gaba, Aman ya rikoshi yana kallon Mehtav dake tsaye saman red carpet tana jiransa yake fadin "comeback uncle prince,look at that girl she's waiting for you all the people inside are here because of you and her tayaya zaka tafi kabarta ita kadai I'll go to Santorini myself I'll take good care of her pls," girgiza kai EHSAAS ya shigayi yacire hannunsa ana Aman yana fadin "this is Islam we are talking about, she's there suffering and you are expecting to enjoy this wedding are you high Aman, if something happened to her I won't forgive myself,that girl is my whole life" yafada yana nufar mota bayan ya zaro key din daga aljihun Aman.

Mehtav dataga kamar tafiya zeyi da sauri tajuya tana kallonshi har ya bude mota yashiga se kuma taga ya fito yanufo inda take, curving face dinta yayi yana kallon cikin idanuwanta da kwalla ta taru alamar kiris take jira tafashe da kuka yay kissing forehead dinta yana fadin

"I'm so sorry please, I need to be somewhere else, you can get started don't wait for me" Yana karasa fadin haka ya saketa yawuce cikin mota yay mata key,kafin tace uffan yabar harabar gurin @360 duk jama'ar gurin suka bishi dakallo, Aman mota ya karba shima yabi bayansa don baze taba iya barinsa yay tafiya shishi kadai ahalin dayake ciki ba.

Mehtav saboda tsabar shock da confusion din data shiga har ya bace bata dena kallon inda motar daya hau tabi ba.

Aunty Ameerah ce ta matso kusa da ita cikin son kwantar ma da Mehtav din hankali dukda itama ba karamin mamakin abinda EHSAAS din yayi taiba tashiga cemata, "Don't worry Mehtav, maybe urgent royal call ne. Yana dawowa soon."

Wani irin abu taji ya tokare mata akirji har lokacin idonta nakan hanyar da EHSAAS yabi, Aunty Ameerah tace "dinner nawa akai ba ango ko yazo daga baya karki damu kinji Mehtav kisaki ranki don't cry pls kinga muntara jama'a agurinnan karsu fahimci akwai matsala tsakaninku"

Jinjina kai kawai tai tana kallon kofar ball room din inda katon screen din wurin ke showcasing "Royal Wedding Dinner,Prince EHSAAS & Mehtav" tambayar kanta dalilin tafiyarsa tai amman duk wani uzuri na duniya data nemo tabashi se taga be cancanta ba,kamar bazata iyamai kowana uzuri ba ayau dinnan,

Abeey ce tasake fitowa daga corridor din wurin don bridesmaid sun shirya duka anata jira amman shiru ganin bataga EHSAAS ba yasa tashiga tambayar Mehtav "yah Mehtav, what's wrong? What happened? Ina prince din yake kufa aketa jira"

"My phone" tafada tana bude purse dinta dasauri,tashiga kiransa amman baya dagawa duk kuwa da tanata ringing. gps tasoma duba location dinsa nantake yanuna mata hanyar Nnamdi Azikiwe International Airport.

Hannunta saki yayi, phone ɗin ta kusa faɗuwa. "He left…?" tafada tana kallon Abeey dake kallonta itama cikeda mamakin jin abinda tace din, Abeey tace "but why yah Mehtav,?" Girgiza kai tai kawai tana fadin "Call yah Taj for me, let's go inside together,"

Dasauri Abeey tawuce takira Taj aciki wanda ya biyota jin tace "Mehtav na nemansa is emergency,"

"Meya faru Mehtav are you okay"

kanta tadan rike jin wani irin mugun ciwo daya farayi tace mai "tell the bridesmaids to just go inside differently zanshiga tareda kai da Abeey," cikeda confusion yake tambayar "why shi ina prince din?" girgiza kai tai tana fadin "he left I don't know where he is?" Taj ganin kamar Mehtav is on the edge zata iya breaking down awurin yasa be tsaurara tambayar ba ya aika Abeey ta sanar da sakon Mehtav aikuwa nan danan aka saka musu wakar dasukai practicing suka shiga da ita.

Seda suka shiga sannan taj ya zagaya hannayensa cikin nata Abeey agaba da flowers ahannayenta suka shiga cikin ballroom din, tanajin yadda zuciyarta ke wani tafasa ko iya daga ido takalli tarin jama'ar dake gurin bata yi,biki yayi guri ya hadu iya haduwa, sukansu yan uwan EHSAAS sunyi mamakin rashin ganinsa se daga baya jalila tazo ta sanar asanarwa da al'ummar daya gayyata wani emergency issue ne ya tashi yasa EHSAAS baze zoba.

Aikuwa nan danan aka shiga mai fatan alheri kadan ne suka ringa gutsiri tsoma amman yawanci dayake jiya anganshi ba'a wani damu ba din, tunda ga wakilansa duk agurin ciki kuwa harda Fulani hajar,wacca itace ta kira Aman ta tambayeshi bayan taga Mehtav tashigo da yayanta nan yake sanar mata "su yanzun ma Santorini zasu wuce Islam ce ba lfy" sosai itama hankalinta ya tashi amman se tace mai "shi yadawo yabar EHSAAS yaje shikadai ai baze yiwu ayi taron auren EHSAAS bashi ba EHSAAS ba" ba don yasoba yana kallo EHSAAS yashige jirgi yatafi Santorini akabarshi a Abuja.

shine Fulani tasaka jalila ta sanarma da MC din don kar wanda sukazo donshi suyita jira suna zuba ido.

Da yake bikin da manya sosai ba'a wani kai can dare ba bridesmaid dai da groomsmen sune sukai enjoying bikin to the fullest don amarya sau daya tafito fili tana komawa tace acewa MC kada ya sake kiranta kanta ciwo yake aiko ana tashi Taj ya saka ta amota suka nufo hanya tun ahanya tacire eyelashes din idanuwanta tashiga kuka kamar ranta zefita.

Abeey ma duk jikinta yay sanyi tana bata hakuri don su uku suka taho, Taj cikanki bece mata ba, tayi kaca kaca da fuskar tata ta dame make up din.

sune suka fara komawa gida hakanne yasa tai gudu tawuce sashen Paa. abandakin falonshi ta wanke fuskarta tas tana kallon yadda bakin liner yasa idonta yay mugun duhu saboda da ruwa ta wanke bada wipes ba,takara fashewa da kuka tazube akasan bandakin tana watsar da gwala gwalan wiyanta akasan gurin, kawai jitake she hate EHSAAS irin immense hatred dinnan dan meyasa ze tafi yabarta, Takai kusan minti ashirin awurin tana kuka.

kwankwasa mata kofa taji anyi tana kuka kamar ranta zefita "Mehtav open the door, Mehtav I said open the door" tajiyo muryar Taj yana fada yana bubbuga kofar, "go away I don't want to talk to you,"

"Mehtav idan baki bude kofar nanba nashigo sena bata miki rai bazaki bude ba," "Noooo I don't want to" tafasa kara tana sakarma kanta shower daman rikar jikinta kadai ta rage tacire mayafin da head din, "zan balla kofar inbaki fitoba,inshigo in mammareki ina miki wasane?" jin muryarsa his super serious tasan kuma ze iyayi yasa takarasa ahankali tabude kofar tana labewa bakin kofa.

hannu yasa ya zarota tatsaya agabanshi har tsakiyar kanta yana gani da yasha kananun kitso yay mugun kyau kanta akasa tana kuka habarta ya riko yana kallon yadda fuskarta tai looking abin tsoro kamar zombie tayi jajir ga bakin daya zagaye mata ido, "you look ugly when crying kukan nameye uhm?" Kara fashe mai da kuka tai tana kankameshi tashiga fadin "I hate EHSAAS, I won't marry him he left me, ina gani yaringa kiranta awaya amota bamata picking and and...."

tafada kamar zararriya tana dagowa daga jikinsa "she then finally called him I'm sure she is the one that called him......" Lebenta har rawa yake tsabar bacin rai da radadin datake ji akirjinta take fadin "bansan me tace mai ba he then left me,he left me on my own, I'm I not important to him I'm I that easy to throw away" tashiga nuna kanta tana fadin "I won't be his second best anymore I won't marry him, nafasa auren I want my own husband alone I don't want to share my man"

tashiga girgiza kai tana nufar cikin dakin tana diga,rikota yay karta batawa Paa farin carpet dinsa da ruwa yace "come here ya jinginar da ita da jikin bango yana fadin "he has a strong reason to leave yanzun na gama waya da Aman, his wife just miscarried their child did you expect him to be here with you itakuma tana can tana suffering,"

kura mai ido tai kamar meson fahimtar me yake cewa sai kuma tai saurin girgiza kai tana turashi baya, cikin daga murya take fadin "and is it my fault tai miscarrying child din nata, don't she have parent's I thought she's with her parents, why out of all people seta kirashi tasan he can't say no to her, bayan tasan this is our big day ni dashi we were happy, just doing well here,but one call from her ta fashe da kuka she ruined everything, everything Taj she did it on purpose" takarasa fada tana zubewa akasa, "And why would she do that Taj" ya tambaya cikeda mamakin gurguntaccen tinani irin na Mehtav. tace "to gain his attention mana saboda batason ya aureni" dariya taji Taj yanayi kafin yace "when did you become a selfish ass Mehtav come in stop over acting, inace dazunnan da safe kika gama fadamin kowa ya iya allonshi ya wanke yasha,kuma keda ita are like sisters, tohm kodai tafiki iya allonne inma abinda kike fada gaskiyane kema sekiyi abinda ze dawo da attention dinshi gurinki ke kinsan your not strong enough kika yarda kika amince zaki aurar mata mijin uhm, abeg my friend get up my friend kije kicire kayannan kiyi wanka ki sauya wasu kafin raina yabaci inbi ta kanki inkarya"

ya fada da authoritative voice din da yasa Mehtav mikewa dasauri tai kofa bata yarda tahada ido da yan uwansu dake falon ba duk sun dawo anata ture ture.

tashige daki takulle tafada toilet wanka tai tanajin auren EHSAAS gaba daya yagama fita aranta, tana fitowa tazira kayan barcinta. aunty Ameerah ce tashigo mata da abinci saboda kowa yaci abinci gun dinner ita kadaice bata ciba dakyar ta lallabata taci kadan itama tana bata baki tace "kiyi hakuri tunda ance abin lafiyane yasa yatafi kamata ma yayi ki kirashi kiji koya isa lafiya yajikin matartashin?" kallon aunty Ameerah kawai takeyi irin bamata da hankalinnan itace zata kirashi yatafi ya barta ya tozartata shine har take cewa takira aiko za'a mutu ba'a kirashi ba tashiga rayawa aranta. plate din kawai ta dauka tanufi kitchen dashi taje ta dire, tanufi dakin Paa cikin sa'a kuwa ta tarar dashi yadawo shida Taj suna cin abinci suma basu wani ci gurin dinner dinba. mamaki ne ya kamata jin Paa yana tambayar kota samu EHSAAS awaya ya jikin Islam din? karasawa tai ta zauna agefensa tai shiru se hawaye shaaa hannu yamika mata alamar tazo dasauri tamike tahau kujerar da yake kai ta rungumeshi tana fashe mai da wani irin maraitaccen kuka tashiga cemai "ita batason auren tafasa auren EHSAAS,ace musu tafasa dan Allah kar adaura aurennan in aka daura aurennan mutuwa zatayi," Paa kusan sandarewa yay yana sauraron abinda Mehtav din ke fada kuma yaji kamar ba wasa atareda ita bilhakki da gaskiya take fadin batason nashi.

dagota yay daga jikinshi yana tambayar ta "yamiki wani abunne dakika fasa, akwai wani abinda yake miki ko halinshi wanda bansani ba kika gane?" girgiza kai tashigayi tana fadin "ai bayasona yafi daukar matarsa da mahimmanci he left me today for her, Paa he will do it again I'm very sure, dan haka nafasa nizan auri koma waye amman ba EHSAAS ba pls papa" takarasa fada tana kankame hannayensa nisawa yay kafin yashiga shafa kanta yana fadin "amman I just heard cewar matarshi miscarried their child bazaki masa uzuri ba" turo baki tai cike da shagwaba tana goge hawayen dayake biyo kuncinta tashiga fadin "ai is not a good reason Paa tana Greece yana Nigeria meye zemata naga dai tana gurin iyayenta su meye amfaninsu" kallonta kawai Paa yake don yasan wannan ba kalaman yarshi bane ba his daughter isn't this heartless, amman dai cikin lallabi ganin gobe zasu rabu bayason su rabu bata dadin raiba ya shiga mata explaining yace "danshine fa suka rasa Mehtav kamar ni ace narasa ki ko Abeey se kuma intsaya dinner din aurena" dan jim tai kafin tace "aimu munzo duniya shida ko duniyar be mazo ba balle asoshi," jinjina kai Paa yay kafin yace "aahhh lallai Mehtav yau na tabbatar bakida hankali, mani kike fadama baza'a soshi ba sbd shiba dabane kenan, ku kune yaya toh tashi kibarmin falona da maganar banzannan kona fasa miki bakinki kaganmin shashashar yarinya" fashewa dakuka tai tana dada makale mai Taj cikin tsawa yake fadin "ke ba dake akeba uban wa zaki mayar kananun mutane, bake kikace kina sonshi ba, tashi kifita awurinnan kafin nai ball dake kuma naji kinkara fadar kinfasa auren EHSAAS Allah se ranki ya mugun baci aure ba fashi gobe iwal haka da igiyar sa uku akanki bi iznillah," wani irin takaici taji yatsaya mata ganin the only people da take da tabbacin will always support her decision no matter what sunki fahimtarta. dasauri tamike tafara baya da baya tana fadin "indai suka aura mata EHSAAS she can kill him saboda ta tsaneshi kuma bazata zauna dashi ba ko kuma takashe kanta kafin ai auren" takarasa fada tana ficewa afalon Paa rike kansa yay yana fadin "Taj kaji abinda Mehtav dina take fada Mehtav dinace wannan kuwa" dasauri Taj yakarasa yana dafa kafafuwan Paa yashiga kwantar masa da hankali yana cemai "karya damu shi zeyi maganinta yarinta ne kawai da kishi ke dawainiya da ita he'll take care of her."

Mehtav na komawa daki ta kulle ita kadai kosu Abeey dasuke kwana tare bugun duniya taki budewa ta zauna taci uban kukanta takoshi, daga karshe tajawo waya tashiga rubutawa EHSAAS text message me zafi kancewar "tunda yatafi yabarta yazabi matarshi akanta don haka itama she won't choose him tafasa aurensa kuma idan yasake ya matsa seya aureta seta kashe shi takashe kanta ta tsanesa bata tabajin wanda tafi tsana aduniya kamarsa ba."

har barci ya saceta anan kasan carpet din dakin,makara tai yau donko sallar asubah bataiba se karfe takwas shima kuma bugun kofarta da aunty Ameerah ta ringayi yasa tabude kofar ganin ko sallar bataiba yasa aunty Ameerah ta tasa keyarta tashiga tadaura alwala tai sallah tana idarwa tamiko mata hijab mai kyau se tashin kamshi yakeyi cikin hijabanta ne taciro mata tace "maza tasaka ga iyayen mijinta can afalo sunzo bata hakuri saboda sakon data tura nafasa aurensa ya isa garesu" aunty Ameerah takarasa sanar da ita cikeda mamaki ita kanta tayi mamakin abinda Mehtav din ta aikata don ayadda taga tana rawar kafar auren EHSAAS bata tsammanin koshine yace yafasa aurenta zata hakura amman ace lokaci daya yarinya ta birkice sosai tasha jinin jikinta.

Gashi yau su Mai Martaba suka musu dirar bazata da sassafe wai EHSAAS ya kira uwar don yanata kiran wayar Mehtav bata shiga don immediately tana tura mai text message ta kasheta wai tace tafasa aurensa ta temaka ta lallabamai ita he didn't do it on purpose shima.

har zasu fita aunty Ameerah ta rikota tana fadin "kika sake kika wulakanta mu agaban manyan mutanen nan wllh munsa kafar wando daya dake, ji yadda iyayen yaronnan kesanki dashi kansa yaron Allah kika rabu dashi Mehtav bazaki taba samun miji kamar shiba har abada" turawa aunty Ameerah baki ta shigayi alamar babu maganar ta daya data shiga cikin kanta.

suka nufi cikin dakin kanta akasa don mugun kwarjini mai Martaba da Fulani suke mata zata zauna akasa Fulani ta rikota tazauna agefenta tana fadin "zauna gefena diyata muda mukazo da kokon barar ban hakuri ayafemana aimu zamu durkusa" dukda tadanji kunyar Fulani yadarsu acikin zuciyarta amman setaji sam bata karaya ba tana kan bakanta akan cewa bazata auri EHSAAS ba.

Tana daga kanta suka hada ido da Paa da taga yana mata wani mugun kallo cikeda bacin rai,don ya dauka tun yamata magana asashensa mgnr tamutu har abada ashe seda taturama EHSAAS sako don batada hankali.

Mai Martaba ne yay gyaran murya gefensa Malam liman da turaki da asafiyar sukazo don daurin auren. suka bude taron da addu'a Mai Martaba yace "diyata naji ance keda mutumin naki kunsamu sabani harkince bakyayin auren wai da gaske ne?" Ba tareda tadaga kai takalli kowa afalon ba ta jinjina kai, Paa yace "Mehtav are you high" zefara fada dasauri Mai Martaba ya daga mai hannu alamar ya saurara mai yay shiru Mai Martaba yace "diyata ina me miko kokon barar ban hakuri dukda bansan meya aikata ba banason hukuncin daza'ai masa ya shafemu kinga alakarnan ba iya ku tashafa ba tamuce gaba daya muna murna munsamu diya sukutum, asassauta masa badan halinsa ba ayi auren inyaso se aimai kowana irin hukunci daga baya kinga yanzun daurin auren saura awa biyu duka duka, gashi mun gayyaci al umma daga garuruwa da kasashe dabam daban" shiru tai batace kalaba, Taj yace "ba magana ake miki bane ba,"

se asannan tadago tashiga kallon fuskokin mutanen dake falon daya bayan idonta ya sauka akan Aman dake watsa mata harara kana kallonshi kasan dole akaimai yazo gurin itama hararar tashi tai tana juyawa suka hada ido da Paa, da yake kallonta shima, Fulani ta tabata tana fadin "don't be scared kifadi ra'ayin ki bame miki dole anan," dasauri tafashe da kuka tana rungume Fulani tace "nidai naji bana sonshi kawai indai aka auramin shi mutuwa zanyi,kawai naji natsani EHSAAS banason shi, don Allah kurufamin asiri koma waye ku auramin amman banda EHSAAS,"

Taj ne yamike gadan gadan yay kanta ze cafkota yadan bubbugeta aniyarsa kota dawo hayyacinta dasauri Mai Martaba yace "karka tabata kaji tajuddeen kada ka kuskura kataba min diya," yakalli Paa yana fadin "don Allah kayi hakuri engr kabar yarinya tunda dama ba wanda yaymata dole da farko yanzun ma kuma bame mata dole ahakura da auren kawai gaba daya,"

Paa dagowa yay yana kallonshi jin me yake cewa yasan kuma in aka fasa aurennan se yafi affecting mai Martaba da image dinsa fiyeda shi tunda shimai Martaba ne da iyalinsa public figures bashi ba, "Mai kake cewane Allah ya temakeka tayaya za'a biye ta hukuncin wannan yarinyar da batasan metake fadaba bansan meya canza mata ra'ayi ba ranka ya dade Mehtav koda bataso nace shinake so ayi zata amsa amman bansan a ina takoyo wannan taurin kan ba" yafada yana girgiza kai, itakuma tayi luf jikin Fulani tanajin kome za'a mata bazata taba yarda ta amince ta auri EHSAAS ba, Mai Martaba yace "Mehtav yata yaki zonan kusa dani" Fulani ce tadagota ahankali tamike takarasa ta xauna kasan kujerar da mai Martaba yake kai gefensa turaki da Mal liman daya zubama Mehtav ido suna hada ido tai kasa dakanta Mal liman kallonta kawai ya shigayi kafin yace ma Mai Martaba "kuyi mata yadda takeso kawai" yana rada mai wani abu akunnensa murmushi suka ga Mai Martaba yayi yace mata "kince mu aura miki koma waye amman banda yarima ko" jinjina kai tai ba tareda tayi magana ba, yace "tohm jeki mun miki zabin miji kuma tunda ke kika bamu wuka da nama muna fatan zaki karba hannu bibbiyu," "zan karba in sha Allah" tafada ciki ciki tana goge hawayen dake fitowa a idonta, "tohm jeki cewar Malam liman, Kiyi kwalliya kishirya don yau daurin aurenki babu abinda za'a fasa angon kawai aka sauya kamar yadda kika bukata" jinjina kai tai tamike tafice afalon Paa kawai yatsaya yana kallon Mai Martaba da Malam liman da suka shiga tattaunawa kasa kasa kafin yakalli Paa yace mai "ya same shi amota insun fita kafin suwuce central mosque" inda daman nanne Venue din daurin auren, Aman kallon Taj yayi cikeda daurewar kai yake tambayar sa "ko Mehtav tana shaye shayene aboye basu sani ba"

It's fatoumspassion EHSAAS Don't forget to Share Like Comment Vote. [10/10, 21:18] Fatima Rufa'i Nasidi: Not edited It's Fatoum's Passion - EHSAAS Another exclusive piece from the passionate writer of AYSAM